gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading DOCTOR ILHAM zuciya Cikin Ruɗani By Amira Saminu Chapter 11 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Maganarta wayarta dake gefe ta yi, kara dubawa ta yi , taga"

"sunan Doctor wata iriyar buga gabanta ya yi da karfi kamar zai fasa kirjinta ya fito cike da faduwar gaba ta ga Wayar amma ta kara cewa komai ,sai Doctor da ya ce'' Ilham kizo a kwaye matsala ,hurgi ta yi, da Wayar ta koma dakin a guje tana kallon na'urar da ke Nuna nunfashin Inteesar Yana tafiya daidai sai taga Yana rage karfi , da sauri ta zura rigarta ta nufi wajen tana fito da daga in da kanta yake ciki idonta a lumshe Bata ko kwakwaran motsi gefen shafarta tafara shafawa tana dan bubuga kumatunta da yatsun hannunta biyu ,shi ko Doctor Yana aiki da wata yar karamar na'ura Yana danna mata a gabanta dan nunfashin ya daidai ,ganin sai kara ragewa yake ya sa Ilham ta fashewa da Kuka tana rumgumo Inteesar ta ce'' Intee na dan Allah Kar ki rufe idonki gani ni ce fa Auntyn ki nice Ilham dan Allah ki tashi kar ki tafi ki barni babu abin da nafi kauna a rayuwa sama dake Intee kar ki man Haka dan Allah .''"

"Cikin galabaitaciyar murya ta yi , Murmushi ta ce'' Aunty na ki barmani Kuka Addu'ar ku ka dai nake da bukata nima"

"ina sonki kuma ina maki fatan alkairi Haka Allah ya Gadara ma rayuwa ta ba mai tsayi ba ce ina sonki Aunty na ki ya femin keda su Mama kuma na yafewa dukan Wanda ya yi ,min laifi dama Wanda na yi wani Irin tari ne ya taho mata sai Alan jini Haka Doctor ya kara kaimi wajen dAnna abin amma ina tun nunfashin Yana 99 har ya Kai 20 Yana ganin Haka kamar mahaukaci yakara danna mata Abin daidai ta nunfashin amma ina Sai da ya gansa 5% sannan ya hakuri Yana Dukan wani table dake gefensa da sauri Ilham ta shiga jijigata tana Zuma salati tana Kuka kamar ranta zai fita tana sambatu Intee me yasa Zaki tafi ki barni bacin kince ba zamu taba rabuwa ba me yasa bazaki ciki Alkawari ba Intee na nice fa nice Ilham dan Allah ki tashi Mama zata ji farinciki dama sauran Yan uwa Wallahi zan maki Dukan abin da kike da bukata Intee na sai da nace ki rinka shan magani amma baki sha gashi yanzu Zaki tafi ki barni rabuwa ta har abada Intee na ,'' karar na'urar ta dauke daga sauti da take badawa ya sa Ilham faduwa kasa sumamiya .''"

Da sauri Doctor da shima baya hayacinsa dan ya jima da son Inteesar a zuciyarsa dan babu baban burinsa da ya huce

ya aure ta yanayin ta ne yake gani kamar baza'a bashi ita ba shiyasa bai Sanar da kowa ba sai Ilham shiyasa ma Ilham Bata barin Inteesar yawan fita ko wani kula samari sabida Doctor amma gashi yanzu ya rasa ta daukar Ilham suka yi suka nufi da ita dakin duba Marasa lafiya nan suka dukufa wajen ce to Nata ran .''

"Tunda Ilham ta koma dakin Opration gaban Mama ya shiga lugude Yana bubugawa da karfi karfinsa sosai ta kara shiga damuwa sabida ganin yanda Ilham ta yi , hurgi da Wayarta ta koma dakin a guje ,Asha ji take kamar ta shiga"

"dakin da tsabar Tashin hankali ,''"

Bayan Sun yi nasarar ce to ran Ilham ta farfado sai kuka take tana wasu maganganu da batamasan tana yi ba nan

"suka mata Allura bacci dan sabida jininta ya hau sosai dan in ba ayi hankali ba cikin ta zai iya zubewa nan bacci yayi gaba da ita ,'' sannan Doctor ya fito Yana goge hawayen da yake boyewa su Mama na ganinsa suka nufosa suna tambayar lafiya dai ko .''"

