gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading DOCTOR ILHAM zuciya Cikin Ruɗani By Amira Saminu Chapter 9 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana shiga ta kwanta wani baccin wahala ya yi ,gaba da ita .''"

WASHEGARI

"Bassira ta shirya tsaf Bayan ta gyara ko ina gidan ta ta yi , gidan kawata a tsan zata huni hunin ranar fira kawai suka"

sha abinsu har sai da Sani ya Dawo sannan ya dauko ta suka Dawo gida abinci suka ci suka suka shiga firarsu ta masoya .''

"Tana ta shi ta yi, sallah ta sauko suka hada abin break Bayan Sun Kammalla kowa yaje ya shirya sannan suka halara"

"a danning suka fara antayama cikinsu abinci ta Riga kowa fida hannunta dan Bata jin dadin abinci Haka ta tashi ta nufi daki dama ta shirya ta dauko mayafinta ta saka ta dauko Jakarta ta fito, ajiyar zuciya ta sauke ta ce'' Ammi zan fita .''"

"Ina zuwa kuma yanzu ?"""

Zan je wajen aikin nan ne mantawa nayi nafadamaki na samu wanan hidimar ce ta saka na manta .''

A'a Masha Allah Allah yasa Alkairi cewar Alhaji .''

Amine Baba sai na Dawo .''

A Dawo lafiya suka yi mata ta fita mai Napepe ta tare ta fadamasa anguwar da zai Kai ta ya fadamata kudinsa sannan

"ta shiga Sun dan yi tafiya kafinsu iso ,suna isowa ta bashi kudinsa ta shige gidan ,Yana cikin bacci yaji ana Nocking ta shi yayi yazo ya buge kofar ganin ita ce yasa ka murmusawa Yana rumgumo ta , dan buge hannunsa ta yi ,ta ce'' ka shirya mana kafito mu tafi Kai nake jira , babu musu ya ce'' To Muje ki ta yani wanka .''"

"Harara ta Ballamasa ta ce'' naki bazan yi ba ?"""

Kai tsaye Haka Cutie .''

"Shiru ta yi ,masa Hakan yasa shi tashi ya tafi ya shirya sai da ya kusan Kai Awa day sannan ya fito suka huce Asubiti"

"*CLINIQUE DU KATSINA* suna isa suka shiga ciki nan suka hadu da D.C Mansoor Bayan ya mata wasu Yan Tambayoyi ta amsa masa ne yasa Aka de bi jinin ta da fitsari ya Kira Norse Asiya ta tafi dashi ,Sun dan jima sosai kafin a Kammalla sannan Norse Asiya ta Dawo dauke da rsultat ta Mikewa D.C Mansoor sannan ta juya ta yi tafiyar ta"

",dubansa ya maido wajen Safiya ya ce'' Flicitation Mdn .''"

"A dan razane ta ce'' Pourquoi fa ?"""

Kina dauke da ciki wata biyu .''

Da sauri ta mike tsaye tana kallon Kitty da D.C ta ce'' ciki kuma har wata biyu wani marayan Kuka ne yazo mata

tareda fadawa jikin Al'ameen ( Kitty ) tana fadin ni dai Banason cikin nan a cire mani shi Bana kaunarsa wayo Allah na bani na bani na lalace nashi ga Tasa'in da tara .''

"Jikin Al'ameen da ya yi , sanyi ne ya saka shi daga ta tana bubuga bayanta alamar rarashi cike da damuwa ya ce''"

Muje gida za muyi magana .''

Babu musu ta mike tsaya Doctor ne ya kallesu ya ce'' ga wanan Ordonnance din a siyama ta magungunan nan ya

"zamana tana shan su a kan Lokaci ,kafar ya yi , yaja hannunta suka fita suna fitowa suka shige mota sai rizgan Kuka take tana nadamar abinda ta aika ta har suka iso gidan Kitty Bata dai na Kukan ba ,parking ya yi , yafito tare da zagaya wa ya Bud mata kofa tare da sungumota suka shiga ciki a falo ya dire ta ya zauna kusanta cike da muryar rarashi ya ce'' Cutie gaskiya ban ji dadin Kika aika a asubiti ba sai ka ce bakisan ko Waye uban dan cikinki ba kenan dama ba so na kike ba .''"

