You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tamkar yadda kikayi a Yanzu.”

Wani irin murmushi tayi, ta kada kanta kadan sannan tace

“Mu zuba dan halak ka fasa, sai dai ina me baki shawarar karki kuskura ki bari na wai wayo ki,ki tsaya a in da na ajiye ki karki tsallake limit dinki.”

“Bana bukatar shawarar ki.”

Sai ta juya ta fice daga gidan. Shiru zeenat tayi bayan fitar ta, ta tabbatar akwai dalilin furucin ammyn, dan haka ba zatayi kasa a guiwa ba, sai ta binciko abinda ta taka. Wayarta ta daga cikin yanayin bacin rai ta danna kira, ta tsaya tana jijjiga kafa da dan sauri sauri tana jiran a daga wayar. Yana dagawa tace

“Follow her.” Sai ta katse kiran ta maida wayar handbag dinta ta fito tana daidaita kanta ta koma cikin gidan ta samu Daddy a tsaye jikin motar suna magana da Moses, bude mata kofar Driver yayi ta zauna sannan daddy ya shiga shima yana tambayar ta ina ammyn.

“Ta tafi.” Kawai tace masa bata sakè cewa komai ba, be kuma tambaya ba shima suka fita daga gidan.

*****Zuciyar ammyn a chunkushe ta tari abun hawa, gidan da ta sauka ta nufa tace me napep din ya jirata, kayanta kawai ta dauka amma sai tayi mantuwa ta bar jakar da ta dauko a dakin Abbyn suka dauki hanyar tasha dan bata jin zata sake kwana a kano. Tayi nisa sosai a tunani har me napep din ya dauke hanyar da suke kai bata lura ba, sai da yayi tafiya sosai da ita sannan ta Ankara, tayi saurin tambayar sa in da zai kaita, juyowa yayi da nufin bata amsa ya fesa mata wani abu a fuska wanda yayi sanadiyyar gushewar hankalin ta.


****A hankali Aryan yake murza hannun ta kadan kadan yana kallon dan bakin ta karami da yake magana, shirun da tayi ya saka shi jawota jikin sa ya rungume ta tsam tsam duk da nauyin da yake ji a zuciyar sa amma dole ya dake domin yana da bukatar nutsuwarsa. Ta dade lafe a jikin sa tana sauke ajiyar zuciya a jere har ta samu bugun zuciyar ta ya daidaita ta samu nutsuwa sosai. D’ago kanta yayi daga jikin nasa ya tallafi fuskar tata da hannun sa biyu, a hankali ya motsa bakin sa cikin muryar sa da ta shige ciki sosai yace

“Zan dawo da daddare kinji? Sai mu karasa maganar for now ki huta sosai, karki stressing kanki kwata-kwata.” Gida masa kai tayi a hankali ya yi mata perk a gefen kumatunta Sannan ya dan ja mata hanci kadan sukayi murmushi a tare

“Me Ya Nabee take bawa kumatun nan naki? Kamar bread irin bugun katon nan saboda laushi.”

Dariya ta kyalkyale da ita, ya tsaya yana kallon ta cike da zallar kaunar ta me chakude da tausayin ta sosai.

“Dariya tana miki kyau sosai, ni Kinga ban iya ba.”

“Tafi maka kyau ai, tunda dama baka yi so idan kayi sai kayi kyau.”

“Really?”

“Umm.”

“Tam zan dinga yi miki, ke kadai kawai kinji?”

“Banda Zainab?”

“Zainab?” Yace

“Umm ta Office.”

“Ohh..” sai yayi dariya kadan

“Ke da ita toh,sai a raba 50/50.”

Turo baki tayi ta juyar da kanta da jikin ta gaba daya daga kallon side din da yake, murmushi yayi yana jin wani dadi a ransa,ya juyo da ita gaba daya zuwa jikinsa ya matse ta a hankali ya dora habar sa a saman gashin ta dake fitar da wani irin kamshi me ratsa zuciya. Ya dade a haka tana manne dashi tana jin heartbeat dinsa kafin ya dan saketa kadan jin wayar sa na kara alamun kira, ciro wayar yayi ta dan yunkura zata tashi ya hanata ya daga wayar yana makala a kunne.

