You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
ya gagara yin masa shi?
"Dad ina saurarenka" ya furta a hankali, gyaran murya general yae kafin yace
"Da farko dai so nakeyi ni da kai dakuma tawagar soja mu shiga wannan jejin mu kai addinin islama a wannan garin, malam da mahaifin sa sunce tare zamuje dasu idan kun aminta, naso inje da 'yan biyu amma ina tantama akan mahaifiyarsu bazata aminta ba kuma kaga tafimu gaskia tayita roqar mu muna kaucewa hakan muyi yanda mukaso, sabida haka ina neman jajircewarka duka duka kwanaki bakwai nakeso muje muyi mu dawo ina gani ina kuma ji ajikina *Doguwar hanya* da yara suka bi ba bisa son ranmu ba har muke ganin be zamar mana alkhairi ba to tabbas alkhairin ne a dunk'ule, idan ka duba da kyau zakaga cewar munjima munawa k'asa hidima me hatsarin gaske amma wace hidimar ce mukaima addinin Allah? Ga kuma dama har gida me zamu tsaya jira? Munyi ta yiwa al'amarin nan kucce kucce amma kaga idan kayi duba da kyau zuwaga lamarin zakga mud'in dai mune Allah ya zab'a kuma da ace bamu bame da baze rik'a kawo hanyoyin daze had'amu da waccen yarinyar ba duk girman nisan duniyar mu data banbanta, sabida haka wannan itace buk'ata ta ta farko, mu musulman soja Allah ya bamu dama da iko da makamai ya dace mu taya annabi yak'i, kaga da arna ne wlhy da tuni sun yad'a manufatsu a wannan guraren, da dukiyar su da iliminsu da karfin su suke tafiya gaba d'aya" Nisawa shmsu yae
"Daddy wannan aiba komai bane ba, wannan tafiyar tayi kuma koda zan kutu acen tabbas sena keta doguwar hanyar domin yad'a addinimun islam, koba komai zan yi farin na mutu a b'angaren bautawa addinina na bada gudummawa domin ci gaban addinin nawa na islam addini me daraja da d'aukaka, addinin gaskia addinin Allah" Fara'a sosai General ya shiga yi babu k'akk'autawa yana shiwa Shamsu albarka ya k'ara da cewar
"Naji dadin wannan al'amarin Allah ya albarkaceka ya tallafeka, se magana ga gaba kuma itace, zancen auren ka nayi nayi kak'i kayi aure Shamsu, sabida haka nakeso wannan yarinyar Naja'atu (Lawuri), ka taimaka ka aureta kaga yarancen dukkansu sonta sukeyi bazan so kansu ya rarrabu ba amma tunda duk sunyi aure kai bakayi ba ka daure ka aureta" Nanma beyi musu ba haka ya zauna ya dinga godiya har seda ran dad ya b'aci.
