You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
ta tafi kauyen su ammi amma kuma the feeling of rejection sai ya hanata.
Yau wedding dinsu shahid sauran 3 days, mufida na tsaye bakin wardrobe tana packing kaya cikin bag, yazid na kwance yana kallon ta, kawai sai tunanin Allah yasa ya shawo kanta kawai yake don yayi deciding ba zaije wedding din ba, instead zai kara komawa jos during the weekend ko Allah yasa yaga dija, dan juyowa tayi ta kalleshi shima ya kalleta tare da sakar mata murmushi, itama maida Mashi martani tayi sannan tace
"Baby na gama packing nawa....it's your turn...." Ta fada zipping bag din
Dan murmushi karfin hali yayi yana lumshe eyes kaman mai jin bacci
"Baby...I think ba zan je ba...." Ya fada ahankali, mufida dakata zipping tayi ta tsaya tana kallon shi for a moment sannan tace
"Why dear?...." Ta tambaya tana komawa kan gado kusa dashi, jawota yayi
"Cos I look horrible... Banason a dinga tambayan what's wrong with me...akwai kije...zan zo daukanki next week...." Yafada yana shafa gashin kanta,
"Haba dear...how is that possible... Ace two of your siblings zasuyi aure kuma your are absent... Gaskiya muje kawai...ko wedding fatiha kayi attending...." Ahankali ya girgiza mata kai
"No baby...kawai kije...after all we have a lot at the office... Kinga few days back da banyi aiki ba yasa aikin sun zama Lodi....." Kai kawai mufida ta dinga girgizawa,
"Baby yau Thursday.... Mu tafi gobe Friday...sai ka zauna gidanmu...amma gaskiya I don't want to travel with out you..." Tafada tana lafewa jikinshi, kissing kanta yayi
"Sorry sweetheart... Just this once...go with out me...", mikewa tayi daga jikinshi
" if you are not going.. Am not... Kai da abunka kace baka zuwa... Ina amfanin zuwa na ni?..." Tafada tana mikewa daga kan gado, wurin bag datayi packing ta nufa ta duka zatayi unzipping, da Sauri ya mike
"Baby mommies zasuyi fushi in baki je ba...." Yafda yana rike mata hannu kar tayi zipping bag din,
"What about you?.. Bazasuyi fushi in baka je ba?..." Tafada kaman zatayi kuka, tallabo face dinta yayi
"Bazasuyi ba...you know they don't care about me any more..." Yafada cikin sanyin murya
"They care mana...muje ko kuma in fasa zuwa...."
"No dear ki zakije....go first thing tomorrow morning... Ni kuma zan zo jibi...." Yayi mata karya, turo baki tayi
"I don't believe you...." Dariya yayi
"My word is my bond....just go and enjoy yourself...." Hararanshi tayi
"Wane irin enjoyment zanyi babu kai?...." Tafada sounding naughty, dariya yayi
"To muje muyi wanka sai in baki na sati daya...." Yafada yana daukanta.
Dariya itama tayi
"Na sati daya na zalunci kenan...."
"Ai kinsan am always gentle...."
"This days ko...amma before you are rude in bed...." Tafada tana tuna yanda yake handling dinta kafin pregnancy case din nan ya fito,
"Yanzu baby am rude?... Duk sauki na?...to yau sai na kwada maki rudeness... Yau my name is rudeboy...." Yafada yana tura kofan bathroom da kaanshi, dasauri ta diro daga hannunshi,
"Gaskiya banson rudeboy...just be gentle...." Tafada tsoro na kwance kan face dinta,
"Ai so nake yau in bar maki tabo yanda da kinje kano dadin na nan jikinki..." Hararanshi ta karayi tare da komawa gefe
"Banson... Na hakura...." Dariya yayi
"Just joking...kinsan I can't do anything like that..." Yafada yana cika bathtub da ruwa at the same time yana tunanin how well he's trying don ji yake kaman ya Dora hannunshi kai ya dinga ihu in ya tuna cewa his seven months baby na Chan wani waje cikin wahala
"That's if she make it...." Yafada under his breath
Mufida kura Mashi ido tayi son in da sabo ta saba several time zai dinga yiwa kanshi magana at times taji wani lokacin kuma batajin abina yake cewa amma she knows it's all about khadija.