“Daddy barka da rana.” Yace a nutse

“Alhamdulillah.” Ya furta sai ya dora

“Ya jikin?”

“Allah ya kara sauki, eh in sha Allah ina kan kokarin, duk yadda ake ciki zan sanar in sha Allah, komai lafiya lou. Ok a huta lafiya.”

Sai ya katse wayar ya tura ta aljihun gaban rigar sa

“Yaushe Ya nabeela zata gama shirya min ke?” Ya watso mata tambayar ba tare da ta shirya ba, bata amsa ba sai dan murmushi da tayi.

“Zan fada mata tayi sauri, dan tafiya zamuyi zamu bi su Daddy Ina bukatar na huta sosai, nauyin dake kaina da zuciya ta yayi sauki, ina so na bar komai behind me for sometime, wanda nake fatan komai ya daidaita kafin dawowar mu, just pray for me kinji? Akwai abinda nake son achieving idan Allah ya tabbatar ba ni kadai ba, mutane da yawa zasu samu farin ciki wanda nake da yakinin samun wanzuwar wani shashe na daga farin cikin da muka rasa a baya.”

“Allah ya bada sa’ah ya tabbatar da alkhaiiri.”

“Amin My wife.”

Daga shi tayi ya mike hannayen sa zube cikin aljihun sa, ya dan sake kallon ta sannan ya nufi hanyar da ya saba shigowa don baya son komawa ta falon su hadu da Ya nabeela tayi masa tsiya.
Yana fita ta yi baya ta kwanta a saman gadon wani irin mixed feeling na bijiro mata, koman sa burgeta yake, nutsuwar sa da yadda yake a kame ga wani irin charisma shi yafi komai birgeta a tattare dashi. Yadda yake treating dinta yafi komai tafiya da ita. Wayar ta , ta dauka ta kira Dadah suka yi hira sosai, sannan ta kira Abbyn ta da su Hamma hydar, dukkan su tambayar ta suke ko akwai wata matsala amma sai tace a ah, suna gama wayar duk suka turo mata kudi a tare kamar hadin baki, wai ko zata bukaci wani abun, murmushi tayi cikin farin ciki da yadda yan uwanta suke kokarin ganin sun faranta mata, da kokarin ganin bata yi lacking komai ba tun kuwa da ta taso.

*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*


*ZAFAFA BIYAR BACTH A*


1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350
*(Bilyn Abdul)*


2.. _KAI MIN HALACCI_ 350
*(Miss xoxo)*


3.. _BURI DAYA_ 350
*(Mamu gee)*

4... _DAURIN BOYE_ 350
*(Huguma)*

5... _SAUYIN KADDARA_ 350
*(Hafsat Rano)*

_Duka biyar 1500_

*___________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*


1... _DAURIN GORO_ 350
*(Hafsat Rano)*

2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350
*(Huguma)*

3... _QAUNAR MU_ 350
*(Mamu gee)*

4... _IGIYAR ZATO_ 350
*(Miss xoxo)*

5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*


_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*

1... _MIN QALB_ 350
*(Mamu gee)*

2... _SARAN ƁOYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*

3... _KIBIYAR AJALI_. 350
*(Miss xoxo)*

4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*

5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350
*(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*

1... _ALKIBLA_ 350
*(Huguma)*

2... _DALAAL_ 350
*(Miss xoxo)*

3... _UBAYD MALEEK_ 350
*(Mamu gee)*

4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*

5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350
*(Bilyn Abdull)*


_Duk biyar 1500_

*____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*

1... _SO DA ZUCIYA_ 350
*(Mss xoxo)*

2... _TAKUN SAAKA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

3... _HALIN GIRMA_ 350
*(Hafsat Rano)*

4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350
*(Huguma)*

5... _DEEN MARSHALL_ 350
*(Mamu gee)*


_Duk biyar 1500_

*______________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*

1... _BAKAR INUWA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

2... _RAYUWAR MACE_ 350
*(Hafsat Rano)*

3... _NOOR ALB_ 350
*(Mamu gee)*

4... _MASARAUTA_ 350
*(Mss xoxo)*

5... _KUFAN WUTA_ 350
*(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (COMPLETED)_*

