You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
oho har ya kwana bakwai a hannunsu babu wanda ya tab'a alamun nuna masa zasu cutar dasu kurin irin kayan jikin sune ajikin sa.....
***********
*Bayan 2 weeks*
Gaba d'aya su OGA shamshu sun zagaye k'auyukan kusa dana kewayen jejin basu samu Abu Hurairah ba, wannan abin ya tashi hankalin su, har garin su Lawuri sukaje amma se sarki K'uru ya tabbatsar musu cewar shidai kam sam bega koda alamar wani yazo garin ba, ya nuna musu damuwar sa akan 'yarsa ya k'ara da cewan baya neman kowa da tashin hankali amma dai yanaso su dawo masa da 'yarsa da wannan suka masa alk'awarin neman ta su dawo masa da ita sannan sukai gaba, su kansu sunsha wahala kafin su d'auki hanyar gida......
************
Tunda OGA shamsu ya soma magana general yake kallon sa har inda yaji k'arshen labarin sa, dukda sanyin Ac dake kad'awa a d'akin hakan be hanashi tsiyayar da zufa ba tako ina ajikin sa, meze gayawa Adama? Da wacce fuska ze kalleta? Me kenan ya aikata? Allah ne shaidar sa yayi hakan domin musulunci da k'arin yad'uwar sa,be tab'a zata abun ze juye haka, mik'ewa kurun yae yabar parlor zuwa saman sa, rayuwar a cunkushe ta ina ze fara ne wai?..
Tsit kakeji a parlor d'in tamkar babu wani mahaluki aciki, bayaga yawaitar dokawar zuciyoyinsu babu abinda kake jiyowa, luguden da zuciyar kowannen su keyi yana tafiya ne tare da tsetserereniyar saukar numfarfashin dukkansu sauri sauri, Abu sufyan shine ya soma mik'ewa a haukace
"A gaskia wlhy ni senabi bayan d'an uwana, kome ze faru sedai ya faru amma bazan dawo ba sena nemoshi, duk laifi nane, dana sanar masa nasan inda yarinyar nan take dabe shiga hatsarin rayuwa har haka ba, dana sanar masa tana guna na b'oyeta dabe tafi yabi wannan muguwar Doguwar hanyar ba, ina zanbi inji sanyi arayuwa ta? Na rud'ar da rayuwar sa na sakashi acikin rububin duniyar dabe sab da irin taba, innalillahi wa inna ilaihiraji'un" Rik'oshi Oga shamsu yae
"Kashiga hankalin ka mana sufyan kana haukane? Koni nan danake soja bazan tinkari wannan hanyar ba shiri ba, me kakeso ka aikata kenan?" Haka aka dinga rarrashin sa, sedaga bisani hankali yakai kan mom dake dafe da xuciyarta tana numfarfashi da k'yar, kowa gunta yae yana qoqarin taimaka mata.
*********
Yaudai sandan dasuke fad'a dashi suka baiwa Huraira, tare da kokarin koyar dashi yanda akeyi, kanshi gaba d'aya ya kunce ga tsoro yanaji bashida dabaran daya wuuce yae yanda suke so, haka yae kusan sati d'aya yana koyan wannan wahalar ba dare ba rana, yasha wahala da bak'ar azaba mara misaltuwa akan wannan koyon fad'an, daga bisani suka soma fita dashi yawon jeji, abinda ya lura dashi shine sata sukeyi, duk wani gari dake kusa sesubi dare aje ayi satan kayan abinci idan ka kara musu su fasa kanka, haka nan dai yaeda walagigi acikinsu dukya rame yafita hayyacinsa, yana bak'in cikin wannan rayuwar dayake cikinta a yanzu, bek'i Allah ya d'auki ransa ba kwata kwata ya huta, be tab'a tsammanin zsyi makaman cin wannan d'abi'an ba, ranar daya bari wani dasuka kama ya kufce kuwa yasha mugun duka harseda yae jinyar kwana biyu, gashi sun lula dashi wata duniyar har naman jeji kake gani a wannan jejin masy matuk'ar cutarwa.
