gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading KELTOUMA Tafiyar Kaddara By takori kabara Chapter 8 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka game, shi, yarinyar da mahaifiyar tata. Da alama yarinyar taji komai na bakin Haladu, hawayen ya kara wanke fuskarta, jikinta yana rawa tace  Ummami kizo mu tafi, na hakura! Idanunta kamar an sunce famfo don karin zubar ruwan hawaye."

"Wannan yarinyar al amarinta yanzu ya dan daina bashi haushi, ya dan soma tabashi, da saka shi a damuwa. Don yaga alamar bada gangan takeyi ba."

"Yaji yana son ya san komai akan yarinyar nan, da sanadin kukanta mara yankewa, da abinda ya kawosu IDP Camp, wanda ga dukkan alamu zaman cikinsa ne yafi"

"komai daga hankalinta, ko kuma akwai wani boyayyen dalili na daban, dake sata yawan kuka, amma ba haka kawai kullum mutum zaiyi ta kuka babu gaira babu dalili ba."

"A halin yanzu idan ka dubi kamilalliyar fuskar Mr. Yassar, zaka ga cewa a cikin idanunsa akwai rahma da sassauci daga yanayinsa na dazu gareta, wato akwai sassauci daga irin kallon da yake yiwa Keltouma a baya, daga wancan kallon na haushi da takaici, warning look da yake yawan kora mata, zuwa kallo na sabawa da halin mutum da sagartarsa, wato kallo yake mata yanzu na zama familiar da sabo da dabi unta da yawan rauninta."

"Sabanin irin wancan kakkausan furucin da yayi mata dazu, cikin kaushin murya da takaici hadi da daure fuska mai nuna gargadi, yanzun ya tausasa halshensa da lafuzansa. A lokacin da ya dubeta harda murmushi na tsokana fatar bakinsa yanzu."

 Ke kam kinci sunan dana dade da baki  Akoke . Akoke anya?! Kina neman albarka da tubarrakin Uwa?

"Kowa yana ji da uwarsa, yana kula da kwanciyar hankalinta, amma banda ke Akoke."

"Na rasa ke wace irin shagwababbiyar yarinya ce, da bata damuwa da feeling din mahaifiyarta a kanta, kullum baki da aiki sai wahalar da taki uwar, kina sakata cikin damuwa da halin koke-koke da take yawan ganinki a ciki."

Ga surutun jama a a kanta duk saboda ke? Anya KHULTHOUM?!

"Keltouma ta dago idonta mai kama da shatin Kwan zabo ta kalleshi, sakamakon sunanta data ji ya furta cikin wata irin siga da wasu sababbin haruffa, idanunta nashe-nashe cikin hawaye take kallonsa. Amma hakika sunan ya mata dadi kwarai a kunne da ya fito straight daga bakin Mr. Yassar. Suka yima juna kyarrr! Da kallo cikin ido, wani maganadisu ya samu muhalli, sabida chemistry din dake fitowa daga idon Yassar yana shiga cikin na Keltouma, hakan ya daukesu  yan sakanni kowanne ya kasa janye idonsa."

"Kafin Keltouma tayi hanzarin sunkuyar da kanta, saboda idanun Mr. Yassar ba irin na sauran mutane data saba gani bane, da zaka iya kallon cikinsu ka jima cikin kallon nasu"

zuciyarka bata shiga wani yanayi na motsuwa da galabaita ba.

Yassar ya cigaba da cewa cikin lallashi.  Ni inason Mamata da yawa Khulthoum. Bana barinta cikin damuwa. Kinga ya kamata ki dinga aiken mahaifiyarki wajen maza karbo miki  hygiene kit kamar  yar aikenki suna yi mata rashin kunya? Ke meyasa bazaki je da kanki ba? Idan yaso ke ki

karbi rashin mutuncin nasu?

"A hankali yarinyar ta sake dagowa ta dubeshi, sai kuma ta sunkuyar da kai cikin rashin sanin amsar da zata bashi. Yassar ya dubi uwar yace."

