gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading KELTOUMA Tafiyar Kaddara By takori kabara Chapter 14 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na tsinci kaina a wulakantacciyar rayuwar da ban taba mafarki ba."

"Wata irin bahaguwar rayuwa ake yi kamar ta dabbobi a sansanin nan na  yan gudun hijira, ma ana babu tsari na addini ko na zamantakewa, babu bin doka ko kiyaye lokutan ibada, wato salloli biyar na farilla, mafi yawan  yan gudun hijira basa kula da yinsu. Ba a maganar tsafta, irinsu wanka da wanki."

Abinda  yan gudun hijira suka fi maida hankali akai shine isowar tallafi daga hannun kungiyoyin NGOs ko idan kusoshin gwamnati ko masu kudin kasar da suka dubi Allah ko don siyasarsu sun kawo ziyara da tallafin

"kayan abinci, magunguna, ko na amfani irinsu gidan sauro, sanitary kits da sauransu."

"A duk lokacin da aka samu wannan tallafin nan zaka ga warwaso da danniya, mai karfi ko mai sa a ko mai uwa a gindin murhu cikin ma aikatan da hukuma ta ajiye mana ya samu, irina da diyata Keltouma kuwa da bamu da karfin komai, bamu kuma da kowa a sansanin sai Allah muna gefe hannu Rabbana a hannun Rabbi."

Duk zafi duk sanyi a kasa muke kwana haka duk Sauron duniya a jikinmu yake hutawa da daddare.

"Taimako daya Allah yayi mana shine da ya kasance lokacin bana damuna bane, da ko dukan ruwa kadai ya ishemu kamuwa da masassara."

"Shikuwa zazzabin cizon sauro ya zame mana jiki. Ya zo ya tafi, ba tareda mun ko sha masa maganin komai ba."

"Abinda na kara lura dashi shine akwai azzalumai da yawa a camp wadanda suke amfani da karfi kafin su bada necessities din. Shiyasa duk bukatuwarmu da net (gidan sauro) nace mu hakura da zuwa karbowa a ofishin ma aikatan, don na fahimci irin"

kazantar da akeyi a sansanin da yara

 yammata kanana.

Su kuma mazan yawanci babu Allah a ransu abinda ake aikatawa babu dadin fada.

"Sabanin ni da ko fitsari Keltouma zata je hankalina baya taba kwanciya in barta ta tafi ita kadai saina rakata, na kuma tsaya a kofar bayan gidan na jirata ta kammala, na kamo hannunta mun dawo muhallinmu tare."

"Watakila wannan kaffa-kaffan dana ke yi da rayuwar Keltouma shiyasa sauran matan sansanin da ma mazan duka suka ki jini na, suka tsangwameni."

Yau kusan watanninmu na hudu kenan a wannan sansanin. Bakin ciki da bacin rai yazo ya hadu da rashin wanka da wanki da cizon sauro.

Na tabbata ganin kaifin idona da ake yi dake yiwa kowa kallon barazana akan diyata da kaffa-kaffan da nake yi da ita ne yasa babu wanda ya kula sha aninta cikin lalatattun mazan da har kwartanci suke da matan mutane a wurin.

"Rayuwar zaman IDP Camp bana yima koda makiyina fatanta. Bana tausayin kaina kamar yadda nake tausayama Keltouma,"

musamman idan na tashi cikin dare na kalleta tana firgita a cikin barcinta.

"Ni Nana Aicha kullum ina rokon Allah ya karbi shahadar Monsour, ina gayawa Allah kukana kan ya kula dani da marainiyata, a ko ina muka tsinci kanmu a gaba Allah ya kular min da al amarinta."

"Kullum addu ata kenan. Dare da rana yini da safiya, har Keltouma ta hardace addu oina domin kullum a fili nake yinsu."

"Na kan mance da kaina a addu ar, kullum dai ita nake yiwa, da marigayin mahaifinta."

