You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
jikinta daga na yazid, bata ji kunya ba saida ta hangi dad dasu mom tsaye kaman ta nutse kasa, shima yazid shafa face dinshi yana kallon inna tare da lekawa ta gefe yana kallon iyayenshi, fuskan mom ya kalla yaga ta watsa Mashi irritating look, sauke kanshi kasa yayi don bai Iya kallon dad, duk iyayen nashi sunyi mamakin ganin yanda ya koma don mom tamkar ta fashe da kuka takeji amma her face is saying something different, da sauri mufida ta fita daga cikin blanket tare da sauka daga kan gado, jikinta sai rawa yake, Allah ya taimaka she's decent, yazid ne kawai dake sanye da boxers da singlet , inna bayan mufida da ke barin dakin tabi da harara sannan ta maida hankalinta kan yazid da Duk ya susuce,
"Kai wannan dan cutan zamani ya debo?...." Tayi directing question dinta to dad daya harde hands a chest dinshi fuskanshi babu walwala shima yana kallon yanda ya chanza kaman bashi ba,
"Wai badaku nake ba?... Sida ya kwaso?..." Inna ta sake tambayansu, yazid daure fuska yayi baice komai ba, jin shuru yayi yawa yasa inna kallon yazid
"Kai ubanme ke damunka?...." Inna ta tambayeshi, baice Kala ba kanshi kasa yana gyara blanket dake jikinshi,
"Wai bakajine!!!..." Dad ya daka Mashi tsawa
"Babu...komai...." Ya fada kanshi kasa, bski inna ta bude
"Lallaima...wato baka fadamin ko?..." Imna ta fada tana nuna kanta,
"Kana fadi kafin rainka ya ya baci?..." Mom ta daka Mashi tsawa,
"To a kyaleshi mana...haba...." Inji Hajiya karama, nunata inna tayi da yatsa
"Kiyi min shuru...badake nake ba.... Mtwsss"
Ta dakawa Hajiya karama tsawa, turo baki tayi ta kauda kanta gefe,
"Ni babu abinda ke damuna..." Inji yazid,
"So kake sai ranka ya baci kenan..." Inji dad a fusace, juyawa yayi ya kalli inna sannan ya fara cewa
"Wannan shegen yaron mugun mayaudari ne...yaudareni...na aminta dashi...na fifitashi kan sauran yaran gidan nan...Ashe dan iska ne ban saniba... Yar yarinya data bata fi shekara sha 14 da haihuwa ba yayiiwa....fyade...." Su Sharif bude baki sukayi,
"Yanzu yanrinya tana chan da ciki babu Wanda yasan labarinta....shine yake wannan munafurcin...wai yana nadama...." Dad ya fada, yanda magana ke fita daga bakin shi kasan ranshi bace yake, inna mutuwan tsaye tayi tare da rike baki, mom kam kara fashewa tayi da kuka ta bar dakin, yazid Kuma sunkuyar da kai kasa yayi, inna data gama bude baki sai cewa tayi
"To yanzu meye dalilin wannan ramar?..." Shine tambayan datayiwa dad, kallon mamaki dad yayi mata,
"Ka tsaya kana kallo na....nace ya akayi ya rame haka?..." Ta sake tambayanshi,
"Wai inna bakiji abinda nace bane?...."
"Naji mana....ai dan fyade ko ciki ba yau aka fara ba!...ko wayan nan banzaye kananan yaran sunayi balleshi?...." Baki dad ya rike haka suma sharif,
"Ban gane ba..." Dad ya fada with a shock on his face,
"Sharifu da shahidu mana...mai gadina sai dayayi min kashedi Kansu...wai in na fita suna kawo yanmata...balleshi yazidu?...."
Baki suka kama daga inda suke sauraron abinda inna ke cewa,
"Muje...muje...muje...." Sharif yayiwa shahid whispering yana turashi daga inda yake tsaye. Da gudu suka shige suka bar gidan
Shima yazid kurawa inna ido yayi yana kallon ta don ya tabbatar da abinda take cewa don at that moment ya mance da matsalanshi, afusace dad ya bar wajen, inna kallon yazid tayi sannan tace
"Kai kuma shege ba ance ana amfani da wani abu mai hana mace ciki ba?...."tafada sounding very serious, daga kai yayi ya harareta.