Ai Kai naga Kana Sona tunda har ka karfi mutumci na ba aure sannan ko maganar baka so ina yi maka Haka kuma

zaka gudu ka barni da wanan wahalar kuma in haife gaskiya ni bazan iya ba cire shi zan yi Wallahi .''

Ki gane ina sonki Dady ne baya Yaki ya mani aure shine .''

Gudan balligi da Kai Haka zaka ce wai bazai maka aure ba ba ka dai fito da matar ba .''

Sorry ki yi hakuri karki zubar da wanan cikin zan kula da shi kuma in dauki nauyin komai na shi in sha Allah .''

"Mikewa tsaye ta yi, ta ce'' wallahi bazan iya ba Haka kawai sai Na haifi dan shege ina yar sunna sai de kayi duk abin"

da zaka yi amma sai na zubar da shi .''

Wani uban mari ne ya sharara mata ya ce'' dan nawa ne dan shege Ashe baki da mutumci Safiya Wallahi kibani

mamaki .''

Karya na fada ba shegen bane fadamin in ji a aure muka same sa ne kuma ka jini da kyau ko ka fito muyi aure Kona

je gidanku da wanan cikin tunda kace kar na zubar da shi nasar da su sai su tsaida ranar aurenmu .''

"Tana gama fadan Haka ta yi tafiyar ta fitowa ya yi , Yana kiranta amma ina har ta tsaida mai Napepe ta shige shi ko"

ya ja suka yi tafiyarsu .''

Ilham da ta tashinta Kenan ta yunkura zata Mike taji duk jikinta Yana mata ciwo wani marayan Kuka ta saka tana

"komawa ta kwanta ,da sallama ya shigo tareda karisa wa wajenta Yana fadin Albi na barka da safiya a she kin tashi.''"

"Hararen sa ta yi , tana juya masa Kai baya ,'' wai fushi ake dani bara nazo na kara sai in yi rarashi .''"

Wani Murmushi da Bata san lokacin da Zoma ta ta saki tana fadin banaso Wallahi .''

Dariya ya yi Yana kariso wa wajenta ya janyo hannunta ya ce'' Ilham hakika Naji dadi kuma nayi farinciki sosai da

"Allah ya mallakamin ke a matsayin mata kuma Kika bani Abu mafi tsada a rayuwarki bansan wace Iriyar godiya zan yi maki ba ina kaunarki Ilham Allah ya barmani ke ya Bamu zaman Lafiya da Hakuri da juna abar Alfahari na ke din daban kike da sauran mata ke zinariya ce Ilham bansan ya zan musultamaki Irin baiwar da Allah ya yi, maki ba .''"

"Murmushi ta yi ,ta ce'' Kamar yanda Allah yabani miji na gari ba nima ina godiya ga Allah Allah yakara mana"

kwanciyar hankali da Hakuri da junanmu .''

"Amine yafada Yana sumbatar ta tareda daukarta ya yi , toilet da ita sai da ya wanke tsaf ta yi, ta tasarkake Kanta"

sannan suka fito nan ya Taya ta shirya wa Bayan Sun Kammalla ne ya ce'' Rayuwa ta Muje kici abinci ko .''

"Bata ce masa komai ba dan ita har yanzu kunyarsa take ji ,'' Murmushi ya yi ,tareda janyo ta da dan karfi ,da sauri ta"

ce'' wash ?

"Dariya ya yi , tareda sungumota suka fito falon tana dire ta a Capet ya je danning ya dauko masu breakfast dinsu"

suna fara cine har zata yi magana Ammi ta banko masu kofa da karfi tana yi kan Ilham tareda................................................................................

27/03/2022 15:38 - Mom Star :

*DOCTOR ILHAM*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS
'<*



"```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alalaminmu ancinmu.```"



*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*Na*

*Mom Khadija*

{{YAR LELEN NOBLE ce}}

34/35

Tareda tsayawa gabanta ta ce'' ke yar Marasa mutumci karuwa mai lalaci nazo ne Naji Sakamako ko yasa meki a

budurwa ko sabanin Haka .''

Cike da Mamaki suke kallonta da Ilham batayi tunanin Ammi ta daka Iskanci ta shanye shi a cikinta wai har ta kalli

"tsabar idonta tana fadamata Hakan wanan wace Iriyar uwar miji ce ,katse mata tunani ta yi , ta hanyar cewa dake nake kinyi jugume kina saurare na , fashewa tayi da Kuka tana Mikewa tsaye ta ce'' ni bani da amsar tambayarki sai"

"dan ki yake da ita ,tana gama fadan Hakan tafara tafiya da kyar har ta iso daki ta fada kan bed tana ta Kuka ,'' Dan"

"fata fuska ya yi , ya ce'' Ammi me Hakan ke nufi me Kika aika ta yanzu a gaban SURIKARKI Kika fadan Hakan .''"

