You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
ta dora bisa kai tana kuka,
"Khadija dan...Allah... Wake up...." Yafada yana girgiza ta da karfi amma ko motsi batayi, mutane taruwa sukayi suna kallon su, doc daya bugeta ya rike yazid don ya samu daman duba dija amma wani naushi yazid ya kai Mashi Wanda ya tsorata shi yayi saurin ja da baya,
"Khadija... Pls....don't do this to me....I will be miserable for the rest of my life...." Yafada yana dorata kan kafanshi at the same time yana kuka kaman ranshi zai fita, duk mutanen dake tsaye babu Wanda yayi kokarin taimakawa, doc daya bugeta nason taimakawa amma yana tsoro kar yazid ya kara naushinshi, yazid tsaya kallon yanda cikinta ke motsi yayi ya daga kai yana kallon faces din mutane yana cewa
"Dan Allah Ku taimaka min....pls help....." Da sauri doc din nan ya zo ya rike wrist dinta for a while sannan yace
"Ka dauketa muje...." Inji doc cikin sauri, da sauri yazid ya mike ya dauketa, ammi da dasu binto babu abinda suke sai kuka, bin bayan yazid sukayi shi kuma yazid na biye da doc, sai sauri yake amma ko gabanshi bai kallo sai dija, yana tunanin yanda ta koma kaman baitaba
"Me zanyi maki in biyaki for all this pain...." Yafada yan kuka, kallon yanda cikinta ke ta motsi kawai yake, bai ankaraba yaji zaa amsheta daga hannunshi, sai lokacin yaga nurses da gadon da ake tura mutum, baisan ya akayi sukazo ba, babu musu ya dorata kan gadon aka fara turata amma yana rike da hannunta, goshinta daya kumbura ya kalla.
Motsin dan cikinta looks so visible da ko daga nesa kana Iya hangen yanda cikin ke motsi kaman zai fito
Doc kallon ta yayi for ya moment sannan yace
"Take her to the labour room..." Hankalin yazid ne ka Kara tashi, baisan lokacin dayace
"Its just seven months....", doc dai baice komai ba amma deep down yana tunanin wanne relationship ke tsakaninshi da ita don they look so different, babu alaman dangantaka tsakaninsu don duk Wanda yagansu yasan they are from two different part of class and level amma yanda yake nuna damuwanshi is questionable to him
Inda dija ta kwana for some days aka shiga daita only she was unconscious, tsaye yazid yayi aka shiga ciki daita, ammi dai kuka yaki tsayawa, yazid goge face dinshi yayi ya fiddo wayanshi dake cikin aljihunshi Wanda ya kashe tun 12am na jiya kuma bai kara kunnawa ba saboda kar mufida ta tisashi gaba. Kunnata yayi sannan yayi dailing number Salem, after like ringing biyu zuwa uku yayi picking yana cewa
"Wai me yayi zafi da zaayi bikin lil brothers dinka amma baka zo ba?.... Gaskiya baka kyauta ba... Dazun saida dad dinku yayi min magana bayan daurin auren... Karya nayi Mashi nace kuna port...." Duk maganar da yake yana fada cikin annoyance ne amma gurin yazid shine ya kai aya sannan ya fada Mashi abinda yake son cewa, yana jin shuru yafara cewa
"Na ganta!..." Ya fada in one word,
"Wa?..."
"Khadija..." Ya amsa Mashi cikin sanyin murya , dasauri Salem ya saki ajiyan zuciya tare dacewa
"Ina?..."
"A jos...."
"Da akwai cikin?..." Ya tambayeshi full of excitement,
"Yes....amma she have an accident while running away from me...." Yazid ya fada muryanshi na rawa,
"Subhanallah!!....how is she?..."
"Yanzu anshiga daita ciki....salem... Na cuceta....you need to see her....ta koma kaman baitaba....I don't know what made me do it...." Yafada yana kokarin sake kuka saboda yanda heart dinshi keyi Mashi zafi,
"Rabo...kaddara...destiny...." Salem ya amsa Mashi in a calmly manner
"Yanzu me doc yace?... Hope it's not serious?..."