๐โค๐งก๐งก๐๐๐๐
Wai kaman ni ummumaryam in bude wattpad account, amma getting to three weeks har yanzu banda upto 1k followers๐ค.
Gaskiya nayi fushi tunda kuma Baku voting Baku following dina. Nima zantafi Hutu har sai kunyi following dina tare da voting.๐ค๐ค๐ค๐๐๐ da gaske nake๐๐ฝโโ
[11:54PM, 4/22/2018] โช+234 806 399 3789โฌ: โค๐งก๐๐๐๐
NA CUCE TA
๐๐๐๐๐โค
ยฎZuwairat (ummumaryam)
2โฃ6โฃ
_Sweetheart thanks for the prayers, am getting better_
_Babyna, sweetheart dina, habibtyna, I wish you happy birthday in advance, I wish ina iya kara typing cos of you tomorrow amma I can't, age in grace, may Allah grant you all you desired, you_ *know my love for you is.....๐คฆ๐ฝโโ ban San yanda zanyi describing dinshi ba amma know that you are special to me. Happy birthday sweet* *Sawwama* .๐๐๐๐๐๐๐๐
_Dedicated to you, and you alone_
Hajiya karama dake tsaye bakin kofa tsoki taja ta bar dakin saboda takaicin abinda inna ke cewa, cikin matsifa inna ta juyo ta kalli bayan Hajiya karama
"Kinyiwa uwarki tsoki...banza fitsararra..." Inji inna, yazid dai gyara blanket dake jikinshi yayi yana harara inna
"Nace kai baka amfani da kayan zamani?... Kanenka basuyiwa kowa ciki ba sai kai banza soko...gaskiya kaji kunya...."
"Inna dan Allah ki rabu dani inji da abinda ya dameni...." Yafada yana daga mata hannu
"Kaci ubanda ya haifeka....ni kake yiwa matsifar dan uwarka...." Tafda cike da fada, yazid dai bai kara cewa komai ba, haka ta zazzaga Mashi fada Kuma ba kan meyasa yayi raping poor innocent gal take mashi ba sai kan me baiyi amfani da CD ba, takaici da haushi duk sun cika yazid, daman yasan wannan Karami daga aikinta kenan, hada kai da gwaiwa yayi yana tuna abinda inna tace game dasu Sharif
"Allah yasa is part of her cork and bull story...ya fadawa kanshi yana daukan wayanshi domin kiran mufida.
Shahid na tuki Sharif dake zaune kusa dashi sai saukar Mashi ruwan balai kawai yake
" I told you mu rabu dasu since its a secret amma ka nace sai mu gano abinda ke faruwa...gashi garin binciko na wani an binciko namu...." Inji Sharif dake huci, tsoki Shahid yaja
"Wallahi kana kara cewa its my fault zanyi parking motan nan muci uban juna yanzu...." Bai idaba sharif ya katse shi dacewa
"Anje an fada...laifin uban waye in ba naka ba?... Its all your fault... Kasan halin dad...we don't know irin action da zai dauka kanmu ba...." Ya fada cike da tsoro, shahid baice komai ba yayi parking motan gefen street dinsu don daman basuyi nisa ba, Dora kai yayi kan staring yana tunani, shi kuma Sharif relaxing yayi jikin kujeran motan yana breathing kaman Wanda yayi race, ahankali shahid yace
"Just relax...dad ba zai hukunta mu kan maganar wannan lunatic old woman ba..." Yafada in a comforting tune don duk da ac dake cikin motan Sharif sai hada zufa yake saboda fargaba, daga kai yayi ya watsa ma Shahid harara
"You are talking kaman bakasan halin dad ba....yana wasa da maganar wannan tsohuwar ne?....kasan what ever she says is final...ni dai am scared... Allah yasa kar dad yayi cutting allowance dinmu...." Inji sharif, shuru ya dan biyo baya for a moment sannan Sharif ya saki wani dan iskan murmushi tare da cewa
"Wai is it true yaya yayiwa wata ciki?.... I still can believe this...." Yafada with amusement, shima shahid dariya yayi yana cewa
"Amma yaya is a disappointment... Ji yanda ya rame kaman kanshi farau....mtwsss...."
