You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gida aka zo aka bani labarin ka cinye kuWin maganinta, kai ba ka ga laifinta ba sai nawa, sai ka fara yi wa kan ka masifar ai"""

"Kamar yadda suka saba, haka suka yi ta faWa su na cece ku ce."

***

"Anty rakiya kuwa, ta samu mami ta din ga surfa mata bala'i, ta in da ta shiga ba ta nan take fita ba, wai ta biyewa tsoron dangin miji, za a raba musu zumunci."

"Ta Wauki gaba da ita, gaba Waya ta rasa abun da yake yi mata daWi, ta na ji tana gani raihan yanzu ya koma mata"

"kamar wani ba™o, sam ba ya sakewa da ita, saboda kar ta yi wata magana a kan ummi, kusan abun da take gudu shi yake shirin faruwa, ummi ta mallake mata Wa."

"Dan labari yana isheta cewar, kullum raihan status Win sa, yabon ummi ne tare da koWata, dan ita ya riga ya rufeta"

daga gani.

"Ta fuskanci sam fushinta da shi ba ya tasiri a kan sa yanzu, dan ya fi zuwa wurin hajiya ma yayi al'amuransa, ga wata"

irin muguwar sha™uwa tsakaninsa da Salim yanzu har ma da Sagir.

"Hakan ya ™ara mata tsananin tsanar ummi, da duk da abun da take yi wa ummin, ta kan kira waya ta gaisheta, tayi girki ko ta bayar da abu ta ce a bata, ta wula™anta amma tun da abun nan ya faru, ummi ba ta ™ara shishshigin raSar"

in da take ba.

"Aka gama gyaran gidan dr. Da idan sun dawo za su tare da mariya, daga can ™asar ya turowa ummi kuWi, a kan ta yi mata sayayya ta haWa da kuWaWen hannunta, ta din ga yi mata sayayya."

"Dan ba ™arya hannun raihan a sake yake, kuma yana sakar mata yadda yakamata, kuma ita ma na ta hannun a sake yake."

"Tun da aka yi scanic aka tabattar wa su ummi, yara biyu ne a cikinta, raihan yake murna, kuma ya gargaWe ta a kan"

kar ta kuskura ta gaya wa kowa.

"Suka yi ta shiri, tare da sayen kayan jarirai."

"Sai dai cikin yana wata bakwai, kamar ummi za ta dur™usa ta haihu, saboda girma, kullum cikin lissafin kwanakin da"

"suka rage take yi, saboda yadda nauyin cikin yake damunta, idan ta zauna sai an Wagota saboda girman cikin."

"Gefe guda kamar yadda ta yi al™awari, tana tura wa yaya magaji kuWi lokaci zuwa lokaci, saboda kula da Iya."

"Farida ba ta ha™ura ba, wurin bin bokaye da malamai, a kan lallai sai an raba auren dr. Da mariya, kuma a sake mallake mata shi ta juya shi fiye da yadda take yi a baya."

"Sai dai abun da ba ta sani ba shi ne, duk da kallon mahaukaciya tuburan take yi wa mariya, a hakan ba ta wasa da"

"addu'a, mace mai son addini sosai da sosai, dan yana Waya daga abun da ya sanya ta ™ara shiga ran dr. Sosai da sosai."

"Hajiya ita ta maye wa ummi gurbin sirika, dan kusan har role Win uwa take yi mata playing, kusan kullum tana tafe"

"zuwa duba ummi, ko yi mata aike take, tana tausayin ummi sosai da sosai, saboda abu ne na fari ba ta san ya yake ba, tana yawan cewa ummi ""Anya ummi ba zaki likitoci su ™ara caje cikin nan ba, girmansa yayi yawa tubarkallah"" sai dai tayi murmushi, ba tare da gaya mata ha™i™anin abun da yake cikin ba."

"Ummi ta daina fita ko ina, gashi ta ™ara zama mafaWaciya, saboda damuwar ciki. Kasancewar Hajiya na gaya wa raihan sai yayi ha™uri da ummi, a wannan stage Win mata masu ciki na fuskantar saurin fushi, dan haka sam baya"

"damunsa, shi tausayi ma take bashi."

