You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
kuka, baki ammi ta bude tana kallon ikon Allah, tana mamakin yanda komai sai dija ta hada kanta da kanwarta, komai Bata yarda itace babba sai tace su binto kasa da kasa
"Wai ke in tambayeki... Ke da binto waye babba?..." Ammi ta tambayeta tana kallon yanda idanuwanta suka chanza kaman zatayi kuka
"Ni..." Ta amsa mata ahankali,
"To meyasa komai sai kin hada kanki da binto?... Baki San kome kika shi su ma Zasuyi ba?... Ke ce babba son haka ki dinga daukan girma..." Ammi ta fada mata cikin lallashin,
"To ammi..." Ta fada rana turo baki don ko kadan Bata gamsu da maganar ammi ba, kullum komai ita, shiyasa kullum tana aduan Allah yasa a dauketa, har wani lokacin adua take tana cewa
"Allah kasa a saceni a kaini katon gida ko shara da wanke2 in dingayi..." Take fada duk lokacin da take tallan fura ba kaman in ta zama frustrated.
"Maza tashi kar a fara ba dake ba..." Ammi ta fada mata,
"To..ammi amma ki bani ashirin din in kashe in naje chan..."
"Ban baki ashirin... Amma ga goma..." Ammi ta fada mata tana bata naira goma daga cikin kudin data kawo, amsan kudin tayi Ta bude wata old Ghana must go ta dauko wata old and faded pant tare da kyalle ta cire pant dake jikinta ta saka Wanda ta dauko tare da tura kyallen data dauko, ta gyara daurin dankwalinta tana fita daga gidan babu hijab, tana tafiya tana kallon yara dake wasa cikin hasken wata har ta kai kusa da wani mai nama, karasawa tayi kusa da inda mutum yake
"Danmusa inayini..." Ta gaida shi tana kallon naman dake maiko a gabanshi
"Khadija ya kike?..." Inji saurayin Wanda bazai wuce shekara 18 to 20 ba
"Lafiya lau..." Ta amsa mashi ko blinking batayi saboda yanda take kallon naman, murmushi yayi
"Har kun dawo kenan?..."
"Eh..." Ta amsa mashi atakaice, har lokacin tana kallon naman tana aduan Allah yasa ya yanmata kaman yanda ya saba,
"Makaranta zaki je?.." Ya tambayeta
"Eh...", dariya saurayin yayi yana kallon yanda take lashe baki, yanka uku ya debo ya zuba cikin takarda ya mika mata, kaman zakin daya shekara bai ci abinci ba ta miko hannu zata amsa sai saurayin ya maida hannun shi yana kallon ta Sannan yace
" yaushe zaki bani amsa ta?..." Ya tambayeta ahankali, Dan turo baki tayi tana cewa
"Gobe..." Dariya saurayin yayi
Hmm dija sarkin wayau..kullum sai kice min gobe...to yaushe goben zai iso?..." Da Sauri tace
"Allah gobe zan baka amsa..."
"Allah ya kaimu goben... Amma in baki bani amsa ba bazan kara baki nama ba...kin amince?.." Da Sauri ta gyada mashi kai tana cewa
"NA amince..." Sai lokacin ya mika mata naman, tana amsa ta bar wajen da Sauri tana bude takarda naman, tana tafiya tana yaga kadan2 wai don kar ya kare. Haka tana zaune makaranta tana cin namanta ahankali daman she's use to it.Har aka tashi karfe goma dija bata gama cinye naman ba saboda yanda take yagan daman ahankali. Ana tashi ta tafi gida tana hamma, daman Tasan kafin ta iso duk sunyi bacci don haka tana shiga gidan taja kaurensu da baida sakata taje ta kwanta tana tunanin yanda gobe zai kasance mata.
Yazid bai shiga apartment dinshi ba sai bayan sallan ishai daman mostly sai bayan sallan ishai yake shiga gida don quarters din is very lonely Kuma shi bayason hayaniya most especially Kuma ba yanayin halinsu daya da sauran guys din ba don mostly su da yan mata suke wining time dinsu shikuma da calling iyayenshi ko Kuma karatun alquran sai kuma kiran mufida Wanda wani lokacin da wayan yake kwantawa a kunnenshi saboda ita.
