gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading DOCTOR ILHAM zuciya Cikin Ruɗani By Amira Saminu Chapter 10 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Murja zata saki jiki Su sha fira da Maryam Bayan Idonsu ne take gallazamata suna Haka har Murja ta haifi dan ta Santatale hadade mai kyau ga daukar Ido dan idan kaga yaron zai baka sha'awa kaji ya birgeka Bayan an sallame su daga Asubiti ne suka koma gida nan Maryam da sauran Yan uwa Murja suke kama aiki kuma har ranar biki yaro ya ci sunansa Musa Abul Khair sosai Aka yi farinciki da murna anyi biki kamar ba gobe anyi kacakaca da kudi ,''"

Bayan biki kullum Maryam tana wanan Murja amma sam Bata Bari ta dauki dan ta yau ma yaron Yana rike da

hannun mai tsaro jego Maryam ta karbesa tana masa Wasa sai Murmushi take sosai take jin yaron kamar ita ta haifeshi Murja da fitowar ta daga wanka taga yaron ta hannun Maryam yasa ta nufe ta da sauri tana kokarin Amsar dan ta tana cewa wai ke dan Allah me yasa baki da zuciya ne Kare ya dauke ke dama kunnen kashi gareki ne .''

"Ki yi hakuri Wasa nake masa ne?"""

Nabi hakuri da gudu ba takalmi naci uwarta idan Wasa kike son yima yaro to ki haifo naki mana .''

"Wani Irin sulaluwa taji zuciyarta ta yi , ta ce'' Allah bai mance dani ba kuma zai bani da yarda sa .''"

To ki fice min daga part tunda kema kinsan naki Yana nan zuwa .''

Haka ta tashi ta fice daga part din cike da takaicin halin Irin na Murja .''

Tun da wanan lokaci Maryam Bata sak tafiya wajen Murja ba dan ta fara gajiya da halinta har sai da ta ji Arba'in ranar da koma dan yi abin sadaka dayake Hajara ma tazo nan sukai ta habaicinsu suka gaji ko ci kanku Bata ce ba ta

"yi , Abin da zata yi Ita da kanwar Ammi ( Mamar Al'ameen) ta yi , tafiya ta.''"

Kullum zamansu babu tsanji Hakan yasa yanzu Maryam Bata tafiya wajenta ganin Maryam ta daina zuwa kwana biyu

yane yasa Murja fitowa daga part din ta tayo waje ganin Maryam a harabar gida ita ka dai sai karanta litafinta take mai Suna Farhat tana sakin Murmushi dan bakamin Dariya take Shaba tsakanin Farhat da Al'ameen musanman in da yake sharara mata karya sunje gidan rasuwa ya ce'' Wai Abba ya ce'' tayi kwanciyarta wajensa shi bazai samu damar zuwa ba.''

Tana cikin Dariya ne taji ta ta howar Murja tana tafe tana Tulla yaronta tana Waka mu dai Allah ya bamu dana dada

Zuci idan fitsari Banza ne kaza ta yi shi mugani .''

"Girgiza Kai Maryam ta yi, ta ci gaba da Harakokin gabanta ,'' Haka Murja ta yi , ta gama Maryam Bata ce da ita komai"

ba .''

"Bayan shakara biyar ne Allah Yaba Maryam cikin Haka ta yi, jan Kayanta sam Bata Bari Murja ta sani ba sai ma kyau"

"da cikin yasaka ta ta kara kyau da haske Murja Bata san da cikin Maryam ba sai labarin haihuwarsa ,dan a tare ma suka haihu ta haiho yarinya ta su duka ya'ya mata ne gare su ,dan tsabar masifar sai da ta je ganin abin da Maryam ta Hafa ta ga kyaukyawa yarinya sabanin tata yar dan yarinyar Maryam sai de godiyar Allah cike da jin haushi da ta kaici ta Baro part din Maryam ta samu yar jaririyar diyarta tana dukanta kamar ta samu Jaka da sauri mai tsaro ta amshe yarinya tana cewa Haba mana Murja miye yasa bakida hankaline me wanan yarinyar ta yi , maki daga zuwanta ki sameta ki yi ta jumga idan Kika kashe ta fa .''"

hasale ta ce'' kin ga iya babu ruwanki ai bake kika haifarmin ita ba taya zata yarda afi ta kyau ita kuma ta fito Haka

.''

