You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya cicciko gaba daya.

“Muje kiga su Ya nabeela .”

Tace tana jan hannun nata, suka fito falon. Da sauri Ya nabeela ta taso ta tare ammyn a hanya ta karaso da ita falon suka zauna tana kallon ta

“Nabeela ta, kece kika sauya haka?”

“Nice ammy.”

“Masha Allah, Allah abun godiya.”

“Ina wuni ammy? Ya jikin kuma?”

“Alhmadulillah, an gode wa Allah. Sannun ku da kokari Kunji? Allah ya saka da allhairi.”

“Amin Ammy.”

“Ina maigidan naki ina yaran?”

“Duk lafiya kalou, yaran sun tafi islamiyya.”

“Masha Allah, Allah Ya raya su. Zan ga jikokina ashe, Masha Allah.”

Yadda ammyn take furucin kasan zuciyar ta a karye take, dauriya ce kawai amma ji take kamar ta fashe da kuka, musamman idan ta kalli yadda Raihanan ta, ta girma sosai, ba a gaban idon ta ba, sai dai a yadda ta ga yanayin su dukka suna cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali. Hakn ya sakata kwantar da hankalin ta. Abinci Raihana ta zuba mata taci, tana cin su Hydar suka shigo tare da Dadah, Abby da Babbo Sadeeq, Adda maimuna da Muhammad da Amina. Nan fa falon Ya kaure da murna Dadah ta rungume Ammyn a jikinta suka fashe da kuka me cin rai, Abby kuwa kamar an dasa shi a wajen idanun yaran da kasantuwar Dadah a wajen ya hanashi zuwa ya rungume matar tashi, sai kallon ta kawai yake, tana nan da kurciyar ta da kyan jikinta da ya santa dashi, sai da suka nutsu sannan sai Dadah ta tuno da Abby yana falon. Sai kuma duk kunya ta kamata, suka shige daki baki daya har su Ya nabeela suka bar ammyn a falo tare da Abbyn.

“Aisha!”

Ya kira sunan ta cikin wani yanayi na son gasgata abinda yake gani din.

“Naam.”

“Ashe rai kan ga rai? Ya Allahu ya rahmanu, nayi bakin ciki nayi kuka da na samu labarin babu ke, nayi tunanin yadda rayuwar yaran nan zata kasance babu mu dukkan mu, sai Allah ya nuna mana ikon sa, na gane ba wayon mu ko dabarar mu bace, komai da kowa yana karkashin kulawa da ikon Azza wa zalla.”

“Haka ne, ni kaina nayi mamaki yadda yaran suka zama. Alhamdulillah!”

“Alhamdulillah, Allah ya duba mu, yayi mana abinda bamu taba zato ba, duk kuwa da zaluncin da akayi mana. Wannan kadai be isa mutum ishara ba?”

“Ya isa!”

“Ya bayan rabuwa?”

“Alhamdulillah! Abinda kawai zan iya cewa kenan.”

“Toh Alhamdulillah! Alhamdulillah!”

Yace yana murmushi. Murmushi tayi itama, ta kasa misalta abinda take ji a zuciyar ta!


***Ya dade sosai a Office din sai da ya tabbatar ya kusan gama komai sannan ya raba sabbin mukamai wadanda yake tunanin zasu iya kula da company idan baya nan. Yaso ya saka zainab dan tasan Aiki sosai amma kuma yana so ya fara nuna mata matsayin sa domin be yi sanyin da har zata fice tayi tafiyar ta haka kawai ba. Wake ya fito rike da takardar ya tara su a dakin da suke yin meeting baki dayan su sannan ya shiga yi musu bayanin sabbin mukaman na rikon kwarya daya bayan daya, sai da ya gama dasu sannan ya bar office din ya wuce side din da Adam yake kula dashi nan ma yayi irin abinda yayi a dayan sannan ya bar office din gaba daya. Office dinsa ya wuce ya shigar da abubuwan da zai shigar ya gama ya fito sai ga kiran Lawwali. Parking yayi a gefen hanya ya daga wayar da sauri amma sai yaji muryar sa a dan tashe

“Ya akayi Lawan?”