" Please Iya, ki daina biye mata tana wahalar da ke a banza, don naga alama Akokenki bata san Annabi ya faku ba."

Bata san girman rufin asirin da Allah yayi mata a wajennan daya bar mata ke a raye ba! Gaki nan cikin koshin lafiya kamar ba ke kika haifeta ba .

Murmushi uwar tayi. Kyakkyawan murmushin data dade bata yi irinsa ba. kafin tace komai Yassar yace.

" Eh mana Iya! Ita  yar gatan  yar gudun hijira ce, tunda kuwa tareda uwarta"

"mahaifiya ta yi shi, su kwana tare su tashi tare, cikin kulawarki take rayuwa, tana jin muryar mahaifiyarta kullum, tana ganin sanyin idanunki suna rage mata radadin zuciya tana jin sanyi daga lafuzan bakinki. Sauran kuwa fa? ."

"Yayi nuni da dan alinsa ga can nesa dasu kadan, yana cewa;"

 tayani duba can Iya! Duba nan!! .

"Wasu yara ne fal, daqa-daqa dasu cikin wasan kasa, mata da maza, kananan yara dasu sosai, zube akan wani Yashin dasu Yassar ke ginin sabuwar makarantar yara dashi a daura dasu kadan, dukkansu yaran an gaya musu ba uwa ba uba su kadai ne a wajen, amma hirarsu suke a tsakaninsu tareda wasan lakar da suke haqowa a cikin Yashin, suna ginin tukwanen laka ba abunda ya damesu."

" Su basu da kowa anan, amma sun karbi kaddarar Ubangiji suna rayuwarsu cikin tawakkali da sakewar zuciya a sansanin nan, har zuwa lokacin da rabbil izzati yaga damar yanke musu, ko hadasu da iyayensu ko dangin iyayensu ."

"Suka cigaba da tafiya tare a filin wurin. Wato shi da Ummami da Keltouma tana daga bayansu. Sai da sukayi nisa da ofisoshin ma aikata sosai, a wannan lokacin sai matar ta dan dakata da tafiya, tayi magana da Yassar cikin tsananin damuwa, ganin maganganun da yayi ma  yarta cikin lallashi da nusarwa ta hanyar bada misalai a gareta yasa jikin Keltouma yayi sanyi, tuni maganganun Mr. Yassar yasa ta shanye/hadiye kukan nata gabadaya. Ummami tace dashi."

" Da na bazaka gane ba, ka yiwa diyata Keltouma uzuri, ba wai bata girmamani bane ko ita take aikena in karbo mata abu, a a nice dai nake yin hakan a kokarina na bata kariya (protection) daga mazan banza dake wajennan. Abunda yasa bana damuwa da yawan kukan ta kuwa saboda duk dan da ya samu kansa cikin halin data samu kanta, Da na dole yayi kuka."

"Keltouma ta kasa manta abinda ya faru da mahaifinta. (Ba a jima sosai ba da kisan mahaifinta), sannan an kawo mana gawarsa jina-jina akan idanunta, bayan an harbeshi a hanyar dawowarsa daga wajen sana arsa, tun"

"daga ranar nan kullum cikin dare bata iya barci, sai firgita da kiran sunan Babanta ."

Yassar yayi dif! Yana sauraron Ummami ta hanyar bata dukkan hankalinsa. Saida ta yi shiru sannan ya daga kai ya dubeta. Itama hawaye sun zubo mata a lokacin.

"With utmost concern Mr. Yassar yace  naji dalili kukanta Iya, to amma bazata yi hakuri ta barma Allah yinsa ba? Kukan zaisa Baba ya dawo ba, kuma bazai kareshi da komai a lahirarsa ba, shi Baba ai yayi Shahada, addu a ya kamata ta dinga yi masa."