**********
Ayusher jikinta se rawa yake tunda Taga yaa sufyan agabanta, yaji sauk'i har suna tab'a hira, ita gashi ko angwancewa basuyiba ya fad'a ciwo, yau dai duk an cire kunya a jikinsa aka makara, anan aketa luguden sa baji ba gani, yanzuma kwance take a saman jikinsa shikuwa yana shafa sumar kanta a hankali, hannun sa yaja zuwa lips nata masu laushi ya shiga murzawa a hankali, bud'e bakin tae ya zura d'an yatsanshi inda ta gallamai cizo med'an zafi, da sauri ya janye yatsansa yana dariyar a hankali
"Baby ni kuma mena miki haka?" Turo baki tae
"Tobayan kaine kak'i kazo muje mui baccin rana" murmushi yae
"Ayush baccin rana yanzu? Shagwab'e fuskar nan ta k'arayi
"Bafa kada lafiya, bayan haka kuma bacci kakeji" murmushi ya k'arayi
"Lallai ma wato nida idona kece kikejimun bacci" Langwab'ar da kanta tae
"Yaa Sufyan dan Allah to muje d'akin mana" d'agata jikinsa yae a hankali shima yae shirin mik'ewa
"Hajiya d'agani ina patient dani baki d'aukeniba amma yau duk ajikina kika wuni, to muje d'akin" Doddoka k'afa tashiga yi a k'asa
"Gwara in huta abuna asaman jikin mijina yanzu dai mijinane babu me shamakanceni daga yin rumfa akanka, ciki kuwa hadda kai" murmushi yae
"Naji me miji, kunyar kuma fa kin siyar?" Ya tambaya yana kafeta da ido, janye idanta tae daga nashi
"Dana baka aro sanda bakada lafiya baka dawon dashi ba ai" Tafurta cikeda zolaya, damk'ota yae ta fad'o jikinsa gaba d'aya, suna kallon juna cikin ido yace "Zona baki kunyar ki ai mantawa nayi ban mayar miki ba" Kallon sa take ta rasa dalilinta na neman kunyar tasa ta rasa ada ko kallonsa bata iyayi ido cikin ido amma yanzu kwata kwata bataso ta dena kallon sa, batai auneba taji bakinsa a nata a tsayen dasuke, bata k'waci kanta ba haka ya dinga wasa da harshensa a bakinta yana tsotsar nata seda dukkansu suka soma fita hayyacinsu tsayuwa ta gagaresu, ganin yanda itama ta shiga mayar masa da martani se abun ya bata kunya musamman dasuka zo fad'uwa seda sukai garkuwa da kujera, zame jikinta tae ta kwasa aguje zuwa d'akin, yabi bayanta yana dariya
"Baby tsaya mana ki karb'i kunyar dakika bani aro, Allah kuwan nagaji da ajiye shi aguna nawan ma yana qara dashi" yana k'arasa tanayin toilet zata rufe ya rik'ota, saman gadon ya ajiyeta ya rage fitilar d'akin duhu ya wadata, d'are gadon yae harnlokacin yana damuwar mugunta
"Tunda kika nemi in baki abinda na ara aikuma na tabbatar kin rik'a da gasken abinda kikeso kenan"
"Yaa sufyan Allah wasa nake maka, ni yaushe ma nabaka wani aron.... Bakinsa ya cura anata dolenta tae tsit, haka ya soma aika mata sak'onnin ban girma, harya soma ciwo kanta, cikin dabara ya zare mata zip ya hankad'a duka hannayensa acikin dukiyar fulaninta, numfashinta ya soma barazanar d'aukewa, murya a sark'e tace
"Kayi hakuri yaa sufyan ba kyau fa" beko kulataba yaci gaba da abinda yakeyi, shida kanshi ba'a hayyacinsa yake ba a wannan lokacin, bekosan sanda yae mata tumb'ur ba duk iya kucce kuccen datake masa da magiya, be gushe ba a wannan ranar seda ya kawar da budurcin Ayusher, a rananr Aisha ta zama cikakkiyar mace kuka kam ta shashi, shikuwa duk ya gama rikicewa da samun nutsuwa abunka ga samun shiga, dayike ma shekaru sun lula ba wani rauni tajiba dukda haka taci gashi.....
*********
Tunda suka shigo gidan hankalin Zuhrah ya tattara zuwaga gogan nata, tarasa dalilin tsorata da ciwon nasa da tae ga uban cikinta daya k'ara girma sosai daka ganta ko ba'a fad'aba kagan maman biyu, hidima take dukda ta kula da take take hanifer nason ta shiga tsakaninta da mijin ta,komai seta wani mak'ale yaya kaza yaya me kakeso, d'aki ta kai abinta ganin isha ta wuce har anci dinner, tunda wannan ta kanainaye ta kafesu a parlor
"Yaya mage shigewa zakayi tun yanzu bazaka bari muyi hira ba?" Kallonta sukai dukkansu Zuhrah cikin qufula tace
"Bakiga be gama warwarewa ba, ai gwara ya kwanta da wuri ko?"
