google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lau..Wallahi I thought she's your daughter... Ah ina kika samo wannan beauty..." Tafada cikin raha kaman sun Dade da sanin juna da Hajiya Aisha, Dariya kawai tayi , Hajiya karama kallon yanda dija ke nonnokewa Kawai tayi ta saki Dariya
"Ya sunanki?..." Ta tambayi dija
"Kha...fi...ja..." Ta fada kanta kasa don ko sau daya Bata daga kai ba,
"Ah...ah...ah....sunan hajiyar mu gareki Ashe...kice NA samu sabuwar uwa...." Tafada cikin Dariya, itama Hajiya Aisha Dariya tayi hankalin ta kwance da Hajiya karama Bata nuna batason dija ba,
"Asabe!... " ta kwala kira, sai ga yarinya data bude masu kofa ta dawo ta durkusa gaban Hajiya karama,
"Ga sabuwar mai taimaka maki an kawo...ki.tafi da ita dakinki..." Ta umarceta, Dariya jin dadi budurwa da bazata wuce shekara sha takwas ba tayi tana nuna jin dadinta karara da samun mai rage mata aiki,
"Taso..." Ta fadawa dija, ahankali dija ta mike jikinta na rawa, sai lokacin ta daga kai ta kalli Hajiya Aisha Kawai sai ta fara hawaye, don Kawai sai taji gidansu take so,
"Ah...ki bar kuka...nan ma gidanku ne kinji?.." Hajiya karama ta fadawa dija, da Sauri dija ta hadiye kukan ta fara takawa ahankali tana bin bayan asabe, Hajiya karama kallon ta kawai take don kallon yar gidan manya kawai take mata don ko kadan Bata kama da yar talakawa, saida suka bar falon Hajiya karama ta kalli Hajiya Aisha
"Amma wannan yarinyan zata Iya aiki kuwa?... Naga she's a little bit dull..." Dariya Hajiya Aisha tayi Sannan tace
"Sosai kam Hajiya...Kawai yanzu kunya take ji..amma ina tabbatar maki.babu abinda bazata iyaba..."
"To shikenan.. Nawa ake biyan yaran da kike kaiwa gidan aiki?..." Hajiya karama ta tambaya, murmushi Hajiya Aisha tayi tace
"Ai duk yanda kika bada daidai ne..."
"To shikenan...masu aikin mu dubu talatin ake basu duk wata ga baki dayansu don haka zaa din biyanta...." Wani irin dadi Hajiya Aisha taji don tunda take kai yara gidan aiki babu inda ake biyan dubu ashirin balle talatin
"To shikenan... Hakan yayi sosai...." Inji Hajiya Aisha,
"To sai ki bada account number in bada a bawa manager kar a manta da albashinta..." Da Sauri Hajiya Aisha ta dauko Biro da paper ta rubuta ta mikawa Hajiya karama Sannan tace
"Ina yaran ne?.." Ta tambayeta
"Suna chan bangaren babban mominsu....bari in sa a hada maki wani abu naci...." Inji Hajiya karama,
"Na gode kwarai... Tafiya zanyi don inason in shiga kasuwa kafin in koma katsina...."
"Haba da wuri haka?... Haba ki bari sau gobe mana..." Injin Hajiya karama,
" sai in NA sake dawowa in Allah ya yarda..." Ta fada tana mikewa,
"Ina zuwa..." Hajiya karama ta fada mata Sannan ta bar falon bayan yan mintuna goma tadawo da wata katuwar Leda dauke da manyan atampa guda uku sai perfumes, sai kudi cikin envelope
"Gashi a rabAwa yan gida..." Hajiya karama ta fada tana mika mata ledan
"Har da wata hidima?... Gaskiya NA gode...Allah ya aka da alkhairi... Allah ya kara girma...nagode kwarai..." Ta fada cikin jindadi,
"Babu komai... Bari muje in kaiki gurin uwargidata Ku gaisa kafin ki wuce..." Hajiya karama ta fada tana shige mata gaba, bayanta Hajiya Aisha tabi har falon da yaran gidan ke wasa ita Kuma Hajiya babba zaune kan kujerana alfarma tana kallo zee aflam, da sallama suka shiga Hajiya karama ta shaidamata an kawo mai aikin. NaN suna gaisa Sannan Hajiya Aisha ta tafi bayan itama Hajiya babba ta Bata atampa da turare.


