You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
tunda hotel ne, gashi batada lafiya scaning ma takeso amata amma abun ya gagareta asibiti sun gaji sun koreta, asibitin datazo da hotel datake zama ma akwai jayawa gashi 600 kad'ai ne a hannunta ga yunwa, yaudai ta yanke shawarar komawa gun iyayenta hatta wayar da aka siya mata ma ta siyar ta cinye kud'in, da k'afa take tafiya gashi tarasa dalilin kumburin jikinta, cikinta yayi saurin girma wataninsa dudu nawane hud'u fa amma kaman gobe zata haihu, jiri ne yasoma kwasarta adaidai sanda tazo tsallaka titin dashine ze sadata da gidansu General kuwa adaidai nanne yake shigo layin yana k'ok'arin kaiwa mahaifinta ziyara domin su nemi mafita dan tun ranar ya taresa da maganar ma, Kad'an ya rage su bigeta seda koda basu kad'e tanba fad'uwa tayi a k'asa warwas!!!
Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins๐โค: *๐๐DOGUWAR HANYA....๐๐*
*Billy Galadanchi*
*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*
*Book nawa na kud'ine, idan kinsan baki biyaba dan Allah karki karantamun kokimun sharin book nawa a groups, idan kina buqatar siya ki nemeni ta wannan number 07084161619.*
28
Sauka sukai daga kan titin suka fito da sauri duk sukai kanta, basu b'ata lokaciba wurin sakata a mota su juya akalar motarsu zuwa asibiti bayan da suka dire General agidan yabasu umarnin su kaita asibiti cikin gaggawa.
Wayar ya zaro a daidai sanda yazo shiga k'ofar parlor bayan an masa iso, Abu Hurairah yakira
"Hello Dad" cikin dakakkiyar murya yace
"Kana ina ne?" Saisaita nutsuwar sa yae
"Dad ina kan hanya da zanje gidana"
"Kaje National hospital na tura wata patient dana kusan bigeta a titi amma seta suma kaman fad'uwar gabane,tare dasu umar take da sauransu u contact of them, kaje ka biya Bill nata ka tabbatar duk wata kulawa ta samu, ka jira a wurin idan ta farfad'o ta gaya maka gidann su asanar da mijinta ko iyayenta halin datake ciki" kafin yae wata maganar harya kashe wayar... Juya akalar kiransa yae zuwaga Abu Sufyan yace a sanar masa yazo ya sameshi gidan zasu koma gida atare.
*********
Kai tsaye asibitin ya nufa yaje ya tarar sun karb'i patient d'in nurse d'in se mita takeyi
"So nawa zan gaya muku bazamu karb'i patient ba kud'i ba, gata da hawan jini ga k'aton ciki agabanta da 4month, tarasa duk duniya wanda ze biya mata kud'i a duba lafiyan ta dana babyn ta, wanda suka kawota idan bazasu iyaba su koma da ita gaba d'aya" matsowa yae dan sojin sun gayamai patient da suka kawo ce akewa wannan izgilin ya kalli nurse d'in
"Meye bill nata duka abinda take buk'ata?" Kallon shi tayi amma bataga alamar wasa ba
"72500 duka kud'in ta ta gagara biya se sintiri take anan" hararata yae
"To zamu biya ki kula da ita cikin gaggawa" ya juya batare daya jira cewar taba, rashin zuhra yana neman hallakar dashi ma gaba d'aya zata bashi haushi akan wasu tsirarrun kudad'e.....Befi 1 hour dazama ba nurse din tadawo gunsa
"Sir likita yanason ganin wanda yazo da patient d'in d'azu" kallon ta yae kafin yaja gajeran tsaki ya mik'e
"Muje" haka suka rankaya har gun likitan, sun gaisa sannan ya zauna
"Dama kane mijin waccen yarinyar, a gaskia kun kusa kasheta yarinyara batada lafiya ga juna biyu amma baku kulaba, ita batacin komai na gina jiki ga yara biyu acikinta ga pcv d'inta yaje down sosai yanzu haka 24% yazatayi surviving da shi gabyara biyu ga hawan jini? What on earth were u doing daze sanya kabar iyalanka su shiga fitina har haka" kallon mamaki yama Dr. D'in amma kfin ya samu damar magana likitan yaci gaba
"Thank God yaran suna lafiya, sedai basuda wani nauyi sabida yunwa basuda kuzari sabida babu wadataccen jini ajikin uwar, yanzu zamu baku cross marching na jini kaje a gwada naka idan zeyi da gaggawa muke buk'atar sa idan bazeyiba ku siya kawai sabida bamuda lokaci wannan ze iya sakawa ta rasa rayuwarta har abada" Mik'ewa likitan yae bayan ya tura masa takardar gwajin ya shige ban d'akin dake cikin toilet d'in nashi, mik'ewa yae jikinsa a sanyaye yakira dad yake sanar masa
"Kaje a gwada jinin naka idan zeyi ka bayar" kan yae magana har Dad ya kaste kiran, yaya ze bayar da jininsa ga wacce beko santa ba? Ko ganinta be tab'a yiba haka yake yaja soja uku akaje gwajin a lab duk nasu baya yi senashi, haka aka eba se qunquni yake aka bashi gado domin ya huta na 1 hour koda yazo har an soma d'ura mata jinin, shiko kallon tama beyi ba yace zeje ya dawo da dare.