Yana shiga apartment dinshi Wanda ta hadu daga company don komai is made abroad, ko zama baiyi falo ba ya shiga daya daga cikin four bedrooms din ya cire kayan jikinshi yayi folding dinsu tamkar mace ya ajiye su cikin closet ya shiga wanka ta fito bai wani shafa mai ba ya saka jallabiya Sannan ya dauki wayanshi yayi dailing number Hajiya babba
Alokacin duk suna babban falon alhaji suna fira yara suna wasa sai sai yanmatan na chatting da wayansu ga katon naman akuya roasted suna ci ana hira, Hajiya dauka wayan tayi yan yara suka taho wurin ta da gudu don sun san shine cos mostly lokacin yake kiran su, sallama Hajiya babba tayi ya amsa yana cewa
"My mommy good evening..."
"Evening sweetie... Ya aiki?..."
"Alhamdulillah... Ya gida da yara?..." Ya tambayeta a nutse, da Sauri yaran sukace
"Yaya ga mu...." Suka fada a chorus, Dariya yayi, Hajiya babba ta ajiye masu wayan bayan ta sashi hands free, nan suka fara labari ko wa NA bashi labarin abubuwa kala saida suka gama Sannan Hajiya babba ta dauki wayan suka fara hira tana cewa
"Son ga junior mom tana hada maka party till dawn..." Dariya yayi yace
"Small mom...nasan kina jina...banason party till dawn..." Ya fada yana Dariya,
Itama dariya tayi Sannan tace
"Kayi kadan..." Tafada cikin high voice, yanda zai jita da kyau, dariya ya karayi yana cewa
"Nidai ko kun hada ban zuwa...sai dai kuyi abunku Ku kadai..." Yafada cikin raha yana jiran amsan small mom don yasan ta da tirjewa kan abu,
"Ai kayi kadan yaro...party kam an hada an gama..." Ta fada again da karfi, alhaji kam ko kallon su baiyi sai cin naman yake yana korawa da juice while suma yan yaran suna ci suna wasa.
"Wai yaushe zaka dawo?..." Hajiya babba ta tambayeshi,
"Sai nan da sati biyu..." Ya amsa mata
"Kai yaro maza ka dawo...nan da sati biyu is too far..." Inji Hajiya karama,
"Sai lokacin hutuna zai fara..."
"Nidai ka dawo nan da sati daya..." Hajiya karama ta umarceshi,
"To momcy..." Ya amsa mata in a funny way.
"Ina twins?..." Ya tambaya, don haka yake kiran Sharif da shahid,
"Basu dawo ba..." Hajiya babba ta amsa mashi
"Aikensu akayi ko yawon ne Mara amfani?..." Ya sake tambaya, dariya Hajiya karama tayi tana cewa
"Suna waje suna shan iska...."
"Ai ba zafi ke da akwai cikin gidan ba...bari in kira su..." Ya fada Sannan sukayi sallama, kashe wayan yayi Sannan yayi dailing number shahid, alokacin Sharif na tukin mota shi Kuma shahid na zaune, yana chatting, yana ganin kiran yazid ya kalli Sharif yace
"Guy ga vigilanty NA kira..." Yafada yana dariya, shima Sharif dariya yayi
"Kar kayi picking.. Kilan ya kira gida an fada mashi muna waje.." Kin picking sukayi har wayan ya gama ringing, yazid dai girgiza kanshi yayi yana murmushi
"Sheggu..." Ya fada yana dailing number mufida. Sai da suka kusa hour biyu suna waya Sannan sukayi sallama ya kwanta yana imagining nan da sati four yana da aure.
The following day ya shirya as usual ya tafi office daman a chan ake kawo mashi breakfast.