The following day suka shirya bayan breakfast wanda ba wani cin kirki yake ba don in don sonshine ya samu liquid abu ya sha ba kawai cos in sau goma zai kai abu cikin bakinshi sai ya tuna da dija ko ta ci ko bata ci ba hakan yasa ko kadan baison cin abinci amma yasan rashi hakan zai batawa mufida rai so dole yake forcing kanshi yana cin abinci.
Trolley bag dake shake da kayan sawan mufida ya dauka ita kuma mufida ta tsaya kashe electronic dake falon. Bakin kofan falon ya tsaya yana jiranta sai da ta gama ta taka cikin kasaita ta karasa inda yake tsaye, hannuwa ya bude mata ta fada jikinshi
"I will miss you..." Ya rada mata cikin kunne,
"For just a day ko....tunda kace zakazo gobe...." Tafada tana kara lafewa jikinshi,
"Amma kaman shekara nakeji...cos am gonna be lonely...." Ya ce mata, kissing dinta yayi for a moment sannan ya bude kofa
"Ladies first..." Ya fada yana nuna mata kofa ahankali ta wuce tana murmushi bayanta yabi tare da locking door dinsu sannan ya kama hannunta suka sauka zauwa parking lot.
Da Sauri ya ajiyeta park don cewa tayi bata iya driving from abj to Kn wai zai bata wahala, empty golf ya amsar mata ya biya ta shiga sannan ya kama hanyan office.
Around noon yana zaune a office yana tunanin rayuwa, yanzu yasan sauran two months dija ta haihu kuma baisan irin halin da zai shigaba muddin har lokacin yayi bai ga dija ba hakan yasa yayi niyyan in ya tafi jos wannan Karin zai je TV and radio stations ya bada description dinta don a tayashi cigiyan ta don ya tambayi pics dinta ammi bata dashi.
"Kai..." Yaji an fada ana dukan desk din gabanshi, hakan ya maidoshi hayyacinshi, gyara speck din face dinshi yayi yana murmushi
"Kai yanzu baka da abunyi sai tunanin..." Inji sultan dake zama kan leather seat dake facing yazid
"Ba tunani nake ba...kawai am just absent minded ne...." Ya amsa Mashi,
"Kai ustaz ne amma sai shegen karya....akamaka red handed amma kace ba haka ba...in ba tunani kake na did you know sanda na shigo ciki?..." Sultan ya tambayeshi, murmushi kawai yayi bai kara cewa komai ba, sultan zai bude baki yayi magana wyanshi ya fara ringing, murmushi yayi yana cewa
"My mommy..." Yafada yana picking wayan, yazid dai kura Mashi ido yayi don yanzu ya mance rabonda mom ta kirashi sannan in ya kirata discussion dinsu very brief ba kaman da da suke hours suna hira a kan waya ba.
"Mommy I promised zanzo ai....tare zamu cinye wannan weekend...." Yazid yaji sultan na fadawa mom dinshi
Murmushi kawai yazid yake saboda yanda sultan ke labartawa da mom dinshi, sunfi minti ashirin suna waya sannan sukayi bankwana, dariya sultan yayi yana cewa
"Wallahi zullumin tuki daga nan zuwa jos kawai nake..." Surprise look yazid yayi Mashi tare da dafa goshinshi
"Kasan na mance you are from jos?.... It escape my mind wallahi...." Dariya sultan ya karayi
"Da gaske kake?..."
"Wallahi kam...ai for the last two months sau uku baje jos....kuma a hotel nake kwana kafin in dawo...."
"Kam....amma baka kyau ta ba....ga gidajen mu chan har da guest house...." Inji sultan
"Ai I tell you na mance...ko gobe ma zan goma jos....." Yafada not sounding happy kaman da farko,
"To me kakeyi a jos?..." Sultan ya tambayeshi, shuru yazid yayi yana Dana sanin fada Mashi yana zuwa jos don ya mance zai tambayeshi dalilin.