"Duk tsaftar ummi, sai da zamana dogon gashin nan sai ya kwana uku babu taza, kusan kullum sai dai ta saka kaya"

"masu sau™in nauyi yadda iska za ta wadace ta, takalmi kuma idan ba over size ba duk haushin takalman take ji."

"Da safe ta fito, tana ta mita noor ba ta Wumamata shinkafa ba, wai ita ba ta cin abun da ta dafa."

"Noor ta ce ""Ke fa ki ka ce ba kya son warin shinkafa"""

"Kamar tayi kuka ta ce ""Haba noor, amma tun jiya na ce miki zan ci, yunwa nake ji, ina magana kina kallo kin yi mini"

"banza"""

"Noor ta ce ""Ai Yaya ummi ban san yaya zan yi miki na burgeki ba, MD ne kawai yake iya miki, ni ba ni na Wora miki"

"nauyin cikin nan ba, amma ki yi ta yi mini faWa. Kuma sai na koma gida tun da faWa ki ke yi mini"""

"Ummi ta marairaice ta ce ""Haba noor, to ki yi ha™uri dan Allah kar ki tafi, wai ni ya ku ke so in yi?"""

"Raihan da yake bayanta ba ta sani ba, ya kama dariya, ba wuya ta bayar da ha™uri, ba wuya kuma ta fara kuka."

"Ciki duk ya mayar da ita wata iri, sai dai bai sanya ta daina kyau a idonsa ba."

"Yayi gyaran murya ya ce ""Ya aka yi ne yau ke da noor Win taki ku ke faWa"""

"A shagwaSe ta ce ""Wai tafiya za ta yi"""

"Ya ce ""Haba nooriya, uwa guda ki tafi ki bar ´ar ta ki?"""

"Noor ta tura baki ta ce ""FaWa take yi mini, kai ma fa shaida ne ta ce ba ta son shinkafa, wai yau kuma shinkafa za ta ci, wai ta gaya mini jiya da daddare, ni ina na ganta jiya da daddaren?"""

"Ummi ta ce ""Ni duk kun tsane ni, baku san me nake ji ba, ko tausayina ba kwa ji"""

"Raihan ya ce ""Mu mun isa, mu kuwa muke ™aunar ki, jeki ki yi wanka ki shirya, har noor tare zamu tafi office yau,"

"kya ji daWin jikinki"""

"Ta juya tana hararar noor, noor ta kama dariya ta ce ""Na fasa tafiyar yaya ummi"""

"""Ki yi ta tafiyar ma, ina ruwana"" suna lallaSata suna yi mata dariya."

Aka ba ta Wunamen shinkafa ta ci hankalinta ya kwanta.

"Tare suka tafi wurin aiki, fitowar ta yi mata daWi tana kallon titi."

"A can wurin aikin, suna zuwa a parking space noor ta ga motar Salim."

"Sun shiga take tuna masa wula™ancin da ya yi mata, ta zo ganinsa."

"Yau bai biye mata ba, ya ce ""Allah ya baki ha™uri, kar na tanka cibi ya zama ™ari"""

"Ma'aikata na ta gaishe shi, yana amsa musu cikin mutuntawa."

"Wani mutum ya taso, ya tare su ya dur™usa a gaban raihan yana dan Allah maigida ka taimaka mini da aikin sharar"

"nan ko masinja, nafi wata ina zuwa an hana ni ganinka, ina cikin mummunan yanayi na babu da fama da rayuwa, dan Allah ka taimaka mini."

"Ummi ta zubawa mutumin ido, raihan ya kalli ummi ya ce ""ya dai? Kin san shi ne?"""

"""Ishaq Abdulkarim magashi"" ta faWa jiki a sanyaye, mutumin ya Waga kai yana kallonta."

"A rikice cikin tashin hankali mutumin ya ce ""Salma Muhammad Bashir, ke ce da ma ke ce? Kina nan dama"" ya fara"

maganar cikin kame-kame.

"""A ina ki ka san shi?"""

"Ummi ta ce ""Šan ajinmu ne a University"""

"Raihan ya ce ""Šan ajinku? Amma yake neman shara?"""