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce'' Mama & Dady Allah yabaku hakurin rashi Allah ya jikanta ku yi mata Addu'a ka dai take

"bukata ,Asha da tunda Doctor ya fara magana ta kara koda motsi dan tayi glass ,Mama kuma sai da Dady ya kireta dan tafiya ta yi, zata faduwa tana rafka Salati nan ta rufe fuskarta da kirjin dady ta fashe da wani marayan Kuka .''"

A Haka suka saka hannun Aka basu gawar Inteesar in da Ilham kwata kwata Bata cikin hankalinta sai da ta kwashe

"Wata day har Aka gama Zaman takabar Inteesar Ilham Batasan wainar da ake toya ba Asha ce da Musa sai Safiya suna zaune kowa ya yi , jigum suna jiran farkowar ta Asha dake zaune saman gadan da Ilham take wajen kafafunta taji suna tabata kallonta ta yi , taga tana kokarin Bud idonta cike da Murna Asha ta ce'' Ilham din Mama kin tashi ne tafada tana Mikewa tsaye nan su Abul Khair suka nufo ta tana kokarin ta shi zaune nan ya kamata tareda gyara mata zama ,'' Kallon Asha ta yi , ta ce'' Aunty ina jin yunwa fa ?"""

Da sauri ta dauko plask ta hadamata tea mai kauri sosai sannan ta Bata sai da ta shan ka dan ta Mika mata ta ce'' ina

Mama da Intee na suke bangansu ba.''

suna nan lafiya Sun tafi gida yanzu zasu Dawo .''

"Fita Musa Abul Khair ya yi , ya sanar da Doctor nan suka shigo tare ya duba ta sannan yaja Musa suka fita nan yafada"

masa abubuwan da ya kamata Ilham ta samu da Yan shawarwari dan har yanzu jinin bai saura ba sai da Suka yi sati

sanan Aka sallama me su lokacin jikin yayi kyau sosai Kai tsaye guda suka Dawo bayan Sun huta ne suka sa taci

abinci tasha ruwa sannan ta ce'' Wai ni Mama banga Intee na ba tana ina ne.''

"Dady ne ya yi , gyara murna sannan ya fadamata cewa Inteesar ta rasu nan ya masu nasiha mai ratsa jiki ta hakuri"

"jurija da fatan Alkairi ,'' kallon Dady ta yi,ta ce'' shikenan yanzu bazan sake ganinta ba kuma bazan sake jin muryanta ba Ashe da gaske ta tafi Kenan .''"

"Dafa kafadarta Dady ya yi , ta kara Bata magana Haka dai ta yi , hakuri amma zuciya ta sosai take soyuwa .''"

Bayan sadakara kwana Arba'in na Inteesar Muhamed Bista.''

Nan Ilham ta tara ta koma gidanta shima Saf bayan kwana kwana biyu yayi tafiyarsa yanzu cikin Ilham da Safiya ya

kara girma ya fito yanzu Ammi ko kadan Bata shiga mutane baki ya mutu dan yanzu ko biki tatafi sai anyi gulmanta ana Nuna ta yau ma bikin Babar kawarta take ma diyarta aure ta shirya tatafi amma matar nan ta yi mata tass har zata zauna ta ce'' A'a Murja lafiya dai Waya gayatoki ko nima kin zo kiga Yana yin yar tawa ki kaima yarki ta lalata mata rayuwa ne dan Allah ki fitarmin daga gidan dangin Karuwai kawai .''

Sosai Ammi taji zafin maganar nan dama abin da take ma wani yau gashi anmata Ashe Haka Maryam take ji a zuciyar

"ta duk lokacin dana ai banta mata yar ta harda Bata taba aika tawa ba amma gashi ni n'a san yar tawa ta yi ,amma na ji zafi gashi har yarinyar da nayi sanadin mai da ita nakasashiya ban je nayi mata ta'aziya ba wani Kukan nadama ta fashe da shi tana cikin wanan tunanin ne mota tayi gaba da ita tareda taka kafarta nan ta fadi kasa somamiya da kyar Aka samu mutanan da zasu daga ta saka mota a Kaita a subiti Suna isa Aka Kiran Yan Sanda nan suka bincika wayarta Aka samu lambar mijinta suka Sanar da shi a asubitin da suke"

Nan ya kariso Yana isowa Doctor Yana fitowa ya ce'' Kai ne mijin marar lafiyar nan .''