"Kwana nake a kanta ina tofa mata addu a cikin dare idan tana kiran sunan mahaifinta cikin firgita, sai dana dage da yi mata tofi kullum sannan ta dan fara samun yin barci cikin nutsuwa."

"Ummami tace  burina a yanzu shine kawai mu samu hanyar da zamu koma Arlit, rabona da gida tun aurena da mahaifinta, da tahowarmu ci-rani kasar Najeriya, ban sani ba ko har yanzu akwai wasu cikin dangina kona mahaifinta da suka saura a raye? Ko sun tashi daga inda na barsu? Ko za a samu wasunsu a wurin?"

"Rashin wannan tabbacin yasa na sakama sarautar Allah ido na zabi zamanmu anan sansanin, muna hannun Allah, naki yarda in biyewa rigimar Keltouma dake son mu bar zaman sansani mu shiga cikin gari muyi bara."

Ummami ta yi ajiyar zuciya kafin tace.

" To kaji Dana Yassar, wannan shine tarihin rayuwarmu nida marainiyar diyata  Keltouma ."

**** **** ****

"Mr. Yassar Jalloh, tuki yake cikin Hilux dinsu cikin wata irin nutsuwa yau, ya samu nutsuwa kwarai da yaji tarihin Ummami da asalinsu, akan hanyarsa ta komawa masaukinsa a Gusau daga Anka, duk tunaninsa ya koma na yadda zai yi ya taimaki Ummami, ya cika mata burinta na komawa kasarsu."

"Sai ya tuna cewa shima ba zamansa kenan a garin Anka ba, zai koma gida ne cikin nasa ahalin shima, da zarar ya kammala project dinsa."

"Barci ya gagari idanun Mr. Yassar a daren yau, ya kwana tunanin yadda zai samar musu mafita, da yadda zai taimaka don inganta rayuwarsu, ta yadda koda ya maida su kasarsu Arlit, to ya zama suna da abunda zasu iya rike kansu. Ko sana a ko aiki ko aure. Sai ya tuna Keltouma din makarantar allo da firamare kawai akace tayi, wane irin aiki zai iya samo mata?"

Itama uwar wace sana a ce ta dace da ita a halin yanzu?

"Haka ya karar da daren cikin tunani akansu, da makomar rayuwarsu, amma har akayi kiran assalatu bai samo solution din da yaga zai dace ba, sai da aka kira sallar Asubahi ya tashi don yin sallah, kafatanin daren yau kona minti daya Yassar bai runtsa ba saboda Ummami da  yarta, ya kasa yanke shawarar abinda ya kamata yayi musu kwakkwara har lokacin guda daya."

"Wayewar garin ranar da safe da ya iso garin Anka, ko Camp bai fara shiga ba, kai tsaye wurinsu ya fara zartowa a asibiti, don dasu ya kwana dasu ya tashi a ransa."

"Yau Dr. ya tabbatar masa ya sallamesu, bayan shimfido masa ka idoji na yadda za a kiyaye lafiyar Keltouma, yace lallai Keltouma ta cigaba da samun abinci akai-akai, mai lafiya da gina jiki, banda zama da yunwa, in ba haka ba ciwon na iya tashi ya murkusheta kowanne lokaci."

"To bayan ya gama magana da Dr. Kazim ya karbo takardar sallama sai ya nufo dakin nasu da niyyar gayawa Ummami yau dai likita ya sallamesu, su hada dukkan kayansu zai maida su Camp."

"Cikin uzuri na sauri yake don yanaso da ya ajiyesu a camp ya dauki hanya ya wuce Sokoto, Babansa babba wato Alhaji Abdulkadir tun jiya yake kiransa kan yana son ganinsa seriously."

"Mr. Yassar ya fio daga ofishin likita a hanyarsa ta zuwa dakinsu Keltouma, tun daga nesa yake jiyo tashin sheshshekar kukan Keltouma, rabonta da kuka yana jin tun kafin ta kwanta ciwo, amma yau kuka take kamar na fitar rai, tsananin dake cikin sautin wannan kukan nata ya sha bamban dana kullum."

