You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
zaune gefen ta, itadai mufida tunanin abinda ke damun Hajiya tayi sai kuma ta tuna kilan sai yanzu suka San abinda yazid ya aikata not knowing they is more to it. Cikin rawar murya Hajiya tace
"Kiyi hakuri kinji?... Komai mukaddari ne...haka Allah ya kaddara... Ki rike mijinki hannu bibbiyu..." Tafada tana fashewa da kuka, itama mufida fashewa tayi da kuka, ahankali Hajiya ta jawota jikinta suka bude sabon babin kuka kaman anyi mutuwa.
"Bansan irin wannan kaddara ba...ko sau daya ban taba kama yazid da wata karamin laifiba sai Kawai Ace yayi wa yar karamar yarinya ciki...." Hajiya ta fada cikin matsanacin kuka, gaban mufida yayi mugun faduwa dajin ciki, ahankali ta daga kanta daga shoulder Hajiya ta kalleta, cikin kuka Hajiya ta kalleta, surprise look dake face dinta ya tabbatar mata batasan wannan zancen ba kuma bataso ace ita ta fara sanar mata ba.
"Mom ciki gareta?..." Ta fada cikin kuka, Hajiya dafe kai tayi tana kuka,
"NA shiga uku...Hajiya gidanmu zani...ban iya zama dashi....." Ta dinga fada kaman wata zautatta, dafa ta Hajiya tayi tana girgiza mata kai,
"Don't say that....hannun ka bai rubewa ka yarda...mijinki ne kuma bazaki kishi saboda jarabawan Allah ba...kiyi hakuri wata rana zakiji kaman ba a taba hakan ba..." Tafada tana shafa bayanta, mufida kukan bakin ciki da kishi Kawai take, watanta biyar da yazid ko batan wata bata tabayiba, kullum tana fadawa mom dinta rashin batan watanta amma sai mom dinta ta fada mata its nothing wai itama saida tayi shekara uku Sannan ta samu cikin mufida, amma yanzu shine wata zata rigata haifawa yazid da ko ya
"Shege ne..." Ta fada cikin ranta, hakan yasa ta Dan saka ranta a inuwa amma still bata bar kuka ba. Tana cikin kuka bacci ya dauketa nan kan gadon Hajiya. Yazid kam yanda ya ga dare haka yaga rana. Haka Hajiya babba da Hajiya karama ma duk basuyi bacci ba.
Abangaren dija kam nan asibiti ta kwana inda yan waiting ke tsayawa, Allah ya taimaketa babu Wanda ya damu daita, kowa ta kanshi yake duk suna jiran yan uwansu su haihu lafiya kuma har garin Allah ya waye baa rasa mutane wajen ba, dija batayi wani baccin kirki ba saboda kuka da cizon sauro, tana fara ganin hasken gari mike ta dauki bag dinta, banda fitsari babu abinda ke damunta, kusa da wata mata dake zaune taje
"Dan...Allah... Ina.. Ake...fitsari?..." Ta tambayeta matar daga kanta tayi ta kalleta from head to toe tana mamakin me yasa zaa zo da irin wannan karamar yarinyan wajen haihuwa, wata kofa ta nuna mata batare data ce mata uffan ba. Da Sauri dija ta shiga cikin wurin rike da bag dinta don rike taje da bag dinta tamkar her life depends on it. Wurin babu laifi its neat, durkusawa tayi ahankali saboda yanda wani abu ke tokare mata maranta, tana fitsari tana wash, saboda yanda fitsari bai zuwa da yawa sai zafi da take ji ba don komai ba sai don tun jiya take jin fitsarin amma batayi ba sai yanzu
Tafi minti goma nan durkushe, for the very first time sai taji motsin abunda ke cikinta, dafe cikinta tayi don kara tabbatar da abinda taji amma sai komai yayi still. Kallon tap dake running tayi sai tayi tunanin why not tayi wanka tunda batasan kowa ba balle ta samu inda zatayi wanka later in the day, ajiye bag dinta tayi ta leka waje don tabbatar babu mai jira Sannan ta koma ciki ta kulle kofan, rataya bag dinta tayi Sannan ta cire kayan cikinta, tsayawa tayi tana kallon cikinta. Jikinta ta kalla da tsawun dukan ammi dake kwance bisa skin dinta. Kuka ts farayi. Tana kuka har ta gama wanka amma bada sabulu ba. Kayan data cire ta maida, bude bag dinta tayi ta koma gefe ta fiddo kudin da ammi ta watsa mata da yawa amma babu kudin kirki cikin su, duk yan biyar, goma, ashirin ne babban kudin dake ciki shine Dari biyu, ta kusa hour tana counting dinsu. Sun kai kusan dubu sha biyar, arranging dinsu tayi according to girmansu daman abinda ta sabayi kenan tun a gida. Saida ta gama ta fito tana tafiya ahankali. Bakin asabitin da akwai masu saida kayanci kala2 irin su taliya, kosai, koko da sauran su, wurin wata mkata dake soya kosai da koko ta nufa ta ajiye bag dinta ta zauna sama Sannan tace a bata koko da kosai, daman jos ba kaman sauran garuruwa yake ba, babu Wanda ya damu da ita. Nan ta zauna taci ta koshi Sannan ta koma gefe tana kallon masu harkokinsu.