“Akwai matsala alhaji, matar nan ce take ta hauka da ife ife wallahi, tamkar ma ta zare ne ko menene wallahi bamu sani ba mun samu mun dai rufe ta a daki amma muna ji yadda take hauka tsaf zata iya balle kofar.”

“Subhanallahi! Me ya sameta?”

“Wallhi Allah bamu sani ba, bayan mun dauki maganar nan ta jiya bata ko nemi fitowa ba saboda tsoro, yau dai Ladi ta je ta kai mata abin kari da safe har sunyi magana ma, dazu kuma kawai ina kwance dakin zaure naji wani irin ihu, na taso da gudu na shigo gidan kawai sai ganin ta nayi suna kokawa da Ladi har ta shake Ladin tana kakari.”

“Yanzu zaku iya kula da ita zuwa safiya? Zaku iya?”

“Toh wallhi abun ne akwai tsoro, ina jin yanzu haka yadda take kokarin bude kofar, idan muka bari ta bude zata fice ne.”

“Kuma kuna ganin ba pretending take ba?”

“Naam?”

“Oh sorry, kuna ganin ba karya take ba?”

Idan lafiya lafiya, bata isa taja da Ladi ba.”

“Toh kuyi kokarin kula da ita, zan yi kokari na shigo gobe da safe in sha Allah, tunda mun samu abinda muke so cigaba da rike tan ma babu wani amfani.”

“Toh shikenan, Allah ya kaimu.”

“Amin, idan wani abu ya taso ka sanar dani kuma. “

“In sha Allah, Nagode.”

“Nima Nagode.”

Be tashi motar ba yayi shiru yana tunanin abinda yake faruwa, ganin ba zai samu amsar tunanin sa ba yasa shi hakura ya tada motar ya dauki hanyar main house dinsu. A waje yayi parking ya dan abu kawai zai dauka ya wuce, ya kashe motar ya fito ya nufi gate din, kafin ya karasa yaji alamun taku a bayan sa,


🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹





**RQ**

Page 64

***Juyowa yayi da sauri sai ji yayi an kwala masa abu akan sa, kara yayi wadda ta jawo hankalin gateman din yayi saurin fitowa a daidai lokacin da wanda ya kwala masa abun ya ruga da mugun gudu, bin sa gateman din yayj amma kfin ya cimmasa ya haye wani machine suka bar layin, da gudu ya dawo wajen da Aryan din yake rike da kan nasa da yake fidda jini sosai,rike shi yayi da sauri ganin jira na neman kayar dashi ya shiga dashi cikin gidan da gaggawa, tasowa su Bob sukayi da gudu suka tare su, suka taimaka masa aka saka shi a mota Malam yahya da Bob suka dauke shi zuwa asibiti dan tuni har idanun sa sun rufe ruf. Asibitin da suka saba zuwa suka je suna zuwa drs suka karbe shi direct suka wuce dashi theater room aaka shiga kokarin tsaida jinin sannan aga yanayin wound din da yake kan. Sosai suka same shi domin sun fasa masa kan mummunar fasawa kuma ya zubda jini sosai ba kadan ba, dressing wajen akyi masa bayan an masa alluran rage Zafin ciwon sannan aka tura shi zuwa dakin da za’a kwantar dashi.

Sanda suka zo asibitin Dr Mahfouz baya nan yaje duba ammy, dawowar sa asibitinn kenan ya tarar da abinda Ya faru da Aryan din, zuwa yayi ya duba shi duk da har lokacin be farfado ba sannan ya fito ya koma gefe ya kira Kamal dan sanar dashi abinda yake faruwa tunda Alhaji baya gari.
Ganin kiran Dr Mahfouz yasa Kamal ya dakata d abinda yake yi domin yasa magana ce me muhimman ci zai yi masa. Da sallama ya daga wayar suka gaisa a mutunce sannan yace

“Sir kana gari ne ko kana wajen aiki?”