***********
Bako kad'an ba Ayusher ta juyawa Sufyan baya, bata damuwa dashi sam kuma dole seda ya kawo me kular masa dame karayar dukda tasoma takawa dakuma Lawuri wacce ba laifi kad'an kad'an takan gane hausa sabida tanada kan d'auka har kuyangar tama takan gane musamman dayake dai idan kamata magana da hausa tana ganewa sedai tayi wahalar mayar maka seta had'a da yarenta, yanzu kam Alhamdulillah Ayusher dama ta rage damuwa dashi tadoma jin sassauci me yawa akan rad'ad'in k'aunar da ada takeji tasa.
*************
Zaman dasuke yanzu yasoma tab'a abu hurairah kasancewar akwai sanyi sosai suba ba zama gu d'ayaba sekace fulanin tashi, sannan ba yarensu yake ganewa ba se maganar kurame, acikinsu akwai wanda suma aka kamo sedai ya kula dukkansu k'abilune kuma arna ne duba da yanda suke yawaita adu'a, se wata mace d'aya da hankalin sa ya kaishi wurin yawan yin sallar ta dukda rabin jikinta a bayyane yake se ganye dayaga duk zatayi sallah takan rufe jikinta da ganyaye har kai, anan yazo ya sameta sedai ya kula sam bata magana, tana burgeshi sosai yakusa Allah kurin ta saka agaba, yau ranar hutuce ba'a fita farauta ba'a kuma zuwa ko ina dan Haka zazzaune kurun ake ana hira masu maganar nayi masu wasanni sunayi, acikinsu har qananun yara akwai, yakula suma sunsan meye aure basa tab'a matayen daba nasuba, dukda matan basudabyawa sedai idan za'a saiya shek'a ayi busa kaga mutane kaman tururwa, abinda yakula shine sun rarrabu ne kurin. Yana zaune shiru kamar kurma tazo ta zauna kusa dashi sosai, cikin basarwa kamar bazatayi magana ba tace masa
"Sannu malam, kamun kamada k'abilarmu ta bahaushi, nakuma tabbatar kai musulmine tunda kake salla" waigowa yae ya kalleta cikin mamaki kafin yace
"Dama ke bahaushiya ce? To baiwar Allah me kike anan?" Murmushin takaici tayi ta kawar da kanta gefe d'aya akaro na barkatai
"K'addarar bautar k'aza, daga zuwa bautar k'asa shikenan na zama tarihi shekaruna uku kenan anan" Mamakin fuskar sa ya k'aru yace
"Har 3 yrs, amma dayaya hakan ta faru?" Langwab'ar da kanta tae cikin tsananin damuwa
"Dogon labari ne, ni yanzu taimakona zakayi dan Allah" shiru yae kurun ita kuwa taci gaba
"So nake mubar nan jejin ina nufi mu gudu, nayita neman guduwa ana k'ara kamani, amma yanzu abu d'aya ne ze tserar damu, dagani har kai, kaga dolen duniya ni yanzu nasoma iya yarensu ma, konace na iya ma, bankosan sunan yaren ba kuwa, abinda yake faruwa anan shine kana da damar kayi yawo kai kad'ai idan kanada mata, ko kuje tare da ita kokuma kai kaje kai kad'ai, tokuma ni anan ban samu mijiba wanda da suka so auramu an kashesa agun farauta, shine nakeso nidakai amana aure, zanwa Songai magana ince munason junan mu, kaga idan aka mana aure semu soma fita yawo muna dawowa a hankali a hankali wataran semu gudu gaba d'aya bayan sun sake jiki inda duk mukaje zamu dawo, kaga anan mun taimaki juna ko kuwa?" Shiru yae nad'an lokaci secen yace
"Zanyi runani akan wannan maganar amma dai kinsan wannan auren dazasu d'aura mana bawai ze auru bane ko? Sabida basusan meye musulun ciba ma" murmushi nanma tayi
"Nida kai gwara mu d'aura auren gaske, na yanka sadak'i koda irin aikine kamun ladan auren mu, inyaso wancem k'abilun zan musu dabara inji kozasu mana shaidu" murmushin baqin cikin hurairah yae shi ganin komai yake tamkar a mafarki kafin yace
"Daga wane garin kake a garuruwan hausawa? Kuma ya sunanki?" Kallon sa tae
"Daga garin sokoto nake, amma muna zama da iyayena a abuja ne,sunana Fatima bintu zahra, mahaifina yana kirana da sunan zahra, mahaifiyata tana cemun bintu se k'awayena da sauran dangin dake kirana Fatima seka zab'i wanda yamaka ka kirani dashi kanka tsaye" Jinjina kansa yae cikeda gamsuwa da bayanin ta, kanya ce
"Kiyi hakuri Bintu, bazan iya auren kiba hanyar barin nan gurin baseta wannan hanyar bane kawai, akwai hanyoyi da dama, zandai tallafa miki mi gudu tare mu tsira tare amma babu zancen aure kam" Rauraurau idanta sukayi
" ka taimakamun, wlhy inaso inga ummata da abbuna, ina cikin masifa watak'il ma ummana ta mutu da bak'in cikin rashin ganina, wataqin hawan jinin datake dashi hakan yayi ajalinta!!!" Jikinsa ne yae sanyi tunawar da yae da mom, dafa kanshi yae
"Zan taimakeki kije ga iyayenki inshaa Allah, amma babu zancen wannan auren".
Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins💕❤: *🏇🏇DOGUWAR HANYA....🏇🏇*
*Billy Galadanchi*
*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*
*littafina ma kud'ine me buk'atar siya ya tuntub'i wannan lambar 07084161619*
21
Zaman shiru yae yana tunanin wannan rayuwar, rannan ma yaga buzu yayi yunk'urin guduwa amma kalar dukan da aka masa seda ya raina kansa, bazasu tab'a kaba kenan se sanda kai ka tab'asu, basuda wani ilimi su akan jejin, ya kula kutanen sun iya hanyar sosai, koda kayi yunk'urin guduwa sesun taddaka, shi yana girmama yanda basa tab'a matan wurin se masu aure acikinsu, besan yanda zeyi da waccen zarah ba, shidai tana matuk'ar bashi tausayi matsayin ta na mace ace an rabota da gidansu daga zuwa bautar k'asa, yaya iyayenta zasuji? Yaya ita kanta zataji akan hakan? Shekaru uku a wannan jejin kana d'an k'walisa rayuwar abuja yaya zaka iya da bak'in ciki?.....
Daga gefensa tazo ta zauna, kan nan yayi futu futu da k'urar hazo kasancewar iskar sanyi tana kad'awa sosai, basu ba koshi kanshi ya dena jin sanyin jikinsa ya soma sabawa da sanyin
"Zuhrah" shine abinda ya fad'a yana sake mata murmushi, mayar masa da martanin tae
"Sunan dakai kuma zaka kirani dashi kenan, senaji naka yafi na kowa dad'i amma banda umma na" murmushin sa ya fad'ad'a sosai har hak'waransa suka bayyana
"Allah ko? Ya hakane bakyajin sanyi ne? Na ganki anan yanxu?" Duk'ar da kanta tae tana wasa da karan hannunta
"Idan ina ganin ka wani sassanyan sanyine yake ratsa zuciyata har qirjina da sauran gabb'an jikina gaba d'aya, bana gajiya da magana dakai badan komai ba sedan yarena dayake tattare dakai, tun bayan zuwana nan kaine mutum na uku dayakeda yare iri d'aya da nawa kuma acikin kuku ukun kai kad'aine me nagartaccen hali abin koyi, nikan rasa duk wani b'acin rai da bak'in cikin danake ciki aduk sanda naganni akusa dakai kanamun magana da harshena" Kallonta kurin ya tsaya yanayi har inda ta sauke k'arshen zancenta sannan cikin dariya kad'an yace
"Nagode" A tak'aice
"Mesane kai kullum sedai ka zauna kayi shiru anan, bafa zasu hanamu yin magana da junaba, sedai idan mun keb'e inda ba kowane" kallon ta yae
"Yanzu ba magana muke ba?" Itama kallon sa tae
"Amma senayi magana so goma bazakamun biyu ba, bansaniba ko ina damun kane, nikuwa banida abokin hira anan sekai dole sedai kake kulani mukeyin hirar" D'age girarsa d'aya yae had'e da tab'e bakin sa
"Kinsan me?" Ya tambayeta cikin rashin walwala, cikin mutuwar jiki tace
"Seka fad'a"
"Banason surutu ne ni, ya kamata ki huta da magana kema sekace ba mace ba, kin dinga zabga surutu kenan cacacaca, ni banason hayaniya" harga Allah nataso ya ansata hakaba amma seta kalli rana taga lokacin sallan magrib yayi ma, wannan ya sanya kurin ta tashi batace masa komai ba ta nufi hanyar neman ruwan alwala.