Dija kam sai data gama surfe geron ta wanke ta shanya Sannan ta shiga wanka, acikin karamin toilet din Wanda babu cement ta tsaya tana kallon tsaraicin ta, daman tunda alamun girma suka fara fito jikinta ta maida kanta tamkar madubi ba kaman in ta shiga kewaye, yau ma haka ta tsaya tan kallon white skin dinta dake fari tas compared to her face don jikinta ya fi fuskan ta haske nesa ba kusa ba, kallon yan boobs dinta tayi ta kurawa dark nipple dinta ido tana mamakin yanda akayi Bata lura da sanda suka fara fitowa ba don ita kaman farat daya ta fara ganin su,Dan juya baya tayi tana kokarin kallon ass dinta amma Bata gani kaman yanda ta bukata, tafi minti talatin tana kallon kanta don ko kadan Bata gajiya da kallon kanta
"Wai ubanme kike in kika shiga kewaye?..." Ammi ta fada da karfi, da Sauri tace
"Ammi kashi nake..."
"Ke kullum sai in kin shiga wanka kike kashi?... Dalla maza ki fito kafin in sameki..." Ammi ta daka mata tsawa
"To.." Ta amsa mata Sannan ta fara wanka. Ko.minti biyar batayi ba ta fito da daurin kirji ta shiga daki ta shafa Vaseline ta saka wata faded but neat atamfa Sannan ta fito lokacin ammi NA jifan Dan wake cikin tukunya
"Ke dauki yaji ki daka.." Ammi ta fada mata, turo baki ta karayi don one thing about khadija ko kadan batason aiki ko sai goma zaa aiketa sai ta nuna bacin ranta dukda zatayi amma ba don ta soba
Haka ta daka yaji tana turo baki har ta gama, bayan kaman minti arbain aka sauke danwake sukaci Sannan ta tafi injin din. Da wuri ammi ta gama mulmula mata furan amma still sai bayan sallan asar suka tafi tallan.
Hajiya karama ce zaune kusa da Hajiya babba a falon Hajiya babba tana cewa
"Gaskiya yaya nidai NA gaji da halin wannan yarinyan... Kokadan Bata daukan darasi...ka barnatar da kaya..gaskiya wata yar aiki zan sake..." Inji Hajiya karama, Hajiya babba shuru tayi for a while kaman mai tunani Sannan tace
"To me zai hana a karo maki wata batare da ki kori ita zulan ba?.." Hajiya babba ta fada mata, da Sauri Hajiya karama ta girgiza kai
"Gaskiya ni ko kadan banason zama da wannan yarinyan yanzu..Kawai wata zansa antyn katsina ta samo min..." Dariya Hajiya babba tayi tana cewa
"Har katsina Neman yar aiki?..."
"Yo yaya ya zanyi ?.. Ai gara katsina tunda yawancin yan Matan birnin nan sun fiya wayewa...amma in aka samu cikin kauyen kayayau basu daukan abu for granted,..." Inji Hajiya karama
"To shikenan amma Dan Allah karki sallami zulai...kinsan babu kyau hana mutum hanyan samun abinci.. Kawai a nemo maki wata ki hada su biyu..." Inji Hajiya babba,
"To shikenan...amma yarinyan nan taci arzikinki wallahi.. Don da nayi niyyan da an kawo min sabuwa zan sallami shegiya ta je Chan gidansu ta bar na tar masu da abinci kaman yanda take nan..." Yanda tayi maganar yasa Hajiya babba dariya
"Wallahi kin Iya bada dariya..." Inji Hajiya babba, itama Hajiya karama dariya tayi
"Ai yarinyan ce da ban dariya...sai ta kusa karar da dettol daya wajen wankin toilet...jiya daga nace ta hadawa Ameera tayi tayi fulling jug da tea ta mika mata..." Hajiya dariya ta karayi,
"Funny Wallahi.. Sakarcinta is written all over her..." Inji Hajiya babba,
"Aikam am feed up with her wallahi... Amma bari insa a samo min wata kilan tayi learning daga gareta don NA lura su ma yaran suna son sakarcinta especially Ameera..."