1... _FARHATAL QALB_
*(mss xoxo)* 400

2... _GURBIN IDO_
*(Huguma)* 400

3... _SANADIN LABARINA_
*(Hafsat Rano)* 400

4... _INAYAH_
*(Mamu gee)* 400

5... _BABU SO_
*(Bilyn Abdull)* 400

_Kuɗinsu a yanzu 2K duk biyar_




*_ZAFAFA BIYAR 2023_*🔥🔥🔥
_*Sabuwar shekara sabon salo sabon taku,*_
_*Makaranta littafan hausa kuma masoya marubutan zafafa kuzo ga sabuwar tafiya zazzafa tazo karku bari ayi babuku *_

_*Zafafan alkaluman haziqan maruban zafafa biyar kowa yasan na daban ne,wannan karon ma sunzo da sababbin salo me kama zuciya.*_
_*ZAFAFAN MARUBUTAN SUNZO DA SABABBIN LITATTAFANSU NA 2023 Kamar haka,*_

1 _*IDON NERA*_
Mamuhgee

2 _*DAUDAR GORA*_ ciki ka shata
Billyn Abdul

3 _*RUMBUN QAYA*_
Hafsat Rano

4 _*KI KULANI*_ mallakin zuciyata
Hafsat Miss Xoxo

5 _*A RUBUCE TAKE*_ qaddarata
Safiya Huguma


_DUKA GUDA BIYAR DIN ZAKA SAMESU A FARASHIN 1200_

Guda 5 1200
Guda 4 1000
Guda 3 800
Guda 2 600
Guda 1 400

_*zaku saka kudin a wannan account din👇*_

_*0022419171 Access Bank Maryam sani*_

Saiku tura shedar ta👇

_*09033181070*_

Idan kuma katin Waya ne zaku tura katin MTN ta wannan layin👇

09166221261



TEAM ZAFAFA BIYAR🔥🔥
MUNGODE🙏🙏❤️
**RQ **

*_55_*


*******Hannun sa daya na kan sitiyari dayan na rike da wayar sa yana neman number Hydar, kiran sa yayi ya dora wayar a gefen sa ya gyara zaman AirPod din dake makale a kunnen sa. Line busy yaji alamun waya yake har zai katse sai kuma yaji ya dauka

“Yallabai barka da rana.” Hydar yace cikin rashin sanin dalilin kiran aryan din

“Barka dai, ya gida ya family?”

“Alhamdulillah. Komai lafiya.”

“Masha Allah, please wata yar tambaya nake da ita idan ba damuwa.”

“Ba damuwa, go ahead.”

“Akan maganar ammy ne…”

“Ok… ina jin ka.”

“Yaushe ne ganin ku na karshe da ita, sannan me ya faru a lokacin?”

“Umm, bari na dan fito daga office zan kiraka minti biyu.”

“Ok ba damuwa.” Yace yana tsaida kansa akan titin daidai lokacin da ya shigo cikin layin nasu. Parking yayi a gaban gate din me gadi ya fito zai bude masa gate din yace ya barshi ya dan yi baya da kujerar da yake kai ya zura hannu ya dauko system dinsa a bayan motar ya kunna ta, a daidai lokacin kiran Hydar ya shigo, ya daga yana bada dukkan attention dinsa gareshi, domin akwai wani abu da yake son karasa tattarawa wanda zai tabbatar masa da abinda ya gano.

“Kana jina?”

“Eh ina jinka.” Yace masa

“Ok…”

*TUNA BAYA*

****Tafiya sukayi da nisa sosai kafin ya isa gidan da zai kai ta, bisa umarnin Hajiya zeenat din, a lokacin ammy bata cikin hayyacin ta bacci take sosai me nauyin gaske don sai da suka sauya mata abun hawa daga napep din suka saka ta a mota duk bata sani ba. Kwana uku tsakani ta farfado cikin wani irin yanayi ga wani azababben ciwo da kanta yake yi mata dan da farko kasa gane in da take tayi da abinda yake faruwa, sai daga baya abinda ya faru ya shiga dawo mata, a zabure ta mike da nufin guduwa amma sai taji ta a daddaure, motsi taji a kofar dakin da yake ta karancin haske kasancewar magriba ce, hasken touchlight ne ya dalle mata ido tayi saurin kawar da kanta, kautar ta hasken yayi zuwa wani shashen sannan ta samu damar ganin shi duk da ba tar ba saboda haske tan da yayi.

