gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading DOCTOR ILHAM zuciya Cikin Ruɗani By Amira Saminu Chapter 8 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na bacci aka Bud kofar da yake tana kulle kofar ta cire makullin shi yasa Aka shigar mata Office jin ana shafata

"ya sa ta gyara kwanciyarta dan a tunaninta mafarki take yi , jin ana daga mata Riga ya sa ta bude idon ta suka yi Ido hudu da shi ,a tsora ce ta tashi zaune gabanta na dukan sha tara tara jikinta na rawa ta ce''"

.........................................................................

....................................

Comment

25/03/2022 09:25 - Mom Star :

*DOCTOR ILHAM*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS
'<*



"```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alalaminmu ancinmu.```"



*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*Na*

*Mom Khadija*

{{YAR LELEN NOBLE ce}}

28/29

"Jikinta na rawa cikin rawar murya tace'' Fa..ruk ,'' wani uban mari ya sharara mata Wanda ya sa sai da taga star uku"

"suna yawo a saman kanta sannan ya fincikota da sauri ta gantsara masa cizo tayi wajen wayarta ta dannan lambar Abul Khair ,da sauri ya kwace Wayar Yana buga mata Kai ga bango aiko hannunta ya danna karaurawar dake Nuna a kwaye matsala ,dan ita tama manta da ita tsabar firgici jin ana nufo dakin yasa ta kwarara ihu Hakan Yaba mutanan damar shiga Kai tsaye ,da mamaki kowa yake kallon Faruk Ilham Na ganin ta nufa wajen fa'iza tana Kuka ,'' d.c Bashir ne yanufa wajen Faruk tareda shako huyansa yayi hurgi dashi kamar Kayan wanki ya Kai masa naushi a Ido cike da facin rai dan ubanka iskancin da kake a waje bai isheka ba har sai kazo dan ka batamin sunan asubiti ko asarare kawai Kai de anyi dan iska kuma kasani daga yau Wallahi bazaka kara sha'awar lalata Yan mata ba dan uwarka kallon scurit din dake wajen yayi yace'' ku fitarmin dashi kuci ubanshi ,cike da girmama umarni suka sungume shi sukayi waje da shi suka fara dumarshi kamar an Sun samu Banza sai da sukayi masa jina jina sannan suka barshi sannan suka daure shi da igiya a wajen asubiti suka koma ciki ,'' kallon Ilham ,Bashir ya yi, ya ce'' babu wata damuwa dai ko"

",'' gyada masa Kai ta yi alamar e'e ,'' to ke ?"" Fa'iza ki zauna anan idan Allah ya kaimu da safe zai ga abin da zan masa.''"

Cike da jin kunya ta ce'' D.C na gode sosai .''

Karki damu babu komai ?.

Ficewa ya yi Ita kuma ta koma ta kwanta amma baccin Yaki daukarta sai de ma Hana fa'iza baccin da ta yi dan sai

"tafara bacci sai ta ce'' fa'iza bacci kike ne ,'' ita kuma sai ta ce'' A'a a Haka har Asuba ta yi ,Mikewa ta yi, duk da kanta Yana saramata amma Haka ta daure ta shiga toilet ta dora Alawa tafito tareda Tashin Fa'iza ita ma taje ta yi alawa a tare sukayi sallah sannan Ilham tafara har hada Kayanta ,''kallonta Fa'iza ta yi ,ta ce'' Ranki shi dade ina kuma zuwa yanzu .''"

"A takaice ta ce'' gida zan je mana?"""

To amma ai nake ganin gari bai yi hasken da Zaki fita yanzu ba kuma gashi motarki Batanan .''

Ajiyar zuciya ta sauke dan sai yanzu ma ta tuna cewa Abul Khair ya tafi da ita zaune tayi tareda dafe Kai dan sosai

"kanta ya bugu ga rashin bacci da Bata samu ba Wayar ta janyo tareda Kiran wayar Abul Khair ,sai da ta yi ringing hudu a na biyar ya dauka tareda da sallama a bakinsa amsawa ta yi ta ce''Mn halal dan Allah in ba damuwa kazo yanzu a asubiti ina son ganinka .''"