"Anty zuhrah kwanansa nawa a kwance? Ai gwara ya zauna kar bayansa yazo yana masa ciwo"
"A d'akin aini nasan mezan masa daze sanya jikin nasa bazeyi ciwo ba, so karki damu" taja hannunsa shikuwa babu wani wadattacen k'arfi ajikinsa se binta yae sekace rak'unmi da akala....
Seda sukai wanka sannan suka kwanta lokacin tara ta gota ma, kwantar da kanta tae asaman k'irjinsa
"Yaa hurairah da gaske kuwa da Dr. Yace yana da kyau kake gayarda yaranka da mamansu, sunyi kewarka sosai muna maka fatan samun lafiya me d'orewa" Hannunsa yakai acikin duhun ya shafi fuskarta yana murmushi
"Allah ko Zuhrah?" Gyad'a kanta tae "Sosai mana yaa Hurairah" murmushiya k'arayi ya sumbaci goshinta kawai, ganin tana shafa bayansa ya sanya ya kamo lips nata ya ciza had'e da lak'uce mata hanci
"Haka ake renon zaki hanani bacci" shagwab'ewa tae gaba d'aya
"Haba mana yaa hurairah " bakinta ya cura a nasa ya soma kissing nata passionately, banda numfarfashinsu dake sauka sauri da sauri, ko wannensu ya fita hayyacinsa se shafar jikin juna suke tamkar zasu yaga jikin juna, seda suka gama birkicewa sannan hurairah ya tuna alk'awarinsa akan baze k'ara kusantarta zuwa cen ba, zame jikinsa yae ya juya mata baya dukda azabar dayakeji ajikinsa na tsananin buk'atarta, matsawa tae a kusa dashi ta rungumeshi ta baya
"Yaa Hurairah dan Allah kayi hakuri" daga cen be waigoba yace
"Me kikamun kike bani hak'uri ne Zuhrah?" Kuka ta saka masa
"Ka taimakeni ka kusance ni yaa Hurairah, wlhy ina buk'atarka, idan laifin danama abayane na tuba kaji bazan k'ara ba har abada" be juyoba be kuma ce mata komai ba haka tayita masa kuka kusan mintun 10, ganin baze iya hak'ura da wannan kukan ba ya sanya ya juyo mata suka k'ara afkawa juna ya kula tana cikin tsananin buk'atarsa beso ya cutar da ita har haka ba, seda akazo kashe boss sannan tutsun ciki yace besan wannan ba, murmushi yae
"Maman twins, ga alama bazasu barki ki mora ba yau, sunce mission impossible" Rufe fuskarta tae da tafukan hannayenta, bashida zab'in daya wuce ya sauya musu style na kwanciyar wanda da hakan aka kashe boss....
Hanifer wacce ta musu lab'el da kuka ta koma d'akinta, tajiyo suna kukan dad'i ita kuwa ta koma na bak'in ciki.
*Nibansan mesa har yau dawood ne kadai besan dawan garin ba lolx....*
Mom Nu'aiym.
[11/26, 6:19 AM] Maamah twinsđâ¤: 37****Tunda ya fara maganar shi take kallo harya kai k'arshen zancen sa, malam ne me isar da sak'on general akan zancen oga shamsu, yaso yae jihadin auren ta amma yanaga hak'ura zeyi yae jihadin da Barbo inhar zata amince masa akan wannan tafiyar, ba shakka Lawuri yanzu data soma sanin menene musulunci ta yarda da k'addararta kenan, bazata ma ta iya tuna waye OGA shamsun ba amma dole haka zata hak'ura ta barwa Allah akan lamarin, ta sani koda tayi galabar rayuwa da d'aya daga cikinsu bazasu tab'ajin dad'in zama da junaba kodan sabida mahaifiyar su, haka tace babu damuwa ta hak'ura ta barwa Allah nasa ikon.......