“Kin farfado kenan, lallai maganin nan akwai mugun karfi na gaske.”

“Ina ne nan?” Tace muryar ta na rawa saboda gano abinda yake faruwa da tayi

“Nan? Baki san ina ne ba ko? Gidan yankan kai ne.”

“Innalillahi wa inna ilahi, Raihana yarana.”

“Tab ai ke da ganin su, sai dai a lahira idan kuna da rabon ganawa.”

“Dan Allah dan girman Allah Kiyi min rai, wallahi yarana basu da kowa sai ni, mahaifin su yana kurkuku dan Allah ku kyale ni na tafi.”

“Tabb, ai kin shigo kenan wallahi. Idan kin ga kin fita daga gidan nan sai dai idan gawar ki ce.”

Sai ya juya zai yayi hanyar fita, magiya take masa tana kuka amma yayi biris kamar be ji ba, ya kai kofar kenan tace

“Toh dan Allah zanyi sallah.”

“Ba dai anan ba.” Yace sannan yayi ficewar sa.

Kukan ta ne ya karu, tabbas akwai matsala gagaruma idan har ta cigaba da zama a wajen, ya rayuwar yaran ta zata kasance? Dole tayi wani yinkurin ganin ta bar wajen. Duhu ya mamaye dakin sosai alamun dare ya fara turawa, babu motsin kowa da komai kamar ma ita kadai ce take zaune a wajen, motsa hannun ta, tayi kokarin yi ko zata iya kwance daurin dake jikin nata amma ta gaza, bata hakura ba ta cigaba da gwadawa duk da bata da yakinin zata iya din. Motsi tajiyo daga nesa kamar suna musu, maganar na tunkaro ta har suka iso kofar dakin sannan suka shigo a kusan tare. Matashin nan ne na dazu tare da wani babba dan zai yi kusan saan su Abby ko ya dara su, bata san musun me sukeyi ba kafin su shigo ta dai ji yana cewa

_”Dole a barta tayi sallah, idan hajiyan tazo kace nine nace.”_

Anan ta fuskanci akan dalilin musun nasu, shi matashin yace ba zatayi ba shine shi kuma yace a ah, da kansa ya karaso ya kwance ta sannan yace ta taso, ta mike da kyar kamar zata fadi dan yadda jikinta yake a sakè kamar zata fadi saboda emptiness din da take ji a tattare da ita hade da wata irin yunwa wadda damuwar da take ciki ta hana ta tasiri a gareta.
Waje suka fito ya samu wata babbar tasa ya zubo mata ruwa ya bata, sai da ta kafa kai ta fara sha sosai har ta kusan shayewa ma saboda tsabar ishirwar da take ji, karo mata yayi tayi alwala bayan ta dan kama ruwa sannan ta koma cikin dakin dan a yanayin wajen da yadda bata jin motsin komai sai kukan tsintsaye ko hanya suka bude mata suka ce ta tafi ba zata iya ba, wani irin waje ne me matukar abun tsoro, tayi mamaki kwarai yadda suka iya zama a wajen sai dai duba da yadda baban yake furta kalmomin sa ya tabbatar mata da bafulatani ne irin na rugar nan wanda suka iya rayuwa a jeji daga su sai dabbobin su. Dankwalin ta, ta cire ta zauna a zaune ta kabbara sallar dan bata jin zata iya yi a tsaye saboda yadda take jin jiri na dibar ta. Ta dade tana jero sallolin kafin ta idar ta kalli kwanon da ya ajiye mata a gefen ta, tana sallar. Jawo shi tayi ta bude sai taga shinkafa ce da mai da yaji, cikin sauri sauri ta hau ci saboda tsabar galabaita batayi tunanin komai ba dan ta riga ta lissafa ba zata yarda ta zauna a gidan nan ba dan haka dole tana bukatar kuzari sosai yadda zata iya tsere musu idan ta samu damar tserewar. Tas ta cinye bata rage komai ba, ta yi hamdala ta gyara dankwalin nata sosai ta kwanta lamo a kasan wajen tana ji aka rufo ta, ta waje tayi shiru tunanin halin da yaran suke ciki musamman raihana da ta kasance karama, bata da alamun yin bacci har dare ya tsala sosai sai kukan sauro da yake tashi kamar ana kada ganga, tashi tayi tunda da alwalar ta, ta cigaba da sallolin ta a tsaye dan dama dazu da rashin kuzari ya hanata yi a tsayen. Har gari yayi sha bata runtsa ba, bata kuma ji motsin kowa ba sai chan zuwa lokacin da rana ta daga sosai sannan taji ana bude kofar. Matashin nan ne ya shigo dauke da kwanon abinci ya dire mata fuskar sa a rufe da bakin abu dama kuma ba gane shi tayi jiya ba saboda babu isahshen hasken da zata iya tantance shi. Fita yayi tayi shiru bata da niyyar daukar abincin bare taci. Sakè rufe ta, taji yayi ya bar wajen chan bayan kusan awa guda taji an sakè bude ta, Yanzu bata d’ago ba tana a zaune a yadda take sai da taji muryar sa ta d’ago suka hada ido.

