google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_"

SAI MUN JIKU

"*YAN NIGER NAKU 300F NE KACAL, KU TURAMA WANAN LAYIN +22795045822, SAI KUYI SCREENSHOT ZUWA WANAN LAMBAR 08167888934*"

"[8/14, 11:40 AM] Mss Flower : *ABULLE ANNOBA* "

(Sanadin neman haihuwa)

_Na_

_*Mss Flower*_

_&_

_*Mrs Abdool*_

EJ- 1D' FE-1D' 'DDG E3(

*                                                                    *

& *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* &

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*                                                                        *

*12*

"Mai gari tagumi ya zabga yana tunanin irin azabar da zaya sha, ta lafiya da ta dukiya in akayi auren nan, a kwanakin nan da zazza'bi yake kwana domin Abulle ta sako shi gaba, cikin dare har zabura yakeyi domin mafarkanta ne yake ta yawan yi tun bayan lokacin da ta fiddashi matsayin"

mijin auranta

"A 'bangarensu masu dukkan Abulle kuma, bayan tayi ligi ligi dasu aka kwashesu kai tsaye kemis aka wuce dasu Yagwalgwal aka fara dubawa kasancewar ita tsohuwa ce, diresin d'in kanta akai mata inda taji mummunan ciwo, sai ihu take a haka aka saka spirit da uban bandeji aka d'ad'daure"

"kan,"

"Ita kuwa Amarya banda kururuwa babu abinda kakeji nata, likitan chemist d'in na duba ta yace"

"""subhanallah baiwar Allah ya akayi hakan tafaru ne, kinga yanzu cikin nan yasamu matsala saura kadan ya 'karasa 'barewa"", wani mahaukacin ihu tasake tareda cewa ""shikenan Abulle kin kashe ni, Yagwalgwal Allah ya isa tsakanina dake duk ke kika kawo mana wannan muguwar shawarar gashi"

"yanzu kin ja min asara wayyo ni na bani na lallace"" haka take ta maimaitawa cikeda azaba"

"Likitan ne ke ta bata baki yana kiyi ha'kuri don Allah, nan da nan aka firda saura cikin aka mata"

"duk abinda yadace,"

"Ita uwargida bama tasan inda kanta yake ba, saboda mummunar karayar datayi a 'kafa an dai samu"

an mata d'ori da 'kyar ankuma shafa mata magunguna.

Maigari dake zaune cikeda jimami duk duniya ya ishe ya kifa uban tagumi sai zufa yake sharcewa

"akai akai,"

"Wani matashi ne ya fad'o fadar Mai gari hankalinsa a mugun tashe sai nishi yake, zubewa yayi"

"yana ""ranka ya dad'e akwai matsala fa, ga iyalinka can a kemis d'aya tayi karaya d'aya kuma tayi 'bari"""

"Mi'kewa Mai gari yayi a zabure yana ""ina kasamu wannan labarin?, suna ina ne?, meya samesu?"""

"ya fad'a zufa na tsatsafo masa saboda tsabar tashin hankali,"

"Matashine yace ""ranka ya dad'e ance sunje dukan Abulle ne shine hakan tasame su"""

"Mai gari zaman 'yan bori yayi tareda rushewa da kuka mai cin rai, nashiga ukku na abulle takasheni, saida nace su kiyayi wannan aljanar yarinyar suka 'kiya, ni kaina suna gani biyayya nake mata na zauna lafiya, amman saboda taurin kai shine suka tafi dukan ta yanzu ga irin ta nan"""

ya 'karashe zancen yana 'kara 'bare baki.

"""Mai gari yanzu ba lokacin maida zance bane muje tukun kaga halin da suke ciki"" cewar saurayin"

cikin muryar lallashi.

