google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng ÿþ"[8/14, 11:33 AM] Mss Flower : *ABULLE ANNOBA* "

(Sanadin neman haihuwa)

_Na_

_*Mss Flower*_

_&_

_*Mrs Abdool*_

EJ- 1D' FE-1D' 'DDG E3(

*                                                                    *

& *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* &

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*                                                                        *

"Yarinya ceh 'yar kimanin shekara goma sha biyu tana tafe tana 'ballar rake, hannunta na hagu na bisa kanta tana susar dan da'kwalin kanta dake d'auke da wani kitso wanda har ya 'bace da wuya ka ke gane kan akwai kitson, tsayawa tayi wajen mai gasa kaza, ta jima tana 'kare ma kajin kallo"

"sanan ta dubi wata dan'kwaleliya jajajur tace ""Halliru bani wanan"" ta ri'ke 'kugu tana yatsina fuska"

Idon Halliru daya ciko da 'kwalla ya zubamata yana kallonta

"""Halliru ko bazaka bani ba ne, na wuce"" ta fad'a tana jijjiga 'kugu"

"""A'a Abulle, ni na isa"" ya fad'a yana jawo ba'kar leda ga idanuwansa sun cika da 'kwalla,"

"fuskarnan tamau kamar an masa bushara da mutuwa, kar'ba Abulle tayi ta wuce tana shilla ledar"

"""Allah kayi mana maganin wanan annoba"" Halliru ya fad'a chan 'kasan ma'koshi"

"Abulle da ta wucesa ta juyo ta tamke fuska sanan tace ""Halliru nafa ji ka, ka 'batamin rai wallahi"

"angama cin kazarka a garin nan"" ta 'karashe tana juyawa tana tsalle tsalle irin na yara"

"""Abulle Ina yini"" cewar wani matashin saurayi har yana d'an rage tsayi"

"""Iya gidan uwarka shi kwanan, hege mai siffar ra'kumi"" tana she'kewa da dariya, shi dai bai ce da"

ita komai ba harta yi wucewarta tana cilla kazarta

"Zugar samari neh zasu 'kwallon 'kafa suka wucewa ta inda Abulle ke tahowa, ai ko da Abulle ta hangosu sai ta tsaya ta hard'e hannayenta a 'kirji ta jingina jikin bishiya tana jiran 'karasowarsu,"

"har sun gitta ta tace ""ku kudawo"""

"Aikuwa nan suka fara dawowa suka zo gabanta kowa na fad'in ""Abulle barka da yamma"""

"Idanunta neh ya sauka kan wani saurayi daya murtuke fuska, ai kuwa tace "" d'an Talle kai hala dai"

"kashin shanu uwarka taci matsayin abinci kan a haifeka?"""

"""Uwarki dai"" d'an Talle ya fad'a, ai nan da nan samarin suka fara matsawa daga kusada shi suna ra'bewa gefe. Dariya Abulle ta kwashe da ita sanan tace "" jar uba, dama ance mai cinikin shan zuma, in reshe bai karye dashi ba watarana 'kwarya ta fashe masa, zo nan dan ubanka"" ta fad'a"

tana masa alama da hannu

"Tsaki d'an Talle yayi ya juya ya fara tafiyarsa, aikuwa taku biyu yayi yajisa timmm a 'kasa sanan wata guguwa tayo baya dashi sai gashi gurfane gaban Abulle, 'kafarta mai uban nauyi kamar ta"

doki goma ta d'ora bisa 'kafarsa ai saukaji 'bass

"Kuka d'an Talle ya fara yana 'ko'karin janye sililiyar 'kafar Abulle daga tasa 'kafar amma ya kasa, ya jigata sosae duk ya had'a hawaye da majina sanan Abulle ta d'agasa tace "" zaka kuma neh"" sanan ta yi jifa dashi jikin bishiya, aikuwa ya rushe da kuka itakuma tayi tafiyarta tana tsalle"

tsallenta

"""Abulle an fito, barka da yamma"" cewar wani magidanci da keta faman jan akuyarsa tana tirjewa"

