You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
Downloaded From https://tknovels.com.ng COMPILED BY ESHATT SMILER HOM OF HAUSA NOVLS DOCUMNTS
WASAPP 08066360176
馃挌馃挏鉂ゐ煐ゐ煉欚煉�
NA CUCE TA
馃挌馃挋馃挏馃枻馃挍鉂�
庐zuwairat( ummu Maryam)
1鈨�
_Alhamdulillah, Allah praise be to almighty Allah_
_Am back again_
Cikin wani gidan Wanda ke ginin kasa mai dauke da daguna biyu wata yarinya ce wacce bazata wuce shekara shabiyu zuwa sha uku ba ke daka sai tim Tim Kawai kakeji saboda yanda take dakan garin furan dake cikin trumi, daga dayan gefen Kuma wata matace ke hura wuta sai kafawa murhun bakin take tana hura wutan, duk idanuwanta sun chanza kala saboda yanda hayake ke shiga idonta, wata yar yarinya na gani ta taho da gudu da wata faifai
"Ammi ki hura da wannan...." Yarinyan ta fada mata, matar dake durkushe gaban murhun dagowa tayi ta sakarwa yarinyan murmushi tare dacewa
"Yauwa...nagode binto..." Matar ta fada tana amsan faifan daga hannun yarinyan.
Da ganin Matan da yanayin gidan kasan gidan kasan masu karfin haline sosai don komai NA gidan is low to the last core, yarinya dake dakan goge zufan goshinta tayi ta kalli matar da aka kira da ammi tace
"Gaskiya ammi gobe mu kai injin...NA gaji da daka Wallahi hannuna duk ya kumbura.. Nidai NA gaji..." Tafada tana turo baki tare da kallon tafin hannunta ya kumbura saboda yawan daka
Ammi kallon ta tayi Sannan ta maida dubanta ga muhur
"In banda abinki dije AI kin San da wannan dakan muke samun abinda zaa bawa awakan nan ...in an kai inji ba su bamu dusa..." Ammi ra fada tana hura wutan, dija Kara turo baki tayi
"Wai ammi dole ne mu bar wayan nan awakan?... A saida su mana Kawai..." Tafada in I don't care manner, ammi kallon ta tayi ta tabe baki
"Ai babu abinda kika Sani..maza ki kara kar su saude su bar ki yau ma..." Ammi ta fada mata bayan ta gama hura wutan. Dija kara turo baki tayi
"Nidai NA gaji....binto..." Ta kwalawa kanwarta kira,
"Naam...." Yarinya ta amsa mata
"Zo ki tayani...." Tafada tana barin tabaryar cikin turmin, ammi kallon ta tayi
"Wai ke wace irin banzar yarinya ce?...yanzu binto zaki barwa dakan furan?.... Dalla ki maida hankali kar lokaci ya kure...sakara Kawai.." Ammi ta fada tana debo taliyan kadi daga kan igiya tana zubawa cikin kwarya dake hannun ta.
Dija tana turo baki ta dake furan ammi tayi molding dinshi ta zuba mata cikin roban da take zuwa talla da ita Sannan tayi mata gammo,
"In kin saida ki sayo magi da hamsin... Fulawa quarter..sai ki sayo sabulu guda daya Dan hamsin da biyar..." Ammi ta fada mata tana Dora mata gammon bisa kanta, dija dai Bata ce kala ba don in da zaa kashe ta ya fiye mata wannan tallan da take amma Kuma Bata Iya kin zuwa saboda ta nan suke samun mostly abinda suke amfani dashi da yau da kullum, furan ammi ta dauki ra aza mata bisa gammon har lokacin Bata bar kumbure2 ba
"Wai ke meke damunki?..." Ammi ta tambayeta, kara turo baki tayi
"Ni wallahi ammi banason talla... In munje garejin daura duk yawancin mazan yan iska ne...." Baki ammi ta bude tana kallon ta, dija ta cigaba dacewa
"Sai suce sai sun taba mutum Sannan su sayi furan sa...." Idanuwa ammi ta zaro tana mamakin abinda yarta take fada mata, kallon yarinyan tayi ta kalli kirjinta dake dauke da boobs yan kanana da basu gama developing ba,
"Wallahi ammi jiya wani cemin yayi in zauna kan kafanshi ya sayi dukkan furan..." Ta fada tana fashewa da kuka, da Sauri ammi ta sauke furan daga kanta tana cewa
"Wai da gaske kike?..."