Dija baki ta bude tana tafiya ahankali tana waige2 har asabe ta bude dakinta suka shiga, dija tsayawa tayi tana kallon ikon rabbi don dakinta katuwa ne Sannan ga katon gadon da ko amaryan garinsu Bata isa ta mallakesu ba,
"Ki zauna mana..." Asabe ta fada mata amma dija bataji ba saboda yanda take kallon ceiling din dakin, kallon katon madubin dake jikin bango tayi ta tsaya tana kallon kanta, sai yanzu ta gan kanta sosai yanda take so, kallon kayan shafan dake kan mirror tayi ta dauke kanta ta kalli wata katuwar bag dake dakin
"Ki zauna mana.." Asabe ta fada tana Dariya,sai lokacin dija ra dawo hayyacinta ta kalli asabe dake dariya, sauke kanta kasa tayi tana murmushi,
"Ya sunanki?..." Ta tambayeta sounding friendly.
"Di...ja...." Ta amsa mata,
"Ni sunana asabe...sannunki da zuwa yaruwa...daga wane gari kike?..." Ta tambayeta,
"Baude...." Dariya asabe tayi
"Inane Baude?...." Dija dai shuru tayi don batasan abinda zata fada mata ba
"Ni yar dala ce...shekaranki nawa?..." Asabe ta sake tambayanta, shuru dija tayi kaman mai tunani Sannan tace
"Sha uku ko hudu..." Idanauwa asabe ta zaro
"Shine kike da tsawo haka?...wallahi nayi tunanin shekarunmu daya...Ashe ke yarinya ce...bari in dauko maki abinci...." Ta fada Sannan ta mike, fita tayi daga dakin dija ta kara mikewa ta nufi wajen split air conditioner, sai kallon abun take hannun ta ta kai wajen taji wani irin sanyi NA ratsa hannun ta, da Sauri ta dauke hannun ta takoma ta zauna har lokacin bata bar kalle2 ba. Rice and stew cike da kifi asabe ta shigo dashi ta ajiyewa dija sai ta bude Dan karamin fridge dake dakin ta dauko ruwa ta ajiye mata
"Bisimillah...." Asabe ta fada mata, da Sauri dija ta sauko kasa ta zauna ta fara cin abincin tana kara godewa Allah, daman dija Bata wasa da cikinta sai gata ta cinye abincin tas Sannan ta sha ruwa, asabe sai kallon ta tana murmushi don haka nan taji tana son dija. Sai da dija ta gama cin abincin Sannan asabe ta fara fada mata ayyukan da zasu dinga yi, itadai dija sauraron ta kawai take tana lumshe idanuwa saboda sanyin dake ratsata daman batayi bacci ba jiya
"Ko zakiyi bacci ne?.." asabe ta tambayeta da Sauri ta girgiza mata kai, Dariya asabe tayi
"In zakiyi bacci ki kwanta kafin..." Bata idaba wayanta ya fara ringing da Sauri tayi picking, shuru tayi tana sauraron abinda Hajiya karama ke fada mata
"To..." Ta amsa Sannan ta ajiye wayan ta kalli dija,
"Hajiya ta ce in kawoki bangaren Hajiya babba,..." Ta fada mata, da Sauri dija ta mike itama asabe ta mike suka fito zuwa part din Hajiya babba, sallama sukayi suka shiga kan dija kasa hannun ta rike da junansu duk yan yaran dake wasa Tare da yanmatan dake kallo kura mata ido sukayi. Durkusawa tayi ta gaidasu har da yanmatan, kallon juna sukayi suka tuntsure da Dariya suna kallonta with adorations, itama Hajiya Dariya take, rarrafawa tayi wajensu Hajiya ta kara gaidasu suka amsa suna Dariya
"Amma wannan yarinyan da abun Dariya take..." Inji Hajiya babba dake dariya, har lokacin dija na nan durkushe kasa itama asabe Dariya take, marzuq da Ameera ne suka ce
"Small mom wannan mai aikice?..." Ihsan ce ta buge masu baki, sukayi shuru don yana daga cikin tarbiyan yaran gidan basu raina maaikatansu,
"Ku koma..." Hajiya karama ta fada masu, sai lokacin dija ta mike suka koma part din Hajiya karama marzuq da Ameera NA biye dasu suna kallon dija kaman madubi don duk a masu aikin gidansu babu mai kyauwun ta, kitchen suka shiga tare dija ta bude baki, su Ameera NA biye dasu har cikin kitchen sai cewa tayi
"Tea zan sha...." Inji Ameera,Dariya asabe tayi tana cewa
"Sarauniyar shan tea..." Ta fadawa Ameera dake yar shekara 8 amma tana abu kaman yar shekara uku saboda sangarta, cup asabe ta dauko zata hada mata tea sai cewa tayi
"Bake zaki hadamin ba...ki bari ita ta hada min..." Ta fada tana nuna dija,
"To kinji da ke take..." Asabe ta fadawa dija, Dan matsawa dija tayi kusa da asabe Sannan tace
"Meye hakan?..." Ta fada cikin whisper, cup asabe ta mika mata, ta kaita ta zuba ruwa Sannan ta bude mata katon tin NA milk da Ovaltine, ta dauki spoon ta mikawa dija Sannan ta umarceta data hadasu cikin cup, yaran sai kallon su suke suna Dariya tana gamawa ta mikawa Ameera ta amsa Sannan suka bar kitchen din.