“Yi maza ki taso, karki bata lokaci har tazo ta same ki anan, zan bude miki hanya kiyi gabas zaki ga wata doguwar hanyar yar siririya kiyi ta binta zata fitar dake har titi, karki tsaya dan daf suke da isowa nan.”

A gigice ta mike tayi hanyar fita suka fita a tare ya fito da ita har waje ta bayan gidan sannan ya nuna mata hanyar da zata bi, zata tsaya yi masa godiya yace tayi sauri. Gudu ta shiga yi na fitar hankali baji ba gani tana gudu tana addua da karfi, ta sha wahala sosai dan sai da taji kamar kafafun ta ba ajikinta suke ba, amma ta daure ta cigaba da gudun har fara hango titin me dauke da motoci yan tsirari, murna ta hau yi ta kara daga kafarta sosai tana jin a ranta ta kubuta har ta karaso titin kanta tsaye ta fada kan kwaltar ba tare da ta duba ko taji karar motar da take shararo gudu na musamman. Shi kansa be lura da ita ba, dan ba hanya ce ta wuce war mutane a kafa ba, dan baya tunanin akwai wani kauye a kusa da wajen saboda hatsarin sa, highway ce dan haka a full speed yake tafiya abinda ya hanashi samun damar taka birki har yayi wani irin tafiyar yaji da ita, ta kwalla kara karar da ta ankarar dashi abinda ya faru.

****Nannauyar ajiyar zuciya Hydar ya sauke kafin yace

“Labarin mutuwar ammmy shine abinda ya taba faruwa damu wanda ya samu a cikin matsanancin tashin hankali, mun sha wahala matuka kafin rayuwar mu ta dawo daidai, munyi kuka tamkar idanun mu zasu rufe saboda azaba, amma Ya zamuyi? Haka Allah ya tsara, abin tashin hankalin shine rashin ganin gawar ta, yafi komai daga mana hankali.”

“Allah ya gafarta mata zububanta, Allah yasa muyi kyakkyawan karshe.” Aryan yace muryar sa a ciki

“Amin.”

“Gobe Friday, zaka iya shigowa kano? Nayi maka booking flight din yamma, idan ka bar Office ka shigo akwai abinda nake son nuna maka.”

“Ok, ba damuwa zan yi kokari nazo.”

“Nagode sosai, Nagode da bani lokacin ka.”

“Babu bukatar godiya,kai dai ka kula min da kanwata, shine kawai.”

“Ko? Zan duba yiwuwar hakan toh.”

“Karka manta dai, kanwar maza ce.”

“Haka kace dai.”