"Wallahi ammi... Da ...gaske...nake....kullum haka suke mana...wasu sun girmi kawu nanu amma duk yan iska me...ni wallahi ammi banason talla..." Ta karasa maganar ta cikin matsanacin kuka, ahankali ammi ta zauna kan Dan kujeran dake gaban ta tayi tagumi Kawai sai ta fara hawaye,
"Ya Allah.. Gamu gareka...ga yar marainiyarka gareka...ya rabbi kar ka bari a cutar da yar marainiyarka...." Tafada cikin kuka, kallon dija dake hawaye tayi Sannan tace
"Dija...inda nasan yanda zanyi da ko kadan bazakiyi tallaba...amma ke kanki kinsan halin da muke ciki... Kin koshi da taliyan da kika CI?..." Ammi ta tambayeta, cikin kuka ta gyada mata kai alaman AA,
"To kin gani...dukda tallan da kike ba koshi muke ba...kiyi hakuri ...wata rana sai labari..." Ammi ta fada cikin kuka, dija Dan turo baki ta kara tana cewa
"To ammi ki yiwa inna ladio magana mana ko zata samo min gidan aiki a birni kaman yanda Ladidi takeyi...." Idanuwa ammi ta zaro,
"Allah ya sauwake...ban yarda kije aikatau....ke Kawai Allah ya rufa mana asiri..Kuma kar ki yarda wani ya taba koda akaifanki ne balle jikin ki...kina jina?..." Ahankali ta gyada mata kai ta Kara cewa.
"Nidai ammi..nafison..." Sallama wasu age mate dinta yasa tayi shuru Bata karasa maganar da tayi niyyan fada ba, yan fura2 ne kusan su takwas suka shigo Dan karamin gidan
"Kam yau anci saa kin shirya baki tsaya bata mana lokaci ba..." Inji daya daga cikin yanmatan, hararanta dija tayi
"To uwar iyayi..." Inji dija, ammi Dora mata furan tayi tana cewa
"Kar ki manta abinda NA fada maki..kinji?.."
"To ammi..." Tafada Sannan suka fita daga gidan, daman da akwai wani mai motan dake daukan su daga kauyansu zuwan cikin garin daura dake jihar katsina. Ammi daki ta shiga, nima binta dakin nayi, ina ganin yanayin rayuwarsu nace alhamdulillah Allah dai yasa babu wayanda ke zaune a irin wannan gidan a zahirin rayuwa don their life is low beyond words, tagumi ammi tayi tana tunanin yaushe wahalan su zai kare don kullum gani take kaman is getting worse, gashi yaranta hudu Kuma dija ce babban cikin su,
"Hmmm..ya rabbi ka tausaya mana..." Tafada tana Dan mikewa kan tabarman dake kasan dakin da ko cement babu.
A chan wani bangare NA Kano kam wani gida ne cike ana ta bude akwatuna da alaman lefe aka kawo, duk wacce ka gani kasan yan Hutu ne don every body around is glowing kaman babu wahala cikin duniya.
"Amma wannan kayan sun hadu da yawa..kayan kaman na mata biyu?.." Inji wata mata, Dariya Matan wurin suka saki Sannan daya daga cikin su tace
"Ai yanda mutum yake hakan komai nace yake...baku ganin yanda diyar tawa take kaman ita tayi kanta?..." Inji wata mata, guda daya daga cikin su ta saki don murna,
A daya daga cikin dakunan gidan kam wata beautiful lady ce zaune kanta babu headtie sai yanmata biyu zaune kusa daita sai hira suke, da alaman lefen ta aka kawo,
"Kinsan wallahi sai kin bani wannan swiss lace din...tunda an kawo maki uban kaya..." Inji daya daga cikin yanmatan dakin, wacce akayiwa magana Dariya ta saki Wanda yasa hakorin Makkah dake bakinta ya bayyana,
"Dan wannan babu case..." Shuru tayi ta kalli wayanta daya fara ringing, murmushi ta saki tana dauka wayan, yanmatan kallon juna sukayi suna cewa
"Halan angon ne?..."