***********
Har wannan lokacin sam ko kad'an Lawuri bata dawo hayyacinta ba, ba abinda ta tuna daya shafi raguwarta ta baya, mutanen data sani kuwa daga Abu sufyan se Ayusher se kuwa me kulawa da ita yanxu Asabe da Barbo data fahimci ita kad'ai kejin yare iri d'aya da nata, bata san ma'anar rayuwarta ba amma tasan shak'uwa da sufyan, batasan komai ba sedai tabbas tasan Sufyan sun shak'u da har bataso ta waiga bata ganshi ba, dukda basajin yaren juna amma suna fahimtar juna koda da idone, tarasa mesa duk sanda ta kalli fuskar sa setakejin wani al'amari game dashi kamar dacen tayi wata rayuwar data gagara tunano ko meye.......
So takeyi ta tambayeshi menene ke damunsa amma sam batasan ya zata saka hausar ba bakuma taso tayi masa da yaransu
"Mene?" Ta furta cikin hausarta wacce bata daidaita ba, murmushin yak'e yae cikin takaici yace
"Me kika ganine Lawuri?" Bata fahimci komai ba sedai ta masa murmushi itama ta girgiza masa kanta, hirar bazata iya tsawo ba haka dai suke jefowa juna kalamai kad'an kad'an ko wanne yana fahimtar yaren d'an uwansa tunda sunajin yaren juna kad'an, ta fahimci rashin zuwan Ayusher gunta inda har take masa k'orafi hak'uri ya bata akan zatazo ne.......
A hanyar sa na barin gidan yae karo da Aysher kawar da kanta tae tamkar bata ko ganshi ba, dan yanzu so take ta koyar da kanta fitar harkar sa kwata kwata, shan gabanta yae yana murmishi
"My Ayush ni kuma? Yau ni ake d'aukewa kai har haka, ni narasa fushin na meye wlhy, inzo gunki bazaki fitoba, in kira waya bazaki d'aga ba, haba mana my Ayush, pure heart d'inki ne fa" K'wallan dataketa k'ok'arin tarewa ne ya silalo mata ta sanya wani farin qyalle dake hannunta ta d'auke shi batare data tab'a makeup nata ba, ta kalleshi sosai
"Ka tab'a zuwa nan gidan dominni ne hala? Waccen bamaguzar kake zuwa gunta kuma naji labarin yayanka agarin nemanta ya b'ata, kai kuma kasan inda take sabida tsabar sonkai irin naka ka barshi ya komawa hallaka yanzu ni meya saura dazaka gayamun? Ka cutar da jininka ma bare ni, duk sona dakai ina tsananin k'yamatar halayenka Yaa Sufyan sabida haka dan Allah nika hassaramun inaso zam sarara, zuciyata dai tawace zan rarrashi abuta" Ta qare maganar lokaci d'aya tana k'ok'arin bud'e motarta ta shige, mamakin ta sosai ya hanashi koda motsi mesashi bame tausayin halin dashi yake cikine wai? Tayaya ze dakatar da Hurairah tunda seda ya yafi tukunna ma ya sani, sumar kansa ya shafa sannan ya taka a hamkali zuwa gun motarsa tare da furzar da iska me zafin gaske daga bakinsa..
***********
Tunda wannan abun ya faru Zuhrah bata k'ara yiwa Abu Hurairah koda gaisuwa ba, kusan kwanaki 4 yanzu ko inda yake bata zama, idan yazo inda suke ma tashi takeyi, dayasan ko ita wacece dabe wulaqantata ba, dan kawai ta nemi ya taimaketa seya mata izgilanci, tundama cen ita ba mace bace me d'aukar wulak'anci akan maza, tasan darajar kanta sosai dan Allah ya qaddare da zama nan bashi ze bata damar zubar da qimar taba.
