gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading DOGUWAR HANYA Dajin Tsafi by Billy Galadanchi Chapter 11 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hade rai yadaure fuska kamar bai taba dariya ba,

"Macuci.... Azzalumi..... Mugu to Allah ya toni asirinka....yanzu dama hamood kasan kana dauke da kwayar cutar HIV amma shine ka aureni ahaka har kake burin hada shimfida dani?"

Wani mugun kallo ya watsa mata sannan yazare farin tabaran dake sanye cikin idonsa, zama yayi kan kujera ya dora daya kan daya yana watsa mata kallon dake kara tafarfasa ranta,

"To sai me dan na aureki ina dauke da HIV? Bake kika manne min kika like min akan dole sai na aureki ba? Karfa ki manta har aurenki kika kashe dan kawai in aureki in zauna dake...."

"Ya isa haka malam.... Ai duk wadannan abhbuwan dakake ikararin cewar na aikata na aikatane acikin rashin sani... Kuma ina nadamar hakan ahalin yanzu, wallahi hamood kaci amanata kuma ka zalunceni wanda bazan taba yafe maka ba har abada.... Sannan ka gaggauta sallamata domin gidan ubana zan tafi insha Allah nagama zama dakai...."

Wata shakiyiyar dariya yasaki irin wacce ke dauke da mugunta tsantsa aciki sannan yayi mata kallon uku ahu,

"U are such an idiot mai gado, sai yanzu nasan bakida tunani sam.... Hmmmm to idan ke shashasha ce ni mai hankaline... Bazan taba sakinki ba koda kuwa za amaimaita yakin duniya akaro na uku.... And lastly abinda zan fada miki shine u should mind ur tongue kisan irin maganar da zaki rinka fada min idan bahaka ba jikinki zai rinka gaya miki....."

Yana kokarin mikewa taje tasha gabansa cikeda masifa da tashin hankali,

"Wallahi hamood koda baka sakeni ta dadin rai ba to yazama wajibi ka sakeni ta dolen dole koda kuwa agaban kotu ne domin nagama zama da macuci,mayaudari, mashayi kuma mazinaci... Ko kana tsammanin har yanzu ban san irin kazamar rayuwar da kuke yi kaida waccan karuwar ba? To Allah yagama tonar asirinku dan haka kasakeni kuma kabani kudina naira dubu dari biyar wanda abbana yabani kai kuma ka lallabani ka kwace....."

Tafa hannaye wasila tashiga yi wacce fitowarta kenan daga cikin daki,

"My dear yanzu kana tsaye kanajin abinda wannan mahaukaciyar take fada maka amma shine bazaka dauki mataki ba?"

Tun kafin wise tarufe baki hamood ya dauke bilkisu da wani gigitaccen mari wanda yayi barazanar makantar da ita, zafin marin yasa bilkisu sake daga murya tana furta,

"Allah ya isana macuci azzalumi kuma wlhi sai ka bani kudina sannan dolenka ka sakeni...."

"Banza yar gidan matsiyata ni zaki yiwa sharrin na karbar miki kudinki? Uban me uban naki yake dashi da har zan karba? Saki kuma bazan yiba ko kin zaci nima irin wannan sakaran yaronne da zan sakeki aduk lokacin da kikaso? Koda zan sake ki yazama dole inmore sadakina dan haka sai kishirya daukar kwayar cutar HIV...."

Tun kafin yakarasa bilkisu ta dadimeshi tana kuka,

"Ni ba yar matsiyata bace sai dai idan kaine dan matsiyata kuma wallahi daga yau nagama zama dakai...."

Wani marin yasake bata sannan yashiga dukanta babu ji ba gani har saida takai kasa lokacin ne yafara ball da ita yana nausa mata kafa aciki, kuka bilkisu takeyi tana ihun neman dauki ganin yana kokarin kasheta yasa wise zuwa tana kokarin hanashi amma yahaukace kwata kwata bayaji bare gani,

"Nashiga uku hamood ka kusa kasheta... Kar kayi kisan kai kaga yanda takeyi fa... Kabarta haka"

Shine abinda wise keta fada amma hamood yaki saurararta ganin haka yasata sulalewa daga gidan tagudu tun kafin hamood yakashe bilkisu azo tafiya dashi ahada harda ita.

