You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

be dawo ba, ta tashi tayi shafai da wutri sannan ta zauna tana yiwa Ammyn ta addu'a ta dade a zaunen sai gashi ya shigo, babu haske ko kad'an a corridor din alamun sun kwanta su Hamman ta, sai hasken dakin kawai yayi tunanin ma ko bata dawo dakin ba tana wajen Ammyn amma ga mamakin sa sai ya ganta a zaune akan abun sallah. Mikewa tayi ta nannade abun sallar ta ajiye ya karaso cikin dakin ya tsaya a gabanta. Hijab din jikinta tayi niyyar cirewa amma sai ta fasa tayi tsaye tana jiran me zaice.

"Baki bacci ba? Na zata fa kina wajen Ammy."

"Yanzu na dawo." Tace dan kar ya gane zaman jiran sa take yi har ta gaji.

"Zaki koma ne?"

"Eh." Tace kamar da gaske take. Sai ya langabe kai

"Ba zaki tayani kwana ba?"

"Um um, wajen Ammy zanje ni." Tace tana kewaye shi zata wuce. Riko ta yayi yana kokarin hana kansa yi mata dariya domin ya riga ya gano ta tun daga yadda ta amsa masa da farko.

"Wajen Ammy zani."

"Wajen Ammy zani." Ya kwaikwayi muryar ta yana murmushi.

"Muje ki tayani wani aiki a daki na, idan muka gama sai ki dawo wajen Ammyn ko?"

D'aga masa kai tayi sannan tace

"Zan dawo ko?"

"Emana, me zaki zauna kiyi a chan? Zaki dawo ai dole."

"Ok."

Tace a tunanin ta da gaske yake da yace zata dawo din, rashin rigar jikin sa ya hanata sakewa dashi har taji tana son komawa dakin Ammyn. Saman suka haye hannun sa a jikin nata zuwa bedroom din nasa da yake shi kadai a bud'e a saman. Murd'a kofar yayi ya dan yi baya ya bud'e hannayen sa yace

"Ladies first." Shiga tayi a nutse ya bi bayanta gami da rufe kofar hade da danna lock dinta yadda babu me iya bud'e ta sai shi, dama security door ce tunda duk abubuwan sa a dakin suke.
Kallon yadda dakin yake a hargitse ya ajiye riga chan takalmi chan ga shi ya barbaza takardu a saman gadon sai system dinsa dake a kunne jone da wayar sa. Wuce ta yayi zuwa gaban gadon ya hau tattara kayan dake kai. Sauran kayan ta hau kwashe masa tana tayashi suka kwashe komai suka saka shi a muhallin sa yayi sauran sai computer kawai da wasu papers. Gadon ya haye yace tazo ta gani ta matsa gaban gadon ta tsaya tana leka system din. Dagowa yayi ya kalle ta yayi murmushi kawai yace

"Zauna anan."

Zama tayi tana kallon jikin system din ya cigaba da jujjuya mouse din ba tare da ta gane abinda yake ba, be dau lokaci yana yi ba ya tattara ya rufe ya dauki system din ya dora ta akan reading table dinsa ya jona ta jikin socket ya wuce toilet. Fitsari yayi ya sake wanke bakin sa da mouth wash sannan ya fito ya tarar da ita tsaye tana jiran ya fito ya bud'e mata ta tafi. Towel ya dauka ya goge fuskar sa tana tsayen ya dauki body spray ya fesawa jikinsa sannan yace ba tare da ya kalle ta ba

"Cire Hijab din mana bakya jin zafi ne?"

"Ai wai tafiya zan dama."

Murmushi yayi gami da taune lips din k'asa ya girgiza kansa kawai yazo ya wuce ta ya kashe hasken dakin gaba daya. Kirjinta ne ya buga ta hau wara ido tana waigawa. Takowa yayi har inda take tsaye sannan ya riko ta gaba daya jikin sa ya zare mata Hijab din dake jikin ta ya jefa shi kan sofa, ya d'aga ta chak ya nufi kan gadon nasa da ita.