"Bata motsi....amma naga cikin na motsi...ka tayani adua...I don't want to loose anyone of them.... Inason in biya Khadija for the pain and agony I caused her....kuma inason abinda zata Haifa....nasan ana iya stigmatizing dan ko yan...amma ba laifin shi ko ita bane....it's all my fault... The child deserve to live...." Yafada in a regretting manner at the same time hawaye na gagarowa daga idonshi,
"Insha Allah the child will live...babu abinda zai samu both of them.... Ka kusa zama dad ko..." Salem ya karasa maganar da zolaya, yazid zai bude baki yayi magana yaji call ya shiga, dubawa yyi yaga small mom,
"Bari zan sake kira...mom is calling..."
"OK..pls give me updates about her..." Inji Salem
"OK..." Kawai ya fada yayi picking call dinta, itama balbaleshi ta farayi kan meyasa baizo daurin auren su Sharif ba, saida ta kai aya sannan ya fada mata ya gan dija
"Kai alhamdulillah...." Ta fada with excitement kaman baita ke fada few seconds ago ba, dan murmushi yayi sannan ya fada mata halin da ake ciki,
"Inna lillahi waina ilaihi rajuun!....hope it's not bad?..." Fada mata komai yayi
"OK...ka kula daita...zan yiwa anty magana don she's so angry..." Ta fada Mashi,
"OK nagode...." Ya fada yana juyawa don gani Wanda ke tahowa, ganin doctor ne yasa yayi saurin katse wayan tare da nufanshi
"Doctor... Ta tashi?..." Ya tambayeshi,
"Yes...pls waye mijinta?..." Shine tambayan da doctor yayiwa yazid Wanda har su ammi sunji Sadda kai ammi da family dinta sukayi while yazid ya kasa replying question din doc,
"Pls ya jikinta..hope its not bad?....." Ya sake tambayanshi,,
"Not that bad...few injuries ne...." Ya amsa Mashi sannan ya sake cewa
"Waye mijinta?..."
"Ni....." Ya amsa Mashi kanshi kasa, kallon up and down doc yyi mashi, yafi minti biyu yana kallon shi inda shi kuma yazid bai yarda suka hada ido na,sai da ya gama kallon sannan yace
"Follow me..." Ya fada Mashi atakaice tare da juyawa, jiki ba kwari yazid ya bi bayanshi, wani office dake kusa da labour room doc ya shiga inda wata babbar mace ke zaune, yazid na daf da shiga yaji kaman dija na cewa
"Wayyo ammi cikina...wayyo mutuwa zanyi...." Da sauri yazid ya shiga cikin office din yana cewa
"Kaman kukanta nakeji....pls what's happening?..." Ya fada cikin tashin hankali,
"Sit...." Matar dake cikin office ta fada Mashi tare da nuna Mashi seat dake opposite to Wanda ya banke dija.
"As a result of event daya faru..ta shiga labor...." Aikam sai ya dafa kai
"Labor doc...its seven months... Anya babyn zai rayu?...." Ya fada kaman zaiyi kuka, kallon juna sukayi don basu yarda He's responsible for the pregnancy ba...kawai suna ganin He's lying,
"Ai seven months na da...baka taba jin an haifi bakwaini ba?... Kawai saidai maganar incidents daya faru...amma da pregnancy is OK..." Inji matar, yazid shuru yayi ya rasa abun cewa,
"So zaa sayo kayan haihuwa...although bamu amsan irin wannan haihuwan but due to the circumstances we will help...." Matar ta sake fada Mashi, yazid dake zufa dag red eyes dinshi yayi ya kallesu
"Pls...Ku cire abinda ke cikinta....I don't think tana da strength da zata haihu...." Ya fada voice dinshi na cracking, kai matar ta girgiza,
"Its a government hospital.. We don't work that way..." Ta fada Mashi,
"Then zan kaita private hospital..." Ya fada yana mikewa, da sauri doc yace
"Ina da private hospital... In that case mu kaita chan..." Ya fada yana mikewa, daman already yazid tsaye yake, fita yayi ya sanar da ammi yanda sukace, fadawa doc din yayi suyi gaba yana biye dasu.
