You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kunya har ki Wau cikin raihan, saboda tsabar abun kunya raihan fa, ni ban ma san yadda aka yi ki ka yi wannan gogewar ba, ko rantsuwa zan yi ba zan kaffara ba, bokaye ki ka bi ki ka aure shi, kuma wallahi tun da na zo garin nan kin shiga uku, sai kin gudu da afafuwan ki, mummuna dangin kwaWayi da asiri, kuma ba zaki taSa haihuwa ba ki haifo mana mahaukata da munana ba"""

"Ummi ta yi murmushi mai ciwo, ta tattare gashin kanta, ta mayar bayanta, tare da goge hawayen fuskarta, ta din ga"

"tuno maganganun raihan na warin gwiwa da oarin kare kanta a duk lokacin da wani ya ci zarafin ta, ta kalli maryam ta ce"

"""Maryam! Da aurena da naki duk sunansu aure, wataila nawa ya Wara naki, tun da ke da ki ke kyakywar ma ba a"

"baki sadakin da aka bani ba. Kuma cikin raihan yanzu na fara Wauka sai na tarawa raihan zuriya, ko zaki mutu, dama na shiryawa arangamata da ke, idan kin isa maryam ki saka raihan ya sake ni, ki zo ki aure shi. Batun bin bokaye kuma kema da zaki samu irin bokana na tabatta zaki bi, dan wasu sai su shekara suna asirin bai ci ba"""

"BuWe baki maryam tayi tana tunanin anya wannan ummin da ta sani ce? Yaushe ta waye tayi baki, ummi ta fice ta"

barta a wurin.

"Tana shiga Waya falon ta tarar da raihan ya fito da dogon wandon bacci a jikinsa fari, yana ganinta ya rausayar da kai"

"ya ce ""Ke na fito nema, baki tashe ni in karya ba"""

"Ba tare da ta nuna masa wani abu ba ta ce ""Na fara shirin Wora abincin rana ne, barka da fitowa maigidana na kaina"""

"ta nufe shi, ya buWe hannayensa ta shiga jikinsa ta rungume shi."

"Ya saka hannunsa Waya ya rie ugunta, Waya kuma ya shafa kanta ya ce ""You look cute baby"" sai dai bai kai ga aikata abun da yayi niyya ba, maryam ta faWo falon."

"Mamaki ne ya kama raihan, dan bai san ta zo ba, ummi ma ta yi pretending da ba ta san da zuwanta ba ta juya da"

sauri tana kallon in da maryam take.

"""Maryam, wannan ai saSa dokar addini ce, ai a main falo yakamata ki tsaya ki nemi izini, kawai sai ki faWo mana haka"

"babu ko sallama?""."

"""Sallama, ni ka ke gaya wa haka raihan, saboda wannan mummunar yarinyar da ka aura, me ka gani a jikin ummi da"

"babu a jikin matan garin nan ka aureta dan asara?"""

"Raihan ya sosa kai yana murmushi ya Wago ummi daga jikinsa ya ce ""Abubuwa da yawa mana, next time karki sake"

"shiga wurin ma'aurata anyhow please, ba girman ki bane"""

"Ummi ta yi murmushi ta ce ""Sannu da zuwa Maryam, yau ina da babbar bauwa"""

"""She ruin my enjoyment"" yayi maganar a taaice."

"Maryam kuwa ta Sarke da masifa ta babu gaira babu dalili, tana alwashin sai ta raba auren nan, dan asiri ummi ta yi"

wa raihan.

"Ummi ta yi shiru, zuciyarta na yi mata zafin cin zarafin da maryam ke yi mata, kuma ta i Waga jikin raihan."

"A hankali ya ce wa ummi ""Go and get some rest, kin san baki gama warkewa ba"" ta jinjina masa kai, ta nufi Waki."

"""Dubeta dan Allah, ko kunya ba kya ji"" sai dai abun da Maryam ba ta sani ba, har da hassada ta kamata, gidan da"

"raihan ya saka ummi ya fi nata haWuwa, kuma gaba Waya yau ta nemi munin ummi ta rasa, a dire take ba abun da wata a mace za ta nuna mata. Ga wani irin amshi da take yi, yau ta ga ainihin kyawun surar da Allah ya yi wa ummi. Dan da ta juya baya ma tana tafiya, ga gashin ta ya kwanta a bayanta, kamar ba bahaushiya ba, dole yaro ya rikice ta faWa a ranta."