Hajiya Aisha NA fita ta duba envelope din da Hajiya karama ta Bata taga mint na Dari biyar, dadi taji tana cewa
"This is what am taking about..." Tafada cikin jindadi. Kasuwa ta shiga tayi sayayya tare da siyan wasu atampa yan 3k guda uku don ta kaiwa ammi
[3:15PM, 3/20/2018] 鈥�+234 806 125 0020鈥�: 馃挏鉂ゐ煉氿煐ゐ煉涴煉�
NA CUCE TA
馃挍馃挋馃挌馃枻馃挏鉂�




庐zuwairat( ummu Maryam)





8鈨�





Daga kitchen dinning area asabe ta kai ta Sannan dakin daukan baki sai dakin su Ameera don dakinta Kawai take gyarawa sauran yaran suke gyara wurin su da Kansu,
"Ba wani aiki ke da akwai da yawa ba...Kawai dai baa sin gani kazanta ko kadan ..." Asabe ta fada mata suna komawa dakinsu, dija dai sauraron ta kawai take don gurin ta dare yayi ta kwanta,
"Kiyi wanka mana kafin lokacin sallan magrib.. Bamu da girki yau don haka babu aikin da zamuyi saidai in Hajiya ta bukaci muyi mata wani abu..." Inji asabe,
"Ina zanyi wankan?..." Dija ra tambayi asabe cikin sanyin murya. Mikewa asabe tayi ta bude kofan dake cikin dakin tace
"Taso ki shiga...." Ta fada mata, ahankali dija ta mike ta shiga bathroom din tana kallon ikon Allah don babu abinda ta Iya amfani dashi a wurin tsaya kallon bathroom din, asabe jawo kofan ta farayi dija tayi Sauri rikewa
"Ban...Iya...ba..." Tafada muryan ta na rawa. Dariya asabe tayi Sannan ta shiga cikin bathroom din ta fara nuna mata amfanin shower da heater tare da bathtub, dija kura mata ido tayi Bata ko kaftawa har asabe ta gama Sannan tace
"Yanzu ki nuna min abubuwa dana koya maki..." Fada mata, nan itama dija ta fada exactly abubuwan da ta fada mata, mamaki ne ya kama asabe cos she explained everything perfectly. Nan asabe ta fita ta barta tayi wankan sai lumshe idanuwa take saboda yanda take jin dadin kamshin sabulun wankan. Atakaice cikin kwana uku dija ta gane kan bangaren Hajiya karama, har da sunayen yan gidan gaba daya kaman yanda asabe ta fada mata Kuma ba karamin dadi take ji gidan ba don within that three days ta chanza cos ko fita batayi Kuma gashi da sun gama aiki kwanciya suke suyi bacci, yanzu kam dija ta bar tsayawa bathroom ta kalli kanta sai dai a gaban mirror dake dakin su amma sai in asabe Bata dakin sai ta tsaya ta kunshe towel dinta ta kalli jikinta da kanta tana kashewa kanta ido tana Dariya , yauma tana tsaye gaban katon mirror tana kallon kanta asabe ta shigo da plate din abinci, da Sauri dija ta gyara towel din tana kallon asabe, itama asabe kallon mamaki tayi mata,
"Me kikeyi haka?..." Asabe ta tambayeta cikin surprise, da Sauri dija tace
"Babu komai..."
"Kaman ya babu komai..."
"Aa... Kawai wanka NA fito....shine nake shafa mai...." Tafada ahankali, asabe dai Bata kara cewa komai ba ra ajiye abincin suka fara ci,.



