You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

komai, amma banda kishi kenan? Aishikenan gaskiya ne Safiyya ita ce wadda ake son haWa ni da ita, ni kuma ke nake so, shiyasa na ce miki akwai alubale, ko ba"

"komai safiyya ta saka na gane in da ki ka dosa, yanzu zaSi ya rage naki sweetheart, ki kula da ni sosai kar Safiyya ta wace miki ni, kin san zuciya na son mai kyautata mata, ke kin ce ba kya so na, safiyya kuma tana so na, ki zage damtse kar ki bari a wace ni, i so much love you baby"""

"aga ido tayi ta kalleshi, ya ga kamar hawaye ne yake shirin taruwa a idon ummi, ya tashi tsaye ya ce ""Bari in tafi"

"wurin safiyyan, tun da ita take so na, na san zata yi mini, idan kin tashi ki kirani"""

"""Idan ka je kar ka dawo, a Waura muku aure yau"""

"Gwalo yayi mata ya ce ""Ki gama iyayin da tsiwar, raihan Win dai ki ke so""."

Ayshercool

08081012143

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefr

iends

"Masu neman free books Wina, da free pages duk akwai a kan watpad account Wina. Irinsu Abduljalal"

Wata kissar sai mata Wuta a masaa Cutarwa

anwar maza Gaba da gabanta Aidata

RuWin uruciya

Zaku iya samun paid pages Win a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuSe ni kai tsaye ta lambar wayata.

8081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

"Ina uwargida, amare, har ma da an mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini,"

masu daWi da amshi.

"Mafaka gidan amshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku"

Oll types of Turaran wuta

Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra

Kulakcha Dilke da kalta Kayan

Garan jiki

Muna turara

Kaya

Kujerar garan jiki Kannada

Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi

Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*

"*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA AN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON AWATA GIDAJENSU DA HAAUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAAUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*."

"*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAAUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*"

"*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ARIN BAYANI, KU TUNTUE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUI GIDA*"

"BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUI."

*CUTARWA*

*BRIGHT PENS*

(FREE BATCH)

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

36

"MASU BUATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL INA, ZAKU SAMU DAGA FARKO"

IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp:

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

"Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan"

abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.

FOLLOW AND SHARE

AYSHERCOOL 08081012143

"MASU BUATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL INA, ZAKU SAMU DAGA FARKO"

IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp:

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

"Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan"

abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.

AFUWAN BAN YI EDITING BA

36

"Ya fice daga shagon yana murmushi, ta iya Soye fushinta da damuwa, amma ta gaza Soye kishinta."

"Yana tui yana tuno fuskarta, wai har da yin fushi saboda shi, fushi sosai kishinta ya fito."

"Ya shafi gemunsa ya ce ""Ina sonki sosai salma, in sha Allah idan na aureki ba zaki sake yin kukan damuwar rashin"

"wani abu ba"""

"Ummi kuwa, tayi shiru tana tunani, tare da ganin kamar tayi wauta raihan ya gano tana kishinsa, tayi guntun tsaki za"

"ta cigaba da aiki, kawai sai Safiyya ta faWo mata."

"Sai gabanta ya faWi, gaskiya ne akwai banbanci tsakanin budurwa da bazawara, amma ita babu abun da ya taSa haWa"

"ta da Idiris har suka rabu, a take kuma tunaninta ya sauya da tunanin kar matsalar da ta faru da ita a farko ta sake faruwa da ita."

"Tayi shiru tana tunani menene mafita? Ita ba awaye ba, mamanta kuma ba lafiya ba su yaya maryam kuma ba"

"sabawa suka yi ba, ko da sun saba ma, ba zata iya gaya musu wannan lamarin ba."

"Ta din ga sae-sae a ranta, ta tuna duk da tsanar da Idiris yayi mata, larurar nan ta ara taka muhimmiyar rawa,"

"wurin kashe mata aure, dan da ya samu abun da yake so, da sai ya gama moreta kan ya saketa, ta tuna yadda ya din ga oarin haike mata tana yarinya, take ta kawar da tunanin, dan a duk lokacin da ta tuna har kuka take yi, yadda Idris Win yake lalubeta, ba ta jin a duniya ko zata yafewa kowa za ta iya yafewa Idiris, ba ta rie CUTARWA! idan an yi mata amma cutarwa irin ta iya da Idiris ba zasu goge a tarihin rayuwarta ba cikin saui."