“Haka ne ma, bari na koma Office na bar ayyuka.”

“Ok, sai ka shigo.”

Suka ajiya wayar.

Hoton dake kan system din ya sake budewa sosai, ya kara kallon sa sannan ya fita ya bude dayan, ya tabbatar da dukkan information din daya ne kafin ya kashe system din ya maida ita back seat din ya d’ago kujerar daidai sannan ya kashe AC motar ya kashe motar ya fito rike da wayar sa ta office a hannu dan da suna magana da hydar kiran zainab ya shigo sai dai be daga ba. Kofar jikin gate din ya tura ya shiga gidan ya hangi motar Adam a parking area ya wuce ciki ya shiga falon. Babu kowa kamar ko da yaushe sai tv dake a kunne tana ta fama ita kadai, kashe ta yayi ya kunna hasken falon wanda yake da a kashe sannan ya haura saman zuwa bedroom dinsa. A falon saman ya tarar da Adam yana waya yana daga muryar cikin tashin hankali dan da gaske karamar magana tana neman zama babba babu labarin Hajiya zeenat babu dalilin ta wanda babu wanda yake zargi illa Aryan gashi ya rasa yadda zai masa ya gano wani. Wuce shi Aryan yayi kamar be ganshi ba yayi saurin shan gabansa yana katse wayar. Wani kallo Aryan din ya watsa masa kafin ya giciye shi ya saka key zai bude dakin kasa Adam din ya rike kofar yana tare shi

“Ina ka kai min uwata?”

“Uwarka? Wacece kuma haka?”

“Baka sani ba? Ko da yake ba zaka sani ba tunda ba wai ka wani san dadin iyaye bane ko kuma kasan shakuwar dake tsakanin uwa da danta.”

Kamar an soke shi da mashi haka Aryan yaji maganar, tayi masifar taba shi amma sai ya dake ya fuske tamkar be ji me Adam din yace ba, ya sa hannu ya fincike hannun sa ya hankade shi baya ya shige dakin gami da banko kofar yana jin Adam din na dura duren ashar ya dafe kansa ya jingina da kofar kirjinsa na wani irin harbawa. Ya dan dade a tsaye a wajen kafin ya karasa gaban side drawers dinsa ya ciro maganin sa ya dauki ruwa yasha sannan ya rage rigar jikinsa ya kwanta a saman gadon ya jawo wayarsa ya kunno karatun alkurani me girma yana saurara a hankali nutsuwa na shigar sa tana ratsa shi har ya samu ya dawo daidai.
Kusan awar shi daya a kwance ba bacci yake ba kawai yana sakawa da warware abinda yake shiri yi ne a cikin yan kwanakin nan, yana kuma fatan ya samu nasara. Yunwa ce ta soma nukurkusarsa, baya son sakè haduwa da Adam bare har ya biye masa su yi musayar magana Shiyasa ya dade a kwancen ma. A tunanin sa ya tafi dan haka ya dauki jallabiyar sa me gajeran hannu ya zura akan farar singlet dinsa ya sakko kasan zuwa dinning area, ya samu an jere abincin akan dinning din sai dai babu plate. Kitchen din ya nufa ya bude wajen da plates din suke ya dauko zai fito Kamal ya kirashi sai ya tsaya rike da plate din a jikin sink ya daga wayar.

“Ina ka shiga ne wai?”

Kamal yace yana fitowa daga meeting din da sukayi, a gajiya yake tikis dan ya matsu da kiran Aryan din ne ma Shiyasa amma da kashe wayar zai kawai ya koma ya kwanta dan kusan kwana uku kenan basa samun isashen bacci akan wani case da sukeyi

“Na dan kwanta ne, Yanzu kuma na sakko zan yi lunch .”

“Ok, kunyi magana da Ya nabeela ?”

“Eh munyi, kasan ta. Komai ma abun damuwa me a wajen ta.”

“Dole ne ai, ni kaina na damu din, kawai dan ni namiji ne. Please Aryan Karki yi wani abu, akwai shirin da nake akan case din nan, amma for now don’t make any move.”

“Ok.” Yace a gajarce

“Good.”