"Duk wanda aka kashe bisa zalunci yayi shahada kuma ana masa fatan aljannah salin - alin, domin ya mutu babu hakkin kowa dana komai a kansa, baba dan aljannah ne in sha Allahu, kinji ko Keltouma?! ."

"Kasancewar ba wai Hausa ta ishi uwar bane sosai yasa ba duka take gane me Yassar yake fadi ba, balle hausar Yassar basakkwaciyar hausa ce (Sokoto accent) ita kuma dadin dadawa ba ainahin bahaushiyar bace, amma ita yarinyar tsaf take gane me Yassar yace saboda cakuduwarta da yara"

sa o inta a nan Zamfara inda anan aka haifeta ta kuma taso. Tayi makarantar firamare tareda yara  yan asalin Sokoto da Zamfara.

"A lokacin suka iso gate din da ya raba filin wajen da azuzuwan da suke kwana. Ummami ta kama hannun  yarta don sun iso inda zasu rabu dashi su wuce wajen kwanansu,"

"Ta cema Yassar  Don haka nakeso kayi ma Keltouma uzuri ka ji! Bazaka gane irin radadin zucin da muke ciki ba dukkanmu, sai in irin haka ta faru a kanka."

"Misali ace asa bindiga a harbe mahaifinka akan idanunka&  . Jinin ya feso har a jikinka. Kafin ka manta wannan majigin (scenario) na tabbata za a jima, ko nace har abada bazaka manta ba, kuma dole kayi kuka don rage ma ruhinka radadi. bai hada sani da Allah! Amma da mun san hakane da tun farko bamu fito ci-ranin ba, To hakan ce ta faru da Keltouma ."

"Tasa habar zaninta ta share ido tana cigaba da cewa  balle uba irin nata, da bai hada kaunarta a duniya da komai ba, bawa da munyi zamanmu a kasarmu, da mun zauna yunwar ta kashemu a cikin danginmu da yafi"

wannan rayuwar da muka tsinci kanmu rana daya a Najeriya .

Zuciyar Yassar har harbawa take a lokacin. Bai san sanda ya fiddo wayarsa daga aljihun gaban rigarsa ba ya kira Haladu.

 Kai Haladu!!!

"Mr. Yassar ya fada da murya mai kaushi yana kiran Haladu dake ofis ta wayar hannunsa, Haladu ya fito daga ofishin yana mika, yana wara idonsa, don yaga inda Yallabai Yassar yake, kafin ya hangosu tare daga can nesa shida mutanen nasa, sannan ya amsa ta cikin wayar yana fadi a cikin ransa wai shin meye hadin Mr. Yassar da wadannan kodaddun matan ne? ."

 Yallabai gani! Ina bayan ku .

Yace  Haladu ka basu abinda suke so maza-maza .

Haladu yace  an gama Yallabai

 daga yau sai yau kada su kara neman taimakonka kana da halin hakan ka ki taimaka musu . Nan ma Haladu yace  an gama Yallabai .

Daidai nan ya iso wajen rike da (hygiene kits) din har guda biyar a leda ya kawo musu.

"Yassar ya karba ya mikawa Ummami. Mr. Yassar ya saka hannu a aljihunsa ya ciro (atm card) dinsa ya mikawa Haladu, yace,"

" ka ciri kudi kaje kayo musu sayayyar abinci mai gina jiki, da sabulun wanka dana wanki, da duk abin amfanin da mata ke bukata wanda zai kai musu akalla wata uku. Zan tsaya anan in jiraka har kaje ka dawo, ka kawomin komai in gani yanzunnan ."

"Babu musu ko jayayya Haladu ya karba, amma a ransa yana ta mamakin Mr. Yassar, ba irin zargin da bai zo ransa game da kulawar Yassar akan mutanen nan ba. Na cewa tausayi ne? Ko kuwa irin nasu taimakon ne (na taking advantage) Mr. Yassar ke son yima bakin hauren nan???"