Tagumi tayi tana tunanin abinda zai biyo baya, ammi ta fado mata ga rai,
"Yanzu ammi ta yafeni kenan?... Yanzu ammi bata Sona kenan?... Yanzsu ammi ta cire ni cikin yaranta kenan?..." Ta dinga tambayan kanta cikin ranta, Dan take baki tayi hawaye suka fara gangaro mata, da Sauri ta da hannu ta goge face dinta.
๐๐๐๐ค๐โค
NA CUCE TA
๐๐๐ค๐๐โค
ยฎzuwairat(ummumaryam)
2โฃ0โฃ
Don't forget to follow and vote me on wattpad @ *ummumaryam29*
_Thanks sweetie, novel am feeling your love and affection_
Ahankali ya amsa ya ajiye gefe daya sannan ya dafa chest dinshi saboda ba karamin zafi yake ji ba, gani yake kaman romon naman zai hau mashi brain dinshi, idanuwanshi su kara ja, Hajiya karama hannu tasa ta dinga shafa bayanshi ahankali Har ya samu sauki.
"Pls kasha tea..." Tafada mashi ahankali, ba musu ya dauka ya sha zuwa rabi amma da gudu ya mike ya kama hanyan bedroom yana kakarin amai,
"NA shiga uku...wannan yaron nason saka kanshi cikin matsala...." Inji Hajiya karama, kafin ya shiga bathroom ya saki amai kasa yellow kaman mai rashin lafiya. Saida ya amai da Dan tea din daya sha ya mike ya shiga bathroom ya wanke bakinshi sannan ya taka ahankali ya dawo bedroom ya kwanta. Hajiya karama ce tasa asabe taje ta goge inda ya bata, yana kwance yana kallon ta tana aikin ta, asabe kam cikin tsoro Kawai take don yanda take ganin kaman zai kamata ya danneta.
Jikinta na rawa ta gama goge wurin Har zata bar wajen ya kirata, jikinta na rawa ta juyo ta kalleshi, ahankali ya daga manyan idanuwanshi ya kalleta sannan yace
"Pls..kinga....khadija sanda tazo nan gidan?..." Yafada ahankali, surprise look ne kwance kan fuskar asabe,
"Ko baki ganta ba?.." Ya sake tambayan ta, da Sauri tace
"Tunda ta tafi..ba kara ganinta ba...." Ta amsa mashi muryanta na rawa,
"Ok..you can go..." Yafada idanuwanshi lumshe. Bayan kaman minti biyar ya mike ya fito tsakar gidansu masu gadi sai gaidashi suke amma banda wannan tsohon guda daya dake da masaniya kan abinda ke faruwa. Ko kallon su baiyi ba ya shiga part din mom dinshi, lokacin an shirya su marzuq da zasu school. Mom dinshi na tsaye rike da lunch box dinshi tana gyara mashi button din Riga, yana gani yazid ya tafi da gudu ya fada mashi, bayanshi Kawai yazid ya shafa bai daukeshi kaman yanda ya saba daukan shi ba cos da kyar yake daukan kanshi. Mom juya baya tayi yayi saurin durkusawa gabanta
"Mom...pls....forgive me...." Yafada hawaye na taruwa idanuwanshi, kokarin wucewa tayi amma ya rike mata kafa,
"Pls ki yafemin..." Yafada yana fashewa da kuka dukda muryanshi bai fita sosai . marzuq tsayawa yayi yana kallon su, horn din motan da akayi yasa marzuq barin su cike da tambaya cikin ranshi abinka da inquisitive child. Mom kwace kafanta tayi
"Laifin me kayi min...its your life.. And you have decided to live it the way you want... So ni babu ruwana...." Tafada tana kokari barin wurin, da rarrafe ya tare gabanta,
"Wallahi..mom ba halina bane...kaddara ne ya fadamin....ban taba kama hannun mace ba..."