"Ummi na barin wurin ya haWe rai ya kalli Maryam ya ce ""Idan har kin san zaki zo gidana ki ci mutuncin matata kar ki sake zuwar mini gida ki Waga mini hankali, Mami idan tayi ta isa ne, ke kuwa kin yi kaWan duk rashin mutuncin da na"

"yi miki ke ki ka saya""."

"""Ni ka ke cewa kar na sake zuwar maka gida? Kodayake ba laifinka bane ba, an kai sunanka gaban bokaye an"

"mallakeka"""

"""Bakomai, ni bokan ya taimakeni da ya mallake mata ni, kar ki sake zuwar mini gida ki Waga mata hankali, definitely na san sai ta yi kuka cin mutuncin da ki ka yi mata""."

"Maryam ta ja numfashi ta jinjina kai ta ce ""Bayan cin mutuncin da ta yi mini, kai ma ka Wora naka, sai na nuna wa"

"Salma haryanzu kanta a kwano yake, yarinyar da na taimakawa a baya mara galihu irint..."

"""Kema ta taimaka miki, dan a irin daiancinki, ba dan taimakon nata ba asarar kuWin tara za ayi a banza, dan haka"

"juna ku ka taimaka"" suka yi wa juna kaca-kaca suka yi faWa ta tafi ta bar gidan."

"Ummi kuwa ta din ga sae-sae a ranta, tabbas yanzu tun da har ta riga ta yi aure ta bar gida, raihan ne kawai ya"

"rage mata source of happiness, idan ba ta yi da gaske ba, Maryam za ta iya aikata abun da ta ce, dan ba mutunci ta cika ba, dan haka a wannan karon ba ta tunanin za ta iya Waga wa maryam Win afa."

"Raihan ya bi ta Waki ya din ga rarrashin ta. Sai dai ta kasa daurewa, sai da ta din ga yi masa kuka yana rarrashinta."

"Wayarsa ce ta fara ringing, ya duba ya ga sunan Yaya Salim, ya Waga suka gaisa, Salim ya ce ""Ina waje"""

"Raihan ya ce ""Yaya ka shigo falo, gani nan"" ya ajiye wayar ya Wauki jallabiyarsa ya ce ""Yaya ne ya zo, ki wank fuskarki"

"ki zo"""

"""Allah ya sa ba laifi na yi masa ba"""

"Ya girgiza kai ya ce ""Haba dai, yaya Salim ya ce ke anwarsa ce, da ya karSo amanarta a wurin mama, idan ban kula da ke ba, ni da shi ne"" Ummi ta yi murmushin yae, ta sanya kaya suka fito."

"Sai dai tun da suka fito yake bin su da kallo, suka zauna ummi ta gaishe shi, ya amsa tare da cewa idan ina ganinku"

"taren nan, sai na ji kamar nima na yi auren nan."

"Da sauri Raihan ya ce ""Yaya da gaske, dan Allah ka yi"""

"Salim yayi murmushi ya ce ""Ya arfin jikin naki"" raihan ya ce ""Ta ji saui sosai"""

"""Kai na tambaya?"""

"Raihan ya ce ""Allah ya baka hauri""."

"""Meyafaru ne? Na ga kamar fuskar ku da damuwa, mussaman ummi""."

"Ummi ta ce ""A'a yaya, komai lafiya alau"""

"Salim ya gyara zamansa ya ce ""Yadda ku ke Win nan gwanin sha'awa yayi wuri ace kun fara samun saSani, duk da ma bana tunanin hakan ne, na san akwai abubuwa marasa daWi a asa, amma ku yi hauri da juna""."

"Raihan ya ce ""In sha Allah babban yaya"""

"Ya ce 'Masha Allah, dama zan wuce ne na ce bari na zo na sake dubata, amma Maryam ta zo gidan nan ko?"""

Gaba Waya suka kalle shi a tare.

"Raihan ya ce ""Eh ta zo"""

"""Tun da na ganta a gida jiya na san za ta zo, kuma yanayin ta ya nuna mini ba zuwan arziki tayi ba, ta yi miki wani"

"abu mara daWi ko?"""