"""Wallahi yallaSai korata aka yi daga makaranta, dan Allah ka taimaka mini"""

"Raihan ya ™are masa kallo ya ce ""Kana cikin wanda ku ka din ga muzanta mini mata kuna makaranta ko?"""

"""Dan Allah ka yi mini rai yallaSai, lamarin Allah kenan, gashi yau ina neman alfarma a wurinta, na yi nadama dan"

"Allah ki yi ha™uri ki yafe mini"""

"Gwiwoyi a ™asa yake yi musu magiya, ummi ta ce ""Kar ka damu, ba ni nake Waukar aiki ba, ni abun da ya faru ya wuce a wurina, wannan wurin kuma ba ni da hurumin Waukar ka aiki, idan ya baka haka nake fata, idan bai ba ka ba"

"ka yi masa uzuri wata™ila babu vacancy ne"" daga haka ta ja jikinta ta yi gaba zuwa office Win raihan."

"Ba ta san yadda suka ™are ba, shima da ya zo office Win bai gaya mata yadda suka yi ba, noor ta ce ""MD a ina yaya Abdul yake?"""

"Raihan ya ce ""Ai ba a nan branch Win yake ba, yana sharaWa shi""."

"""To ina first born?"""

"Ya kalleta ya ce ""Wa kenan?"""

"""Yaya Salim mana, ba ka san last born yake ce mini ba, shi kuma first born?"""

"Raihan ya yi dariya ya ce ""Ni ina zan sani, baya nan"""

"Noor ta ce ""Na ga motarsa fa"""

"Ummi ta ce ""Kai noor, me zaki yi masa an ce miki baya nan"""

"Raihan ya ce ""Da gaske kin ga motarsa?"""

"""Wallahi na ganta"""

"Raihan yayi murmushi ya ce ""Yaya hukuma sai da rarrashi, office fa na bashi, nake ta bin sa ina yi masa magiya,"

"ofishin kula da ma'aikata da ladabtar da au na bashi, ya ce ba ya so ba zai yi ba wai wata sana'ar zai yi. Na ce Alhaji ya saka baki, amma ya ™i shi ne yau ya zo ban sani ba, ko ma ya neme ni, bari na je office Win nasa na duba"""

"Noor ta bi raihan har office Win da Salim yake, sai haWe rai yake yi."

"Ya kalli raihan zai yi mita, sai ya ga noor a bayansa, sai kuma ya saki fuska."

"Raihan ya ce ""Yaya ashe ka zo Win ban sani ba""."

"""Eh da ka je ka haWa ni da hajiyan Bauchi ko?"""

"Raihan ya sosa kai ya ce ""Tuba nake babban yaya, with due respect kuma kai ne mataimaki na zan Webo sauran"

"ayyukan da nake gabatarwa, na kawo maka zuwa next few months kuma, i will step down ka yi taking over"""

"Salim ya yi masa wani mugun kallo ya ce ""Raihan ba ka da hankali ko? Tayaya makakke zai jagoranci wannan abun,"

"kai da ka ke a nutse ma kana fama"""

"Noor ta ce ""Ahh ba ka daina ba? Ka ce mini ka rage sosai ai"" Raihan yana ja da baya yana dariya ya ce ""Yauwwa noor"

"gaya masa dai"""

"Kwanaki suka cigaba da tafiya, wasu rayuwarsu na daidaituwa, wasu kuma suna girbar abun da suka shuka."

"Ummi ta shiga watan haihuwa, dr. Suka dawo ya kammala karatun da zai ba shi damar zama professor."

"Duk wanda ya kalli mariya ya san ta samu kwanciyar hankali, shi kamaa dr. Ya canza."

"Bai sauka a ko ina ba sai tsohon gidansa, in da za su zauna da mariya, gida yayi kyau ummi ta gyara komai."

"Abdul ne ya Waukko su daga airport ma, farida sam ba ta san ma sun dawo ba."

"Ummi ta yi wa Allah godiya, ganin mama cikin ™oshin lafiya da kwanciyar hankali."