"Lafiya dai ko Ilham Me ya faru ?"""

"Sai kazo tafada tareda kashe Wayar ta ajiye ta gefe, jin Hakan yasa shi dauko makullin motarta yafito zai fita suka"

"hadu da Alhaji a hanya ,sai da ya gaida shi ,ya amsa Yana fadin ina kuma zaka je yanzu.''"

Wajen aiki ne aka kirani amma yanzu zan Dawo .''

"To ba damuwa ?""ka kula da hanya sai Dawo ko ."""

Insha Allah Baba.''

Baba Yana shiga ciki shima ya yi wajen motarsa ya shige sannan get man ya Bud masa kofa yafice daga gidan sai

Asubiti .''

Yana isa ya sauko ko kulle motar bai yi ba ya fito yanufa office din Ilham dan a yanayin da tayi masa magana zaka san

"tana cikin damuwa ,'' Yana kaiwa ya yi , fa'iza ta Mike tareda Bud kofar da Aka saka ta kullawa da Key ,'' bai tsaya Wata wata ba yanufa inda take tareda ajiye hannunsa a kafadarta ya ce'' rayuwa ta lafiya kike me yasa meki hakane"

.''

"kallonsa ta yi , da idonta da Suka cika kwalla ta ce'' Babu komai .''"

"Ya Zaki ce babu komai ?"" Kin ga tell me hankali duk a tashe yake Waye ta jimaki ciwon nan .''"

Fa'iza ce ta ce'' Kar ku na tsoma baki Akan abin da bai shafeni amma jiya kadan ya rage yallabai Faruk ya mata fyade

.''

Wani Irin garam gabansa ya buga da karfi idonsa sukayi jajir jijiyoyin Kanchi suka taso ya ce'' ina yake ne .''

A tsora ce Fa'iza ta ce'' Yana Bayan Asubitin nan an jima za'a fito dashi dan nunawa Al'umma sannan a huce da shi

police station .''

"Fitowa ya yi ,yanufa Bayan Yana isa bai tsaya Wata wata ba yashiga kaima Faruk mazga sosai yake ihu har muryarsa"

"ta dusashe ,da gudu scurit din dake wajen suka yo kansa da kyar Aka kwace Faruk a hannun abul Khair da sai sauke ajiyar zuciya yake .''"

"Safiya nayi Alhaji yatafi gidansu Ilham nan ya saka mai gani ya masa magana ,bai wani jima ba yafito nan suka gaisa"

"cike da mutumtawa , Alhaji ne ya ce'' Muhamed dan Allah nazo ne Akan maganar yaron wajena da yar ka Ilham .''"

"Lafiya dai ko ?"" Alhamdulilah dama nazo nema masa auren tane idan Allah ya sa ba'ayi mata mijiba .''"

"Washe baki Dady ya yi , ya ce'' Masha Allah to ai Ilham yarka ce babu damawa fairakat ( na baka ita).''"

Kai amma Naji dadi sosai nagode Allah ya saka da alkairi ya basu Zaman Lafiya .''

"Amine fairaturage ( Allah yasa Alkairi)."""

To Na gode Muhamed Inde gyara muzai .''

"Nan sukayi sallama sannan kowan nansu suka koma gida ,alhaji Na shiga Kai tsaye part din Ammi yanufa da sallama"

"a bakinsa ,amsawa sukayi dama ita da Safiya ce zaune a falo suna jan tarbi ,'' Baba ina kwana ?"""

Lafiya lau Safiya ana zaune .''

E'e baba .''

"Baice da ita komai ba ya duba Ammi ya ce'' Hajiya Ta yau nazo maki da baban Albushir ,'' Murmushi ta yi , ta ce'' To"

Bani labari in sha .''

Dazun munyi magana da Muhamed Bisa kan maganar Ilham da Musa Abul Khair sosai yafini murna ya ce'' yabamu

ita .''