"Amma Har ka Iya raping yar yarinya ..." Mom ta katseshi, yana girgiza kai yana cewa
"Mom sharrin shaidan ne...am sorry.. Pls...." Yafada cikin matsanacin kuka, mom goge hawayen face dinta tayi ta fixge kafanta daga hannun shi ta bar wajen, ahankali ya koma ya zauna kasa yacigaba da kuka, kofa aka bude ya daga kai ya ga mufida ce tsaye itama Sam fuskanta babu walwala, amma ganin yanda yazid ke kuka yasa ta saki ranta, ahankali ta karaso wajenshi itama ta zauna nan kasa, kura mashi ido Kawai tayi tana mamakin irin wannan kaddara.
"Baby am sorry... Khadija is pregnant..." Yafada mata cikin kuka, dukda zuciyanta na tafasa hakan bai hanata tallabo face dinshi ba,
"Stop crying... Haka Allah ya kaddara..."
"Baby NA CUCE TA...NA zalunceta...she's too young for this...." Yafada cikin kuka, baki mufida ta tabe
"But she's not young for you to sleep with... Yanzu dai zaa Haifa maka shege kafin ka samu na halal..." Tafada sounding very angry,
"Ba laifina bane...laifin kaddara ne...." Dan guntun tsoki taja,
"Da wannan kaddara yasa kaje kayi sata an harbeka dayafi maka gaskiya..." Ta fada atakaice ta mike ta barshi nan zaune, yana nan zaune yana tunanin halin mufida, one second she nice the other second she's mean. Ahankali ya mike ya shiga dakin da mom dinshi ta shiga, tana zaune bakin gado tana kuka, ya karasa gabanta
"Mom am sorry... Pls..." Banza tayi dashi ta cigaba da hawaye abinta
"Mom zan tafi....zanje Neman ta...." Yafada ahankali yana hawaye, mom dai batace uffan ba. Yana nan durkushe gabanta yana kuka tana kuka Har Salem yazo suka bar gidan. Yanayin shi ba karamin tadawa Salem hankali yayi ba don gani yake kaman wani mugun abu na Iya faruwa da best friend dinshi.
Yana tuki ya juyo ya kalli yazid daya rumtse idanuwanshi yana Allah Allah su isa katsina yace
"Guy wai ka manta kaddara ne?... Duk kabi ka damu kanka saboda wannan abun...we can't stop destiny... What will be will always be...ka sassautawa kanka pls...." Inji Salem, yazid dai baice kala ba Kuma bai bude idanuwanshi ba. Kusan a haka suka isa garin katsina around 10:30, amsan address din yayar Hajiya karama yayi yaga goruba road da number gidan, baisan goruba road ba don wurin grandparents dinshi Kawai yake zuwa
"Bari muje family house dinmu don mu nemi wani cousins dina su rakamu...." Salem ya fadawa yazid, ahankali yazid ya girgiza mashi kai,
"No pls...zaa bata mana lokaci...Kawai Bari in kira small mom ta fadawa sister dinta muna wajen round mai kwarya don ta aiko driver dinta yayi directing dinmu...." Yafada ahankali Sannan ya fiddo wayan shi yayi dailing number Hajiya karama ya sanar daita.