To shanyaye daga aure jiya har ta gama da Kai ko Daya ke su din dangin mayune dole Hakan ta faru .''

Naji Ammi kiyi hakuri bazan Bari ta shanye ni ba zan yi ta zabga Sallolin dare kuma kema ki Taya ni yafada Yana

gumtse dariyarsa .''

Banason iskanci Musa ni zaka yi ma rashin kunya ne .''

A'a Ammi ki zaune ki huta an jima na Kai ki gida .''

Banaso Kai ka kawo ni ne kuma ba zama nazo yi ba dan Haka kaga tafiya ta .''

Fita tayi shiko yabi bayanta har sai da yasa ka ta Adaidaita sai masifa take amma ko kyalla bai ce da ita ba bare ya

amsa mata tana shigewa suka tafi shima ya Dawo gidan direct dakin da Ilham take ciki ya nufa ya sa meta kwance tana Kuka wajenta ya kariso tareda janyota jikinsa ya ce'' Amarya ta dan Allah kiyi hakuri nasn Ammi Bata kyauta ba nasan ki da Hakuri ki kara da Wanda kike da ba Tun yau Kika Saba ganin Haka ba gashi kuma duk Irin abin da take maki sai da Muka auri juna to a nan ne Zaki Nuna mani kallar naki hakuri Haba ke fa jaruma ce yar Aljanah.''

"Shiru ta yi , tana share hawaye ta amma Bata ce komai ba Haka dai yayi ta rarashi har yasa mu ta saki jikinta suka"

Dawo Wasa da Dariya .''

"Haka rayuwa ta yi , ta tafiya in da Ammi kullum sai Tazo dan ta kurawa Ilham har ta samu ciki Haka take rayuwa babu"

"dadi a cikinta sai de in mijinta Yana gida amma Ammi sam Bata raga mata wani ta yi ,Kuka wani kuma mamaki amma Hakan bai sa ta Sanar da gidansu ba dan ta san Asha Bata da dadi da hakurin magana shi yasa ma Bata Sanar da ita ba sai de in ta Kira ta suyi Waya bisa kan Abin da ya shafi rayuwa ko yanda zata kara kulawa da mijinta sai ta katse Wayar .''"

Asha ce kwace akan cinyar Mama yaranta kuma suna wasa da Inteesar ce tsale tsale suke abinsu nan Saf ya kira ta

"dagawa ta yi , Bayan Sun gaisa ya ce'' Matar Saf wai yaushe Zaki dawo Wallahi akwaye matsala fa.''"

Dariya ta kyalekyale da ita ta ce'' Sorry sai kanwar da Aka baka ta sak ka .''

Af toh kema sheganta Zaki yi man Irin na Al'hassan wai cemin yake gabro ni dai dan Allah ki Dawo .''

To zan Dawo amma da sharadi sai na bikin Ilham idan ta haihu ka yarda .''

Haba yanzu fa kina cikin wata na biyu Kuma ki Dawo da Watan goma in da rai .''

E'e in ba Haka ba gaskiya sai de in yi zamana ko kazo muga Juna ka koma.''

Gaskiya na yarda da Hakan idan Na jayeki wa zai kulamin da Amarya ta .''

Hmm ba dai zaka Bari ba ko zan fadama Musa fa ya dauki mataki a kanka .''

"Dariya ya yi , ya ce'' zan zo nan da jibi sai nayi sati na koma .''"

To ba damuwa Allah yahomin Kai lafiya mijina .''

Amine matar Saf ki kullamin da kanki kafin nazo ta Dawo hannuna .''

Insha Allah Karka damu ka dauka an gama sahibi na.''

"Katse kiran ya yi , ita kuma suka ci gaba da firarsu da Mama.''"