To kaji wani ikon Allah lanle sai yanzu na yarda cewa baki da hankali Wallahi kishi kike da Maryam ne har yanzu

kema kin san ba daga Diya ba ko ke Maryam tafiki kyaun kallo bare kuma abin da zata Hafa ko da basu yi kyau ta to zasu yi na ubansu kuma shima Musa kibar ganinsa hadaden yaro kyaukyawa wajen ubansa ya gadosa dan indai yaran ki zasu biyoki nasan sai muni kamar buri Haka zasu yi ta yi .''

"Shiru ta yi ,sai cika take tana batsewa har zuciyarta ta sauko ,ranar biki ne yarinyar wajen Maryam ta ci sunan Asha Humaira , in da yar Murja ta ci sunan Bassira duk da ba wani shagali Aka yi sosai ba sabida ubannin yaran basu gari"

amma Alhamdulilah kowa ya wadatu .''

Tunda Murja ta Lura da Musa yafi Shakuwa da Maryam sakamakon yawan jansa da take a jiki shi kuma uwarsa babu

"abin da take yi sai aiki latse latsen waya hakn yasa duk yaranta suka ja baya daga gare ta zuwa wajen Maryam nan zata biye masu suyi ta guje guje cikin gida da Sun gaji su huta in lokacin Sallah ya yi , su je,su yi suci abinci su dora daga inda suka tsaya .''"

Dan shiyasa ta dauke shi ta kaishi wajen yayarta dake tsan kasashan waje da kyar ya Saba da ita kuma yake yarda da

"ita ,nan ya koma da rayuwarsa sai de suyi Waya da Murja .''"

Bayan Shekara uku ne Aka haifi su Ilham da Safiya sune suka sha gata da soyaya musanman yanda Dadyn su Asha

ke kulawa dasu wannan ma ba karamin haushi yake ba Murja ba ganin duk yanda ta so huce Maryam sai Allah tafita da wani Bangaren mai mahinmanci in da lokacin Bassira da Asha suna primaire Ajin na farko suko su Ilham lokacin ko tafiya Bata fara ba .''

Shekaru Sun ja kwanaki Nata tafiya Allah ya sak bama Maryam cikin inda Murja take ta jiran tsanmani dan tunda ta

"Lura da cikin Maryam yasa ta ke yawan takura ma Mudanssir a doli sai ya Bata wanan Abu tun yanayi da dadin rai har yafara gajiya dan bai san mi yasa take yawan takura shi ba,'' ganin Bata samu ba yasa kullum sai ta nemi Maryam da dambe dan cikin ya zube amma sam Maryam taki yarda da Hakan dan da taga take Taken ta zata gudu part din ta ta saka Key sai da cikin Maryam ya kai wata tara kullum Murja sai taja fada Rana t'ai ta zaginta Hakan yasa Maryam kasa jurar zagin ta ce'' Murja ina baki girmanki amma bakisan Hakan ba ina daraja ki ke kuma kina kasa da kimarki shiru shiru ba tsoro bane hakuri kawai nake dani dan Allah ki fita a hanya ta Bana son kina zagin iyayena dan nasan mutumcinsu kuma suna Dukan komai na rayuwata Banason na fara sa'in sa dake sabida nasan kin bani har Shekara biyu kuma kin rigani shigowa a wanan gidan kafin nashigo duk da ranar day Aka kawo mu amma na lura ke bakasn Ana daga maki kafa ba .''"