"Dr. Ya ce noor ta kwana tare da mariya, duk da jikinta yayi sau™i sosai da sosai, shi kuma ya tafi can gidansa, sai dai ko kallon kirki bai samu daga farida ba, balle karSa mai kyau."

"Tana saka ran asirin da ta yi ya ci shi, ya biyo ta yana lallaSata, amma ta ga ko ta kanta bai bi ba shi ma, yayi wanka ya shiga Wakinsa ya hau bacci."

"Tsananin takaici da ba™in ciki ya sanya ta je ta tashe shi da masifa, har da i™irarin sai ta kashe mariya, bayan ta gama"

ci mata mutunci da kiranta mahaukaciya.

"""Wallahi farida ban taSa gaya miki ba, amma yau zan faWa na yi dana sanin aurenki farida, baki da tarbiyya ko kaWan."

"Suffar da ki ka mu'amalance ni daban kan na aureki, wadda ki ka nuna mini bayan auren daban. Wallahi na yi dana sanin rashin auren mahaukaciyar da ki ke faWa tuntuni ta fiki sanin darajata."

"Wallahi ki ka kuskura ki ka yi mata wani abu, a shirye nake da kowa ya kama gabansa da ni da ke, ba zaki kashe ni ba wallahi"" ta dafe ™irji tana zazzaro ido ""Da can ba ka san bani da tarbiyya ba sai da ka auri mahaukaciya?"""

"""Na sani mana, kara nake yi miki ina yi miki kawaici, ke kuma ba kya gani, gara na fito miki a mutum, ina kuma"

"jaddada miki, idan ki ka kuskura ki ka taSa mariya kin taSa igiyar aurenki, dan ba zaki cutar da abun da nake samun farinciki daga gare shi ba""."

"""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku wallahi yahaya kai butulu ne, azzalumi ni ka ke gaya wa haka?"""

"Dr. Ya ce ""Ke ki ka so, ai ni ban san tuntuni kamar a kurku nake ba, sai yanzu na yi ´anci ai. Ke ki ka janyo duk abun da na yi miki, ke ma kin san na yi ha™uri da ke, kuma bani da niyyar cutar da ke, amma halinki ya fara kaini bango"""

"Gaba Waya farida ta ji duniyar tayi mata zafi, komai ne naman ™wace mata."

"Washegari dr. Ya shirya ya tafi gagarawa duba iya, babu yadda bai yi da mariya ba, ta ce masa ita fa ko rasuwa iya ta"

"yi ba za ta je ba. Sam mariya ba ta da zafi, amma tun da ta faWi haka ya san abubuwan da iya tayi mata suna cigaba da ™ona mata zuciya ne, dan haka ya ™yaleta."

"Ya je ya tarar an mayar da iya asibiti, babu wata kulawar kirki, babu jinya mai kyau tana iya magana amma ba sosai"

"ba, sai ta yi zawo har ya fara bushewa a jikinta ba a Wagata an gyara ta ba."

A wannan karon mariya ta matsa sosai a kan lallai sai ta je sun gaisa da maman raihan.

"Raihan ya sanar da Alhaji, Alhaji ya ja wa mami kunne sosai a kan kar ta kuskura ta wula™antawa ummi uwa."

"Mai hali baya fasa halinsa, dan sai da tayi abun da mariya ta fuskanci akwai wani abu a ™asa, Hajiya kuwa ta"

karramata sosai da sosai.

"Sai dai mami ta yi mamakin ganin maman ummi, sam ba ba™a ba ce ba ga dogon hanci har baka."

"Sati biyu da dawowar su dr., ³an maiduguri suka zo ganin gidan mariya, suka din ga murna ganin yadda ta yi ™alau"

da ita.

"Bayan ummi ta koma gida daga gidan mariya, cikin dare na™uda ta tayar mata."

"A cikin daren ita da raihan suka tafi asibiti, dan noor ta gudu wurin mariya, wia sai ummi ta haihu za ta dawo, yanzu"

ta zama masifaffiya.

"Da safe raihan ya kira waya ya sanar suna asibiti, sai dai haihuwa ta gagari ummi, ga ciwo amma labor baya gaba,"

"duk ta galabaita, likita ya ce sai dai ayi mata aiki."