"Novice ne...don da gani he's regretting it...." Dariya sukayi duka, wayan shahid ne ya fara ringing,
"The boss is calling..." Ya fada yana nunawa sharif screen din wayan,
"Wallahi wannan tsohuwar najadun ta ja mana...." Inji sharif yana kallon screen din wayan da aka rubuta my hero, which means their dad, yana picking yayi saurin saka a loud speaker,
"H...." Bai karasa ba dad dinsu yace
"Ku sameni now!!!..." Yana kaiwa nan ya katse wayan. Kallon juna sukayi sharif ya hadiyi wani abu sabida tsoro, shahid hannu ya Dora bisa kai, few seconds later yace.
"See we have to be bold... We shouldn't look suspicious...." Inji shahid dake juya kan mota zuwa gida.
Dija na nan kwance har karfe 10, wani irin bacci mai nauyi ya kara daukata amma ba mai dadi ba, taba bacci tana firgita, kudundune kanta tayi sabida sanyin da takeji amma rana da fara dukan jikinta ta fara jin dadi amma fever da takeji kara rising yake don inda zaa aunata da thermometer sai ta bawa 48 baya, abunka da jos babu mai maida hankali kanta, kowa ta kanshi yake amma wasu sukan tsaya su kalleta for just few seconds sai su wuce while wasu ko inda take basu kallo, ahankali ta bude idanuwanta da sukayi mata nauyi, ganin mutane na wucewa da yawa yasa tayi karfin halin mikewa zaune, kokarin mikewa tayi amma she couldn't, da crawling ta koma jikin wani bango dake gefe daya ta Jingina, duk abinda ke faruwa tana rike da bag dinta tare da drugs and sauran bread data saya, she never needs her mother the way she needs her now, she don't want anything, kawai abinda takeso is someone she can hold on to, somebody that will hold her back,
"Ammi...." Tafada ahankali tana nishi, maganin da aka bata ta dauko, ahankali ta daga kai ta yiwa mai saida ruwa alaman yazo da hannunta, da sauri yaron ya kawo ruwa ta mika Mashi goma ya bata ruwa daya batare datace uffanba, maganin ta balla ta saka a baki sannan tasha ruwa, bread tayi kokarin ci saboda yanda cikinta ke crumbling amma ta kasa, kara daga kai tayi tana kallon masu wucewa ko Allah yasa taga abinda zatayi shaawanci Allah so kind sai ta hangi mai saida gurasa, sai taji she can eat it despite her lost of appepite, kiranshi tayi ya zo ta sayi na hamsin, ko rabi bataciba ta ajiye sauran gefe daya, inda ta jingina babu rana so she was so cold, hawaye ne ya kara gangaro mata.
Ahankali ta daga hannunta ta goge, tana gogewa wasu na fitowa, yanzu takejin rashin uwar tattare daita, she's missing her family like crazy, adua take ko Allah yasa taga mutum daya Wanda tasani, she really needs a comforter, she's so lonely, she is wondering how cruel and wicked the world is, gata yar yarinya in pain and agony amma no body cares, gani take inda zata mutu nan babu bai bin ta kan gawanta,
"Mutuwa...kazo...dan Allah....." Ta fada sounding so feed up. Tana nan zaune har karfe sha biyu inda taji wannan fever ya sauka, amma she still feels weak, ganin babu mai damunta kan ta tashi inda take zaune yasa ta kara relaxing, bag dinta ta ajiye kayi tayi pillow dashi, few minutes later bacci ya kara dauketa.