"Ta cigaba da tunani a irin wa'azin da take bibiya, mussman na malamai daban-daban da sauran shirye-shiryen"

"gidajen rediyo, domin kasancewar ta ar jarida, ya sanya tana yawan sauraren Radio, da bibiyar labarai, ta fuskanci cewa duk soyayyar da namiji yake yi wa mace, idan aka samu naasu akwai matsala, ila ba lallai raihan ya jure ba ya auro safiyya su juya mata baya, kamar yadda aka yi wa inteesar."

"Sai kuma kawai ta ga abun banbarakwai, wai ace raihan ya aureta shi ne mijinta, ta haWa shimfiWa da shi, goWai-goWai"

"da ita, kawai ta ji wata kunya ta sake kamata."

"A arshe ta yanke shawarar yin haWin da malamar asibitin nan ta taSa bata, na kanumfari, citta, namijin goro da tafarnuwa, tun da maganin sanyi ne sosai."

"Aikin ma dai ta kasa mayar da hankali a kansa sosai, sai sae-sae, rayuwar aure rayuwa ce da ke buatar a zaunar da mace a karanta mata darussa daban-daban, ba kuma wai sai lokacin da aka kawo kuWin aure aka saka mata rana"

"ba, yakamata mace ta san wasu abubuwan, amma ummi ba ta da wani da zai zauna da ita ya buWa mata, duk da daga ita har mijin nata ba wani mai yawan shekaru sosai."

***

"Yaya maryam ta kira dr. A waya,suna yi masa tunin ya kawo musu ummi, suka cigaba da shirye shiryen su na al'ada, ga mariya ma duk ta ishesu, har da koke-koke a kan a dawo da ummi."

"Ya ce mata so yake arshen wata, tayi sallama da wurin aiki ya rage saura wata biyun sai ta dawo."

"Ya gaya musu yadda aka tsara bikin, ta ce a matsayin su na dangin uwa, zasu gabatar da nasu bukukuwan a nan"

"maiduguri, sai su taho da ummin kano, suma su yi nasu."

"""Amma ina ganin kar Wawainiya tayi muku yawa, ba sai kun yi ba, ku bari duk ayi a kanon"""

"Ta ce ""Haba baban ummi, ar mariyar waya Waya tal mu kasa bajinta a bikinta, a'a ka bari zamu yi mata bikk na gani"

"na faWa, sai mu taho da ita, da mu da abun da Allah ya yassare mana"""

"Ya ce ""To shikenan, in sha Allah zan kawota da kaina, amma saura sati biyu biki, zan zo na kaita gagarawa, ta je ta yi"

"musu sallama, ta kuma basu katin bikinta"""

"Yaya maryam ko sunan garin ba ta aunar ji, balle wani abu da zai sake haWa su da garin, ta kasa jurewa ta ce ""Amma"

"ba a iya aika musu ba, dole sai ta je"""

"Dr. Ya ce ""Na san abun da yake cikin zukatanku, amma ba a canzawa tuwo suna, dangin mahaifinta ne dole ku yi"

"hauri"""

"Ta ce ""To shikenan, Allah ya kaimu arshen watan, sai kun zo Win"""

Ya amsa mata da Amin.

"Raihan daga shi sai Hajiya da kuma Hajiya Aisha suke ta shirin bikin, sai Alhajin sa, tausayin Wawainiyar da yake ta yi, ya sanya Salim Wan shiga lamarin, yake taimaka masa da shawarwari, dan shi abokansa duk sun yi aure, raihan kuwa"

age mate Win sa wasu ma ba su kammala makaranta ba.

"Saura watanni biyu bikin ummi, dr. Ya ce ta haWa kayanta, zata tafi maiduguri kamar yadda ya yi alawari."

"Ummi murna kamar ta taka rawa, dan dama jin ta take yi a matse a gidan nan, farida ta sakata a gaba da masifa iri-"

iri.