Tunda yafara maganar Ammi ta hade fuska kamar ta makure huyansa ta ce'' bangane me kake nufi ba Kana nufin

wanan karuwar yarinyar zata zama Sakakuwa ta Allah ya sauwake kaga Alhaji ni wanan shedaniyar yarinya bazan taba laminta ta shigo mani gida ba Wallahi .''

Kallon bakida hankali ya mata ya ce'' nawa Kika kashe wajen gina wanan gidan ne to ni bazan kaminci wanan

iskancin banzan naki ba Wallahi idan har baki dai na abin da kike ba to da alama wata zata shigo wata kuma ta kama hanya dan ni bazaki mai dani karamin mutume ba .''

"Yana gama fadan Hakan yafice daga part din ,a hasale Ammi ta ce'' ko da za'a yi auren nan Wallahi sai de wani gidan"

amma ba nawa tafada tana kallon Safiya taci gaba da cewa munafika ai duk kune Kuka jawo za'a kawo mani diyar watsan mutumniyar banzan ta kara she tana bankada mata Harare .''

Allah yabaki hakuri Ammi .'' tafada tana shigewa daki sabida Kiran wayarta da ake yi .''

Tana shiga ta fada kan bed tareda amsa Wayar tana fadin Hello Kitty na ya kake .''

Lafiya lau Cutie ke jiya kike gudu ba ko sallama .''

"Murmushi ta yi, ta ce'' ba doli ba ai naga baka da niyar sallama ta shiyasa gashi mangari ba ta Kurato so kake yau a"

Hanani zuwa ne.''

Haba in sa Raina ina bacin Baki kusana ni dama Kira nayi inji Zaki zo yau ne .''

"Me zai Hana sosai ma zan zo ?"" Dan farincikin ka mana .''"

"Idan fa Amma ta Hanaki ?"".."

Haba ina ji koda satan hanya ne sai na fita dan nayi tauri bazan tankwasu yanzu ba .''

"Dariya ya yi, ya ce'' my Cutie love kin fa iya soyaya ba dama .''"

Ai ban kaika ba ko Kitty na.''

Babu gwani dai to da wane lokacin Zaki zo ne .''

Bayan sallah La'asar in sha Allah .''

To Allah ya kahomani ke lafiya ta kirkin .''

Amine ta fada nan sukayi sallama ta katse kiran .''

25/03/2022 09:25 - Mom Star :

*DOCTOR ILHAM*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS
'<*



"```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alalaminmu ancinmu.```"



*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*Na*

*Mom Khadija*

{{YAR LELEN NOBLE ce}}

30/31

Da kyar suka samu abul Khair ya kwantar da hankalinsa Hakan yasa yayi hakuri ya koma ciki wajenta yanufa ya ce ''

"rayuwa ta garin yaya wanan dan Iskan ya samu damar shigowa wajenki ,'' nan ta fadamasa abin da ta sani ,iska mai zafi ya fizgar ya ce'' Muje gida ko ?"""

Babu musa ta Mike suka yi hanyar gida babu mai magana kowa da abinda yake sakawa a ransa har suka iso sai da ya

shiga da ita har cikin gida sannan suka yi sallama ya tafi gidansu Ilham Na shiga ta tarar dasu Mama suna breakfast Inteesar ta kalleta da karkatacen kanta tana zubar da yawu ta ce'' Aunty na har kin Dawo .''

"E'e ?"" Kawai ta fada tareda gaishe da su Mama ,'' suma suka amsa sannan ta huce daki babu Wanda ta sak yima"

magana .''

"Tana shiga ta fada toilet wanka ta yi , ta saka Kaya Marasa nauyi sannan ta bi lafiyar gado sai bacci .''"

Dady ne da sai da Ilham ta shigo ya tuna da maganar Alhaji ya ce'' Maryam dama dazun ban Sanar dake ba yau da

sasafen nan Alhaji yazo gidan nan neman auren Ilham .''

A'a Masha Allah gaskiya nayi farinciki sosai .''

Amma Maryam Ilham ta san abin da ke tsakaninku da Murja ne .''

A'a Bata sani ba kuma Bana fatan ta sani tunda babu anfani Hakan .''