"Yes...babyna ne..." Tafada tana picking wayan,
"Baby..." Ta fada cikin sexy voice, daga Chan bangaren aka saki murmushi, wani saurayi ne zaune a office, yana Dan buga pen dake hannun shi ahankali kan desk dake gabanshi, yana jin muryan Mufida ya ajiye pen din tare da yin mika Sannan yace
"My angel ya kike?..."
"Lafiya lau...ya kake ya rayuwa?.."
"Alhamdulillah... An kawo kaya ko?.." Ya tambayeta in a low voice
"Yes baby....is so beautiful..." Tafada cikin whisper, Dariya yayi yana biting lip dinshi ahankali Sannan yace
"Not as beautiful as you...ai in ma shigo Kano sai NA kara kai personal shopping.. Kayanda babu idanuwan da zai gani sai ni kadai..." Murmushi mufida tayi tana sauraron yazid cikin so da kauna,
"Is that necessary?.." Ta tambayeshi ahankali,
"Yes mana...ai wannan da kika gani choice din Hajiya karama ne...ni zanyi nawa bayan sun gama nasu..." Yarinyan da bazata wuce shekara 22 ba ta saki murmushi Sannan tace
"Baby yaushe zaka dawo?..." Ta tambaya ahankali,
"In biki sauran sati biyu..."
"Haba mai baby...ina missing dinka...ko baka missing dina?...." Ta tambayeshi cikin sanyin murya, Dariya yayi ahankali Sannan yace
"Ina missing dinki mana...in nazo kusa dake inajin kaman in cinyeki shiyasa ban San in zo sai nan da sati biyu..." Kukan karya ta farayi tana cewa
"Yanzu nan da abuja shine bazaka zoba?... Don Allah kazo wannan weekend din...pls..."
"No...sai in the next two weeks... By then wedding din sauran sati biyu.. Kinji babyna..." Ya karasa maganar cikin whisper,
"Hmm shikenan...kana ina?.."
"Office..."
"Kaci abinci?..."
No..ko zaki zo ki bani?.." Shuru tayi Bata amsa mashi ba, hiran sukayi for almost an hour Sannan sukayi sallama, mufida wulla kanta kan gado tayi saboda murna, shi kuna ya kashe wayan ya Dora kafa daya kan daya tare da relaxing, karewa gayen kallo nayi sai naga kaman yafi mufidan kyau don ya hadu sosai, he's every ladies dream guy, bai ankaraba yaji an ture mashi kafa daga kan desk dinshi bude idanuwa yayi ya saki murmushi
"Wai ka baka sallama ne?...kullum always boosting into people's office..." Inji yazid dake gyara zamanshi, Dariya gayen da ya shigo yayi Sannan yace
"Ka koya min sallama
Mana...ustazz..." Gayen ya fada yana zama kan kujeran dake gabanshi, murmushi Kawai yazid yayi yana cewa
"Ai kasan ban yi karya ba..."
"Muje muci abinci..." Gayen ya fada mashi, agogon dake kwance hannun shi ya kalla yaga har 3pm,
"Muje..." Yazid ya fada yana mikewa, laptop dinshi ya maida cikin bag tare da wasu files, kara kallon gayen nayi nace hmm am definitely dropping dead don yazid is killing me, tsayawa nayi INA kallon yanda yake abu very slow, komai nashi a nutse babu alaman Sauri ko.hanzari tare dashi, yafi minti goma yana parking abubuwa shi Kuma dayan gayen yana zaune yana kallon shi, sai da ya gama Sannan yace
"Mu tafi..." Yafada yana rataya bag din a shoulder dinshi, gayen kallon shi yayi
"Are sure ka gama don NA san halin ka da delay kaman mace..." Yazid tabe baki yayi yabi ta gefen shi ahankali ya wuce, yanda yake tafiya sai ka rantse bashi da bone ko daya a jikinshi don tafiya shi so sluggish. Gayen mikewa yayi yana cewa
"Allah ya huci ran ango..."ya fada ya tarda yazid dake tafiya a hankali, banza yayi dashi
" wai sauran kwana nawa bikinka?.." Gayen ya tambayeshi,
"Four weeks exactly..."