"""Lahiya lau Isiyaku, aikuwa akuyan nan zatayi mai"" Abulle ta fad'a"

"Cikin in ina idanuwansa na kawo ruwa yace "" wallahi kuwa, jiya na kaita asibitin binni aka ceh"

"tanada Corona, shine zan ke'banceta gudun kada ta shafawa mutane"" ya fad'a 'kwalla na zubomasa"

"""Allah sarki, ai waraka ma tazo"" ta fad'a tana tsalle"

"""Iyyehhh!"" Ya fad'a yana 'kwalalo ido"

"""Eh, bari zan ke'bance maka ita a cikina"" ta fad'a tana yashe baki"

"""Abulle dan All """

"Bai 'karasa tayi masa wani mugun kallo, ai sai ya saki akuyar"

"""Toh Allah bamu alheri, Allah i yaye Corona inta shafeku"" ta fad'a sanan ta maida dubanta kan"

"akuya tace "" taho muje"" aikuwa Akuya ta fara binta zungwi zungwi"

"""Hansatu!!!"" Abulle ta 'kwala kira, ai da sauri wadda aka kira Hansatu ta fito tana d'aura zani,"

wadda kallo d'aya zaka mata kasan itace mahaifiyar Abulle

"""Abulle gani"" Mahaifiyarta ta fad'a"

"""Hansatu ungo akuya ki yanka, ki fed'e kiyi mana dabge"" cewar Abulle"

"""Abulle ina kika samo akuya"" Hansatu ta fad'a"

"""Bani akayi"" Abulle ta ansa tana janyo wani daro da shinkafar ciki tayi rabin kwano ta d'ora"

kazarta ta fara ci

"""Abulle sai dai a jira Malam yazo ya yanka"" Hansatu ta fad'a"

"""Hansatu Qur'ani sai kin yankata yanzu"" cewar Abulle"

"Aikuwa Hansatu bata kuma 'bata lokaci ba, ta hau jan akuya qiiiiii......."

Mss Flower & Mrs Abdool

_MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA

SIYAN LITTAFIN NAN_

"*NAIRA 300 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA"

ILMANTUWA*

"_ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS, SAI KIYI SCREENSHOT KI TURO TA WANAN LAYIN 08167888934. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_ SAI MUN JIKU "

"[8/14, 11:33 AM] Mss Flower : *ABULLE ANNOBA* "

(Sanadin neman haihuwa)

_Na_

_*Mss Flower*_

_&_

_*Mrs Abdool*_

EJ- 1D' FE-1D' 'DDG E3(

*                                                                    *

& *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* &

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*                                                                        *

*NOTICE!!!*

"_Bisa ro'kon readers a rage kud'in, toh mun amsa ya dawo *200* sai ku hanzarta kada ayi babu"

ku_

_MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA

SIYAN LITTAFIN NAN_

"*NAIRA 200 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA"

ILMANTUWA*

"_ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_"

SAI MUN JIKU

*02*

"Hansatu ce sai faman jan akuya take, akuya kam sai tirjewa take tana 'ko'karin kada Hansatu da ta"

had'a zufa kashar'bam ga hawaye dake d'igo mata

"Abulle da keta had'ar shinkafa da kaza sai dariya take 'babbakawa kamar ta'babbiya ""Hansatu zata"

"tad'iyeki"" Abulle ta fad'a tana she'kewa da dariya, aikuwa rufe bakinta keda wuya Hansatu ta fad'i sai ji kake timmmmm"

"""Wayyoni wayyo Allah, Abulle kwi'bina ya karye, dan Allah ki rabani da yankan akuyar nan"" ta"

'karashe tana 'bere baki da kuka

"""Hansatu in baki yanka akuyar nan ba, kwarankwatsa kin bar cin nama"" ta fad'a tana sakin"

mahaukaciyar dariya tana buga 'kasa

"Wata yarinya ce ta shigo gidan a guje tana sosa jikinta, zubewa tayi gaban Abulle tace "" ranki ya dad'e yanzu daga gida nake, naji Baba na sanar da Iya wai za'ayi taron malamai ranar juma'a a"