"Who will pay the bills..." Doc ya tambayeshi,
"Money is not the problem..." Inji yazid, cikin mota gidan su Salem ya shiga ya zauna baya, gudun kar dija ta kara ganinshi ta rude, few minutes later aka fito daita zaune kan wheelchair, sai kuka taka tana cikinta, tana ganin ammi ta mika mata hannu, da sauri ammi ta mike taje inda ake turota ta rike mata hannu, duk ta manta da aladansu, babu abinda ke cikin ranta sai tausayin dija,
"Ammi cikina....cikina...marata..." Kawai dija ta take fadi, yazid na kallon ta daga inda yake zaune cikin mota, cikin mota doc aka sakata su ammi suka shiga suka bar wurin, yazid ya umarci driver yabi bayansu.
Kawai adua kawai yake kar wani abu ya sami dija he can bear loosing the child amma banda dija. Shi gani yake the child won't make it amma yana da hope cewa he will have any number of kids he want in the future
"Pls make it...." Ya fada under his breath, kiran mufidane ya shigo wayan, da sauri yayi picking yana cewa
"Baby am so sorry I lied... Kiyi hakuri....pls don't be offended..." Ya fada mata in a whisper don kwantar mata da hankali,
"What can I say...kawai kullum sai...." Bata idaba ya katseta dacewa
"Baby ki yafemin....pls don't say anything OK..." Ya fada mata cikin sanyin muryan dayasan she can't resist,
"OK...yanzu kana ina?...." Ta tambayeshi, shuru yayi for a while sannan ya fada mata exactly abinda ke faruwa, cikin karfi hali tace
"To Allah ya bada saa...." Zai bude baki yayi magana yaji ta katse wayan. Murmushi kawai yayi.
Achan family house duk cikan dayayi sabida yan taro bai hana Hajiya karama kebewa da Hajiya babba ba, bayan sun Shiga inda babu kowa, sai Hajiya karama ta fadawa Hajiya babba exactly abinda yazid ya fada mata, shuru tayi hawaye na taruwa idonta,
"Allah yasa kar dan yazo da rai....in yaso sai ya aureta batare da ansan exact abinda ya faru tsakaninsu ba...." Inji Hajiya babba, idanuwa Hajiya karama ta zaro
"Aa wallahi...Allah yasa yazo da rai...yo haka Allah ya kaddara....besides ni fa ban ga wani aibun abinda ya faru ba...ai duk Muslim na kwarai yasan kaddara...yazid dai ba dan iska bane balle ashe daman ya saba....kuma duk Wanda yaga yanda ya damu yasan ba halinshi bane...don haka ni dai wallahi yazo da rai koni da raineshi...." Ta fada in I don't care manner kuma she's serious,
"Wai ke ko kadan baki tunanin abinda mutane zasu ce?...." Inji Hajiya babba, shoulder ta daga
"Who cares....kowa na da nashi cockroach in thea cupboard...so kowa yaji da abinda ya dameshi...." Ta fada sannan ta dafa shoulder Hajiya babba da Duk ta susuce
"Anty ki kwantar da hankalinki.... In mace CE ba sai taje waje aure ba balle ayi mata surutu...cikin dangi zaayi mata miji...in kuma na mijine babu case don for as long as he's rich no body cares...." Yanda take magana yasa Hajiya babba dariya, dan hararanta tayi
"Wato ke har kin gama plan din komai...." Ta fada in a funny way,
"Yo me yafi raina..." Ta fada tana dariya.
Bayan kaman minti ashirin suka isa hospital, hospital din is not that big but it is unique and beautiful, da sauri nurses din wurin suka amsheta deyeka doc ya sanar dasu, fita yayi daga cikin motan yq nufi motan da yazid ke ciki, shima yazid fitowa yayi ya nufoshi,
"Zaa bada deposite of 80k...in an gama kafin a sallameta zaa bada balance of 70k,...150k muke cs anan..." Inji doc, yana kiran 80k yazid ya fiddo wayanshi, few seconds later ya daga kai yana yace
"Pls I don't have cash on me...kuna amsan transfer?..."
