You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kallon wajen Raihana take cike da burgewa kad'an kad'an suna hira har aka ce su taso aka shiga dasu ciki Ya Nabeela kuma ta nufi office din kawarta da tazo saboda Ya Nabeelan amma ba ko yaushe take shigowa ba ma.
Cike da kwarewa aka shiga wanke musu kafa dukan su daga ciki kuma ana shirya kayan da za'a soma mata gyaran jikin na alfarma irin na manyan mata yan kwalisa. Ita aka fara gamawa wankin kafar aka ce ta taso, kafar tayi wani irin kyau da taushi ta dinga kallon kafar kamar ba tata ba saboda yadda tayi kyau kwarai. Ciki aka shiga da ita wadda zata mata gyaran jikin ta soma aikin ta bayan ta sauya kayan ta zuwa rigar da ake amfani da ita idan zaa ma mutum gyaran.
Sai la'asar likis sannan suka gama da wajen dan ma dai akwai ma'aikata itama Ya Nabeela an gyara kai da kafa haka ma Khadijan Kamal. Wani irin kyau fatar Raihanan ta fara tun a yau din kuma a kalla zasuyi kwana biyar zuwa sati daya suna zuwa ta tabbatar idan aka yi kwanakin nan ita kanta ba zata gane kanta ba. Har suka isa gida Khadija na ta koda ta Ya Nabeela na dariya suna zuwa sallar magriba sukayi suka ci abinci. Sosai Raihana ta sake da Khadijan dan tana da sakin fuska da wasa da dariya sosai a dakin da aka bawa Raihanan suka zauna suna hira har Kamal yazo daukar ta. Duk sai taji babu dadi kamar kar ta tafi haka dai ta rakota falon in da Kamal da Ya Nabeela suke maganar Aryan din da kiran da Kamal yayi masa be d'aga ba daga baya kuma wayar tasa a kashe

"Na zata ma zai dawo wallahi."

"Ai yana jin nauyin ki, da dai nine marainin wayon sa. Amma bansan me yasa ya kashe waya ba gaskiya, haka kawai baya kashe waya sai dai idan akwai yar matsala."

"Ko fushi yake na dauke masa matar sa?"

"Anya? Zan dai biya ta gidan na same shi idan yana chan."

"Ok."

Tace a sanyaye. Gaishe shi Raihana tayi sannan ta yi wa Khadijan sai da safe ta juya ciki. Duk sai taji ta kasa nutsuwa da ta ji suna maganar ya kashe wayar sa kuma shiru be dawo ba duk da Ya Nabeelan ce tace kar ya dawo amma ai da wasa take masa.

**RQ**

    49

***Kwantawa tayi lamo akan gadon cikin tunanin ko lafiya? Juye juye ta dinga yi har Ya Nabeela tayi knocking ta shigo ta sameta a kwance ta tashi zaune bayan ta shigo.

"Kin gwada kiran Aryan kuwa?"

Tace tana zama a gefen gadon. Girgiza kai tayi tace

"A ah."

"Call him please, na fara jin babu dadi, ko maida ke zanyi? Wai so nake yadda akayi auren nan urgent a kalla ki samu gatan da kowa ta samu, amma idan hakan zai takura masa gwara ki koma, bana son abinda zai taba lafiyar sa an samu ya fara warewa"

Shiru Raihana tayi bata san me zata ce ba tunda har lokacin nauyin Ya Nabeelan take ji sosai.

"Kira shi kinji? Bari naje naji shigowar Daddyn su Amna xan dawo."

"Ok tam."

Tace a sanyaye ya Nabeelan ta fita ita kuma ta dauki wayar ta, ta yi dialing number tasa. Kunna wayar sa kenan bayan ya tashi da k'yar daga wajen da yake zaune tun da ya idar da sallar isha. Ji yayi yana son kiran ta a kalla zai dan ji saukin abinda yake ji din a zuciya da ruhin sa. Sai ga kiranta ya shigo a daidai lokacin. Kallon number yayi kafin ya daga cike da mamakin co-incidence din da aka samu dan har ya hau kan number tata zai kira kiran ta ya shigo masa. Mikewa yayi sakale da wayar a kunnen sa ya koma saman gadon ya kwanta rigingine yana jin tayi sallama ya amsa a chan k'asan makoshin sa. Shiru ya biyo bayan amsa sallamar tasa saboda rashin sanin abinda zata ce masa, muryar kadai ta isa ta tababtar mata ba lafiya ba.