Bilkisu kam tajima da fita daga cikin hayyacinta sakamakon na jakin da hamood ya lakada mata abu na karshe da zata iya tunawa shine taji hamood ya gwarata da kujera ta fadi akan hannunta na hagu wanda take awurin wani azababben zafi ya ziyarceta, cikin azababben ciwon kai take bude idanuwanta ahankali wadanda suka kumbura suntum sakamakon uban bugun da suka sha,

Ammah ce da meenah zaune acikin dakin wanda ko ba afada mata ba tasan asibitine domin ga alamu nan sun nuna hakan, ga ruwa nan ana kara mata a hannunta na dama sannan hannun hagun ta kuma an daddaureshi dasu bandeji alamun dori,

Wasu hawayen nadama ne suka zubo daga cikin idanuwanta, ganin ta dan motsa yasa ammah da meenah azamar tasowa dukkaninsu Wanda har bakinsu na haduwa wurin yimata sannu,

"Sannu mai gado..." Inji ammah,

Kai ta dan daga cikin azabar ciwo ta rinka binsu ammah daya bayan daya da kallo kamar yau tafara ganinsu. Bata iya cewa komai ba sai ciccije baki da takeyi sakamakon ciwon da dukkanin jikinta keyi mata musamman ma hannunta na hagu,

"Sannu adda labour.... Allah yatashi kafadunki"

Dagawa meenah kai tayi tana cije baki hawaye na kwaranya daga cikin idanuwanta ahaka su maama suka shigo itada Hindu,maama na dauke da sultan ita kuma Hindu tana goye da meenal abayanta sai hudah wadda hannunta ke rike da nata, cikin zuciyarta take wani irin kuka mai tsuma rai saboda ganinsu mama da 'yayayensu yasake fama mata raunin da take fama dashi, su gasu da yaransu agidan mazajensu cikin walwala da kwanciyar hankali amma ita tanata shiga cikin runtsin rayuwa,

"Allah ka gafarta min... Allah natuba... Astagfirullah..." Shine abinda taketa fada cikin zuciyarta, jinta take ta tsani hamood ta tsani duk wani namiji mai irin halinsa ahalin yanzu,

"Allah ya isa..." Shine abinda lebanta suka furta amma babu wanda yaji, cikin tausayawa da jimami maama da hindu suka karaso gaban gadon su dinma kamar zasuyi kuka,

"Sannu Adda.... Sannu... Sai Allah yasaka miki insha Allah" inji mamaa,

"Kuma inbanda zurfin ciki irin na Adda labour bata fa taba fadar irin zaman da sukeyi ba bare tafadi cewar yana dukanta..." Hindu tafada tana kokarin zama agefen gadon,

"Ni dama tun jimawa wallahi na fuskanci akwai matsala kugafa irin ramar da tayi har iyallo ke cewa ciki ne..." Meenah itama dake tsaye kusa da amma ta tofa nata,

"Ai Dr yace babu wani ciki yanzu... Yace bata da komai, gara ma da Allah bai bata ba domin hada zuri'a da irinsu wannan hamood din hatsarine... Allah yabata masu albarka nan gaba" maama tafada tana kokarin mayar da kwallar da take kokarin cikowa idanunta, ammah dai har akayi aka gama bata tofa tata ba suna nan zaune sunata yimata sannu har Abba yazo yadubata yatafi hakama mazajensu duk sunzo sun dubata, khulsum amarya itama daren ranar sai gata, kowa yaga bilkisu sai yaji tausayinta sakamakon kumburar da fuskarta tayi tsabar duka. Lokacin da dare yayi meenah ce tace zata kwana da ita amma ammah tace a'a kowa yatafi gidansa inyaso Rabi mai aikinta sai tazauna su kwana tare hakan kuwa akayi, ita dai bilkisu kasa baccinma tayi sakamakon suyar da zuciyarta keyi motsi kadan zata furta,

"Allah ya isa..." Acikin zuciyarta kokuma afili. Saida tayi kwana uku agadon asibiti sannan tafara tashi har ta zauna kuma an danyi sa'a kumburin fuskar tata ya dan ragu, har ranar babu wanda yayi mata maganar hamood may be suna son abar asibitinne tukunna sai asanar mata abinda yafaru, aranar tana zaune maama na kusa da ita agefen gadon tana bare mata ayaba tana ci sai ga hajiya iyallo ita da yakumbo mai gado, tunda iyallo tashiga dakin take tsinewa hamood,