"Taf..fiya fa zanyi." Tace cikin in da in da, ya dire ta a saman gadon sannan ya dora mata dukkan nauyin sa yana jin har sai da tayi yar Kara

"Me yasa kike da tsoro ? Umm?"

"Tsoro? Ni ba tsoro nake ji fa, tafiya zan."

"Ba wani, ina ganin yadda idanun ki suke shigewa da tsoro, me nayi?"

"Ba komai."

"Ba wani, tsoro na kike ji bayan ni babu abinda nayi miki, infact nine ma ake wahalarwa da rayuwa dan an ganni bawan Allah babu ruwana."

"Me nayi maka?"

"Gashi nan, kinsan dai ai ba haka miji da mata suke rayuwa ba ko? Kina ji kina gani Ya Nabeela ta hanani ke, kamar ma dadi kike ji har wata kiba kikayi ta musamman."

Ya taba saman wuyan ta zuwa saman kirjinta.

"Ni Allah ba ruwana, yanzu fa wajen Ammy zanje."

"Um um ni ba in da zaki. Anan zamu kwana Hydar suna k'asan babu abinda zai faru."

"Toh d'aga ni."

"Ina da nauyi ne?"

Gid'a masa kai tayi

"Haka zaki dinga daukata."

Da sauri ta kalle shi, dan hasken da ya hasko daga corridor din wajen window ya bata damar ganin fuskar sa. Daga mata gira yayi sannan yace

"Gwara ma ki saba da nauyin."

Shiru tayi bata ce komai ba, ya dan sassauta yadda ya danne tan sannan ya mirgana gefen ta ya jawota ta dawo saman jikinsa gaba daya, yasa hannayen sa ya zagayo su ta saman bayan ta ya riketa da kyau.

"Ke baki da wani nauyi, a haka zamuyi bacci. Goodnight."

Yace yana rufe idon sa. Kwantar da kanta tayi a saman kirjinsa lamo tana sauraron heartbeat dinsa da take fita da dan sauri, dago kanta tayi daga kai da sauri da niyyar yi masa magana bakin sa da dama yake daidai saitin kan nata ya hadu da nata, cikin wani irin salo ya kama lips din nata ya shiga kissing dinta da sauri da sauri. Gwalalo ido tayi ganin yadda ya soma birkicewa, ya shiga hautsinata ta ko ina yana cigaba da kissing din nata, hannun sa dake jikinta ya shiga zazza gayawa a jikin ta yana bin ko ina da ko ina. Sosai ta kara tsorata domin yanayin sa na yau har ya fiye mata na kullum, da zafi zafi yake komai ya kuma k'asa tafiyar da ita a hankali kansa tsaye kawai domin da gaske ya kai karshe a hakuri, dama irin su ka kalle su kawai amma idan suka birkice maka zaka dauka basu bane ba. Cikin salon da yake mata da yafi karfin hankali da tunanin ta, taji shi sama sama yana kokarin aikata abinda kwakwalwa da gangar jikinta ba zasu iya dauka ba. Kuka ta fashe masa da karfi fiye da wanda take yi a dazun. Be ji ta ba kwata-kwata, ko da ma yaji ta toh ba zai iya fasa abinda zuciyar sa ke ingiza shi ba, duk kuwa da ya riga yayi ma kansa alkawarin har sai komai ya daidaita, amma ya k'asa, ya gaza hakurin. Muryar sa a matukar shake taji kamar yana karanto addu'ar da manzon Rahma ya koyar damu, anan hankalin ta yayi masifar tashi, ta tuna Ammy, Lamido d Hamma Hydar duk suna gidan, tabbas za'a yi abin kunya idan ta miye ma Aryan, amma kuma ya zatayi? Idan ta ki tabbas zata kware shi, amma kuma ba zata iya ba, hankalin ta ba zai iya daukar azabar da take ji ba, kuma ba zata iya daukar matsanciyar kunyar da zasu shiga ba. Daidai saitin kunnen sa ta shiga gaya masa

"Ammy nah, dan Allah! kayi hakuri. Dan Allah zan mutu wallahi dan Allah, Wayyo hamma na."

