ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://arewanovels.com ÿþ"Tambuwal:; December, 21"

A Jikinta ya manna kanshi da cikinta kana kuma ya cusa fuskarshi acikin jikin nata.

Tare dasa hannunshi na dama ya dam™e mararshi.

"Gaba Waya jikinshi rawa yakeyi tamkar mazari, wani irin ciwo cikinnasa keyi masa, wanda har hakan yasa"

"numfashinsa, ke kokarin kwacewa."

"Hannunshi na hagu yasa abayanta ya zagayeta, tare da ri™e ta gam-gam cikin gigitan ciwo da fitan"

hayyaci.

"Hakan kuwa yayi masifar gigita Jannart, wanda gaba daya jikinta ya d auki rawa, kamar yadda nashi jikin"

ke rawa.

Kana ya kwakumeta ya kanainayeta ya hanata ™wa™™waran motsi.

"Jannart kuwa Ganin hakan yasa cikin firgici ta buWe baki, murya na rawa ta fara cewa."

"""Innalillahi wa innailaihi rajiun Mamy! Mamy!! Mamy!!! Kalli yadda yakeyi fa!!!! ."

"Yayinda ita kuwa Mamy cikin tsananin tashin hankali da kidima, ta fara juyawa tsakiyar falon cikin rashin"

sanin abinyi taketa rabkawa Ramadan kira.

 Ramadan! Ramadan!!! Kazo!!! Rayyern ba lfy .

"Dr. Sulaiman ne wanda shi ya dawo da Rayyern din, ya turo ™ofar da hanzari,"

"baishigo da wuri bane kuma, saboda ya tsaya fadawa Baba MauWo cewar ciwon Rayyern ne ya tashi."

"A hanzarce ya faWo cikin falon,"

Baba MauWo na biye dashi a baya.

"Yayinda sukabar Hadi da Ari mai gadi kuwa tsaye a harabar gidan, sunyi jugum-jugum domin duk mai"

"imani, muddin yasan yadda ciwon Rayyern ke yi in ya tashi tamkar zai tafi da ransa to tabbas zai cika da fargaba."

"Hakan ne ma yasa Hadi zaro wayarshi ya kira Abba, yana Wagawa cikin yanayin tashin hankali yace."

 Alhaji jikin Rayyern fa ya tashi .

Cikin kidima Abba ya kalli mutanen da yake tare dasu tare da mi™ewa tsaye yace.

 Rayyern ba lfy .

Yana faWin haka ya fita daga falon da bisa alamu duk mgnar sirri yakeyi.

Yana katse kiran Hadi ya kira Ramadan yana Wagawa yace.

 Kai Ramadan kana ina .

Da sauri yace.

 Abba ina Minjibir ne. Lfy kuwa? .

Cikin bada umarni da tashin hankali yace.

 Maza ka wuce kayi gida yau kuma cikin Rayyern ya tashi .

"Cikin tsananin tashin hankali Ramadan ya mike tare, da barin duk wani abu da yakeyi, hankalinsa"

amatukar tashe yace.

 innalillahi wa innailaihi rajiun! Jikin Hamma Rayyern ya tashi? Yanzu Abba Hamma Rayyern din yana

ina?

"Abba dake tsaye, cikin alhini da fargaba yace."

" Yana gida, kayi sauri kaje. "

Yana gama fad in haka ya katse kiran.

Kana yaci gaba da tu™in da yakeyi.

Shi kuwa Ramadan a kidime ya kalli Riyyam-nsra dake cewa.

 Hamma Ramadan meya faru .

Ya ™are .mgnar yana firfito da idanunsa.

"Idanu Ramadan din ya rumtse da karfi, cike da alhinin abunda Abban ya gaya masa, ya kamo hannun"

"Riyyam-nsra tare da jansa, suka nufi parking lot, hankalinsa atashe yace."

" Riyyam mu tafi gida yau kuma ciwon cikin Hamma Rayyern ya tashi,"

"abunda yafi shekara biyu ya kusa shekara uku bai tashi ba, amma yau gashi ya sake tashi mishi. "

 Innalillahi!

shine abinda Riyyam-nsra ke ta maimaitawa.

Dai-dai lokacin da suka shiga mota.

A 360 Radaman ya figi motar yana cewa.