"Amma dai da mamaki kuma kamar wuya ma ace Mr. Yassar din zai bukaci wani abu na physical relationship ya hadashi da daya daga wadannan masu kama da an fizgosu daga bakin Kurar, saboda rashin nutsuwa da rashin wanka, shi da har wani kyalli na musamman zaka ga fatar jikinsa nayi kamar daka tabashi jini zaiyi tsartuwa, gashinan sumul kamar sai ka wanke hannu kafin ka taba, Yassar shalelen Ammih, kullum kamar"

"an baro shi daga cikin kwai saboda tsafta da wanka da suka kama jikinsa, in ka kalli tafin kafarsa sai kace Mr. Yassar Jalloh baya taka kasa."

"Tunanin da Haladu keta yi kenan shi yasa bai ji sanda uwar ke yima  yarta umarni cikin yarensu da tayi ma Mr. Yassar godiya ba. Maimakon amsa godiyar, wadda Keltouma keyi masa cikin  yar siririyar muryarta daga can kasan makoshinta, Mr. Yassar hararar Keltouma yayi, sannan ya kara kora mata  warning dinsa, na kada ta sake yayi mata gani na gaba cikin halin kuka da"

asarar hawaye. A karshe yace.

" Daga yau inaso ki koyi tawakkali. Ina so ganin da zan yi miki na gaba ya zama na ganki ne cikin yanayi na kwanciyar hankali, son samu in ganki da murmushi akan fuskarki ."

Keltouma ta sunkuyar da kai tace a ranta  ko yaushe murmushinta zai dawo? Ko yaushe zata kara yin wani abu wai shi murmushi ko dariya a rayuwarta bayan babu Modibbo mai sakata yinsu? Modibbo ne kadai yake sakata murmushi a duniya tana so ko bata so in dai yana wuri sai tayi shi .

"Memeories din da ta tabbatar zasu cigaba da bijiro mata har abada, wato Kakanta da Babanta."

"Daga haka suka sa kai zasu wuce wajen kwanansu, daidai lokacin da zasu gifta ta gabanshi sai da Keltouma ta dan saci kallonsa ta wutsiyar idanuta, sai taga har lokacin Mr. Yassar bai bar kallonsu ba, yana tsaye a wurin da hannunwanshi biyu zube cikin aljihun kaftanin makubar shaddar dake jikinshi, yana kallon wucewarsu ta gabanshi. Suna iya jin sanda Haladu cikin lallashi da kankan na kai da ladabi wannan karon yake cema Yassar in sha Allah zai bi umarninsa, bazai kara harassing dinsu ba balle yayima Ummami rashin kunya, yace zai sayo ma Ummami da  yarta komai da ya dace da amfanin mata kamar yadda yayi masa umarni, ya kara da cewa  Yallabai, ba sai ka tsaya a wurin nan ka jirani ba. Zan yi komai bisa umarninka ."

"Ummami nata yi masa godiya kamar ta fashe da kuka don dadi, Keltouma kuwa ko uffan bata kara cewa ba, bayan  yan siririyar godiyar data yi masa, yi tayi kamar ma bata fahimtar me suke cewa cikin harshen hausa. Kana neman miskilar yarinya ka samu"

"Keltouma to ka gama nema. Ta dauke hankalinta bakidaya daga kansu, ta mayar ga fuskantar kofar shiga sansani."

"Tausayin matar Yassar yake ji a ransa sosai, har bai san yadda zai kwatanta ba, bai kuma san maiyasa Ummami ta shiga ransa ba, ta samu matsugunin Uwa a zuciyarsa."

"Ya samu kansa da yi mata kallon Uwa agareshi mai Daraja, tun daga rana ta farko da ya fara ganinta, duk da ba wai ta haifi kamarsa bane a shekarunta. Akwai wani nasibi mai yawa a tareda matar, ikhlasi da tawadi u, mai nuna cewa mace ce mai tsarkin zuciya, wadda yaji  yar ta na kira da suna UMMAMI."