Sunan Ammyn ne ya shiga kunnen sa sosai, sai kuma tunanin suna cikin gidan ya fado masa. A wani irin yanayi ya zame jikin sa da sauri, ya mike kamar zai fadi ya nufi toilet ya sakar ma kansa ruwa idanun sa a rufe. Tashi tayi da sauri ta hau lalubar kayanta da yayi mata watsi dasu, da k'yar ta gano rigar tata a k'asan gadon ta saka, gaba daya jikinta wani irin ciwo yake mata da zafi. Bakin ta har wani zum yake saboda a zaba, tana jin karar ruwan a toilet din sai dai babu motsin sa ko kad'an, tasan ba abu bane me sauki a garesa ba, musamman tunda ta riga ya saka rai sosai.amma ya zatayi? Sakkowa tayi idon ta ya sauka akan wayar sa ta dauka ta dan haska tayi wajen kofar fita amma still ba zata iya budewa ba, hakura tayi ta dawo ta zauna akan sofar tana jiran ya fito. Ya dade sosai a ciki har sai da yaji ya dawo daidai sannan ya dauro
alwala ya fito daure da towel, ya wuce ya dauki jallabiyar sa ya saka sannan ya dauki sallaya ya shinfida ya tada sallah. Tana zaune har ta gaji ganin bashi da niyyar tsayawa, sai kawai ta koma saman gadon ta kwanta tana curewa waje daya tana leka shi, har ta gaji bacci ya dauke ta. Ya dade akan abun sallar sannan ya nannade ya ajiye yazo daidai saitin kanta yana kallon ta cike da tausayawa. Allah ya rufa asiri da an yi abun kunya, shi kansa ba zai so hakan ta faru ba, yafi so daga shi sai ita yadda zai kula da ita sosai. Be san me ya hau kansa ba har ya kasa controlling kansa ya tafi haka da karfin sa. Kissing saman goshin ta yayi, ta sauke ajiyar zuciya a wahale, ya dan gyara mata kwanciyar ta shiga gadon sosai dan da a gefe take, sannan ya kwanta a dayan side din yana kallon innocent fuskarta.

**RQ**

62

***Da safen wuri Ya nabeela suka zo gidan ita da Khadija, lokacin raihana ko tashi ma batayi ba sai aryan din tare da su hydar a falo suna zaune suna magana. Ammyn ma bata tashi ba har lokacin baccin take yi. Zuwan su ne yasa ta tashi bayan yazo ya dan taba ta kadan ta tashi da sauri, murmushi ya sakar mata yana nuna mata agogon hannun sa dake nuna lokaci, sosai tayi mamaki dan bata dauka zata iya bacci har haka ba. A kunyace ta sakko ta wuce toilet din dakin shi kuma ya sakko kasa suka bishi da kallo Ya nabeela ta harare shi a wasance tace

“Wai ina kanwata ne?”

“Bacci take yi sai yanzu ta tashi.”

Yace yana zama a gefen Hydar bayan ya zare hannayen sa dake zube a cikin aljihun dogon wandon shaddar sa da farar shirt da ta dan kamashi.

“Ga breakfast chan toh na kawo muku, sai ku tashi nasan baku ci komai ba.”

“Kamar kuwa Anty Kinsan yunwa muke ji.”

Hydar yace yana dariya

“Ya kukayi da Sadeeq din?” Aryan ya tambaya

“Sun dauko hanya ai ma ai, babu available flight yau dole sai dai subi mota, Dadah ma nake tausayawa zaman motar dan kwana biyu tana complain din kafa sosai.”

“Allah sarki, Allah ya Kawo su lafiya. Sai suke ji labari me dadi.”