"Yes...no problem..."
"OK...pls account number..." Inji yazid, nan take ya karanto Mashi ya saka
"Bank name pls..." Inji yazid, fada Mashi yayi, ko minti biyu baiyi ba yayi receiving alert na 170K, kallon shi doc yayi zaiyi magana yazid ya katseshi dacewa
"20k din na wanda nakeson ka duba min ne....that woman...." Ya fada yana ammi data rafka tagumi,
"OK..." Doc ya fada ya juya da sauri. Ciki ya shiga, kafin ya shiga har an shanzawa dija dake ihu kaya, nan take aka hau aiki.
A waje kam ammi mikewa tayi don tasan bai kamata ace tana zaune nan dija ta haihu ba, magana tayi da yar uwarta kan su tsaya da dija. Ahankali ta zo ta wuce inda yazid ke tsaye,
"Ina zaki kuma?..." Ya bi bayanya yana tambayan ta,
"Gida...." Ta amsa Mashi atakaice,
"Dan Allah ki tsaya a dubaki..." Ya fada mata cikin sanyin murya, kai kawai ta girgiza sannan tace
"Aa...."
"To bari ya maidaki..." Ya fada yana juyawa, fadawa driver yayi a kaita inda ya dauko ta.
Driver zuwa yayi da mota inda take tsaye ta bude ta shiga. Yazid kallon agogon hannunshi yayi yaga kusan 5:30, sai lokacin ya tuna baiyi sallan asr ba. Dan shiga cikin yayi yaga har lokacin doc bai fito ba, fita ya karayi yana tafiya yana tunani, har yaje bakin titi bai Sani ba saida wani mai mashin ya kusa bugeshi sannan ya dawo sense dinshi.
Bayan thirty minutes ya dawo direct ciki ya shiga ya nufi reception, nan wacce ke nan ta nuna Mashi office din doc, jikinshi na rawa ya shiga ciki, kallon face din doc yayi ko zai iya understanding halin da ake ciki, murmushi ya sakarwa yazid tare dacewa
"Congratulations... It's a boy..."
💜💙💚💛❤🧡
Sweethearts kuyi hakuri am soooooo busy ne shiyasa kuke jina shuru. Sorry for waiting too long and pls don't forget to vote and comments.
NA CUCE TA💜💙💚💛❤🧡®Zuwairat (ummumpls am)3⃣0⃣ _Follow me on:_ *Wattpad @ummumaryam29* *Email:Zuwairat.nuhu@gmail.com* *IG: zuwairatummumaryam* *Website:Www.ummumaryam.com* *And also join my new Facebook group: Zuwairat ummumaryam and Zuwairat ummumaryam page.* *Snapchat: ummumaryan29*Baki yazid ya bude yana sucking maganar doc into his brain, ganin shuru yayi yawa yasa doc cewa"Yes...its a boy..." Yafada yana kallon how still yazid is, ahankali yazid ya daga kai ya kalli doc"Babyn lafiya lau?...I mean...lafiya dan yake?..." Yafada sounding out of word, "Yes....he's alright...""Khadija fa?.." Ya tambayeshi still notbelieving his ears,"Itama tana lafiya....sai dai..." Da sauri yazid ya zaro eyes dayaji saidai"I want to ask you...pls ka fadamin gaskiya..." Inji doc,"Ina son sanin relationship dake tsakaninka da wannan yarinyan..." Doc ya tambayeshi"She's... My...wife....pls can I see the boy now?..." Ya fada don kar doc ya sake yi Mashi wannan tambayan,"Eh ana cleaning dinshi ...babu kayanyaro amma daman muna ajiye wasu in case if emergency..."",OK...." Yazid ya fada yana mikewa jikinshi har rawa yake."Pls sit...." Doc ya kara umartanshi, da sauri ya koma ya zauna kaman wani Mara wayau "Pls wane dalili yasa ka bar pregnantgal haka?.... Indai kai mijinta ne as you proclaim... Don ni har yanzu banida assurance da gaske kake...." Inji doc, yazid shuru yayi yana tunanin abinda zai fadawa doc don ko kadan bai iya fada Mashi gaskiyar alamarin,"Guduwa tayi daga gida as a result ofaljannu da suka shafeta....yau na ganta...." Yayi Mashi karya which is written