“Ina wajen Aiki Dr, akwai abinda ake bukata ne?”

“Eh toh, dama Aryan ne!”

Tsaye ya mike chak cikin yanayin tsoro yace

“Me ya samu Aryan din?”

“I think thugs ne suka yi masa rauni akai, wanda yayi sanadiyyar sun ji masa deep wound a kan masa…”

Da sauri ya katse

“Yaushe? Aina? Garin yaya? Subhanallahi!”

“Yanzu aka fito dashi an samu nasarar tsaida jinin kuma he’s stable now, but akwai bukatar ayi masa scan domin mu gano how deep ciwon yake.”

“Yanzu kenan abun ya faru? Waye ya kawo shi asibitin?”

“Daga gida ne kamar, naga driver da wani, but su chan gidan nasa I don’t think sun san me yake faruwa, cox daga chan nake na duba Hajiya Aisha, and banji wani magana akai ba.”

“Basu sani ba, ya Allah! Shikenan Nagode Dr, za’a zo daga gidan yanzu, duk abinda ya kamata ayi kawai, zan shigo gobe in sha Allah.”

“Ok ba damuwa.”

Zagaye dakin Kamal ya dinga yi hankali a tashe, ya ma rasa abinda zai yi, wa zai kira wa zai gayawa? Baya so hankalin raihana ya tashi amma dole ne a sanar da Ita, amma ba yau ba, sai dai zuwa safiya Kila ya farfado lokacin. Lamido ya yanke shawarar kira kawai, lokaci suna tare dukkan su a falon suna hirar yaushe gamo, Dadah da Raihana suna daki suna hirar su suma Amma rabin hankalin raihanan na wajen Aryan musamman da taji shirun yayi yawa, lokaci lokaci tana duba wayar ta tana ganin time. Ganin dai shiru jiran ba zai yiwu ba sai ta fito da niyyar kawo ma su Ammy ruwa ta shiga kitchen ta kira shi amma no answer, dauko ruwan tayi da juice ta fito a daidai lokacin abby na cewa zai tafi hotel ya kwana ba zai kwana a gidan nan ba, Lamido ma yana cewa shima daga chan zai wuce da asuba zai koma wajen aiki,ajiye ruwan tayi ta koma kitchen din ta dauko cups Kamal ya kira Lamido, suka gaisa sannan ya sanar dashi abinda yake faruwa,

“Subhanallahi, yaushe hakan ta faru? Yanzu ina Aryan din?”

Tsayawa tayi chak bata karasa kitchen din ba jin an ambaci sunan Aryan,

“Ok ok, Yanzu zamu je in sha Allah, Allah ya bashi lafiya.”

Ji tayi kafarta na neman janta zuwa kasa, da sauri ta dafe kitchen din tsoro na shigar ta, menene ya same shi?

“Wai wasu wanda ba’a san su waye bane suka kwala masa abu a Kansa,Yanzu haka yana asibiti ma.”

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, toh Subhanallahi, abinda ya samu Aryan din kenan? Allah sarki Shiyasa shiru be dawo ba ina taso na tambaya .”

Ammy tace cike da alhini.

“Yaron nan yana bani tausyai, wallahi yasha wahala sosai ya kamata ace zuwa Yanzu ya huta.”

“Hutun ya zo ma Abby in sha Allah!
Sadeeq, Hydar ku tashi muje.”

“Nima dole zanje ai, muje tare.”

Abby ya mike dan be ga zaman me zaiyi ha kuma.

“Ku duba shi dan Allah, Allah dai yasa ba Wani serious abu bane.”

“Toh Amin, amma yadda naji muryar Kamal.”

“Dan Allah Hamma Nima zan je.”

Raihana da ta fada kamar wadda aka tunkudo basu ji zuwan ta ba sam sai maganar ta.

“Auta ki barsu suje kinji.”

“A ah Ammy,mace da mijinta a hanata zuwa ganin shi? Dauko hijab dinki.”