"Wow...zan je Kano..I can't wait.. Allah ya hadani da mata yar Kano..." Inji gayen
"Ameen sultan..." Sultan kallon shi yayi yace
"Amma nasan kana da younger sisters.. Ka hadani da daya daga cikin su mana..." Sultan ya fada mashi,
"Ni ba hadani akayi da my mufi ba...kaima ka nemo naka..." Ya amsa mashi atakaice yana danna lifter, kofan ya bude suka shiga ya jingina da jikin lifter yana cewa
"Am so tired.. NA gagara in fara Hutu wallahi..."
"Ai kai kullum a gajiye kake..lazy guy..." Sultan ya fada mashi.
"Ai am not a racer balle in ce anason inyi gudu,...I believe in easy way ..."
"Yeah...you believe in easy tunda you are lazy...kasan muje gym wannan weekend din kaga yanda guys ke motsa jiki...." Dariya yazid yayi Wanda ta bayyana well set of teeth dinshi mai dauke da madaidaishin wushirya daga tsakiya
"Hmm mufida you are one lucky gal....," NA fadawa kaina,
"Workout kaman wani Dan danbe?... Kai am OK the way I am...Kawai I love my self...I don't need to workout.." Ya fada suna fita daga cikin lifter, hallway suka nufa suna gaisawa da wasu Colleagues nasu na CBN abuja har suka isa parking lot Kowanne su ya dauki elegant car dinshi mai tsadan gaske sukabi bayan juna zuwa wata expensive restaurant inda suka saba cin abinci.
[3:11PM, 3/20/2018] 鈥�+234 806 125 0020鈥�: 鉂ゐ煉涴煉氿煐ゐ煉滒煉�
NA CUCE TA
馃挋馃挌馃挏馃枻鉂ゐ煉�
庐zuwairat( ummu Maryam)
2鈨�
Suna cin abinci yanmatan wajen NA Dan flirting dasu daman sun saba da behavior dinsu, yazid kam ko daga kai baiyi balle ya kallesu shiya sa suke ce mashi oga ustaz, kullum in suka zo wajen bai daga kai balle ya kalli mutum daya cikin tsalatsalan yanmatan dake sayar da abinci shi kam sultan sunayi yanayi har wani lokacin ya batawa yazid rai,
"Hot Bomboy...." Wata yarinya dake sanye da mini skirt ja da white shirt da aka rubuta eleganza gabanshi ta fada tana tsaye kusa da sultan amma yazid dake zuba salad kan abincin shi Kawai take kallo. Cikin dariya sultan yace
"Yes sweet baby...how far..." Yafada yana cin abincin shi don in da sabo ya saba shi ko kadan bashi da kyaliya while shi yazid ko kallo basu isheshi ba,
"Oga ustqz...how is work today..." Budurwan ta tambayi yazid, banza yayi daita yacigaba da cin abincin shi,
"I will come to CBN quarter this weekend... Can I visit?..." Yarinyan ta tambayi sultan, sultan kallon hot legs dinta dake salki yayi zuwa boobs dinta dake cike dam da kirjinta Sannan yace
"No thank you...I don't want to do anything stupid..." Yafada yana maida kanshi wurin abincin shi, yarinyan dafa shoulder shi tayi Wanda yasa yazid Sauri daga kanshi ya kalleta tare da watsa mata wani irin irritating look Sannan yace
"Do you want to loose us as your customer?..." Ya tambayeta babu alaman wasa cikin muryan shi, da Sauri yarinyan ta dauke hannun ta tana kallon inda madam mai wurin ke zaune don kar taji don tasan hakan NA Iya zama matsala, sultan kam sai dariya yake yana cin abinci,
"No sir..." Yarinyan ta amsa mashi,
"Then stop all this...we're not here for gals...we are here to eat...so if you don't want to loose us then stop it..." Yafada yana bugun table din da karfi Wanda hakan ya jawo hankalin wasu costumers garesu, yana kaiwa nan ya mike, da Sauri madame ta yo wurin shi amma bai tsaya ba ya nufi kofan fita, da Sauri babban matar ta tardoshi tana cewa
"Sorry... What's the problem?..." Ta tambayeshi ahankali, afusace ya juyo yana cewa
"Tell your gals to stop disturbing us...we only come here for food... Nothing else..." Yafada Sannan ya fita, kai Kawai sultan ya girgiza ya tashi tabi bayanshi, ita Kuma madame ta balbale yarinyan tana cewa
"Daga yau kar ki kara zuwa wajen wannan Hausa boys ...kinji ko?.." Ta fada mata cikin yarensu na Igbo.
