You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wahalarwa domin suna da masifar taurin kai, ba dukka ya samu suka fita ba a lokacin, sai dai yaci karfin su sosai, kuma ya karya lagon su ya kona da dama a cikin su, abu daya yafi tsaya masa a rai, inda suka tabbatar masa sai da aka yanka musu jinjiri sabon haihuwa akan aikin nata. Shekaru da dama suna tare da ita, sun hanata sakat sun saka mata ciwo, sun sakata manta kowa da komai da ya jibance ta, sannan sun dora mata ciwon kai me tsananin gaske.
A hankali ta soma dawowa hayyacin ta, ya kira sunan ta na asali Aishatu,ta amsa masa da k'yar dan ko ina a jikinta ciwo yake mata, fita yayi ya barsu ita da Asiya ta sauya kayan ta, ta kwanta zazzabi me zafi na rufe ta.
A cikin zulumi ya samu su Lamido da Hydar a waje, sai ga Aryan ya fito tare da Raihana sanye da Hijab, kallon ta malamin yayi sannan yace

"Wannan ce Raihanan?"

Gida masa kai tayi Lamido yace eh itace

"Ki dinga azkar kinji? Akwai aiki babba akan mahaifiyar ku, dole sai kun dage da addu'a kar a dinga yin tufka ana yin warwara, suzo suna shafar yayanta, domin yanzu matsafa turke suke yi a jikin uwa,sai suje suna shafar yayanta suna wucewa."

"In sha Allahu Malam, yanzu ya jikin nata."

"Alhamdulillah, amma dole ne sai mun dage, sai munyi addu'ar nan kullum a kalla mu dauki wata guda munayi, domin ba karamin aiki akayi akanta ba, baiwar Allah an cutar da ita, sun zuba mata kaya sosai a jikin ta, domin duk wanda nace ya fita sai yace kayansa yake kwashewa, zan dauka sun tafi sai na sake zuba ruwan sai na gane makalewa yayi."

"Wanne irin Kaya Malam?"

"Cututtuka ne, idan kaji sun ce kaya toh sun saka ma mutum cuta, idan kuka tambayi wadanda ke tare da ita zasu gaya muku abubuwan dake faruwa da ita wanda duk su suke saka mata."

"Mun gode Malam, yanzu muna so mu tafi da ita, amma muna tsoron kar ta rikice mana."

"Babu matsala, tare zamu tafi baki daya ai, in sha Allahu babu abinda zai faru, domin ko a yanzu fa anci karfin su, sai dai nasan naci irin nasu, zai yi wuya su hakura a Zama daya, sai an kusan kone su kurmus sannan zasu hakura."

"Mun gode Allah ya saka da Alkhairi "

"Amin Amin, zan dan shiga gari wajen wani tsohon aboki na, idan kun gama shiryawa sai ku kirana nazo mu wuce."

"Toh Malam, muma yanzu zamu fara shiri dama abinda ya zaunar damu kenan."

"Ba laifi hakan, Malam Ibrahim sai ka kirani idan kun gama."

"Toh Malam, muje na sauke ko toh."

"A ah, je kaga mahaifiyar ka, ni zan iya karasawa da kaina ba wani nisa bane ba."

"Isa yana waje ai, ga Malam Yahya sai su sauke ga Malam."

Aryan yace yana bin bayan sa, yasa Isa ya tafi kaishi tare da Malam Yakubu da suka kulla sabuwar alaka da Malamin.