“Wallahi Anty, Alhamdulillah!”

“Ina mutanen gidan ne?”

Ammy tace tana budo kofar dakin da take bayan ta farka kusan mintuna goma kenan. Tashi sukayi dukkan su, suka karasa wajenta Lamido ya riko ta ganin kamar har yanzu da jiri a tare da ita, dakin ya maida ita suka shiga dukka shi kuma aryan ya dauki jakar Kayan raihana da Ya nabeela ta kawo mata ya haye saman. Wanka tayi tana tsaye tana tunanin kayan da zata saka bayan ta maida na jikinsa duk sai taji ta takura, ba zata iya zama da kayan ba dan ita a kaidar ta bata maimaita Kayan da ta saka sai an wanke. Turo kofar yayj ya dire jakar a tsakiyar dakin sannan yace

“Ammy ta tashi, ki shirya ki sakko su Khadija suna jiran ki.”

Da kai ta amsa ya juya ya jawo mata kofar ita kuma ta dauki kayan ta saka a gaggauce kin ammyn ta farka. Kasan ta sakko ta tarar da Ya nabeela da Khadija a falon bayan sun fito daga dakin duk sai taji kunya ta kamata ganin yadda suke kallon ta musamman Ya nabeela da take mata kallon tsaf kamar me shirin gano wani abu. A daddafe ta karaso tsakiyar falon tayi saurin dukawa kasa ta gaida Ya nabeelan da sauri tace

“Tashi tashi daga kasa, ba’a zaman kasa musamman tiles din nan me shegen sanyi, yanzu sai sanyi ya shiga mutum.”

Tashi tayi ta zauna a gefen Khadija suka gaisa sannan ta nufi dakin da ammyn take. Tana zaune Hydar na bata tea ta shiga, ta kalle ta kadan sai kuma ta cigaba da shan tea din har Raihanan ta karaso ciki ta zauna a gefen Ammyn suka sakata a tsakiya ita da hydar. Cup din ya mika mata sannan ya mike

“Karasa bata sai tayi wanka time yana tafiya.”

“Ok.” Tace ta shiga bata tea din tana sha a hankali tana ta kallon raihanan amma bata ce komai ba. Sai da ta gama bata tsaf sannan ta shiga toilet din ta hada mata ruwan wanka tazo ta taimaka mata ta kaita har toilet din ta nuna mata yadda zatayi sannan ta fito ta hau gyara dakin , ta gama ta fito mata da kayan da zata saka hade da Hijab sannan ta zauna ta jira ta fito ta kuma taimaka mata ta shirya sannan tace ta zauna tana zuwa. Wajen su Ya nabeela ta dawo Ya nabeela tace zata raka Khadija asibiti daga nan zata dauko su amna daga school amma zasu dawo da yamma. Sallama sukayi mata suka tafi dama ba kowa yan mazan sun shiga ciki shiryawa za’a kaita rijiyar lemo gidan malamin nan, shi kuma Aryan zai je Office yaga abinda ya kamata yayi kafin su dawo. A tare suka shirya suka fito harabar gidan aryan ya dauki karamar motar sa su kuma Malam Yahya ya dauke su suka wuce Rijiyar lemon shi kuma ya wuce Office.