โค๐๐งก๐ค๐๐๐
NA CUCE TA
๐๐๐๐ค๐๐งกโค
ยฎZuwairat (ummumaryam)
2โฃ1โฃ
Don't forget to follow and vote me on wattpad *@ummumaryam29*
Salem na tuki yayi dailing number Hajiya babba few seconds later Hajiya dake zaune kan gado tayi picking tare da sallama, gaidata yayi sannan ya fara cewa
"Mom...yazid yaki tahowa...." Ya fada ahankali, Hajiya shuru tayi for a while sannan tace
"Wannan matsalan shine...if he wants he can remain they for ever...." Ta fada atakaice sannan ta katse wayanta, Hajiya Aisha dake jin abunda Hajiya ta fada shuru tayi amma she feels pity for yaxid, Salem ajiye wayan yayi cikin sanyin jiki ya cigaba da tuki. Yana isowa kofar gidan Hajiya Aisha yayi parking ta fito yayi mata godiya har zata shiga gida ya tsaida ta tare dacewa
"Pls Hajiya da akwai wani babban supermarket nan?..." Ya tambayeta
"Yes...if you reverse... Kayi taking left turn then drive for like 8 minutes zaka
ga wata babba supermarket, ..." Hajiya Aisha ta fada Mashi, godiya ya sake yi mata sannan ya barwajen, directions dinta yabi har gaban wata medium size supermarket, parking yayi har zai fito sai a dauki waya ya kira dad din yazid, bayan yayi picking ya gaidashi yake fada Mashi exactly abinda ya fadawa mom, ko uffan baice ba ya kashe wayanshi. Salem girgiza kai yayi yana cewa
"Ko so suke su kashe shi sabida just one mistake.... Ko tuna halin yazid basuyi,...mtwww..." Yafada yana dailing number Hajiya karama. Bayan sun gaisa har zaiyi magana Hajiya tace
"Ina yazid...." Cikin sanyin murya Salem yace
"Small mom yaki tahowa..."
"Ban gane yaki tahowa ba..."
"Mungano gidansu khadija...Ashe motan jos wannan hajjyan ta sakata saboda amminta ta koreta....to shine mukaje har wajen amminta amma taki bamu address din ta....shi kuma yazid yace in bata bashi ba bai dawowa...."
"What sort of thing is this?....yanzu yana chan gidansu khadija kenan?..."
"Yes mom...."
"Kai kana INA?..."
"Na maido hajiyan data rakamu gidane...amma zan koma chan....kuma I think uwar khadijan needs a medical attention..." Inji Salem,
"To ya zaayi kenan...ko zaka nemi wani doctor ka tafi dashi ya dubata?...I will repay....." Inji Hajiya karama
"Wannan ba matsala bane..Allah yasa in samu...don wurin is a little bit low ne...amma I will search...."
"Yauwa thanks.... Bari in kira shi yazid...." Ta fada Mashi sannan ta katse wayata. Salem shiga cikin supermarket din yayi
Daga chna gidan su dija, yazid daya gaji da jingina da bango sai ya dan kwanta tare da yin pillow da hands dinshi. Idanuwanshi lumshe amma ba bacci yake ba don yana jin duk tarin da ammi dake kwance takeyi. Bai Dade da kwanciya ba wayanshi ta dau kara, bai bude idanuwa ba ya saka hannu cikin aljihunshi ya fiddo wayan yayi picking.
"Yazid... " yaji muryan Hajiya karama ta kirashi
"Yes mom..." Ya fada in a very low voice da sai mutum ya Kasa kunne zaiji abinda yake cewa
"Wai me nakeji?..."
"Babu....komai...pls..." Bai idaba ta katseshi dacewa
"To in bakason ranka ya baci... Ku taho da Salem...." Ta fada Mashi atakaice, daga kwance ya girgiza kai
"Mom...am...sorry... Ban dawowa...sai an fadamin inda khadija take..."
"Ina fada maka ka dawo kana arguing dani?...."