***********
"Maganar auren nawane bakyaso kuma Ayusher? Mena miki yanzu wai kika tsaneni haka?" Kallon sa tae tana murmushi
"Ba abinda kamun nikam kurun dai nabaka damane ka wofintar yanzu kuma kaga Raubil ma yazo yace ze gabatar da manyan sa ya kakeso nace masa? So tari abinda muke rainawa shine yake mana wahalar samu wataran, kayi hak'uri kawai kaje gun Lawuri ka koma doguwar hanyar dazata sadata da garinsu ka aurota tunda Abu Huraira be samu ba" sumar kanshi ya shafa
"Ayusher pure heart d'in ki nefa? Wani kallon banza ta masa
"Pure heart d'in kuwa to sai me?" Shiru yae maganar tafi k'arfin sa yace
"Zan koma sena kiraki a waya" murmushi ta k'arayi
"Base ka kiraba idan na nutsu zan kiraka da kaina" murmushi shima yae
"Ba damuwa nagode" daga haka ta juya shima yabar gidan zuciyar sa ba dad'i.
********
"Me kake tunani game dani ne wai Al-hassan?, tun jiyan dama baka koma ba? Haka mukai dakai? Bance ka bari ta farfad'o ka nemi iyayen taba, kasan dama ina cike dakai ne fam ko? Wlhy ka kiyayeni maza katashi kaje ka duba ta, zancen yarinyar cen kuma anduba duka dangi kaf bata cen sekasan nayi" godiya yae ya mik'e jikinsa a mace zuwa gunta.
Anyi nasarar fitowa daga jeji su Lawuri sedai en riga sun kafe akan bazasu rakasu wajen gari ba, da k'yar me gari danya sanya ya basu kud'in jirgin dazasu hau su tsallaka ruwan na garuruwa uku, gasu dai a inda zasu hau mota amma ko anini basuda shi, ta rik'e sunan Abuja rad'au sedai bazata iya kai kanta gidansu ba, abu d'aya ta sani kota halin yayane setaga Abu Hurairah, kwanansu hud'u suna kwana a tasha, har lokacin motar ma taba tashi se bayan sati biyu kuma, mutanen garin sun soma gajiyawa dasu suna yaren fulani suke jiba.
*********
Kai tsaye wurin gadon patient d'in yaje ya kalleta tana baccinta cikin nutsuwa, wutsiyar hannun ta ya kalla ya tuna last maganar su sanda suka kwana hotel data karb'i wani agogon fata daya siya dasuka isa garin tace tanaso, shine rad'au a hannunta, d'ayan hannunta na dama sanye da ruwa ana k'ara mata, murza idansa yae cikeda mamaki, lokaci d'aya maganganun likitan nan suka dawo masa, kenan dukkaninsu akan shi yakeyi, dama zuhra ce ke cikin wannan mawuyacin halin lallai ya aikata zunubi Allah ma baze barshi ba........ Zama yae a d'akin har kusan sa'a fiye da d'aya seda ta farfad'o sannan ya tashi da azama yae kanta
"Zuhra sannu ya jikin?" Kallon mamaki take binsa dashi, runtse idanta tae gagam cikin rashin fahimtar komai, kafin ta bud'e su ta zuba su akansa
"Al-hassan inane nan mafarki nake?" Girgiza masa kanta yae
"Bakida lafiya please save your strength basekinyi magana ba, basekinyi tunani me yawa ba Al-hassan ne" rufe idanta tae kurun tarasa tunanin me zatayi.