" Yah Rabbi, Yah Allah ka bawa Hamma na lfy, gaba Waya mun sakankance, da cewar ya worke tunda"

mukaga yayi shekaru bai tashiba .

A nan gidan kuwa.

"Cikin yanayi tashin hankali Mamy ta kamo hannun Dr Sulaiman, a gigice ta jawoshi zuwa gaban Jannart"

"da Rayyern ke kwance kanta, irin kwanciyar nan ta rubda ciki."

Murya na rawa Mamy tace.

 Sulaiman duba min Rayyern yana raye kuwa duba minshi kaga fa baya motsi .

Ta ™are mgnar wasu irin masifaffun hawaye na kwaranyo mata.

"Yayinda sai a lokacin kuma Jannart ta sunkuyo da kanta, ta zuba mishi ido tabbas kuwa ya daina motsi,"

duk rawa da karkarwar da jikinshi keyi ya bari.

Wani irin zaro ido tayi tana kallon Mamy dake cewa.

" Innalillahi wa innailaihi rajiun Sulaiman ka duba min Rayyern, kada ya tafi ya barmu akwai nauyinshi da"

"bamu sauke a kanmu ba."""

"Shi kuwa Dr Sulaiman kamo hannunta yakeyi, yana son zaunar da ita amman ina, gaba daya ta gama"

"gigicewa, ga hawayen dake ta Kwarara acikin Idanunta."

"Baba MauWo kuwa da sauri ya matso gaban Jannart ya tsuguna, cikin kuma tashin hankali yasa"

"hannunshi, akan wuyan RAYYERN sabida a kife yake, murya na rawa dattijon ya fara kiran sunanshi."

 Rayyern! Rayyern!! RAYYANU!!! Muhammad Muhammadu tashi.

BuWe idanunka MauWona!!! .

Ya ™are mgnar hawaye na kwaranyo mishi.

Wanda ganinsu ne kuma yasa hawayen idanun Jannart tsinkowa.

Tausayin tsohon da Mamy ne sukayi masifar raunata mata zuciya.

"A fili zaka gano tsananin tashin hankali da kidimar da suke ciki, kana da tsananin sonshi dake cikin"

kwayar idanunsu.

"Shi kuwa Rayyern da yakejin kansa acikin wata duniya, mai dauke da tsananin azaba gami da radadi,"

sama-sama haka yake jiyo muryarsu.

"Saidai kuma bazai taba iya amsawa ba, duk da yana jiyo kiran sunansa da Baba MauWo keyi, saidai baya"

"da hakikanin cewa, ko yan siraran labban bakinsa zai iya motsawa, saboda tsananin ciwon da yakeji."

"Dr Sulaiman kuwa cikin samar da kwanciyar hankali wa Mamy, ya samu ya ajiyeta bisa kujera kana a"

hankali yace.

" Mamy Rayyern yana numfashi fa, babu abunda ya samesa, Dan Allah ki kwantar da hankalin ki, Insha"

"Allah zai samu lfy, na mishi allura tun a asibiti, yanzu haka ciwon ya fara lafawa, Insha Allah gaba daya zai daina ."

"Dr. Sulaiman din ya kare maganar cikin, kwantar da murya da kuma son samawa Mamyn nutsuwa."

Dai-dai lokacin ne kuma Abba ya shigo.

Da sauri ya iso tsakiyar falon.

Sai kuma ya iso gefen Baba MauWo a kidime ya fara kiransa.

 Rayyern .

Sai kuma ya juyo da sauri jin Dr Sulaiman na cewa.

" Abba dan Allah ku kwantar da hankalinku, ku barshi zuwa anjima kaWan zai iya amsa muku, nayi masa"

allura Insha Allah zai samu sauki .

"Wani irin dogon numfashi Abba ya sauke, kana ya koma ya zauna bisa kujerar dake gefensa."

Yayinda Mamy kuwa har yanzu ta gaza tsaida hawayenta.

"Gaba daya hankalinta yaki kwanciya, tsoro takeji kada wani abu ya samu Rayyern din, badon komai ba"

"kuwa saidan sanin da tayi, cewar ciwon cikin baya tab a yi masa da sauki idan ya tashi."