"Mi'kewa Mai gari yayi yana share 'kwalla tareda cewa muje, taka babbar rigarsa yayi Aiko ta tad'iyeshi ji kake timmm Mai gari a 'kasa, wani kukan yasake saki yana ""inalillahi wa innailahi"

"rajiun Abulle kashe ni zakiyi nima"""

"Da 'kyar aka d'aga shi suka nufi chemist d'in,"

"Mai gari shi ya biya kud'in sannan aka tattarosu Yagwalgwal aka nufi gida,"

"Mai gari komawa yayi fada ya zuba uban tagumi yana tunani, ""to tinyanzu nafara fuskantar"

"wannan barazanar ai Idan akayi auren ma kila kashe ni zatayi dole akiyin auren nan wallahi ko mai zai faru"" mai gari duk a tunaninsa a zuci yake wannan maganar,"

"A 'bangaren Abulle kuwa ko da ya fad'a mata sonta yake sai ta kece da wata uwar dariya, Mai Indomie kuwa nan da nan idonsa yayi 'kwal da hawaye domin a tunaninsa zata 'ki amincewa da shine. Chan Abulle ta dakata da dariyarta sanan tace "" bari nayi nazari akan wanan batu, ko mai"

"ake ciki zaka jini mai kama da ludayi"" ta 'karashe tana kwashewa da dariya"

*Dr Saddiq POV*

"Sanye yake cikin suit dinsa baka mai masifar kyau, yafito agaggauce kasancewar yakusa makara,"

"Part din mom din yashiga, yagaishe ta samasama, yajuya zaifata,"

"Kallonsa mom tayi tana ""a'a sadiq bazakayi break fast ba zaka fita"" mom wallahi nayi latti ne Ina"

"sauri Idan naje zanyi a can"""

"To ubangiji Allah y tsare Allah y taimaka, ameen Ameen mom nagode saina dawo,"

"Murmushi tayi tana daga masa hannu ""adawo lpia"""

"Kai tsaye motarsa yashiga, aguje ya isa Asibitin, ko parking bai gama ba yafito kasancewar kiran da ake tamasa akan zaiyi ma wata mata aiki,"

Fitowa yayi rikeda brief case dinsa ya nufi office nasa cikin sauri nurses dinda ke ta gaishe sa ma

"saidai kawai yadaga musu hannu ya wuce,"

"Mamakine yakama shi ganin office dinsa a bude, shiga yayi da mamaki cike a fuskar sa yana"

"kallon burdurwar dake kwance kan three sitter dinda ke office din,"

"Cikeda masifa yace "" ubanwa yace kishigomi min office without my permission, kina hauka koh, shin bance kar na sake ganin ki a gun aikina ba, ohh I know u want to tarnish my image koh arinka kallona mutumin banza koh, tunda daman already ke duk wanda ya ganki yasan ba mutuniyar kwarai bace daga kallon shigarki, cos a good lady can never dress to tempt a man, c'Mon get out"

"kafin na bude idona"" ya daka mata uwar tsawar da nikaina saida na tsorata."

"Mikewa tayi da sauri ta dauki handbag dinta tayi waje, ganin yanayinsa zai iya maketa,"

Kwafa yayi tareda saurin canza dressing zuwa na theaterya kwashi kayan aikinsa yafita dasauri

ya nufi thearter room......

*Mss Flower *

&

*Mrs Abdool*

_MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA

SIYAN LITTAFIN NAN_

"*NAIRA 200 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA"

ILMANTUWA*

"_ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_ SAI MUN JIKU "

"[8/14, 11:40 AM] Mss Flower : *ABULLE ANNOBA* "

(Sanadin neman haihuwa)

_Na_

_*Mss Flower*_

_&_

_*Mrs Abdool*_

EJ- 1D' FE-1D' 'DDG E3(

*                                                                    *

& *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* &

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*                                                                        *

"_INA FARINCIKIN GANIN YANDA KUKE SIYAN WANAN BOOK, INSHA ALLAH SAI KUNYI FARINCIKI DA SIYA. MASU TURO ALERT SUYI SHIRU PLEASE KU DINGA MIN"

"MAGANA TUNDA BA SANINKU NAYI BA, SON SO FISABILILLAH _"