*********
*Bayan sati biyu*
Babu yanda iyayen ta basuyi ba amma ta kafe ita lallai idan ta haihu yaransa zata bashi su rabu, yama sauwaqe mata auren sa itakam inyaso yama haihuwa tayi iddah kenan, anyi anyi taqi, taji zafin abinda ya mata sosai taji zafin tozarcin daya janyo mata yaci amanar ta fiye da k'ima, ya tona mata asirinta dan haka ta kafe
"Ina ga zmu baku sati biyu nan gaba, ku sasata kanku, idan har kayi galaba akant ta hak'ura shi kenan amma idan har Zarah tace bazata koma ba a gaskia ni bazan tilasta mata aurenka ba, kaima shaidane akan abinda kayi sam sam baka kyautaba wlhy" shiru yae daganan aka basu wuri, mik'ewa tayi
"Idan da zakabi shawara Ko Al-hassan karka wani jira sati biyu suzo danko shekaru biyu suka zago nida aurenka har abada" kanma yace wani abin tayi ciki, gabaki d'aya duniyar juya masa take, shi yama rsa dalilin daya sanya yakejin sonta har cikin b'argon sa yanzu, ya tabbatar Allah ne ya jarabcesa da sonta dan ya wulak'anta aure.
**********
Su Lawuri dai se gasu asaman lodin yaji, sabida rashin kud'i yunwar cikinsu ma ta ishesu ga gardawan garin su sun koma dama haka akai dasu, bamusan yanda zata kaya ba idan suka isa OGUN state gamu gani dai.
Mom Nu'aim.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins๐โค: *๐๐DOGUWAR HANYA....๐๐*
*Billy Galadanchi*
*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*
*please idan kinsam baki siyaba bakida haqqin sharing ma family and frnds, idan ma kin siya ban yarda ki tura a groups ba indai ba k'awarki ba, idan kika tura a groups kina kashemun kasuwa ne, me buqatar siya 07084161619*
29
Lawuri tunda suka shigo garin OGUN STATE take rarraba ido, duk wanda suka gani zasu masabyare sama Allah ya taimakesu akwai yarbawa sosai a garin, idan tace Abuja take so suje se ace akwai nisa sesun hau mota, sunyi yawo harsun gaji, atasha ma cewa sukai a sakasu koda saman motar ne amma aka koresu akan basuda ko k'wandala.
***
Dafa hannunshi yae bayan ya gama jin komai
"Haba Hurairah, sekace ba namiji ba, karka kulata kuma koda zata kasheka karka saketa, kayi amfani da iliminka da basirar wurin ganin ka saka ta soka kota halin yayane" kallon Dawwo yae cikin damuwa
"Dawood koda inason inyi hakan dole seta bani damar yin hakan, bata fitowa koda zuwa nayi gidansu fa, waya inta kira bata d'agawa wani zubin ma sekaji wayar a kashe" Dafe kanshi yae
"Muje gidan yanzu" ya furta bayan daya d'ago yana kallon sa, ba musu ya karkata akalar motar sa zuwa gidan nasu, me gadi na ganin motar sa ya wangale masa gate ya zura kan motar ciki, suka parka suka fito.