"Yo daman yara haka suke...sunfi son naughty people..." Inji Hajiya babba, Hajiya karama Bata kara cewa komai ba ta dauki wayanta tana cewa
"Bari in kira yayan katsina muji ko zan samu mai aikin...." Ta fada tana dailing number elder sis dinta dake aure a katsina
馃挌馃挋馃挏馃枻鉂ゐ煉�
NA CUCE TA
鉂ゐ煉欚煉涴煐ゐ煉滒煉�
庐zuwairat(ummu Maryam)
4鈨�
_Three days later_
Dija ce dauke da roban furan ta tana yawo tana shiga manyan gidaje don ita gani take yan kananan gidan basu da kudin siyan fura
"Duk daya muke daku..." Take fada duk sanda taga yar karamar gida. Tana cikin tafiya ta shiga cikin wani beautiful house, daga tsakar gidan ta hangi wata mata zaune kan carpet tana waya, daman ta taba shiga gidan Kuma an saye dukan furanta, hakan yasa ta tsaya Bata tafiba ta tsaya tana sauraron abinda matar ke cewa
"Eh wallahi Hajiya ce tace kanwata na son yar aiki Kuma duk Wanda NA samu sai suce Kano yayi masu nisa..." Ta fada ahankali tana sauraron abinda ake fada mata, bayan few seconds ta kara da cewa
"Ni ma ko kadan banason ace wasu su kai mata yar aikin ba muba saboda cewa tayi yayarta matar isa bala ce..kinga da akwai samu...." Ta fada Sannan shuru ya kara biyo baya tana sauraron abinda ake fada mata,
"To shikenan.. Dan Allah ki bincika.. Nima zan cigaba da nema amma fa ance wacce zata Iya aikin komai..." Matar ta fada, dija kam duk tana jin abinda matar ke cewa, shuru tayi tana tunanin inama a dauketa, bayan kaman minti biyu matar ta kashe wayan ta Sannan ta daga kanta ta kalli dija, da Sauri dija tace
"Kuna sayen fura?..." Ta fada ahankali, matar murmushi tayi Sannan tace
"Ki kawo in gani..." Ta fada mata fuskan Hajiyan dauke da murmushi da ganinta kasan irin yan duniyan nan ce don da gani tana shan taba, ahankali dija ta karasa ta sauke furan gaban Matan ta yaye ledan furan don matar ta samu daman ganin furan da kyau,
"Kece kika kawo min fura kwana kin baya?..." $ matar ta tambayeta, da Sauri dija ta gyada mata kai tare dacewa
"Eh nice..." Ta fada har lokacin Bata daina tunanin abinda taji matar NA cewa ba,
"To ki bani NA dari biyu in saka a fridge...don naji dadin furan kwanakin baya..." Da Sauri dija ta dauko Leda daga gefen roban ta ta fara zuba furan cikin natsuwa kaman ba ita ba, sai da ta gama ta ta dauko biyu ta kalli matar tana cewa.
"Ga gyara..." Ta fadawa matar, murmushi matar tayi Sannan tace
"Nagode..." Ta fada tana daukan purse dinta, budewa tayi ta dauko dariya biyu ta Bata, dija ta amsa tare dacewa
"Nagode..." Rufe furan tayi da ledan Sannan ta mike tana son yiwa matar magana amma ta kasa, daukan furan tayi har ta kai bakin gate ta juyo ta kalli Matan dake latse2 wayanta, tsayawa tayi bakin gate din Wanda yasa matar kallon ta,
"Lafiya dai ko?..." Matar ta tambayeta, da Sauri tace
"Eh...daman...." Sai tayi shuru, matar tsaya kallon ta tayi don sauraron abinda zatace, jin tayi shuru Kuma Bata tafi ba yasa ta cewa
"Daman me?..." Inji matar cikin natsuwa, dija kasa cewa komai tayi Kawai tayi tsaya kikam dauke da robanta akanta,
"Dawo inji..." Matar ta fada mata, ahankali dija ta dawo , gefen ta matar ta nuna mata
"Sit..." Matar ta fada mata, dukda dija batajin turanci ta gane abinda matar ta fada mata, ahankali ta sauke roban kanta ta zauna gefen Matan.