An je an zaga kiyi Dukan abin da zakiyi wani daraja da mutumci ke da iyayenki su wanan yar uwayan tsishine bacin

shara bolla dabbobi jakai .''

jin maganan ganin Sun yi muni yasa Maryam sharar ma Murja mari ta ce'' ilar rashin tarbiyar Kenan da daga gida

kinsamu tarbiya babu ta yanda za'ayi ki rena uwayen wasu koda daga sama suka fado kuma Wallahi na rantse da Allah Kika kara zagin iyaye na sai kin gane baki da wayo wahuya kawai shasha .''

Sosai Maryam ta bawa Murja mamaki dan ta dan ji shakarta musanman marin da ta da sharara mata sai da ya tsara

jikinta amma tsabar masifa irinta Murja yasa ta kaima Maryam duka da kadan a cikinta nan Maryam ta same ta

"kamar diyar ta yi ,Bawa Murja shegen duka da yake gaban mai gadi komai yake Faruwa Hakan yasa ya Kira"

"Mazajansu ,'' Bayan Maryam ta gama bama Murja kashi ne yasa ta Mikewa daga ruwan cikinta har ta juya Kenan ta ji Murja ta Kamo kafanta duka biyu ji kake Tum Alamar faduwarwa Maryam Hakan yayi daidai da shigowar S Muhamed kafin su karisa yin parking Murja ta Haye Maryam da ke fita da jini dan kasan Tillas ne mai Sulfi ta fada wani jiri na dibanta amma Hakan Murja ta dage sai Dukan cikin Maryam take babu tausayi bare Imani da ta dauko wani Katon dutse ta dage ta a cikin wata iriyar razananiyar kara Maryam ta saki tareda sumewa amma Hakan baisa Murja ta daina Kafkamata shi ,'' a guje su Muhamed suka yo kanta inda Muhamed ganin jini ga matarsa Bata ko motsi jini sai zuba yake ba kyakyawa ta yasa shi hurgi da Murja ya suri matarsa Mudanssir yabi bayansu suka nufi Asubiti sosai zuciyar Muhamed ta karaya dan har Yaga matarsa ta mutu dan ba ta dan yake cikinta yake ba ta uwar dan yake , da taimakon likitoci Aka shiga da Maryam cikin daki da kyar suka samu tafara nunfashi dan tun safe da Aka kahota sai wajen Karfe 12h na dare ta Farka nan wata sabuwar na kuda ta tasoma amma sai de bazata iya haihuwa da kanta ba sabida karfinta ya Kare ,Hakan ya bama DOCTOR damar fitowa dan saka hannu za'ayi mata aiki ,ganta ya kwantata ma Muhamed Halinda Maryam take ciki bai yi wata wata ba ya aminci Aka yima ta aiki Aka fido wata kyakyawa yarinya sai de da Alama Bata da lafiya dan komai na jikinta a Karka ce yake ba daidai yake da day bangaren ba har ta kanta ya langafe Sun ajiye yarinyar ne suka fara duba uwar a nan ne suka tabatar da akawy Babar matsala sukayi Dukan abin da ya dace sanann suka dumke mata wajen ita kuma yarinyar Aka fito masu da ita dan su ganta ,Kuka Muhamed ya fashe dashi dan a tunaninsa yarinyar ma bazatayi rai ba sai gashi cikin Ikon Allah ta rayu rumgume diyar yayi wani Sonta na kara shiga ransa dan sai yaji yafi son ta duk cikin yaransa ,dan Dago da kallonsa ya yi , Yana cewa Norse ina uwar yarinyar take ne da fatan dai tana lafiya .''"

"To Alhamdulilahi ne amma Doctor ya ce'' kuzo Yana son magana da ku ,kallon juna sukayi"

Tsakanin Muhamed da Mudanssir suka bi Bayan norse din ta Nuna masu bureau din Doctor Bayan Sun gaisa ne D.C ya ce'' Waye mijin Maryam a cikinku ne .''