Abu hurairah yasha mamakin jin dawood yace akira masa mahaifiyar zuhra, bayan tazo kuwa suka gaisa cikeda mutunci yace
"Dama Mama zancen daine na zuhra da kuma Abu huraira, labari ya samen akan hukuncin data yanke masa, yanata k'ok'arin ya gyara kuskuren sa amma be samu damar hakan ba, sabida bata bari ya ganta ga kuma sam bata d'aukar wayarsa, wlhy mama bmason mutuwar auren nan wancen ma abun yarasa yanda ze fad'a ne kamar yanda ta gagara gaya muku, sabida dukkansu suna tunanin bazaku yarda dasu ba, ga kuma besn an samu k'aruwa a tsakanin su ba" Jinjina kai umma tayi
"To yanzu ni wace gudunmawa kuke tunanin zan iya baku a rayuwa? Ni nafiku qin yanda auren nan yake shirin lalacewa amma ya zanyi, matsalar Bintu halin mahaifinta sak tayo, kafiya sosai idan tajewa abu, nayi nayi nima sedai adu'a kawai" Nisawa yae
"Nasani babu uwa ta gari dazataso mutuwar auren 'yarta Mama, Doguwar hanya tayi sanadiyar zuwan auren haka, amma idan so samune a bashi damar ziyartar ta a d'akinta, tunda bata bari su gana dole seda hakan" murmushin manya uwar tayi sabida ta kula dawwod duniyanci yazo dashi a ladabce
"Duk inda ze ganta ai iyalinsa ce har yanzu, bayida shamaki da wannan indai ganin matar sane, ko yanzu ya shirya zan sanya a kaishi b'angaren su, dayake b'angarena daban nida su, se Hafsat tazo ta rakashin" Murmushi yae
"Hakane mama mungode sosai da fahimta, kuma dan Allah muna roqon iri aci gaba dayi mana ban hak'uri, lallai bamu kyautaba amma muna neman yafiyar ta daku baki d'aya, muna kuma neman alfarmar abamu wata damar domin gyaran b'arakar damuka aikata" Godiya tae mus sosai da karamci sannan ta juya domin turo hafsat sabida tayiwa Abu Hurairah iso zuwa wurin Zuhra batare da sanin zuhra ba dan idan tasani seta datse k'ofar......
Akaratun k'urani me girma takeyi daga ita se er vest duk ta gama d'ameta d'am, zafi sosai takeji wannan ya sanya ta rufe iya kanta sabida ambaton ayar Allah, taji sanda ake knocking k'ofar amma batace komai ba seda takai aya, sannan tace
"Waye" hafsat dake tsoron masifa tace d'ari d'ari
"Hafsat ce anty" tsaki taja tace
"Kije bar wanki anjima kya had'a" kallon Abu Hurairah tayi tace
"Ka shiga kawai, kayi sallama" tayi 1mns dabarin gun kafin cikeda jarumta ya d'aga k'farshi ya tura k'ofar da sallama d'auke a bakinsa murya k'asa k'asa, waigowa tai a daidai sanda ya shigo d'akin gaba d'aya, da zama cikin dabaru na masu ciki ta mik'e cikeda mamaki
"Al-hassanx meye haka? Yaya zaka shigomun cikin d'aki babu izini, beside wayema ya baka damar ka shigomun d'aki waya nuna maka nan d'in?" K'ura mata ido yae cikin kasala ya gaza furta wata kalma gaba d'aya yaran cikinta tunka suzo duniya yaji yana musu wani so dabesan akwai ironshi ba a duniya, ganin kallon ya ankrar da ita yanayin shigar ta, da sauri ta zari ta janyo hijab zata saka yae azamar rik'e mata hannu, kici kicin k'wacewa tashigayi cikin azama yae saurin k'wace hijabin ya jefar gaba d'aya, cikin zafi tace
"Wannan wane irin wulak'anci ne abinda kazomun dashi kenan har cikin gidan ubana? Me kake tsammani danine eh?" Manyan idanuwan shi ya zuba mata tanata masifa, be cika son surutu ba halin yana nan tunda ya shigo aikin kenan na zuba surutu
"Zuhrah calm down mana, bakya ganin bake kad'ai bace ba?" Kallon sa tae cikin takaici
"Nida waye? Idan ma mu dubu ne meya shafeka eh?" Mamakin tsiwarta yake ba haka ya santa ba sam
"Kiyi Hakuri zuhrah dan Allah ki baki second chance wlhy zan kula dake" Tab'e bakinta tae
"Nagaya maka neman kai nake da kaina? Kokuma rasa me kulawa dani nae, niba yarinya bace ka sauqwak'e mun zan kula da kaina" Fuskar sa ya kwab'e tamkar zeyi kuka
