You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ILMANTARWA RAYUWAR MU TA YAU DA KULLUM...


SAFIYYAH HUGUMA
A RUBUCE TAKE (KADDARATA)β™₯️

HAFSAT RANO
(RUMBUN QAYA)πŸ₯°

MAMUH GEE
(IDON NERA)🀩

NANA HAFSATU
KI KULA NI (MALLAKIN ZUCIYA)😘

BILLYN ABDULL
DAUDAR GORA (CIKI KA SHATA)πŸ’—

DUKA DUKA WADANNAN LITTATTAFAN ZASU ZO MUKU NE CIKIN FARA SHI MAI RAHUSA KAMAR KO DA YAUSHE.

DUKA BIYAR DIN AKAN NERA DUBU DAYA DA DARI BIYU 1200

GUDA HUDU AKAN NAIRA DUBU DAYA 1k

GUDA UKU AKAN 800

GUDA BIYU AKAN 600

GUDA DAYA AKAN 400


DADIN DADAWA, MUNA TALLATA HAJOJIN KU AKAN FARASHI ME SAUKIN GASKE! SANNAN GA BIYAN BUKATA


HANYOYIN DA ZAKU IYA TUNTUBAR MU DOMIN ZAMA CIKIN SAHUN FARKO NA WANNAN SABUWAR TAFIYAR SABUWAR SHEKARAR SUNE;




MASU BIYA TA BANKI ZAKU BIYA A WANNAN ACCOUNT DIN


BANK: ACCESS BANK

ACCOUNT NAME: MARYAM SANI

ACCOUNT NUMBER; 0022419171

SAI A TURA EVIDENCE OF PAYMENT HADE DA ACCOUNT NAME TA WHATSAPP TA WANNAN NUMBER;

09033181070



IDAN KUMA KATIN WAYA NE NA MTN SEKU TURO KATIN VTU/SHARE AND SELL KO NUMBER KATIN HADE DA SHEDAR SA TA WHATSAPP ZUWA: 09166221261

FARASHIN LITTTAFAN ZAFAFA BIYAR NA CHANJAWA DA ZARAR AN KAMMALA SU. SAI KU YI SAURI KU GARZAYA DOMIN A DAMA DAKU A WANNAN SABUWAR TAFIYAR SABUWAR SHEKARAR 2023πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ’₯


KU GARZAYO A SAKE DAMAWA DA KU A WANNAN SABUBAR TAFIYAR MAI DAUKE DA SALO NA BAN MAMAKI. KAR KU BARI AYI BABU KU.


DOMIN ZAFAFA BIYAR NA KU NE. 😘🀩
[05/01, 21:53] Billyn Abdul 2: πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

*INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR MAZAUNA K'ASAR NIJER?*🀏🏾

*TO KU MARMATSO KUSA TA SAMU!!*πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ

*MUN SAURARI KOKENKU MUN KUMA AMSA*

*Zafafa biyar dinku sun samo muku hanyar biyan naku kudin karanta litattafan zafafa har guda biyar din*

*ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE*

+22799643131

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

*KUDIN LITATTAFAN ZAI KAMA KAMAR HAKA*

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

*MUNA GODIYA DA SOYAYYARKU GAREMU AL'UMMAR NIJER,MUNA MUKU FATAN ALKHAIRI TARE DA GODIYA BISA ZABIN ZAFAFA BIYAR*πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ

*RQ*

23

*TUNA BAYA*



****Gidaje guda biyu a jere da juna iri daya sak, hatta fentin jikin gidan da na gate din iri daya ne komai da komai. Daga cikin gidajen biyu akwai wata kofa da tayi linking gidajen biyu wanda baka da bukatar fitowa ainahin gate din idan zaka shiga daga wannan gidan zuwa wannan. Fiye rabin rayuwar su a tare suke yin ta shiyasa zaka samesu a kowanne lokaci a taren idan basa gidan wannan toh suna dayan anan suke komai.
Nasir da Ibrahim Aminan juna ne tun daga zamanin kuruciya har kawo girman su har kawo yanzu da sukayi aure har suka samu zuria suna yadda suke babu wani abu da ya taba shiga tsakanin su. Asalin mahaifin su Nasir dan Zamfara ne sai aiki ya kawo shi kano in da suka hadu da mahaifin Ibrahim suka zama abokai ta in da abokantar yaran ta samo asali kenan. Tun daga primary suke tare sai da aka zo university sannan suka rabu in da Nasir ya karanci bangaren law shi kuma Ibrahim ya karanci mass communication. A university din suka hadu da matan su, kawaye ne su uku suma duk da banbancin jahohin da suka fito amma sun zama kawaye sosai. Khadija, Aisha da Zeenatu. Khadija itace yar kano sai Aisha daga Adamawa sai Zeenatu da ta kasance yar kogi state. Duk weekend a gidan su Khadija suke zama sun yi mugun sabon da babu wadda take boye wa wani sirri saboda shakuwa. A haka suka kammala karatun su lokacin har su Ibrahim sun fara business ba tare da sun jira aikin gwamnati ba dan sun kusan shekara uku da gama karatun kafin su Khadija su gama, Nasir dai yana dan zuwa chamber shima ba kowanne lokaci ba, saboda haka basu wani damu da dole sai sun samu aiki ba, suka fara business dinsu cikin ikon Allah komai ya soma bunkasa. Kiwon kifi suka fara Allah ya saka musu albarka a hankali sai suka yi expanding dinsa zuwa babban gidan gona cikin shekara daya komai ya kankama dan ba karamin samu suke da harkar ba, daga nan ne suka fara shawarar aure, tunda already suna da yan matan nasu a hannu. Ibrahim ya auri Khadija shi kuma Nasir ya auri Aisha wanda aka daura auren a Yola Adamawa tunda ita chan ne garin su. Duk shagalin bikin nan da Zeenatu akayi shi musamman da ta kasance babbar kawa kuma aminiya ga amaren dan haka ne ma ya kasance kusan itace akan komai har aka kai amaren gidajen su da suke a manne da juna.
Rayuwa ta cigaba da garawa a hankali lokaci zuwa lokaci Zeenat ta kan kawo musu ziyara musamman idan ta shigo Kano wanda take sakewa tamkar a gidan ta ne saboda babu wani shamaki a tsakanin su saboda yadda suka yarda da junan su, duk sanda tazo suna jin dadi sosai dan ba karamin kirki ne da ita ba haka kuma ta saba sosai da nasir da Ibrahim dama tun a school. Aisha ce ta fara haihuwa ta haifi Namiji wanda nan take Nasir yayi masa huduba da sunan Ibrahim wanda suke ce masa Lamido. Bayan lokaci kadan itama Khadija ta haihu amma sai ta haifi mace ita, aka saka mata Nabeela. Rayuwar su gwanin sha'awa suka cigaba da rainon yaran su har shekara biyu sannan suka sake samun wani cikin a kusan lokaci daya amma wannan karon Khadija ta riga Aisha.


*Mafarin Matsalar su*

Watarana da azumi bayan sun yi sahur nakuda ta tasar wa Khadija, nan da nan suka dunguma zuwa asibiti aka bar Aisha da yaran a gida. Wajen azahar ta haihu ta haifi dan ta namiji, Zeenat a lokacin tana gari dan ta dawo Kano saboda ta fara masters a lokacin dan haka tana jin suna asibiti ta shirya ta tafi tana chan akayi haihuwar itace ma ta fara kira ta fadawa Aisha, nan da nan sai gata nan ta taho ita da Lamido da Nabeela. Daga nan aka sallamo su suka yo gida. A tsakanin gidajen biyu Zeenatu take zama, daga wannan gidan ta koma wannan har ranar suna in da sukayi anko su uku hadda ita, akayi suna gagarumi saboda ko a lokacin business dinsu ya sake bunkasa sosai har sun fara harkar man fetur. Bayan an gama suna mutane sun watse Khadija ta shiga wanka, ta bar Zeenat da Aisha a dakin. Ta dade a ciki sosai tana fitowa ta tarar basa nan dukkansu, ta dauka suna falo sai kawai ta hau shiryawa ta gama sannan ta fito falon. Basa falon babu kuma jaririn sai ta dauki waya ta kira Aisha.

"Ashe kun shiga ciki."

"Eh wallahi, ai kina shiga wanka na dawo na dan gyara gidan, na bar Zeenat dai ko itama bata nan?"

"Eh bata nan."

"Ok kira ta."

"Gata ma ta shigo." Khadija tace idonta akan hannun Zeenat din ganin ita kadai ba jariri

"Kin fito sister?"

"Eh, na zata kuna falo sai naga bakwa nan, waye ya dau Ahmad?"