Kallon kallo aka tsaya yi tsakanin Lamido, Hydar da Raihana. Kowa na tsoro da shakkar zuwa wajen Ammyn, duk da shi Lamido be ga yadda tayi ba, amma kuma yana cike da zulumi, sai dai a matsayinsa na babba shine zai shige gaba, sai kawai ya kama hannun Raihana suka nufi dakin Hydar da Aryan suka taka musu baya. Tana kwance Asiya ta lullube ta da zani suka shiga, taji shigowar su amma bata dago ba, bata kuma yi komai ba sai dai bata kalle su. Hawaye Lamido ya sharea boye da ya tabbatar da Ammyn tasu ce, ta chanja sosai kamar ba ita ba. An zalunce su zalunci mafi girma, be taba jin da gaske yana son ganin bayan Hajiya Zeenat irin yau, ko zaman prison din da Abby yayi be kai zaluncin da akayi ma Ammyn ba. Hannu tasa ta yafito Raihana dake faman kuka wiwi, ta shiga jan jikinta da sauri zuwa wajen Ammyn, ta fada jikin ta sannan ta fashe da wani irin kuka me cin rai.



***Kun jini shiru jiya glasses dina ne ya karye sai da na sake wani. In sha Allahu zamu koma posting din safe zuwa Monday. For now dai ku dinga expecting dina around magriba zuwa Isha. Nagode!
**RQ**_

Page 60


****Kuka wiwi suke daga ita Har ammyn, su kansu yan mazan dauriya ce kawai da taurin zuciya irin tasu ta maza amma dukkan in su jikin su yayi wani irin sanyi. Mikewa Aryan yayi, zai fita Lamido ya dakatar dashi.

“Please karka tashi.”

“Wai abu zan duba a waje ne.”

“No ka zauna, dukkan mu daya ne kuma na tabbatar ammyn na cike da farin cikin ganin ka.”

Zama yayi ya fasa tashin amma duk nauyi ya cika shi ga kuma kukan da raihana take yana taba shi sosai. Tashi tayi zaune da kyar dan har lokacin jikinta babu gwari, kokarin kokawa suka dinga yi da malam dan haka duk jikinta ciwo yake mata sosai. Matsawa Lamido da hydar sukayi gabanta bayan ta zauna sai ta yafito Aryan da hannun ta

“Zo d’ana.”