"Jannart kuwa da tayi k asa da kanta, tana jin yadda Rayyern din ke kwakume da ita da masifar ™arfi,"

"yanayin rikon da yayi mata, dinne kuma yasa kugunta ya soma sarawa, saboda ba wai riko ne na wasa"

yayi mata ba ri™one na neman mafita.

"Ramadan da Riyyam-nsra kuwa kusan a jere da sassarfa suka shigo cikin falon, kowannensu hankalinsa"

amatukar tashe.

"More especially Ramadan da yasan irin yanda ciwon, keyiwa Hamman nasu idan ya tashi."

"Da sauri suka nufi kanshi, saidai basu k arasa ba kuma suka tsaya, saboda ganin su Abba duk suna zaune."

"Baba MauWo na zubda hawaye, Mamy ma haka kana Jannart da yake kwance lib a cinyarta kamar"

"matacce, itama hawayen take tsiyayarwa."

"Abba kuwa habarsa ya tallafe, saidai kallo daya zakayi masa, ka karanto tsananin tashin hankalin dake"

kwance akan fuskarsa.

"Ganin hakanne kuma yasa, zuciyar Ramadan wani irin harbawa, lokaci daya kuma gaba Waya jikinsa ya"

"fara tsuman tashin hankali, dan su a zatonsu Rayyern din ya rasu ne."

Cikin wani irin tashin hankali rauni gigita da kuma kidima.

"Riyyam-nsra ya saki wani irin raunataccen kuka, tare da zamewa ya zauna a™asa ya kife kansa bisa sawun"

"Rayyern, cikin rauni murya na rawa kuka na danne abinda yake faWa yake cewa."

" Innallahi wa innailaihi rajiun Mammy mutuwa zata hanani cika miki burinki,"

"Wayyoooooooo Allah na Mammy na inama kina kusa kizo kiga halin da tsatsonki yake ciki, Mammy wlh"

shine wlh sune .

"Su Abba kuwa, tsananin tashin hankalin da suke ciki, yasa gaba Waya basa iya fahimtar kalaman Riyyam-"

"nsra, asalima basa jin me yake faWa da kyau."

"Sai dai shi kuwa Rayyern da tunaninsa ke kokarin gushewa, a sama sama yake jiyo kukan yaron, da kuma"

abinda yake faWi.

"Duk da bawai yana fahimtar kalaman sosai bane, amma yaji wasu daga cikin maganganun, wanda"

ayanzu baya cikin Lfy da kuma hayyacin da zai iya nazari ko hasashen kalaman.

"Dr Sulaiman ne ya matso kusa da Riyyam-nsra, ya jawoshi jikinsa ya zaunar dashi tare da cewa."

" Kai Riyyam-nsra kabar kuka bafa rasuwa yayi ba, ciwon ne ya fara lafawa kaga Abbanku ma yayi shiru ."

"Sai alokacin Ramadan ya sauke wani irin numfashin daya, sakar masa da wani nannauyan abu mai kama"

da dutse daya tsaya a ™irjinsa.

Sabida gaba Waya ya fara rasa numfashin sa.

Shi kuwa Riyyam-nsra cikin kasa danne kukan sa yace.

" Yah Sulaiman, da gaske kake Hamma Rayyern dina, yana numfashi? ."

"Kai Dr. Sulaiman ya jinjina, kana cikin sauri yace."

" Eh Riyyam-nsra bai rasuba gashi yana numfashi, nanda y an mintuna zai tashi insha Allah. "

Ajiyan zuciya suka sau™e baki Wayansu.

Sai lokacinne kuma Mamy ta iya tsaida hawayenta.

Yayinda Baba MauWo Kuwa sam hawayen shi ya gaza tsayuwa.

"Hakan kuwa shi yasa Jannart ta gaza tsaida hawayenta, saboda acikin rayuwar ta akwai rauni sosai,"

"matukar zata ga hawayen Babba, To Lallai zuciyarta saita karye, ba kuma zata iya lallashin kanta ba."

"Ganin duk sun d an nutsu ne kuma yasa, cikin sanyi Dr. Sulaiman ya samu ya zauna, tare da d go kansa"

ahankali yayi gyaran murya kana anutse yace.