Bata farka ba sai bayan asr, mikewa tayi taji jikinta da sauki sosai, tanason dan yawo kaman yanda ta saba amma gani take zata hadu da yazid, har yanzu sunanshi bai zauna mata sosai ba, at times she recall Yasir wani lokacin Kuma ta tuna hes yazid not Yasir,
"Allah yasa kar in ganshi...." Ta fada tana tashi tsaye daga inda take zaune.
Bayan sallan magrib dad ne zaune ya hada tagumi sai Hajiya karama da Hajiya babba da suke zaune both side dinshi, then inna dake zaune kan kujera da plate hannunta tana cin tuwo shinkafa sai fada take wai bai yi taushi ba
"Wai tuwon shinkafan sai gris...gris...yake...mata babu abinda suka Iya.....ko danko tuwon baiyi ba.. Ko saurin uban mu kuke oho...."tafada tana kai loma Kuma from all indication tana jin dadin abincin amma she cant stop complaining, Hajiya babba bata daga kai ba don abinda ya dameta daban, ita Kuma Hajiya karama kallon ta tayi ta watsa mata annoying look batare data bari ta ganiba, sallama akayi Hajiya karama ta daga kai ta amsama su sharif dake sanye da jallabiya kaman wasu ustazai, don suna dawowa suka tarda dad zai fita masjid, suma da sauri suka karasa tare da watsa ruwa suka tafi masjid, kowanne da tunanin dayake, direct daga masjid part din dad sukayi. Itadai Hajiya karama tasan abinda ke nan amma Hajiya babba bata Sani ba cos bata nan lokacin da inna ta fasa wannan kai, inna na ganin su shigo dakin ta daga kai ta watsawa each and everyone dinsu harara tare dacewa
" shegu Ashe kuna sallama...dayake ni kun raina ni...." Tafada masu, basu kalli inda take ba suka samu gefe daya suka rakube, sunfi minti biyar da zama sannan dad ya daga kai idanuwanshi kaman garwashi ya fara cewa
"Ba....." Da sauri inna ta daga Mashi hannu,
"Me zakayi?...."
"Magana zanyi masu... "
"Ina yazidu?... Ai shine babba... Don haka...kome zaayi dole a kirashi...." Inna ta fada atakaice, dad dai baiso hakan ba amma bai yiwa inna gardama don haka ya umarci shahid ya kirawo yazid, Shahid na zama shima ya shigo da sallama ya samu wuri ya zauna tare da mike legs dinshi sannan ya soka hands dinshi cikin cinyanshi, kanshi kasa, daman yana shigowa dad ya kara hade rai, saida kowa yayi settling sannan dad ya fara cewa
"The reason Dana kirawo Ku nan is not for anything sai don Ku biyu...." Ya fada yana nuna sharif da shahid, gabansu ne ya kara faduwa, matsawa shahid yayi kusa da Sharif ya Dora hannunshi kan hannun sharif dake kasan tiles,
"Na Baku nan da sati biyu kowannen Ku ya fiddo matar aure!!....." A razane su shahid suka daga kai suna kallon dad, surprise look ne kwance kan face din Hajiya babba, Hajiya karama tayi saurin cewa
"For what?...." Bata idaba inna ta katseta dacewa
"For meye?....basu isa auren bane?....ko da akwai abinda shegun yaran nan basu Sani ba?...." Shi kam yazid eyes dinshi lumshe Kuma tunda ya shigo falon bai daga kai ba,
"Gaskiya ni ban son aure...." Sharif ya fada
"Nima wallahi am not ready for marriage...." Inji shahid,
"Kai!!!...." Dad dinsu ya daka masu tsawa,
"Ina wasa daku?...." Da sauri suka girgiza kai,
"Then kowanne ya fiddo wacce yake so ko Kuma ni in zabar maku...." Dad ya fada atakaice,
"Ni wallahi bani da wacce nake so...." Shahid ya fada kaman zaiyi kuka at the same time yana harara inna dake lashe hannunta kaman babu gobe,
"To ai an gama...isa ka bari ni zan zaba masu mata cikin dangi....." Inji inna dake ajiye empty plate dake hannunta kasa, da sauri suka mike,
"Wallahi bamu son aure...yanzu ...." Suka fada in chorus,
"Sit now!!...." Dad ya daka masu tsawa, da sauri suka koma suka zaune, yazid dai ko uffan baice ba cos hes absent minded,
"Bakuson aure kuke bin Matan banza?..." Inji inna, da sauri suka daga kai suka kalleta
"Mu!!!!!" Suka fada tare kaman basu San abinda take cewa ba, itama Hajiya babba daga kai tayi tana kallon inna cikin tashin hankali
"Inna matan banza Kuma?..."