*******
A parlor hanifer da zuhrah zaune suna kallon wani film na india, haka nan hanifer ta d'auki remote tana shirn sauya channel zuwa wani b'arin, arewa 24 ta mayar inda ran zuhrah be mata dad'i ba, kobazataci darajar zamtowar ta mata a wurin yayanta ba aitaci darajar gidanta ne ko, kallonta tae da kamar ma bazatae magana ba sekuma tace
"Hanifer inaso in k'arasa kallon film d'in nan ki mayar mun mana" harara hanifer ta aika mata
"Ban ganeba? Nikuma wannan nakeso?" Ta fad'a cikeda tsiwa yau dai zuhrah takai mak'ura wurin jin takaicin wannan wulak'ancin na hany
"Amma ya kamata kisan cewar nan d'in gidanane ko? Kuma kayan dasu nazo bawai anan nazo na samesu ba, haka kawai kinzomun gidan mijina kin hanani rawar gaban hantsi?" Wani mugun kallo hanny ta wurga mata
"Mijin da ake cin amanar sa? Ana waya da wani gardin ana masa alk'awarin za'a kashe wannan auren aje a auresa? To wane kuma daren ne jemage be ganiba?" Wani yanayi zuhra ta tsinci kanta aciki
"Sharrin dazakimun kenan?" Harararta ta k'arayi
"Sharri a ina? Nan nan ko sanda yaya bashida lapia zaman waya kike dashi agidan nan ba dare ba rana, wlhy sekin shiga taitayinki dani danni nan har recorded audio inadasu na conversation naku, kije ki bud'e wayanki kema zaki jisu ai, ana d'auke da igiyr auren wani ana zuba shashancin bin maza a waje, andaiji haushi wlhy ina tantama idan wannan cikin ma na yaya nane, tunda an iya waya da gardawa agidan miji" shiru zuhrah tamkar ruwa ya had'iyeta, batasan ya zatayi da yaa Faruk bane, tayi tayi ya d'age mata k'afa har su rabu da Abu hurairaih amma yaqi, kira naci kodawane lokaci, yatasan zatayi dashi, dariyar hanny ce ta katse mata tunanin ta
"Idan mutum ya isa daya musa dan gyatumar sa, wlhy kifi yana ganinka mejar koma, abu d'aya zaki ki tsira da sharrukana shine kafin kibar gidannan ki sanya yaa Hurairah yae ta biyu dani, nikuma zan taimakeki ya sakekin yanda kika buk'ata dazaran kin haihu, kinga daganan kema kyaje ki auri wanda kike so" wani abu zuhrah taji ya daki k'irjinta dabatasan yana duniyar bama, mekenan taji da wannan kalaman na hanny? Koda take cewa ta kamata tana waya da wani da zancen waiko cikin bana yayanta bane hankalinta danqirjinta basu doka kamar wannan maganar datake yanzu ba!!!! Da k'yar ta mik'e tsaye sabida nauyin cikinta ta kalleta
"Duk wani abun da zaki fad'a akan yaa faruk bana tsoron ki gayawa koma ubanwa zaki gayawa, abu d'aya nakeso ki sani shine mijina ko mutuwa naga zanyi bazance ya aureki ba, bakizo a kishiyaba ma kinzo da salon iskanci kala kala balantana kinzo a kishiyar?" Wani shak'iyar dariya hanifer tayi
"Yarinya zakisha mamakin abinda zan miki wlhy, muje zuwa" tana kai nan ta wurgar da romote tae juyawarta zuwa d'akin ta....dafe kanta tae tana mejin duniyar tana juyawa mata, yaya zatayi da Hanifer? Ina zataje da wannan nauyin da xuciyarta ke mata?...