"miki addu'a a rakaki bakin gari"" ta 'karashe tana 'kwalla"

"""Ke Bintalo meye na kuka, sai kace iya korar tawa zasuyi, yanzu ki tashi kije ki kiran shi uban"

"naki da mai gari, kice ina jiransu yanzu"" Abulle ta fad'a"

"""Angama ranki ya dad'e, yawwa wata ya kusan 'karshe ba kud'i a asusu da za'ayiwa ma'aikata"

"albashi"" cewar Bintalo"

"""Haka neh fa, bari nagama da mai gari da ubanki, sai mu fito siyarda maganin mata"" Abulle ta"

fad'a

"""Angama ranki ya dad'e, bari na 'karasa na isar da sa'konki"" tana ficewa"

"""Hansatu bari haka, dawo zauna uwata, ai baki kuka tunda kin haifi Abulle"" ta fad'a"

"Hansatu da zufa suka ji'kata kamar an watsa mata 'karamin bokiti ta zauna tana haki, ta jima kafin tace ""Abulle dan Allah ki daina saida kayan matan nan, wallahi kina zaluntar mata, ki duba wasu"

"fa basuda kud'in siya, ki tausaya musu"""

"""Allah sarki, Hansatu sai ki min bayani, kema kinasan maganin mata na amma bakida kud'i, bari"

"zan baki in aka daka kyauta"" cewar Abulle"

"""Abulle kwarankwatsa ni ba so nake ba, ri'ke abinki Allah kawo kasuwa"" Hansatu ta fad'a"

"""Hansatu Qur'ani tunda kika tanka sai kin kar'ba, na matsi zan baki kuma, in bakiyi ba kinsan"

"sauran"" Abulle ta fad'a"

"Mai gari da tawagarsa tunda aka fad'a masa kiran Abulle suka fito, sun kawo dai dai 'kofar gidan"

"Bintalo ta tintsire da dariya tace "" yau za'a ci 'kwal uba, ba dai korar Abulle zakuyi ba"""

"Mai gari baya yayi yana tangal tangal aikuwa cikin sa'a babbar riga ta tad'iyesa sai kuwa ya fad'i timmm a 'kasa, bai damu da mummunar fad'uwar da yayi ba ya nufi Bintalo yana cewa "" dan"

"darajar Allah waya sanar da Abulle"" duk ya rikice"

"""Zakayi bayani ne"" Bintalo ta fad'a tana shigewa ciki da gudu."

"Mai gari da tawagarsa nan kowa ido ya kawo 'kwalla, haka suka kutsa kai cikin gidansu Abulle,"

"Abulle dake hakimce bisa tirmi ta she'ke da dariya tace "" ko yanzu zaku koran neh?"""

"Mai gari zubewa yayi 'kwalla ta 'ballemasa yana fad'in "" ranki ya dad'e dan Allah kimin rai,"

"wallahi jita jita ce, ba gaskiya ba, kada ki d'auki zigar ma'kiya"" ya 'karashe yana ri'ke sililiyar 'kafarta"

"""Jar uba, ka daiyi nadama amma ba sheri aka maka ba"" Abulle ta fad'a tana girgiza"

"""Iyyehh, eh nayi nadama"" ya fad'a yana fyace majina"

"Sallamar mahaifin Abulle ne yasanya hankulansu ya koma garesa, cikin sauri ya nufi mai gari"

"dake shararar 'kwalla ya zube yana gaishe shi, sanan ya maida dubansa ga Abulle yace "" Abulle mai ke faruwa"""

"""Shirin korata daga garinsa ikeyi"" ta 'karashe tana yatsina"

"""Wa!!, Ni wallahi ban isa ba"" Mai gari ya fad'a yana 'bere baki"

"""Abulle barshi ya tafi dan Allah"" Mahaifinta ya fad'a"

"""Isuwalle zaka kar'ba masa hukuncin ne"" ta tambaya"

"""Miye hukuncin"" Isuwalle ya fad'a"