"Ya Nabeela ce tace na kiraka dama."

"Ok." Yace ya sake yin shiru. Sai ta rasa me zata ce masa kuma. Tana jin yadda yake sauki numfashi da dan karfi dan tana jin sound din sa. Kusan minti biyar suna a haka sai kudin ta ya kare. Kiran ya biyo a take ta d'aga jikin ta a sanyaye.

"Raihanaaa." Ya kira sunan ta cikin jan sunan. Har cikin kwakwalwarta taji yadda ya kiratan.

"Kina so na?"

"Na'am?"

"Tell me, kina so na? Zaki zauna dani duk tsanani duk runtsi? Ba zaki gujeni ba?"

"Menene ya faru?"

"Just answer me please, did you love me?"

Hadiye yawu tayi jin yadda ya tsare ta, muryar sa kuma a chunkushe alamun ba da wasa yake ba. Sake maimaitawa yayi a karo na uku ta tashi tsaye tana tattaro kalaman bakin ta da take jin sun mata nauyi tace

"Yes, ina sonka. Amma me ya faru? Me ya same ka?."

Wata irin ajiyar zuciya ya sauke me karfi sannan ya k'ara gyara kwanciyar sa ya dora wayar a saman kirjin sa a hankali yace

"Nagode sosai, babu abinda ya faru inaso kawai na sani ne."

"Ok, but muryar ka..." Katse ta yayi yace

"Missing dinki nake, inaso na ganki. Nazo?"

"Eh kazo." Tace zuciyar ta na wani irin harbawa da sauri.

"Ok, I'm coming right away."

"Ok." Tace a sanyaye suka ajiye wayar. Sai ta kasa tashi daga in da take zaune kirjinta na cigaba da dukan uku uku, yanzu idan yazo ya zatayi dashi? Daga jin yadda yake magana rigima kawai yake nema,kar Ya Nabeela tace ma so take ta tafi, amma kuma ya zatayi masa? Ba zata iya hanashi zuwan ba dan tana son ganin shi ta kuma san halin da yake ciki.
   Dawowa Ya Nabeela tayi dakin ta tambaye ta sunyi waya? Eh tace mata amma sai ta kasa fada mata yace zaizo yanzu. Sai da safe tayi mata ta ja mata kofar ta nufi part din Dr Farouk saboda lokacin kusan goman dare.
  Da kansa yake driving din duk da jikin sa babu kwari sosai amma kuma yasan idan ya ganta zai samu wani kaso daga cikin energy din nasa, duk da yasan Ya Nabeela zata masa tsiya amma kuma bashi da wani option idan ba zuwan ba, yana so ya rik'e ta a jikinsa yana shak'ar kamshin jikinta me dadi da yake saka shi manta dukkan damuwar sa. A waje yayi parking motar ba tare da ya shigo ba, ya kwankwasa kad'an gate man din ya leko ya ganshi sannan ya bud'e masa da sauri. Haske sosai a harabar gidan ba zaka ce daren yayi har haka ba. Suka gaisa ya zaro wayar sa ya kira Raihanan ya ji tana ina. Sai da kirjin ta ya buga da karfi da taga kiran nasa wanda ta tabbatar da ya karaso kenan. Dagawa tayi jiki a sanyaye yace tana ina, ta fada masa tana dakin sa. Murmushi yayi da ya tuna da kofar baya ta dakin da yake amfani da ita idan baya son shiga cikin gidan. Ce mata yayi ta bud'e masa back door din, ta tashi ta bud'e masa ya shigo ya maida kofar ya rufe. Taku daya tayi da nufin komawa tsakiyar dakin ya riko ta da sauri ya sakata a jikinsa yana sauke nannauyar ajiyar zuciya. Boyayyar ajiyar zuciya ta sauke itama dan ba karamin nutsuwa take ji ba a duk lokacin da ya rungume ta a jikin sa. Hancin sa ya kai saman wuyan ta ya shiga shinshinawa a hankali kamshin da jikin ta ke fitarwa na gyaran jikin da akayi mata ya shiga fizgar shi. Hadadden kamshi ne me aji da sanyin dadi wanda be taba jin irin sa ba.

"I love this scent!"

Yace yana kara kai kansa sosai ya zura a jikin wuyan nata wanda take jin hakan tamkar tafiyar tsutsa. Kankame shi tayi yayi murmushi yana raba jikinsa da nata ya zaunar da ita sannan ya durkusa a gabanta ya rike hannun ta.