Kallon Ammy tayi itama sai ta kalle ta, sai kuma Wasu ahubuwan suka shiga dawo mata a dan zaman da tayi dasu na kwana biyu, babu wanda ma ya tabo maganar auren raihanan tunda suka zauna. Kasa magana tayi har raihana taje ta dauko Hijab dinta tabi bayansu da sauri Dadah ta biyo bayanta tana bata baki. Suna fita ammy ta kalli Dadah

“Dama auta an mata aure Dadah!”

“Eh, an mata wallahi, babu wanda yayi miki magana r ko? Abubuwa ne da yawa sai a rasa abinda ma zaa fada, sai a hankali komai zai dawo daidai.”

“Ikon Allah, lallai shekaru sun ja.”

“Kwarai d gaske, sai dai muyi fatan gamawa lafiya.”

“Tafiya zamuyi Dadah, gwara na koma gidan Maimuna akan na zauna anan, ashe nan din gidan su ne, jaira dana tambaye ta sai cewa tayi gidan sa ne?”

“Toh zata ce miki an min aure ne ammy?”

“A ah, da Amma ai sai ta bani haske, mu jira su dawo gaskiya gwara na koma chan, ba zan kara kwana anan ba.”

“Toh mu jira su din, Allah yasa yaron kalou yake, yaro me hankali da nutsuwa kai.”

“In sha Allah zai samu lafiya.”


****Kuka take a boye a motar Hydar na jinta tunda shine a kusa da ita, tabo ta yayi ta kalle shi Ya girgiza mata kai, cikin kasa da murya yace

“Ki daina kuka.”

Share hawayen tayi da bayan hannun ta Amma still wani yana sakè zubowa, tsoron ta daya kar wani abu ya same shi, bata san yadda zatayi da rayuwar ta ba. Ko da suka isa asibitin tsoronta karuwa yayi har sai suka shiga dakin da yake, drip ne a hannun sa yana kwance sambal sai dan jinin da ya bata masa jikin rigar sa kadan sai ciwon dake kansa. A baya ta tsaya tana cigaba da kukan har suka gama duba shi suka fita zuwa wajen Dr. Karasawa tayi gaban kujerar dake gaban gadon ta zauna tana kallon fuskar sa da tayi ja sosai, hannun ta tasa ta gyara masa hannun da drip din yake jiki yadda zai dinga shiga sosai kamar ya dan taba shi, sannan ta goge masa gefen bakin sa tana cigaba da hawayen. Tana zaune suka dawo dakin ta tashi ta matsa gefe Dr Mahfouz ya sake duba shi sannan yace zai tashi zuwa safiya Amma dole sai an zauna an kula dashi da duk moves dinsa kafin safiyar idan an ga wani unusual abu a kira nurse.

“Tunda ga amarya ma ai nasan zata kula dashi sosai.”

Ya kara she maganar da sigar tsokana tana kallon raihanan

“Ko Hydar ya zauna.”

Lamido yace,

“No a bar matar sa, zata kula dashi ai.”

Abby yace yana matsawa wajen kofa,

“Toh amarya sai d safe, ki kula dashi sosai please, duk da dai nasan va ma sai an fada va.”

“Muma tafiyar zamuyi, sai da safe Kanwata, Allah ya bashi lafiya.”