" Kwata kwata abun bai wuce 30mnt da fara mishi ba, domin tun da ya fara mishi na fahimta, saboda"

"naga yana ta haWa zufa, kasancewar alokacin muna cikin meeting ne da sauran Doctor's din mu,"

"Akan wani course da muke son wasu daga cikin Doctor's Win namu suje suyi a Mascow,"

"So dana fahimci cewa, ciwon cikin nasa nason tashi ne, sai na bukaci da mu tashi taron, amma sai yaki"

"bani dama, to kafin mu gama ma abin har ya fara tsanan ta. "

"Idanu duk suka tsurawa Dr. Sulaiman din, saboda Jin abunda yake fad a."

"Shikuwa Dr. Sulaeman gyara zamansa yayi, tare da fuskantarsu, cike da son sake samar musu nutsuwa"

yace.

" Insha Allah Rayyern zaiji sauk i, domin muna fita a meeting din nayi masa allura, saidai kafun nan ma"

"tuni abin ya gama tashi, shiyasa ya Wan wahal dashi amman Alhamdulillah, bayan 50mn idan alluran ta"

"fara aiki zai dan ji sau™i, wanda kuma zuwa yanzu inada yakinin, fara aikin allurar Dan shiyasa ma kukaga"

yayi shiru jikin ya daina bari.

"Cikin gamsuwa Ramadan da Abba suka gyaWa kai, saboda wannan bayanine da likitocin suka saba yi"

"musu, sudai fatansu shine samun saukin Rayyern din."

"Baba MauWo dake zaune kuwa, ahankali yasa hannunshi ya shafa kan Rayyern din zuwa wuyansa."

Kana ya mi™e tsaye.

Tare da sharce hawayen sa.

Cikin tausayawa yace.

" Toh Alhamdulillah Allah ya bashi lfy yasa zakkan jikine, Allah ya daga kafadunsa. "

Ya ™are mgnar yana nufar hanyar fita.

"Cikin sau™e numfashi Riyyam-nsra da Ramadan suka bishi da ido, da kuma wani kallo mai cike da wani"

irin so na musamman.

Abba da Mamy kuwa.

Numfashi suka fesar tare da cewa.

 Amin ya Allah baba MauWo .

Shi kuwa Baba MauWo yana fita

"Hadi da Ari sukayi kanshi, cikin girmamawa da kwarjinin dattijon suka hada baki wurin cewa."

 Allah rene ya jikin nasa? .

A hankali yace.

 Alhamdulillah jiki da sau™i.

 Allah ya kara sauki.

suka had a baki wajen fad a.

Shikuwa Baba Maud o.

 Amin ya Allah .

Yace yana mai wucewa cikin Wan side Winsu.

Kai tsaye Bathroom ya wuce al'wala yayi kana yazo.

"Ya dauki Kur'ani ya fara karatu wai ko zaiji sanyin zuciyarshi, da wani nauyi daya danne mishi ™ahon"

zuciyarshi.

"Amma ina hakan ya gagara,"

Hawaye kuwa tamkar an bude bakin famfo.

"Allah ya sani yana jin wani irin azabebben son yaran a zuciyarshi,"

Baya son gani ko jin duk wani abu da zai cutar dasu duk kankantarshi da yanada hali da ko kuda bazata

sauka kan Rayyern ba.

"Da ya dauka kawai dan kyautata mishi da sukeyi ne, kuma dan kasan cewarsu yaran uban gidansa."

"Toh amman zuwan Riyyam-nsra yasa ya fahimci, kawai yana son duk wani abinda ya shafesu ne."

"Wasu lokutan yakanyi tunanin ko dan kamar da Riyyam-nsra din, yakeyi da Rayyern ne yasa yake masifar"

sonshi ma din.

Hannun shi ya daga sama yana mai yiwa yaran addu'a.

A nan cikin falon kuwa.

Shiru Jannart tayi ta sunkuyar da kanta ™asa.

Yayinda hawayenta keta kwaranya ba ™a™™autawa.

"Tana ciwo amman bata taSa ganin irin wannan tashin hankali a fuskar Daddy, kamar yadda ta gani a"

fuskar Baba MauWo da Abba ba.

Bata taSa ganin makamancin gigitar da Mamy tayi a fuskar Mom ba.

Duk da tasan mom tana masifar sonta.