"Yafi alaqanta dalilin tausayin nata da yake ji da ganin yadda miskilar  yarta ke wahalar da ita. Amma yanzu data yi masa cikakken bayanin dalilinta na tolerating halin rigimar  yar tata da dalilinta na jurewa rikicinta da miskilancinta, shin bai isa dalili ba da shima zai yiwa  yar Ummami uzuri???"

"Femi yazo ya taddashi a inda yake tsaye har lokacin, bayan wucewarsu Keltouma cikin gate dinsu, bayaraben mutum da son jin tsegumi, duk abinda ake yi tun tsayuwarsu a"

"wurin Femi yana hangosu, ya tattara hankali wajen nazartar Ogan nasa akan mutanennan yanzu, uwar da  yar na kulewa cikin dafifin mata  yan gudun hijira Mr. Yassar na cigaba da tsayuwa a inda suka barshi. Shi kansa bai san tunanin me yake yi a wurin ba, kawai dai Ummami da  yarta sun maidashi very curious and extremely intrigued ga son jin ainahin labarinsu, tarihinsu, asalinsu, da dalilin zuwansu wajennan wanda ko kadan bai dace da dasu ba, to amma shin ina ruwan kaddara da zaben kalar fata? Daga bayansa yaji hannun Femi ya dafa kafadarsa."

" Boss, yaya dai? You are completely"

lost!

"Ni Femi, in aka kyaleni sai in yi"

karambani na da kankanbata ince da alama something is fishy here& .. or somewhere else& .. tsakanin my Boss& . da jajayen matan IDP Camp .

"Wani sakaran kallo da Yassar yayi masa ya sashi dariya, Femi na cigaba da dariyarsa ya cigaba da cewa."

" Sabida yadda hira tayi dadi, da uwar ne koda  yar e ni ban gane ba, har ka manta"

"maqasudin me muka shigo yi Camp yau, alhalin ba ranar wani aiki bace? "

Da ya duba sai yaga cewa kwarai da gaske saboda su Ummami yau gabadaya ya manta abinda yazo yi.

Femi bai barshi ya gama dawowa daga wannan tunanin ba ya zarce da cewa.

" Sorry Boss da shishshigina, da yawan karambanina ."

Femi ya fada cikin neman tuba don kallon da Yassar ke masa yanzu warning look ne.

"Ya san Yassar baya gajiya da hararar wanda ya bashi haushi, yanzunma hararar abokin aikin nasa yake tayi da fararen idanunsa, ya rasa meyasa Femi ke son saka mashi ido irin haka, bayan shima bai sakawa kowa ba. Ko matan da yake dauka daga clubs yana kawowa hotel dinsu kullum ranar Allah in suka koma cikin gari, ko daga ido baya yi ya kalleshi, balle ya tambayi me suke zuwa yi masa har daki."

" Once and for all Femi, mind your business! Ka daina shiga sha anina zanfi son haka ."

Iya abinda ya iya ce dashi kenan.

Tun fil-azal shi mutum ne mai takaita magana.

"Daga haka ya taka a hankali ya bar Femi a gurin yana kallonsa yana masa murmushi, bazai iya kayyade alkhairin wannan musulmin gareshi a rayuwarsa ba, don haka shima sosai yake kaunar Yassar din, hatta aikin da yake yi din Mr. Yassar ne ya samo masa shi tun haduwarsu a Jami ar Texas Yassar Jalloh yake kyautata masa."

"Yassar ya dan sassauta daga zazzafan kallon da yake masa yace dashi  idan ka gama tsegumin, sai ka taddani a mota mu zaga masu ginin, sannan mu wuce cikin gari muyi lunch kuma ko? ."

"Da sassarfa Femi ya biyo bayansa har ya taddashi, suka hada kafada suka jera.."

"Suna tafiya a tare, Femi na cewa  to be honest, ba tsegumi bane mamaki nake tayi akanka Boss, ko zan iya sanin me ye

Please Login or Register in order to submit comment