"Ni dama wallahi wannan yaron ban yarda dashiba... Yaro sai kace dan dambe wani murgujeje dashi... Wallahi tsohon mijinki shine miji mai gado... Yaro mai kunya ko gaisheka yakeyi idanuwansa akasa bazai taba yarda ya hada ido dakaiba amma shi wannan idonsa atsakar ka yake sai yasaka idonsa cikin naka sannan zaiyi maka magana....Allah yasawwake,Allah ya kwashe masa albarka macuci"

Tun abun na bawa su maama haushi har yadawo yana sakasu dariya, iyallo nata faman hamuki ya mudan yashigo wanda dama shine yakawo su,yana yiwa bilkisu yajiki iyallo tahau cewa,

"Ai shikenan yanzu sai acika min burina ayi hadin nan.. Ni dama tun farko mudansiru naso abawa aka ki..."

"Dan Allah iyallo mu ki kyalemu muji da abinda muke ji..." Maama tafada tana hararar gefe,

"To fitsararriya dadinta ma dai bake naceba balle kiyimin rashin arziki... Fitsararriya kawai.."

Shi dai ya mudan ficewa yayi daga dakin da alama shima baiji dadin maganar iyallo ba ko meye dalili? Bilkisu kuwa jin iyallo ta ambaci fahad har tana yabonsa yasata dulmiya kogin tunani.....


*Wannan littafin na siyarwa ne me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*



*_Ummi Shatu_*๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins๐Ÿ’•โค: *๐Ÿ‡๐Ÿ‡DOGUWAR HANYA....๐Ÿ‡๐Ÿ‡*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*

23

"Oga munshiga uku mun kawo kanmu gidan aljanai" kanma ya rufe baki dukansu sun runtuma aguje bako waiwaye, anan suka bar bindigogin su dama jakar kud'in baki d'aya, Suna nan a lab'e kan bishiyar su kuwa har sa'o'i biyu suka shud'e kana suka sakko, Abu Huraira ya bud'e jakar yaga kud'i me tarin yawa gashi bashida wurin zubasu bayaso ya d'auki jakar dukanta amma yasan kud'in zasu masa amfani nan gaba kad'an dan a wannan hanyar besan ina zasu fad'a ba shikam, ba wata suturar kirki ajikin sa, fatane kurun a kunkurunsa ita kanta Zuhra fatar ce a kunkurinta se a k'irjinta

"So kake ka d'auki kud'inne?" Kallonta yae had'e da sauke ajiyar zuciya

"Banaso na d'auke musu kud'in duka, so nake mu d'eba kud'in koda munje inda semun hau mota da kuma abinci, hanyar dasuka biyo tanan nakeso muma mubi, sabida tunda kikaga sunbi hanyar tokuwa inshaa Allah zata b'ulle ne"
Cikin damuwa ta kalleshi sosai tana gyaran tsayuwarta

"Nasani,gasu d'auke da yare irin namu ma, amma ni ba wannan ganin mugwayen mutane sun fito daga hanyar se jikina yae sanyi, banso mu bi hanyar hankalina be kwanta da itaba kuma" Yama rasa tayaya ze rarrasheta, ganin ya tsaya yana kallonta kurun ya sanya tace tana tara ruwan hawaye a idanta

"Kaji fa me suke cewa akan mace, idan kuma muka k'ara had'uwa dasu fa?"

"Kiyi adu'a yanda kikaga Allah ya korar mana su cikin sauqi hakan ko yanzu da k'afarsu zasuyi ta kansu ko k'ara ganinmu sukayi Allah ne ze kawo mana mafita" Raurau tae da ido tamkar zatayi kuka

"Dan Allah ka kula dani kaji?" Murmushi ya d'anyi

"Karki samu damuwa zuhra" haka suka ebi kud'i suka d'aura akunkurunsu jikin fatar shikamma zagayewa yae gaba d'aya, harsun kama hanyar ya waigo, bundiga k'arama k'waya biyu ya d'auka da adda d'aya yace

"Muje" ba musu tabi bayanshi suka kama hanya..


***********
Seda ya iso wannan k'auyen sannan suka tsallak ruwa zuwa k'auye na farko, suka k'ara wuce na biyu seda suka isa na ukun sannan seya isar da umarnin mom haka ya samu samari se shewa suke su kusan 10.sukace zasu rakasu har gida acikin kwana 6, da wannan ya kwana agarin seyaji meya faru tukunna.