"Ta rubuta takarda ta kai wa manager na barin aiki, manager kamar yayi kuka, saboda sun saba da ummi sosai da"

"sosai, kuma suna jin daWin aikinta, ba yuya babu ganin ido komai na ta tsakani da Allah, sai dai sun yi mata fatan alkhairi sosai da jin ummi za ta yi aure."

"Tana ta shirin tafiya maiduguri, raihan ya kirata a waya, ya ce mata manager yana nemanta, tayi mamakin yadda aka"

"yi manager bai kirata ba, ya kira raihan, kai ka ce shi ma ma'aikacin su ne."

"Ko da suka je, manager ya ce yayansa ne yake son ganin ummi, su Wan jira shi zai zo. Manager sai cewa yake"

"""Shikenan tayi aurenta ta huta da nacinka, ko gidan nata zaka din ga bin ta kana takura mata?"""

"Raihan yayi wani irin murmushi ya ce akwai wanda ya isa ya raba ni da ummina ne? Kullum ina gidanta, ko kuma ka"

"bani anwarka na aura a haWa mu biyu"""

"Manager ya harare shi ya ce ""Aikuwa da mijinta ya zaneka saboda hayyatarka, in baka anwata kai wa zai maka aure yanzu? Raihan da kana ganin ka fi ni girma gani ka ke kai wani babba ne ko? In sake jin ka yi maganar auren nan, sai"

"na zaneka"""

"Wata irin kunya ta kama ummi, ta san da kunya idan ya bayyana raihan za ta aura, dan manager ya Wauka kawai Wan uwanta ne, irin sako da sakon nan."

"Raihan kuwa ya din ga dariya, ya ce ""Zan baka mamaki kwanan nan"""

"Shugaban wurin ne ya yi sallama, da yaransa suka amsa masa, ya samu wuri ya zauna suka gaggaisa, ya Wan yi musu raha kasancewar sa mutum mai barkwanci."

"Ya ce ""Ummi yanzu haka zaki tafi ki barmu, mijin ba zai bari ki cigaba da zuwar mana ba?"" Ummi ta sunkuyar da kai"

"tana wasa da yatsunta. Raihan ya zuba mata ido ya ji me za ta ce, amma tayi shiru."

"Ya yi ta yi wa ummi nasiha a kan zaman aure, ba tare da sanin da angon a wurin ba, sai dai raihan ya fara jin haushin"

"yadda manager ya tsare ummi da ido, yana yi mata faWan kamar mai rarrashinta."

"Bayan sun gama ya ce ya bawa ummi kyautar sabon fridge babba, da kuWi dubu hamsin da certificate na karramawa"

"saboda gaskiya da rion amana, da kuma oarin da tayi wurin cigaban wurin."

"Raihan cikin girmamawa ya ce ""Masha Allah, mun gode sosai da sosai, Ubangiji Allah ya saka da alkhairi, ya sa afi"

"haka"""

"Ummi ma godiyar take yi masa, ta san kuWin fridge Win nan ba kaWan ba ne ba, ga kuma kuWi da ya bata."

"Manager ya ce wa raihan ""Ka gani, hauri mai tarar da rabo, da ba ta raina 15k ba, ga rabon da ta tarar nan, ka canza hali raihan. Ko kuma tun da ta tafi kai ka zo mu baka aikin"""

"Ya harari manager ya ce ""Ba zan yi ba"""

"Har da masu kai fridge Win aka haWa ummi, masinjojin su."

"Ummi ta kira dr. Ta gaya masa, ya din ga murnda sanya albarka ya ce zai je yayi musu godiya."

"Ana gobe ummi za ta tafi maiduguri, raihan kamar yayi mata kukan ba ya son ta tafi, saboda zai daina ganinta a kai-a"

"kai, sai dai yayi mata alawarin zuwa ya gaida mama."

"Haka zalika ya tura mata kuWi a account Win ta, ya ce idan ya tashi zuwa maiduguri zai taho mata da kayan fitar biki."

"Suna zane suna hirar, wayar ummi ta fara ringing, ta Waga wayar, sai ya ga ta yi shiru tana kallon sa, amma ba ta ce"

komai ba.