*09*

*ABULLE POV*

"""Abulle na ro'keki da Allah ki janye zancen aurena, na fa kusan haihuwar ubanki"" cewar Mai gari"

"da zufa tayi masa wanka, idanuwa sunyi tulu tulu kamar an bad'e da barkono"

"""Tsufanka ba shine damuwata ba, kasan shi so baruwansa da tsufa"" Abulle ta fad'a tana dariya"

"""Abulle mene ne son"" Mai gari ya fad'a yana zare babbar riga domin wani zafi da ya ishesa"

"""A ci abinci mai dad'i, a saka miji aiki yayi yana rawar jiki"" Abulle ta fad'a tana 'ko'karin mi'kewa"

"""Kiyiwa Allah ki za'bi saurayi dai dai ke kuyi aure ku kwashi soyayya"" Mai gari ya fad'a cikin"

tausayin kansa

"""Da kaima zamu kwashi soyayya, kai dai jira daren farko kagani"" Abulle ta fad'a tana mi'kewa"

had'e da dariya mai bayyana jajayen ha'koranta

"Ko da Abulle ta fice wani ihu Mai gari ya saki yana kuka sosai sanan ya tattare babbar rigarsa yayi cikin gida, zaune ya tadda uwargidan da amaryar had'e da Yagwalgwal suna sauraren radio kasancewar wanan 'kayataccen littafin na _(NAMIJI)_ *GUMBAR DUTSE* ake karantawa, Yagwalgwal ta share 'kwallar idonta ta dubi Mai gari daya zamna bisa tudunka ya rafka tagumi"

'kwalla na tsiyaya

"""Mi yake faruwa, ko kaima kukan littafin kake ne?"" ta tambaya, bai amsata ba sai girgiza kai da"

yayi wasu sabbin hawayen suka zubo masa

"""Mai gari, haba kai ba 'karamin yaro ba ka zauna kayita kuka, ka fad'amana damuwarka man"""

cewar uwargida

"""Nima dai shi nagani Yaya"" amaryar ta d'ora"

"""Aure zan 'kara"" ya fad'a wasu hawayen masu mugun zafi suna sauko masa"

"""Mai gari ai abin farinciki ne, hala kukan murna kake ne""cewar uwargida bakinta d'auke da fara'a"

"""Wallahi ba'a isa ba, wanan ma ai tozarci ne, du du du yara nawa na juye da za'a min kishiya,"

"wanan ma ai cin fuska ne"" cewar amarya tana rushewa da kuka"

"Yagwalgwal kam shewa ta saki had'e da rafsa gud'a sanan tace ""Mai gari a 'kara aure, in anyi ta"

"ukun a cike da ta hud'un nan kusa, ai cikar kamalar namiji mata hud'u"" ta 'kare da dariya"

"""Yagwalgwal ai ke na kula kin tsanan, duk wani abu da zai 'batan burinki ayi shi, toh wallahi bari tsinanniyar kishiyar ta shigo taga yadda zanci uwar ubanta nan gidan, wallahi in karya ha'kar'karin"

"yarinya ba damuna za yayi ba"" ta 'karashe tana wucewa d'aki cikin kuka"

"""Ohoo dai, 'yan ba'kin ciki dole d'ana iyi aure tunda Allah ya hore mar"" cewar Yagwalgwal tana"

afa goro cikin baki

"""Iya banisan auren nan ba d'iyar arzi'ki ba ceh"" Mai gari ya fad'a yana 'bare baki"

"""Mai gari wa aka baka hala"" uwargida ta tambaya baki sake ganin yana kuka"

""" *ABULLE ANNOBA*"" ya fad'a yana kuma 'bere baki"

Yagwalgwal wata muguwar hantsilawa tayi aikuwa ta bigi garu (bango) ihu ta sake alamun taji

"zafin buguwar sanan tace ""mi ya kaika neman wanan aljanar, so kake ta 'karasani hala"""

"""Ni kuma ta kasheni da maganin mata"" uwargida ta d'ora idanunta na kawo ruwa"