************
Sunyi tafiyar data basu mamaki, kusan kwanaki 2 amma basu ga alamar wani garin ba kusa ko nesa dasu, hankulansu atashe yake ga ynuwa da uwar qishiruwa suna ji kamar me, zuwa yanzu Zuhrah tasoma kasawa sabida acen akwai abinci koba komai ana cin nama da sauran abubuwa

"Kace Al-hassan sunan ko?" Kallonta yar cikeda tausayi shi kanshi ya gaji sosai

"Ea sunana kenan" jinjina kanta tae

"Wlh na gaji Al-hassan, a mugun gajiye nake kuma yunwa nakeji ga uwar qishin ruwa danake ji" Dafe goshinsa yae

"Kiyi hakuri zuhra, inshaa Allah zakiga mun qarisa wani garin" batace komai ba suka ci gaba da tafiyar cikin gajiya, wani k'auye suka ci karo dashi mara hayaniya kuma kaman bashida yawa ma k'auyen, ganin da mutane sukai musu kurun se suka fara gudu yara da manya suna magana da harshen fulatanci akan ga yaran songai nan, sarai Zuhrah taji me suke cewa, da wannan tayi k'arfin halin soma tunka rarsu amma kowa se gudunta yakeyi......

**********
Bayan kwanaki hud'u ma sega wannan mutanen akan sunkai su Lawuri har gida sedai basu isa cikin garin ba suka juyo amma tabbas har hayewar garin sunyi dan har suna hango mutan smgarin suna sha'anin su da wannan dai suka dawo abunsu, godiya yae ya saka da abinda ya alqawarta ya juyo zuciyarsa babu dad'i ko kad'an.

Kafin kace meye wannan har an zagaye su kaf, ana zuba musu ihu akai da ababen makamai a hannu, da k'yar Zuhrah ta samu wani ya saurareta tamai bayani sosai akai abinda ya fito dasu daga wancen rundunar ta songai harta fulatancin dasuke ya sanya aka yarda da ita tayi bayani akan Hurairah sam baya jin fulatanci sabida shid'in mutumin k'abilar hausa zalla ne, ita kua mahaifiyrta en mutan fulanice kuma bata musu magana ta hausa, gun sarki aka kaisu ta qara koromai bayani, yace shisam be yarda dasu ba se idan zasu amince a d'aura musu auren dasukace shiya fito dasu, nan tamai bayanin cewa dama kosun d'aura babu auren nasu tunda maguzawa ne basusan Allah ba, su kuwa musulmai ne kuma basusan juna ba se agun, cikin harshen fulatanci ya furta

"Kinga yarinya dole fa semun d'aura muku auren nan zamu yarda daku, idan kuma ku masu lek'en asiri ne fa? Indai har hakane menene zesa ku gudu kuku biyu mace da namiji ba muharamman juna ba, so ake amana wayau, aini inada ilimi na, shekara nawa jama'ar songai suke hallaka mana en uwanmu da dukiyoyin mu? Basuda mafaka d'aya sedai su cutar damu su gudu, ko yanzu wlhy kasheku zamuyi annuyarku ta biyu" murya na rawa tace

"Kayi hakuri ka yarda damu sarki me adalci, yaya za'a samu fulani a jama'ar songai? Wlhy kamamu sukayi suka riqemu bamusan manufarsu tayin hakan ba" Kallon shek'ek'e ya mata

"Yarinya kasheku fa zanyi" Durk'ushewa tae agun

"Na yarda ka d'aura mana aure, na yarda zamu zauna harna tsawon lokacin daka ambata tare daku lokacin daya maka a matsayin miji da mata,idan har kaga wani abu a tattare damu na rashin gaskia ka kashe mu, amma yanzu kamun rai ka bamu wannan damar" seda yae magana da en fadawansa sannan yace zasu d'aura aurensu zakuma su basu wurin zama su zauna dasu na watanni biyu, idan songai da jama'ar sa suka kawo musu wata ziyarar to suma sesun kashe su har lahira, a garin su kuma baliga girmanta da baligi seda aure bazasu lamunta ya lalata musu yara mata ba, dan Haka dole sesun d'aura musu auren koyayane" Shiru tae tana kallon Al-hassan dankuwa tasani besan me ake cewa ba sam

"Ranka ya dad'e sadaki nafa" kallon kunkurunsu yae yace

"Kamar ba'a nigeria muke ba? Ai ga kud'inan a hannun ku?" Kallon Al-hassan take

"Muma ba damu bane ba kud'in" tsaki yaja

"Kuyita rik'ewa nine zan biya sadakin amma ko bakwaso yanzu zan had'a shaidu a d'aura muku aure" haka ta zauna ta baiwa Alhassan labari duk hankalinsa ya tashi babu yanda ya iya dole ya amince, sunaji suna gani tsohon nan ya biya sadakin su suka kuma d'aura musu aure!!!!.

Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins๐Ÿ’•โค: *๐Ÿ‡๐Ÿ‡DOGUWAR HANYA....๐Ÿ‡๐Ÿ‡*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*

******

"A tunninki zaki iya ne? Kina ganin hakan daidaine ya dace kenan wannan auren?" Kallon sa take cikin wani yanayi me matuk'ar wuyar fassara

"Kayi Hakuri kaji, bamuda zab'in daya wuce hakan, kuma ai dakai nayi maganar seda muka yanke shawarar atare idan ba dan ka bada bakin yin hakan ba babu kalar k'aud'in daze kaini in fad'a hakan kona zartar da hukunci kaina tsaye" Shiru yae

"Lawuri itace ta janyomun akanta na shiga wannan halin danake ciki, nazo neman wata dan in musuluntar da ita itada ahalinta amma na fahimci Allah be turo anan dansu ba, Allah ya turo ni anan ne danke dakuma wata k'addarar rayuwata, ban tab'a tunani akwai ranar da za'a d'aura aurena batare da iyayen da uwana ba, bansan me Allah yake nufi da hakan ba Amma ina matuk'ar godiya agaresa duk yanda yae dani, nasan hakk'in aure nasan hakk'ok'in ki dake kaina zan zamto me cikasa hakk'ok'in ki akaina gaba d'ayansu se wanda yafi k'arfina" Shiru dukkansu sukai koda ya duba Zuhrah kuka takeyi cikin murya mara sauti, besan meya sakata kuka ba, sedai tabbas ta bashi mugun tausayi,har yake gani ko kalaman same sukai mata zafi

"Babu abinda nake nufi da kalamaina se Alkhairi zuhrah, banyi magana ko d'aya danna ci miki zafari ba, kiyi hakuri nasani kema bakiwa kanki wannan burin ba, nasani kema had'uwata dake agareki k'addarece ta rayuwarki kiyi hak'uri kinji" Bata ce masa komai illa tashi datayi tabar masa d'akin da aka ware akace nanne mallakin su zuwa watan nin dazasuyi subar garin idan har ba'a kawo musu wani harin ba.......

Shiru yae yarinyar tana bashi matuk'ar tausayi, duk da bawai ya santa bane ba acen baya amma tabbas tana bashi matuk'ar tausayi, danya kula tasan hutu bata mik'e acikin wahala ba ko kad'an, yana tunanin rayuwa dakuma halin da Lawuri take ciki, shin kota koma gida? Kokuma itama wata k'addarar ta tsayar masa da ita akan hanya, yanzu kam ya gano kuskurensa na k'ara dawowa wannan hanyar mara b'ulllewa, be nemi zab'in Allah ba ya bazamo neman ta kaman dole shisa Allah ya jarabcesa da wannan matar.

***********
*Bayan sati hud'u*

Kallo d'aya zaka yiwa Abu Sufyan ka gano samsamsam baya cikin hayyacinsa, rashin Abu Hurairah yafi damunsa fiye da rashin Lawuri ayanzu, duk wani tashin hankali yana zaune daram a zuciyarsa da kansa, yana gani idan har yau akace d'an uwansa ya mutu ta wannan hanyar meze gayawa Allah? Son zuciya kome? Yanzu da wanne zeji ne wai?, haka yake wuni a damuwa mussaman idan yaga yanda Mom duk tayi wani iri ba ita ba ba dad ba yanzu rigima ta k'are banda adu'a babu abinda sukeyi yanzu, yakanfi shiga damuwa fiye da kullum

"Amma yanzu baka tunanin cewar mom hankalinta ze k'ara tashi idan taga cewar ka sh8ga wannan yanayin kaima? Duba fa kaga yanda ka dawo Yaa Suf, duk kayi wani fayau dakai ba kyaun gani, da wanne kenan zataji?" Kallon ta yae

"Cya yazan samu nutsuwa bayan atadalilin son zuciyata Twin ya b'ata, bamuda tabbacin yana raye ma koya mutu, irin wannan tashin hankalin yaa ze barni in rayu cikin walwala da farin ciki? Ki dubafa ki gani su dad sun hana inbi bayansa, acewar su bazasu salwantar da rayuka da dama irin haka ba, ina cikin tsananin damuwa CYa" tausayin sa sosai taji ya kamata

"Bakada laifi Yaa suf, sharrin shaid'an ne dakuma yanda Allah ya k'adarto zata faru, so just pray for him inshaa Allah ze bayyana" bece komai ba sam shi bashida nutsuwar hankalin sa ko kad'an.