Abun kuma seya dami Hurairah, yaudai da kanshi yaje gunta amma ko kallonsa batayi ba harya zauna
"Musulunci dai ya hana gaba ko?" Batako kalle saba ya qara cewa
"Assalamu Alaikum" shareshi tae
"Amincin Allah ya tabbata agareki ya bint" waigowa tae suka kalli juna cikin takaici ta amsa
"Amin wa Alaikassalam"
"Nazone yau mui maganar mafita, yau da dare nakeso mu tsere amma ke me kika gani, naga ke kinsan hanyoyin da suke bi, naga kuma suna shan burkutu duk dare kuma ni sun dena d'aure ni yanzu" kallon sa yanzu kam tae sosai
"Idan kuma suka kama mufa? Kasan hukuncin wanda ya gudu da mace anan gun?" Kallonta yake shima ido cikin ya girgiza mata kai alamr aa, taci gaba
"Kashesa akeyi idan an kamashi, ni kuma bnso maka mutuwa yanzu ba" haka dai ya kafe akan se sun tafi dole ta amince masa, cikin dare kuwa suka had'e inda yace suka nemi sulalewa....
Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins💕❤: *🏇🏇DOGUWAR HANYA....🏇🏇*
*Billy Galadanchi*
*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*
*Book nawa na siyar wane, please karkui sharing wasu groups kuma karki karantamun idan baki biyaba,meso ya siya ya nemi wannan lambar 07084161619*
22
Tafiya me nisan gaske sukai dan kuwa basu suka sararawa tafiya ba se kusan asuba, seda sukai sallah sannan suka kalli juna, zuhrah tace
"Nagaji wlhi" cikin hasken dabe gama wadata gun ba ya furta
"Aikuma baki isaba Zuhra, yaya zakice
Kin gaji, karaya da wuri haka?" B'ata fuska tayi
"Ni gudun damukene ya ishen, bakaga ba har bayana ya soma mun ciwo" murmushin takaici yae
"Mutanen cen fa kinsan sunsan kan jejin, zama su fimun sanin shortcut daze iya had'asu damu batare da wani b'ata lokaci ba, bama wannan ba aiba su kad'ai bane mutanen wannan jejin macuta akwai dubun dubatar su miliyoyinsu ma suna nan, bamuda wani makami se adu'a idan zaki tashi muje ki tashi muje" mik'ewa tae cikin takaici da gasken ta gaji, istigfari yae Allah yaga zuciyar sa sannan ya damk'o hannunta suka soma gudu baji ba gani.
************
Abu sufyan kuwa duk wata damuwa damuke tsammanin yana cikinta tawuce hakan ma, sabida kwata kwata mom batada lafiya gashi bata kulashi akan ya bata kunya ya cutar da d'an uwansa, yauma kamar kullum durk'ushe yake agabanta yana xubar hawaye
"Mom dan Allah kiyi hak'uri ki tallafeni ki gafartamun, wlhy sharin shaid'anne" kawar da kanta tae daga dubanshi, tana fushi dashine kurun amma dukkanin laifin general ta d'audawa shi kacokam, sabida koba komai shine ya kafe akan yin tafiyar tun farko, dabe tura subin wannan doguwar hanyar ba dababu abinda ze rarraba kan yaranta har haka, seda ta share k'walla sannan tace
"Zan hak'ura amma da sharad'i" Da sauri yace
"Na amince mom, duk girman sharad'in dazaki gindayamun zan jura zan d'auka inshaa Allah namiki alqawarin komai girman sharad'in zanbi shi batare da wani tunani ba" Gyaran kwanciyar ta tae
"Ka tabbatar nanda kwana biyu yarinyar nan ka d'aurata akan wannan k'auyen na fulanin garin dakuka b'ulla bayan da kuka baro muguwar hanyar nan, akwai garada da OGA shamsu yae sun rakasu ka basu kud'i Maira dubu d'ari biyar su d'auki yarinyr nan da kuyangarta su kaisu garinsu, ka kuma manta da ita har abada wannan shine sharad'in nawa, sabida Abu Hurairah bamuda tabbacin qara sanyashi a idanmu har abada" Jikinsa har rawa yakeyi tsabar firgici yana cikin tsananin rud'u da tashin hankali, har ya mik'e ya qara durk'ushewa
"Mom Dan Allah ki duba lam......"
"Wlhy kaji na rantse ka sanya wannan yarinyar akan hanya tayi garinsu nanda gobe ma na dawo sa abun baya" Yama rasa meyake masa dad'i haka ya kasa ya tsare ta da ido cikin rud'ani bashida bakin magana haka yabar d'akin jikin sa babu k'wari ko kad'an.....