"E'e Nine lafiya dai ko ?"""

"To lafiya amma ba lau ba matar ta tayi hatsari wajen tsaidar motar wanda ya Bud ta ya sa , ya taka kafarta Hakan"

yasa kafar ta tatake dole sai an yanke kafar so muna son saka hannunka .''

Girgiza knsa yayi ya ce'' yanzu Doctor sai an yanke kafar babu data dabara .''

Gaskiya nayi iya kacin kokari n'a amma Hakan bai samu ba Kawai yanke kafar shine mafita .''

Haka Alhaji ya saka hannu badan ya so ba nan Aka yi mata aiki Aka yanke kafar ta dan kwana biyu Bata farko ba tana

shi ta ganta babu kafa sosai wata nadamar ta sake ziyarta ta tana da Ta Sanin da Allah ya wadai da mai Irin Hali Irin Nata sai da jikinta yayi kyau sosai Sannan Aka sallame su .''

BAYAN WATA TARA

Ilham ce kwance sai juyi take da Alama tana labour ne Haka ta ci abar ta gida sabida ta sannan Yanayin aikinsu sai da

"faya ta fashe sannan ta Kira Musa Abul Khair dama Yana cikin anguwar nan ya kariso suka dauki Kayan haihuwa suka huce Asubiti suna isa ya Kira Mama ya Sanar da ita nan suma suna suka zo asubiti nan suka shiga Safa da Marwa suna nan zaune suka jiran Allah ya suke Ilham lafiya ,Aka shigo da Safiya ita ma tana labour da ka ganta sai kafi tausaya mata yanda duk ta Kare bama zaka gane ta ba ,Bayan ta kuma Ammi ce tana ba da kafarta cikin koyan tafiyar guragu .''"

Mama na ganta tata shi ta kama ta ce'' haba kema Murja me ya kaiki fitowa yanzu ba ki koda lafiya ki zauna bara sai

su karisa da ita ciki mana .''

Tunda Mama tafara magana Ammi ke kallonta cike da Mamaki mutume sai mantuwa babu ruwan shi da lamarin

duniya abin da ke gabansa kawai yake yanzu duk Irin abin da ta yi mata Hakan bai sa ta Nuna wata damuwa ba Kai gaskiya Allah ya wadaran mai hali Irin nata ya shiryar da shi .''

Sun dan jima sosai har Aka yi Sallah Mangariba babu Wanda ta haihu Haka sukayi ta rokon Allah suna Kai masa

"kukansu ,Haka ma Musa Abul Khair tunda yatafi masallaci bai dawo ba har Ilham ta haihu bai dawowa nan ta santolo Yan beby boy dinta Masha Allah da shi bazan iya masulta maku Irin kyau yaron ba dan ya kwaso kyau uwa da uba wai sai de muce Masha Allah ,'' Bata jima ba ita ma Safiya ta haihu ta haifo mace mai kama da ubanta saka wato Al'ameen Haka fito dasu Bayan an fito da iyayen dakin hutu ne Mama ta kalli diyar Safiya ta ce'' gaskiya dole in yi kishi ace sai da ta ga na tsufa ita kuma ta shigo dunya to nima zan je a tsanza min fata .''"

Dariya suka saka Dady ya ce'' To ai ko kin tsanza ba zai Kai tata dan ina gama kar Alhaji Mudanssir ya min kwace dan

ance da zafizafi ake bugun karfe tun yanzu ma nayi kame .''

Mama ta ce'' To ai da tsofuwar Zuma ake magani dan Haka ko kaje sai ka Dawo .''

Inji wa ya fadamaki bazan dawo ba nayi sabon jini.''

Cike da kunya Ammi ta ce'' ki Rabu dashi mana ke da Kika yi sabon miji me nene na kishi da wanan tsugudidin

kishinyar.''