Tunda daga ranar da Safiya taje asubiti ita da Al'ameen Bata sake ganinsa ba ko ta kira shi bata shiga in ma ta

"samesa to bazai daga ba duk tabi ta rame ta kanjame ta yi baki ga kuraje da Suka fito mata burma burma Sun Bata mata fuska kullum tana cikin Hijjabi Bata Bari su hadu da kowa a gidan dan tun safe idan tafita aiki sai ta daura ci Ammi ta shiga sallah ko Batanan take shigowa kuma da ta shige dakinta Bata fitowa abinci a sace take cinsa yau de karya ta Kare sabida a tunaninta ba yanzu Ammi zaka Dawo ba dan ta san idan ta fita sai yamma lis take dawowa Sai gashi yau Allah ya Dawo da Ita kwance take sai bacci take sha abin ta babu Hijjabi a jikinta ga cikin nan yakara fitowa dan yanzu watansa uku sabida koshin da ta yi , sai ya kara fitowa ,'' turus Ammi ta yi , tana kallon Ikon Allah me take shirin gani Safiya da ciki duk Irin tsananin da ke yi masu amma a banza shine taji ta zubda masu mutumci da kimar gida ajiyar zuciya ta sauke ta huce daki sai da ta dauko dorina mai Harshe Hudu duk ta sha mai sai kyalli take sannan ta dawo falon tana cikin baccinta mai dadi ta ji saukar bulala har cikin kwakwalwar ta Batasan lokacin da ta tata shi tana kwarara ihu nan Ammi taci gaba da zabga mata ita ita ko sai ihun neman dauki take amma babu kowa a gida sai da tayi mata lis yanda ko yatsan hannunta bazata iya dagawa ba ta kyale ta tareda zaunawa ta Kamo kunnenta tana janyota da shi ta murde shi ta ce'' dan Ubanki sabida kin daukeni yar Iska shine Kika je Kika aika ta faskanci dama tunda ganki da watsan shegiyar yar Asarar yarinyar Ilham nasan kema sai kin yi Irin Nata halin ta koya maki karuwanci ta aure yayanki yanda asirinta zai rufu ke kuma ta tona naki ko walahi sai kin fadamin Waye uban yaron nan .''"

Cike da Tsoro da rawar jiki Safiya ta ce'' wallahi ba laifin Ilham a wanan harakar dan tun kafin mu shirya da ita nake

yi abu na kuma ita kanta Bata sani ba da ta hanina kuma Al'ameen dan gidan Aunty baraka ne ya mani ciki .''

"Al'ameen ?""Ammi tafada ta ce'' zanci uwarki dan kanwar tawa kike son lakama ma laifi ne kuma ina Kika san shi har"

Kuka hadu da shi .''

Lokacin da yaya ya Dawo daga karatu ranar Muka hadu da shi tun daga ranar muka fara sabawa da shi har ta Kai ni

"da ina zuwa gidansa idan shi bai zo ba soyayar sa da kaunarsa suka shigeni sosai ta yanda bazan iya hanamasa Dukan abin da yake bukata daga gareni ba mun kai Shekara biyu fa haduwa yane mi da Na bashi kaina in ba Hakan ba Zai iya rasa ransa duk yabi ya damu sai hada gumi yake Ashe abokansa ne suka sakamasa maganin ta da sha'awar kasancewar ranar haihuwarsa ce wai ya more ranar ni kuma bazan iya rayuwa in ba Shiba ganin zai mutu yasa na bashi Kai na har ya samu natsuwa tun da ga wanan lokacin Muka fara rayuwa kamar mata da miji har ta kaimu ga munsamu ladan zinar da Muka ke aikata wa ,sunkuyar da Kai ta yi, tana Kuka sai ta baka tausayi sake lakada mata duka Ammi ta yi , sai da taga tana fitar da jini daga kasanta sannan ta kyale ta shigowar Alhaji Kenan Yaga wanan Tashin hankalin ga Safiya na zubar da jini Ammi ta yi , zaune sai lalatsa Waya take kamar ba uwarta ba Hakan yasa ya sure ta ya yi , asubiti da ita taimakon gagawa Aka Bata ta hanyar ta karbanta suka yi ciki da ita tareda dakatar da Alhaji .''"