"Eh sharri zanyi masu?...to aure babu fashi... Sai anyi ko kuna so ko baku so...." Tayi directing maganar ta to su Hajiya, Da sauri hajia babba ta mike tana cewa
"Nifa ban gane abinda ke faruwa nan ba...." Itama inna mikewa tayi
"To dukana zakiyi ne....naga kin tashi tsaye,..." Kallonta dad yayi ta koma ta zauna
"Mu wallahi babu ruwanmu....sharri take mana...." Inji shahid, hannu innata Dora bisa kai,
"Ni kuke kira da makaryaciya?.....inna lillahi.....isa kana ganin yaranka suna kirana da makaryaciya?...." Inna ta fada kaman zatayi kuka, hararanta Hajiya karama tayi,
"To gaskiya baa yiwa wayan nan yaran da basu mallaki hankalinsu ba aure....how old are they?....ni dai ...."
"Keep quite!!...." Dad ya daka mata tsawa sannan ya maida hankali shi kan su shahid
"Both of you are getting married in the next two months... That's final..." Inji dad
Hannu suka Dora bisa kai
"Dad dan Allah kayi hakuri.. Babu abinda mukayi....wannan innan karya take...."
"Quite.. Inna ke karya?..." Inji dad, yazid ko nude eyes baiyiba balle ya daga kai har yace kala,
"You can go..tunda baku da wacce kukeso....sai inna ta nema maku mata...." Inji dad, da sauri shahid yace
"Ina da wacce nake so...." Wani irin disgusting look Hajiya karama ta watsa Mashi,
"Wai da gaske kake ne?..." Ta tambayi dad,
"Do I look like am joking?..." Ya amsa mata atakaice
"Haba alhaji...pls let's do some investigation.... It might not be true..." Inji Hajiya karama, Hajiya babba kam confusion bai barta tayi magana ba, ita ba aure ne damuwanta ba, kawai matar banza da inna ta ambata, daga kai tayi ta kalli yazid dake zaune wuri daya ko daga kai baiyi balle motsi, she feels for him har cikin ranta,
"Yauwa dan albarka...wacece kakeso?..." Inji inna ta tambayi shahid, bai amsa ba ya watsa mata harara
"Ba da kai akeba?..." Inji dad, da sauri shahid yace
"Asabe...." Ya fada yana tunanin his feelings towards her, kallon shi Sharif yayi
"Wacece ASABE?...." Dad ya tambayeshi,
"Mai aikin small mom...." Yafada kanshi kasa at that moment sai yaji ko yanzu aka daura aure its OK, wani irin tsoki small mom taja
Good....kai kuma fa?..." Dad ya tambayi sharif,
"Ai dad ni wayanda nakeso suna da yawa..." Ya fada yana turo baki,
"Made up your mind...." Inji dad, hajia babba mikewa tayi itama Hajiya karama tabi bayanta inna tabisu da harara.
"To mutum biyu nakeso...." Ya amsa wa dad,
"Zan aura maka daya kai kuma in kana da hali ka auri daya da kanka...." Inji dad
"Ai dad ban iya auran daya in bar daya...sai dai kayiwa shahid kadai in na fara aiki in hada su biyu in aura...." Ya fada babu kunya,, yazid baisan sanda murmushi ya bayyana kan face dinshi ba
"Wallahi dad karya yake....in baa yi Mashi yanzu nima kar ayi min...." Inji shahid, hararanshi sharif yayi
"Ai kai kana da wacce kakeso....kawai kayi ni nayi nan gaba ...." Shahid zai magana dad ya daka masu tsawa don ya lura abin zai zama wasa inna kuma tagumi tayi ta cika tayi fam.