Wannan kawai ya isa shaidar son uwa da banne a duniya.

Mamy kuwa numfashi take ta saukewa kawai.

Riyyam-nsra kuwa mi™ewa yayi ya haura sama.

Yana shiga kuwa ya kira Mammyn sa.

Abba kuwa cikin sau™e numfashi ya tallabe haba.

Tare da cewa.

 Ramadan dagashi a kanta.

Sai ka gyara mishi kwanciyarsa .

Cikin sauri Dr Sulaiman yace.

 A'a Abba barshi shida kanshi zai tashi in allurar ta gama ratsashi.

Cikin sanyi Mamy tace.

 Ai kuma Jannart din zata gaji .

Kai ya dan juya tare da cewa.

 Bazai dadeba zai tashi .

Shiru sukayi.

Kana shi kuma Dr. Sulaiman mi™ewa tsaye yayi tare da cewa.

 Toh Abba ni bari in wuce gida anjima zan dawo.

 Toh mun gode Dakta .

Abba ya faWa yana mai gyara zamanshi.

Shi kuwa Dr Sulaiman Ramadan ya kalla tare da cewa.

" Kasan idan ya tashi zai tashi ba ™arfi illar alurar kenan, shiyasa ba'a cika son yawaita yiwa mutum itaba."

"Zaijishi duk ba ™arfi, so dole sai an taimaka mishi ka sani ."

Kai Ramadan ya jinjina tare da cewa.

 Eh na sani .

Daga nan ya sallamesu ya tafi.

"Su kuwa, shiru sukayi suka zauna jugum-jugum."

"Ganin kuma yamma lokacin daura girki yayine, yasa Mamy mi™ewa a hankali ta nufi Kitchen."

Bayan ta cire lallenta ne kuma ta fara aiki.

Ita kuwa Jannart gaba Waya ta kasa kwakwaran motsi.

"Sabida masifar kunya da nauyin Abba da takeji, kana ga kuma nauyin zaratan namiji dake kanta."

Wanda agaba daya rayuwarta bata taSa fuskantar makamancin hakan ba ga wani irin masifeffen

"™amshin jikinsa dake narkar da jikinta, tattausan sumar kansa da sajensa ta zuwa idanu."

Yanzu kusan 50 minutes kenan suke a hakan.

Yayinda kuma har yanzu hawayenta ked an disowa kadan-kadan.

Suna mannewa ajikin gashin idanunta.

Shi kuwa Rayyern dake kwance a hankali ya Wan ja numfashin wahala tare da fesar dashi.

"Kana ya rumtse idanunshi da ™arfi tare da taune lips Winshi, duka biyu saboda so yake ya tashi, amman"

gaba Waya jikinshi daga kugunsa zuwa sawun takawarsa sunyi lakwas.

Wannan abun shiyasa baya son allurar.

Dan muddin akayi mishi ita sai yayi kusan mako guda karfinsa bai dawo dai-dai ba.

Da sauri Ramadan ya matso kusa dashi.

Dai-dai lokacin kuma Riyyam-nsra shima ya sauko ™asa.

"A tare suka Wan sunkuyo kanshi, ahankali ya buWe idanunshi jin muryar Abba nakiran sunansa."

 Rayyern! Rayyern!! .

Cikin wata iriyar sassanyar murya can ™asan ma™oshi yace.

 Na'am Abba .

"Jin Rayyern din ya amsa ne kuma, yasa Abba cikin jin daWi yace."

 Alhamdulillah! Alhamdulillah!!

Rayyern kuwa cikin ™arfin hali da jarunta ya tattaro ragowar kuzarin sa baki Waya.

Ya yun™ura alamun zai tashi.

Da sauri Ramadan yasa hannunsa zai tallabeshi.

Cikin sanyin murya yace.

 Barni zan iya .

Cike da rauni Ramadan yace.

 Hamma Rayyern bazaka iyaba .

Kar-kar haka jikinsa ke rawa.

Lokacin da ya samu ya juyo ya Wago kanshi.

Da sauri ya rumtse idanunshi ganin kamar kan Jannart yake.

Haka yasa ya mi™awa Ramadan hannunsa.

Da sauri ya kamoshi kana ya yun™ura ya zauna.

Lokacin Mamy ma ta iso cikin jin daWi tace.