“Em akwai abinda nake so dama na fada maka.”

“Ok, ina ji.”

“I think na gano in da Ammy take.”

“Wait what!? Are you serious?”

“Yeah, ba kace I should take over ba, so na gano in da take, kuma na gama planning yadda zamu je mu ganta, ni da hydar.”

“Ku jira ni, zan shigo Sunday sai muje.”

“Saturday zamu je, zai shigo kano gobe sai muje Saturday.”

“Noo ku jira ni.”

“Why? Ba zan iya yi ni kadai ba? Dole sai kazo?”

“Zaka iya, but Inaso nazo nima.”

“Wannan karon dai just allow me please.”

“Aryan?”

“Pleaseee.”

“Ok,ok. Shikenan.”

“Yauwa, Atleast nayi wani abu, Inaso raihana ta kara sakin jiki dani, idan hakan ta faru zata kara yarda dani. Zata yarda ni ma I’m a good person, ba Halin mu daya da daddy ba.”

“Naji naji, don’t change the topic. Na gaji tikis zan je na huta, zamuyi magana anjima.”

“Ok.” Yace ya katse wayar. Da sauri Adam dake makale a jikin kofar kitchen din ya bar wajen yana wani irin murmushi.
_**RQ_**

56


****Katse wayar yayi ya fito zuwa dining ya zauna gami da jawo warmers din ya bud'e ya zuba abincin dan madaidaci ya yi bismillah ya shiga ci a hankali yana danna wayarsa da yake kokarin tura mata sako. Yaci ba laifi dan ba wani breakfast yayi sosai ba ya ture plate din yana mikewa, ya koma tsakiyar falon ya zauna a cikin kujerun falon da ya dade be yi irin zaman ba.

***A firgice ta farka daga baccin da take, ta kwala sunan Aryan dan dama da sunan nasa baccin yaci karfin ta. Ladi ce ta shigo da saurin, ta zura mata ido tana kallon ta kafin ta kurma uban ihu bayan ta lura da in da take. Tashi tayi tana yunkurin kakkabe jikinta saboda wani irin mugun kyankyamin wajen da take da yadda dakin yayi mugun datti.

"Ahe kin farka." Ladi tace tana matsowa kusa da ita, da sauri Hajiya Zeenat ta daka mata tsawa tana kallon ta cikin yanayin kyankyamin tace

"Karki kuskura ki matso kusa dani."

"Aradun Allah sai na matso ki, mune yanzu dangin ki tare damu zakiyi rayuwa."

"Inji uban wa, na rantse da Allah kika sake matso ni sai nasa anyi maganin ki."

"Tab lallai, baki san ma wacece ni ba."

Kallon banza Hajiya Zeenat tayi mata, ta yi hanyar fita daga dakin a fusace, dariya ladi tasa tana gyara daurin zanin ta, ta bita da kallo dan tasan ko kusa bata isa ta zura kafarta waje daga dakin ba. A tsorace ta juyo dakin gami banko kyauren da ya kusa karyewa jikinta na rawa tace

"Menene a waje?"

"Jeki ki gani mana, aradun Allah sai ta cinye ki tas har kashin ki."

"Dan Allah menene? Kamar kura na gani."

"Ba kamar ba, itace wallahi. Kuma an riga na sanar da ita da kin fito tayi kalaci dake."

"Na shiga uku, abinda yaron nan zai min Kenan?"

"Ke kika san shi, kinga tafiya ta gashi nan garin buga kyauren kin kusan balla shi, idan ya karasa ballewa aradun Allah har cikin dakin nan sai ta shigo ta shinshina ki kuma."

Da sauri Hajiya Zeenat ta damke ta ganin zata fita ta barta ita kadai, wani kallo Ladi tayi mata me cike da izgili tace

"Ke da kika ce kar na matso ki, uban mi yasa zaki rike ni?"

"Kiyi min rai, wallahi zan baki kudi, idan har kika taimake ni duk wata matsalar ki ta kau, sai kin zama abun kwatance a garin nan amma dan Allah ki barni na tafi, ba zan iya rayuwa anan

Please Login or Register in order to submit comment