"Ina zuwa wajen families ne..." Yazid yayi Mashi karya, girgiza kai sultan yayi
"Ban yarda ba ...kodai mata zaka kara...amma zuwa jos don ganin family har sau uku a cikin wata biyu is not accepted...." Dariya yazid yayi
"Ai ba mugun abu bane...kawai na fada maka gaskiya...."
"Hmmm ai ku ustazai ne...baku karya...saidai Ku fadi ba daidai ba....." Inji sultan, yazid dan daure fuska yayi don yasan he's no saint,
"Gobe sai mu tafi tare kawai..." Inji sultan,
"Ai ni ba cikin gari zani ba....sai dai zan kwana gidan Ku ne...."
"Ai wannan ba matsala bane ...kawai muje tare ..zanyi escorting dinka zuwa inda zaka...." Da Sauri yazid ya girgiza Mashi kai
"No.... "
"OK...muje sai kayi amfani da motan gidanmu kaje inda zaka ...." Sultan ya fada mashi,
"OK then....daman banson kwana a hotel wallahi...." Haka suka cigaba da hira sannan sultan ya koma office dinshi, the following day which was Saturday suka kama hanyan jos run da sassafe, da motan sultan sukayi amfani.
❤💜💛💙💚🧡
NA CUCE TA
💚🧡❤💙💜💛
®Zuwairat (ummumaryam)
2⃣8⃣
*Wattpad @ummumaryam29*
_Www.ummumaryam.com_
*Email me @ Zuwairat.nuhu@gmail.com*
*Don't forget to vote and comments. Thanks*
*This page is for all my wattpad follower, voters and readers, thanks for the love*
Sultan na tuki yazid yayi relaxing with his eyes closed, tunanin rayuwa, kawai adua kawai yake Allah yasa yaga dija wannan Karin don yasan sauran two months dija ta haihu, in har bai gantaba before then baisan yanda zaiyi da ranshi ba. Sunfi hour suna tafiya amma ko uffan baice ba, saidai sultan ya dan jashi da hira kuma he chooses the short word to reply him don kar hiran ya Dau lokaci.
"Wai pls what is wrong with you?....ba haka kake ba...." Inji sultan, cikin kasala yazid ya kalleshi
"Babu komai...kawai dai na gaji ne....amma am OK?..." Sultan kallon shi yayi for just few seconds sannan ya maida hankalinshi kan titi
"Kasan wallahi ina iya sharing problems dina da kai...though we are just co workers amma you have a special place in my heart...amma kai ba haka ba... Ga damuwa karara a face dinka amma baka iya fadamin abinda ke damunka...." Sultan ya fada yana tuki, dan murmushi yazid yayi yana gyara zamanshi
"Kasan ba Komai mutum ke iya fadi ba...wani abun sai hakuri...." Yafada cikin sanyin murya
"Amma ance problem shared is problem solved....taya zaka samu maganin matsalan ka in baka fadi ba?.....ni wallahi ina ganin kana daga cikin mutanen da zan iya sharing komai dashi....you are nice... Religiou...." Bai idaba yazid ya dan daga mashi hannu
"Am not all you have mentioned.... Am a monster... Am bad and dangerous... In short am dangerous than I gave myself credit for...." Yafada muryan shi na cracking kaman zaiyi kuka, ajiyan zuciya sultan ya saki
"Just let it out....zakaji sauki sosai...." Kai yazid ya girgiza Mashi,
"Something are better left unsaid.... Am not proud of abinda nayi....saying it ruins my happiness... Kawai kasani am not who you think I am....." Yafada yana murmushi wanda yafi kuka ciwo,
"OK....amma take it easy on yourself...." Inji sultan.
"I wish...." Inji yazid, haka sultan ya dinga driving har suka isa gidansu, kafin su iso babu abinda yazid keyi sai kalle2 yake har sultan ya gane maybe he's looking for something,
"Kana Neman wani abune?..." Sultan ya tambayeshi, kai ya girgiza
"No...kawai ina kallon garinku ne..." Ya amsa mashi, har cikin ranshi yanason fadawa sultan amma how would it sound ace shi yazid yayi impregnating yarinya. Shuru kawai yayi.