****Kayan jikinsa yake so ya sauya zuwa na gida sannan yaje yaga abinda yake faruwa. Dukkan ranakun nan a cikin busy yake akn wani babban case da yake da yakinin zai kara daga darajar sa dan kuwa da kasan zuciyar sa yana jin zai iya barin aikin nasa nan kusa wanda yasan hakan bata yiwuwa a yanayin aikin nasu sai ka taka wani mataki. Familyn sa na bukatar sa a yanzu fiye da ko da yaushe, daga Baban nasa har Daddy suna bukatar Hutu a Halin yanzu domin dukkannin su girma ya kamasu sannan yasa aryan kadai ba zai iya cigaba da kula da companies din nasu shi daya ba, abubuwan zasuyi masa wahala at least Shima yana bukatar ya huta sosai ya fuskanci rayuwar sa da ta iyalin sa. Apartment dinsa ya koma ya shirya cikin kananan kaya marasa nauyi saboda yadda garin ya hade yake neman zubda ruwa. Direct in da aka ajiye Adam din da yaran sa ya wuce da knsa. Khadija ya kira yana driving ya saka wayar a jikin motar har ya isa suna waya sai da yayi parking sannan sukayi sallama ya fito ya kulle motar. Dakin da yasa aka ajiye su Adam ya wuce yana zuwa aka bude masa kofar ya shiga. Babu wadattacen haske a dakin amma yana iya hango Adam din a kwance a kasa gabansa da wani kwanon abinci. Shi kadai ne a dakin sauran yaran an maida su sashen masu kula da masu manyan laifuka domin an kamasu da laifin kidnapping, shigo da manyan makamai da amfani dasu wajen cutar al’umma. Ya daku sosai yayi likis dan dama yace kada su raga masa ko kadan domin yaron ya riga ya kaishi karshe shiyasa yasa suka masa liks ya zama ko mikewa baya iya yi sai jan ciki da yake yake karasawa dan gaban pit din dake hade da dakin idan zai yi bukata. Zarnin d dakin yake yi ya hana Kamal daurewa ya yayi saurin ficewa zuwa Office dinsa ya zauna ya rufe kofar sannan ya jona system dinsa mail din aryan ya shigo masa. Be duba mailbox dinsa ba tun kwana biyu saboda yayi busy dan haka ne yasa be san Aryan din ya turo masa ba, budewa yayi yana relaxing sosai akan kujerar sa ya shiga duba documents din zuwa video da yake attached da write up din.
Yanayin yadda ya shigo Office din ya saka kowa shan jinin jikin sa, a daure tamau fuskar sa take be ko tsaya yayi attendance ba yayi wucewar sa Office ya bude ya shiga. Uwar iyayi zee tana zaune ta mike ta dauki files din dake ajiye a desk dinta ta nufi Office din duk kuwa da kallon kar ki je din da chomzy ta aikata mata amma tayi tafiyar ta bayan ta gyara jikinta. Knocking ta yi tana kara daidai ta fuskar ta, ya dago yana kallon kofar yasan babu me zuwa duk kuwa da yanayin da ya shigo sai zainab, yarinyar ta sakè da yawa zai yi maganin ta kuwa dan ya dawo aikin sosai kafin tafiyar tasu. Sakè kwankwasawa tayi a zafafe yace

“Waye!!!”

“Zainab ce Sir.”

“Na neme ki?”

“Mmm dama sir files din nan ne da mukayi magana jiya.”

“Na saka ki kawo mjn ne?”

“No sir na dauka zaka…”

“Kije sai na neme ki da kaina.”

Kamar an buge mata guiwa haka taji, ta waiga reception din taga duk ita suke kallo, gashi tasan ko basu ji abinda suka ce ba zasu gane korar da yayi, kamar kasa ta tsage ta shige ciki haka taji, ta rasa ma ya zatayi, tunowa da tayi da toilet a chan gaba sai kawai ta wuce, taji sanda chomzy da Ali da Fadila suka kwashe da dariya, ta kuma san ita suke wa dariyar.kuka ta fashe dashi a toilet din kukan takaici, ga wata zazzafar soyayya da take masa amma ya kasa ganewa. Sai da tayi kukan ta gama ta wanko fuskar ta fito ta koma Seat din ta, ta bude jakar ta, ta shafa powder da janbaki sannan ta rataya jakar ta fice ba tare da ta ce ma kowa komai ba. 10mint da tafiyar ta ya kira reception din Ali ya daga yace ya karbi file a wajen Zainab ya kawo mishi office.

“Ta fita sir.”

“Ta fita!? Ina taje?”

“Bamu sani ba, ta fita dai cikin fushi.”

“Check her table ka kawo min files din.”