"You are all dismissed.. Kuje Ku fara shiri...your wedding is in two weeks time...." Dad ya fada atakaice, da sauri suka mike
"Ku tsaya dan waje Ku maidani dan ubanku..." Inji inna, basu CE komai ba suka fice, inna mikewa tayi tabi bayan su shahid, ahankali shima yazid ya mike ya koma part din shi.
Inna ba karamin jijjiga tasha a motansu shahid on their way back ba, sai tsine masu take amma basu juyawa balle su tanka mata, har bump suke tsallakawa da gudu.
_Two months later_
Atakaice cikin wata biyu saida yazid ya je jos sau uku duk don neman dija amma all to no avail, duk zuwan dayake bai fadawa mufida the exact place da zashi sai dai yace office things, amma duk zuwan zan in har ya dawo sai yasha drip sabida rashin cin abinci.
Abu kaman wasa anata preparation din auren sharif da shahid, babu irin magiyan da su Mom basuyi ba amma babu abinda dad ke cewa sai ban barin yaran nan sukani cikin hallaka so better in fita hakkinsu.
Su kam yanzu basu damuwa don sun San dadin mace so suna tunanin they don't have to screw and be afraid anymore, they are free to do what so ever da matansu, kuma sun San money won't be the matsala cos dad yayi masu starting elaborate business kowa da nashi, wani lokacin sai sharif ya rafka uban tagumi da shahid ya tambayeshi matsalan sai yace
"Yanzu @ 25 zamu samu yara kenan?..." Sai shahid yace
"Haven't you had of family planning?..."
"Amma ance it's dangerous.... I love asiya( ASABE)...."
"Then get ready tobe a dad...nidai am not ready... Abinda nakeso is non stop sex...har inji na bar shaawa...." Inji shahid dake mika.
"Hmmm..."
"Ni one thing is that zan kara mata ko zuwa next year ne..." Shahid Yafada not planning at all.
Ita kam ASABE tunda sharif yace ita zai aura dad yasa aka maidata gidansu without reason, gidansu fada suka dinga mata kan ta watsar da damanta tunda tayi laifi an maidota, duk explanations da take masu kan batayi komai ba is not accepted by her guidance har sai bayan sati daya da dad da wasu friends dinsu sukaje Neman auren asabe ga shahid. Da gudu suka amince amma ita da kanta bataso.
Su Mom basuki zabin shahid ba don sun San da talaka da maikudi are all from Allah, and what will be will always be nor matter the obstacles. Lefensu irin daya akayi duk expensive and elegant kaya aka zuba. Tunda ake maganar wedding din yazid bai taba magana ko sau one ba, shidai nashi ido don according to him his problems are enough for him.
Abangaren dija kam taga rayuwa cos tayi spending two whole months on the street of jos, yanzu her pregnancy is 7 months, in ka San dija last three months to yanzu bazakayi identifying dinta ba don tayi baki tayi dirty kafanta yayi developing cracks she looks so tired and pale, yanzu ko hijjab bata yawo dashi kanta kaman na mad person, she looks older than her age, people around sun Riga sun San she's homeless hakan yasa wasu ke dan bata abinci kyauta, tayi kukan rashin kowa har ta hakura ta barwa Allah komai. Amma one thing shine babu Wanda ya kara molesting dinta don kafin a farga da she's aloner har cikinta ya fito. At time in Tana zaune gefe daya kafin ta kwanta sai ta rungume cikinta da kanta don yanzu tasan da akwai da cikin cikinta, the moment tayi hugging cikin sai taji all loneliness is gone, wani lokacin sai ta dinga yiwa cikinta magana in short kaman wata insane person ta koma.
Sweetheart kar wacce tayi min kuka cos of dija, remember its just a fiction nothing real.๐๐ฝโโ
Once again thanks for the prayers.