"Muhamed da zuciyarsa ta gama karaya ya ce'' ga ni?"" Yawa sakamanko Dukan da akayi mata a marar ta Hakan ya sa"

Mahaifarta lalacewa bazata kara haihuwa ba sai wani Ikon Allah Dan Idan ma Aka bar Mahaifar a jikinta zata iya yi mata kumbri a cikinta Hakan zai iya haifar mata da kansa Hakan yasa Muka cire ta .''

Wani marayan Kuka Muhamed ya saki dan babu abin da yafi kauna sama da iyayan sa sai Maryam dan tsabar

"biyayarta da hakurinta ga iya kulawa da miji dama shimfidarsa sosai ya tausayamata kallon D.C ya yi , ya ce'' yanzu tana wane hali ne .''"

Lafiyar ta lau sai de abinda Ba'a rasana ba dan yanzu ma munyi mata Allura bacci sai munga Tashin ta .''

Sosai D.C da Mudanssir suka shiga kwantar ma da Muhamed hankali yarinyarsa ta rike da hannunsa Yaki Bari kowa

"ya karbe ta har garin Allah ya waye Maryam Bata Farka ba sai wajen Bayan Sallah Mangariba ta tashi a hankali ta fara Bud idonta ta sauke su bisa kan mijinta dake zaune yaka karema halitarta kallo Yana ganin zan dutsen da Aka Dakar masa mata ,suna hada Ido ta sakarmasa Murmushi shima ya maida mata gani ta farfadone ya sashi Kiran iyayenta dan Sanin halin da take ciki sannan ya Kira Norse Bayan Sun gama Wayar .''"

Bayan Bayan da su Maryam Suka je Asubiti Asha da gabanta akayi komai lokacin Ilham tana tafiya ita da Safiya

amma basuda wani wayo kuma suna School ita ma sabida batada lafiya ne yasa ta ganin abin da yafaru a Idonta sai Kuka take dan ta kasa cin komai tun daga lokacin tafara koyan rashin kunya Bata sararama kowa musanman Murja da tafi tsanarta a rayuwar ta dan a zaton ta taka she mata uwa .''

Ita ko Murja hankalinta kwance zuciya zauna dan tasan ko da Maryam Bata mutu ba to abin da zata Hafa doli ya

mutu dan dama shine har Bata so yazo duniya sosai take more rayuwar ta cike da farinciki da jin dadi musanman da tunda mijinta yabi Muhamed bai Dawo ba har yanzu .''

Sai da Suka yi sati day sannan Aka sallami Maryam daga Asubiti suka Dawo gida inda Mamarta ta Dawo kulawa da

"ita sosai har takara watsakewa ranar biki yarinta ta ci sunan Inteesar kowa sai santinta yake dan tafi diyan Maryam kyau dan de Halitarta ba dai take da tasu ba amma babu hadi tsakaninsu har Ilham , inteesar tafita haduwa .''"

Tun daga wanan lokacin kuma Aka yima mazanjensu transfr zuwa garin Maradi nan ne kowa ya nemi gidansa sai

"de suna kusa da juna daganan kowa yafara rayuwarsa har Aka aurar da Asha ita Bassira amma Ammi bata daina jin haushin su Maryam sabida su kullum abin karuwa suke samu ita Kuma tana komawa baya. Haka kawai Murja zata shigo gidan Maryam tayi ta zagin ta tana ce mata ba dai kin aurar da Asha to insha Allah Ilham sai ta zama rikakiyar karuwa kullum idan Sun hadu sai ta furta wanan Kalmar har Ilham suka tasa ita da Safiya suka zama kawayen juna komai nasu Irin day gasu Sun zama Yan mata sosai A lokacin ne Musa Abul Khair ya Dawo in da Suka fara haduwa da Ilham lokacin zata je Asubiti suka bida Buge juna da mota ,Bayan zuwan Musa ne Al'ameen ya shigo suka hadu Safiya nan suka fara aika ta Barnansu asiri a rufe babu Wanda ya sani.''"