Hakane nasan wata rana dole ne ta sani in dai ana tare kuma ana raye .''

To banki idan lokaci ya yi Sata sani ai .''

Allah yasa Alkairi a cikin wanan hadin da mukayi .''

Amine .''

Safiya ce ta fito cikin shirinta Irin na isanan tana taunar shiwgom ta ce'' Ammi na shirya ni zan fita ko .''

"Da Mamaki take kallon Safiya wanan kuma wace Iriyar shiga tayi wai tana nufin a Haka zata fita,'' katse mata tunani"

ta yi tana fadin sai na Dawo Ammi .''

"Fita ta yi , batare da taji cewar ta ba ,dan tsabar Mamaki sosai Ammi take kallonta har ta bacewa ganinta Anya kuwa"

Safiya ce wanan.''

Da wann tunanin ne Abul Khair ya shigo tareda gaishe da Amma ko kallonsa Bata yi bare yasama ran zata amsa .''

Ina kwana Ammi? ''

Bansani ba tunda kaine mai Bada lafiyar .''

"Shiru ya yi ,n'a dan lokaci dan Yaga yau abin ba sauki Mikewa ya yi ,ya ce'' Ammi zan fita babu abin da kike da bukata"

ne .''

"Ko hmm Bata ce masa ba bare kallon arziki ,'' fita ya yi ,ya koma part din sa Ya kwanta nan ya Kira Wayar Ilham"

amma ba'a daga ba sai da ya jera mata miss call 3 sannan ya shafamata lafiya tashi yayi ya shirya dan zai fita .''

Janye suke da shi saman jaki Sun Rataya masa takalmi a huya ko Riga babu a jikinsa sai zagaye gari suke yi da shi

kowa ya gansa ya san me ya aika ta Haka sukai ta yawo da Faruk tun safe har yamma sannan suka Dawo da shi nan

D.C ya Kira Yan Sanda suka yi gaba dashi.''

"Ilham na tashi ta je ta d'aura Alwala ta yi Sallah sannan ta fito falo dan yinwa take ji, babu kowa a falon sai Asha wajenta ta zo ta zauna tana fadin Matar Habibi yakk .''"

Bansani lafiya dazun Kika shigo kamar da damuwa a fuskarki.''

Sosai ma nake cikin ta Wallahi wani abokin aiki nane ya takurani Aunty yau fa bidar cin zarafina ya yi fa .''

"Amma garin yaya Ilham ?"""

Nn ta fada mata abinda yafaru sosai Asha ta ce'' dan Iska dama Bari suka yi Wallahi su kashe sa kowa ma ya huta .''

Wallahi kuwa Aunty har yanzu abin Mamaki yake bani .''

Kinga kibar saka damuwa a Ranki Ilham ni kam me yasa ? Kike son auren Musa Abul Khair ne baki tsoron ki fada

"cikin Matsala dan na lura fa wanan uwar ta shi ba kaunarki take ba me zai Hana ki hakura da sonsa ."""

"Aunty ?"" Hmm ni ba ita zan aura ba dan ta ne mijina baki na da ita biyaya a matsayin ta na uwa ta kuma uwar mijina"

amma kibar maganar cewa in dai na soyaya dashi dan intatara in damu zulafate( Wallahi ina sonsa kuma zan aure shi .''

"To Babar magana ?"" Ki kwantar da hankalinki kin kusa zama amaryarsa dan da zun Alhaji yanzu suka yi maganar da"

Dady .''

"Rumgume ta Ilham ta yi ,tana Mikewa tsaya ta ce'' Wai daga gaske kike Aunty Kai gaskiya Naji dadi zan auri jarumina"

",dan take rawa tafara tana Waka ,Allah Nagode daka bani abin kauna Yan uwa kuzo ku tayani farinciki kwanan zan shige lanle zanje dakin yayana kuma shine angona Allah ya kaimu ranar musha shagali shoky.''"