**********
*Bayan sati biyu*
Anyi nasarar zuwa garin nasu Lawuri sedai anci bak'ar wahala, inda fiye da rabin mutanen sun karb'i musulunci bayan da bayarben malamin nan da mahaifinsa suka jagoranci tafiyar, abubuwar da dama sun faru inda daga bisani Sarki k'uru me sunan (ABUBAKAR) a wannan lokacin ya tilastawa sauran karb'ar addining na islam, had'e da rufe duk wani abu daya shafi tsafi a garin dakuma mugwayen al'adu, wasu marasa rabo sun gudu yayinda fiyeda rabi da kwatar mazaunan yankin suka karb'i addinin islam, k'auyen dake cin naman junansu ma bawai an barsu a baya bane, inda seda aka gano sud'inma yarbancin suke sedai su tasu rayuwar mara 'yancine, cin naman junan ya samo asaline tun kafuwar garin, Allah yayisu wasu irin dabbobin mutane marasa dabara, yunwa data soma addabarsu sesuka soma yakutar naman jikin juna daganan kuma se abun yazama al'ada duk wani abu daza'ayi indai aka kamaku kuna magana me tsayi ta kanku akeyi..... Shisa zakaga garin tsit, da abinci da sauran abubuwan jin dad'i aka rud'esu take suka bi addinin islam.
**********
*Bayan watanni biyu*
Yanxu kam lawuri agidan su Abu sufyan take da zama, kuma babu lafiya takanji hausa sosai harta mayar acikin gwarancin ta, ta karantu ba laifi a fannin addini ita da twins sun yarda cewar *Doguwar hanya* haske ce agaresu, yanda suka bi bisa k'addarar Allah haka tabiyosu bisa k'addarar Allah domin yad'uwar hasken musulunci, itada mom ma suna zaman lafiya yanzu, aure gaf yake da k'ulluwa a tsakaninsu da OGA shamsu.
Nak'udace ta tasowa zuhrah haik'an, babuji ba gani, a wannan lokacin kuwa Abu hurairah baya gidan kuma 'yar neman fitinar hanifer tana gun aiki, kiran duniya kam tayiwa Abu hurairah be d'aga wayar ba sabida baya kusa, haka ta juya akalar kiran wayarta zuwa gidansu inda tayi nasara mahaifiyarta tazo har gidan nata suka kwasheta zuwa asibiti, taci bak'ar wuya har sanda huraira yazo asibitin shida ahalinsa kanta samu ta haifi yaranta biyu duka maza kyawawan gaske masu tsananin kamanni da mahaifinsu tun suna yara kamanin suka bayyana, murna awurin Abu burairah ba'a magana baki har kunne, ba'a sallameta ba sabida wuyan datasha yasanya ma jininta yak'i ya sauka....... Tana kwance ita kad'ai a d'akin Abu hurairah ya shigo zama yae akujerar dake kusa da gadonta ya fuskanceta sosai yace
"Ina fatan miki samun lafiya me d'orewa zuhrah, sannu da fama Allah ya baki lafiyarki, nazone dama akan maganar mu ta kwanan baya, kin buk'aci rabuwa dani duk ranar da kika sauka lafiya, inaji mom taje da yara wurin wanka gida, so kema kuma munyi alk'awari dake akan duk ranar dakika sauka lafiya zan baki takardarki, toni nasan muhimmancin alk'awari, sabida haka ga wannan takardar seki nunawa iyayenki ki kuma gaya musu yanda mukayi tun farko.....nizan kula da yarana, wannan kuma kud'ine ki kula da lafiyarki zuwa sanda zaki fita ajego, nagode sosai da dauriyar ki har zuwa wannan lokacin, ina fatan zaki dakatar da faruk har zuwa lokacin daya dace kuma dukkanin wayar dakike dashi agidana na yafe miki seki neki Allah gafara sabida kinci zarafin aure" koda ya kammala maganganunshi bata fahimtar komai, cikeda firgici ta firta
"Kamun rai Abu hurairah karka rabani da yarana ina k'aunar na rayu dasu kaji" mik'ewa had'e da sanyawa fuskarsa murmushi yace
"Aikuma tun ran gini tunran zane zuhrah, yara ina tuni kikace zaki ijiyemun nine ubansu? Kinga bako semunja da tsayi ba, takardar nan ta gama raba mana gaddama akan wannan zancen, kiyi k'ok'arin sanar da iyayenki hukuncin dakika d'auka, yara kuma na d'auki abuna me reno zan d'auka" yana kaiwa nan ya juya, se faman k'walla masa kira take amma ko waiwaye beko waiwayo ba.