Wani abu ya daki aryan, a lokaci daya tunanin mummyn sa ya dawo masa. Sai yaji yana jin tausayin kansa da kansa, domin yasan shi tasa mahaifiyar ba zata taba dawowa ba. Matsawa yayi kamar yadda su Hydar din sukayi gabanta, duk ta shafa kansa tana murmushi. Kamar Aryan sak da na Khadija, babu in da ya barta a kamanni da dabiun ma sai dan abinda ba zaa rasa ba. Ko na a gayawa ammy shi din waye ba, tasan jinin aminiyarta ne, ballantana kamannin sa sune tun na kuruciya be chanja mata ba, sai dan abinda ba zaa rasa ba. Shi Ya fara zame wa da wayo da wayo ya bar musu dakin sai kuma asiya ta biyo bayan sa itama yanin suna da bukatar gamawa da mahaifiyar su. Sadeeq ne babu da Abby, wanda duk cikin su babu wanda yasan wainar da ake soyawa, sai kuma uwa uba Dadah da ba’a san kalar farin cikin da zata shiga ba. Da laasar sakaliya suka baro garin bayan Aryan fa hydar sun yiwa malam yakubu da isa harda asiya e sha tara na arziki, sannan Aryan ya basu complimentary card dinsa yace suzo Har gida su same shi. Sunyi ta godiya a haka suka rabu da niyyar idan ammyn ta warke sumul zasu dawo dukkanin su, zuwa na musamman wajen malam yakubun asan ahinda ya kamata ayi masa dashi da ahalin sa. Mutanen gidan basu ji dadin tafiyar ammyn a haka ba, tunda mafi akasarin su basa nan, Wasu sun tafi suna chan kauyan su kanwar malam yakubun yaran kuma sun tafi makarantar islamiyya.
Hydar, Aryan da Malam Yahya mota daya suka hau kamar yadda suka zo, raihana ta gudu motar Lamido, ita da ammy da malam a motar. Tana lura da ammyn duk bata da sukuni shi kansa malam din ya lura ya kuma san dalilin hakan shiyasa yace kar su saurareta su tafi kawai idan sun isa lafiya sai a sakè yi mata adduar. Haka akayi kuwa, dare suka shigo Kano Aryan yace su wuce gidan su amma sai Lamido yace a ah, a kaita gidan adda maimuna, shiru aryan din yayi yana nazari, duk da kanwarta ce adda maimuna Amma be kamata akai ta gidan a yanayin nan ba. Magana yayi ma hydar idan ma gidan su ne Lamidon baya so aje toh akwai gidan sa dan Allah akai ta chan zaifi. Magana hydar din yayi ma Lamidon Ya tunasar dashi fa ba dan Aryan din ba da basu san ina ammyn take ba. Sai kuma abin ya dawo masa yace toh sannan aka wuce gidan Aryan din dake kusa da tsohon gidan su wanda yake har yanzu. Baba maigadi na zaune a gate yaji tsayuwar motoci, duk da kwana biyu ma Aryan din ya rabu da zuwa gidan yana chan main house din Amma yayi tunanin shine, lekowa yyai ganin motar yasa shi saurin janye gate din suka shiga sannan Lamido ma ya shigo da tasa yana karewa gidan kallo.
Shi da Hydar suka taimakawa ammyn suka shiga da ita ciki Aryan ya kaisu bedroom din sa dake kasa suka zaunar da ita dan jirin ne ya sake dawowa. Sallah suka fita suka yi tare da Malam sannan suka dawo ciki Lamidon da malam
Suka shiga dakin ita kuma raihana ta fito. Sai a lokacin suka hada ido da Aryan da yayi zuru zuru a kwana dayan nan kachal duk ya sauya, irin kallon da tayi masa taga ya rame shima shi yayi mata dan sai yaga har ta fishi ramewa ma ga wani abu me kama da tsoro dan kare a idon ta. Da hannu yayi mata alamar tazo gareshi, ta saci kallon falon babu kowa sai su biyu dan hydar ma ya shiga cikin dakin. A hankali ta isa wajen da yake tsaye daga jikin kafar bene kusa da wani dan corridor. Hannun ta yaja zuwa cikin wajen yana kokarin saka kwasar idon sa a cikin tata

“Menene?” Yace mata cikin muryar tausaya wa. Kamar me jiran kiris sai hawaye shar shar shar suka soma zuba, jan ta yayi ya bude dayan bedroom din suka shiga ciki sannan ya rufe kofar ya jingina a jikin ta yana jawota gaba daya jikinsa. A hankali suka saki ajiyar zuciya dukkan su.

“Please ki daina kuka,idan kina kuka bana jin dadi, zata samu sauki zata warke, amma sai kin zama strong, idan ba haka ba gidan Ya nabeela zan maidake har sai an gama komai.”

“Na daina.” Tace da sauri tana goge fuskar tata da bayan hannun ta.

“Good girl.” Yace yana murmushi. Murmushin da maida masa itama sai kuma wayar sa tayi ringing. Rike ta yayi da hannu daya ya saka dayan hannun ya jawo wayar daga aljihun wandon sa. Zainab ce take kiran sa, ya kwana biyu rabon da ya shiga office, dazu yaga kiran abdulhakeem be bi ba, yanzu ga na zee. Dagawa yayi yana sakata a handfree

“Hello sir.” Muryar ta cike da yauki da rangwada ta fito daga cikin wayar tasa. Gaban raihana ne ya fadi, ya dan kalle ta kadan jin yadda ta motsa sosai.

“Ina jinki.”

“Ya gida ya aiki sir?”

“Alhamdulillah, ya akayi? Naga kiran abdulhakeem dazu yanzu kuma ga kiranki, hope komai lafiya?”

“Lafiya lou sir, wasu files ne dama da ake da bukatar kayi signing, sai kuma meeting din da za’a yi tun last week Monday muke ta daga shi, sun yi magana suna so a sake fixing musu wata ranar.”