"Ahmad? Baya dakin?" Tace tana kallon ta. Wani irin faduwa gaban Khadija yayi, ta juya da sauri zuwa dakin Zeenat ta mara mata baya.

Abun daukar sa ne kawai a gadon babu komai, jikinta ne ya hau rawa cikin tsananin tashin hankali suka shiga dubawa, lungu da sako har da leka kasan gado amma babu jinjiri babu dalilin sa. Kanwar Khadija Habiba ce ta shigo daga waje dan suna chan dakin dake compound din basu san me ake ba.

"Habiba kun dau Ahmad ne?"

"A ah." Tace, hannu Khadija ta dora aka ta fara kuka,

"Na shiga uku." Da sauri suka yo waje suka shiga gidan Aisha, tana gyarawa Nabila riga kenan bayan tayi musu wanka ita da Lamido suka shigo a birkice wai basu ga Ahmad ba, nan fa hankalin ta ya tashi itama suka yo waje gaba daya cikin tsananin tashin hankali. Wasa wasa ya tabbata an sace jaririn!

Duk irin binciken da za'a yi an yi, babu jariri babu dalilin sa kuma babu wanda yasan sanda aka fita dashi daga gidan. Iyakar tashin hankali iyalan biyu sun shiga, an kai report din police station amma babu wani labari, haka suka zauna jigum-jigum yadda suka ga rana haka suka ga dare babu wanda ya runtsa.
Tsawon lokaci ana saka ran zaa samu wani abu game da batan Ahmad Amma shiru har suka fitar da rai, Zeenat ko wanne lokaci tana tare da Khadija tana kwantar mata da hankali har Aisha ta haihu babu wani taron suna ko wani abu da akayi dan duk basa cikin nutsuwar su, ta sake haifar danta Namiji aka saka masa Abubakar Sadeeq.
Rayuwar iyalan biyu ta sauya sosai tun bayan batan Ahmad, wanda har lokacin Khadija ta kasa hakura kullum cikin kuka take sosai dan ma Zeenat da Aisha suna kwantar mata da hankali sosai Amma duk da haka abun ya riga ya bar mata gibi me girma a rayuwar ta wanda zata dade bata cike shi ba.
A hankali rayuwa ta cigaba da turawa yaran suna dada wayo sosai kuma suna kara shakuwa da juna, dan ko yaushe suna tare da juna a gida daya. Bayan wani lokaci suka sake samun wani cikin, tsoron Mommy (Khadija) ya dadu sosai tun bayan da ta gane tana da ciki, dole ta matsawa Daddy (Ibrahim)suka saka CCTV a kowanne sako da lungu na gidan sannan aka kawo megadi dan har lokacin bata amince cewa babu saka hannun na gida a dauke mata d'a ba, dan dai bata san wa zata ce ba dan dukka mutanen da suka yi ragowa a gidan a lokacin na jikinta ne makusanta. Ita ta fara haihuwa wannan karon ma, ta haifo dan ta namiji kyakkyawan gaske, ta rungume shi tana hawaye sosai tana tuno Ahmad, babu wanda yazo asibitin daga ita sai Ammy (Aisha). yaran suna gida tare da me aikin su da kanwar Mommy Habiba. Babu wanda ya san da labarin haihuwar sai yan gidan su har sai da aka kwana sannan ta kira Zeenat ta fada mata, ta nuna rashin jin dadin ta da ba'a fada mata tun jiya ba. Muhammad Aryan shine sunan jaririn, wanda baki daya dawainiyar sa Zeenat ta dauke saboda yadda take tsananin son shi. Yaro ne me shiga rai sosai da abun sha'awa, ada Sadeeq ne nata amma ana haifo Aryan ta tattara ta watsa Sadeeq a dustbin tayi sabo, suka dinga tsokanar ta tana dariya. Ko da Ammy ta haifi Hydar still dai Aryan din shine nata, dan duk wani kudi da zata samu toh Aryan ne, duk wani abu da yake so shi take masa, duk wani abu da ta gani nasa ne.
Watarana suna zaune su uku suna hira sai Ammy tace mata yaushe zatayi aure wai? Lokaci yana tafiya gasu duk da yaran su ya kamata ta yi aure saboda shekarun sun fara tafiya. Murmushi kawai tayi tace ta kusa lokaci kawai take jira suka barta a haka da addu'ar Allah ya kawo lokacin kawai. Tun daga lokacin ta dauke kafarta daga gidan nasu, sai dai a waya kawai suke magana sai rana daya ta kirasu wai an daura mata aure a garin su. Dukkan su basu ji dadi ba ace har tayi aure sai bayan an daura zata sanar dasu amma sai ta nuna musu itama baa son ranta bane ba, dole sukayi mata uzuri amma a kasan zuciyar Mummy sam sai taji bata gamsu ba.