"Wani abu zai faru dani wanda ni kaina bansan menene ba, abu daya na sani shine, sai na cika alkawarin da nayi wa kaina, ko da kuwa hakan na nufin katsewar numfashi na. Ina fatan zaki zauna dani duk runtsi duk wuya, ba zaki gujeni ba."

gid'a masa kai tayi idon ta na cicikowa da kwalla. Hannu ya kai ya share mata saman idon yana girgiza mata kai

"Karki zubar da hawayen ki akan abinda be chanchanci zubar su ba, zan yi komai da kaina ba tare da kowa ba, kuma sai na tabbatar da duk wanda yake da hannu ya fuskanci hukunci me tsanani."

"Su waye menene suka yi maka?"

"Karki damu, just pray for me."

"Tom, please karka saka kanka a wani abun dan Allah."

"Ba abinda zai faru kinji? Na miki alkawari amma karki sanarwa kowa, sirri ne tsakanin mata da miji."

"In sha Allah."

Tace a sanyaye. Mikewa yayi daga gabanta ya zauna a gefen ta yana jawo ta jikin sa. Ya lumshe idon sa yana jin saukin abinda yake ji a ransa na bacin rai. Abinda ya rasa a baya da har ya bari bacin ransu yayi masa mummunan tasiri a rayuwar sa. Amma banda yanzu da yake jin yana da abu me muhimmanci da zai yi protecting, yana kuma da burin tara family nasa na kansa. Yayi musu irin tarbiyyar da yake so. Su rayu cikin so da kaunar junan su.
Ba zai kyale duk wanda ya shiga gonar sa ba a wannan karon, idan har ya tabbatar da Barr Awais amanar su suka ci, sai yayi maganin su da duk wanda suke yiwa aiki, zai aje rigar hukuma ya saka wadda ta dace dasu zai kuma yi amfani da abinda Hajiya Zeenat din take ji da takama dashi wato dukiya wajen yakar ta.
    Baya yayi dasu suka kwanta akan dan madaidacin gadon da yafi kama da na mutum daya, ya kara jawota sosai jikinsa har kusan rabin ta na saman sa. Hannun sa ya kai saman gashin ta yana shafawa a hankali, yana sauraron heart beat dinta take tafiya kusan daidai na nasa bugun zuciyar.

"Inason babies Raihana."

Da sauri ta yinkura zata tashi ya matse ta yana murmushi

"Ba yanzu nace ba, kawai nace inason yara ne, da yawa da yawa kinga mu bamu da yawa, ina sha'awar naga mutum da yara masu yawa."

"Ni ba ruwana." Tace tana turo baki.

"Da ruwanki, kece zaki bani dukka kuma."

"Ka tashi ka tafi kar Ya Nabeela ta dawo."

"Um um ba in da zani, idan tazo ma shikenan kinga"

"Dan Allah ni dai ka tafi."

"Kora ta kike?"

"Eh." Tace tana tashi zaune.

"Ba in da zani, ai daki na ne nan din."

"Yanzu ai ya zama nawa."

"Aro dai aka baki."

"Toh ka tashi ka tafi." Ta ture shi ganin yana matsowa gareta.

"Kinaso in tafi?"

"Eh."

"Ok zan tafi, amma har yanzu b3 na a low yake, dazu ma 30% kawai yayi kuma ya zuke nan da nan, yanzu 50 nake so yayi kawai sai na tafi."

"Toh ba sai ka saka charjin ba, ai akwai wuta." .

Tace pretending bata gane me yake nufi ba. Murmushi yayi yana mata wani kallo me dauke da ma'anoni. Bakin ta da yake maganar ya bawa attention dinsa sosai. Kunya taji ta rufe fuskarta da sauri ganin yadda yake kallon ta.

"Kinga yanzu ma ya koma 0, anya ba bari zanyi yayi 100% ba kawai?"

Mikewa tayi ta hau yunkurin sauka daga gadon cike da dana sanin cewa yazo, ita wai ta tausaya masa ne amma ashe ba haka bane ba. Riko ta yayi ya dawo da ita kan gadon ya yi mata rumfa da jikinsa ya dora mata baki daya nauyin sa.

"Kin yarda in samu full charge din?"

Girgiza masa kai tayi alamar a'ah da sauri tana matso kwallar jin yadda ya danne ya hanata kwakkwaran motsi.

"Dan Allah kayi hakuri."