*Ina neman afuwarku, banida lafiya amma inshaa Allah zan daure zuwa sanda zamu kammala, zanyi a gurguje sabida yanayin lfiyata nagode da adu'arku*
Mom Nu'aiym.
[11/27, 9:48 PM] Maamah twinsđâ¤: 38****** kuka takeyi tamkar ranta ze fita, bazata iya fassara yanayin datake jiba a wannan lokacin, babu abinda takeso fiyeda ace yau gata ga yaranta, tasani tanaso tawa Faruk halacci amma ta dena waya dashi kwata kwata, ya kamata Abu hurairah yasan wannan ya barta da yaranta koda baze rayu da ita ba, kai ina bama ze yiyu ta koma gidansu ba mahaifinta ze hallakar da ita, wayarta ta zaro ta kira abu hurairah har ya k'araci ringing d'insa be d'aga wayar ba, ganin ta kirashi yakai so 10 be d'auka ba ya sanya ta juya akalar kiran wayar nata zuwa ga Ayusher, ringin biyu ta d'auka take sanar mata tana son ganin ta.
Babu abinda ta b'ye mata daya faru, take agun ta bata shawarwari masu kyau tare da nuna mata illar ha'intar aure be dace ba sam daganan suka yanke shawara akan ana sallamar ta su wuce gidan mom.
*********
*Agurguje plss*
Hakan dasuka yanke haka akayi, atake suka wuce gidan mom ana basu sallama inda murna suka tarar mom nayi hadda gud'a, soyayya me tsanani ke shigarta ta yaran duk yayin data kallesu seta tuna ranar haihuwar mahaifansu, bata tare da kowa se Baba Ladi, agida ta haihu amma taci bak'ar uk'uba sosai. Hurairah ma yayi mamakin ganinta gidan amma be isa yace komai ba haka ya zuba har ranar suna tana gidan amma babu mewa wani magana, su d'inma sunan da aka mayar musu kenan Hasan da usaini, aka laqabamusu Affan da haifan, an kashe dukiya kam ba laifi.
Har wannan lokacin Zuhrah bata bud'e takardan sakinta ba, washe garin suna tana zaune a d'akin da aka bata sega Abu hurairah ya shigo fuskar nn babu yabo babu fallasa ya kalleta sosai yace
"Ina kyautata zaton dakin bud'e takardar dana baki dabakiyi rashin hanklin zuwa gidan mu ba" batace masa komai ba sedai kam k'irjinta yayi mugun dokawa, kallon sa tae cikeda tsoro tunawan datae da takardar amma ta kasa furta wata kalma k'wak'wara
"Ki tabbatar yau kinduba takardar" ya fad'a sannan ya juya abunshi, kuka wiwi ta saka, kan daga bisani ta mik'e tsaye cikin rashin kuzari ta janyo handbag d'inta takardar ta d'akko amma har akafi k'arfin awa ta gagara bud'ewq, sea tayita faman du'a'i kafin ta bud'e takardar cikeda kasala, ga abinda akace
**** "Zuhrahty na sani nine na sab'a miki, nine kuma na janyo kika shiga halin tozarci da wulak'anci, kikaga rayuwa mara d'ad'i iri iri, amma ina nrman alfatmar yafiya, dan Allah ki yafemun, na tuba ina k'aunarki matata, banida kamarki uwar 'ya'ya na, ina me k'ara baki hak'uri akan abinda na miki abaya dakuma wanda nake sharin miki yanzu, kamar yanda mukai alk'awari akan idan kika sauka lafiya zan sauwaqe miki kije gidanku, to hakan bame yiyuwa bane ba, bazan iyaba, ina zan rayu babu farin cikina? Ina zan rayu babu rabin raina, ina zan rayu babu ruhina zuhra? Kece komai na ina k'aunar ki fiyeda tunani, ina miki sonso fisabilillah my zuhrah, kiyi hakuri zan baiwa d'an uwanki hak'uri akan matata inason abata ya janye yaje ya nemi wata kurin. Daga k'arshe ki sani wannan kalmar mara dad'i babu ita tsakanina dake har gaban abada, bazan lamunce taba, bana buka tarta bana sonta kuma har abada, bakuma zata tabbatar har abada, ina jiran amsrki ko nai miki fushi ki taimaki marayan nan dan Allah kinji?"...