"""Wai wace jarabar ce ta sanyaka nemanta yarinya ko 'kirgan dangi bata fara ba ga 'yammata nan"

"cikakku amma kace wanan annobar kake so"" Yagwalgwal ta fad'a tana fyace majina"

"""Iya hauka nake zan nemi aurenta, wallahi ita ta neman"" ya 'karashe cikin raunin murya"

"Amarya dake la'be a tagar d'aki ta rafsa gud'a domin tana jinsu ta d'ora da cewa "" Ahayyee ras, wayaga Mai gari angon Abulle, Iya Yagwalgwal za'ayi suruka mai hankali"" ta 'karashe da"

she'kewa da dariyar mugunta

Mai gari daya fusata ya mi'ke yana 'ko'karin cimmata

"Cikin sauri Yagwalgwal ta ri'kesa tana cewa "" barta namiji baya bugun mace sai sauna, ko dan cikin jikinta ai an 'kyaleta, kuma iskancin da take ai Abullen ba 'kyaleta zatayi ba, dai dai take da"

"kowani shege"" cewar Yagwalgwal tana hura hanci"

"""Shine ai"" Mai gari ya fad'a yana shigewa d'aki domin ya 'karashe matse ruwan idonsa"

"""Abulle amma kin iya tsiya, ai labari ya riskeni kin za'bi Mai gari"" cewar Hansatu daga shigowar"

Abulle gidan

"""Hansatu ni fa banason munafunci, mene ruwanki da gwarzona da har za'a zo a fad'amiki"" ta fad'a"

tana yatsina

Hansatu tayi shiru da bakinta sai 'kwalo ido da ta farayi kamar sabuwar mayya

"""Abulle amma dai bikin ba nan kusa ba ko, domin ban shirya ba"" Isuwulle ya fad'a"

"""Chalama!! Isuwulle bikina ai bazaya wuce satittika ba domin kuwa auren nakeso, maganar kaya ka kwantar da hankalinka kwarankwatsa binni zamu da Mai gari iyi mun siyayya"" ta fad'a tana"

zama bisa tabarma tana janyo daron da ake zubamata abinci

Isuwulle kam murna tayi masa yawa jin ba shi zayayi kayan d'aki ba sai washe baki yake kamar

gonar auduga

"""Jar uba, Hansatu!!!"" Abulle ta 'kwala kira, Hansatu da tashige d'aki tana murnar zata rabuda"

ala'ka'kai ta fito tana gyara zanin dake 'ko'karin kunce mata

"""Abulle gani"" ta fad'a"

"""Hansatu dan wula'kanci shine zaki ajiyen tuwo malmala bakwai, wanan kwatan cikina ai ba"

"zaya cika ba"" ta fad'a tana watsa mata harara"

"""Abulle wallahi shinkafar tuwon ce ta 'kare"" Hansatu ta fad'a idonta na kawo ruwa"

"""Ke nawa kika ci?"" Abulle ta tambaya"

""" 'Daya da rabi"" Hansatu ta fad'a"

"""Kutumelesi shine kika ci har haka, meyasa baki ci rabin ba"" Abulle ta fad'a tana watasamata uwar"

harara

"""Abulle kiyi ha'kuri nima ba 'koshi nayi ba"" Hansatu ta fad'a idanunta rau rau"

"""Hansatu wallahi sai kin daka sakwara da miya agushi"" Abulle ta fad'a"

"""Abulle dare fa yayi"" Hansatu ta fad'a idanunta na kawo ruwa"

"""Hansatu toh......"