"Haba Zuhrah anya wannan hukuncin bemun tsauri ba ya dace ki saurreni ai ko?" Tureshi tae iya k'arfin ta
"Sanda ka wulaqanta budurcina neman ka nai? Sanda ka ketamun haddi na nemn ka nae? Sanda kake zuwarmun da sauk'i alfarmar hakan na nema? Kokuma aa sanda aka mana aure ban nemi shwararka, dangina kowa ya d'auka shege nayi har masu aikin gidan nan da masu gadin k'ofa gulmana suke akan nayi shege, ban tab'a aikata zina ba duk zamana a jeji kame nake sa kaina sabida mutuncina dana iyayena da hakk'in musulunci, ka sanya ina cikin gidanmu amma zuwa tsakar gida seya gagaran sabida bakowa ya gama yarda dani ba, Allah kad'ai ne yasan wanda bazuwanka ba ko'a gabansa aka d'aura aurwnmu baze yarda dani ba sabida mugun abun daka aikata mun, na rayu wulak'ance a hotel sama da watannin biyu, naga wulak'anci harme gyaran d'akunan hotel seda yanemi yin lalata dani danyasan halacci baze kaini zaman hotel ba, na wuni da yunwa na kwana da yunwa duk a ta dalilinka, ka d'irkamun ciki ka barni da d'an hals ana cewa shege, me ya saura zaka gayamun? Kai a tunanin ka wannan abubuwan zasu gogene duk a wuni d'aya? Kana ganin akwai ranar dazatazo dazan yafe maka ma bare ayi zancen wai mu zauna a inuwa d'aya ta miji da mata, kayi kuskure wlhi Abu Hurairah, hakk'oki'ina daka take bazan yafe ba har abada, kuma kome zakace na dad'in baki na gama zaman aure dakai damacen rabon wannan cikin ne maza kaficemun saga d'aki" Jikinsa yayi mugun sanyi ba abu bane me sauk'i kam ace wai ta yafe masa a yanda ta d'auka da zafin nan, yama rasa me zeyi, bashida bakin magana gwiwa a sace ya baro d'akin batare daace kanzil ba sam yawun bakinsa bazasu isheshi ya kashe bushewar mak'oshin saba!!!
*********
Tunda ya soma magana dad ke kallonsa yana murmushi
"Lallai Al-hussain ba kunya, yanzu dai so kake inje nema maka auren Aisha kenan? Lallai ma dole inwa wannan aure" sadda kanshi yae a k'asa batare dayace k'ala ba yana zuba murmushi
"Katashi kaje zanyi yanda ya dace kaji?" Shiru yae ya mik'e aranshi yanajin dad'in wannan ita kad'ai ce hanya madaidaiciya....
Waya ya kida mahaifin Aysuher akan yanaso suzo zancen yaran, Alhaji yusha'u yace
"Ba damuwa Ganeral ran sati su yaya Mu'az zasuzo dama inyaso se kazo kaima ranar lahadi da safe semu zauna a tattauna kawai" godiya ya masa kan suyi sallama.
********
*Bani tunanin Yusha'u kanada hankali wlhy, Aishan yarinya ce? Akan me bazamu d'aura mata auren yanzu ba, ina manemin auren ba mara k'arfi bane? Tun yaushe muke bibiyarka akan batun nan? Kana sani ka take zancen mu ka turata london, shekarunta 4 acen, ta dawo munata zamcem aure kace wai ba miji yanzu shekarunta biyu kenan da dawowa, akan me zaka nemi mayar damu k'ananun yara, to zab'i ya raga naka kodai ka janye sha'anin dogon burin nan naka akan bidi'o'in banza kokuma na aura mata Auwalu ina komawa kai kokumama wlhy tallahi nida al'amarinka dana iyalanka har abada" mahaifin Ayusher sadda kanshi yae k'asa ganin yayanshi yanata yarfashi agaban manyan mutanen dasuke girmamashi gashi babu halin musawa
"Kayi hakuri Yaya Hamza, duk yanda kayi ai daidaine, dakai da kaya duk mallakan wuya ne, idn auren a d'aura a yanzu yafi maka kwanciyr hankali ai banida ikon hanawa, dama shawarace na bayar kuma tunda batayiba ai dole a duba mafi maslaha" kallon General yae
"General bakada damuwa idan aka d'aura auren a yanzu? Inyaso kaga daga bisani ta tare?" Murmushi general yae wannan shine ikon Allah daga zuwa zance se daurin aure, cikin murna yace
"Ba komai a shirye muke ku yanka sadaki inyaso ko daga bayane sea shirya zancen tariya da sauran al'adu wannan ai shine me wuyar.
Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins๐โค: *๐๐DOGUWAR HANYA....๐๐*
*Billy Galadanchi*
*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*
30
Acikin yaren su ta kalli Barbo tace
"Barbo na gaji ga uwar yunwa inaji, da zan samu zomo ko burgu dana gasa naci" cikin takaici Barbo tace
"Ai nan babu jeji, sedai hak'uri kwana biyu sedai musha ruwa, ranki ya dad'e ki daure mu koma gida tunda kinga bamusan ina zamu dosa ba, nan seda wannan takardun ake baka komai fa" shiru tae tana nazarin kalaman Barbo
"Barbo kiyi hak'uri amma bazan komaba sena ga hurairah gaskia,inason in zama kamar su ke bakiga rayuwar rashin 'yancin damuke a wancen jejin ba, kinga Sufyan ya gayamun su musulunci suke kuma akwai Allah yace dani, inaso inji qarashen labarin dayake bani, ban manta komai ba na yaya sufyan, ya sanar dani akwai abinda ze taimakeni sa al'ummar mu kowa yashiga haske, wace komawar bayan zata mayar dani kuma, kina kallo suturar jikin su ma da banbanci da tamu mu muna rayuwar wahala ne amma bawai suba" shiru Barbo tayi tana nazari cikin mamakin kafiya irinta Lawuri koda yake haka mahaifinta ma yake.
***********
Ganin abun yazo da sauqi ya sanya suka yanke shawarar gayawa sufyan, ba shiri ya janyo twin d'inshi aka bazamo, General bashida d'an uwa nakiji dama se mace suna kuma shiri sosai da mijin na yayarshi mahaifiyar hanifer dan haka yamai waya shima cikin qalilan d'in mintuna yazo da goro, atake aka yanka sadaki aka biya sannan aka d'aura musu auren, Abu Sufyan dukda bawani jin Ayusher yakeba seya tsinci kansa cikin tsananin farin ciki mara misaltuwa, se washe baki yake tamkar gonar auduga, haka dai taro ya watse yana cikin tsananin farin ciki.
Mommyn Ayusher ma murna tayi sosai dajin zancen agunta wannnan babban blessing ne bako qarami ba ace 'yarka ta samu daman yin aure cikin k'ank'anin lokaci....
Zaune take agaban dad da yaya Hamza ta duqar da kanta tana sararen bayanin Baba hamza dake tabbatar mata ta kame k'afanta daga fita konan dacen seda izinin mijinta tare da bayanin yanayin suturun dazata saka yayin fitar bayan tabbatar mata an d'aura aurenta da sufyan, ya k'ara da cewar
"Arziki kikayi dama ya kasance gwaninki ne aka d'aura miki auren dashi dabadan shi yazoba da babu Abinda ze hanani had'a aurenku keda Auwalu d'an gidan Baba tete ki koma cen da zama tunda sakarci kika saka a gaba shashasha kawai" Jin komai takeyi tamkar a mafarki, babu abunta take ganewa sam!! Tana cikin rud'u bata gane an d'aura mata aure da Sufyan ba? Sekace wasan yara? Ko zawarawa ba'a wa haka beside ta dad'e da cire Sufyan a ranta sabida sam bata gaban sa.
"Abba dan Allah kayi hak'uri wlhy ni na fasa sufyan d'in" kallonnta yae cikin mamaki
"Tonidai matsayina na ubanki da musulunci ya bani hakk'in d'aura aurenki da wanda naga ya dace ban fasa dashi ba kuma nacika umarnin musulunci, idan kin isa karki masa biyayya" kuka ta saka wiwi cikin tashin hankali daddy yace
"Kiyi Hakuri Aishana, babu abinda ze faru dake se alheri, kedai kawai kiwa iyayenki biyayya kuma ni nasan kinason Sufyan shima kuma haka, bakiga yanda yake fara'a ba kafin ma a d'aura sabida haka kema ki rungumi k'adsararki hannu bibbiyu tashi kije" haka ta wuce cikin gidan tanata zubar da hawaye tasani Abu sufyan baya sonta batasan mesa ya zab'i aikata hakan agareta ba, dudu yaushe tace masa ya rhakura da ita? .....