"""Bulala d'ari ce, aka sosa ta zube"" ta fad'a tana jefa agwaluma baki tareda taunewa"

"Mai gari da idonsa ya kawo ruwa har yana tsiyaya yace "" Abulle ranar da kika min biyar,"

"kwarankwatsa nayi sati ina jinya, ko fada ban je ba"" ya 'karashe da kuka wiiwi"

"""Sharad'i da shawara"" Abulle ta fad'a"

"Cikin sauri ya zabura ya 'kara yowa kusada ita daff yace "" Ina jinki"""

"""Ka kawo zuma farar sa'ka 'kwarya biyu, ka soyomin zabbi bakwai"" ta fad'a"

"""Na amince"" ya fad'a yana washe baki"

"Mi'kewa Abulle tayi tana cewa "" Bintalo jeki kirawo Kandala mu wuce gidan mai gari mu daka"

"kayan mata"" tana wucewarta"

"Karara, ciyawa, da abincin dabbobi had'e da kashin shanu suka samo wanda za'ayi maganin"

mata .........

Mss Flower $ Mrs Abdool

"[8/14, 11:33 AM] Mss Flower : *ABULLE ANNOBA* "

(Sanadin neman haihuwa)

_Na_

_*Mss Flower*_

_&_

_*Mrs Abdool*_

EJ- 1D' FE-1D' 'DDG E3(

*                                                                    *

& *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* &

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*                                                                        *

*03*

"Abulle ce ke tafe yayinda zugar yara 'kidaga guda ke biye da ita a baya, basu tsaya ko ina sai"

gidan mai gari

"""Abulle mun jima ba'asiya mana lemo ba"" cewar Kandala"

"""Ke dan uban bunsurun gidanku ban hanaki fad'in sunana gatsal haka ba"" Abulle ta fad'a tana ciza"

le'be

"""Allah ya huci zuciyarki Iya Abulle"" Kandala ta fad'a idanuna 'kurrr kan Sule mai kayan marmari"

"""Muje a kar'ba"" Abulle ta fad'a"

"Tunde Sule yaga basu shiga gidan mai gari ba sun nufo hanyarsa yaketa zufa, idanunsa ya cika da 'kwalla cikin zuciya sai fad'in "" Allah kasa zawo ya kamata kan ta 'karaso, kai Isuwalle Allah kwashe maka albarka daka haifo wanan jinnun d'iyar, ni ba na hanata ba, ta turan macizai cikin"

"dare su hanani bacci"" 'kwalla na saukomasa"

"""A'a Sule kukan me kakeyi neh"" Abulle ta tambaya"

"""Kayana neh sukayi espaya"" ya fad'a yana rushewa"

"""Allah sarki, lemon ko ayabar"" Abulle ta tambaya"

"""Duka Qur'ani sukayi espaya"" ya fad'a yana hawaye"

"""Bari kuka Sule, kai ku taimaka ku kwashe masa ku rage masa aikin zubarwa"" Abulle ta fad'a, rufe bakinta da wuya yara suka daka ma kayan marmarinsa wawa, wasu na 'kullewa a zani, wasu d'an kwali wasu suka jawo leda. Sule kuka ya dinga rerawa kashar'bam, chan yayi su'bul da baka yace"

"""Allah ya isa"""

"""Mai kace?"" Abulle ta tambaya"

"""Cewa nayi, Allah saka da alheri kun ragen wahala"" ya fad'a yana shasheka"

"""Ba damuwa, duk sanda suka kuma espaya ka kirani"" ta fad'a tana wucewa yayinda Sule keta"

tsinemata a zuciya

"""Assalamu Alaikum munzo sana'a ba sata ba"" Abulle ta 'kwala sallama"

"""Shegiya Annoba, Allah karki ya kar iyayen da suka haifi wanan annobar"" cewar wato tsohuwa"

dake gurza goro bisa tabarma

"Abulle da ta jita tace "" Yagwalgwal ki kiyayeni fa wallahi, tsufa ne yasa nake raga miki"" ta"