Ci gaban labari .''

28/03/2022 16:58 - Mom Star :

*DOCTOR ILHAM*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS
'<*



"```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alalaminmu ancinmu.```"



*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*Na*

*Mom Khadija*

{{YAR LELEN NOBLE ce}}

36/37

Godiya dubu gareku fan's ina godiya ga kullawarku kuma ina jin dadin comment naku masu kirana kuma ina godiya

ga fatan alkairi Allah yabar kauna Arakam

Barka sister Meenah barkanki da Kammalla Littafin Wasu kawaye masifa ne) Allah yakara Bassira da Zakin hannu

Sai ke Shafa'atu kema barkanki da Kammalla Littafin Kishin Mace Allah yakara basira da fahimta SAHIBAR

NOBLE

Kam amma Wallahi wanan matar muguwace yar jaririyar ma Bata ragama ba sabida son zuciya Irin Nata da bakinci

Allah ma yakara da yar tata ta dauko mata Abin kunya fatan da take min Allah bai nufa Kai na ba sai cikin data Hafa Allah yakara kiyaye mu daga shairinta kuma ga dai ta nan duniya Wanda bai zo bama ta ishe sa Riga da Wanda harda zanin daurawa .''

Hakane Ilham Allah yabamu hakuri shiyasa kwata kwata na tsani wanan matar Wallahi Bana ma na kaunar ganinta .''

Wajan Mama Ilham ta zo ta tsuguna gaban ta ta ce'' Mama kiyi hakuri ban san Haka maganar take ba abinne ya

"dameni kulllum tana zagina tana mani cin fuska cikin mutane kuma fa har yinkurin kasheni ta yi , bisa kan wanan dalilin da ban sani ba Fassto Mama na tuba .''"

Hakane gashi ai yanzu furicin da take maki ya koma bisa kan yar ta ta dauko masu abin kunya yanzu bakin ta sai ya yi

", shiru ke kuma sai ki zauna tana gallazamaki .''"

Kam Allah taiwarail Khair ( Allah ya sawake ) .''

"Dariya Asha ta yi , ta ce'' ki Rabu da ita dan ta san ba muyi gadan bakin hali Irin Nata ba kinsan ance idan ta karewa Kare cizo yake yabari ya koma tunni.''"

Hakane nima naga alama dan gashi kan yar ta .''

Dady da ya yi jigum Yana sauraransu ya ce'' shi yasa ka fadi Alkairi a kan dan mutume ko kayi shiru ko kuma ka bishi

da Addu'a amma dayawa basu gane Hakan har ta da Yanayin shigar mutume suka gani sai Sun saka bakinsu bisa kan abin da bai shafesu ba kuma basu ganin abu a tatare da su sai a jikin Wani dan Abu kadan idan kayi mutane basu san farko ba zasu Kai ka karshe ko TUSHAN LABARI basu ji .''

Hakane Dady Allah ya kiyaye gaba .''

Amine .''

Inteesar ce ta shigo tareda yaran sai tsale tsale suke da sallama suka shigo suka Ruga a guje cikin daki .''

"Girgiza Kai Ilham ta yi, ta ce'' Allahu tuwarate warde Alkair Intee na .''"

Amine ya Allah .''

Dady ne ya kalle ta ya ce'' Ilham mijinki ya san kinzo gida ne .''

"A'a bai sani ba ina son ya je gidan Yaga yanda ya yi , nasan zai ne meni .''"

To ita Ammi ta Sanar da shi baki gida ne cewar Asha.''

"Na kanne ( An ya dai )."""

"Haka dai suka yi tautauna maganarsu suna ciki zantawa ne Musa ya Kira Ilham taga ta yi , tareda da sallama a"

"bakinta ,'' amsawa ya yi , sannan ta ci gaba da cewa Wayamin killi ( ina huni ) .''"