Yazid kam motanshi ya shiga shima sultan yashiga nashi ya bi bayanshi yana cewa
"Ko rabi abinci NA banci ba...mtwsss...".
Gaban wani medium restaurant yazid yayi parking shima sultan parking yayi, fitowa yazid yayi ya kalli sultan daya nufoshi,
" why did you follow me?.. Ai kai kana jin dadin abinda suke maka...you shouldn't have followed me..." Yafada fuskan shi daure, tsoki sultan yaja,
"Wallahi kana da matsala... Kaga we are all Muslim amma kai you are always taking things to high... Gaskiya wannan abun da kake bai dace ba..." Sultan ya fada mashi ranshi bace, kallon up and down yazid yayi mashi
"Wato kam abinda nake bai dace ba...kana barin yarinyar da ba matarka ba tana taba ka....well is your life..." Yafada yana nufan hanyan restaurant din bayanshi sultan yabi da harara,
"Kai dai Kawai you are sadist... In ba haka ba don yarinya ta tabani sai ya zama iskanci nayi daita?..."
"Ai daga yanzu ban Kara zuwa wannan restaurant din..kai dake jin dadin abinda suke maka sai ka cigaba da zuwa wurin..." Ya fada nashi ataikace, dariya sultan dake biyedashi kaman bindi yana cewa
"Am really laughing in Swahili...kai dai Kawai kace 8k per plate of food is too expensive for you shiyasa kakeson chanza wuri..." Wani irin bazwaran dariya yazid yayi yana cewa
"Kaima kasan ba haka bane don ko ban aiki a CBN common 8k a plate na abinci bazai gagareni ba....amma don't worry Allah ya kawoka Kano lafiya zakasan ba da CBN nake takama ba...." Dariya sultan yayi Yana cewa
"Oho dai...kai zaka biya kudin duk abinda naci..." Inji sultan
"Wannan ba case bane..." Yazid ya fada adaidai lokacin da aka bude mashi kofan restaurant din suka shiga tare.
Wannan shine kaidan yazid, baya dauka lack of moral character, ko gidan su ansan da hakan, din duk yanda kannanshi ke jin dadin rayuwa da yazo gida komai nasu yake tsayawa don dole su dawo gidan by 8pm ko su kwana waje, alhaji wato babanshi yana sonshi saboda wannan halin nashi, haka Hajiya babba wato mahaifiyarshi hakama Hajiya karama kishiyar mamansu, amma yaran gidan especially shahid da Sharif basuson zuwan shi don yana slowing rayuwan su kaman yanda suke cewa, amma yan Matan gidan irin su Zainab da yusra tare da Maryam NA sonshi kaman lollipop, likewise yan yaran gidan marzuq, mimata, ihsan da Ameera suma basu wasa da shi they love him so much don gani suke duk sun fi sonshi fiye da kowa,. Yazid ne babba a gidansu, sai da akayi shekara takwas da haihuwanshi Hajiya Bata kara haihuwa ba sai alh ya kara aure wanda month din da alh ya kara aure Hajiya babba ta samu cikin shahid itama amarya ta samu cikin Sharif wanda hakan yasan ake kiransu da twins from different mothers, saboda kamaninsu daya da alh, Kuma komai masu iri da har tsawon Sannan behavior dinshi NA rashin ji is the same, don ko da wasa Hajiya babba Bata isa ta siyawa shahid abu bata siyawa Sharif ba,
Bayan shahid Hajiya Bata kara samun haihuwa ba saida Hajiya karama ta haifi yusra da Maryam Sannan Hajiya babba ta samu cikin Zainab, atakaice dai yaran Hajiya babba 4 yazid, shahid, Zainab sai auta marzuq ita Kuma Hajiya karama nada 6, Sharif, yusra, Maryam, mimata ihsan sai auta Ameera. Zaman su is very lovable saboda ko kadan alh bai basu room din kishi ko wani abu makamancin wannan ba, he make all of them feel special don duk lokacin da yake tare da daya yana mantar da ita wata kishiya, zai nuna maki babu kaman ki so kowacce gani take yafison ta alhalin ba haka bane yana sonsu daidai amma fa bai wasa da Hajiya babba saboda karamcinta.