*DAWOWA LABARI*

Da sauri ya dawo cikin building din yana hawowa suka hadu da Kamal kunnen sa sakale da waya yana magana, rike hannun sa yayi yanayin Aryan din yasa shi katse wayar yana duban sa

"Na kwafsa Kamal."

"Da kayi me?" Yace yana duban sa

"It's a long story, kasan gidan su Raihana please?"

"Raihana kuma? Gidan su? Me ya faru?"

"Ka sani? No wait ka sani Kamal, ranar nace kayi dropping dinta, please take me, inaso naga Hydar."

"Wai me ya faru? Ka fada min naji tukunna."

"Muje zan fada maka a hanya." Ya shiga jansa,binsa yayi yana cewa

"An yanka ta tashi, Barrister yace mu dakata da zuwa."

"Mu dakata? Akan me? Ba zai gan mu ba Kenan?"

"Be dai ce ba, amma yace a dakata dai."

"Zanje kuwa, kuma zai ganni. Na gaji da wannan jeka ka dawo din, dole ma ya ganni."

"Toh yanzu fada min, menene ya faru? Me ya hada ka da Raihanan."

"Shiga mota please."

Ya bud'e masa kofar gaba da kansa, shi kuma ya shiga baya Habeeb ya tada motar

"Kasan Raihana yar gidan Barrister Matawalle ce Kamal?"

Juyowa yayi bayan

"Na sani."

"What? Ka sani Kamal? Baka fada min ba amma."

"Ban dade da sani ba nima, kamar yadda ka sani yanzu, kuma ina shirin fada maka dama."

"Shit!" Ya daki kujerar da Kamal din yake kai ta baya

"Ouch, Aryan karya min baya zakayi ne?"

"Ban sani ba, Adam yayi fooling dina, he sent me some audios da pictures da suke nuna Raihana tana ma Hajiya Zeenat aiki ne."

"Yes? Sai kayi me?"

"Na kore ta."

"Kaji matsalar ka, kaji matsalar ka. Habeeb please drop me here, ba dani zaa ji ba gaskiya, me yasa zaka yarda da maganar Adam without proper investigation, me yasa ba zaka bata damar kare kanta ba? Me yasa kowa ba zai dinga wasa da hankalin ka ba, abu kad'an zai bata maka rai ka yanke hukunci, me yasa zaka damu yanzu? Ka yarda bata aikata bane shine zaka je ka ganta ko kuma dan ka gane yar gidan Barrister Matawalle ce shine zaka je? Wanne a ciki.?"

"I don't know, I just want to see her, sannan naji her own side of the story."

"Ba zata saurare ka, ko zata saurara sai na hanata, kuma nasan komai da ya faru, Raihana saved your life sau ba adadi, duk abinda tayi saboda taimakon ka tayi, kasan wace Hajiya Zeenat, kasan wayon ta, tayi amfani da innocent mind din yarinyar ta sata abu da niyyar wai taimakon ka zatayi, duk abinda tayi saboda kai tayi, idan zaka tuna ranar da tazo tana kuka, a ranar ta gane Hajiya Zeenat amfani take da ita, sannan ta gano tasa anyi poisoning tea din ka, hakan yasata cikin tashin hankali har sai da ta kwanta ciwo, she saved you a ranar har ta zubar da tea din ba tare da kasha ba, nasan duk wannan saboda ta fada min tun a ranar, tsoron yadda zaka yi reacting yasa naki sanar da kai."

"Habeeb sauke ni anan." Kamal yace ransa a bace. Parking Habeeb yayi da sauri Kamal ya bud'e kofar ya fita shima Aryan ya fita ya tare shi

"Nayi laifi, na ji kuma ban kyauta ba I'm very sorry."

"Ni bani kayi ma laifi ba, fisabillillah tunda yarinyar nan tazo Aryan kake mata abubuwa, menene laifin ta?"

"I'm sorry."