"Ummi za ta yi magana raihan ya ce ""Haka ne yaya, amma in sha Allah i can handle it"""

"Salim ya mie ya ce abun da nake son ji kenan, bai sake ce musu komai ba ya fice."

"""MD meyasa zaka gaya masa haka?"""

"""Wai dan kin ga yana shiga sabgar aurenmu? Idan na yi masa arya a gabanki zai zageni, ba a ayi masa musu, na"

"gaya miki kallon anwa yake yi miki,ko na Soye masa idan ya gano na kaWe"""

"Ummi ta ce ""Ni dai duk da haka da baka gaya masa ba, ai na san da ta tafi shikenan."

"Salim kuwa fitar maryam ya gani a mota, ya samu nihal ya ritsata ya tambayeta ina maryam ta tafi daga zuwanta"

jiya? Ba ta Soye masa ba ta gaya masa gidan raihan ta tafi.

"Maryam kuwa bayan komawarta gida, ta samu mami ta zayyane mata abun da ya faru da wanda bai faru ba, wanda"

"hakan ya ara tunzura mami, mussaman da maryam ta gaya mata baaen maganganun da ummi ta faWa wanda suka ba ta mamaki."

"Bayan la'asar Salim ya shiga sashin mami, wanda rabonsa da sashin, yayi shekaru. Mami na cin abinci maryam kuma"

na kallo yaranta na ta wasa a falon.

"Ya tsaya a kan Maryam ya ce ""Zuwa na yi nayi miki gargaWi, idan ki ka sake taka afarki a gidan raihan, ki ka ci zarafin"

"matarsa wallahi sai na casa ki, ba soja ba ko bindiga ki ke aure tun da ke mahaukaciya ce"""

"Mamk ta mie tsaye ta ce ""Saurara kai a wa?""."

"""Ni a wanta, wanda na isa na saka na isa na hana, wallahi ba zan yi kaffara ba, na sake jin labarin kin je masa gida kin"

"yi masa hauka, sai na ci Ya Wirka mata ashar mai zafin gaske."

"""Shaye-shayen ka yi zaka zo ka sauke iskancinka a nan?"""

"Salim ya ce ""Ras nake, sai dai da sannu zaki gane manufata, let her make another scene zaku gani"" fuuu ya fice"

kamar zai tashi sama.

"""Yaushe yaron nan ya samu kusanci da raihan, har yake shiga cikin lamarinsa haka?"""

"Maryam kamar tayi kuka ta ce ""Mami arata suka kai masa kenan? Mami raihan ya fifita matarsa a kaina, mami ki yi"

"wani abu a kai tun kafin raihan yafi arfin control Winki""."

"Babu tunanin komai, ta hau kan maganar ta zauna."

"Ummi tana sallar magariba a bedroom Win ta, ta ji yo hayaniya a falo, wanda ko tantama ba ta yi muryar mami ce,"

mamin da tun da aka yi bikinsu ba ta taSa takowa gidan ba.

"Bayan ta idar da sallar, cikin tsananin fargaba da tashin hankali ummi ta fita falon, raihan yana ta oarin shawo"

kanta daga masifar da take yi.

"""Mami sannu da zuwa"" rie sannu da zuwanki, idan kin so ma ki kirani da bilki, dan ban haifeki ba, saon da ki ka bawa maryam na ji, na zo kuma in nuna miki na isa da Wa na, kai kuma ka aiwatar da abun da na ce"""

"""Mami dan girman Allah ki yi hauri, mai zai sanya na aikata haka babu wani dalili""."

"""Ni ka ke gaya wa haka? To ka saka a ranka zaka canza wata uwar bani ba, kai ba ka isa ba ma, wallahi sai ka saketa"

"raihan na riga na rantse maka, ko in yi maka abun da ba ka zata ba"" tayi maganar tana watsa masa biro da takarda. Tuni jikin ummi ya fara rawa, ta ji numfashin ta kamar zai Wauke, da sauri ta bar falon, ta tafi Waki, lallai tsuguno ba ta arewa rayuwarta ba."

"Ta Wauki aramar akwatin ta, ta zuba kayanta, ta buWe wurin da raihan yake zuba kuWi ta Wiba ta zuba a jakarta ta"

"Wauki ATM Win ta ta fito, tana zubar da hawaye."