Kallonta yakeyi bayako k'iftawa harta tsargu da kallon dayake mata, cikin bak'in ciki da takaici yace
"Lawuri zan sanyakai a hanya ki koma gida badan raina yana buk'ata koson hakan ba sedan yin biyayya wa mahaifiyata nasani ba dole bane ki fahimci yarena amma ko ba yanzu ki sani kina raina har abada ina miki sonso bana wasa ba banida wani zab'in dai daya wuce in hak'ura in barki ki tafi" bata gane sosai ba amma ta fahimci maganar ya shafi shi da ita kuma maganar tafiya yake mata, kuka ta saka dan batasan mekenan yake nufi ba, ya hau aikin rarrashi, washe gari tunda safe yazo gidan kai tsaye Ayusher ya nema ba musu tazo suka gaisa yace
"Zanyi tafiyane, zanje OGUN STATE" kallon mamaki tae masa ganin sam baya walwala
"Wurin me kuma Yaa Sufyan?" Ta tambayeshi cikin kulawa
"Lawuri zan sanya a hanyar garinsu, kuma daga OGUN STATE D'in ake dauke hanya zuwa garin, ga tafiyar da nisan gaske ina barar adu'ar ki" Sadda kanta tae a qasa cikin tausayin sa
"Mesa zaka mayar da ita?" Kawar da kanshi yae daga dubanta
"Hakan shine daidai dear, so karki damu fatana kimun adu'a kinsan yanda hanyar nan take" jinjina kanta tae
"Allah ya tsare hanya ya kaika lfiya yakuma dawo dakai lafiya" godiya yae mata sannan ya shiga se mamaki Lawuri keyi ya gama tattare musu kayansu yace su fito, haka suka kama hanya bata fahimtar komai sabida batare kai, se Barbi ce me gane inda aka dosa....
**********
Tunda mutanen songai suka gano guduwa sukai se suka shiga nemansu, koda suka fahimci hanyar dasukabi bame b'ullewa bace sesuka dawo suna
Dariya sun tabbatar bazasu yau ba sesun juyo dan kuwa akwai makasansu a hanyar bila'adadin, idan ma sun samu sun dawo kenan kafin a kashesu acen ba.
Kallon tausayi ya sake mata sanda suka iso hanyar data rabu kashi uku abun mamaki acikin jejin nan
"Zuhrah menene?" Duqar da kanta tae
"Yunwa nakeji" Ta bashi amsa a tak'aice, shida kanshi daurewa yake amma yunwa yakeji
"Kiyi hak'uri Allah baze barmu haka ba, indai har munada rabon sake ci da shan wani abu agaba zakiga mun samu, babbar damuwa ta shine hanyar nan, bansan wacce mafi alheri agaremu ba, sabida haka zan d'auki duwatsu k'waya uku, zan sanya qanana biyu da babba d'aya zan yi adu'ar neman zab'in Allah sena jefa a tare, duk inda babban yatafi anan zamubi" Kallon satek cikeda gamsuwa da bayanin sa, runtse idansa yae ya soma kwarara adu'a yakai tsawon 30mns yanayi sannan ya jefa duwatsun, hanyar data kalli hannun damansu ta gabas anan dutsen babba yabi sauran kuma suka watse, kallon ta yae
"Ki shiga da Bismillah nima haka da ita zan shiga" haka suka shige sunata adu'a, yanzu bako waya bare ya saka karatun Alk'urani sedai yanata rerosa abakinsa har mamaki yake baiwa Zuhrah yanda sam baya kuskure sekace akanshi yake kaf, haka yae yae shiru sabida k'ishiruwa danma lokacin sanyi ake sosai dase sunsha azaba.
Sunyi tafiyar wuni d'aya cur har dare ya taradda su, anan suka nemi mafaka taimama sukayi suka sallaci magrib harma da isha sannan sannan suka k'arayi gaba acewar hurairah inda suka tsaya d'in shi sam be masa ba.