"Ita zaka bawa hakuri bani ba, gashi kila dalilin da yasa Barrister yace ba zai ganmu ba, kasan yadda Raihana take a wajen yan uwanta? Ka sani? Suna sonta fiye da yadda suke son kansu."

"Na fisu son ta wallahi." Ya fada kansa tsaye, wani kallon Kamal yayi masa kamar be ji me yace ba, ya girgiza kunnen sa yana sake duban sa

"Me kace?"

"Yes, I love her Kamal, tun bata san kanta ba."

Kafadar Aryan din Kamal ya daka ya bud'e masa kofar motar yace

"Let's go, idan muka je bata saurare ka ba, ba ruwana dan muna zuwa zan juyo, kasan yadda zaka yi."

"Just take me, zan ga Hydar, I need to talk to him kafin Raihanan."

"Wai corper?" Kamal yace yana dariya, bugo shi Aryan yayi daga bayan yayi murmushi kawai




ZAFAFA BIYAR.....Γ— 2023
πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ’₯πŸ’₯πŸ’₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ’₯πŸ”₯πŸ’₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ’₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ’₯πŸ’₯πŸ’₯πŸ’₯πŸ’₯πŸ”₯πŸ’₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

INA MAABOTA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR WRITERS? WANNAN KARON MA MUN SAKE DAWO MUKU DA ZAFAFAN LITATTAFAN MU, MASU DAUKE DA ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A ZUCIYA

KU GARZAYO. ZAFAFAN NA KU SUN SAKE TAHOWA DA WASU ZAFAFAN LITTATTAFAN MASU DIMBIN DARUSSA NA MATAKAN ILMANTARWA RAYUWAR MU TA YAU DA KULLUM...

SAFIYYAH HUGUMA
A RUBUCE TAKE (KADDARATA)β™₯️

HAFSAT RANO
(RUMBUN QAYA)πŸ₯°

MAMUH GEE
(IDON NERA)🀩

NANA HAFSATU
KI KULA NI (MALLAKIN ZUCIYA)😘

BILLYN ABDULL
DAUDAR GORA (CIKI KA SHATA)πŸ’—

DUKA DUKA WADANNAN LITTATTAFAN ZASU ZO MUKU NE CIKIN FARA SHI MAI RAHUSA KAMAR KO DA YAUSHE.

DUKA BIYAR DIN AKAN NERA DUBU DAYA DA DARI BIYU 1200

GUDA HUDU AKAN NAIRA DUBU DAYA 1k

GUDA UKU AKAN 800

GUDA BIYU AKAN 600

GUDA DAYA AKAN 400

DADIN DADAWA, MUNA TALLATA HAJOJIN KU AKAN FARASHI ME SAUKIN GASKE! SANNAN GA BIYAN BUKATA

HANYOYIN DA ZAKU IYA TUNTUBAR MU DOMIN ZAMA CIKIN SAHUN FARKO NA WANNAN SABUWAR TAFIYAR SABUWAR SHEKARAR SUNE;


MASU BIYA TA BANKI ZAKU BIYA A WANNAN ACCOUNT DIN

BANK: ACCESS BANK

ACCOUNT NAME: MARYAM SANI

ACCOUNT NUMBER; 0022419171

SAI A TURA EVIDENCE OF PAYMENT HADE DA ACCOUNT NAME TA WHATSAPP TA WANNAN NUMBER;Β 

09033181070

IDAN KUMA KATIN WAYA NE NA MTN SEKU TURO KATIN VTU/SHARE AND SELL KO NUMBER KATIN HADE DA SHEDAR SA TA WHATSAPP ZUWA: 09166221261

FARASHIN LITTTAFAN ZAFAFA BIYAR NA CHANJAWA DA ZARAR AN KAMMALA SU. SAI KU YI SAURI KU GARZAYA DOMIN A DAMA DAKU A WANNAN SABUWAR TAFIYAR SABUWAR SHEKARAR 2023πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ’₯

KU GARZAYO A SAKE DAMAWA DA KU A WANNAN SABUBAR TAFIYAR MAI DAUKE DA SALO NA BAN MAMAKI. KAR KU BARI AYI BABU KU.