Yazed ne kwance yana bacci, alarm ne ya tadashi ya mike da Sauri tare da godiya ga Allah ya shiga bathroom yayi wanka Sannan ya fito daure da alwallah. Kaya ya saka yayi salla nan cikin dakin Sannan ya cire jallabiya dake jikinshi ya shirya cikin suit ya fashe kanshi da perfumes ya fito looking handsome than ever, kallon agogon hannun shi yayi yaga 6:15am
"I still have some time..." Yafadawa kanshi tare da fiddo wayanshi daga cikin aljihunshi, number Hajiya yayi dailing suka fara hira
"Son ka dawo haka nan mana...wai nan da abuja kake wannan abun kaman Wanda ke abroad?..." Dariya yayi
"Ai mom wahalan tuki nakeji...Kuma sauran sati daya hutuna..."
"To shikenan... An turo maka pic din gidan ?..."
"Yes mommy... It's beautiful... Amma nan abuja zaa kawota....".
Yafada yana naughty laugh
"Kaci gidanku...nan Kano zaa ajiyeta..." Turo baki yayi kaman yana gaban ta Sannan yace
"Mom NA....aikin fa?..."
"Ka dinga zuwa every weekend..." Idanuwa ya zaro, yayi shuru Kawai baice komai ba don kar Hajiya tace yana mata rashin kunya, haka suka gama hiran ya fita daga quarters din zuwa office.


Yau Hajiya Aisha ta koma gidansu dija din kai mata kayan data sayo mata, da sallama ta shiga cikin gidan, da Sauri ammi dake zaune ta rafka ban tagumi ta mike
"Ah..ah..Sannu da zuwa..." Inji ammi Tafada cikin murmushin karfin hali,
"Yauwa..." Sannan suka fara gaisawa, ledan Hajiya ta mikawa ammi
"Gashi inji uwar dakinki dija...." Ahankali ammi ta bude ledan Bata wani yi murna kan kayan ba,
"Ya dija take... Ina Iya zuwa ganinta?.." Ammi ta fada har jikinta NA rawa, murmushi Hajiya Aisha tayi
"Ki kwantar da hankalin ki..diyarki tana gidan Hutu...Kuma albashinta dubu ashirin..." Da Sauri ammi ta kalleta,
"Wane irin aikine zatayi da zaa Bata dubu ashirin cikin kwana talatin?.." Ammi ta fada cike da mamaki.
"Ai NA fada maki yarki tana gidan manyan mutane... Yanzu karshen watan nan zan sayo maki waya sai ki dinga waya da yarki..." Inji Hajiya Aisha, dadi ammi taji har cikin ranta.

_A week later_


Yau yazid zai dawo sai shirya kayan dadi ake kala2 kaman sarki zaizo gidan mussanman Hajiya karama duk wata in yazid zai zo gida weekend haka zata dinga hidima ko kadan Bata gajiya don tana ji dashi tamkar ita ta haifeshi shima bai wasa daita.

Dija NA tsaye gefen asabe dake yankawa mai dafa abinci cabbage cos ba su ke dafa abinci ba,
"Wai me akeyi naga anata dafa abinci kala2?.." Dija ta tambayi asabe cikin kunnenta,
"Babban Dan gidan ne zaizo..." Ta amsa mata, kai Kawai dija ta karkata, haka suka yi aiki har suka gaba aka cika dinning da abinci dija kam sai mamakin yawan kayan take don gani take ko mutane goma abincin yayi masu yawa
"Kilan ci gareshi..." Ta fada cikin ranta. Sai wajen 12 suka gama komai suka koma dakinsu. Kwanciya tayi tana tunanin ammi da kannenta don she missing them beyond words, da tana tunanin it won't matter amma she's so wrong she miss them so much, at times in suna cin abinci da asabe sai tace
"Inama su ammi suna nan..." Take fada cikin ranta.