"Alhaji ya ce lallai sai mami ta je asibiti ita ma, ayi komai da ita ai matar Wanta ce."

"Ummi ta tayat da hankalinta, ta din ga kuka tana cewa tsoro take ji, duk aka kewayeta ana rarrashinta."

Noor kuma tana gefen ta tana tayata kukan.

"Ummi ta kalli mariya, ga mama matar kakanta, ga Anty maryam, ga hajiyar su raihan, ga Abdul ga raihan kansa har"

"da Salim, ga Nihal ™anwar raihan, ana rarrashinta. Duk da mami ita sai yatsuna fuska take yi."

"A ranta ta ce ""Allah sarki, haka family suke dama? Kowa ya damu da kai"" wani irin farinciki ya cika mata zuciya."

"Ta ce sai dai a shiga aikin har da raihan, idan mutuwa za ta yi ya ri™e hannunta."

"Mami ta ja wani uban tsaki, raihan kuwa ya ri™e hannunta yana ta kwantar mata da hankali."

"Raihan ya kasa zaune ya kasa tsaye, aka shiga da ummi, awa guda da wani abu, aka fara fito da jarirai, mace da"

namiji.

"Sai dai hankalinsa ba a kansu yake ba, Ummi yake jira a fito da ita."

"Yana nan tsaye aka turo ta a kan gado idonta a rufe, an rufeta da green Win yadi."

"""Salma"" ya kira sunanta da Wan ™arfi."

"Ta buWe ido tare da ri™e hannunsa ta ce ""Ka yi magana a hankali mana, ban mutu ba"" yayi dariya ya dur™usa ya"

"sumbaci goshinta ya ce ""Thank you very much sweetheart, Allah ya baki lafiya"""

"Can waje kuwa ana ta murna an fito da jarirai, mami ta kallesu ta ce ""TaS, wannan wane irin yara ne, mu kaf"

"danginmu babu wannan kalar, meye wannan?"""

Ayshercool

8081012143.

CUTARWA!

AYSHERCOOL

(BRIGHT PENS)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

49

PAID ADVERT

"*Hajiya ina zaki? Saurin me ki ke yi haka? Šan bani aron mintuna biyu kacal, na gaya miki albishir Win da na zo miki da shi. Shin ko kin san sirrin she™in fatar ummi, da ya sanya ta kama zuciyar MD raihan ta hana shi sukuni? Kai ba ma"

"skin care ba, har da sirrin gyaran gashi, ina masu fama da amosani, karyewar gashi ko kuma san™o, jan gashi ne da ke? Ko taurin gashi kamar soson ™arfe. Idan matsalar ki budurwar fata, tare da rashin glowing, Annur skin scrub da hair bliss sun shirya tsaf domin magance muku kukanku, me ku ke jira ku tuntuSe su a kan lambar wayar su dan ™arin bayani 07045971194 ko 08140450950*"

49

"Tsit kowa ya yi ya zuba wa mami ido, tana wani yatsune fuska."

"Hajiya ta ce ""Amma meyasa zaki ce haka? Wannan ai ba magana ba ce ba"""

"""Eh na faWa, ko a dangina kin taSa ganin irin wannan?, kalli kalar uwarsu ki kalli raihan ki kalli yaran""."

"Jajawur yaran, haskensu ya wuce ace hasken raihan kawai suka Waukko, gasu manya sosai, kuma kansu ™wal babu gashi, kuma ba su da gashin gira ko kaWan sai alamarta."

"Mariya cikin jin kunya ta ce wa Hajiya ""Bari na gansu"""

"Aka mi™a mata yaran, ta zuba musu ido tana murmushi sannan ta kalli mami ta ce ""Hajiya, ai yaran nan da babansu"

"su ke kama, haka na haifi ummi, Iya ta din ga ce mata aljana, sai dai kwana biyu kanta ya cika da gashi ko anty maryam, sai dai ummi tun tana jaririya ba™a ce""."