all over his face don bai iya karya ba,"OK..amma she will need a medical care..." "OK...pls can she fly out of the country?..." Ya tambayeshi cikin ranshi yana aduan yace yes"No bazata iya ba yanzu... Amma don't worry.... Wannan hospital is among the best in town...zamu bata dukkan kulawan da ya kamata...." "OK...do...pls....can I see the baby now?..." Ya sake tambayanshi, mikewa doc yayi shima yazid ya mike, har doc ya kusa shiga dakin dajaririn yake sai yazid yace"Pls tana nan dakin?..." Ya tambayeshi gabanshi na faduwa,"No...tana postnatal... " doctor ya fada yana bude kofan dakin. Nurses biyu ne zaune sai gadajen newborn kaman ten, babu newborn sai na Yazid, doc na gaba har wajen gadon yaron, da sauri yazid ya tsaya gaban gadon yana kallon yaron ko kiftawa baiyi,"Doc. He's tiny... Are you sure he's alright?..." Ya tambayeshi yana taba small cheek din yaron,"Ai bakwaini ne...kuma from all indication the mother have not been feeding well.... Amma in yana samunkulawan daya kamata...he will group in no time...." Doc ya fada Mashi Still yazid bai gamsu da maganar doc ba, dan daga white towel dake jikinshi yayi yana karewa tiny boy dinkallo,"Pls doc a kara dubashi....he don't look fit...banga ya motsa ba...." Ya fada yana shafa hair din yaron, cikin ranshi kam yana tunanin rabon wannan yaron ne yasa ya aikata abinda bai taba aikatawa ba"Am assuring you...lafiyan yaron lau....kawai ka bashi few months ka gani..." Inji doc, ganin irin kallon da yazid ke wa yaron yasa shi daukan yaron"Will you like to hold him?..." Inji doctor, ahankali yazid ya gyada Mashi kai tare da mika Mashi hannu, ahankali doc ta dora Mashi yaron dake motsi, yazid ji yayi kaman he's dreaming, wai yanzu wannan danshi ne. Kallon tiny legs din yaron yayi with excitement. "Yanzu me dame suke bukata?...am new to the whole system..." Inji yazid,murmushi doc yayi"First zaka kwantar da yaron....then kayo shopping baby wears...sai kayan shayi da matarka zatasha...saika fadawa masu kula dasu suzo...." Inji doc dake amsan yaron daga hannun yazid don dagani bai Iya rika yaro ba,"Pls doc zan Iya samun nurse da zai dinga kula da both of them kafin su bar hospital?.... Zan biya..."_ya fada don ko kadan baison yan kauyensu ammi suce zasu kula da dija ko new boy dinshi." OK..." Zan nemo maka daya cikin nurses dina..." Inji doc daya mayar da yaron kan gado, Bayan doc ya tabbatar yaron yayi balance ya juya yazid yabi bayanshi yana waigawa yana kallon yaron, har tuntube ya kusa yi saboda yanda yake waigawa, "Doc why ba zaa kaishi inda take ba?../""Because tana bacci..." Doc ya amsa Mashi, ji yayi he needs this opportunity ya ganta koda na minti biyar ne don bazaiyi gangancin shigadakin in idonta biyu ba."Can I see her?..." Ya tambayi doc,"Yes....tana wancan dakin.." Ya nuna Mashi wani right handside door da aka rubuta mother resting, wucewa doc yayi office din shi shi Kuma yazid yaje bakin kofan. Da kyar ya samu courage din bude kofan, hangota yayi kwance, an rufeta da sky blue kyalle kaman yanda akewa yan operation, hands dinta biyu kan cikinta, ahankali ya shiga dakin bayan ya maida kofan ya rufe, bakin gadon ya isa yana kallon ta from head to toe, kallon how dirty her hair and feet is kawai yake, hmmm nace don ma tayi wanka yau kenan, face dinta ya kurawa ido yana tunanin how