"Ganin Sun fita yasa Ammi saka Hijjab din ta ta yi , gidan Musa lokacin baya gidan ya fita Ilham take kwance tana jin"

"jiki sakamakon jaririn cikin dake Bata azaba tana shigowa tayi kanta tareda shake mata huya ta ce'' dan Ubanki Irin masikancin da kike yi ne Kika koyawa Safiya dama ta tabata ke karuwar ce mijinki ya rufamaki asiri Wallahi sai nayi Ajalinki uban kowa ma ya huta nan ta shiga duganta hannunta day tana shake da huyan Ilham ta kar ta samu Allah ya taimaka ta tataro Dukan karfinta ganin fa zata Ila tata yasa ta ture ta ta fito daga gidan a guje ita m Ammi ta biyo ta da gudu ta tare mai Napepe ta ta shege sai da Suka fara tafiya ta fadamasa inda zai Kai ta ,ita ko Ammi nan ta yi , ta tsayuwar babu Abin hawa har su Ilham suka bacewa ganinta sosai ta ji haushin Hakan ,su Ilham Na isa gidansu ta fito ta ce wa baba mai gadi ya bawa mai Napepe kudinsa har ta fito ,'' ganin yanda take babu hijab ba mayafi bare takalmi ya sa shi Mikewa ya basa kudinsa ,tana shiga falon Mama ce da Asha babu ma kowa a gidan dan tunda yaran Asha suka tawo suke tafiya makaranta da Inteesar wani marayan Kuka ta saki tana fadawa jikin Mama ,'' in hankalin Mama da Asha ya yi , dubu to ya ta shi nan suka shiga tambayarta ganin Kuka bazai tsaya ba ne ya sa Asha janyota jikinta tana shafa bayanta alamar rarashi sai da ta tsagaita kukanta sannan ta ce'' Aunty ba rarashi nake nema ba dubanta ta mai do ga Mama ta ci gaba da cewa Mama ina son yau ba gobe ba ki Sanar min miye tsakaninki da Ammi na gaji da cin fuskar da take min yau fa bidar kasheni ta yi , tana kirana karuwa mai lalasisi me nayi mata bansan hawa ba bare suka ta dauki karan tsan ta daura min Wallahi ta ci mutumci auran dan ta da nake yi da ta gane ruwa ba sa'an kwando bane.''"

Tunda ta fara magana Mama take kallonta dan tunda Take da Ilham Bata taba tunanin yi ma wani rashin kunya bare

Babar Mace kamar Ammi cike da rarashi ta ce'' Ilham ki daina Kuka kiyi hakuri komai ya huce miye abin mai da shi baya kiyi hakuri kin ji .''

Mama ba hakurin ki nake bukata a yanzu ba ni kawai ki Sanar da ni Bana son jin komai in ba abin da nake son sani

ba .''

Kuma Mama ta fashe dashi tana sunkuyar da Kanta sai ta ji abin da ya huce Shekaru masu yawa Yana dawo mata

yanzu .''

"Ganin Mama baza ta fadama ba yasa Asha cewa ki zauna ni zan Sanar da ke ,'' Babu musu ta zauna tana jiran fewar"

Asha Dady ne ya shigo dan yaji komai Ilham ke fada dan tun shigowar ta shima ya danno Kai .''

*TUSHAN LABARI*

"Alhaji Muhamed Bisa, baban abokine ga Alhaji Mudanssir wato ( baba ) dan tsananin shakuwar da Suka yi ne yasa"

"har suka zamana ana masu kallon Yan uwa a tare suka Kammalla makaranta su tun basuda ko sisi Haka suka fara akin gini kuma suna neman aiki abinci a tare suke cikinsa komai nasu Irin day Hakan Allah ya nufa Muhamed Bisa samin aiki inda Mudanssir har yanzu takardunsa basu fito ba har Muhammad yafara aiki har ya taka baban matsayi ya dauki Mudanssir aiki sosai yaji dadi da farinciki Kuma suka je gaban iyayensu nan suka ta yashi murna inda Mamar Mudanssir ta yi , ta ma Muhamed godiya har da kwallar ta kuma ta je gidansu ta yi ma iyayenshi godiya dan Baban Mudanssir ya jima da rasuwa ana cikin Hakan ne Bista wato Mahaifin Muhamed yafara masa maganar aure shida Mudanssir tareda gargadin kar Wanda ya Dawo masa ya ce'' bai samu mata ba dan duk wace ya ga dama zai hadasu da ita jin Hakan ne ya sa Muhamed saka manajensa ya samosa Yan mata Haka Aka yi Kai masa su Yana cewa a samu wato cikin wadan da Muhamed ya ce'' ba ya sone Mudanssir ya yi kitibus da Murja ita da kawar ta dan Murja ta so Muhamed ya aure kawar ta Hajara amma ina sam yaki yarda har suka fara shan soyayarsu kullum sai ta yi , ma Mudanssir zan tsen Hajara wajen Muhamed Bisa amma shi Bata gabansa wata Rana da marice sunje Shopping shida Mudanssir da Murja shiko Muhamed dan rakiya ne Bayan Sun gama ne suna fitowa Maryam zata shiga ita da familly Nata tunda Muhamed ya hangota yake ta kallonta dan har da budan faduwa ya yi , sosai yarinyar tata fi ,cike da siyasa ta dauki photon ta sannan suka tafiyarsu ,Murja na ganin wacce Muhamed yake kallon yasa tafara kishi da ita sam ta ji Bata kaunar ta a Haka yasa Managen sa nemo masa Maryam har Allah yasa suka gano gidansu Bayan sati day ne su Muhamed zuwa gidansu Maryam suka saka a kayi masu sallama da papanta ya masu ISO zuwa falon baki bayan Sun zauna ne suka shiga gaisawa nan Mudanssir yafara koro masa maganar dake tafe da su ,sosai papan Maryam ya ji dadi dan hanyar da Suka biyo ita ce daidai Hakan yasa ya ce'' tabbas Kuma hakika Naji dadin Hakan da Kuka yi amma bazan yi saurin baku ita ba har sai Naji daga gare ta ina son ku dawo nan da sati day .''"