Around two yazid ya shigo gidan cikin wata beautiful and expensive car, da gudu yaran gidan sukaje bakin gate, shima da Sauri ya fito ko parking baiyiba ya dauki Ameera hannun daya ya dauki marzuq da hannun daya, nishi ya farayi
"Wai ...me kukeci....duk kunyi adding weight..." Tafada yana nishi kaman Wanda ya dauki buhun cement. Sauke su yayi suna Dariya, hannun shi cikin nasu suka shiga part din Hajiya babba
Da gudu mimata da Zainab dake zaune falo suka nufoshi, bude masu hannuwanshi yayi yana murmushi, rungume su yayi
"Nayi missing dinku...." Ta fada masu
"Yaya bakayi missing dinmu ba...jiya dakayi waya da big mommy baka nememu ba..." Inji Zainab dake turo baki, Dariya yayi Wanda ya kara bayyana handsomeness dinshi
"To in ni ban nemeku ba Ku bazaku kirani ba?..."
"Ai bamu dakudi..." Inji mimata, kai ya girgiza yana cewa.
"Baku da kudi amma kullum kuna online..." Yafada tare da kama hanyan mini falon dake wurin, nan ya hangi Hajiya babba da Hajiya karama zaune fuskan su dauke da murmushi, da Sauri ya karasa wurin su ya durkusa Sannan ya gaida su,
"Ji yanda ka wani koma...duk ka rame saboda rashin abincin kwarai..." Inji Hajiya karama, Dariya Kawai yayi Hajiya babba kam murmushi Kawai take tana kallon danta cikin so da kauna
"Ai gani yanzu sai ki bani mai dadi inci in yi adding weight kafin in koma...." Hararanshi Hajiya karama tayi tana cewa
"Kana zuwa kana maganar komawa...." Tafada kaman tana fushi, zama yayi kan hannun kujeran da take ya rungumota,
"Da wasa nake mommy...." Yafada yana manna mata kiss a cheek dinta, mikewa Hajiya karama tayi ta kama mashi hannu,
"Muje kaci abinci..." Tafada tana janshi, Dariya yayi yabi bayanta don in da sabo ya saba,
"Yaya ina sarabanmu?..." Marzuq ya tambayeshi,
"Ban sayo komai ba..Ku bari da yamma sai in kaiku eleganza,..." Tsalle yaran suka fara, suka fita Hajiya karama NA rike dashi kaman wani karamin yaro, gate aka bude motan shahid ya shigo, tun daga nesa ya hangi yazid da Hajiya karama, Dan karamin tsoki yaja yana cewa
"The fun killer is back..." Yafadawa kanshi yana parking motanshi, Fitowa yayi ya nufosu sanye da three quarters dake low waist a kugunshi, yazid tsayawa yayi yana kallon shi
"Yaya sannu da zuwa..." Ya fada mashi kanshi kasa, yazid bai amsa ba ya tsaya kallon dressing dinshi,
"Ki daga ina kake?..."
"Daga factory...". Kallon up and down yayi mashi
" ina Sharif?...." Ya sake tambayan shi, hannun shi Hajiya karama ta kara rikewa
"Ka rabu dashi ..muje kaci abinci.. Don't waste your precious time on those silly boys...." Ta fada mashi, kai kawai ya girgiza ya bi ta, shi Kuma shahid ya tabe baki ya nufi part dinshi da Sharif yana tafiya irin NA niggas wandonshi sai Neman kwalewa yake. Saida suka isa dinning Sannan ta saki hannun shi, zama yayi yana kallon jerin abincin
"Small mom ya zanyi da wannan abincin?..."
"Kaidai kaci Iya cinka ka bar sauran..." Ta fada tana dauko mashi ruwa daga cikin fridge dake wurin, ajiye mashi tayi Sannan ta bar wurin ta koma bangaren Hajiya babba.