"Mom ba haka bane....I can't leave thinking I have made an innocent gal an outcast... Pls mom kuzo Ku bata hakuri ko zata ga girman ku ...pls..." Yafada hawaye na gangarowa daga closed eyes dinshi,
"Dalla rufemin baki....ba ance tana wajen families din amminta ba?...." Ta daka Mashi tsawa,
"Mom...in suma sun koreta fa?.... Amminta ta koreta ballesu?...pls kuzo...." Ya fada yana kuka ahankali
Ajiyan zuciya Hajiya karama ta sauke sannan tace
"Haba dear...in ka zauna wurin zai nuna kaman you are proving stubborn... So ka dawo sai Ku koma bayan few days...." Yazid kai ya dinga girgiza kaman tana tsaye tana kallon shi
"I can't mom...I will stay...." Bai idaba Hajiya karama ta katse dacewa
"Wato gardama kake dai yimin ko?.... Kanason in cire hannuna cikin cases dinka?...".
" no..Mom... "
"Then come back home..." Yana shesseka yace
"Am sorry... Pls am sorry...I can't leave...." Ya fada ahankali sannan ya katse wayan tare da kashewa completely, sulalar da wayan yayi nan kasa yana goge face dinshi daga inda yake kwance.
Abangren dija yawo ta dingayi nan cikin gari kuma duk in taga hankali mutane zai zo kanta barin wurin take ta koma wani wajen, kuma duk inda taga mata most especially age mate dinta masu tallah da sauransu take zuwa. Har zuhr bata karacin komai ba sai da cikinta ya fara motsi sosai sannan ta samu wurin masu saida abinci ta zauna ta saya taci
Tana ci tana hawaye sai kuma tayi saurin gogewa don kar ganta, tana gamawa ta mika kwano ta mike daga wurin tare da rataya bag dinta. Duk yawon da take bata nesa da hospital don tamkar resident dinta ta dauki. Har asr tana cikin yawo amma saitaji her legs is getting cold hakan yasa ta nufi cikin hospital, abunka d general hospital babu Wanda ya damu da harkan wani balle a gane she's not a patient, har zatayi hanyan Inda ta kwana sai ta tuna kar a ganeta, haka yasa ta fara searching inda zata zauna ta dan huta, tana tafiya ta hangi wata katuwar hall mai dauke da many sits wasu da akwai mutane amma most of them are vacant, ahankali ta biya ta wurin tana tafiya a hankali hannunta rike da bag dinta dake kan shoulder dinta kaman her life depends on it. Daga bayan sit ta koma ta zauna the last row don gani ko zaa koreta amma har kusan minti goma da zamanta babu mai kallon ta haka ya bata kwarin gwaiwan kwanciya tare dayin pillow da bag dinta, batafi minti biyar da kwanciya ba bacci ya dauketa.
Salem baiyi wasting time ba ya shiga cikin Supermarket din ya sayi yoghurt drink da snacks kala2 sannan ya fito har zai shiga cikin mota ya hangi wata babba chemist, ajiye ledan hannunshi yayi sannan ya nufi chemist din, wani matured man ya gani rike da news paper sai medical specks a face dinshi. Sallama Salem yayi Mashi mutum ya amsa gaisawa sukayi sannan Salem ya fada Mashi abinda yake bukata. Nan mutum ya shaida Mashi hes a medical doctor kuma zai bishi amma wai he will not go alone saboda tsaro, dariya kawai Salem yayi. mutum kiran wani saurayi yayi yasa ya rufe chemist din sannan suka shiga mota su uku suka kama hanyan gidansu dija
A gidansu dija around 5:30 suka dawo daga makarantan allo, nan suka ga mutum kwance tsakar gidansu, kasa motsi sukayi dukkansu, especially binto,
"Ammi!!...Ammi!!..." Ta dinga kwalawa kira tana Jan baya, ihunta ya sa yazid bude ido ahankali, same ihun yasa Ammi dake kwance daki mikewa zaune don batasan d mutum wurin ba
"Ammi... Zo ki gani...wani ne cikin gidan mu!...." binto ta fada da karfi, ahankali yazid yaso mikewa zaune aikam sukayi waje da gudu daman bakin zaure suke, dukda halin da yake ciki saida yayi murmushi don da bai cikin matsala da dariya zaiyi har ya koshi cos ba karamin dariya suka bashi ba, ahankali Ammi ta rike bango ta fito tana takawa ahankali kaman mai tausayin kasa, tana fitowa tayi tozali da yazid
"Me...kake....anan?..." Shine tambayan datayi Mashi tana magana da kyar, ahankali yazid yayi kneeling
"Dan Allah....kiyi min rai....kiyi hakuri..." Yafada kanshi kasa, hanyan waje ta nuna Mashi
"Ka...fita...ka barmin....gida....ka.fita kafin...in tara maka...mutane...." Ta fada tana dafe da chest dinta. Yazid kam ko gizau don ya rantse bai barin gidan sai da address din dija.