“Zan shigo Office din gobe, duk abinda ya kamata sai ayi.”

“Ok sir, ka huta lafi…”

Kit ya kashe kiran sannan yace

“Zainab ce.”

Bata ce komai ba, ta zare jikinta a hankali ya kalle ta

“Zanje na duba ammy.”

“Um um, ki zauna ki jirani anan, idan malam ya gama ma Dr Mahfouz ne zaizo ya bata magani, tana bukatar Hutu tayi bacci sosai, so ki barta ta huta kinji? Yanzu zanje na dawo.”

“Toh zanje falo na zauna, bana son zama anan.”

Rike hannun ta yayi zuwa gaban gadon, ya zauna sannan ta dora ta saman cin yarsa domin ya lura rigima take ji, yi tayi kamar zata tashi ya rike ta sosai yayi kissing lips dinta na kasa. Shiru tayi ta nutsu kamar ba ita ba, murmushi yayi kawai ya zaunar da ita a gefen sa sannan ya tashi

“Yanzu zan dawo just wait for me.” Da kai ta amsa masa, ya fita ita kuma ta kwanta lamo akan gadon komai na dawo mata daki-daki. Be jima ba sai gashi ya dawo, kamar wanka yayi dan ya sauya kayan jikinsa zuwa marasa nauyi, dama a takure yake tun a chan din shiyasa ya hau saman ya chanja bayan ya watsa ruwa a gaggauce, sannan ya fita ya karbo abincin da Ya nabeela ta aiko dashi wanda yayi mata waya tun suna hanya. A dinning ya ajiye sannan ya dawo dakin sai kuma ya kara fita da sauri ganin hydar na kiran sa a waya. Malam ne zai tafi suka raka shi waje Lamido yace zai maida shi yaki yace zai tafi da kansa gobe sai suzo tare da ammyn su kawo ta domin akwai Aiki sosai akan ta. Godiya sukayi masa ya tafi suka dawo ciki Aryan yace ma hydar akwai abinci a dinning idan akwai me bukata. Ammyn ya dibarwa Lamido ya bata taci kadan sai ga Dr Mahfouz ya karaso, ya duba ta sannan ya bata magunguna yayi mata alluran da zasu taimaka mata ta huta sosai sannan yace a barta ta huta zuwa safiya. Jawo mata kofar akayi suka dawo falo raihana kuma ta koma dakin da Aryan din ya kaita dazu ta zauna sai ta rasa me zatayi ma. Tashi Aryan yayi ya je dinning ya dauki plate ya zuba mata abincin sannan ya nufi dakin hydar na satar kallon sa kasan ransa kuma yana cike da jin dadi da farin cikin kanwarsa ta samu wanda yake sonta yake kulawa da ita.



****Tana kwance gaban katifar duk abin duniya ya dame ta, sau biyu tana yinkurin guduwa amma da ta zura kafarta take cin karo da kurar nan, abun mamaki yake bata yadda mutum zai yi rayuwa da kura babu abinda ya shafe su kuma. Ruwan pure water da take sha ta kalla, saura uku ya rage, bata san ko zaa sake kawo mata ba, ko kuma haka zata cigaba da zama. Turo kyauren akayi, Ladi ce dauke da abun kari tuwon dawo miyar kuka kamar kullum, shine abincin ba’a taba fashi ko a chanja ba tun da tazo, ta farko bata iya ci sai da taga uwar bari yunwa zata kasheta ta soma dan tsakura shima ba da yawa ba, gashi minti kadan Ladi take bata idan bata ci ba tazo ta kwashe kayanta tayi gaba. Shiyasa ana kawo wa in dai tasan zata ci take yin sauri ta dauka dan ta gama gane rashin mutuncin Ladi kadan daga aikin ta, ta zauna da yunwa, ruwan ma sai kadan ta bata ta shanye sauran tayi magana kuma taci zata chuna mata kura a dole ta hakura take kankan da kai a gabanta duk kuwa da bata san wacece ita da kalar abinda zata iya aikatawa ba, Amma babu komai da zarar ta fita daga wajen zatayi maganin yar iskar matar dan sai ta batar da ita daga doran kasa kamar yadda ta batar da sauran da suka yi yinkurin shiga rayuwar ta.