Sultan bai gama parking ba lil sis dinshi da bazata wuce 17 ba ta fito a guje, sauran kadan data kadashi kasa sabida yanda ta diro Mashi kaman wata karamar yarinya, yarensu suka farayi daga inda suke, dan kauda kai yazid yayi tare da yin dariya for 0ne to two seconds saboda how funny it sounds
"Baki gaida friend dina ba..." Ya fadawa sis dinshi, da sauri tayi juya ga yazid dake wearing murmushin karfin hali ta gaidashi amsawa yayi yana cewa
"What a remarkable resemblance...." Don daka gansu kasan blood daya ke running through their vain. Sultan na rungume da sis dinshi ya juya ga yazid
"Ustaz...you are welcome to my home...." Murmushi yayi yana tunanin he wish zai ya fada mashi ya bar kiranshi da wannan sunan amma yasan ko ya fadi a banza,
"Gidanku dai...ka wani CE my home kaman naka kai kadai?...kaida baka da mata?..." Yazid ya fada mashi cikin zolaya. Haka suka shiga cikin katafaren falon, da sauri mom dinshi ta taresu cikin murna da jin dadi
"Mom wannan shine yazid isa bala?...wand...." Bai idaba mom dinshi tace
"Ohhh...you mean isa bala dai?..."
"Yes mom...shine mukayi wedding dinshi last few months...." Dariya mom tayi farin ciki karara a face dinta,
"Yanzu kuje kuyi wanka kuyi freshening up sai Ku fito kuci abinci...." Inji mom din sultan, sultan bin wata hanya yayi bayan ya umarci yazid daya biyoshi.
Nan suka shiga wani part mai dauke da falo da dakunan bacci biyu.
"Uztaz kayi amfani da wannan dakin.. " ya nuna mashi left hand side room,
"OK..thanks... Amma yanzu zanje inda na fada maka.... In na dawo da yamma zanci sbuncin...pls help me explain it to mom kar tayi fushi...." Tsaya kallon shi sultan yayi
"Amma why not ka watsa ruwa nima in watsa ruwa sai muje tare?.." Da sauri yazid ya girgiza Mashi kai kaman Mara gaskiya,
"No...I will find my way back...." Amsa mashi
"Hmmm you are just unbelievable.... To bari driver ya kaika tunda ba garin kasani ba sosai..."
"OK.. " yazid ya amsa mashi amma ba don ya so ba
Sultan fita yayi ya fadawa mom dinshi yanda sukayi da yazid, Sam bataji dadi ba amma daya fada mata nan gidan zai kwana sai ta saki ranta. Wurin driver yaje ya sanar dashi ya shirya zai fita da abokinshi.
Part din shi ya koma ya tarda yazid daya rafka tagumj, nan ya fada mashi motar is ready da sauri ya mike kaman wanda ke zaune kan allura. Bayanshi sultan yabi da kallo yana mamakin how boring yazid have become. Yazid na fita ya tarda driver dake zaune cikin motan yana jiranshi da sauri ya jefa kanshi gaban motan yanda zai samu view din gari da kyau,
"Ka kaini supermarket..." Ya fadawa driver don sayawa su ammi foodstuffs kaman yanda ya saba saye duk sanda zaije kauyensu. Daya daga cikin supermarket driver ya kaishi. Fita yayi ya shiga yana kalle2. Bayan kaman minti ashirin aka biyoshi da kayan abinci kala2. Daga nan suka kama hanyan kauyensu ammi.