[11:55PM, 4/22/2018] โช+234 806 399 3789โฌ: โค๐๐๐๐๐งก
NA CUCE TA
๐งก๐โค๐๐๐
ยฎZuwairat (ummumaryam)
2โฃ7โฃ
Yau anyi ruwa sosai a jos hakan yasa garin yafi da sanyi, dija da rakube gefe daya a inda take kwanciya wato inda masu ganin doc ke zama, ji tayi sanyin yayi yawa, ga jikinta nayi mata itching don har ta mance rabon da tayi wanka, she can smell her body, amma hakan bai hanata jin sanyin ba, bodyguard dintane ya motsa don tana ganin cikinta amatsayin abinda ke tsaronta don duk yanda take da jin tsoro data tuna da akwai wani cikin jikinta sai ta rage jin tsoro, duk yanda take cikin damuwa data tuna abin cikinta sai ta saki murmushi, kawai sai ta zauna tana picturing face din abin dake cikinta,
"Da sanyi ko?...." Ta fada ahankali bakinta na rawa,
"Kaima kana jin sanyin?..." Ta sake fada tana kallon cikinta, kuma Allah so kind in tanawa cikin magana bai dadewa sai yayi motsi kaman yana replying ba karamin dadi hakan ke saka dija ba,
"Banji ba...da sanyi?..." Ta sake tambayan silent tummy dinta, shuru tayi tana sauraron movement as usual amma nothing, shafa cikin tayi,
"Babu motsin yau?.... Kayi motsi....kaga yau babu wuta ....tsoro nakeji ...kuma ga sanyi...." Ta fada tana shafa cikin ta, still shuru babu response, sikam daga hannunta tayi ta laftawa cikin duka, Wanda sai da ta dan saki kara saboda zafi. Nan take abinda ke cikinta ya fara juyawa kaman yanda take bukata, murmushi ta saki
"Nace kana jin sanyi?...." Ta tambayi cikin, motsi ya danyi
"To bari in rufeka...karkaji sanyi...." Ta fada ta bude bag dinta daya kara tsufa yayi dirty saboda yanda take pillow dashi always
Daya daga cikin kayanta da sukayi dirty ta dauko ta rufe cikinta,
"Sanyin ya dainako...." Ta tambayi cikin tana shafa shi tro and fro, dan biting lips dinta tayi sabida yanda sanyi ke rasta legs dinta, Riga daya ta kara daukowa ta rufe legs dinta sannan ta samu sauki. Dan juya kanta tayi gefe daya kawai sai yazid ya fado mata arai, sai take tunanin da batayiwa ammi gardama ba da yanzu tana zaune lafiya da family dinta, she's young and innocent amma yanzu tasan yiwa babba gardama is bad don ta koyi darasi a rayuwa, tasan duk abinda babba ya fada is always right don she promise herself never to disobey an elder again. Tana tuna sanda ammi ke kukan kan kar ta tafi ta barsu amma she wanted a better life for herself and her family, bata yi zaton such an awful destiny awaits her ba,
"Mutane basu da mutunci...in nayi kudi zan dinga taimako....in naga yar karamar yarinya zan taimaka mata....dukkan mutane basu iya taimaka min...." Tafada tana fashewa da kuka at the same time tana scratching jikinta, bata iya good ten minutes batayi scratching private part dinta ba saboda yanda take ji, cikin kuka tafara cewa
"Na gaji...nagaji.. Allah nagaji...Malam yace aljanna da dadi...ka kasheni ka sakani a aljanna...ni dai nagaji...." Ta fada tana dukan kasa same time abun cikinta ya kara motsi, dan saurarawa tayi sannan tace
"Da gaske nagaji...kawai mu mutu ko mun huta...ko mun samu wurin bacci mai kyau
..ko mun dinga samun abinci kan lokaci...." Tafada tana goge face dinta sannan tana tuna ta kusa gama kashe kudinta, despite tana managing sosai. At times tanajin kaman