"Wani mugun kallo ta yi wa mariya ta ce ""To ni danginmu babu irin wannan abubuwan, ni ban taSa ganin jarirai a"

"haka ba, danginmu dai kaf babu mai wannan farin"""

"Nan da nan Maryam ta harzu™a ta ce ""To mu namu akwai, duk tsiya dai ai na Wanki ne ba wani ba"""

"""Ba ni da tabbas, ni Wa na ma ba shi da cikakkiyar lafiya"""

"Hajiya da ta fara fusata ta ce ""Ke dai ya rainawa hankali, dan ya tsallake son zuciyarki"""

Mariya ce ta din ga basu ha™uri.

"Raihan kuwa yana can Wakin da aka kai ummi, sai zuba yake yi yana yi mata kalamai masu kwantar da hankali da"

™warin gwiwa.

"Likitan da yake yi mata allura ya ce ""Maman twins ai ba Kya bu™atar maganinmu, wannan kalaman sun ishe ki"

"warkewa"" suka din ga dariya, sai da bacci ya Wauke ta sannan ya tafi Wakin da su Hajiya suke."

"Noor ji take kamar ta kwaWawa mamin raihan mari, ko karar ganin idon mariya bai saka ta yi alkunya ba."

"Abdul da yake Wakin ya tashi ya fita, Salim ma surutun ya ishe shi, ransa ya fara Saci."

"Mariya ta kalli Salim ta ce ""Salim, dan Allah jariran nan ba da babansu suke kama ba, dan Allah kar ki saka zargi a"

"kansu tun suna jarirai, su sha wahala kamar ummi, idan ta tashi ta ji, ba za ta ji daWi ba""."

"Salim ya ce ""Mama, muna murna muna fatan Allah ya bawa ummi lafiya, mun gode wa Allah kyautar da ya bamu"""

ya ™arasa maganar yana yi wa mami mugun kallo.

"Kamar daga sama raihan ya shigo ya ce ""Hajiya ba ni su na gansu"""

"Hajiya ta maze kamar babu abun da yake faruwa ta ce ""Tun yanzu ka fara nuna wariya, ka tafi wurin matarka ko"

"Waukar su ba ka yi ba"" cikin washe baki ya ce ""Tuba nake, dole in fara zuwa kanta, saboda su an yanka mini mata"" yayi maganar ko a jikinsa yana Waukar su, wanda hakan ya sake ™ular da mami."

"Ya ce ""Tubarkallah, Hajiya irin idon ummi ne da su, brown masu kyau masha Allah, yaya ka ga namijin kallesu duk"

"farare. Alhamdilillah"" yayi maganar yana kallon Salim."

"Farincikin da mariya ta gani a fuskar raihan, sai ya mantar da ita takaicin abun da mami ta yi musu."

"Sauran mutanen maiduguri da suka zo ganin gidan mariya, suka cika asibitin. Ana jimawa ma sai ga dr. Ga Alhaji."

Raihan ya din ga sanar da ´an uwa batun haihuwar.

"Tsabar takaicin yadda raihan yake rawar ™afa, ya sanya ta tashi ta bar asibitin."

"Sai da ummi ta yi awa shida tana bacci, sannan nurses suka tasheta, suka Wagata aka wanke ta, sannan aka bata"

abinci.

"Ta saka kaya tayi kyau, kamar ba ita ba, sannan aka turo ta a kan gado aka mayar da ita main Wakin da take."

Suka din ga murna ganin an fito da ummi ras da ita.

"Sai jerawa ummi sannu ake yi, aka mi™o mata yaran dan ta shayar da su, amma ta kasa saboda yadda ido ya yi yawa."

"Hajiya tare da Salim suka koma gida, ta yi wanka ta yo girki, suka dawo da Alhaji."

"Shi ma Alhaji baki buWe yake ta murna, yana yi wa jariran addu'a, duk da babu wanda ya gaya masa abun da matarsa"

ta yi.

"Sai dai noor ta gaya wa ummi, abun da mamin ta ce, wanda ba ™aramin ciwo yayi mata ba, sai dai ta basar saboda"

tana cikin murnar kyautar da Allah ya bata.

"Ummi ta ce ""Mama, jikin yaran nan kamar jariran mage, basu da gashi kwata-kwata""."

"""Me ki ke ci na baka na zuba? Zai fito in sha Allah"""

"Dr. Ma da daddare ya zo ganin jariran, tare da yi mata sannu."