'karashe tana 'kwafa

"""Kar ki raga dan butar ubanki"" cewar Yagwalgwal"

"Abulle kallon kaji dake kiwo tsakar gida tayi tace "" ku casamin ita"" tana rufe baki, Yagwalgwal ta mi'ke tana 'ko'karin shiga d'aki har ta kusa santsi ya tad'iyota aikuwa aikuwa ta fad'i kifff, kaji"

"kuwa suka yo kanta kusan su sha wani abu suka hau caccakarta, sai ihu take tana tsinema Abulle"

"Jibgegen tirmin gidan mai gari suka d'auko suka had'a karara da kashin shanu da ya bushe suka hau daka baji ba gani, har sai da ya koma gari, cikin kula suka kwashe sanan suka zuba ciyawa da"

"dusar tumaki nan ma suka dake lu'kwi, sanan sukayi zaman 'kulli"

"""Abulle maganin matan neh, ni dayake inada ragowar na satin da ya wuce sai wani satin zan siya"""

cewar uwargidan mai gari

"""Allah sarki, ai ba irinsu d'aya ba, sai ki 'kara akan wancan"" Abulle ta fad'a tana mi'komata d'auri"

"biyu da na matsi da na sha, hakanan ta kar'ba fuska ba walwala ta kunto jaka hud'u daga zani ta"

mi'kamata

"Abulle ce ta bankad'a d'akin amaryar mai gari dake baccin 'karya, hannu Abulle ta d'aga ta nana mata a cinya, ai a kind'ime ta tashi tayi zaman 'yan bori tana sosa wajen da ya kwaile kamar sabuwar 'kuna, cikin hawaye tace ""Abulle banida lafiya fa, kuma ciki garan mai gari ma baya"

"tarawa dani kinga maganin ba amfani, ga kuma rashin kud'i"""

"""Allah sarki, toh Allah ya raba lafiya, magani kuma ke yafi cancanta ki amsa kyayi gyaran haihuwa, kud'i kuma kya had'a ki bani da na wani satin"" Abulle ta fad'a tana diremata 'kulli biyu"

sanan tayo waje

"Yagwalgwal da keta bori a tsakar gida, kaji na caccakarta har sun janye mata zani, yara sai dariya"

"suke mata, itakuwa sai tsinar Abulle da iyayenta take. Sai da zasu fita sanan Abulle ta cewa kaji "" kai ku barta haka"""

Gida gida suke shiga bada maganin mata........

Mss Flower & Mrs Abdool

_MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA

SIYAN LITTAFIN NAN_

"*NAIRA 200 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA"

ILMANTUWA*

"_ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_ SAI MUN JIKU "

"[8/14, 11:33 AM] Mss Flower : *ABULLE ANNOBA* "

(Sanadin neman haihuwa)

_Na_

_*Mss Flower*_

_&_

_*Mrs Abdool*_

EJ- 1D' FE-1D' 'DDG E3(

*                                                                    *

& *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* &

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writters-Association-111719967001810/?reffer=whatsapp

04

"Gida gida suke shiga bada maganin mata, Abulle ce agaba taci uwar damara kamar zata dambe,"

"kara gyara Dan Kwalin Kanta tayi wanda ya rune sai tsamin dauda yake, turoshi tayi gaban Goshi irin na yan duniya,"

"Gaba tayi zugar yaran daukeda kayan Matan na biye da ita, gidan kusa da na mai gari suka shiga tareda cewa ""salamu alaikum munzo sa'a ba sata ba, jikin matan gidan ne ya hau kerma kamar"

"mazari jin muryar abulle,"

"Kicibus tayi da uwargidan zata cefene Abulle tace ""madallah ga naki"" tareda miko mata kulli biyu"

"na sha Dana matsi, karba tayi badan ranta naso ba tareda cewa ""abulle inada saurafa"""

"""Eh sai ki kara ai, bani nan tafada tareda mika mata hannu"""

"""Abulle banida kudi wallahi wannan kudin cefene ne"" cewar uwargidan kamar zatayi kuka"