"Dariya Asha ta yi , sakamakon su Mama dake tsaye suna kallon Ikon Allah amma ita Ilham Bata ma san suna tsaye"

"ba , cike da izgili Asha ta ce'' Ilham Ashe kin iya rashin kunya bansani ba Kenan aure kike so da kin sanar tun huri ai da yanzu kema kina da yaranki .''"

"Tsaida rawan ta yi , ta ce'' Aunty Kenan ribar soyaya ita ce aure rasa Abul Khair Dina tamkar rasa rayuwa ta ne dan"

Haka Banason ana mani tangal tangal dashi ina fatan kin gane ko .''

"Wata dariya ta sak shekewa da ita ta ce'' ke da Wasa fa nake yi Dady cewa ya yi ,ya maki miji Ali ne dan gidan baba"

mai gadi .''

"Tabe baki tayi ta ce'' To fadama Wanda bai san halinki ba ,''"

har Bud baki Zatayi magana ta ji Mama na fadin Sannu da kokari Ilham bansan kin iya Waka mai dadi Haka ba.''

Waya kunya ce ta kama ta ai ko ta zuba a guje ta yi sai harabar gida tana sakin Murmushi .''

Suma dariyan suka yi Dady Yana girgiza Kai ya ce'' A'a gwara Musa ya fito idan ba Haka ba akwaye matsala .''

Gaskiya dai kam Alhaji da Alama dai .''

To Mairiri na ni zan tafi sai idan Allah ya Dawo da dani kuma .''

A Dawo lafiya Alhajina Allah ya tsare ya kiyaye hanya .''

Yana fita yanufa motarsa ya bar anguwar baki day ma .''

"Safiya na isa kofar gidan Kitty din ta ta yi , Nocking ,nan yazo ya Bud mata tareda rumgume ta jikinsa Yana fadin"

Cutie kamar kinsan jiranki kawai nake yi .''

To gani Kitty na ai kasan ya huce matsayin ka nemi Abu ka kasa samu a wajena dan Kai fa dan gata ne .''

"Murmushi ya i , ya ce'' Mu shiga daka ciki ko .''"

Babu musu suka shiga ciki a falo suka zauna sai da Suka sha firansu sannan suka sha shiga soyayarsu a takaice sai

yamma sannan ta koma gida badan ta so ba sai dan marice ya yi sosai dan da kyar ma suka Rabu .''

Kwanci tashi babu huya wajen Allah dan yanzu manyan har Sun shigo lamarin Ilham da Musa maganar aurensu Aka

"tsaida nan da sati uku ,sosai suka ji dadi a kowane bangare amma banda Ammi dake cike da haushin Ilham dama duk me son ayi auren nan dan yanzu Ilham ta Asha na kara kulawa da ita Haka Mama dan yanzu har ta dauki hutu aiki .''"

Tun randa Safiya ta Dawo gida tafara sheka Amai kamar Yan cikinta zasu fito tun tana daukar abin kamar Wasa har

dai sai da yafara sakamata zazaga yau Yana lafiya gobe ba lafiya Haka take murkusan abin ta batare da ta Bari wani ya fuskanci halin da take ciki ba duk da batasan ciki ne da ita ba .''

"Bassira ce zaune ta nama Khairat wasa babanta kuma Yana aiki da computer dan Daho da kallonta ta yi, garasa ta"

ce'' Ruhi na dan Allah inba damuwa ina son zan je gidan kawata gobe .''

Murmushi ya sakarmata ya ce'' Allah ya kaimu Ruhi na dan sosai yaji dadin Hakan dan tunda sukayi aure Bata taba

tambayar izini ba Hakan yasa yau babu musu ya yarda ta je din godiya ta yi masa .''

Ya ce'' karki damu babu abin da Zaki in ki yimaki shi sai de in yafi karfina ko banda halin yin sa .''

"To Allah ya barmu tare Ruhi na?"""

Amine yafada Yana ci gaba da maida hankali bisa kan aikinsa .''