"Kawai sai ya tsargu, ya karSi wayar ya saka a hansfree."

"Muryar Safiyya ya ji, tana ta zazzaga rashin mutunci, da kalaman muzantawa ga ummi."

"Jin ummi ba ta ce komai ba ya sanya safiyya cewa ""Malama ba magana nake yi miki ba?"""

"""Da raihan Win ki ke magana ba ummin ba"" hankali a tashe ta kashe wayar, tana salatin Allah ya rufa mata asiri."

"Ya kalli ummi ya ce ""Dama haka take kiranki tana ci miki mutunci ba ki gaya mini ba?"""

"Ummi ta ce ""To me zan ce, kullum sai in are a kan ara, ni ba zan iya ba tun da ka ji yanzu da kanka shikenan, dan Allah idan zaka aureta ka aureta amma ni ta daina zagina"""

"Ya jinjina kai ya ce ""Ina fatan dai ba shiru ki ke yi mata ba?"""

"""Ni mu bar wannan zancen bana so"" tayi maganar tana zumSura baki, ya Wan ura mata ido, kishin ne yake"

"damunta, dan haka yayi mata shiru kawai."

"Daga wurin ummi da niyyarsa ya je gidan su safiyya, sai dai ya fasa ya tafi gida kawai."

"Ummi ta tattara muhimman kayanta, ranar tafiya ta je yi wa farida sallama, amma ta ka da baki ta ce mata Allah ya"

raka taki gona.

"Mami na ta sake maimaitawa raihan idan ya kuskura ya kashe kuWi sosai a harkar auren ummi, sai ta ci masa"

mutunci fiye da yadda yake zato.

"Kwana biyu da tafiyar ummi maiduguri, Raihan ya je gidan su safiyya, anty rakiya har ta fara yashe baki, tana cewa"

"""Babban mutum barka da zuwa, yau kai ne a gidan namu?"""

"Ya ce ""Eh, safiyya fa"""

"Ta ce ""Ahh wurin mutuniyar aka zo kenan, to bari na yi mata magana"""

"Kasancewar Safiyya ta san abun da ta aikata, ya sanya gabanta faWuwa ta ce ba zata ba."

"""Dan ubanki abun da muke neman zaki ce ba zaki ba?"""

"Kamar za ta yi kuka ta ce ""Ni fa tsoro nake ji, na gaya miki abun da ya faru"""

"""To sai ki bari kanki ya kulle, ba mace ba ce ke? Guda nawa raihan Win yake banda ma ya jajibo aure? Tashi ki je"

"dalla"""

"Har ta shiga falon tv yake kallo, bai ko Waga kai ya kalleta ba, sai da ta zauna ta fara gaishe shi ya amsa, ya tambayeta"

"ya makaranta ta ce masa lafiya alau, sannan ya kalleta ya ce ""Safiyya na san kin san abun da ki ka aikata, to ki sani, ba zuwa na yi bin ba'asi ba, kuma ba wani ya gaya mini ba, ta gaya mini na farko na kawar da kai, ban zaci irin wannan zagin ki ke yi mata ba, to ba sa'arki ba ce ba, kuma hakan da ki ke yi ba zai canza komai na batun aurena da ummi ba, wallahi idan ki ka sake kira mini mata ki ka ci zarafinta sai na gwada miki waye raihan, ba ruwana da wani zumunci sai na Waureki an ci tarar ki, na gaya miki. Ni ba yale-yale nake bi ba, mutunci, tarbiyya da soyayyar da nake yi mata ya sa zan aureta, kalli jikinki kowa ya gama gani, ba shigar mutunci a tuninki wannan ce wayewa safiyya? Dan an ce miki matar da zan aura kidahuma ce, ni a wurina hakan ne wayewa, kar ki bari abun da ki ka yi ya taSa zumuncinmu, dan bana magana biyu, idan kuma Anty na da kuWin belinki ki cigaba da kiran Salma kina ci mata mutunci tun da baki da kunya"" bai ko tsaya yin sallama da anty rakiya ba, ya tashi yayi tafiyarsa."