Lafiya lau arahas zayuwa .''

Arahaz wadurtole ( ya kake)

Arahaz Agurmi ( ya gari )

Hmm Agurmikus ( gari yayi zafi )

"Me yasa ?"" ta tambaya tana fido Ido .''"

"Nazo gida ba kyanan duk wajen a ya mutse ina Kika je e ya faru ?"""

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce'' ban san me zan ce da Kai yanzu ba amma kaje ka samu Ammi zaku yi magana da ita

idan kazo sai ka buyo Muje gida tare .''

Tom shikenan yafada ? Dan tunda yaji ta ambaci Ammi ya san akwaye matsala .''

"Katse kiran ta yi , tana ajiye Wayar gefe .''"

Asha ce t kalle ta ta ce'' me ya ce maki ne duk jikinki ya yi sanyi.''

Komai kawai dai Inde iniya ( ya bani tausayi )

"Dan tabe baki ta yi , tana mata hararen wasa ta ce'' a gaisheku masoya .''"

"Murmushi ta yi, ta ce'' E'e dan ki fadama mijinki ko Longin sonsa babu dan gata ya dame ya shanye .''"

"Dariya su Dady suka yi ,Mama ta ce'' Wai Ilham issi Harakta iskanci nan dan yanzu kwata kwata utuleri turakil.''"

A kunya ta ce'' Yanzu Mama bani da kunya kenan Asha Madami sulmada .''

Da sauri Asha ta ce'' Bana son Iskanci fa Ilham ni ce na koyamaki rashin kunyar ma .''

"E'e mana ?"" Kam Lanle Asha isirin darbarardi.''"

Dariya suka kwashe da ita Dady ya ce'' kenan Ilham kin yarda ke yarinya ce cewa fa take a kula dake ma'ana

utularigris .''

"Dan hade fuska ta yi , ta ce'' Mama wai bani da hankali .''"

Ba fa Haka nake nufi ba ina nufi ita ke Baba gareki ta kula dake Dadynku Yana son hada fada ne .''

Sai a lokacin ta saki Dariya tana cewa Haba yanzu hankalina ya kwanta .''

Dama ai a tashe Kika shigo a ta shi a koma inda Aka fito Tazo kwarakar tuwo to mun tsaye Kayanmu Agulu.''

Ke ya kamata nace ma ki tafi ba ni ba sabida ni a garinmu nake ke ce zance kinzo tsanye mana abincin gida .''

Suna cikin wanan maganar ne Ihsane ta rigo da gudu tana fadawa jikin Asha tareda fashewa da Kuka .''

"Hankali a ta she tace'' Ihsane pourquoi pleure tu ?"" C'est quoi ton problme.''"

Aunty Inteesar ce ta fadi kasa muna cikin Wasa .''

Qu'est que vous allez faire a elle .''( me Kuka yi mata ne)

Rien Momy kawai muna Wasa ta fadi Haka Kawai .''

"Kallon Mama Asha ta yi,sannan ta maido Dubanta ga Ihsane ta ce'' Fassto zata ta shi kin ji .''"

Tana gama fadan Haka duk suka nufi dakin Inteesar ruwa Ilham ta watsa mata nan ta fara tari tana Aman jiri

idanunta duk Sun yi sama jikinta sai rawa yake .''

Ajiyar zuciya Ilham ta sauke ta ce'' Mama Muje mu Kai ta Asubiti ciwan ta ne ya taso kar mu rasata ta fada a

dumauce .''

"Sungumarta Dady ya yi , suka nufi Asubiti suna isa Aka basu taimakon gagawa.''"

Da taimakon Allah da likitoci Inteesar ta samu jinin ya tsaya ta daina komai sai Bacci da ta samu sakamakon Allura da

akayi mata ta bacci .''