Lamido yace sannan ya fita, sallama Abby sukayi mata da Hamma hydar Abby yace tasa Key a kofar karta barta a bude sannan suka tafi.
Locking kofar tayi ta dawo ta zauna a gabansa tana kallon sa, ta dade a zaune sai ta mike ta shiga toilet din dake jikin dakin tayo alwala ta hau kan dan madaidacin carpet din dake dakin ta dora dan kwalin ta akai ta tada sallah, isha tayi sannan tayi shafai da wutri tayi masa addua sosai sannan ta zauna jigum tana kallon sa daga in da take zaunen.
Yadda taga rana haka ta kusan ganin daren domin ko bacci barawo be iya sace ta ba, sau biyu yana motsa wa idan ta rike hannun sa sai ya sauke ajiyar zuciya ya cigaba da baccin. Daf da za’a kira asubah ta sakè yo alwala tazo tayi raka’atanul fajri sannan ta hau saman sofa din ta dan kwanta tana facing din gadon nasa.
Da safe gateman ya fito sai yaga karamar waya a kasa, hannu yasa Ya dauka ya kunna ta, sai wani tunani yazo masa, ko dai wayar wanda ya kwala wa Aryan abu ne? Ciki ya koma ya dauki wayar sa ya kira Kamal lokacin har ya dauko hanya ma, ya sanar dashi abinda ya cinta, ajiye ta yace yayi sannan sukayi sallama.
Wajen bakwai da rabi Ya nabeela ta iso hankalin ta a tashe, sai a lokacin Kamal ya fada mata aikuwa tasha kuka tun kafin ta karaso tana zuwa ta rungume Raihana kafin ta karasa tana kallon yadda ya sauya a lokaci daya

“Ba zai yiwu ba, kuzo ku bar kasar nan raihana, rayuwar shi suke nema gwara ku tafi, zan kira Daddyyanzu,nasan Ya samu sauki sosai gwara ya dawo kawai, ayi muku Emergency Visa ku tafi, wannan masifar har ina?”

“Su waye suka yi masa hakan ?”

“Ban sani ba Raihana, amma Kamal yana hanya, zai kuma binciko ko su waye, kuma sai sun fuskanci hukunci. Amma tabbas ba zaku zauna ba, gwara ku tafi kafin su kassara shi, gashi da naci da kafiya idan ba tafiya yayi ba Shima ba hakura zai ba.”

“Allah ya bashi lafiya.”

“Amin Amin, Dr din sun shigo?”

“Wata nurse ta shigo da asubah, tace Dr Mahfouz zai shigo anjima kadan.”

“Ok.”

Ta zauna akan sofa din tana ciro wayar ta dan kiran Daddy din.


.

*
*RUMBUN QAYA🔥

*DAUDAR GORA*🔥

*IDON NERA*🔥

*A RUBUCE TAKE*🔥

*KI KULANI*🔥

*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊

*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*

*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*

*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️

*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*

*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*

*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

0022419171
Maryam sani
Access bank

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+227 90 16 59 91

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥


🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾😂😂😂




***RQ***

65

***Ta jikin tagar dakin Ladi ta zura kanta ta leka, tana tsaye a tsakiyar dakin duk ta yaga kayan jikinta kanta a barbaje tana ta jansa da karfi sai ta cizge shi, gwalalo ido Ladi tayi cikin tsoro ta juya ta samu Lawwali a dakin zaure zaune yayi tsuru dan baya jin zasu samu damar yin bacci a ranar.

“Gashin kanta take cizgewa fa.”

Tace masa tana rike hab’a cikin alajabi

“Akwai matsala ,Allah yasa ba abinda ta dade tana aikatawa bane ba ya dawo kanta.”

“Shi din ne ma, karshen shegiya ne yazo, mummunan karshe dan daga gani haukan nata babban ne, Allah yasa ba na yawo bane tsirara Innalillah.”

“Yanzu ya zamuyi? Na kira shi dai yace zai shigo da safe.”

Kafin ta bada amsa sai ihun balle kofar suka ji, sannan suka ji har ta fito tsakar gidan. Kusan gware sukayi da Ladi da Lawwali wajen fita daga gidan gaba daya, dan sun tabbatar ta zo ta cimmasu zata iya lahanta su. Suna fita ta karaso zauren a guje tana ife ife, tayo waje duk da duhun da garin yayi, ta yi gaba kawai tana tafe tana ihu da surutai tana jan gashin kanta, kusan minti goma suna labe jikin wata danga, sai da suka ji shiru suka fito zuwa lokacin tayi nisa ma, dan kamar iska haka suke kada ta, hanyar suka dan bi Lawwali na haska musu touch light dinsa amma babu alamun ta, dawowa sukayi kawai suka koma cikin gidan suka kulle cike da tsoron kar ta dawo musu cikin dare.
Gajeren bacci suka yi a daren ranar da sun ji motsi sai su fito. Da gari yayi shaa suka dan sake fita neman ta tare da Malam sani Amma babu wani alamun ta ko in da tayi, dan ko sahun kafafunta babu a hanyar sam.