"""Ke nide dai na bata min lokaci"" tafada tareda warce kudin dake hannunta tana turawa cikin Zane,"

"Kada kugu tayi tareda shigewa cikin gidan tana ""dije Amarya fito ga naki"","

"Nakurewa DIJE tayi kamar bata nan Don tasan halin Abulle tsab,"

"cikin tsawa Abulle tace ""dallah ziko karba acikin canjin uwar gida ai naira dubu ce na karba a"

"hannunta karbi"" itama aka mika mata kulli biyu,"

"Fita tayi daga gidan tana wake waken ta irin na kauye, Dije kam tsinuwa tabi Abulle dashi har"

tafice tabar gidan.

Next gidan tashiga shima nan saida Asha daga don since sunada saura Amman tace wallahi sai sun

siya haka suka siya badon ransu na soba.

Haka tadinga shiga gida gida tana basu magani suna karba wanda basuda kudi kuma suna karbar

bashi tareda musu gargadin zuwa na gaba zasu biya.

"Sai can da yamma liss bayan Abulle tagama siyarda maganin tass don dama ita bata kwantai,"

"ka'idace Kullum sai ta saidoshi,"

"Washe jajayen hakoronta tayi tana kwance zaninta nan kudi suka Watso kirgasu tayi taga dubu ukku ne, gakuma bashin na dubu daya, dubu daya tacire taba zugar yaran dake mata tallah suka"

"karba suna tsalle tareda mata godia,"

"Bintalo ta kalle Abulle, ""iya Abulle yaushe za'a kuma yin wani""sai gobe Amman kuzo da wuri"

"""to iya Abulle"" suka wuce suna tsalle,"

"Abulle har takama hanyar gida tatuna Idan taje tuwo zata ci kuma gaskiya yunwa take ji, canza akala tayi zuwa gidan mai gari, a zaure ta iske shi zaune da babbar Riga kamar wanzami, wani mugun kallo ta balla mai nan da nan ya zube kasa yana ""Allah y taimaki Abulle wallahi daman yanzu nake cewa azo akaimiki zabin nan tinda nasan yanzu kindawo yawon sa'anar yagama tareda"

"sharce zufar dake tsatssafo masa kamar ankama malam a gidan karuwa,"

"Harara ta kuma zabga masa tareda cewa ""bani su nan"" aguje ya ruga ya dauko kwarya biyu ta farar"

"saka saikuma zabi bakwai, warcewa tayi daga hannunsa tareda kama gaban ta ranta fess,"

"Tana tafiya mai gari yafashe da kukan bakin ciki yana ""Allah y tsine ma hansatu da isuwalle duk sune suka ja mana wannan annobar."

"Wallahi dole mu kashe abulle ina haka bata barin mu muzauna lpia,"

"Gida tashiga ta jawo turmi tazauna tareda kwala ma hansatu kira da gudu ta karaso, turus tayi"

"tareda sakin bakin tana kallon Abulle sai tandar Zuma take,"

"""Ungo wannan soye zakimin yanzun nan Don yunwa nake ji.........."

Mss Flower & Mrs Abdool

_MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA

SIYAN LITTAFIN NAN_

"*NAIRA 200 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA"

ILMANTUWA*

"_ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_"

SAI MUN JIKU

"[8/14, 11:34 AM] Mss Flower : *ABULLE ANNOBA* "

(Sanadin neman haihuwa)

_Na_

_*Mss Flower*_

_&_

_*Mrs Abdool*_

EJ- 1D' FE-1D' 'DDG E3(

*                                                                    *

& *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* &

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*                                                                        *

05

"Hansatu ce dauke da zabin da Abulle tashigo dasu don yankawa,"

"""Ke hansatu guda ukku zaki yankamin ki ajemin sauran hudun gobe zakimin dabge dasu""Cewar"

Abulle har lokacin sai tandar Zuma take kamar sabuwar mayya.