she survived for almost two months on the street with pregnancy. "Am sorry... Daga yau baki kara shan wahalan rayuwa....I promise you that...." Ya fada in a whisper, kallon yanda kirjinta ya kara cika yayi as a result of ciki, gira daya ya daga ya juya ya bar dakin, yana fita yaga binto da yar uwar ammi, nan ya sanardasu ta haihu na miji kasancewan doc bai CE masu komai ba. Tsalle binto ta dingayi while ita matar bata nuna wata alaman murnaba, yazid ya ga the look on her face"Ku kwantar da hankalinku...I won't let her face any of your stigmatizations...." Ya fada cikin ranshi yana dailing number Hajiya karama don ita kadai yake Iya fara fadawa. Bayan tayi picking ya sanar da ita, har da guda tayi saboda murna,"Yanzu wake kula da ita?..." Shine tambayan da Hajiya karama tayi Mashi,"Babu...amma nayiwa doc maganan ya samo min masu kula da ita kafin asallameta insan abunyi...." Yazid ya amsa mata,"Wane irin masu kula alhalin ga wayanda keyi mana nursing yara?... Zan turo daya gobe...." Inji Hajiya karama, "Ai mom kafin goben dole a kula dasu....Kuma kinsan ba lallai bane dad ya amince da hakan...Kuma banason a sani da yawa...." Tsoki Hajiya karama taja,"Naji a kawo mai kula dasu just for tonight... First thing in the morning zanturo doc fatima,...sannan don't worry ba dole bane sai sun sani abinda ya faru...iyaka tayi aiki a biyata...." Ta amsa Mashi sharply, "I love you mom...." Ya fadawa Hajiyakarama saboda yanda take nuna damu a duk alamuranshi,"Keep quite..." Tace Mashi, dariya yayi sannan yace"Mom...pls banason khadija ta shayar dashi.. I possible ya sha babyformulars...""Why?..." Ta tambayeshi, shuru yayi for a while sannan yace"Cos hakan zai zame mata more stress... I don't want her to waste anymore time...I want her to go to school..." Ya fada yana jinginawa da wata bushiyar umbrella dake compound din hospital din."Hmmm kana ganin hakan ya kamata?... Kasan breastfeeding yanasaka more shakuwa tsakanin da da uwa...." "I know mom...amma I don't want herto go through that right now...she's too young for all this...." Yafada idanuwanshi lumshe,"OK if you say so....sai a fara bashi ko sma gold 1 ne kafin ayi Mashi ordering na almarai nuralac...." Hajiya karama ta fada mashi, zai bude baki yayi magana tayi saurin katseshi dacewa"Kai kyaleni inje in bada good news...." Tana kaiwa nan ta katse wayan. Murmushi kawai yayi sannanyayi dailing number Salem, same story ya bashi, shima ba karamin dadi yaji ba, he feels so excited har da cewa"The latest dad in the world...." Inji Salem cikin zolaya"Hmmm ka manta he's out of wedlock?..." Inji yazid cikin sanyin murya,"Mudai wannan bai hanamu shashewa next week Saturday...." InjiSalem, hira suka dan taba sannan yazid ya je inda yayi sallan asar yayi na magrib,, bakin gate din hospital yakoma ya zauna yana jiran dawowan. Bayan kaman minti ashirin da zamanshi ya dawo da wasu mata guda biyu da alaman still family din dija ne, bayan ya ajiyesu shikuma ya shiga mota sukayi gaba. Gaban katuwar plaza suka tsaya da taimakon driver, dukda darene ammawurin kaman rana, bangaren baby wears suka hau bayan ya tambayi wani ya nuna masu wurin. Jugum yayi yana kallon kayan wurin ya rasa mai zai saya, kallon wasu mata dake siyayyan kaya yayi, "Dan Allah Ku tayani zabar abubuwan da jariri zai bukata..." Ya fadawa Matan