"Ki fada min...me kike son fada min..." Matar ta tambayeta, dija dai shuru tayi tana wasa da yatsunta,
"Ke nake sauraro..." Matar ta sake fada mata, ahankali ta fara cewa
"Daman....naji...kina...cewa....kinason... Mai..aiki...shine..." Sai tayi shuru saboda yanda gabanta ke faduwa, Matar ta gane inda ta dosa dukda muryanta NA cracking
"Ina jinki..." inji matar,
"Nace..in..babu...damuwa....zan....yi..." ta kai.karshen maganar da kyar, murmushi matar tayi tana cewa
"Da kaman bazaki ida maganar ba...kina Iya aikin ne?..." Da Sauri dija ta gyada mata kai tana cewa
"Eh.." Yanda tayi maganan yasa matar dariya tana cewa
"In iyayenki basu yarda ba fa?..." Da Sauri tace
"Babanmu ya rasu..nasan ammi zata yarda...in kin je ..kin fada mata ..." Ta fada muryanta na cracking, matar kura mata ido tayi tana kallon beautiful and innocent face dinta Kuma tana tunanin wane irin dalili ne zaisa yarinya ta so zuwa gidan aiki Kuma da kanta ba wai forcing dinta akayi ba, amma tana kallon how faded her hijab and wear looks sai ta gane she will definitely needs some income Kuma Tasan ta cancanci irin gidan da ake magana.
"In Bata amince ba fa?.." ta sake tambayan ta, muryan NA rawa tace
"Nasan zata yarda..." Ta Bata assurance dukda tana ganin da kyar hakan zai yiwu don Tasan stand din ammi kan barin ta tafi wani wuri aiki amma gaskiya ta gaji da wannan wahalan tallan Kuma tayi deciding zatayi anything necessary don ammi ta amince NA wannan zancen
"Wane wuri kike?..." Ta tambayeta, nan dija ta fada mata sunan kauyensu, baki matar ta bude
"Yanzu daga Chan kuke zuwa nan cikin garin?.." Kai dija ta gyada mata
"Lallai kam..amma ina ganin da nisa Kuma aikin ba a garin katsina zaayi ta..Kano ake bukatan mai aiki..." Da Sauri dija ta katseta dacewa
"Ai ba komai... Tunda baa kasa zanje ba..." Dariya matar tayi
"To..yanzu tunda an fadamin ana bukatan mai aikin da wuri bari in kaiki garin naku sai muyi magana da amminki..." Wani irin dadi dija taji amma sai cewa tayi
"Ai ban gama saida furan ba..." Dariya matar tayi tana cewa
"Ki kirge min sauran..." da Sauri dija tayi counting sauran cikin Leda ta mika mata
"NA nawane?..." Matar ta tambayeta
" sauran na dari uku da sabain..." Dari biyar matar ta dauko ta Bata,
"Ki jirani nan..." Inji matar Sannan ta shiga cikin falonta, Bata yi wasting time ba ta fito da gyale tare da car keys dinta, sai adua take Allah yasa a amince don Tasan ba karamin samu bane in kayi hulda da family isa bala, dija sai mar mar da idanuwa Kawai take, mota matar ta fidda daga parking lot dija ta shiga ciki duka kama hanyan garinsu.
Karfe biyar da minti ashirin suka iso kofar gidansu dija, da Sauri dija ta fita ta shiga gida matar ta fito tana kallon kauyen tana mamakin
Ya akayi suke rayuwa a irin wannan wuri don tamkar bayan duniya suke saboda karanta kauyen, dukda ba cikin gari take ba amma Sam batasan daura yayi extending zuwa haka ba. Dija na shiga gidan ta fara kwala ammi kira
"Ammi!!...ammi!!!..." Ta dinga fada tun.zaure, ammi dake kada miyan kuka ta mike da Sauri saboda yanda gabanta ya fadi don kiran dija har cikin zuciyanta saboda yanda take kwala mata kira on top of her voice, da Sauri ta ta taro dija dake shigowa, kallon ta tsaya yi hannun ta dafe da kirjinta,
"Dija lafiya?..." Ta tambayeta cikin tashin hankali, dija kallon ta tayi da gwala2 idanuwanta tana murmushi
"Ke lafiya?..." Ammi ta sake tambayeta tana kallon ta from head to toe,
"Lafiya lau..wata Hajiya ce ta zo wurin ki..." Ta amsa mata tana ajiye roban furan ta, kallon mamaki ammi tayi mata,
"Wacce Hajiya?..." Ta tambayeta,
"Gata nan..." Dija ta fada tana nuna matar data shigo cikin gidan da sallama, da Sauri ammi ta amsa tana kallon ta,
"Barka da zuwa...shigo mana..." Ammi ta fada jikinta NA rawa don batasan abinda dija tayi ba da aka biyota, da Sauri ammi ta shiga cikin dakin matar ta bi bayanta tare da daga labulensu da ya kasu kusa kashi takwas saboda yanda ya yage, ta kasan wusiya matar ta dinga kallon dakin tana mamakin how living creature can sleep in such an awful place, ammi kakkabe tabarma dake kasa tayi jikinta sai rawa yake Kuma zuciyanta tamkar ya fito ta bakinta saboda fargaba. Dija kam gefe daya ta tsaya tana aduan Allah yasa a samu nasara, Da Sauri ammi ta debo ruwa cikin randa ta mika wa matar tana cewa
"Maraba..maraba..." Cikin faraa matar ta amshi ruwan amma tasan ko da wasa bazatyi gigin kai kofin bakinta ba, rike cup din tayi tana kallon dija dake ragube jikin bango tana kallon su, murmushi ta sakar mata itama dija tayi karfin halin maida mata martani, ammi durkusawa tayi kasa kneels dinta biyu kasa sai tafin hannun ta biyu suma kasa
"Ina yininmu..." Ammi ta gaidata, cikin faraa matar ta amsa da
"Lafiya lau..ya gida ya yara?...."