"Ta tarar da raihan a zaune ya dafe kansa, cikin tashin hankali bai yi zaton mami zata aikata masa haka ba."

"Tana ganin ummi ta ce ""Ita akwatin ai na san ba daga gidan ubanki ki ka zo da ita ba, dan haka ajiyeta"" ummi ta"

durusa ta kwashe kayanta ta ajiye akwatin.

Raihan ya mie yana kiran sunanta.

"""Wallahi ka taka ka bita ban yafe maka ba!!!. Ummi ko waiwayawa ba ta yi ba ta fita."

"""Kuma ka san duk yadda zaka yi ka kareni a wurin babanka, wallahi ka kuskura ka gaya masa umarnina ne ka rabu da"

"ita sai na saSa maka, ba zan zuba ido ka zama soko ba"""

"Zuciyar sa na tafasa ya ce ""Mami kina ganin wannan hukuncin shi ne farincikin ki ko? Ni kuma kin untata mini,"

"shikenan tun da haka ki ka yanke kin isa ne, na gode"""

"ura masa ido ta yi ta ce ""Raihan kuka zaka yi dan na rabaka da masifa"" ya kalleta hawaye na gangarowa daga"

"idonsa, ya san komai zai ce mata ba zata fuskanci irin son da yake yi wa ummi ba."

"A falon gida ummi suka yi karo da farida, da ita da kausar da alama ba su daWe da dawowa daga unguwa ba."

"Ta arewa ummi kallo da kaya a hannu ta ce ""Lafiya?"""

"""Ya sake ni ne"" ta faWa a hankali."

"Kawai farida ta rafsa guWa ta ce ""Har an yi an gama? Soyayyar da Waga hancin ya are? To wallahi ba zan rie bazawara har karo biyu ba, ki nemi wurin zuwa ba dai nan gidan ba!!!."

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

"Ina uwargida, amare, har ma da an mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini,"

masu daWi da amshi.

"Mafaka gidan amshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku"

Oll types of Turaran wuta

Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra

Kulakcha Dilke da kalta Kayan

Garan jiki Muna turara Kaya

Kujerar garan jiki Kannada

Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi

Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*

"*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA AN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON AWATA GIDAJENSU DA HAAUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAAUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*."

"*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAAUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*"

"*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ARIN BAYANI, KU TUNTUE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUI GIDA*"

"BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUI."

*CUTARWA*

*BRIGHT PENS*

(FREE BATCH)

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

42

"MASU BUATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL INA, ZAKU SAMU DAGA FARKO"

IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp:

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

AYSHERCOOL

08081012143

"MASU BUATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL INA, ZAKU SAMU DAGA FARKO"

IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp:

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

42

"Cikin sanyin jiki ummi ta ce ""Dan Allah anty ko zuwa da safe ne, sai na tafi in sha Allah"""

"""Wallahi ba ki isa ba, ba zan sake zama inuwa Waya da ke ba, ai ni ba zan manta cin kashin da dr. Ya din ga yi mini saboda ke ba, a samu ki auru da yar sannan ki dawo mini, bana maimaita kuskure, haka Allah ya yi ki da bain jini,"

"kamar mai hatimin jaSa duk in da ki ka je sai an tsaneki an kore ki"""

"Ummi ta yi shiru ta rasa abun da yake yi mata daWi, ina zata tafi ga duhun magariba."

"Kausar ta nufo ummi gadan-gadan da niyyar ta hankaWata ta koreta, ummi ta ja da baya ta kalli kausar ta ce ""Kar ki"

"kuskura, akwai banbanci tsakanin da da kuma yanzu, ko da aurena ya mutu da yardar Allah na fi arfin komawa baya, ba sai kin hankaWa ni ba, zan tafi"". Duka suka kalli ummi, yaushe bakinta ya buWe har haka da take mayar da martani."

"Ta juya ta fita, ta Wan yi nisa kaWan sai ga noor, sanye da uniform Win islamiyya."

"""Yaya ummi, da tafiya zaki yi ban dawo ba, to Allah ya kama ki"" tayi maganar tana murmushi."

"Sai kuma ta yi saroro tana kallon ummi, ganin ummi a saSule."

"""Ya na ganki a haka? Ina yaya raihan Win?""."