Ta gaji iyakar gajiya shi d'inma a wahalrce yake, haka har asuba tae musu, wayewar garin ne ya basu matuk'ar mamaki ganin su a inda basu zata ba, akwai yalwar Bishiyoyi sosai tare da manya manyan 'ya'yan itatuwa tamkar wani ne ya shhukasu a gun, wurin sekace wata fad'ama, dan komai na lambu akwai, zuciyar Abu Hurairai sam bata kwanta ba, dan haka duk irin kukan da Zuhra take masa hakan be saka ya barta taci komai agunba, haka yana ta adu'a yajata suka bar wurin tate da d'aukar hanyar gabas domin neman mab'oya.....
Ihun dasukajiyo ne da shewa acikin harshen hausa ya ankarar dasu suna kusa da mutane, dukda haka hankalin abu huraira be kwanta dasu waye ba, dan haka yae qoqarin janta zuwa saman bishiya, da k'yar ya samu ya d'are itama kuma ta d'are da k'yar suka haye suka b'uya, basufi mintuna 5 da d'arewa kan bishiyar ba sega gardawa da manya manyan makamai harda bundigogi suna zancen kisa
"Ai Baba wlhy duk wanda muka rik'a yanzu se miliyan 50, koda ubansa ze siyar da uwar sane ya fanshesa kuwa, kaini idan ma aka matsa da ciniki wlhy sena harbe mutum, mutanen nan suna zuba sha'anin su wlhy ga uwar dukiya a hannunsu amma basa baiwa kowa se iyalansu, shisa bana tausayin yaran tsaf zan kashe mutum in kashe banza" Dariya suka saka dukkansu da shewa kafin wani yace
"Yanzu wane mahaluk'in ne ze iya zuwa nan gun? Ai banaji akwai shi har abada, sabida haka mu binne kud'in anan, idan muka shaqata zuwa anjima semu juya cikin gari, danni akwai wasu danake hari, nan gun kaga ai ko ntwrk ma babu" jinjina kai d'ayan yae
"Hakane, mu binne kud'in danni idan muka samu irin wannan so ashirin tuba zanyi inje Niger inci gaba da kasuwanci" Dariya dukkansu sukayi, Gigicewa Zuhrah tae ta soma zubar da k'wallah, girgiza mata kai abu Huraira yae, tunda yake ai mutanen a qarqashin bishiyar suke, koda k'wak'warn motsi sukayi zasu jiyo su, wani daga cikin sune ya mik'e ya fuskanci bishiyar ya zaro zandariyar abarsa ya soma fitsari, da sauri ta walk'ata had'e da rufe idanta ta rungumi Abu hurairah jikinta har rawa yake tsabar tsoro, ai idan aka kawo sabon kamu a qungiyar songai tsirara ake masa amma bata tab'a ganin abu haka ba, kuma ma ba'ayi agabansu sam, ganyayen bishiyr ne sabida motsawan datayi suka soma kad'awa har wasu suka zubo dama sun bushe dayake lokacin sanyi ne, yagama fitsarin sa yazo yana zancen duk inuwar ma takusa qarewa kaf sabida sanyi, kishingida yae yace
"Wai meyasa bamuzo da mata ba? Wlhy uwatace kurun bazan hayayyaqewa ba yanzu, amma yanda nakeji na a sandaren nan kowacece sena sauke wahalata akanta nikam" Dariya suka saka d'ayan cikeda shaqiyanci ya kaiwa tsakiyar wandon sa cafka
"Nafika matsuwa Alaji, dazan samu mace yanzu niko aljanace wlhy seta gurzu a hannuna kowaye ubnta" Dayan ma dake gefe se cewa yae
"Ai wacce duk ta shigo hannu idan ita kad'aice lugude zatasha dankuwa layi zamuyi koni nan sanda goma zan mata, Allah nama matsu mu adana kud'in nan mu shiga gari mu wawashe mma ai a sammana wani abun ko?" Jin wannan zancen nasu sekijin Zuhrah ya ebi karkarwa kan kace meye wannan ta soma zubo fitsari dga kan bishiyar tsabar tsoro, abu Hurairah gaba daya yama rasa mezeyi haka sukaji sakar ruwan fitsari sunsan ba damuna ba ba komai ba suka soma magana akan ruwa na sakkowa daga kan bashiyr fa....
Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins💕❤: ***Tunda hamood yashigo ta dauke kai tamayar dashi gefe daya ganin haka yasashi shima