“Tashi ki yi maza idan kina da niyyar cin abincin kici, ki bani kwanon idan baki da niyya kuma nayi gaba da kayana dan ba ajiye ni kikayi da zan dinga dafa miki abinci kina wulakanci ba.”

“Yanzu Dan Allah ba zaki barni na tafi ba?”

Kallon ta Ladi tayi, kamar ba zatayi magana ba, sai kuma ta matso ta zauna a gefen katifar daf da hajiya zeenat din, kamar tace ta matsa amma sai ta daure dan idan tayi magana tata ce zatayi zafi.

“Kina so ki bar nan?”

Tace tana sunce gefen zanin ta,

“Ina so sosai wallahi, ki taimaka min na rantse da Allah sai na inganna rayuwar ki, na daga darajar ki zuwa daraja mafi girma a duk garin nan.”

“Toh Madallah, zaki bar nan amma sai na samu abinda nake so, idan kin yi hadin kai toh, idan bakiyi ba na rantse da Allah barki zan gaki ga kurar nan.”

“Zanyi koma me kika ce,wallahi zanyi nayi alkawari.”

“Tah! Ba naje na dawo.”

Ta mike tana yashe baki, ta girgiza kai ta fice da sauri. Dakin Lawwali dake daura da zauren gidan ta nufa tana kwalamar kira, kafin ta karasa ya fito da sauri

“Ya akayi?”

“Matar nan ce mukayi magana, ina ganin abinda alhaji yace ayi Yanzu ne daidai lokacin, taji uwar bari dole zata fadi gaskia akan komai.”

“Allah ko? Bari na dauko abinda ya bani, mun yi waya dashi ma jiya yace zai dan yi tafiya, zamu iya fara aikin muga.”

“Dauko maza, maganin dan iska karen maguzawa, ka daure ta a wuya sai ka shigo da ita, idan tasan wata ai bata san wata ba.”

“Hajiya Ladi ikon Allah, duk an buga dake an barki, me maganin yan iskan gari dana jeji, ke kadai gayya kin tare nan kin tare nan. Manya manya maganin kanana kanana.”

Ya hau yi mata kirari yana dariya

“Kai dai yi da jiki, na matsu naga idon yar iska. So nake ko banza ta danyi zawo a jikinta, shegiyar mata me zubin karu wai.”

“Haka kika tsaneta wai Hajjaju.”

“Kasan ni bana son rashin mutunci, duk kawaicin yaron nan sai da ta kure shi.”

“Wallahi, bari na dauko.”

Ya juya dakin ita kuma ta koma tsakar gidan ta jirashi tana cije lebe irin na mugunta. Dauke da camerar ya dawo ya mika mata yace ta rike masa, ya karasa gaban kurar da suka gada wajen mahaifin su ya sunto ta, ya makala mata abu a wuya da baki sannan ya ja ta suka nufi dakin da Hajiya zeenat din take ciki😂
Ladi ce ta gaba dan haka bata ga abinda yake bayanta ba sai da taji gurnanin da take ji a waje yana matso ta har ta tabbatar a dakin ne, idonta ne suka hasko mata kurar muraran dinta a tsakiyar dakin harshen ta a waje tana kallon hajiya zeenat din.

**RQ**

61

***Kwanon dake kan kafarta ta yi jifa dashi saboda tsabar kidimewa.

"Na shiga uku, dan girman Allah ku fita da ita." Tace cikin k'araji

"Hegiya ashe kinsan girman Allah."