"Amma general ni gaskiya ba'a kyautamun wlhy, kenan duka yaran haka zaka dinga musu aure sekace wasu tsofaffi auren fari babu wani armashi, kuma ace waini banida hakk'in dazaka kirani koda a wayane kaji ra'ayina anci zarafina gaskia" Takaicin mom dad keji sosai
"Anqi aji ra'ayin naki, shashasha kawai, kina tsufa kina zabga shirme, munje nema an bamu semuce bama so, suda sukeda mace basuji zafin bayarwa daga sama ba seke, sannan ina kinsa da zancen zuwa neman auren? Bama wannan ba dakike zancen Abu hurairah nina d'aura masa aure? Look adama dena ganin ina baki dama kina murzamun shirme, wannan karon bazan lamuntaba ki sakawa aure albarka faqat" sanin halinsane ya sanya tayi shiru badan ta hakura da masifar ba, cikin mugun takaicin sa take bako kad'an ba badai tada yanda zatayi bane ba.
**********
Yauma Hafsat ce tawa Abu hurairah jagoranci zuwa d'akin Na Zuhrah, be b'ata lokaci ba wurin shiga da sallamar sa, had'e da turo k'ofar ya rufe, bata cikin d'akin amma ya jiyo k'arar ruwa a ban d'aki, wannan ya sanya ya zauna ya k'urawa d'an k'aramun plasma Tv dake manne a bangon d'akin ido, a zahiri kallo yake amma zuciyar sa da tunanin sa sam basa gurin sun tafine wurin tunanin wata duniyar ta daban, lugude ma qirjinsa keyi sabida fargabar zuhra da fitinarta, yana nan yana nazari harbesan sanda ta fito ba, seda yaji ta rufe k'ofar, iya towel d'aure a k'irjin ta kuma sarai ta ganshi agun amma setasha mur tayi tamkar bata ganshi ba, mik'ewa yae ya matsa inda take, kallonta yake ita d'inma shita zurawa na mujiya
"Zuhrah" ya ambata cikin wani yanayi, ita yau batajin rigimar shisa ma batako ce masa k'ala ba
"Dan Allah zuhra ki gafarceni" kallonsa take har yanzu amma tarasa kalaman dazata masa magana dasu, hannunta ya rik'o ta warce da sauri, ya k'ara k'ok'arin riko hannun nanma warcewa tayi, besan menene Allah ya jarabcesa dashi ba akan zuhrah kwanakin nan, duk jarumtarsa ji yake tamkar yae mata kuka, gaba d'aya ya rungumeta ajikinsa, jikinsanhar rawa yakeyi
"Kiyi hak'uri zuhra, dan Allah kiyi hak'uri ki gafarceni wlhy bazan k'araba jar abada" k'ok'arin k'wace kanta tashigayi amma ya matseta, nutsuwa tae ganin bazata iyaba ya kai bakinsa saman wuyansa ya sumbaceta, ya janye bakknsa zuwa saitin kunnenta yace cikin rad'a
"Kiyi hakuri zuhra, ki taimakeni ki janye zancen rabuwar nan bazan iyaba, doguwar hanyace sanadin had'uwata dake na tabbatar Allah baze tsara hakan ba face alherine agaremu baki d'aya, ki tausayamun na tuba kinji" batace masa komai a haka ya soma k'ok'arin shafar jikinta, zare jikinta tae
"Al-hassan dan Allah kamun taimakaon dazaka janye wannan maganar, bana buk'atar auren kwata kwata" zama yae a bakin gadon ya janyo hannunta ya mata masauki akan cinyar sa
"Fatima!" Ya kira sunanta da kakkausar murya, jin yakira da hakan ya sanya ta kalleshi
"Kinsan kalar tsinuwar da Allah yawa matar dake neman saki daga wurin mijinta kanta tsaye, mena miki fatima? Meye laifina, samsam bana tunanin nayi