Ta k'arashe karanta wasik'ar tana me daka tsalle da ihun murna, wanda yae daidai da shigowar Ayusher inda atake ta rungumeta, bata b'ata lokaci wurin sanar mata abinda wasik'ar ta kuns ba suka dinga murna da yaron cikin Ayusher amma haka take daka tsalle.
*****
*Bayan sati shida*
Aure dai a d'aura tsakanin Lawuri (Naja'atu) dakuma Oga shamsu, ansha budiri se murn suke dukkansu sabida sun fahimci juna sosai, mahaifiyar Lawuri tazo sedai mahaifinta yana jinya be samu zuwa ba, murmna kam bama sena fad'a ba awurin su....
Hanifer ganin ba sarki se Allah ya sanya ta hak'ura ta gbatar da tsohon saurayinta me suna khamis, inda aka shirya musu aure nanda 6month lokaci daya dana cyama da dawood.
Mom ta tuba da halayen sonkai tayita istigfari, ta yarda *Doguwar hanya* Alhkhairi ce arayuwar su, babu abinda yafi ace yau naka yay8 sanadin yad'uwar addinin Allah da guminsa, dan haka take godewa Allah da wahalar dasuka sha bata tashi a banza ba suke k'aunar junansu kuma sukai sanadiyar shiriyar wasu mutane masu d'inbin yawa.
Barbo tanata zuba soyayya da malam inda har ake shirin musu aure inshaa Allah.
*Tammat bi hamdillah. Bamso na tsaya anan ba, ban shirya dakatar da labarina anan ba, amma dalilai da dama sun tilstani aikata hakan, banida lafiya banida k'arfin dazan muku typing kowace rana, Allah shine ya d'auramun da wannan nake fatan zaku fahimceni, zakuma ku gane inda na dosa, a yanda dai na fahimta nake kuma zato, duk wani me hankali ya gan inda alk'alamina ya dosa.
Bazan manta kuna Masoyana dasuka siya littafin nan, Allah ya baibaiyeku da zuri'arku da d'inbin alkhairi ya sanya albarka a rayuwarku ya shiryar daku da yaranku da dukkanin zuri'a.
Bissalam.
Mom Nu'aiym
www.aihausanovels.com.ng For More Novel.
AIHAUSANOVELS is website consists of hausa novels note, the reason of launching this site is to Entetaint, Motivate and Educate our readers.
We provided hausa novels of many type, Such Adventure, love, romance, fiction, non-fiction, mystry, fantasy, action e.t.c from hausa Authors
We provided a new and old novels both softcopy and hardcopy from our Author with thier permission.
AIHAUSANOVELS shafin yanar gizo ne wanda yake Éauke da littattafan hausa, dalilin bude wannan shafin shine domin Kayatar masu karatu da kuma ilimantar da su.
Mun samar da littattafan hausa na nau'uka daban-daban, kama daga littafin, soyayya, tatsuniya, almara, Hikayoyi, gyara kayanki (yadda mata zasu kula da kansu a gidan mijinsu) da dai sauransu, daga Marubutan hausa.
Downloaded From https://arewanovels.com