"Ka...tashi... Nace...." Ammi ta fada this time tana fashewa da sabon kuka,
"Kiyi hakuri ki yafemin....kukanki kawai is a enough to get me burning in hell...the cry of an innocent widow will definitely take me to hell...." Ya fada kaman tanajin abinda yake cewa, ammi kam tari ya sha kanta don haka ko kallon shi batayi ba at each minutes tarinta na increasing, ahankali yazid yayi crawling zuwa inda take tsaye tana tari, ammi bata ankaraba taji an rike mata kafa, tsoro taji tayi saurin ja da baya, tana Jan baya ya kara rike mata kafa
"Ki yafe ni...kiyi hakuri... Ki fadamin inda khadija take.... Dan Allah...." Yafada dan guntun hawaye da fitowa daga swollen eyes dinshi
Ammi tsayawa tayi tana kallon shi, kura Mashi ido tayi tana ganin nadama koina na fuskanshi, amma dayake tana da dakakken zuciya sai ta kara janye kafanta don gani take abinda ya aikatawa yarta ba abu bane wanda zaa yafe, gani take he deserves to die for what he did to her dija,
"Ka barmin...gida...." Shuru tayi tana kallon zaure da ake sallama, bata amsa ba haka shima yazid, daman Salem bai expecting a amsa don haka shigowa kawai yayi tare da mutane dake bayanshi, ammi kallon haushi da takaici tayi masu,
"Wai nace...Ku bar min...gida....wallahi.. Zan tara maku mutane...." Tafada tana tari, this time vomiting ta farayi sosai tana saukowa kan knees dinta, da sauri yazid ya mike d sauran strength dinshi shima Salem tahowa yyi da sauri ya rike shoulder dinta, ammi sai a man jini kawai take, amma sai ture hannun Salem dake shoulder dinta kawai take.
Su binto kam ko da suka fita suna ihu basu tsaya koina ba sai gidan kawu nanu,
"Kawu....kawu....wayyo Allah kawu wani mutum ne gidan mu.....kuma bamu ga amminmiu ba...dan Allah ka taho...." Binto dake haki kaman wacce ta kubuto daga bakin kura ta fadawa kawu nanu dake alwallah, kallon banza ya watsa mata,
"Wai Ku ba a koya maku gaida manya ba?..." Ya fada bbu wasa, binto dafa chest dinta tayi saboda yanda yake beating very fast,
"Kawu..amminmu...." Karamin cikinsu ya fada yana fashewa da kuka sai lokacin ya gano da akwai matsala,
"Me ya samu amminku?..." Ya tambayesu, nan binto ta kara fada Mashi abinda ta gani, kaman kar yaje don shima tsoro yakeji
Amma yayi ta maza ta mike ya shige masu gaba.