"Zuciyarsa ta doka ta sake dokawa& . Saboda yau Keltouma ba kukan shagwaba take yi ba, kuka take kamar na neman ceto."

"Wato tana yin kukanta ne bilhaqqi (daga baka har zuci), kukan fita yake tun daga kasan zuciyarta, bana sakalcin nata bane ko shagwaba na neman tsira ne& & "

Kuka take da sauti mai ban tausayi mai

nuna hakikanin maraicinta& .

"Tana kukan ne don son tursasa Ummami ta bi ra ayinta na (kada su koma IDP Camp) amma Ummami yau ta nuna itace UWA! Keltouma  yarta, dole tayi mata biyayya, ta tsaya kyam! Ta kafe akan ra ayinta itama, ta daure ta shanye tausayinta na uwa taki bari kukan na Keltouma yayi tasiri a tareda ita shiyasa ko tanka mata taki yi."

 Akoke sai fatan Allah ya shirya!

Tunda mai hali baya fasa halinsa.

Inji zuciyar Mr. Yassar.

Yana mai kara sauri don isa dakin Akoke. Wani irin suka zazzakar muryar

"kukan nata take yi a kirjinsa, daidai saitin zuciyarsa, jikinsa har  yar kyarma ya dauka, tsigar jikinsa na tashi. Ya rasa kowanne irin tasiri kukan yarinyar nan yake dashi a kansa."

Daidai lokacin yayi tozali da Keltouma ta hada kai da guiwa a dandaryar kasa kusa da kafafun mahaifiyarta tana rera mata kuka mai ban tausayi.

"Wannan shi ake kira  kukan mace a kunnen namijin da ya riga ya kamu da ciwon So& Long time ago& , ba tareda shi kansa ya sani ba."

"Wanda da ace Keltouma wata babbar mace ce mai wayewar kai, sai ace kukan kissa takeyi da gayya da jin tahowarsa, kuka irin na motsa zuciyar namijin da aka san already yana cikin wani hali na kaka-nikayin soyayya mai girma da azabtarwa akanta& ."

"Yassar ya shigo dakin da wata shaqaqqiyar sallama daga maqogwaronsa, sannan jikinsa na dan kyarma na rikicewa da daburcewa ya rufe kofar, ya juyo ya nuna ta da yatsa a matukar hassale. Amma me? Sai ga sautinsa ya makale, daga bisani ya fito a"

"tausashe, a lokacin ya buda baki da kyar cikin karkarwar murya yace."

 Um-ma& mi! .

"Sai kuma muryarsa ta sarke, harshensa ya sarke, ya kasa karasawa don wani sabon nauyin Ummami daya zo farat daya yau ya saukar masa. Saboda kwayar idanunsa sun kasa boye halin da zuciyarsa ke ciki, jikinsa har bari yake cikin jin azabar soyayyah& .."

"Ummami ta gama gane Mr. Yassar tunda jimawa baya son jin kukan Keltouma ko kadan, amma bata kawo komai ranta akan hakan ba, da zai iya da ya gaya mata cewa kukan Keltouma rikitashi yake yi ya daburta shi, ya luguiguita zuciyarsa, ya tabo can wani sako dake kwance kasan ransa kamar fami akan na ciwo tsahon lokaci."

"Don haka duk da ya kasa furta abinda yake son furtawa a take Ummami ta gane korafi yake so zaiyi, ko nuna bacin ransa akan kukan, ganin girmanta da idanunsa keyi yasa ya kasa yin magana."

"Sai tayi murmushinta na kamala, da hausarta irinta  yan koyo tace."

" Kayi hankuri Mallam Muhammadu Yassar! Hakurin kawai zan iya cewa kayi, kuma tunda nace kayi shi na san ba a kyauta maka bane. Bansan yaushe Keltouma zata girma ba ."