Ita kuma dija data tashi yau taji duk jikinta babu dadi, haka nan take samun weird feelings, kawai cewa cikinta tayi batajin dadi, ta fita tana yawonta amma she walking tana bude legs sabida yanda batajin dadin tafiyan. She feels so uncomfortable. Inda take cin abinci Safiya taje ta gaida matar
"Dija an tashi?..." Matar ta tambayeta,
"Eh...." Ta fada tana zama dan nesa daita don tana ganin the look on people's face duk sanda ta zauna kusa dasu hakan yasa take zama dan nesa dasu. Tafi minti goma zaune bata ce kala ba, juyowa mai kosan tayi
"Yau dija baki sayen kosai ne?... Ko sai ta kare?...." Matar ta tambayeta,
"Zan saya...." Ta amsa mata cikin sanyin murya, shuru ya an biyo baya sannan tace
"Dan Allah....inyi wanka.....gidanki?...." Ta tambayi matar muryan ta na rawa,
"Eh...babu matsala...amma ki jira in gama sai muje tare tunda da nisa kadan..." Matar ta amsa mata, wani irin dadi taji don tunda aka gano she's on the street bata kara samun wurin wanka ba, da tana wasta ruwa cikin bathroom din hospital amma yanzu angano she's not a patient aka hanata wanka wurin. Yanzu ta manta rabonda ta sakawa jikinta ruwa. Kosai ta saya na hamsin ta zauna nan ta ci tana jiran matar ta gama su tafi.
Sai wajen 10:30 matar ta gama ta tattara kayanta dija tabi bayan ta suka tafi gidanta
Suna isa ta nuna mata kewayenta
"Bissimillah...." Matar ta fada mata,
"To...na...gode..." Dija ta fada ta nufi tiny toilet din, tana shiga taga empty bucket, daukowa tayi,
"Ina...ruwa...da sabulu?..." Ta tambayi matar da ke kaikaye gidanta saboda yanda yara suka hargitsa mata gida.
"Ga ruwa cikin wannan drum..." Ta fada tana nuna mata drum dake tsaye
"Sannan da akwai sabulu bakin window..." Ta nuna mata inda soap yake, jiki na rawa ta debo ruwa, bata diba da yawa ba ta dauka ta kai toilet sannan ta dawo ta dauki sabulun.
Tana rufe kofa ta fara rage maranta sannan ta cire kayan jikinta, tana yi tana dan cije labe ko ina ke mata zafi oho, tana gama cirewa ta ratayesu, tsayawa tana shafa cikin ta,
"Yau zamuyi wanka...." Ta fada cikin whisper, hannunta biyu rike da tummy dinta ta jingina da bango, sai tayi saurin dagowa tare da Dan sakin kara, hannu ta dan zagaya bayanta tana tabo inda keyi mata zafi, still inda ammi ta doketa da itacene, tana tabawa taji kaman wajen na ruwa. Kurawa cikinta ido tayi kaman baa gobe, tana shafawa tana murmushi,
"Ko ta ina zaka fito?...." Ta tambayi cikin, ahankali ta duka ta fara watsawa jikinta ruwa sannan ta dauki soap da soso dake rataye ta fara wanke jikinta kaman wacce bata taba wanka ba, the more tana wanke jikinta the more tana jin relief especially her private part, wani irin sakayau taji, bag dinta dake gefe daya ta bude ta dauki wata riga amma ba neat one ba, saka kayan tayi ta maida wanda ta cire sannan ta fito. Adua take Allah yasa matar tace ta zauna ko da na minti ashirin ne,
"Na...gama...." Ta fadawa matar, juyowa matar tayi da murmushi fuskanta
"To dija...." Ta amsa mata
"Nagode...." Dija ta fada mata ahankali,
"Babu damuwa...." Ta amsa mata. Ahankali dija ta juya ta bar gidan.
Wankan datayi yasa taji kaman ta samu wuri ta kwanta, still tana jin yunwa cos kosan bai isheta ba, tana tafiya cikinta na crumbling,
"Yi hakuri....kudin mu ya kusa karewa....dole muyi maleji...." Ta fadawa cikinta tana tafiya.
Wani waje Mara yawan mutane ta samu ta zauna nan kasa tare da mike legs dinta ta harde hands dinta kan cikinta ta zauna tana kallon masu wucewa.
A kano kam ba karamin shagali ake ba, family house dinsu yazid ya cika tatul da mutane. Da mufida tazo ranar Friday tambayan yazid hajuya karama tayi ta sanar da ita zai zo yau asabar, mom dinshi kam haushi da takaici ya cikata da bata ga yazid ba, amma data tambayi Hajiya karama ko tayi waya da yazid sai ta shaida mata mufida tace zai zo yau. Hakan yasa ta dan kwantar da hankalinta.