Kwanaki suja kuma suna ta tafiya muna satin bikin Amarya Ilham sai shirye shiryen biki ake amarya ta sha gyara

"sosai sai Kyali take tana daukar Ido ta wani kara kyau kamar balarabiya ga gyaran da take sha Kai abin Ba'a magana , Haka Safiya ke daurewa tana zuwa gidan duk da Ammi Bataso amma Haka ta kyaleta sabida Alhaji ya ce'' ta kara shiga sabgarsu Wallahi duk Abi da ya biyo baya to ita ta jawa kanta ,a bangaren ango ma Ba'a barshi a baya ba abin Ba'a cewa komi sai Masha Allah babu wani shagali da sukayi sai Arabian Night sosai nan ma suka rakashe nan naga fan's din *DOCTOR ILHAM* Sun fito sai kwasar rawa suke suna kwaso shoky .''"

WASHEGARI

Yaune Ranar ASABAR kuma yaune Duban mutane suka shaida auren Musa Abul Khair Iliyas and Ilham Muhamed

Bista bisa daki duba dari biyar Sosai mutane su kai ta ya ango murna shiko wai Washe baki yake har kunne .''

A cikin gidansu Ilham sai hidima ake kowa Yana harakar gabansa anci ansha anyi shagali san gwangwaje .''

Bangaren gidan Ammi babu walwala dan Mutanan dake gidan sunke hidimarsu sai dangin Alhaji da Suke ta murna

suna zolayan Musa sai de yayi Dariya ko Murmushi amma bai tankamasu har dare yayi Aka zo daukar amarya zuwa gidan Musa Abul Khair

Nima anan nake tsaida Alkalamina sai da safenku

27/03/2022 10:08 - Mom Star :

*DOCTOR ILHAM*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS
'<*



"```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alalaminmu ancinmu.```"



*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*Na*

*Mom Khadija*

{{YAR LELEN NOBLE ce}}

32/33

Dare nayi Aka zo daukar amarya da tasha nasiha mai ratsa zuciya sai Kuka take har sai ta baka tausayi har za'a a fito

"da ita ta kiya tace'' zan yi magana da Asha ,kanwar Mama ce ta ce'' ai tareda ita za'aje sai kuyi maganar ,'' Kuka ta sak fashe dashi ,'' kanwar Mama ta ce'' Wai Ilham bazaki shiru ba minene ,'' sai da taja nunfashi ta ce'' yinwa nake ji zanci abinci tafada cikin muryar Kuka ,'' Dariya suka kwashe da ita suka ce Zaki amma Muje mutane mu suke jira"

",Haka Aka fito da Ilham suka saka ta a mota sai sai gidanta kowa ya ga gidan sai yayi santinsa ya hadu iya haduwa kuma an tsara shi yayi kyau Haka Aka huce da ita dakin Jahid Bayan an yi Sayan baki kowa ya watse sai Safiya da Da'ifa sai Arifa ,da sauran abokan Ango ,nan su ka yi ta tsula tsiyarsu har suka gama kan Ilham Na duke tana Kuka ango ne ya kallesu ya ce'' Kai dan Allah baku ga dare ya yi ba ku tafi mana dan in samu damar rarashin Amarya mana"

",'' Sadik ne Baban Abokinsa ya ce'' To dan Iska zamu tafi Allah Bamu Alkairi amma kabi yarinyar mutane a sannu dan kar ta ji ciwo ,'' Sahib dake gefen Sadik ya Kai masa duka Yana fadin Kai de anyi dan iska ,Haka dai suka yi suka gama ango ya rakasu ya jima waje dan sai da ya saka su Safiya a mota sannan ya Dawo ciki da sallama ya shigo ,a kasan makoshi ta amsa masa nan ya kariso wajenta tareda janyota jikinsa Yana dage Sakalar da Aka rufe ta da ita Yana kallonta fuskar ta a sunkuyi yasa ka hannu Dago ta ya ce'' Ilham din Abul Khair Waye Ya tabamin ke ne ,'' kara sunkuyar da Kai tayi ta ce'' Kai mana ?"

Ni kuma Yan mata na me nayi .''

Dan turo baki ta yi amma Bata ce komai .''

To na gane kiyi hakuri nayi laifi amma wajen masoyinki Zaki kwana ko .''