 Alhamdulillah sannu ko Babana .

Kanshi ya gyada mata.

Ita kuwa Jannart a hankali ta mi™e tsaye.

Cikin son tsaida hawayenta ta nufi Kitchen.

Tashinta ne yasa Abba matsowa kusa dashi.

Hakama Mamy nanfa sukayi ta mishi sannu.

Ita kuwa Jannart tana shiga Kitchen aikin da Mamy ta fara taci gaba da yinsa.

"Su kuwa A falon cikin ™arfin hali ya maida kansa ya jingina da jikin kujera, kana a hankali ya fara yun™urin"

tashi tsaye.

Da sauri Abba ya tallabeshi gefen damanshi.

Kana Riyyam-nsra ya tallabe gefen hagunshi.

"Ramadan kuwa da Mamy ido suka zuba musu, sunaga yadda yake taka kafafunsa da suke karkarwa."

A hankali suka fara take steps din da taimakon su Abba ya samu.

Suka haura.

Kai tsaye Bedroom dinsa suka wuce dashi.

Suna shiga suka kwantar dashi.

Sanin kuma allurar zata sashi bacci ne yasa Abba juyawa ya fita.

Shi kuwa Riyyam-nsra gefensa ya zauna.

Yana gyara masa pillow.

"Rayyern din kuwa yana kwanciya, lokacin Waya bacci ya fara fuzgarshi."

"Ramadan ko ganin sun haura sama ne, ya sashi fita kaitsaye kuma Mai-nasara pharmacy ya nufa, inda"

yaje ya d auko magungunan da Rayyern din Kesha Idan ciwon ya tashi.

Ita kuwa Mamy Kitchen ta koma nan sukaci gaba da aikinsu ita da Jannart.

Bayan sallan isha'i.

"A hankali Jannart ta dan juyo tana kallon kofar babban falon,"

daga nan cikin falonta.

Da sauri kuma ta mi™e jin muryar mutumin nan da taji ana kiransa da Baba MauWo yana sallama.

Da alamun kuma babu kowa a main falon.

Da sauri ta mike ta nufo falon.

"Baba MauWo Kuma tsaye yake bakin ™ofar, ya Wan turota yana sallama da Wan buga kofar."

A hankali tace.

 Wa alaikassalam Baba ka shigo mana .

Dai-dai lokacin kuma Mamy ta fito daga side Winsu.

Cikin girmamawa tace.

 A'a Baba MauWo ka shigo mana .

Cikin kamala yace.

 Toh .

Kana ya shigo.

A hankali Jannart ta dan rusuna tare da cewa.

 Barka da dare Baba .

Juyawa yayi ya kalleta cikin wani irin mamaki da nazarin fuska da kammanin muryar yarinyar yace.

" Barka dai, Ya mai gidan naki da jikin? ."

Cike da girmamawa tace.

 Alhamdulillah jiki da sau™i .

 Masha Allah. Allah ya ™ara mana sauki .

Ya faWa yana mai juyowa yana kallon Mamy dake cewa.

" Bismillah mu isa yana sama, Abbansu ma yana can ."

Hakan ne yasa ya nufi saman.

"Ita kuwa Mamy juyowa tayi ta kalli Jannart, da idanunta suka dan yi ja cikin kulawa tace."

 Kinyi salla ko? .

Kai ta gyaWa mata alaman eh.

Ita kuwa Mamy.

Ba tare da tace mata komaiba ta nufi Dinning area.

"Foodflask ta Wauko wanda tasa mata,"

"Abincin da sukayi sakwara ce, da miyar agushi."

Mi™a mata tayi tare da plate da spoon tace.

" Gashi ki zauna kici abinci, ki kuma bar zubda hawayen nan haka kinji ko Mamana ."

Cikin sanyi tace to.

Kana ta amshi kular ta wuce Wakinta.

Ita kuwa Mamy Kitchen ta koma tazo ta shiryawa su Ramadan nasu ta kai musu falon sama.

Anan ta samesu.

Baba MauWo da Abba Kuma suna cikin dakin Rayyern Win.

"Ganin har yanzu bacci yakeyi ne, yasa suka fito."

Ita kuwa Jannart ajiye kular tayi a falon.