Yau tun ten suke saka ido don ganin yazid amma babu shi, number shi mufida ta kira taji switch off. Mom dinshi fada ta dinga yi dataga har karfe 1 babu yazid kuma karfe biyu ake daurin auren. Itama kira tayi taji kashe
"Wannan yaron na naiman raina ni ko?... Zai ci ubanshi ne..." Inji mom dinshi dake tsaye kusa da Hajiya karama cikin wata karamar daki wanda babu kowa,
"It's not late...kilan ya iso kafin daurin auren..."
"I doubt that... Gashi wayanshi bai zuwa?... Wallahi in bai zo ba to he better remain in abuja... Don ranshi zaiyi mugun baci in har ya taka Gidan nan...."
Inji Hajiya babba dake huci
"Kiyi hakuri anty..kinsan yazid ya chanza...nidai Allah yasa yaga dija ko hankalin kowa ya kwanta...." Inji hajia karama in a calming tune. Hajiya babba bata kara cewa komai ba ta fice daga wurin, Hajiya karama daukan wayanta tayi ta sake trying number yazid amma shuru.
Yazid dai nan zuwa gidansu ammi driver ya fito ya fara shiga da kayan da yazid ya sayo. Ammi ta koma rai da kashi don babu sauran flesh jikinta, duk wanda ya ganta sai yayi tunanin bazata kai hour daya da rai ba, yazid yayi sallama ya shiga bayan an gama shiga da kayan, an gidan ya fara gaidawa suna amsa mashi, da suna fushi dashi kan abinda yayiwa jikansu amma yanzu sun gane haka Allah ya kaddara, ji yayi binto nacewa
"Har yanzu bamu ga adda ba...." Ta fada mashi don tasan saboda ita yake zuwa. Nan take yazid yaji legs dinshi sunyi sanyi, amma daman he wasn't expecting su ganta. Inda ammi ke kwance ya nufa, gabanta ya durkusa ya gaidata, ko bude ido batayi ba balle ta amsa mashi, sai nishi kawai take
"Dan Allah ki bari in kaiki asabiti....dan Allah ki rufamin asiri kar hakkinku yayi min yawa...." Inji yazid dake magana kaman zaiyi kuka, still ammi bata ce kala ba, yafi minti goma nan durkushe amma ko eyes bata bude ba balle ta tanka mashi, ahankali ya mike ya je wajen tsohon gidan. Request ya nema kan a fadawa ammi ko zata yarda ya kai ta hospital, tsohon mikewa yayi ya tarda ammi inda take kwance ya dinga sauke mata zafafan words wanda yasa ammi fashewa da kuka
"Zanje...." Naji ta fadawa tsohon,
"Maza tashi ki shirya...in banda abinki ai wannan yaron nada tsoron Allah...ji yanda yake wahalan zuwa nan....INA tabbatar maki in wasu ne ko tunawa basuyi....maza tashi ..." Ya daka mata tsawa, ahankali ta mike jikinta sai rawa kawai yake Kaman 100 years old woman. Da taimakon binto ta shirya, yazid na waje yana jiran fitowanta, few minutes later ta fito binto rike da hannunta, sai wata mata dake biye dasu. Da sauri yazid ya bude mata bayan motan ta shiga da binto sai yaruwan ammi.
Shima yazid shiga yayi,
"Ka kaimu asiti...." Yazid ya fada ma driver,
"Wanne?..." Driver ya tambayi yazid,
"Nima ban sani ba....amma ka kaimu mai kyau..." Yazid ya amsa mashi, tada motan driver yayi yana cewa
"Ko in kaiku general hospital?..." Da sauri yazid yace
"Aa...nasan da akwai cikowa..."
"Zanyi masu bayani tunda momin abokinka babbace a asibitin... Na tabbatar basu bata maka lokaci..." Inji driver,
"In ka tabbatar da hakan mujeto..." Ya fada ba don yaso ba don shi anything general ba so yake ba.