"""Ya sakeni noor"" ummi ta samu kanta tana gaya wa noor."

"Ta dafe irji ta ce ""An shiga uku, saki? Me ki ka yi masa? Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ashe da gaske maama take"

"idan Abba yayi mata laifi ta ce namiji ba Wan goyo bane ba, ashe da gaske ne me ki ka yi masa?"""

"Ummi ta dafa kafaWarta ta ce ""Kul ki ka sake faWar haka, mata mukan yaudari kanmu da Worawa maza kaso mafi"

"yawa na zaluntarmu, alhalin a zahiri mu ne azzaluman kanmu, mu yi ta ciwon a mace na a mace ne, amma a zahiri kowace mace ciwonta na ta ne ita kaWai, noor maza an goyo ne, kuma iyaye ne, Sata garin cikin su ba zai sanya ayi musu kuWin goro ba. Mami ce ta saka ya sake ni, ba laifin sa bane ba, ni duka da na san bain cikin Wa namiji a rayuwata, amma maza sun tallafi rayuwata fiye da yadda mata suka yi""."

"Tuni noor ta fara kuka ta ce ""To ina zaki je? Ba dai gagarawa ba ko? wannan garin da ba sa sonki, me zaki je ki yi"

"musu, ki zo mu tafi gida kawai"""

"Ummi ta girgiza kai ta ce ""A'a ai ni in da ba a so na da yawa noor, ki yi maza ki tafi, magariba ta yi"""

"""To ina zaki je?"""

"""Ke dai kar ki damu, zan dawo maza ki arasa gida""."

"Noor ta tafi gida da gudu, sai dai ta tarar farida suna sake tattauna abun da ya faru, a nan ta ji korar ummi suka yi,"

suka ce ba zata zauna a gidan ba.

"Duk da arancin shekaru na noor, sai da ta jinjina mugunta irin ta mahaifiyarsu."

"""Maama yanzu idan wani abu ya sami yaya ummi a hanya fa, dare ya fara yi ki ka ce ta tafi gida? Idan Abba ya ji fa?"""

"""Idan ina magana kina saka baki, sai na murWe miki wuya, tun da ita ta haife ki, duk irin cin kashin da aka yi mini a"

"gidan nan saboda ita ke ba kya gani, saboda ita aka saka miki sunan uwarta ban haWa dangi da ita ba, ki cigaba da saka baki a kan irin wannan maganganun ki ga yadda zan yi da ke""."

"Noor jikinta a sanyaye ta ce ""Malaminmu ya ce; duk wanda ya shuka alkhairi ana yi wa aansa ko an uwansa, haka"

"ma sharri, ni dai tun da ban yi aure yanzu ba, Allah ya sa a rama a kan anty inteesar ko kausar tun da dama ku ne kuke cin zalin yaya ummi"" gaba Waya sai suka kasa magana, wata maganar idan noor ta yanko ta, sai ka kasa ba ta amsa."

"Farida ta yi arfin halin cewar ""A gidan Ubanki aka zalunceta?"" Tayi shiru ta rungumi jakarta ta shiga ciki."

Raihan yana zaune din ga jujjuya takardar a hannunsa.

"Mami ta zuba masa ido tana kallon ikon Allah, duk zafin ciwo ko na mutuwa raihan ba ya kuka, amma yau saboda ta"

"raba shi da ummi, har da hawaye."

Nan ta ara tabattarwa da kanta cewa ummi asiri suka yi wa Wan ta.

"Ta mia hannu za ta karSi takardar hannunsa, ya janye takardar."

"Saki nawa ka rubuta a jiki?"" Tayi maganar tana kallonsa."

"""Dan Allah mami ki yi hauri ki yale ni, ai na rubuta"""

"""Kar ma ka rubuta, kuma ka tabattar a yau ba sai gobe ba, ka bi ta da takardar nan, kuma bana buatar sake wata"

"alaa a tsakanin ka da ita. Abu na gaba shi ne zan je na nema maka taimako a warware sihirin da suka yi maka, azo ayi maza a yi bikin nan""."

"Bai ce mata ala ba, ta gama surutun ta tafi, ji take kamar ta yaye wa kanta wata babbar damuwa da ta hanata"

sakewa.

Tana tafiya raihan ya shiga Waki ya Wauki wayarsa ya tura wa ummi sao.