"Dan Allah kiyi hakuri." Ya ciji lips dinta na k'asa ya kwaikwayi muryar ta. Runtse idonta tayi ganin ya saka kansa a jikinta yana bin jikin nata da wani irin salon kiss. Jikinta ne ya dauki rawa ta rikice tsoro ya shigeta tayi kokarin ture shi amma ta kasa kwata kwata, numfashin sa yake sauke mata yana cigaba da abinda yake matan yana kuma saka idon sa a nata yana kallon reaction dinta. Hannun sa ya shiga zagaya a jikin nata zuwa saman cikin ta da yasa hannu ya yaye rigar t-shirt din dake jikinta ya zura hannun zuwa in da batayi tsammani ko tunani ba.

"Wayyo Daadah." Ta furta da dan karfi jin yadda ya kaiwa b***b dinta riko, saurin hade bakin ta da nashi yayi waje daya ya cigaba da yawo da hannun nasa a saman kirjinta yana mata kamar tafiyar hawainiya. Sosai ta rude jikin ta ya hau rawa ta rasa in da zata saka kanta sai jujjuya kanta take saboda abinda yake mata ba karamin rudata yayi ba. Romancing dinta ya shiga yi sosai yana cigaba da kissing din bakinta cikin salon da ya sata fashe masa da kuka. Kukan tane ya ankarar dashi abinda yake aikatawar, da kuma abinda yake shirin zarmewa idan har ya biye wa mahaukacin feeling din da ya taso masa a lokacin. Cikata yayi ya dagata ya kwanta a gefen ta yana maida ajiyar zuciya ya jawota jikinsa ya manne ta yana lumshe idon sa da yake jin kamar kansa zai fashe saboda yadda ya yi masa nauyi. Be san me ya hau kansa ba, duk da abinda yayi din ba haramun ya aikata ba amma ba yanzu bane right time din. Dan light romance yaso sai gashi ya zarme da yawa har yana neman wuce gona da iri. Zafi sosai bakinta yake mata da saman kirjinta, haka ya saka ta kuka k'asa k'asa yana jinta ya hanata tashi duk da attempt din da tayi na son tashin. Bacci ne ya soma fusgarshi bayan wasu mintuna ya sake kankame ta yana jin baccin sosai na rinjayar sa. Tashi tayi ganin yayi bacci ta zubawa fuskar sa ido zaka rantse ba zai aikata abinda ya aikata a yanzun ba, innocent face gareshi da wani irin shariya wanda zaka dauka irin su rike hannun mace ba zasu iya ba bare har su iya hada jiki da ita. Ita gaba daya ma tsoro ya bata dan yadda ya sauya mata lokaci daya. Saukowa tayi daga gadon ta dan harare shi kad'an tana cije bakin ta da lips din suka dan yi ja kad'an ta wuce toilet tana gyara rigar jikinta da ya maida mata ita sama.
  _**RQ**_