Yazid zama yayi yana kallon abincin sai yaji ya koshi don ya rasa abinda zaici Kuma ko kadan baison bata mata rai, Ahankali ya bude warmer daya yacikaro da white rice ya diba kadan Sannan ya bude next warmer ya zuba thick stew dake ciki ya fara ci bayana ya debi dambun nama ya zuba akai, saida yaci ya koshi ya sha ruwa yayi relaxing nan yana waya da mufida. Kawai kaman daga sama sai yaga dija ta bude kofa ta fito asabe NA biye daita, Dan tsaya kallon ta yayi har saida muryan mufida ya dawo dashi hayyacinshi, itama daga idanuwanta tayi ta kalleshi tayi Sauri durkusawa
"Ina kwana?..." Ta fada da Sauri, sai kuma tace
"Aa.. Ina yini..." Ta fada muryanta NA rawa, Dariya asabe tayi yazid kam zaro idanuwa tayi yana kallon ta har lokacin waya NA kunnenshi, hade rai yayi ya daga mata hannu, da Sauri ta mike ta koma ciki, itama asabe gaidashi tayi itama ya daga mata hannu ya cigaba da wayanshi
Saida ya gama ya zauna nan yana tunanin wacece wacce ta fito daga dakin masu aiki, zama yayi nan ko zata Kara fitowa. Dija kam da Sauri ta zauna kan gado kanta kasa,
"Wai ya akayi kika rude?...ko baki taba ganin mutum mai kyauwunshi ba?..." Asabe ta tambayeta, dija dai kasa magana tayi saboda abinda ya makale mata a wuya,
"Ko kin taba ganin shi?.." Ta sake tambayanta, da Sauri ta girgiza mata kai,
"Kinyi shuru..."
"Ba..bu...komai..." Ta amsa mata tana Dan kwantawa,
"Bazaki sha ruwan ba?... Tunda NA manta ba sa ruwa a fridge ba..." asabe ta fada mata don diban ruwa suje amma ganin yazid yasa ta dawo don wani irin faduwan gaba taji data ganshi Sannan ko daidaida minti daya Bata fatan kara haduwa dashi don yayi mata kwarjini da yawa
"Anjuma zansha...." Tafada tana kara lafewa kan gadon,
"Kije ki debo mana...ko so kike in debo maki?..." Da Sauri dija ta girgiza mata kai
"To ki tashi ki debo ruwan..." tafada tana bude fridge ta dauko roban da take zuba ruwa ciki ta ajiye ta mika mata, ahankali dija ta amsa ta mike tana tafiya ahankali ta nufi kofan ta bude gabanta na faduwa, tana budewa ya kara daga manyan idanunshi suka kara hada ido, da Sauri dija ta kara komawa ciki ta maida kofan ta rufe.
[3:16PM, 3/20/2018] 鈥�+234 806 125 0020鈥�: 馃挋馃挏馃挌馃枻馃挍鉂�
NA CUCE TA
馃挋馃挏馃挌馃枻馃挍鉂�




庐zuwairat( ummu Maryam)