Dija tana nan kwance ta har daf da magrib, jitayi ana taba mata kafa, da sauri ta mike data tuna da inda take bacci, wata babbar mace ta gani tsaye tare da wata yarinya wacce bazata wuce 16 to 17 ba, dija hannu tasa ta goge bakinta tare da sadda kanta kasa,
"Ya akayi kike nan wajen har magrib?...ko baki samu ganin doctor bane?...." Shine tambayan datayi mata, dija ajiyan zuciya ta saki don gani take dukanta zatayi, da sauri ta gyada mata kai,
"Ke kadai kika zo ganin doctor?..." Hajiya ta kara tambayan ta, kara daga mata kai, matar tsayawa tayi ta kura mata ido for a while kaman xatace wani abu sai kuma tayi shuru tace
"To ki tashi ki tafi... Baa ganin doctor yanzu...sai in emergency ne...." Da sauri dija ta mike jikinta har rawa yake, budurwan dake tare d matar kura mata ido tayi tana kallon ta, same ita ma Hajiyan sai kallon dija dake sauri kawai take,
"Mom ni tausayinta nakeji...." Yarinya ta fada tana rike hannun mom dinta sannan ta tale baki kaman zatayi kuka, ni kuma kurawa yarinya ido nayi sai naga remarkable resemblance dinta da sultan coworker don yazid,
"Me akayi na tausayi yanzu da kike Neman kuka?..." Matar ta tambayeta suna takawa ahankali xuwa wajen wata black jeep dake tsaye,
"Mom kilan bata da mommy... Nasan inda mommy tana da uwa tare zasuzo ganin doctor...." Ta fada tana kankame hannun mom dinta, matar batace kala ba suka kusa zuwa wurin motan wani ya fito ya bude kofa amma yarinya ta tsaya
"Mom dan Allah ki sa wani doctor ya duba ta....mom daga gani ba daga nan garin ta ke ba....." Yarinya ta fada tana buga kafa kasa,
"Zaki fara rigiman ko?... To ki shiga hankalinki ko kuma you will never set foot in this hospital again...." Ta daka mata tsawa, kuka ta fara yi tana
"Sorry mom...." Ta fada ahankali tana shiga motan,
"Shahida kiyi hakuri, da akwai mutane da yawa irun wannan... In kace zaka fara kiran doctor suna dubasu daga baya bakinka zaa gani a dinga cewa sabod you are ahead of them shine kake yi masu haka...." Ta fada tana gogewa daughter ta face dinta,
"Kin San halin mutane...." Ta karasa maganar tana jawo yar ta jikinta
Bata kara cewa komai ba driver ya jasu suka bi hanyan gate amma sai waige2 take chan ta kara ganin dija dake tafiya zata tsallaka titi tana rungume da bag dinta.
Dija na tsallakawa ta koma wajen yan matan dake saida abinci ta zauna nan kusa dasu, wani irin fitsari take ji don maranta yayi fam, zama tayi tana matse legs, da kyar ta iya bude baki ta tambayi wata inda zatayi fitsari, kallon ta yarinyan data tambaya tayi sannan tace
"Wai ke baki da gida ne?.... Jiya ma na ganki?..." Ta tambayi dija ahankali, dija shuru tayi bata ce komai ba. Ganin bazata bata amsa ba yasa itama ta daure fuska sannan tace
"Ga wani gida chan...kiyi sallama killan su barki kiyi fitsarin....", da sauri ta mike tayi gidan da aka nuna mata, cikin Saa aka barta tayi fitsari wannan Karin ma fitsari bai fitowa sosai, tafi minti goma nan durkushe sannan taji saka ta mike ta dawo wurin yarinya mai saida abinci ta saya yanda zai isheta.
Ammi tafi minti biyar tana wanna amai duk hankalin yazid da Salem ya mugun tashi, mutum da salem ya zodashi ya fara cewa
" gaskiya sai dai a kira ambulance a tafi daita hospital wannan yafi karfin home medicine.... " yafada Mashi atakaice, yazid dai kasa magana yayi.
"Waye nan cikin gidan?!..." Aka fada da karfi daga zauren gida Dukkansu maida hankalinsu, ammi ta kara ture hannun Salem dake shoulder dinta, da sauri yazid ya taka ahankali xuwa zaure, yana ganin babban mutum yayi kneeling cos he knows mutum family ne kuma a nashi tunanin yasan abinda ke faruwa,
"Dan Allah kuyi hakuri....Ku yafemin Ku fadamin inda khadija take...." Ya fada palm dinshi biyu harde wuri daya,
"Kai waye?...." Shine tambayan da kawu nanu ya yiwa yazid, yazid sadda kai kasa yayi sannan yace
"Ni....ni...nine....nayi...." Tari ammi ta dingayi da karfi don kar ya fada amma ko waigowa baiyi ba don shi bai gane manufar ta ba
"Ni...ne..nayi...mata...ciki...."
โค๐งก๐๐ค๐๐๐
NA CUCE TA
๐๐๐๐ค๐๐งกโค
ยฎZuwairat (ummumaryam)
2โฃ2โฃ
Wattpad: ummumaryam29
Or
Visit www.ummumaryam.com for more
_Love you beautiful people_
Kawu nanu bude baki yayi don bai gane inda yazid ya nufa ba,
"Dan Allah