"Kusan kwanaki uku, ana ta shigowa ana fita duba ummi, a kwanaki ukun nan gashi ya cika kan yaran nan fal."

"Kwanan ummi biyar, aka sallame su daga asibiti, raihan ya ce bai yadda a Wauki hoton yaransa ba a saka a waya."

"Saboda masha Allah kai ba zaka ce ummi ce ta haife su ba, dan sun fi kama da larabawa sosai."

"Su Hajiya Aishan bauchi, da sauran jama'arta, duk suna kano, sai da ummi ta yi kwana goma da haihuwa, sannan aka"

shirya gagarumin taron suna a wani katafaren event center.

"Sai ranar suna ´an gagarawa suka zo, aka ci aka sha, ummi sun samu kyaututtuka sosai da sosai ita da yaran,"

"manyan mutane abokan hulWar Alhaji Tahir, da abokan aikin Raihan, ban da ´an uwa da abokan arziki."

"Sai dai kan ranar sunan nan, yaran nan sun juye kalar larabawa sosai da sosai, gashi ya cika kansu da girarsu, kuma"

"dukkansu brown eyes ne da su, namijin mai ba™in gashi, macen kuma irin na ummi."

"Sai dai sunan da aka sakawa yaran ya yamutsa hazo, dan kuwa raihan sunan ummi ya saka wa macen Salma, namijin"

"ya saka masa Muhammad, wai ya yi wa kansa takwara, ya yi wa Alhajin su, kuma ya yi wa mahaifin Ummi, tun da duk sunansu Muhammad la™anin ne daban-daban, aka yi musu la™ani da Iman da kuma Ayman."

"Ba yadda ummi ba ta yi da raihan ba, a kan ya canzawa macen suna, kar ya janyo mata magana a cikin dangi."

"Amma ya ce ""Kome mutum zai ce ya ce, son da nake yi miki, dole na yi miki takwara dole duniya ta shaida ina son"

"matata""."

"Noor ta sha kwalliya, kamar amarya."

"Ta je ta saka salim a gaba, sai ya yi mata hotuna da iphone Win sa."

"Ya gama yi mata hotunan yana nuna mata, sai murmushi take yi, ya kalleta ya ce ""Kin yi kyau kamar ranar bikinmu"" a"

"razane ta kalleshi ta ce ""Bikinmu kuma?"""

"""Eh mana, ko ba kya so na?"""

"Ta Wan sosa kai ta ce ""Yarinya ce fa ni"""

"""Ba kya son tsoho ko?"""

"Ta girgiza kai ta ce ""A'a kai ba tsoho ba ne"""

"Ya ce ""Tsoho ne mana a kan ki, am 37 you are just 15, dama so nake bayan suna in yi wa Alhajinmu magana, amma"

"tun da kin ce haka shikenan, idan kin gama hotunan ki kawo mini wayar""sai kuma ta ji babu daWi."

"Mami kuwa a ranar sunan sai da ta kira raihan, ta ™are masa zagi da cin mutunci, wai ya ™are a gidin mace, saboda"

"asara har da saka wa ´ar sa sunanta, bayan uban kuWin da ya kashe mata ita da yaranta."

"Shi dai yayi shiru bai ce komai ba, dan ya san duk abun da ya yi wa ummi bai faWi ba, kuma ba zai yi hidimar da"

Alhajinsu yake yi wa iyalinsa ba.

"Da daddare ummi ta yi wanka ta saka kaya, Anty maryam ma ta wanke jariran, an samu sun yi bacci saboda sun gaji,"

sun sha kuka da jagwalgwalon ´an suna.

Raihan ya shigo yana yi wa ummi murmushi.

"""My MD, murmushin me ka ke yi ne?"""

"""Kallonki kawai yana sani murmushi, amma murmushin na yau na musamman ne, guess what?"""

"Ta girgiza masa kai ta ce ""I have no idea"""

"Ya kamo hannunta ya dan™a mata mukullin mota ya ce ""Gashi in ji Alhaji, ya ce a baki ya riga ni"""

"Ummi ta waro

Please Login or Register in order to submit comment