Page 50


***Wajen karfe uku da rabi na dare ya farka daga baccin da ya dauke shi. Kansa ne yayi masa wani irin nauyi har zuwa idanun sa. Shi kadai ne a saman gadon tana k'asa ta shinfida sallaya ta kudundune a cikin Hijab dinta tana bacci. A hankali ya zuro kafafun sa ya sakko ya dagata daga k'asan zai maida ita sama ta bud'e idon ta da sauri dan ba wani bacci me nauyi tayi ba. Be lura da ita ba, ya ajiyeta a gadon ta yi saurin maida idonta ta rufe tana jinsa ya zare mata Hijab din jikinta sannan ya tashi ya nufi toilet din. Wanka ya fara yi sannan ya dauro alwala ya fito ya haye sallayar da ta tashi daga kai ya shiga raya daren cikin neman taimakon Allah a abinda yake shirin yi. Karfe hudu da rabi akayi kiran farko ya dauko wayarsa ya bud'e application din alqur'ani me girma ya kunna ya dan rage volume din ya jinginar da kansa a jikin gadon yana sauraron karatun yana shiga chan cikin zuciyar sa yana saukar masa da nutsuwa. Yana zaune har aka yi kiran sallar, ya duba time din yaga biyar da kwata. Sai ya mike tsaye yana gyara zaman rigar jikin sa. Ya kalle ta tana bacci hankalin ta kwance. Sai ya sunkuyo kanta yayi kissing dinta a saman goshin ta a hankali sannan ya bud'e kofar ya fita daga dakin. A gate suka hadu da Dr Farouk ya kalle shi da mamaki dan be yi tunanin a gidan ya kwana ba duk da yaga motar sa amma be kawo yana nan ba, Sai dai yana ganin shi yasan dalilin da ya kawo shi dan shi kansa sai da yayi wa Ya Nabeela fadan akan me zata dauko masa mata ta ajiye ta dai kawo excuse dinta amma shi sam be gamsu ba, dan be ga amfanin zaman ba. Ganin da yayi wa Aryan din a yanzu ya bashi dariya ganin yadda ya Nabeela ta hakikance jiya akan maganar ashe Aryan din na cikin gidan ma a lokacin. Lallai shaanin maza sai a barsu kawai. Gaishe shi yayi ya amsa yana tsokanar sa yayi murmushi kawai dan yasan bazai fadawa Ya Nabeelan ba. Tare suka je masallacin sukayi sallar sannan Aryan din ya tafi shi kuma ya shiga ciki yana murmushi shi kadai. Ganin yadda yake ta faman smiling yasa Ya Nabeela tambayar sa dalilin Murmushin sa amma sai yace mata sirri ne ba zai fada mata ba, sai an kwana biyu idan ma zata ji abinda ya faru. Tasan halin shi sarai ko me zatace ba fa zai fada matan ba tunda yayi niyya shiyasa sai ta kyale shi ta nufi dakin Raihanan taga ta tashi.
Ta riga ta tashi tana ma toilet sanda Ya Nabeelan tayi Knocking a kofar sai kuma taji alamun ruwa sai ta juya kawai tasan ta riga ta tashi. Yana fita tana tashi ta shiga toilet din dan yin alwala tayo alwalar tazo tayi sallah bayan ta idar ta zauna tana azkar tunanin abinda ya faru tsakanin su na dawo mata a kwakwalwa. Bakin ta, ta dan shafa sai taji ya saki ba kamar jiyan ba. Samun kanta tayi da yin murmushi kawai ta chusa kafarta a tsakankanin cinyoyinta kunyar abinda yayi matan na kamata. Zai yi wuya ta iya kallon sa face to face a yanzu dan jiyan nan sosai ya wuce gona da iri da wasu irin salo da kwanyar ta, ta gagara dauka sam. Sake dawowa Ya Nabeela tayi dakin ta tashi taje ta bud'e mata ta shigo ta zauna Raihanan ta gaishe ta, ta amsa a sake tana tambayar ta bakunta. Amsawa tayi a kunyace ta dan zauna a dakin har garin yayi sha sannan ta tashi zata fita Raihana tace ko akwai aikin da za'a yi? Girgiza mata kai tayi tace

"Akwai masu aiki karki wahalar da kanki, idan kin gama sha'awa zata shigo ta gyara miki dakin."

"Zan iya gyarawa ma Anty."

"Ban saki ba, kar ace ina wahalar da amarya." Tace tana dariya murmushi Raihanan tayi itama

"Kinsan halin mutanen naki, jiya ma munsha fama da Daddyn su Amna wai akan me zan dawo dake, haka Kamal ma yayi ta mita suji kuma yanzu na barki da aiki ai sai kiji an aiko min da sammaci."

"A ah dai Anty."

"Ahaap, baki san halin su ba ai, sun iya son kansu."

"Me zaki ci breakfast, ko da yake ma nasan me ya kamata na baki."

Ta juya ta fita ita kuma Raihanan ta hau zare zanin gadon da duk ya yayyamutse kamar an yi dambe a kansa.


***Bacci ne a idon sa dan haka yana isa gidan tubewa kawai yayi ya haye gadon ya kwanta. Ba shi ya farka ba sai kusan sha daya, shima knocking ne ya tashi shi ya mike da k'yar muryar sa a chunkushe yace waye

"Bud'e ka gani mana."

Adam yace da full confidence. Muryar sa Aryan yaji, yayi tsaye cikin tunanin abinda ya kawo shi a lokacin bayan sai da ya tabbatar ya kwashe kayan sa tas daga gidan. Sake knocking yayi da dan karfi, Aryan din dake tsaye ransa ya soma baci ya isa kofar ya bud'e yana kallon sa. Kallon sama da k'asa Adam din yayi masa sai kuma ya bushe da dariya yana rik'e baki

"Ina matar? Ko ba aure kayi bane ba? Naji ance kayi auren boye."

"Me ya kawo ka?" Yace a fusace fuskar sa na sauyawa nan da nan zuwa bacin rai

"Relax." Yace yana wara hannun sa.

"kamar yadda kake da iko da gidan nan haka nake dashi, so karka daga min murya please. Zuwa nayi na maka murnar aure a matsayi na, na dan uwanka. Sai kuma nagan ka a haka."