"Aikuwa kan ya je gida, tuni sun sanarwa da mami, yan zuwa ta dirar masa da masifa tare da kashedi iri-iri, ciki har da"

"barazanar sanyawa a fasa auren sa da ummi, tare da jaddada masa cewar aurensa da safiyya ba fashi."

"Ummi kuwa yadda su yaya maryam suke kula da ita da gyarata, har gajiya ta fara yi, a murza mata wancan, a shafa"

"mata wannan, gashi aka hanata aikin komai, kullum tana kauwwame a wuri Waya, daga ci sai sha, banda kayan magungunan gyaran da ake ta yi mata."

"Tulin turarukan wutan da ake ta haWawa kuwa, kai ka ce ci za ayi, ga uban kayan kitchen."

"Ummi har hawayen daWi tayi, saboda irin so da aunar da dangin mahaifiyarta ke nuna mata, gashi dai ba wani arfi"

"ne da su ba, amma sai zuciya da oari."

"Ga isasshen lokaci da ta samu tare da mama, ga isasshen abinci mai kyau, komai na ta daban."

"Saura wata guda biki, raihan yana ta shirin zuwa maiduguri, yana zaune suna shawara da hajiya, a kan yadda"

"abubuwa zasu gudana, ya haWa akwati guda na kayan fitar biki kawai. Salim yana zaune sai dai bai tsoma musu baki ba."

"Sai daga baya ya ce ""Wannan akwatin Waya kawai zaka kai sai ka ce tsiya, ba zaka yi lefe ba?"""

"Cikin sanyin jiki ya ce ""Mami ta hana, ta ce bazawara ce, wai kuWin auren da aka kai ya isa, shi ne na ce bari na yi"

"mata kayan fitar biki, lefen idan ta je gidana na yi mata, amma kalli kayan ka gani masu kyau ne fa"" yayi maganar yana buWe masa akwatin."

Tabbas manyan kaya ne sosai da sosai na alfarma.

"Salim ya yi ajiyar zuciya ya ce ""Idan ka kai musu sai dai ka yi musu bayani, na ji ka ce maiduguri zaka kai mata, ana yi"

"wa iyaye akwati fa su ma, dole ka yi oarin fitar da su kunya, aurensu da tsada sosai"""

"Hajiya ta ce ""Kai a ina ka sani?"""

"Ya amsa mata da ""Abokina umar Wan can ne ai, kuma ar can ya aura, ni da shi muka din ga shirin bikin ai"""

"Cikin marairaicewa raihan ya ce ""To ka taimaka mini mana nima"""

"Ya girgiza kai ya ce ""Bana son babarku ta zo ta ce ba a kyauta ba"""

"Hajiya ta ce ""Ba aninka bane ba? Babu abun da za ta ce"""

"Haka kuwa aka yi, dan sai da suka sake sayen akwati, aka zuba atamfofi da shadda, wanda ake yi wa iyaye, sannan ya"

gaya masa zai bayar da kuWin turaren wuta.

"Gwiwar raihan ba ta yi sanyi ba, dan shi a ganinsa komai zai kashe wa ummi bai faWi ba."

"Yadda raihan Win ya din ga yi wa salim biyayya, ya sanya da Hajiya ta lallaSa shi ta ce su tafi tare maidugurin bai yi"

musu ba.

"Can Maidugurin ma da ummi ta ce musu raihan zai zo, aka din ga shirye-shiryen tararsa, dan bai gaya mata da Salim"

zai zo ba ma.

"Mami ta so hana tafiyar nan, amma Alhaji ya taka mata burki, ya ce babu abun da zai hana raihan zuwa maiduguri,"

tun da matarsa a can take.

"Kasancewar ana idar da sallar asuba suka tafi, arfe sha Waya na safe suka sauka."

Suka bi adress Win da ummi ta basu har gidan suka je.

"Kasancewar sun yi shigar kamala, daga shi har Salim, hakan ya ara musu kima a wurin an uwan ummi."

"Sai rarraba ido kawai yake yi ya ga ummi, aka kawo musu abinci na alfarma."