Godiya suka yi masa sukayi sallama suka Baro gidan .''

Papa Yana shiga gida ya samu Momy ya fadama ta abin da ke tafe da su Muhamed sosai ita ma nayi murna dan

"yanzu ba yawan samari suke neman izinin iyaye ba suke fara soyaya da Yarinya har suzo gidansu ta ce'' to Babu damuwa ?"" Zuwa an jima da marice dan Sanar da Maryam din idan Sun dawo daga School .''"

Gaskiya dai kam amma ke kina tunanin zata yarda ne .''

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce'' ina tunanin Hakan dan Maryam bazata taba watsamana kasa a Ido ba .''

Hakane nima Na yarda da Hakan .''

Bayan an yi sallah La'asar Maryam ta Dawo daga School sabida rattrapage suka yi tana shigowa sai da ta watsa ruwa

ta huta sannan ta ci abinci nan Momy taje Sanar da ita maganar Muhamed a nutse ciki tautausar maganar ta dan karamin bakinta Yana motsawa hankali tayi kasa da Ido tana wasa da yatsun hannunta ta ce'' To Allah yasa Alkairi a ciki ni bazan iya jayaya da Dukan zafin ku gareni ba dan nasan na gari ne Zaku bani dan Haka bani da Abin fada face Allah ya saka Alkairi ne ke tafe da shi .''

Amine Maryam Allah ya maki Albarka .''

"Amine Momy ,'' Bayan Sun gama firar ne ta shiga gyara gida da dora girki tana Taya masu aki .''"

Tun lokaci da Muhamed ya zo gidansu Maryam Papa ke bincike Akan sa ganin babu wani aibu garesa yasa bai yi

"yinkurin hannashi auren yar sa ba ,'' satin da ya basu nayi suka Dawo nan suka ji Sakamako mai kyau .''"

Bayan wasu watanni Aka fara maganar auren Mudanssir da Murja sai kuma Muhamed da Maryam sosai Murja ke jin

"haushin Maryam dan ta fita da komai ba kyau tarbiya girmama na gaba da ita dama Wanda ta girma dan kar girman ta ya fada sosai take Kare mutumcinta dan har yanzu Bata Bari Muhamed ya taba ko da hannunta ne har Aka daura masu aure ranar biki an sha shagali anyi facaka da dukiya har Allah yasa amare suka tare gidansu day sai de kowa da Nata bangaren babu ruwan kowa da dan uwansa sai ma Maryam ce idan ta gaji da zaman taje wajen Murja amma babu abin da take mata sai habaici Hakan bai sa Maryam ta ji haushi ko ta taki komawa wajenta Haka rayuwa ta ci gaba da zuwa Murja sam Bata kyautata ma Maryam sai mugunta wani lokacin har ta nemi yin dambe da ita amma Maryam Bata yarda da Hakan ba dan ta san Murja ja mata shairi take son yi tunda tana da ciki sai de ta koma part din ta ta ci Kuka idan abin da Murja ta yi ya Bata mata rai musanman Gorin haihuwa da take mata amma duk abin da ake mazajensu basu sani ba dan in a gabansu ne to

Please Login or Register in order to submit comment