“Ok sir.” Ya ajiye wayar. Bama ta da hankali, idan kuwa haka zatayi zai iya bata suspension taje chan tayi ta haukanta.


****Ba kamar karon farko da akayi ma ammyn addua ba, wannan karon abun ya dasu zafi sosai domin ashe duk suna nan babu wanda ya tafi, dama malam din yayi tunanin hakan shiyasa wannan karon yaki raga musu sam, ya dinga ragargazar su da ruwan addua da ayoyin Allah suna gunjin kuka sosai, sai da ya tabbatar yayi musu babbar illah, sannan ya nemi su fice su barta bari na har abadah.

“Ina zamu? Ka riga ka kone mu.”

“Ku koma chan wajen wadda ta turo ku.”

Ya basu amsa yana Kara daga ruwan zai sakè shekawa, ihu suka saka sai kuma ammyn ta hau attishawa ba kakkautawa tana wata irin mimmikewa tsawon lokaci tana a haka kafin a hankali ta shiga sauke ajiye zuciya. Duk yadda raihana taso boye kukanta, ta kasa kuka take sosai kamar zata shide, kukan tausayin zaluncin da akayi ma ammyn. Kallon ta hydar yayi yace ko zata je waje? Malamin yace a barta itama akwai bukata a duba ta, haka akayi kuwa itama aka yi mata amma ita babu komai.

“Kina azkar ko?” Ya tambaye ta.

“Inayi malam.”

“Masha Allah, ki cigaba Karki daina, azkar tsari ne sosai amma sai wanda ya gane, ita kanta mahaifiyar ku da bata addua da abin sai yafi haka, domin so akayi a haukata ta, ta shiga duniya karshe ta mutu irin wannan mutuwa ta wulakanta, amma karfin addua da azkar din da take ya sa ta tsallake wasu tuggun, dan haka ku dage da azkar kamar yadda manzon Allah SAW ya koyar damu, in sha Allahu babu wani mutum ko aljan da zai samu damar cutar daku.”

“In sha Allahu Malam, mun gode sosai Allah ya saka da Alkhaiiri.”

“Amin ya Allah, zaku cigaba da kawota yanzu duk Asabar da lahadi muna cigaba da yi har sai mun samu ta samu lafiya gaba daya.”

“In sha Allah, mun gode.”

Sallama sukayi ma malam din suka shigo mota da ammyn da tayi shiru bata ce komai ba sai kanta da ta rike da yake mata wani irin ciwo. Dafa mata kan raihana tayi ta shiga yi mata addua tana tofa mata, sai kuma ta jawo kanta ta dora a saman cinyar ta, ta cigaba da matsa mata kan a hankali.

***RQ***

**63**

*****Har suka isa gida babu wanda ya sake daga maganar da Malam din yayi, dukkannin su kowa da abinda yake sakawa a ransa. Sau daya Hydar yayi magana bayan ya daga wayar Babbo daga nan kowa yayi shiru. Daki Raihana ta wuce da ita suna zuwa ta kwanta saboda ciwon kan a hankali kuma sai bacci ya soma daukar ta, gyara mata kwanciyar yadda zata ji dadi raihana tayi sannan ta dan karo mata ac dakin ganin tana zufa ta goshi sannan ta jawo mata kofar dakin ta dawo falon. Shirun da taji yasa ta gane sun fice daga gidan sai ta fara tunanin abinda ya kamata tayi musamman dasu Dadah zasu zo ya kamata tayi girki ba sai Ya nabeela ta kawo ba. Kitchen din ta wuce ta duba abinda zata bukata babu kayan miya sai kayan abincin a store kawai. Mayafin ta, ta yafa ta fito zuwa bq sai taga malam Yahya tare da baba maigadin yana ganin ta fito ya taso da sauri.

“Hajjaju Kina bukatar wani abu ne?”

“Eh malam Yahya, wai da cefene nake so ayi mana.”

“Sai naje ai, me ake bukata?”