*SECOND TO THE LAST PAGE*

_MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA

SIYAN LITTAFIN NAN_

"*NAIRA 200 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA"

ILMANTUWA*

"_ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_ SAI MUN JIKU "

"[8/14, 11:40 AM] Mss Flower : *ABULLE ANNOBA* "

(Sanadin neman haihuwa)

_Na_

_*Mss Flower*_

_&_

_*Mrs Abdool*_

EJ- 1D' FE-1D' 'DDG E3(

*                                                                    *

& *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* &

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*                                                                        *

*10*

*ABULLE POV*

""" hansatu toh yama zaayi naci abinci ba nama, ai wannan labarine"" mikewa tayi tareda kada"

"bujenta tayi waje,"

"tafiya tadanyi kasancewar masu kajin dake kusa dasu duk suntashi, tindaga nesa taji wani mahaukacin kamshi na tashi miyau Tahideye tareda karasawa gun mai balangu, gashi kuwa yasha"

"mai sai kyalli yake,"

"Saurin isa tayi wajen tace ""a bani balangu"" tana kada kugu,"

"""Na nawa"" cewar mai balangu, ""jar uba Amman kai bakone agarin halan cewar Abulle,"

"""To kwarankwatse ko kazubamin balangu kokuma na Mayar da shege kashin shanu"" ta karashe"

zancen tana huro hanci

"Mai balangun da dawowarsa kenan da buta a hannu alamun yazagaya jin abinda Abulle tace yace ""haba waya isa ya hana Abulle nama, ai ko na dubu kikeso sai akasamiki"" mai balangu yafada"

"yana kallon Abulle zuciyarsa fal tsoro,"

Yanka naman yashiga yi a jarida saida ya yanka mai uban yawa ya bade shi dayaji yasaka abakar

"leda sannan ya mika mata, ""Allah y kiyaye Abulle"","

"""Ameen"" tace tareda karba tayi gaba"""

"""Tana tafiya mai balangu yafashe da kuka yana Allah ka kawo mana karshen wannan annobar banji ba banganiba nayi asarar dubu biyu, naman dubu biyu Nasaka mata wallahi, yakarshe yana"

"sharce majina"""

"Kallon kaninsa yayi yace ""Dan jakar uba kai Kuma daga zuwa zakamin asarar jalina,wallahi da baka bata ba tsab zata maidashi kashin shanu daga yau Idan wannan aljanar tazo ko me take so"

"kabata shine zaman lpia na"" kanajina koh yafada cikeda kunar rai."

Abulle data tasa uban balangu tanaci tana dangwala yaji saidata cinye shi tsab sannan tabi da tuwo

"malmala bakwai ta sha ruwa tamike, tana sakin gyatsa tareda mika tanufi daki...."

"""Yanzu yagwalgwal kina kallo maigari zai kwaso mana annoba"" cewar uwargidan maigari"

"Cikeda da bacin rai yagwalgwal tace ""dalla rufamin baki ni banfiki damuwa ba, duk gidannan akwai wadda wannan aljanar yarinyar ta raina sama da nine"" yagwalgwal tafada tareda sakin"

"sabon kuka,"

"""Ai yagwalgwal dole musan yanda zamu hana wannan auren inba haka ba babu wanda ya tsira a cikin gidannan dole muci uwar abulle wallahi, bayan wannan ma ai karya ma maigari tattalin arziki zatayi saboda ci kamar gara"" fadar uwar gida tana jawo kwanon shinkafa gabanta kasancewar uwar yunwar dake damun ta don rabonda taci abinci tinjiya da mai gari yazo da"

"labarin auren Abulle,"

"Mikewa yagwalgwal tayi tanufi dakin amarya, bakincikine ya turnuketa ganin barcin ta kawai take"

"kwasa, waje taje ta dauko botiki cike da ruwa tana zuwa ta sheka mata,"

"Afirgece ta miki tareda cewa ""abulle kimin rai don girman kiyi hakuri,"" shekewa yagwalgwal tayi"

"da dariya tana ""ai ba Abulle bace, tashi dallah jaka kawai, Idan zaki ajiye wannan jakin kishin ki"

"ajiye shi don bashine gabankuba ku nemi hanyar cin uban Abulle shine zancen, Amman saboda"

"hasara shine kike barci,"