Around three suka kama hanyan cikin gari, ammi ta jingina idanuwanta lumshe,binto sai kalle2 kawai take, adaidai lokacin da suka kusa isa gate da zai sadasu da hospital ita kuma dija ta taho zata cin abinci rana don tun wannan kosai bata kara cin komai ba duk don tayi manejin yan kudinta da baifi 1k ba, binto ta fara ganinta daga nesa amma bata yarda cewa itace ba, shima yazid ya ganta kuma kallo daya yayi mata ya kauda kanshi gefe, da sauri ya kara maida kanshi yana kallon ta while motan na shiga hospital, da sauri binto tace
"Laaaaa....wannan kaman.. Adda dija...." Tafada da sauri, da sauri ammi ta bude ido, yazid ji yayi gabanshi yayi mugun faduwa,
"Stop the car!!!!!....." Ya fada cikin muryan da shi kanshi baisan yana dashi ba,
"Adda!!!!...." Binto ta kwalawa dija dake wucewa gefensu, dija daga kai tayi sukayi ido hudu da binto, tsayawa tayi tana kallon binto then ammi data fashe da kuka ganin yanda dijarta ta koma kaman almajira ga kuma ciki, yazid dai mutuwar zaune yayi yana kallon dija at the same time hawaye na bin juna, dija na tabbatar amminta da binto ta gani ta saki bag dinta ta fara bin motan nake Neman wajen parking da gudu tana kira ammi on top of her voice, motan na tsayawa ta karasa wajen tarufe Marfin motan ta bude, nan take ta fada jikin ammi tana kuka, babu abinda take cewa sai
"Ammi....ammi...kiyi hakuri....ban...karawa....ammi waje nake...kwana.....ammi kalli cikina....ammi Dane cikin cikina...ammi yana motsi..ammi...ki maidani gida....ammi kar ki barni nan...ammi ban kara yi maki gardama....ammi dan Allah ki maidani gida in barjin sanyi daddare....." Yanda take magana sai ka rantse Mara hankali ce, babu abinda yazid yake sai kuka, yana hawaye hannunshi biyu kan bakinshi. Dija kara rike ammi tayi tana kuka tana magana, binto kuka likewise sis din ammi, shima driver dake zaune kusa da yazid juyawa yayi yana kallon yar yarinyan dake irin wannan maganar shima saida hawaye ya tarar mashi, ammi tallabo face dinta tayi
"Dijata...." Tafada cikin kuka, dija na kuka jikinta na rawa ta kama hannun ammi
"Ammi ki taba kiji....yana motsi...." Ta fada cikin matsanacin kuka, tun yazid na hawaye kawai sai kukan taci karfinshi, jin kukan mutum yasa dija daka kai ta dan leka gaba, nan suka hada ido da red and tearful eyes din yazid, da sauri ta mike tana
"Ammi shine....ammi wallahi shine...." Tana maganar tana ja da baya, ganin mota ya taho ita kuna na ja da baya2 yasa yazid saurin fita daga cikin motan, aikam tana ganin ya fito kuma su ammi basu hanashiba yasa ta juya da gudu wanda yayi daidai da zuwan motan. Before driver Motan ya taka break it was late, wani irin karo dija tayi da motan yayi sama daita.
Hannu yazid ya dafa ga kai tare da saki wani irin razanannen ihu.
🧡💜💙💚💛❤
NA CUCE TA
💜💙💚💛❤🧡
®Zuwairat (ummumaryam)
2⃣9⃣
_Follow me on:_
*Wattpad @ummumaryam29*
*Email:Zuwairat.nuhu@gmail.com*
*IG: zuwairatummumaryam*
*Website:Www.ummumaryam.com*
*And also join my new Facebook group: Zuwairat ummumaryam and Zuwairat ummumaryam page.*
*Snapchat: ummumaryan29*
Ammin data dade batayi tafiyan kirkiba sai gata ta fito daga cikin mota da gudu, haka zalika su binto da driver dake cikin mota, yazid bai San sanda ya karasa inda dija ke wance ba, shima doc daya bugeta fitowa yayi cikin tashin hankali,
"Khadija!!!....." Yazid ya dinga kiranta yana rike daita nan kasa, hannu ammi