"Lafiya kalau suke...." Ammi ta fada Sannan tayi shuru tana sauraron abinda ke tafe da matar, ahankali matar ta ajiye cup din Sannan ta fara cewa
"Sunana Hajiya Aisha...ina zaune a cikin garin daura...ina Sana'a kala2 cikin su har da kai yara gidan gidan manyan mutane don suyi masu aiki don gyara rayuwan yaran..." Ta Dan yi shuru ita Kuma ammi dai tana nan durkushe tana sauraron ta, Hajiya Aisha ta cigaba dacewa
"To da akwai wata kanwar aminiyata dake son mai aiki karama daidai kaman yarki dija...shine ta shaidamin..." Da Sauri dija ta dan buga kafa kasa wai ita mai wayau don kar ta fadi ita tace tana son aikin, Kuma Hajiya ta gane sai tayi shuru ta chanza maganan zuwa
" shine naga yarki nace bari in biyo in tambaya ko zaki amince in kaita..." Ammi da kanta ke kasa sai ta fara girgiza kai alaman AA, dija dake tsaye tana kallon su nan take taji kwaiwanta yayi sanyi don Kawai so take ta je.
"Gaskiya Hajiya kiyi hakuri... Yarana marayune...nice uwarsu nice ubansu tunda yawancin yan uwan ubansu basu damu da suna raye ko suna mace ba...nasan muna cikin hali amma gaskiya nafison in wayi gari in gan dukkan yarana kusa dani...ko kadan banason abinda zai taba masu mutuncinsu saboda nasan yanda ake wulakanta marasa karfi cikin birni..." ta fada ahankali cikin natsuwa da sanyin murya Kuma har lokacin bata mike daga inda take ba, ahankali matar ta daga kai ta kalli dija da idanuwanta suka ciko da kwallan bakin ciki, murmushi Hajiya ta saki Sannan tace
"Babu komai...amma yar uwa inason in shaida maki cewa babu inda mutuncin ya mace ke saurin zubewa kaman talla saboda yanda duniya ta lalace... Da akwai maza azzalumai Wanda suke gurin lalata rayuwan yaran mata mussanman wayanda ke yawo kan titi...." Ahankali ammi tace
"Allah NA tsarewa ai...ni kaina don babu yanda zanyi ne amma ko kadan yata Bata talla" Ta fada cikin sanyin murya, ahankali Hajiya Aisha tace
"ga dama nan...NA daya yarki Bata zuwa koina tana cikin gida..Kawai ta kula da bangaren uwar dakinta Kuma ba ita kadai bace...Sannan duk wata zaa aiko da albashinta Wanda INA tabbatar maki yafi talla saboda ita Bata wahala ba ke baki wahala ba....Kuma wannan gidan da nake fada maki suna kuka da masu aikinsu tamkar yaran da suka Haifa don har boko da islamiyya suke saka su sai na karshe ina tabbatar maki dacewa zaa kare maki mutunci yarki...don haka ina baki shawaran da zan bawa kaina...ki gwada ki gani in hakan baiyi maki ba kina iya bukatan a maido maki ita...." Hajiya Aisha ta karasa maganar ta tana kallon dija dake hawaye, ammi dai shuru tayi har saida Hajiya ta kai aya Sannan tace
"Ni gaskiya nafison in tashi in ga yarana kusa dani...Sam hankali na bazai kwanta ba duk lokacin Dana tuna yata tana wani wajen Kuma basan irin halin da take ciki ba..." Ta fada kanta kasa, da Sauri dija ta fita daga dakin tayi waje ta fara kuka sosai kaman an doketa