Kuma fa hakane Murja kema kin yi magana .''

Kuka ne ya subucema Ammi dan Bata Masan yazo ba ta durkusa kasa tana Kamo hannun Mama ta ce'' dan girman

Allah Maryam ki yafemin ki gafartamin laifina nasan n'a yi maki laifin da har ki Mutu bazaki taba mantawa dani ba ki yafemin dan Allah badan nima kuma badan halina ba .''

Murmushi Maryam ta ce'' Haba mana Murja ya muna murna Zaki daga mana hankalinki dama ni ko tsan ban rike ki

a Raina ba kuma na jima da yafeme ki sabida Allah gafirar Rahim mu kanmu muna masa laifi ya yafemana bare kuma mu Yan Adam butulu ki Bari dan Allah ki manta da wanan maganar ta huce Bana son bara tana dawowa Bana .''

"Murmushi Alhaji Mudanssir ya yi, ya ce'' Alhamdulilah Mun gode ma Allah kuma muna cikin yi masa godiya hajiya"

Maryam Allah yasa ka maki da Alkairi hakika ke yar halak ce kuma kinsan Darajar dan Adam a madadin Matata muna godiya Sosai .''

"Babu komai Allah yafemana baki dayan mu nan Asha da Ilham ,da Safiya suka rumgume Ammi da Mama suna"

godiya ga Allah Daya kawosu wanan ranar farinciki bisa jindadi .''

Musa dake gefe sosai ya ji dadi Hakan Yana kara yima Allah godiya .''

Doctor ne ya shigo ta duba masu jego Yaga basu da wata Matsala sannan suka sallama mesu Haka Mama ke kulawa

"da Ilham da Safiya Ammi ma da yar guntuwar kafarta take dan yi wani Abun dama Mama tana hanata har Allah ya kaimu ranar suna Inda dan Ilham ya ci sunan Dady amma za suna kiransa da Najbudeen ,diyar Safiya kuma ta ci Sunan Inteesar sosai kowa ya ji dadi dan wanan Ammi ce tasa Aka saka sunan Inteesar din Masha Allah anci an sha shagali ba ka dan ba kamar basuma san inda dukiyar take fitowa ba Haka Aka Kammalla biki lafiya inda DOCTOR ILHAM Fan's suka zo Taya Ilham murnar karuwar data samu suma Sun Bada gudum muwarsu wajen Taya murnarsu Sunsha rawa ba kadan ba sunsa mu tarba ta musanman .''"

Bayan suna da sati day Al'ameen ya samu labarin haihuwar Safiya Haka yazo gidansu Bayan Sun gaisa da Alhaji ne ya

ce'' wajen Safiya yazo .''

Babu musu Alhaji ya mashi ISO dan yasan shi kuma jikanyar tasa tana kama da shi shi yasa ma ya shiga da shi ciki da

sallama a bakinsu suka shigo .''

Ammi ce zaune ita ka dai karanta jarida Bayan Sun gaisa ne Ammi ta kwallama Safiya Kiran nan ta fito kire da

yarinyar ta tana ganin Kittyn ta ta hade fuska tana fadin Ammi gani .''

Dama bani nake nemanki ba uban yarki ne ya zo .''

Sosai Al'ameen ya ji kunya dan a tunaninsa ba susan shine yama Safiya ciki ba .''

"Dan sunkuyar da Kai ya yi , ya ce'' Ammi ,Baba dan Allah ki gafartamin ku ya feman a hakika na sakaku cikin damuwa"

da nayi niyar tafiya ta na bar garin nan na fito Kenan na bi ta gefen wani Masallaci Naji Malamin Yana wa'azi bisa kan aikata zina da ma Dukan me yinta sosai Na yi na dama dan walahi naga masifu dan yanzu komai nawa ya lalace banida komai sai masa'antar da Aka raba mana ta gado Nida Yayana Hakan yasa n'a koma wajen Malam din Dana ji Yana wa'azi ya ce'' Hakan ba zai fasa Faruwa dani ba har sai Na nemi gafaran yarinyar kuma sai ta yafe shine nazo dan Allah ki yafemin Safiya kuma Wallahi na shirya auren ki ko yanzu ma a daura .''