Yau suna zaune falo Hajiya babba tare da Hajiya karama kowacce taci ado cikin expensive swiss lace little brats of the house NA wasa cikin tsakiyan falo kaman yanda su Sharif ke kiran marzuq ihsan da Ameera kenan,
Hajiya babba kam tamkar carbon copy NA yazid don komai nasu iri daya har red lips dinta. Wata matace dauke da yar paper da pen hannun ta da alaman list take, Hajiya babba kallon Hajiya karama tayi
"Ni iyakan abinda nakeson ayi kenan... Ki fada naki..." Tayi directing maganan ta to Hajiya karama,
"Ni dai ayi dinner.. Ko Kuma party till dawn..." Tafada tana girgiza kirjinta, da ganinta irin civilised women din nan ce, itama ta hadu ba kadan ba, dariya Hajiya babba tayi
"Kinsan Dan naki..Yana iya cewa bai attending..." Inji Hajiya babba,
"Kam har ya isa?.. AI bai isa ba...first wedding da zaayi a family din isa bala should be the talk of the nation..." Hajiya karama ta fada, kallon Matan dake zaune tsakiyan su tayi Sannan tace
"Hajiya wedding planner...kiyi adding party till dawn...." Shuru tayi ta kalli kofan da aka bude, shahid ne ya shigo ya zauna gefen Hajiya karama don mostly sunfi yi daita saboda Bata fiya hanasu duk rashin jin da zasuyi ba, baki ta bude zatayi magana shima Sharif ya shigo ya zauna dayan side din Hajiya karama, Hajiya babba kallon su tayi ta saki murmushi tare da girgiza kai, Hajiya karama tacigaba dacewa
"As I was saying before my angels interrupt me...kiyi planning big till dawn party..." Wannan irin shewa Sharif da shahid sukayi tare da manna mata kiss a both cheek dinta
"That's why I love you little mom..." Inji shahid don haka suke kiranta da little mom, dariya tayi tana lumshe idanuwa don jindadi,
"Wallahi haka ya kamata ayi Kawai..." Inji Sharif, Hajiya babba dariya tayi tana cewa
"Ai kunsan da Kyar Zai yarda...kun San halin yayan naku..." Daure fuska sukayi shahid yace
"Big mom..Kawai ki fada mashi yayi zaman shi Chan abuja in yaso in an gama bikin sai ni da Sharif mu saka matar a mota mu kai mashi..." Yafada babu wasa,
"Ai hakan Kawai zaayi...zuwan shi ma bai da amfani..." Inji Sharif,
"Kunci gidanku... First son dina kuke cewa hakan?... Zanci ubanku wallahi kunsan halina sarai..." Hajiya karama ta daka masu tsawa, shuru sukayi din sun San tana Iya birkice masu yanzu, Hajiya babba dai kallon su Kawai take with adoration, tana tunanin lokacin da akace zaayi mata kishiya komai nata tsayawa yayi saboda bakin ciki amma yanzu kam kullum cikin hamdala take da Allah ya hadata Dana gari,
"Kuma ki hada mana get together NA mothers Kawai..." Inji Hajiya karama, matar da aka kira da Hajiya wedding planner sai rubuce2 kawai take, duk abinda aka fada sai ta rubuta, sai da aka gama fada mata komai da zaa bukata sannan tace
"To zanyi listing komai Sannan in aiko maku da bill..." Inji Matan
"Wannan babu case..." Inji Hajiya karama dake magana tamkar danta zaayiwa biki, matar mikewa tayi Hajiya babba da Hajiya karama suka bi bayanta, har bakin motan Matan suka rakatq Sannan suka komo cikin part din Hajiya babba don most of the time nan suke zama suci susha, har yan yaran ma basu zama a dakin wasansu sunfi son su kwaso kayan wasansu su dawo part dinta Kuma bata hanasu tunda da akwai masu aiki da zasu gyara waje ko sun Bata.
Falo suka dawo suka zauna suna listing wayanda zasu gayyata din kar lokacin ya kara matsowa su rikice, Hajiya babba NA fadan sunayen mutanen itakuma Hajiya karama NA rubutawa cikin iPad dake hannun.