"To shikenan... Allah ya shige mana gaba..amma zan dawo gobe koda kin chanza shawara.. Ba don komai yasa na fadi hakan ba sai don dija ta shiga raina...haka nan naji ina sonta tamkar nawa..." Itadai ammi shuru tayi Bata kara cewa komai ba, Ahankali Hajiya ta mike tare da dauka handbag dinta, itama ammi mikewa tayi tana cewa
"Don Allah ki tsaya kici turo..." Dariya Hajiya Aisha tayi
"Aa ..nagode kwarai..." Itama ammi Dariya tayi tana cewa
"Ai Baku Iya cin irin abincin mu dake lami..."
"Sam ba haka bane...Kawai na koshi ne..." Ta fada tana fitowa waje ammi na biye daita har waje, ta wutsiyar ido ta kalli kukan dake tafasa tsanwa shar babu alaman kayan miya ciki. Kallon yaran ukun dake zaune tayi ta bude bag dinta ta Ciro Dari biyar ta mikawa babban cikin su wato binto, durkusawa tayi ta amsa tana cewa
"Mun gode..."
"Haba Hajiya...har da wata hidima...mun gode kwarai Allah ya saka da alkhairi..." Tafada tana raka ta zaure,
"Babu komai... NA gode nima...sai goben..." Hajiya tafada tana fita waje, sai ihun dija ke tashi duk ammi najinta amma tayi banza daita dukda Tasan halin yarta da kwallafa amma saidai ta mutu. Hajiya kallon dija data Dora hannu bisa kai tayi tana Dariya
"Haba dija...ki bar wannan kukan mana...in Bata amince ba to Allah bai kaddara zaki ba..kiyi shuru kinji..." Ta fada tana kallon yanda take Bata baki tana kuka kaman anyi mata mutuwa, kara volume din kukanta tayi dataga Hajiya ta shiga cikin motanta. Da gudu ta shiga cikin gida ta kwanta kasa tana cewa
"Wallahi... Ban kara zuwa talla..."
[3:12PM, 3/20/2018] 鈥�+234 806 125 0020鈥�: 鉂ゐ煉滒煉涴煐ゐ煉氿煉�
NA CUCE TA
馃挏馃挍馃挌馃枻馃挋鉂�
庐zuwairat( ummu Maryam)
5鈨�
Tafada cikin matsanacin kuka tare da kwantawa kasa tana rolling kaman wacce akayi wa albishir da mutuwa, babu Wanda ya tanka mata su binto tsayawa sukayi kanta suna kallon yanda take birgima kasa, ko kallon ta ammi batayi ba har tagama zuba wa su binto miya kan tuwon dake cikin kwano Sannan ta shiga ciki, har lokacin dija NA kwance kasa yaran neighbors sai lekota suke don ba karamin ihu take ba tana cewa
"Ban kara zuwa talla...ban kara zuwa talla...saidai yunwa ta kashe mu gidan nan...." Ta fada cikin kuka, ammi na shiga cikin dakin ta nufi inda take ajiyan bulala ta yo waje, dija dake kwance na ganin ammi da bulala ta tashi tayi waje da gudu tana kuka,
"Shegiya da kin tsaya yar banza...." Ammi ta fada tana maida bulalan. Har bayan sallan magrib dija Bata dawo gida ba tana nan labe gefe daya tana kuka gashi har lokacin Bata bar fargaban abinda ammi zatayi mata ba.
Ammi na ganin Bata dawo ba tasa binto ta nemota, sanin inda take zama in tana kuka yasa binto bata sha wahalan gano ta ba,
"Kizo inji