DOMIN ZAFAFA BIYAR NA KU NE. 😘🀩
[05/01, 21:53] Billyn Abdul 2: πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

*INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR MAZAUNA K'ASAR NIJER?*🀏🏾

*TO KU MARMATSO KUSA TA SAMU!!*πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ

*MUN SAURARI KOKENKU MUN KUMA AMSA*

*Zafafa biyar dinku sun samo muku hanyar biyan naku kudin karanta litattafan zafafa har guda biyar din*

*ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE*

+22799643131

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

*KUDIN LITATTAFAN ZAI KAMA KAMAR HAKA*

Books biyarΒ  1250CFA
Books huduΒ  1050CFA
Books ukuΒ  850CFA
Books biyuΒ  650CFA
Bookk dayaΒ  450CFA

*MUNA GODIYA DA SOYAYYARKU GAREMU AL'UMMAR NIJER,MUNA MUKU FATAN ALKHAIRI TARE DA GODIYA BISA ZABIN ZAFAFA BIYAR*πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ

*RQ*
24



****Kamal ne yake yiwa Habeeb kwatance har suka karaso kofar gidan Adda maimuna, Kamal ya juyo yace

β€œMunzo, amma ban ga alamar suna nan ba.”

β€œCall her please.” Aryan yace yana langwabe kai

β€œI can’t gaskia, ai da kunya wallahi.”

β€œPlease please, ka taimaka.”

β€œSai kace please oga Kamal.”

β€œPlease Oga Kamal.” Ya fada da sauri

β€œOk let me call her, ba dan halin ka ba.”

Ya Ciro waya yayi dialing number raihana, lokacin suna zaune a wani park ta gama bawa hydar labarin komai, fada yake mata sosai bayan da Ya gama jin komai din, be san zata iya saka kanta a irin wannan abun haka ba da tun farko basu barta tazo kanon ba. Abinda ya kawo shi kanon kenan a ranar dan Abby ya samu labarin in da take aiki da kuma labarin taraiyar su da hajiya zeenat har prison da ta rakata ganjn shi shiyasa yace lallai hydar yazo Ya dawo masa da ita, sannan kuma yace ya fasa ganin su Aryan din domin Abby yayi matukar fushi da daddyn su Aryan, baya jin zai iya yafe masa ballantana har wani abu ya sake hadasu, ba zai so taraiyar Aryan da raihanar sa ba, dan ba zai iya taba daukar yarsa Ya bawa dan gidan Mukaddas ba. Ba zai taba ba!

β€œGobe zamu wuce tare, kin daina zuwa sai karshen wata ni zan dinga kawo ki da kaina Kina clearance.”

Bata ce komai ba, wayarta ta dauki kara

β€œWaye?” Yace yana mika mata hannu, bashi wayar tayi Ya daga ya sakata handfree

β€œRaihana gamu a kofar gidan ku.” Kamal yace shima wayar a handfree din take

β€œBa ita bace ba, yayanta ne.”

β€œOk Oga Barka da rana ya gida’?”

β€œLafiya lou, please dama zan wuce da raihana gida, idan yaso zata dinga zuwa karshen wata tana clearance.”

Da sauri Aryan ya karbi wayar

β€œHydar please kuna Ina? Inason ganin ka dan Allah.”

β€œNa riga na wuce.”

β€œPlease nasan baka wuce ba, nasan kana nan ka fada min inda kuke, zanzo Yanzu muyi magana dan Allah.”

Kallon raihana yayi da itama shi take kallo sannan yace

β€œSkypark.”

β€œGamu nan toh.” Yace yana katse wayar

β€œMe yasa baya so ku hadu?” Kamal yace

β€œSaboda fushin abinda ya faru tsakanin Daddy da Alhaji Nasir ya shafe mu.”

β€œMe yasa kake son ganin shi toh?bayan ya nuna baya so.”

β€œMuje dai please, kar mu bata lokaci ya gaji su tafi .”

β€œOk, muje Habeeb.”

β€œOk.” Ya tada motar

A cikin sabon wajen sukayi parking, Kamal ya kara kiran raihana sannan ya bawa aryan bayan an daga yace wa hydar sun shigo wajen, in da zasu same su ya kwatanta musu.

β€œKaje kai kadai Aryan, zamu jiraka anan.”

β€œBa zakayi mata magana ba?”

β€œWa, nace mata me? Kai zaka gyara mess din ka da kanka.”

β€œNi? Ni fa Hydar nake son gani ma, not her.”

Yace yana yatsine fuska

β€œHaka kace?”

β€œYes, ni ba abinda zan ce mata, salon ta raina ni. Noo I can’t.”

β€œIkon Allah, Yanzu yanzu fa ka gama cewa you love her, ko ka manta?”