9鈨�



Da Sauri asabe ta mike
"Lafiya?..." Ta tambayi dija da ta komo ciki kaman ta ga ghost,
"Ya...na... Nan....nidai tsoron shi nakeji...." Kallon mamaki tayi mata,
"Tsoro Kuma?... In kina haka kina Iya rasa aikinki...ya zaki dinga haka kaman kinga gawa?...shine fa babban gidan nan...in Hajiya taji tana iya koranki don Bata hadashi da kowa ba...yanzu kije ki debo ruwa kaman babu abinda ya faru kar ya fadawa Hajiya...." Asabe ta fada mata cikin fada, da Sauri tace
"To...." Tafada tana kara komawa bakin kofan, yazid kam zama yayi yana kallon ikon rabbi,
"What such of insanity is this?.." Ta tambayi kanshi, mamakin yanda take gwalo dukkan manyan idanuwanta in sun hada ido Kawai yake,
"Did she know me from somewhere?..." Ya sake tambayan kanshi, jin an kara bude kofan yasa ya kara maida hankalin shi ga kofan, dija ce ta fito wannan Karin Bata daga kai ba, Allah ya taimaketa da akwai distance tsakanin inda yake zaune da inda take, tunawa tayi da ya yana Iya fadawa Hajiya abinda tayi kaman yanda asabe ta fada mata, ahankali ta fara takawa kanta kasa, yazid kam kara balancing yayi yana kallon each and every step dinta yana mamakin yanda take tafiya kaman an somata cikin ruwa, kafanta sai rawa yake, Kawai sai ya tsinci kanshi da kallon waist dinta, dukda tana sanye da doguwar Riga yana ganin hip bone dinta, da Sauri ya kauda kanshi gefe har lokacin bai bar tunanin ina small mom ta samo wannan unique gal ba, dija NA jinta cikin kitchen ta saki ajiyan zuciya tare da dafa saitin heart dinta dake beating a very high rate, saida tayi rike sink din da zata debo ruwa for like ten minutes Sannan ta dawo normal, da Sauri yazid ya mike daya tuna baiyi sallan zuhr ba, barin falon yayi amma to his surprise he found himself turning back to look at the kitchen kafin ya bar falon. Direct ya wuce part dinshi NA gidan Wanda shi kadai ne gurin. Alwallah ya dauro ya fitoyayi salla ya zauna nan kan praying mat. Ko tunanin me yake oho. Yafi minti talatin zaune Sannan ya chanza kayan jikinshi zuwa English wear ya fita. Part din Hajiya babba ya tafi ya samesu nan ya shaida masu zaije factory wajen Abba sukayi mashi adawo lafiya , at that moment Kawai sai yaso ya tambayi Hajiya karama inda ya samo yarinya amma sai ya tuna da halin ta da saurin zargi da Kuma tambaya. Haka ya fita ya shiga motanshi ya nufi daya daga cikin factory din babanshi.
Dija na Gama deban ruwan ta fito ahankali tana aduan Allah yasa ya bar gurin Kuma luckily Bata tardashi ba, da Sauri ta shiga dakinsu ta maida kofa ta rufe, asabe kallon yanda tayi tsuru2 Kawai take, ajiye ruwan tayi cikin fridge Sannan ta koma ta zauna har ta tagumi,
"Wai meke damunki?.." Asabe ta tambayeta cikin kulawa, girgiza kai Kawai tayi alaman nothing,
"Ya zaayi ki ce babu komai alhalin cikin minti daya kika chanza...ki fadamin.. Kinga tamkar yaya nake a wajenki..." Tafada mata ahankali,
"Ni banason... wannan mutumin..." Ta fada cikin sanyin murya, maganar ta Dariya ya bawa asabe,
"Me yayi maki.daga ganinshi zakice bakison shi?..." Da Sauri dija tace
"Babu komai... Nidai...banason shi..." Tafada muryan ta na rawa, rike kunne asabe tayi
"Kinsan wallahi kar ki bari aji wannan maganan daga bakinki...haka nan zakice bakison shi... " dija dai shuru tayi tana tunanin how she feels about him the first instant, Kuma ita kanta Bata iya defining feeling dinta amma she's just calling it hate,
"Amma wayan nan biyun sunfi shi kirki..." Dariya Asabe tayi tana cewa
"Lallai bakisan kan abun ba...kina nufin shahid da Sharif sunfi shi kirki?... Kambu...to wallahi karkiyi fatan lambanki ya fito wajensu don har wanki mota sai su sakaki...Kuma suyi zaune suna kallon ka suna dariya....shi kam babu ruwan shi da kowa..mussanman mu maaikatansu..." Baki dija ta bude dataji ance wanki mota
"Kuma gabansu Hajiya suke kasaku wanki mota?..." Kai.asabe ta girgiza mata
"Aa.. In sun ga su Hajiya sun fita sai suce ni da haya... Muyi masu car wash....kaman yanda suke fada..."
"To meye maanan ka...was..." Dija ta tambayeta,
"Oho masu..." Dan Bata rai dija tayi Sannan tace
"Kilan yan iska ne..." Tafada Ahankali, da Sauri asabe ta kalleta,
"Ki bar furtan irin wannan maganar..babu kyau.." Kai dija ta gyada mata,
"Ki je kisha ruwan..ki kwantar da hankalin ki bashi da matsala Kawai kin tsorata ne da kyawunshi...kar ki kara nuna alaman tsoro in kin ganshi ..kinji ko?..." Ahankali ta kara gyada mata kai don tamkar babbar yaya ta maida asabe yanda Bata yiwa kawo gardama to itama batayi mata gardama.

Yazid na barin factory ya nufi gidan su mufida, daman Tasan da zuwan shi don haka ba karamin haduwa tayi ba don tasha shadda skirt da riga ta gyara kanta sai ta daura dankwali yanda gaban goshinta zai bayyana, har cikin gidansu yayi parking ya fito yayi sallama bakin falinsu, cikin wata irin sexy voice da ya kusa sa shi shivering ta amsa mashi, ahankali ya shigo

Please Login or Register in order to submit comment