Ladi tace tana kwashewa da dariya,

"Matso ciki Lawwali, tasan ba da wasa muka zo ba. Kwarankwatsa dubu idan baki sanar mana da duk abubuwan da kika dinga aikatawa ba sai kurar nan ta gwaigwayi kafarki."

Ta jawo hannun Lawwali ta turo shi zuwa wajen da Hajiya Zeenat din ta makale idanun ta sun fito waje cikin tsananin tsoro. A dan zaman da tayi da Ladi ta fuskanci mace ce jajirtacciya mara tsoro kuma, duk hargagin da take mata be sa taji tsoro ko karaya ba, burin ta kawai tagan ta a masifa.

"Na roke ke ki girman Allah ki kyale ni, na miki alkawari duk abinda kike so a duniyar nan zan miki Shi wallahi."

"Na sha gaya miki babu abinda zaki iya bani,matsiyaciya ma irin ki, me rayuwa a cikin kudin haram da jinin mutane."

"Zaki gaya mana ko sai na sako miki ita?" Lawwali yace yana zama so serious sannan yayi kamar zai saki kurar da take ta faman fitar da harshen ta

"Zan fada!" Tace da sauri

"Taji uwar bari, yar tasha. Zauna ki nutsu ki fara tun daga farko, kuma wallahi kikayi mana karya sai kin yabawa aya zakin ta."

"Zan fadi komai wallahi, amma kafin nan waye ya saku kamani? Aryan ne ko?"

"Tun yaushe nake gaya miki bamu wani san Aryanu ba, kin ga alamun wai mutane tunda kika zo wajen nan?"

"A ah."

"Toh mu ma aljanu mun gaji da shegen halin ki ne shine muka ga dacewar dauko ki mu kawo ki nan, tunda kin zama annoba cikin al'umma."

"Aljanu?" Tace tsoron nata yana ninninka na da sau dubu

"Kwarai, dan haka kiyi da jiki ki fada mana komai da bakin ki, duk da mun sani amma ta bakin naki muke son ji, kuma na rantse da girman me dukka kika yi karya sai kurar nan ta gwaigwayi kafarki."

"Na rantse zan fada,wannan wacce jaraba ce? Babu me nema na ne?"

"Ko sun neme ki ba samun ki zasuyi ba, alkadarin ki ne ya karya, sai ma kin soma ganin sakayya."

"Wannan masifa dame tayi kama?"

"Da uwarki tayi, do Allah Lawwali idan ba zata sanar damu ba mika mata lanto ta dan gutsiri kaurin shegiya."

"Zanyi." Tace ta zauna sannan ta nutsu sosai ya mikawa Ladi camerar ya nuna mata yadda zata rike aikuwa ta shiga daukar ta tana bayani tiryan tiryan tun daga farko har karshe, sosai Ladi ta yi masifar firgita da matar tsoro ya kamata dan bata taba ganin tsantsar zalunci irin wannan ba, amma sai ta dake kamar bata ji komai ba ta boye yanayin da ta shiga har suka samu duk bayanan da suke so. Lallai Hajiya Zeenat abar tsoro ce, domin samun mara Imani kamar ta zai yi yuwa duk da akwai su sosai amma kuma bata dauka ana irin wannan masifar ba. Ta cuce su ta bata musu rayuwa da lokaci sosai. Jikin ta yayi sanyi kalou ta fice daga dakin bayan tasa Lawwali daure kurar a daidai kofar dakin Hajiya Zeenat din da sau kusan uku suna shuna ta yi balain tsorata.

Tagumi Ladi ta zabga sai kuma wasu hawayen tausayin Aryan da ahalin su ya saukar mata, da tasan irin wannan kalar rashin adalcin akayi musu da bata bari ko ruwa Hajiya Zeenat din tasha a gidan ba, lallai ma yana da karfin zuciyar da har ya iya kulawa da ita anan din ma. Zame fuskarta tayi real fuskarta ta fito, itace dai mai aikin gidan nasu wanda Hajiya Zeenat ta kora saboda yadda take kula da Aryan din,ashe bayan tafiyar ta abubuwan sun sake lalacewa sosai.
Abinda suka dauka Lawwali ya turawa Aryan ta WhatsApp domin dama abinda Aryan din yake so kenan.