β€œYea I love her, tun tana yar babyn ta nake nufi ba fa Yanzu ba.”

β€œOk, a kyale ta.” Kamal yace yana gyara zama a motar Ya dauke kansa

β€œA kyale.” Shima aryan din yace yayi gaba. Murmushin mugunta Kamal yayi, dole sai ya kure Aryan a wannan lokacin yaga karshe miskilanci. Text ya shiga ya rubutawa raihana

β€œKarki kula aryan kanwata, ina parking lot come and meet me.”

β€œOk.” Tayi masa reply ya sake yin murnushi kawai dan ya riga ya san halin Aryan.


Daga chan nesa ya hango su, raihana na facing din ta side din da yake hydar kuma ya bashi baya, sai da yazo daf dasu sannan ya lura sosai da yadda idanun raihanan suka dan tashi alamun taci kuka, kallon ta yake yana tuna shekarun baya tana yar karama suyi ta goya ta shi da hydar har suna fada akan wanda ya riga, tafi son Aryan dan haka ne ma kusan kowanne lokaci tana manne dashi yana fama da ita. Murmushi ne ya subce masa, a duk memory din rayuwar su ta baya wannan sune memory masu dadi a gare shi, kafin komai yazo ya tarwatse ya zama babu wani sauran haske a rayuwar sa sai bakin duhu da ya mamaye ko ina. Dagowa tayi da niyyar kallon wasu saurayi da budurwa dake gefen su sai ta ganshi a tsaye daga kusa dasu yana kallon ta. Saurin dauke idon ta tayi zuwa wani wajen tasa hannu a idon tana jin kamar wani abu ne ya fada mata a idon bayan tuno irin ihun da ya gama yi mata dazu dazun nan. Mikewa tayi tsaye hydar ya kalle ta da alamar tambaya

β€œZan je toilet ne Hamma, ga bakon naka nan yazo.” Sai ta bar wajen ba tare da ta ko kalli bangaren da Aryan din yake ba

_β€œGet out of my life, bana son sakΓ¨ ganin ki.”_

Kalaman da ya gama jifanta dasu suka shiga dawo masa a kansa. Kenan abinda take nufi da bako tana nufin ta fita daga rayuwar tasa har ma ta shafe babin sa kenan ko me?

β€œBismillah.” Hydar yace yana nuna masa wajen zaman da raihana ta tashi. Zuwa yayi ya zauna kamar wanda kwai ya fashe wa a ciki saboda rashin kuzari. Kwarjini sosai yaji hydar din yayi masa musamman bayan abinda ya faru ya kuma tabbatar raihana ta sanar masa da komai. Hannun sa ya zaro daga aljihun rigar sa da ya zube su ciki ya mikawa hydar din suka gaisa.

β€œHope kana lafiya, ko da yake from all indications kana lafiya din, well menene maganar da zamuyi saboda ina sauri ne, yau nake son barin kano ko mai dare.” Ya kalli agogon dake daure a tsintsiyar hannun sa yana maganar

β€œI want to know Dama yadda kuke, ya bayan rabuwa!”

β€œWe moved on Aryan, tun bayan abinda ya faru muka dauki kaddara muka cigaba da rayuwa, duk kuwa da Daddy yaso rayuwar mu ta katse mu ta gayyara, sai dai bamu mutu ba, mun yi rayuwa me inganci duk kuwa da wahalar da muka sha din.”

β€œMenene banbancin mu Hydar? Karka manta a gaban idona aka raba mahaifiyata da ranta, a gaban ido na aka tarwatsa ma wadanda suka fi kowa kusanci dani rayuwa, ka dauka nayi wata rayuwar jin dadi ne bayan haka? Ko ka dauka na manta daku? Allah ne shaida ta, rana bata taba fitowa ta fadi ban tunaku ba, ban kuma yi missing dinku ba.”

β€œKasan rayuwar da mukayi kuwa aryan? Ka sani? Kasan rayuwa babu uba babu uwa, ku zakuyi wa kanku komai, Atleast ka tsira da mahaifi Aryan, mu fa? Kayi karatu me kyau cikin rayuwa me kyau baka rasa komai ba, mu fa? Kasan da ya akayi muka zo har nan? Mu muka dauki nauyin kanmu da kanmu.”

β€œBani da banbanci da rayuwar da kukayi Hydar,

Please Login or Register in order to submit comment