“Kayan miya.”

“Toh ba damuwa, zaa samo hajjaju.”

Kudin da ta dauka ta mika masa yace

“A ah Oga zai bada kudin ai, kiran sa kawai zan.”

“Toh,Nagode.”

Ta juya zuwa bq su gaisa da Hajara shi kuma ya dauki mota ya fita. Sai da ya isa kasuwar sannan ya kira Aryan din ya sanar dashi yazo cefene.

“Wa yace ayi cefene?”

“Hajiya ce, ta bada kudin ma nace ta barshi zan gaya maka.”

“Ok, ka siya duk abubuwan da muka saba siya, zan tura maka kudin sai a siya.”

“Ok gani ma a kasuwar.”

“Ok! Bari na saka maka.”

Ya ajiye wayar ya tura masa kudin ya siyi komai da komai har abubuwan da raihanan bata ma san suna existing ba ya kai mata. Mamaki ne ya kusan kashe ta ganin uban kaya kamar zasu dawwama a gidan. Ta riga ta dafa white rice tuni dama sai kawai ta hada kayan miyan da chicken tayi stew ta hada musu hadin salad 🥗 me salad cream ,baked beans da egg. Ta gama ta dora su akan dinning sannan ta sake komawa ta duba Ammy still tana bacci. Dawowa falon tayi ta zauna shiru har aka kira laasar sannan ta tashi ta yi alwala tazo ta yi sallah a falon tana idarwa sai gasu Ya nabeela sun dawo. Dadi taji domin zaman dama ya isheta shiru ita kadai. Abinci ta kawo musu suka ci suna hira itama sai a lokacin ta dan ci kadan sannan ta koma kitchen din ta dora ruwa ta dafa spaghetti dan ba lallai kuma rice din ta ishi kowa da kowa ba, ta dora kenan Ammy ta tashi sai ta tafi wajenta ta barwa khadija ta karasa mata. A zaune ta samu ammyn tayi wanka tana gyara daurin dan kwalin kanta, mamaki Ya kama raihanan ta karasa da sauri wajenta ta tabbatar da abinda idanun ta suke gani.

“Menene kike kallo na haka auta?”

“Ammy? Kin sanni? Kin ganini dama?”

“Kaji min yarinya, ni kike tambaya ko na gane ki? Tabbin jam.”

“Wayyo dadi, wallahi ammy na zata kin manta ni, dan Allah ammyna kin tuna ni?”

“Ikon Allah, kin taba ganin uwar da ta haifi da ta manta shi? Duk girman da zakiyi auta ba zan manta ki ba, duk kuwa da shekarun da yawa amma ke din dai kece.”

Rungume ta tayi tana kyalkyalewa da dariya, sai kuma ta d’ago cikin tsananin farin ciki tace

“Sannu Ammy, kan naki Ya daina ciwo?”

“Um da sauki, sai a hankali. Ina yayannaki, banga Abubakar ba, Allah yasa yana raye.”

“Kowa yana nan ammy, Abby, Dadah, babbo da su Hamma na, duk suna nan, su Dadah ma daf suke da karaso wa.”

“Masha Allah, ashe ina da rabon sake ganin su dama?”

“Kwarai da gaske, al’amarin Allah!”

“Lallai kuwa al’amarin Allah, Alhamdulillah Allah shine abun godiya.”

“Wallhi ammy.”

“Ina Aryan? Ina Nabeela?”

“Shi ya fita, Ya nabeela tana falo.”

“Tashi muje falon toh.”

Ta mike tsaye, rike hannun ta Raihana tayi har sun kai kofa sai kuma ta tsaya

“Auta, nan gidan waye?”

Kallon ta Raihana tayi da sauri, sai kuma tace

“Gidan Ya Aryan ne.”

“Duk da sauye sauyen da gidan ya samu, be chanja min ba ko kadan daga yadda na sanshi.”

Sai idon ta

Please Login or Register in order to submit comment