Sai daf da sallan ishai su dija suka dawo daga tallan daman kusan kullum haka suke dawowa saboda sai bayan sallan asar suke tafiya, agajiye ta shigo gidan ba ko sallama ta shiga dakin ta tarda ammi zaune su binto suna bacci kan tabarma, ajiye ruban tallan tayi da karfi ta zauna kasa gaban ammi
"Sannu da dawowa..."
Ammi ta fada mata tana cire gammo daga kanta,
"Yauwa..." Ta fada tana kallon su binto dake bacci,
"Har sunyi bacci?.." Ta fada har lokacin Bata bar kallon su ba,
"Yan rigima sunyi bacci...ya kasuwa?..."
"Lafiya lau..." Ta amsa mata tana kwanciya kasan inda take,
"Madalla..."
"Ga kayan da kikace in sayo nan cikin roban,...." Ta fada tana nuna Roban data ajiye
"Yauwa yar albarka..." Ammi ta fada tana jawo roban gabanta tana kallon abubuwan da dija ta sayo, dija gyara kwanciya ta tayi yanda zata Iya dauko kudin dake daure a haban zaninta, daga kwance ta fara kunce daurin ta dauko kudin
"Ga sauran...dari biyar ne da ashirin.. NA sayi awara ta talatin cikin kudin..." Ta fada tana mikawa ammi kudin
"To dijata...nagode kinji...dafatan babu Wanda yayi maki zancen banza yau?..." Daga kwance ta girgizawa ammi kai
"Yau ban shiga garejin ba...cikin garin dauran na shiga kuma na saida duka...."
"To alhamdulillah...." Ammi ta fada tana jin dadi, ammi mikewa tayi ta dauki roban ta ajiye shi gefe
"Ammi gobe Dan Allah a kai gero injin... Wallahi marata ke ciwo...." Tafada tana Dan dafa maranta, ammi ajiye roban tayi ta dawo ta zauna
"To sai a kai injin din..amma ki kokarta muyi surfe mu wanke don mu bawa awaki su sha..." Dija turo baki tayi tana cewa
"Ammi ni marata ke ciwo...irin ciwon da yayi min wancan lokacin yake yi min..."
"To kilan bakon watanne zai zo..." Sai lokacin dija ta tuna da watan da ya gabata ta fara ganin jini Wanda ammi ta shaida mata cewa alaman girma ne.
"Wai ammi duk wata sai nayi wannan abun?..ni wallahi banason shi...." Tafada hannun ta biyu kan maranta,
"Ai lalura ne Kuma Allah ne ya dorawa mata Kuma ba din bayason mu ba...wasu ma sai sun nema amma basuyi...don haka ki bar cewa bakison shi...."
"To ammi..."
"Tunda bai kaiga zuwa ba kije kiyi sallan ishai...." Dija ta fi minti biyar kwance Sannan ta mike ta fita ta dauki buga ta shiga kewayen su da aka zagaye da buhu. Few minutes later ta Fito tana cewa
"Ammi yazo..." Tafada da karfi, ammi murmushi Kawai tayi Bata amsa mata ba.
[3:12PM, 3/20/2018] 鈥�+234 806 125 0020鈥�: 馃挏馃挍鉂ゐ煐ゐ煉欚煉�
NA CUCE TA
鉂ゐ煉滒煉涴煐ゐ煉氿煉�
庐zuwairat(ummu Maryam)
3鈨�
Da Sauri ta dawo cikin dakin tana cewa
"Ammi NA ganshi..." Tafada cikin jindadi
"Naji...wai in tambayeki...murnan me kike?...." Ammi ta tambayeta tana kallon ta,
"Babu komai..." Ta fada ahankali,
"Hmmm NA gane Kawai don bakison yin sallah ne...to kiji tsoron Allah... Maza ki tashi ki tafi makaranta....nasan an zauna tunda anyi sallan ishai...." Ammi ta fada mata, nan ta kara Bata rai tana cewa
"Ammi NA gaji..." Bata idaba ammi tayi mata dakuwa
"Kinci mai garinku...maza ki tashi ki tafi..." Ammi ta umarceta, bata fuska tayi kaman zatayi kuka ta fara cewa.
"Ammi gasu binto basu je ba?...ni ki bari sai gobe.. " ta fada kaman zatayi