bayan yayi masu sallama sun amsa. Nan suka fara zaba Mashi kayan sawa Dana amfanin, har dasu bombom baby perfumes kala2. Gefe daya ya tsaya saida suka gama sannan ya kwace kayan da taimakon yan aikin wurin zuwa inda aka duba kayan. Komawa yayi inda ake sayarda kayansawa nan ya dinga kwasan gowns not minding the amount da zaiyi costing, daga nan ya je bangaren, shoes ya dauki simple but expensiveslippers guda biyar sai, yana tura kayan yaje inda mayuka suke, ya rasa Wanda zai saya mata amma yasan da makari mufida ke amfani and yayi mata kyau, hakan yasa shima ya dauki makari da sabulunta ya zuba cikin trolley da yake turawa, daga wannan sai perfumes da hair shampoo don har yanzu bai manta how silky and shiny kanta yake ranar da yayi molesting dinta ba. Yana turawa ya je wajen beverages da kayan malaki, katuwar nido da Ovaltine ya dauka gida bibbiyu sannan ya dinga sayan su juice da kayan dadi kaman ba gobe, sai wajen9pm ya gama before then sultan ya kirashi don jin why basu dawo ba haryanzu sai yayi Mashi karya da hira yakesha inda yaje amma ya kusa dawowa.Bayan ya bada credit card dinshi aka zari kudin masu yawa sannan suka saka Mashi kayan a bayan booth suka koma hospital. Saida yaje wajen doc ya fada Mashi ya taimaka Mashi yayi jagora a kai kayan Kuma ya fada mata in ta farka dole tayi amfani da kayan, doc bai nemi jin dalilin hakan ba yasa masu gadi suka shigar da kayan har inda dija kekwance su Kuma Matan da binto na zaune suna jiran farkawanta. Ajiye kayan akayi Matan suka bude baki suna kallon ikon rabbi.Doc komawa yayi ya shaidawa yazid an kai kayan, sai bayan nan yazid ya kara tambayanashi kan wacce zata kula dasu, sai doc ya shaida Mashi an samu daya daga cikin nurses dinshi da zatayi wannan aikin. Dadi sosai yaji ya kara shaida Mashi kan dan Allah kar a bari a jagwalgwala yaron doc ya bashi assurance kan hakan bazai faru ba. Hannu yazid ya mika Mashi sukayi sallama sannan ya mike ya fita cikin ranshi yana cewa"Am taking responsibilities for my actions..."Da sauri ya Kuma dawowa daya tunamaganar shayar da danshi. Nan ya fadawa doc abund yakeso ko gardama baiyi Mashi ba y amince da yayi hakan, sai lokacin ya fita har cikin ranshi yana son kara ganin facedinta amma haka ya hakura likewise yana son ganin danshi amma shi ko kadan baison ganin yanda yake dan Karami. Haka ya hakura ya fita daga cikin hospital din feeling so relaxed, ya mance rabon da yaji irin wannan farin cikin, ji yake kaman an dauke Mashi wani katon stone dake weighing dinshi down. Jefa kanshi yayi bayan mota yana murmushi with his eyes closed. Kafin su kai gidan was around ten, wanka yayi yaci abinci sosai sannan yayi salla ya kwanta bayan sunyi brief hira da sultan.Dija bata farka ba sai wajen 10pm lokacin matan na zaune, sai nurse dazata kula daita dake kicingide kan kujera ita kuma binto tana kwance nan kasa, lokacin doc na shirin tafiyagida. Tana bude ido taji cikinta empty da Sauri ta fara shafa cikinta don ta manta events daya faru, ganinMatan dake zaune sai ta tuna taga amminta, then...yazid....da Sauri ta widening idanuwanta data tuna taga yazid tare da amminta da binto, sai ta tuna mota ya bugeta, daga nan ta tuna ta farka in do much pain, Then an saka ta a mota an taho daita, she remember she was screaming saboda azaba then an shiga daita wani daki