"Hararensa Ammi ta yi, ta ce'' ka ci Albarkacin Murja Bata Da bace da ka gane baka wayoo Al'ameen wai Safiya tana"

yar uwa amma sai ita ka ci zarafinta Hmm tayi mata kyau Allah ya fe mana baki day .''

Hakika Al'ameen kaga jarabawa babu damuwa Allah yafe mana baki dayan mu sannan kuma kaje ka turo da

magabantanka sai anyi maganar auren .''

"Godiya ya masu Sannan suka barsu daga shi sai Safiya nan ya karfi yarinyar Yana kallonta Dago da kansa ya yi ,Yana"

aika mata da salon kallonta mai tafiya da ita bata san lokacin dana saki Murmushi nan suka dan taba fira ya yi tafiyarsa .''

Alhamdulilah yanzu dan Ilham ya kara murmujewa ya zama katuwa dan zaka dauka zai Kai Shekara biyu amma nan

Shekaransa day da wata takwas dan Harma ta yaye shi yanzu Haka ma tana da wani cikin sosai abul ke kulawa da ita babu abinda ta nema ta rasa sai Wanda yafi karfinsa .''

Kwanci tashi babu huya wajen Allah yau ne auren Safiya da Al'ameen Masha Allah duk da ba wani shagali Aka yi

sosai ba Amma Alhamdulilah ciki Rufi assiri Aka yi komai Aka gama lafiya amarya ta tare gidan ta yanzu suna rayuwarsu cikin tsafta ita tana samun Kulawa daidai gwargwado mai rufin asiri .''

Asha ita ma ta koma gidanta suna zaune lafiya ita da mijinta da yaranta dan yanzu ma tana dauki da ciki sosai Saf

ke kulawa da ita kamar ya maida ta a cikinsa tsananin lele suna rayuwa cikin farinciki dan yanzu kafin ta Kira Mama sai ta Kira Ammi yafi a kirga .''

Mama da Ammi kuma yanzu Sun zama manyan manyan kawaye kuma abotar mazanjensu Takara dankon karuwa

"Haka suke rayuwa dan yanzu Ilham Ammi tana ji da ita dan sai de in Bata ce tana son abu ba rayuwa mai kyau mai cike da nishadi suke yi har cikin Ilham ya Kai haihuwa ta santalo baby girl kyaukyawa Haka ma Safiya ta haifo Yan biyu Mac da Na miji ,Asha ma ta kara haihuwar dan namiji abin da taji ma tana burin samu sai yanzu Allah yabata ranar sunan Yara sunci manyan manyan sunaye Ilham Nata Ahlam ,'' Safiya nada Rashida da Irshad ,asha Dana Ammar .''"

Alhamdulilah ! Alhamdulilah ! Alhamdulilah !

Masha Allah duka yabo ya tabata ga Allah Subahanahu wata'alla duka duka anan na kawo karshan wanan litafin mai

Suna DOCTOR ILHAM inda nayi daidai Allah yabamu lada inda nayi kuskure kuma Allah ya gafartamin .''

Ina godiya Sosai masoyan DOCTOR ILHAM masu comment Allah ya saka da Alkairi ya biya maku Dukan bukatar da ta

duniya da lahira Allah ya sa kowa ta Rabu da iyayenta lafiya sannan ta gama da duniya lafiya nagode sosai da fatan Alkairin ku gareni Alkairi ya lulubeki Alfarman Annabi Muhamed (S.W.A)

Nagode sai mun hadu Bayan Sallah insha Allah

Nazo maku da tsarabar litafina mai Suna *INA KA SHIGE .'' Dan ta Yaku Munar Sallah ya kaimu ya sa muna da rai da

lafiya Allah ya sa mu shiga Watan Ramadan Allah ka kara tsarkake mana zuciyoyin mu ya sa mu aikata aikin Allah

Allah ya shirya Wanda basu saman bisa hanyar daidai Amine ya Hayu ya kaiyum ina sonku Fan's fatan alkairi gareku

da Dukan kowa ma

Wasalam daga taku Amira saminu kalla transa YAR LELEN NOBLE


Downloaded From https://arewanovels.com


Please Login or Register in order to submit comment