***Tura kofar yayi da hannu daya da babu abincin a hannun sa ya shiga da sallama. Tashi tayi zaune tana amsa sallamar sannan tana kokarin gyara rigar jikinta da ta dan ya mutse. Akan bedside drawer ya ajiye dan karamin tray din yana kallon fuskarta da yanayin walwalar ta.

"Tashi kici abinci." Yace yana zama a gefen. Zaman ta gyara sannan ta dauki tray din ta sauke shi k'asa ta zauna a gabansa tana kallon kayan ba tare da ta taba ba. Zamowa yayi ya zauna a kusa da ita ya bud'e ya saka mata fork yace taci. Bata ce komai ba ta dauki fork din ta soma cin stir fry spaghetti da minced meat me dan karen dadi. Ganin ta fara ci ya sashi komawa saman gadon ya dauki wayarsa ya kira Ya Nabeela.

"Yanzu nake shirin kiran ka."

Tace tana zaune tare da Dr Farouk yana dinner a tsakiyar falon su

"Nima abubuwan ne suka yi min yawa na manta, thanks for the food."

"Nasan dama kun gaji sosai dole,kira zanyi nace ina kanwata wai? Shiru an dauke min ita ba wani bayani dai?"

Kallon shashen da take zaune yayi sai yayi murmushi kad'an mara sauti, Ya Nabeela ba abokiyar maganar sa bace irin wannan amma da sai ya bata amsa. Abu daya kawai ya sani shine ta dawo kenan, yan kwanaki kawai zasu kara su fice daga k'asar gaba daya sai kuma an gansu. Dstriya Kawai tayi jin yaki magana ta kuma tabbatar da ba zai yin ba dan tasan halin sa, dama kuma Dr ya fada mata an ga Aryan din a passport office yaje renewing sannan yace zai kawo Raihanan itama, wani abokin sa a passport office din ne ya gaya masa tun last two weeks ma. Sallama sukayi bayan ta tambayi jikin Ammyn sannan tace zata shigo gidan gobe tare da Khadija Matar Kamal su dubata sannan su taya Raihana zama. Ajiye wayar yayi ya dan leka plate din sai yaga taci sosai, dadi yaji domin baya son yanayin da yake ganin tan. Mikewa tayi a hankali zata dauke plate din ya hanata ta hanyar rigata dauka.

"Allow me please, your majesty!"

Yace yana sakar mata tsadadden murmushin nan nasa. Murmushin ta samu kanta da yi domin taji dadin yadda yayi maganar. Dauka yayi ya fita ita kuma ta yafa mayafin ta, ta fito zuwa dakin da Ammyn take ta tarar tana baccin ta a nutse. A gabanta ta durkusa tana kallon fuskar ta hawaye na bin fuskar, bata san wanne irin godiya zatayi ma Aryan din ba, soyayyar sa da matsayin sa ya karu sosai a wajenta har tana jin zata iya zama dashi a kowanne irin hali. Ya dan dau lokaci a dakin tana jin kamar tayi kwanciyar ta a bayan Ammyn amma kuma sai ta tuna zai bukace a kusa dashi tunda ita Ammyn bacci take kuma ba lallai ta farka ba kwata kwata ma sai zuwa safiya, tasan kuma Hamma Hydar da Hamma Lamido zasu dinga dubata sai kawai ta tashi bayan tayi mata addu'a ta jawo kofar ta fito ta koma dakin. Babu kowa a ciki,yaga lokacin da ta shiga dakin Ammyn shiyasa kawai ya haye sama bayan ya samu sakon Lawwali ya hau kan aikin kawai a gaggauce.
Shiru shiru

Please Login or Register in order to submit comment