"Ni gida zanje fa ?"""

"Muje na Rakaki ,'' Mikewa ta yi ,tareda mai da Sakalar ta ta fito waje har ta Kai gaban get ganin da gaske take yasa"

"yama mai gadi Alama ,ai ya kulle kofa, da gudu ya kariso ya sure ta kamar baby suka Dawo suna Dariya ,suna shiga dakin ya ce'' Wai har kin Dawo ta gajiyar hanya .''"

Babu tafada a takaice .''

To yanzu dai Muje muyi sallah mu godiya Allah Daya gwada mana wanan ranar ta farinciki mai Albarka .''

Babu musu ta Mike suka nufa toilet a tare sai da ta jira ya Kammalla sannan ta saka Key wai dan kar ya shigo sannan

"ta dora Alwala tafito ,'' tana fitowa dama ya shimfida darduma ya jamasu sallah Bayan Sun Kammalla ne yamasu addu'a suka shafa sannan ya janyo mata kazarta ,da kyar yasa mu ta ci kadan sannan suka je suka kwanta .''"

Safiya ce dake zaune ita da Ammi suna dan taba fira taji zuciyar na tashi sabida kamshin abinci dake tashi ai ko tayi

"waje da gudu tana kwarara Amai kamar Yan cikinta zasu fito musanman ma Bata ci wani Abu sosai ba Hakan yasa ta gallabaita sosai , sai da ta gama ta Dawo falon kallonta Ammi ta yi, tace'' Safiya lafiyarki lau kuwa?"""

Lafiya lau Ammi jiya ne naci abinci wajen Arabia Night to ina ganin Zafi ne ya tasomin .''

Eyahh yaka mata kisha magani .''

To yanzu zanje in sha .''

Tana gama fadan Haka ta shige daki tareda kiran Wayar Kitty Yana dauka babu wani gaisuwa bare kuma soyaya ya

ce'' Kitty Kana ina ne .''

Lafiya dai ko ? Cutie da wanan daren Haka .''

To ba zance komai ba ina son za muje gobe asubiti ni da Kai. '

Asubiti kuma wani za muje dubiya.''

A'a ni zaka Kai sabida ina zargin wani Abu .''

Shikenan Allah ya kaimu sai kinzo ki.''

Ok bye Kitty na .''

"Katse kiran ta yi , tareda yin kwanciya tana tunanin rayuwarta me ya Aike ta biyewa shairin zuciya ta Bada mutumci"

wajen wani Wanda ba mijinta me zata ce ma Allah wasu hawaye ne zafafa suka gangaro da kwarin Idonta sai da taci Kuka mai isarta sannan ta share hawayenta kanta dake saramata ta dafe tana karanta Addu'a ta samu yayi dama sannan wani bacci yayi gaba da ita .''

Bayan tafiyar Ilham gidanta ne Mama ta kalli Asha ta ce'' Asha Wallahi hankali sam bai kwanta da auren nan ba

sabida watsan Murja wace baka tsokane ta ba tayi ta surfa ruwan masifa bare kuma an jata kiga fa ko diyarta bassira Bata zo ba sunan ana auran Yayanta .''

Mama ki kwanta da hankalinki kiyi mata fatan alkairi insha Allah babu abin da ta isa ta yi mata in Allah ya nufa yasa

me ta ba .''

Hakane maganarki to ina fatan Alkairi ya basu zaman Lafiya .''

Amine Mama ni zan je in kwanta a gajiye nake .''

To yau baza kuyi fira da Saf bane .''

A kunya ce ta ce'' A'a ya sha kanwa ba zai iya magana ba sai ya sauko.''

"Dariya Mama ta yi , ta ce'' lanle dai kam buhu nawa ta bashi ne .''"

"Mikewa Asha ta yi, ta ce'' Yana da yawa ni kaina ban san yawansa .''"

Lanle zamu ci tarar Ilham duk Randa ta shigo gidan nan .''

"Dariya Asha ta yi tana hayewa sama

Please Login or Register in order to submit comment