“Ko dauke ta sukayi?”

Ladi tace

“Wa ya sani ne,lallai sharri dan aike ne, kuma komai daren dadewa sai ya dawo duk kuwa in da ka aike shi, ji sakayyar Allah.”

“Yanzu menene abun yi?”

“Mu jira zuwan sa, duk abinda ma ya kamata ayi idan yazo din sai ayi.”

“Toh, Allah yasa ma ta tafi kenan, shegiyar mata jiya da ta shake ni wallahi na hango lahira, kai nasha azaba ba kadan ba.”

“Ai karfi ne dasu.”

“Naga alama.”

Juyawa sukayi suka koma gidan suna tattauna abinda ya farun.


*****Tashi tayi ta fita bayan sun yi magana da Daddy, tayi dana sanin fada masa abinda ya faru da Aryan din dan ya rikice sosai sai da ta kwantar da hankalin sa sannan ya hakura yace ta hada shi da Mahfouz din, a office ta same shi yana dora labcoat dinsa akan kayan sa, zai taho dakin Aryan din. Gaisawa sukayi ya tambaye ta me jiki sannan tace

“Daddy ne zakuyi magana , bari na kirashi.”

“Ok.” Ya zauna akan kujerar sa ta kira Daddy din ta bashi sukayi magana,yayi masa bayanin abinda ya faru.

“Muna tunanin going for MRI or CT scan muga ko akwai internal injury ko bleeding.”

Ya karkare bayanin

“Wanne zaifi?”

“CT scan is faster that MRI, but za dai mu duba tare da colleagues dina muga abinda zaifi.”

“Please just do the needful Dr, zan fara ganin yadda za’a yi processing komai within a week, sai su wuce, na dade dama Ina binsa yazo ya samu doctors anan musamman akan severe headache din nan nasa.”

“In sha Allah zamuyi iya kokarin mu kafin su wuce din.”

“Nagode Dr, thank you very much.”

“You are welcome sir.”

“He’s so worried, naji a muryar sa.”

Yace ma Ya Nabeela yana mika mata wayar

“Nayi regretting sanar dashi nima.”

“No dole ne ai, but in sha Allah ba wani serious case bane da zai fi karfin mu, dan dai yana so su tafi din ne kawai, but anan ma we can handle it.”

“Dama da akwai plan din tafiyar tasu, suje ya huta sosai abubuwan sun yi yawa.”

“Haka ne, nasha fada masa nima yana bukatar hutu, ko maganin sa baya samu yana sha yadda ya kamata, Shiyasa har bugun ma ya samu tasiri sosai akan sa.”

“Yanzu tunda yana da mata dole ta sashi ya sha ko baya so.”

“Yes zata sashi, bari na ga Dr Fredrick sai mu shigo dakin nasa.”

“Ok Dr, mun gode.”

Ta tashi ta fita. Ammy da Dadah sun karaso asibitin sun duba shi sai suka fito waje suka zauna duk da dakin babba ne kuma vip ne, zuwa Ya nabeela tayi suka gaisa suka yi mata ya mai jiki sannan ta shiga dakin. Raihana na zaune a gabansa, hannun sa cikin nata ya rike ta kam tun dazu tana so ta tashi amma bata so ta zare hannun sai ta hakura kawai ta zauna a gaban gadon tana gadin sa. Ya nabeela na shigowa tayi saurin cewa

“Ya rike min hannun ya hanani tashi.”

“Me Ya faru Raihana? Kunya ta kike ji ko? Karki ji komai Aryan yana bukatar kulawar ki fiye da kowa a yanzu, take good care of your husband kinji? don’t be shy.”

Nodding kanta tayi tana sakè yin kasa da kanta

“Tafiya zakuyi, za’a yi masa scan aga komai daga nan zaku bi daddy New Zealand.”