"Yace  ina! Ai na gama hakurinnan da ita daga yau Ummami, saboda kunnena bai jure jin kukanta, zuciyata take azabtarmin& . tana yi min mummunan fami akan ciwo na& . Ai kawai Ummami ki kauda kai, ki barni na saka kafar wando daya da Akokenki saboda tana son kasheni da raina."

"Banda sakalci da shagwaba bata san komai ba, ta yaya yarinya mai shekaru irin nata da hakora 32 zata cinye rayuwarta a koke-koke, kamar wata mage ko  yar jinjira sabuwar haihuwa? "

"Maganarsa ta karshe ta baiwa Ummami dariya, yayin da ta farkon ta jefa mata waswasi, shakku da jin nauyinsa. Yassar yace."

" Har can waje fa ana jiyo ihunta Ummami. Wallahi saura kadan na fadi dana dumfaro dakinnan na jiyo tahin sautin kukanta, saboda yadda gabana ya fadi, na"

dauka wani abu ne ya faru na tashin hankali. Me aka yi mata haka saboda Allah?

"Ummami sai tayi dan murmushi ta sunkuyar da kai cikin kokarin maida nata hawayen, ta rasa amsar baima Mr. Yassar, bazai gane damuwar Keltouma ba har yanzu, tunda shi ba a camp yake kwana ba, kuma bai rasa gatansa ta ko ina ba."

Su yanzu yaya sunan makomar rayuwarsu?

Ma ana meye future dinsu idan suka cigaba da rayuwa a sansanin  yan gudun hijira?

Meye amfanin zamansu a kasar Najeriya ma gabadaya?

"Babu shakka a wulakance a Camp zasuyi ta zama har illah masha Allah in suka cigaba da zaman sansani, kamar Keltoumah ta fita gaskiya, tunda dai baza a dawo musu da Monsour ba, gatansu shine komawa kasarsu kawai amma ba shiga cikin gari yin bara"

"yadda Keltouma ke so ba, tunda babu Monsour da yayi silar zaman Najeriya, kuma babu wani mahaluki da zaiyi jihadin maidasu cikin ahalinsu. Sannan bata da ko sisi a hannunta."

"Tayi kuskuren rashin tambayar Monsour tun yana raye ina danginsu suke zaune yanzu, don bayan rasuwar Modibbo da nata mahaifin ya taba gaya mata sun sake matsawa kadan daga kudancin Arlit zuwa gabashinta."

"Nan idanunta suka kawo ruwa itama, saboda bata son gaya masa dalilin kukan Keltouma na yau, da kuma abinda zuciyarta ke dada saka mata yanzu-yanzu, tana jaddada mata cewa Keltouma tafita gaskiya RAYUWARSU BATA DA SAURAN"

FUTURE idan suka cigaba da zama a IDP Camp.

"Abinda yasa Keltouma wannan kukan shine; tun jiya da likita Kazim yace mata gobe da safe za a sallameta hankalinta ya tashi, ta tuburewa Ummami kan ba inda zata, bazata koma sansanin  yan gudun hijira ba."

"Yau Keltouma harda rantsuwarta ga Ummami kan cewa saidai akai gawarta, ko a binneta da ranta yafi mata zaman IDP Camp."

"Ummami ta rasa yadda zatayi ta lallasheta, daga bisani ganin bazata ji lallashi ba yau Ummami tace mata sai sun koma, don basu da inda zasu je a yanzu da ya wuce musu can rufin asiri da kyakkyawar mafaka."

"Amma idan ta fada masa wannan dalilin na kukan Keltouma, da yadda ta kasa shawo kanta a matsayinta na Uwa-mahaifiya a gareta ai ai sai Mr. Yassar yaga kamar tayi saken da Keltouma tafi karfinta ne bayan kusan a zahiri kusan haka din ne."

Soyayyarta ga Keltouma tayi yawan da har take kasa tankwarata a wasu lokutan.

"Keltouma ta kafe akan bakanta itama, tana jayayya da ita yau."