Mikewa tayi jikin ta tsamo tsamo sai rawar sanyi take tabiyo yagwalgwal

"Numata turmi tayi tace zauna nan, kallon uwargida tayi sannan ta kalli Amarya tace ""inada shawara ku saurareni, kunajina kutashi yanzu muje gidansu Abulle muci uwar uban ta kawai Inbahaka ba auren nan ba makawa kuma kunsan bani kadai zanci ubana ba harku don haka kutashi"

"kunsan ance sarkin yawa yafi sarkin karfi"""

"""Yagwalgwal kina ganin wannan shawarar tayi kuwa ni wallahi tsoron Abulle nan nake"" cewar"

"amaryar maigari idonta yayi raurau yana shirin kawo ruwa,"

"""Ke dalla ja can matsoraciya ai Abulle don taga Anan tsoronta shiyasa take iskanci dataga dama,"

"dallah kutashi,"""

Mikewa kowace tayi tashiga taciwo uwar damara sukayo waje ya gwalgwal ce gaba matan mai

"gari na biye da ita,"

"Hankada kofar gidansu Abulle sukayi suka shiga, hansatu suka gani duke tana ma Abulle wanki,"

"Uwar gidan mai gari cikeda balai tace ""ke hansatu Ina wannan aljanar diyar taki, saboda raini wai maigari shine gawaninta mu saointane Iye yau zamuga uban da ya tsaya ma Abulle take iskan cin"

"dataga dama. "" ta karashe zancen tana girgiza cike da balaie,"

"Yagwalgwal ce ta Dora da "" yarinya yar ficika tabi ta addabi kowa ta yau saida akwashe"

"kasusuwan Abulle"" itama tana wani huci kamar zakanya,"

"Hansatu ce tafara kwalla tana ""Dan Allah kumin rai ku kyalemin Abulle in dan mai gari saita"

"Janye Amman ku kyaleta. """

"Hansatu bata karasa taga Abulle tsaye tana kallon su, kallon hansatu tayi tace ""share hawayen ki"

"uwata ga Abulle nan"""

"Yagwalgwalce tafara matsawa baya ganin idon Abulle yafara canza kala zuwa ja, Amarya kam"

"tuni takai kofa ma, ganin su Ya gwalgwal sunyi gaba yasa itama uwargida tabi bayansu tana ""yarinya tajanye ko muyi maganin ta ehe,"""

"Har sunkai fita Abulle tayi wani gurnani nan da nan guguwa ta bade gunsu yagwalgwal baka ganin komai sai kura, Banda kururuwa babu abinda ke tashi, can na hango yagwalgwal iska ta"

"wancakalar da ita gefe guda Kanta yabugi garu nan da nan Jini ya balle,"

Ita kuwa amaryar me gari can talulu saida tayi sama sannan takifo kasa cikinta ya bugi dutse nan

"da nan tafara burgima tana ""wayyo cikina"" Banda Jini babu abinda ke malala,"

Uwargida kuwa haba ai can bayan randa aka lalubota ko magana bata yi sai kafarta dake lilo

"alamun karaya,"

"Hayaniya tasa makwafta suka cika gidansu Abulle Amman ba mai bakin cewa komai sai ido,"

"wasu maza ne suka kawo ma su ya gwalgwal dauki aka nufi chemis da su,"

"Abulle kam ko ajikinta illa ma fadar mai gari data nufa tana murna, tana zuwa tace atara mata"

"mazan garin,"

"Babu bata lokaci kuwa kowa da kowa ya hallara, kallon bainar jamar tayi tace kusan dalilin wannan kiran gaggawar"" hada baki sukayi gun cewa ""a'a "" to ni Abulle na tsaida ranar Aure na nan da sati mai zuwa nida angona mai gari akan sadaki dubu hansin"" takarshe zancen tana Washe"

jajayen hakoronta

Tuntsirewa mai gari yayi akan Kujerar sa yana fashewa da wani Sabon kuka.......