"Fitowa ya yi , ya ce'' Yanason ganin Dady babu musu yabi Bayansa suna shiga ya bashi izinin zama ,ya zauna Doctor"

ya jima Yana Yan rubuce rubucen sa daga bisani ya Dago yana Mika masa takardar hannunsa ya ce'' wanan Kayan Akin da za'ayi ma Inteesar ne a siyosu nan kwana biyu za'ayi aikin Insha Allah dan da Alama jikinta Yana son zama daidai ne .''

"Dagaske Doctor ?"" A'a ban tabatar ba sabida dazun abin da nagani shi nafada ku dai Taya mu da addu'a Allah yasa"

muyi a sa'a .''

Amine Dady yafada Yana fitowa daga Office din ya fita ba tareda yama kowa magana ba Pharmacie 17 portes ya tafi

ya Sayo magungunan da sauran kayan aiki Yana dawowa ya je wajen Doctor ya Mika masa shi kuma ya bashi takarda ya saka hannu .''

Nan mijin Ilham yazo asubiti sai dare suka koma gida Bayan yaji Ba'asin abin da ya hadasu da Ammi Haka ita ta fada

Masa babu abin da ta boye .''

Hakuri ya Bata sannan suka ci gaba da zamansu lafiya .''

BAYAN KWANA BIYU

"Inteesar ce saman bed ga su Mama da Asha Dady da Ilham kallonsu ta yi , ta ce'' Aunty na me yasa me Nine?"""

"Suma kikayi t?"" Ta Bata amsa a takaice .''"

Nan Mama ta shiga labarta mata Abin da ya faru .''

"Murmushi ta yi , ta ce'' Mama wane aiki za'ayi mani nasan bazan taba samun sauki ba kamar ku kashe kudinku a"

banza.''

Ke Inteesar Fassto dan Allah kina ja da ikon Allah ne .''

Ko kadan Mama Allah ya bani lafiya .''

Amine Haka Zaki ce tun farko .''

Cike da tausayin kanta t ce'' Mama and Dady Aunty's dan Allah idan mun shiga za'ayi mani aikin nan idan Allah ya

dauki Raina ku yafamai tafada duk jikinta ya bace da miwo .''

Baki mana laifi ba Inteesar kuma Insha Allah za'ayi aikin nan lafiya a gama shi lafiya.''

Suna cikin firar ne Doctor suka shigo dan za'a tafi da ita Haka nan Aka fita da ita Cike da fargaba kowa da ka gansa

"kasan Yana cikin damuwa Haka shiga dakin Bayan ta saka rigar bleu ta Marasa lafiya ta kwanta a bed din tareda Tura kanta cikin wata farar na'ura ta daga idonta sama sai haske take gani sai wasu fitulo da Suka haska inda za'ayi mata aikin kallon Ilham Doctor ya yi , ya ce'' Mdn ki kwantar da hankali ki tsaya muyi aikin nan a nutse in sha Allah zamu gama lafiya .''"

Ajiyar zuciya ta sauke cikin raunataciyar murya ta ce'' Kai anya zan iya Doctor .''

Zaki iya mana ki sama Ranki bamuda lokaci ku matso mu fara .''

Sai da Ilham ta kalli Inteesar da idonta ke kallon hasken hutar da ke cikin Mashin din tana girgiza Kai sai da Doctor ya

kara kwantar mata da hankali sannan ta dan saki jiki suka fara aikinsu cike da iyawa da kwarewa Ilham suna cikin yi tana karanta Addu'a har Allah ya sa suka Kammalla suka gyara komai sannan taje ta wanke hannunta ta cire tsanwar rigarta ta saka fara sannan ta fito tana Murmushi .''

Tunda suka ga hakan Su san Allah ya taimaka Sun gama lafiya tana karisa wa ta rumgume Mama tana fadan Mama ki

"mana murna Allah ya sa mun kammll bata karisa

Please Login or Register in order to submit comment