"""Salma, ki jirani a gida komai ya lafa, zan zo na Wauke ki, dan Allah kar ki gaya wa kowa, ban rubuta komai ba, ban"

"sake ki ba, zan dai-daita komai. Ki kwantar da hankalinki da safe in sha Allah zan zo"""

"Bayan ya aika mata saon, ya ajiye wayar ya shiga yayi alwalar magariba."

"Sai dai hankalinsa ya kasa kwanciya, ji yake kamar ya bi ummi, amma da ya tuna gargaWin mami sai ya kasa bin ta."

"'Ban kyauta ba salma, am very sorry, baki cancanci haka ba' haka ya din ga sintiri yana surutai."

"Kasa jurewa yayi, ya Wauki wayarsa ya kira tata, sai dai ba ta Wagawa, tun yana saka ran za ta Waga har ya fara sarewa"

ya sanyawa ransa ummi ta yi fushi da shi.

"""Haba ummi, meyasa ki ke tunanin zan iya sakinki? Ba zan iya ba wallahi ban sake ki ba"" ya din ga surutai yana kiran"

wayarta.

"Ummi kuwa arfe goma na dare, tana cikin motar haya, ta nufi gagarawa, tana ta lissafi kala-kala a zuciyarta, yanzu"

shikenan lissafin rayuwarta ya koma baya?.

"Ta san zaman gagarawa ba zai kai ta ba, to sai ta tafi maiduguri daga yin aure ace ya mutu, ga mama ba cikakkiyar"

"lafiya ba, suna murnar sun aurar da ita, kuma ta koma ta zaune musu a gida yau da gobe sai Allah."

"Ta share hawayen ta a hankali ta furta ""Mami ba ki yi mini adalci ba raba ni da Wakina da mutumin da nake matuar"

"auna"" tayi maganar tana unshe kanta a hijjabinta tana kuka."

"an cikin motar sai ba ta hauri suke yi, ba tare da sanin dalilin kukan na ta ba."

Sai sha Waya da kusan rabi ta shiga family house Win su na gagarawa.

"Duk an rufe wasu ofofin wasu duk sun kwanta, jiki a sanyaye cikin tsananin fargaba ta shiga sashin iya da sallama."

"Iya ta amsa daga Waki tana tambayar waye, ummi ta shiga tana amsa mata da ni ce."

"Kamar sokuwa iya ta kalleta, ta Wau fitila tana haskata. ""Lafiya zaki shigo mana gida a tsakar daren nan kamar wata"

"ar fashi?""."

"Ummi ta ce ""Lafiya alau"""

"""Kamar yaya? Ki rasa lokacin da zaki zo sai a wannan tsohon daren, yahaya dai an ce ba ya asar nan me ki ka aikata"

"ki ka gudo nan, ba zaki kwaso masifa ki yo nan ba, dan na san ba alkhairi ne ya kawo ki ba a daren nan dai"""

"Ummi ta yi ajiyar zuciya, ga gajiya ta kwaso kanta har ciwo yake, ga uban kuka ta sha ga tuhumar wulaanci daga iya,"

"kodayeke ba yau ne farko ba, dan haka ta ce ""Mun rabu ne"""

"""Da wa?"""

"""Ya sake ni"" ta faWa a taaice."

"""Kuma da ya sake ki ki rasa ina zaki zo sai gagarawa? Garin da ki ka ce ba zaki sake zuwa ba? Amma ke dai an yi mai"

"ashin tsiya, a yadda ki ke Allah ya rufa miki asiri ki auru da yar ki kaso auren? Kodayeke kin gaji tsiya da rashin arzki a wurin uwarki, wallahi sai dai ki koma can wurin yahayan, ko ki koma wurin uwarki ba ki da wuri a gidan nan, ke ko kunya ma ba ki ji ba?"""

"Ummi ta ce ""Dan Allah iya ki yi a hankali, ki rufa mini asiri ko sati na yi zan yanke shawara idan bai mayar da ni ba"

"shikenan, ba a san ransa ya rabu da ni ba, na san zai neme ni da....."

"""Dan Allah ki rufe mini baki, kin manta iskancin da ki ka din ga zubawa saboda zaki auri mai kuWi? Wallahi sai kin

Please Login or Register in order to submit comment