"Kana tunanin wai kana da waje a gidan nan Adam?"

"Yes ofcouse, baka sani ba? Ko da yake ba zaka sani ba nasan. Kamar yadda kake da iko da right da gidan nan haka nake dashi nima."

Tabe baki Aryan yayi yace

"Ok yayi, zaka iya bani waje ko?"

Ya kama kofar zai rufe Adam din ya rik'e da sauri

"Ina matar wai? Ko dai ka kasa... Nooo don't tell me baka da wannan energy din, nooo."

Sai ya rufe bakin sa da sauri yana dariya. Rufe kofar Aryan kawai yayi ba tare da yace komai ba. Yana jin dariyar Adam din cikin izgilanci ya wuce toilet ya sakarwa kansa shower ruwan ya dinga shiga simar kansa yana ratsa shi sosai. Ya dade a haka kafin ya dawo daidai sannan ya fito ya hau shiryawa a tsanake tamkar wani abu be faru ba. Shigar kananan kaya yayi masu kyau da aji ya saka sandal ya fito ya fice daga gidan yana jin hayaniyar Adam din kamar ba shi kadai bane a gidan ba ko kuma waya yake. Gidan Kamal ya wuce kai tsaye ya kirashi yana hanyar yace zai karaso. Lokacin Khadija na tayashi had'a kaya domin tafiyar tasa ta dawo yau saboda wayar da ya samu daga chan sama dole a yau zai wuce dama hutun nasa yaso yayi yawa dan dai shugaban su mutumin sa ne sosai. Zuwan Aryan din yasa ya bar ta, ta karasa hada kayan ya dawo falon wajen Aryan din da zuwan nasa haka urgent ya bashi mamaki. Sai dai a yadda ya ganshi a nutse tsaf ya samu kwanciyar hankali sosai har yayi masa maganar tafiyar sa da ta taso wanda da yaso sai yaje zai gaya masa amma ganin komai normal yasa kawai ya sanar dashi. Aryan din be nuna komai ba yayi masa addu'ar nasara sannan suka dan taba hira har suka gangaro kan shari'ar da za'a zauna gobe wanda Kamal din yaso yana nan za'a yi. Sam Aryan be fada masa abinda yake shirin faruwa ba, ya barshi kawai a goben suke saka ran za'a gama komai.
Har bayan azahar suna tare a gidan Kamal din, sai da Habeeb yazo daukar Kamal din sannan Aryan yayi masa sallama ya tafi. Company ya wuce duk da yau ba ranar aiki bace ba, ya bud'e office dinsa ya shiga ya rufe ta ciki, ya dade sosai har kusan tara yana wajen sannan ya fito ya wuce gidan sa dan ba zai koma main house din ba yasan Adam yana chan. Shiryawa yayi ya saka kayan sa da yasan zai bukata a booth din motar sa, wajen sha daya ya fito ya nufi main house din ya ajiye motar tasa ya dauki kayan ya saka a motar Daddy sannan yasa Yahya ya kaishi gidan Ya Nabeela. Kiran ta yayi suna daf da gidan ta kalli wayar ta kalli Ya Nabeela da ta shigo suna maganar abubuwan da take da bukata duk da tana jin nauyi da kunyar ta amma haka ta dan dake ta fada mata, sun so tsayawa yau ma bayan sun baro wajen gyara jikin amma babu lokaci tunda kuma suka dawo Ya Nabeelan ta sake fita tare da Dr Farouk din sai past 10 suka dawo abinda ya sa suke maganar a lokacin kenan. Da wuri Ya Nabeelan zasu tafi Lagos da safe tare da Dr Farouk din zata rakashi wani taro shiyasa kuma bata so a sake bata lokaci. Sake kira yayi a tunanin sa ko tayi bacci jin bata daga ba sai tasa wayar a silent ta tura masa text suna tare da Ya Nabeelan. Bayan kusan 30min ya Nabeelan tayi mata sallama ta tafi ganin dare yayi sosai. Fitar ta da minti biyar taji yana kwankwasa kofar, sai da tayi wani irin jan numfashi kafin ta tashi ta bud'e masa ya shigo ciki. Kofar da Ya Nabeelan tabi ta fita ya nufa ya murda key sannan ya dawo cikin dakin. Gaishe shi tayi a hankali maimakon ya amsa sai ya zauna ya jawota ta zauna a saman cinyar

Please Login or Register in order to submit comment