"Ba tare da tayi niyar ciba, ta kwanta a ™asa bisa carpet din, tana rike da wayarta."

"Sam ta rasa me take tunawa,"

saidai kawai ta fahimci cewa yau gidan babu daWi dan ciwon Rayyern Win.

Sabida su Ramadan masu Webe mata kewa da Riyyam-nsra mai sata farin ciki duk yau basa da Gud Mood.

Tana nan kwance ahaka har tayi bacci.

A folon kuwa suna fitowa suka samu Dr Sulaiman ya iso.

Nan Abba ya koma dashi ya Wan ™ara dudduba shi.

Kana ya sallamesu ya tafi.

Haka dai su Ramadan suka tafi dakinsu.

Mamy kuwa falon Jannart ta le™a ganin tana bacci ne yasa ta wuce side Winsu.

Dan tasan yau Abba a dakin Rayyern zai kwana.

Haka

Hakan kuwa akayi.

Rayyern kuwa baccin yayi mai zurfi sai karfe uku da rabi ya farka.

"Abba da kanshi ya hada masa ruwa yayi wonka,"

Kana yayi al'wala.

"Yana fitowa yayi ramuwar sallan magriba da isha'i, sannan ya dan sha tea Win da Abba ya hada masa da"

kansa.

Toh kuma daga nan sai idonsa ya Wan bushe.

Sai da akayi sallan asuba.

Kafin ya koma wani baccin.

Koda Abba suka dawo masallacin sun sameshi yana bacci.

Nan suka fito.

Mamy da Jannart kuwa Kitchen suka shiga dan haWa breakfast.

Kasan cewar yau Win asabar ce ba aiki.

Yasa Riyyam-nsra da Ramadan ma basu tashi da wuriba.

"Sai karfe tara suka fito,"

d akin Rayyern suka shiga.

Zaune suka sameshi bisa carpet ya jingina jikinsa da gado.

Mamy da Abba ne zaune agabanshi.

Mamy na haWa mishi tea.

Abba Kuma da kanshi yake zuba mishi ferfesun jan nama da Jannart tayi mishi yayi laushi tibis.

A hankali ya Wan juyo ya kalli Radaman dake cewa.

 Hamma ya jikin naka? .

Cikin sau™e numfashi yace.

 Alhamdulillah .

Riyyam-nsra kuwa matsoshi yayi da kyau tare da cewa.

 Hamma Rayyern Mammy ta gaishe ka da jiki.

Zaiton ma tace in gaisheka da jiki .

Cikin sanyi yace.

" Ngd""."

Ganin kuma alamun bai son surutune.

Yasa suka sau™o ™asa.

Abba kuwa cikin kulawa yace.

 Rayyern kaci abincin tunda Wuminsa kaji .

Cikin sanyi yace.

 Abba na gaji bazan iya cin nama da sassafen nan ba .

Da sauri Mamy tace.

 Rayyern yayi laushi sosai fa .

Cikin narke fuska yace.

" Bani tea Win kawai is okay""."

Haka suka hakura suka barshi.

Tea Win yasha.

Kana Abba ya kuma hada masa ruwan wonka yayi.

"Koda ya fito daga wankan, wasu tausassun riga da wondo yasa wanda Abban ya fito masa dasu."

"Mamy kuwa tuni ta sauko k asa,"

"a™asan ta samu su Ramadan da Riyyam nsra a dining area suna zaune, Yayinda Jannart ke zuba musu"

abinci.

Da sauri Mamy tace.

 Kai kun kai abincin su Baba MauWo kuwa?

Kai Riyyam-nsra ya gyaWa tare da cewa.

" Eh Mamy nakai musu, yanzu ma na dawo ."

 To yayi.

"Mamyn tace tare da zama gefensu, nan sukayi Karin kumallon."

Wunin ranar dai haka sukayi shi a gida gaba dayansu.

"Alhamdulillah kuma jikin Rayyern da sauki, sai dai rashin karfi da rashin cin abinci, dama kuma da rashin"

"son mgn da bayayi, dama kuma shi ba gwanin surutu bane, balle kuma yanzu ga halin ciwo."

Washe gari ranar lahadi ma

Haka suka wuni.

"Duk da surutun Riyyam-nsra ya rage,"

saboda jikin Hamman nasa.