"Sun kai a alla awa guda, yaya maryam ta tsare ummi, ta hana ta zuwa, sai daga baya ta shirya cikin lafaya mai kyau, sai amshin turare take yi, hujin hancin da suka yi mata, ta saka barimar azurfa, sai yalli take yi a kan baar"

fuskarta.

"Da tayi sallama tare suka Waga kai suka kalli ummi, babu kunya raihan ya kafe ta da ido."

"Salim ya jinjina kai a ransa ya ce ""Lallai yaron nan akwai tsaurin ido"""

"Ummi ta wani ara cika sosai, ga wani irin amshi da ya cika Wakin."

"""Oyoyo sweetheart"" yayi maganar cikin sanyin murya."

"Durusawa tayi har asa ta gaida Salim, ya amsa mata fuskarsa babu yabo ba fallasa."

"Ta juya wurin raihan ma ta gaishe shi, ya amsa yana washe baki."

"Ya ce ""Tun da ga yaya salim, akwai kuWi a jikina, sai a Waura yanzu kawai"" hararsa tayi ta samu wuri ta zauna."

"Salim ya mayar da hankali a kan wayarsa, kamar bai san suna wurin ba, raihan kuwa ya rasa control ya din ga zuba a"

"gaban Salim, ummi kuma kunya kamar ta nutse."

"""Baby me mama take baki ne? Kin ara iba, kalli skin Winki"""

"""Ni fa bana son ibar nan"" ta faWa a hankali."

"""Ni kuma ina so, baki ga kyan da ki ka ara ba, kin ji amshin da ki ke yi kuwa? Anya zan iya jiran lokacin nan, Innalillahi kin ganki kuwa? You look take away, ko dai in yi zamana a nan"""

"Dukan da Salim yayi masa a eyarsa ne, ya sanya shi yin shiru yana sosa kai."

"Ummi ta yi masa gwalo, ta ce ""Bari na je n yi wa mama magana, mu shiga ku gaisa"" ta tashi ta fita."

"Tana fita Salim ya ce ""Kai dan ubnka a gidan sirikai fa ka ke? Wannan da bamu zo tare ba me zaka yi?"""

"Raihan ya ce ""Bakomai"""

"Yayi asa da murya ya ce ""Zaka ara da kuWin gyaran jikin da ake yi mata, kara fa aka yi maka da duk ba ta"

"tambayeka ba, zaka saki bakin aljihu tun da Wiyar an maiduguri zaka aura"""

"Raihan ya ce ""To ai duk ba ta gaya mini ba"""

"Salim ya ce ""Ni yanzu na gaya maka, kuma wannan ginin da ka ke yi, ka je ka ce wa Alhaji ya saya ko ka bashi jingina,"

"ka samu gida mai kyau ginanne ka saya"""

"Raihan ya ce ""To ai ina son gidan sosai """

"""To ka ce wa Alhaji ya baka gudunmawar bikin, ka arasa"""

"Raihan ya yi dariya ya ce ""Haka za ayi yaya"""

Ya Waga masa gira.

"Ummi ta ce ""Bisimillah ku shigo"""

"Suka tashi suka shiga, suka din ga gaisawa da mutanen gidan, ummi tana gabatar musu da kowa."

"A Wakin mama suka yi sallama, suka zazzauna, ta din ga murmushi tana amsa musu gaisuwar."

"Ta kalli yaya maryam ta ce ""Yaya, wannan suwaye?"""

"""Sirikanki ne, wannan ne zai auri ummi"""

"Sai tayi dariya ta rausayar da kai ta ce ""Ummin za a yi wa aure yanzu? Ai tayi arama da yawa"""

"Maryam ta ce ""Wai ke ummin haryanzu a kan cinyarki take ne tsawon shekaru ba ta girma ba?"""

"Ta kalli raihan ta ce ""To kai ba ka ga munin na ta ba? Iya ta ce mummuna ce babu mai aurenta"""

"Raihan ya ce ""Haba mama, ummi ba mummuna ba ce ba, kalleta fa ki gani tubarkallah masha Allah"""

"Ta ce ""Yauwwa, da ma na faWa, wani zai ce yana son ummi a

Please Login or Register in order to submit comment