*DR SADDIQ POV*

"Umma ce zaune gaban Abba, ""uhmm dande kar ace nayi ma Dan kishiya sharri Dana fadi wani abu amman abun yana damuna Kullum dashi nake kwana"" tafada tana share hawayen karya a"

habar zani

Abba ne yace safiya kinga banson haka kifada mana ai saddiq dankine kema Idan kinga yana abu

ba dede ba sai ki Kwaba masa

"""Ina na isa uwarsa ta daure masa gindi yayi son ransa, nayi magana ace na tsane shi saboda ban"

"haife shi"""

"""Yanzu Ina jinki me sadeeq din yayi ne?"""

"""Yanzu Alhaji sai ace sadeeq, kamar danda da ka Haifa kaduba kamalar ka da mutuncinka a garinnan Amman ace sadeeq wai mata yake kwasowa yana kawowa gidannan har da rana tsaka, nayi masa magana yanunamin ban Isa ba shine nace gara nafada maka kayi masa aure kawai shine"

"mafita"" tafada tana barkewa da wani Sabon kuka"

"Cikeda kidima Abba yace ""wani sadeeq din wai """

*Mrs Abdool* &

*Mss flower *

*LAST PAGE*

_MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA

SIYAN LITTAFIN NAN_

"*NAIRA 200 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA"

ILMANTUWA*

"_ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_ SAI MUN JIKU "

"[8/14, 11:40 AM] Mss Flower : *ABULLE ANNOBA* "

(Sanadin neman haihuwa)

_Na_

_*Mss Flower*_

_&_

_*Mrs Abdool*_

EJ- 1D' FE-1D' 'DDG E3(

*                                                                    *

& *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* &

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*                                                                        *

*11*

"""Abulle na ro'keki kada a sanya wanan biki nan kusa, na rantse da Qur'ani sumuni sittin ban gama"

"shiri ba"" cewar Mai gari idanu sun kad'a sunyi jajawur"

""" Mai gari wai ni shirin me zakayi, kayi lefe ghana masigo d'aya sai kayan d'aki da kud'in shagali"

"fa sun wadatar ka bar tada hankalinka kan abinda bai kai ya kawo ba"" cewar Abulle tana washe"

baki

"""Abulle a d'aga dai dan darajar Allah"" Mai gari ya fad'a"

"""Gaskiya aure nakeso dan haka baza'a d'aga ba"" ta fad'a tana gaba yayinda ta bar fadar Mai gari"

jugum jugum

"Tafiya take tana tsallenta duk inda ta ratsa ana zubewa ana gaisheta ta zagi wanda takeso, ta amsa"

"wanda taga dama, ta ya'bawa wanda tayi ra'ayi magana, har ta kai gidan kallo"

"Mazan da sukayi dafifi suna kallon Indiyan Hausa ganinta ya sanya suka fara matsawa domin ta shige, tana zama aka nuno wani scene inda wani actor yayi kissing actress d'in, nan 'karatan suka hau ihu alamun abun ya musu dad'i, Abulle ce ta yafito wani saurayi dake kusa da ita a d'arare tace"

""" kai meyasa ya cijeta kuma aka saka ihu, ko muguwa ce?"" Ta tambaya"

"""A'a budurwarsa ce"" ya bata amsa yana sunkuyar da kai"

"""Jar uba! Kuma ya cijeta, wayaga Mai gari ya cizan za'ayi bura uba"" ta 'karashe tana she'kewa da"

"dariya, maida kanta tayi kan majigin sai kuma taga macen na dariya abin ya kuma d'aure mata kai ta yafitosa"

"""Kai, wai ya zai cijeta maimakon ta kwad'a masa mari irin na fim d'in ranan sai tayi dariya"" ta"

tambaya

"""Ba cizo bane, soyayya ceh"" ya bata amsa"

"""Hehehe wallahi har na hango ina gantsarawa Mai gari cizo ran da aka d'aura aure"" ta fad'a tana"

she'kewa da dariya

"Bayan Abulle tagama kallonta ta taho komawa gida, idanunta suka sauka kan Mai Indomie,"

'karasawa tayi wajensa

"""Abulle barka da dare"" ya fad'a yana mata wani

Please Login or Register in order to submit comment