Da yamma kuma Nasir Ahmad yazo ya duba Rayyern din da jiki.

"Bayan sun d an taba hira shida Riyyam nsra ne kuma, yayi musu sallama daga nan kuma gidan Malam"

Mai-nasara ya wuce.

Nan yake sanar masa abinda ke faruwa...

Jannart kuwa tun ranar tun lokacin kuma bata sake ganinsa ba ko jin muryarsa.

"Yayinda Mamy kuwa duk a zatonta Jannart din, duk safiya tana zuwa duba jikin Rayyern din."

"Washe gari Ranar Monday Alhamdulillah jikin da sauki sosai, domin karfinsa ma ya Wan fara dawowa."

Bayan sunyi breakfast ne kuma Ramadan ya tafi asibiti.

"Hakan yasa Jannart da kuma Riyyam-nsra, sai kuma Mamy ne ke zaune afalon."

"D ago kai Riyyam nsra din yayi, tare da kallon Jannart dake ri™e da wayarsa, tana kallon comments Win"

followers Winsa akan wata wakar fullancin daya bibiya.

"jin wayar tasa tana ringing ne kuma yasashi kallonta, tare da d an gyara zamansa yace."

 Aunty Jannart Waye .

 Mammy ce .

Ta bashi amsa tana mi™o masa wayar.

Da sauri ya amshi wayar tare da amsa kiran

 Assalamu alaikum yah Mammy .

"Jim ya Wanyi na tsawon kusan da™i™u 2, kana a hankali ya mi™e tsaye tare da fara haurawa sama yana"

cewa.

" Afwan Mamma wlh shine baya son surutu, ko wayarsa bai amsa kira, tun ranar nake son hadaku toh"

ganin baida lfyarne yasa nai shiru .

Ya ™are mgnar yana ida hawa saman.

Kai tsaye dakin Rayyern Win ya nufa da sallama a bakinsa.

A falon kuwa cike da mamaki Mamy ta bishi da ido.

"Zuwa yanzu ta fara tsoron wani al'amarin, to wai ma ya akayi bata taSa tunanin Riyyam-nsra ya nuna"

mata hoton Mammansa ba?.

Tayi wannan tunanin.

"Jannart kuwa da sauri ta juyo ta kalli wayarta dake gefenta, cikin mamaki ta zubawa wayar ido ganin"

number dake kiranta...

Shi kuwa Riyyam-nsra a hankali ya isa gaban Rayyern dake zaune bisa kujera.

Yasa system Win shi a gaba da alamun aiki zaiyi dan yanzu ya buWe ta.

Idonshi ya Wago ya zubawa Riyyam-nsra su.

Shi kuwa Riyyam-nsra cikin karya wuya.

"Da rauni ya iso garesa, murya a raunace yace."

" Ayyah Hamma Rayyern, dan Allah ga waya kayi mgna da Mammy na, tun shekaran jiya take cemin in"

hadaku ta gaidaka da jiki taji muryarka .

Ya ™arashe mgnar yana karya wuya.

Ga mamakin Rayyern kuwa sai ga hawaye na zubowa a fuskar yaron.

Shi kuwa Riyyam-nsra cikin yin rau-rau da ido.

Ya mi™a masa wayar tare da cewa.

 Dan Allah Hamma Rayyern kada kace a'a .

Ya rigada ya gama karya mishi zuciya da hawayensa.

Duk da ko mgnar yayi sai yaji ya gaji shiyasa baya son yawan mgn.

A hankali yasa hannunshin ya amshi wayar.

Cikin nitsuwa ya manna wayar a kunneshi tare dasa kafaWarsa ya makale wayar.

Murya a sanyaye yace.

 Assalamu alaikum .

A can ™asar Ethiopia kuwa.

"Wani irin lumshe ido Mamma tayi, tare da jan wani irin dogon numfashi, kana cikin tsananin harbawar"

da zuciyarta keyi tace.

 Wa alaikassalam MauWo am!!! .

Wani irin rumtse idanu Rayyern yayi da azaban ™arfi tare dasa hannunshi y...!

"*Albishirinku! Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku"

ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA*

NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA.

"Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce,"

"akan ma aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ™ishinsa ta zame masa

Please Login or Register in order to submit comment