“Ok.” Tace a hankali

“Bari naje wajen su Ammy.”

Juyawa tayi suka yi kichibis da su Dr Mahfouz, ta matsa musu hanyar suka shigo ta fice ita kuma

“Madam ya patient dina?”

Dr Mahfouz ya tambaye ta yana kallon drip din hannun Aryan din

“Alhamdulillah,ina kwana?”

“Lafiya lou, wanne ne drip na nawa da aka saka masa.”

“Uku, tace idan ya kare ba zaa saka wani ba.”

“Ok.” Ya taba gefen wuyan Aryan din

“He looks stable akan jiya, I hope he regain his consciousness very soon.”

“In sha Allah.”

“Dr Ahmad me kake gani?”

“I think we should go for the CT scan din.”

“Ok, Madam wannan shine Dr ahmad, head neurologist na kano gaba daya, zamu yi ma oga scan na kai saboda mu san iya in da ya samu injury, ba wai wani babban abu bane as baya ma daukar wani babban time,.”

“Ok, Allah ya bada sa’ah, ya bashi lafiya.”

“Amjn ya Allah, zasu zo su tafi dashi.”

“Ok, mun gode Dr.”

“Yawwa.”

Suka fita, ta dawo wajen zaman ta. Ta sakè rike hannun nasa tana kallon sa a marairaice, hawaye ne taji yana zubo mata ta yi saurin share wa bata so wani ya shigo ya ganta, Amma har ga Allah zuciyar ta a kusa take, ji take kamar ta zauna tayi ta kuka, daga wannan sai wannan su kenan? Shigowa nurses din da zasu tafi da Aryan din sukayi, tayi saurin mikewa tana goge fuskar ta, suka dora shi akan gadon da zasu tura shi suka fita dashi. Da sauri ta shige toilet ta rufe ta shiga rera kuka yadda ba zaa ji ta ba.
Ammy ce ta biyo ta cikin jin bata fito ba, bata dakin ta karasa kofar toilet din ta kwankwasa

“Auta?”

“Umm!”

“Ok Kina ciki.”

“Umm.” Ta sakè cewa dan bata so tayi magana ammyn ta gane kuka take. Fuskar ta, tayi saurin wankewa sannan ta fito tana goge fuskar. Kallo daya ammy tayi mata tasan kuka tayi

“Addua zaki masa auta, ba kuka ba.”

Ai kmar wadda take jiran kiris sai ta sakè rushewa da kukan ta fada jikin ammyn, a kalla yanzu itama kamar sauran masu iyaye ne, zata yi kuka a jikin mahaifiyar ta har ta rarrasheta.

“Ya isa toh, kar kizo ciwo Ya kamaki kema, ki kwantar da hankalin ki kinji? Zai samu sauki in sha Allah.”

“Babu abinda zai same shi ko Ammy? Ya sha wahala sosai wallahi, shine kuma ya gano in da kike yayi risking life dinshi for my happiness, bana so wani abu ya same shi.”

“Babu abinda zai same shi, amma sai kin daina kuka, kin zama strong kinji? Kiyi masa Addua.”

Gid’a kanta tayi, ammyn ta share mata hawayen ta sata sakè wanko fuskar ta goge ta sannan suka fito wajen da su Ya nabeela da Dadah suke zaune.


****Ba karamin gudu yayi ba, har Allah ya sa ya iso lafiya, shi kansa be san ya iya taka mota haka ba sai ranar, sanda ya iso an shiga dashi scan din, gaisawa sukayi da kowa Ya nabeela ta taso suka shiga ciki ganin yadda idanun sa suka yi ja babu walwala ko kadan a tattare dashi

“Kamal, ka ganka kuwa?”

“Na gaji ne Ya nabeela, hakuri na Ya kare, an kaini karshe wallahi.”

“Na sani, but dole mu zama strong, for Aryan, yana bukatar mu a wannan lokacin.”

“An samu wayar daya daga cikin yan iskan, tana mota na zan wuce station zan duba

Please Login or Register in order to submit comment