"Yanzu kam Ummami ta kai koluluwa a bacin rai, ganin cewa zuwan Mr. Yassar da nuna bacin ransa da yayi akan kukan duka bai sa Keltouma ta hakura tayi shiru ba, don haka"

"yanzu cikin daga murya mai nuna fushi Ummami take mata magana cikin yarensu, don kada Yassar yaji, tana cewa a hassale,"

" ki nuna masa banda wata martaba a idanunki da har zanyi hukunci kice a ah, ki nuna min ban isa dake ba balle shi dake tsaye bilhaqqi akan lafiyarki, ya samu arzikin girmamawa daga gareki tunda kinsan baya son kukan nan."

"Na rantse idan baki yi mana shiru haka ba, zan kai ga bugunki, nayi rantsuwa zan bugeki mummunan bugu idan kika kara cewa tak! ."

"Yassar bai ankara ba yaga Ummami ta dauki warin takalminsa dake gefe, ya dauka matsar dashi zata yi sai yaga wuf! Ta kai mata uban duka dashi a gadon bayanta."

"Keltouma aka daka amma Yassar ne yaji saukar bugunnan har cikin tsokar jikinsa. Rana ta farko kenan da Yassar yaji Ummami ta kwabi kukan Keltouma, tunda kullum uzuri takema kukan nata ta bashi kariya, yau gashi tana tsawatar mata har da bugu, mai nuna ta kaita bango, ya kuma ga fushi na hakika a"

cikin kwayar idanunta akan kukan Keltouma yau. Sosai yaji Ummami ta dada burgeshi.

"To ita kanta Keltouma bata zaci duka daga Ummami a daidai wannan lokacin ba, a tasowarta ma bazata iya tuna yaushe rabon da Ummami ta kai mata bugu ba sai yau. Don haka ta hadiye kukan gabadayansa ba shiri, ta soma ajiyar zuciya."

"Mr. Yassar dai yana zaune gaban gadon Keltouma, ya dauki hannayenshi bakidaya ya tallabi fuskarsa dasu yana kallonta, sai sauke ajiyar zuciya take yi mai nauyi. Jikinsa yayi sanyi kwarai da dukan da yaja mata. Yace  kiyi hakuri Ummami . Ummami tace dashi."

" Kai za a baima hakkuri, nasan baka son kukan, ina rokonka da ka kuma yi mata uzuri, ka kara da guda saba in a kan na baya, kaji ko Muhammadu Yassar?! ."

"Yassar yayi wani kasalallen murmushi mai bada sauti, yace  nayi mata Ummami, na kara akan na baya, ni daga yau ma zan yi kokari in daina damuwa da kukan nata, don na yarda bana kare bane, ta mayar dashi halittarta."

"Khulthoum, kullum bazan gaji da cewa dadi ne yayi mata yawa ba. In banda haka sau"

nawa zan gaya mata ita  yar gatan  yar gudun hijira ce?

"Sauran yaran dake sansanin marasa iyaye da mai lallashinsu, su yaya suke gudanar da tasu rayuwar? "

"Sai wannan lokacin Keltouma tayi kokarin yin magana cikin sautin kukan da ya dakushe, taga in ta cigaba da yin shiru, ita za a yi ta baiwa laifi, tana bukatar yau a fahimceta, a bata listening ears dinda ba a bata kullum. Cikin sanyin murya tace."

" Ni bazan koma sansani ba, bana son komawa Ummami, in kika tursasani na koma komai na iya faruwa dani."

"Don Allah kace da Ummami kada mu koma, gara mu shiga cikin gari, cikin mutanen gari, ko bara ne mu dinga yi, na tabbata sai yafi zaman sansani albarka."

"Baka san yaya muke rayuwa a wurinnan bane, Ummami bata taba gaya maka ba, kullum bama iya barci, saboda fargaba da tsoron fadowar kwarto kanmu a tent dinmu da tsakar dare, da azabar cizon sauro ."

"Idanun Mr. Yassar suka dan firfito waje. Yau

Please Login or Register in order to submit comment