"Guda ukku hansatu ta ware gefe guda, tazuba sauran a wani tsohon keji, nan da nan ta hau yankawa don Abulle tace tayi sauri yunwa takeji,nan ta dafa ruwan zafi tafige tayi tafashe sannan"

"tahau suya,"

"Abulle dake hakimce tana bin hansatu da umurni, zabga wata uwar hamma tayi kamar tsuwar"

"mayyar da ta Kwan bataciba jin kamshin soye yafara gauraye gidan,"

"Isuwalle ne ya kwado uwar sallama tindaga soro, sannan ya karaso cikin gidan, zaune ya iske"

"Abulle kan turmi tana karkada kafa, ""isuwalle Dan karbomin lemo a gun idi mai shago"","

"""wani irin lemo kuma Abulle"" cewar isuwulle yana kallon ta"

"""Wanda kasani kuma kalar baki nan nake so karda ka karbo wanda bashiba kadeji Mena cemaka"""

"tabashi amsa,"

"Babu yanda ya iya haka yanufi shagon idi, tsayawa yayi bakin shagon don takaici duk ya ishe shi, kamarshi da girman shi ace Yarinyarshi tana aike shi cikin iko da gadara Idan kuma mutum baije ba ta Aiko masa macizai suna shi bacci mtswww duk a zuci isuwalle ke wannan maganar, ganin yana bata lokaci yasa yace ""idi Abulle tace kabata lemu baki"" Allah sarki Idi jiki na rawa yace"

"""guda nawa"" ""guda biyu""tace isuwalle yabashi amsa"

"Mika masa yayi harda sakawa a leda sannan ya karba yatafi, yana shiga lokacin kuwa hansatu"

"tagama soye sai kamshi suke,"

"""Juye min a kwanan nan kikawo su nan"", haka ko tayi tadire mata su agabanta, ""to daukomin yajin nan mai tafarnuwa Wanda zanyi Dangwale tareda plate dinda zan saka miki naki, mikewa hansatu"

"tayi don yin umarnin Abulle,"

"Miko mata ledar isuwulle yayi, tako karbe ba sannu bare nagode,"

"Hansatu mikomata yajin tayi tareda plate din, nan Abulle tazabe kawunan da kafafun tasaka musu ""kici keda isuwulle"""

"Isuwulle yace yanzu Abulle Kai zaki bamu, cikeda tsiwa tace ""to daka samu ma nabaka koh, Idan baka ci bani"" tsinto fukafuki tayi tace hansatu ladan suya, karba tayi suka koma gefe, shima"

"isuwalle saboda tsabar kwadai saida yaci,"

"Abulle kuwa 'kasa takoma don taji Dadin cin naman tabude yajin ta tareda balle robar lemu tanaci tana korawa, saida tacinye su tass ta shanye lemun sannan ta saki wata uwar kara alamun ta koshi, gantsarewa tayi ta narko wata uwar gyatsa irin ta yara marasa tarbiya sannan ta Mike ta karkade"

"bujenta tayi da'ka abinta,"

Hansatu ce dake wanke wanken kwanukan da Abulle tagama cin abinci ceh ta saki tsaki tana cewa

""" Allah wadarai"""

"""Ai kece abin Allah wadarai Hansatu, kece sanadin komai tubda ke kika haihota, ni dai tsakanina dake sai dai na ce Allah sakamin"" cewar Isuwalle da ke zaune bisa turmi yana tsotsar 'kafafun"

zabbi

"""Isuwalle ai kaine musababbin komai, da kan na haifeta wani wula'kanci ne bakamin ba kai da danginka, kai ka tasoni gaba dole kasa na kauce hanya kai da danginka"" cewar Hansatu dake"

mi'kewa

"""Yarinyar da kika haifa mana yanzu ai gashi tazame mana annoba, tun shekarar data wuce data karya 'kugun Baaba har yanzu Baaba jinya takeyi, sam ta'ki bani fuskar magana da ita duk saboda abinda 'yarki ta jawo, ni dai kin cucan Qur'ani, ga uban ci kamar gara kullum kusan kwano biyu na hatsi take ci, duk ta 'kararmin da kadara, ga ba'kin jini data jawomin a

Please Login or Register in order to submit comment