**************
Tunda ta soma rawar d'arin yake kallonta cikeda tausayawa, besan meze mataba yanzu kam, an bata magungunansu na gargajiya amma jikin ko alama beyi nufin sauka ba, dukda a rufe take ruf da zani irin na fulani hakan be sanya ta dena rawar sanyin na, matsawa yae akusa da ita cikin tsananin damuwa ya yane bargon yakai hannunsa akan goshin ta yaji zafi rau, d'ago idanta tae cikin hasken na fitilar k'wai dake d'akin idan ya kad'a yae jajir ta kallesa

"Kaina yanamun ciwo sosai, kozaka kamamun dan Allah?" Gyaran zamansa yae ya kama mata kan nata had'e da mata wasu adu'oin

"Sannu zuhrah kinji, inshaa Allah ze dena, ni zanje na kwanta a zaure ki kula da kanki kinji" rik'o hannun sa tayi

"Al-hassan aurene irin na musulunci a tsakanina dakai, ban tab'a tilastaka zama dani ko kwanciya d'aki d'aya dani ba, amma na rok'eka da Allah da manzansa ka kwana atare dani, ka kula dani koda kulawar taka zata tsaya iya yau ne, amma yau kad'ai kamun wannan alfarmar kaji" Tausayinta sosai yaji ya dawo ya zauna kusa da ita sosai, hannunta ya kamo ya shiga murza mata da nashi cikin tausayi yaga alamar sanyin sosai take jinsa, idan ya sake wanan hannun ya kama wancen

"Kina samun sauk'in sanyin a haka ne Zuhrah" gyad'a masa kanta tae alamar e, shiru yae yana tunanin wani korean film daya kalla, sanda suke wani kogo namijin bashida lafiya yanata rawar sanyi ya samu high fever macen ta had'e jikinsa da nata seda ya samu sassauci a haka ma dukkansu sukai bacci, matsawa yae kusa da inda take kwance, kayan fulanine dama ajikin sa ya cire rigar cikin rintse ya soma k'ok'arin zare rigar jikinta, hannu takai ta rik'e tace

"Karka ciremun sanyi nakeji har cikin b'argona" tausayinta ya k'ara kamashi yace cikin murya me rauni

"Nasani zan taimakeki ne kawai" sakewa tae batare datace komai ba sabida yanda takeji, shiga jikinta sosai yae ya qara rufe su ruf sannan ya soma murza mata tafukan hannayensa kota ina ajikinta, duk yanda yaso ya daurewa abinda yakeji game da ita seda ya rik'a sauke numfarfashi a hankali, tunda yake be tab'a tsintar kansa a yanayi irin wannan ba, haka Zuhrah ma dukda tana cikin yanayi irin na ciwo, hakan be hanata samun wani yanayi na musamman ba awannan lokacin, a hankali dukkansu suke sauke numfashi a hankali hannunsa yakai ya shafi sumar kanta dayake a barbaje saman matashin kan,cikin wani irin yanayi da wata murya dabata tab'a ji yayi magana da itaba

"Zuhrah how are you feeling now?" Bud'e baki tae tayi magana amma seta sark'e bazata iyaba sam batasan meyake damunta, k'ara shafar sumar yae

"Ehm zuhrah nace ya kikeji yanzu?" Da k'yr ta iya furta

"Nasoma rage jin sanyin" murmushin dabesan dalilin saba ya sub'uce masa yace

"In janye kenan kokuma in kwanta ahakan kinajin sauk'in idan ina kusa dake?" Lumshe idanta tae kurin bazata iya cewa komai ba, da wannan shima yae shiru yaci gaba da bata d'umun jikinsa har bacci yae awon gaba da ita, saukar numfsahin ta dayaji ya sauya ne ya tabbatar masa da cewar lallai ta samu bacci se gumi take had'awa alamar tana samun sauk'i, be hana mata samun sauk'i ba ya kwanta duk inda ta juya yana rungume da ita har seda bacci ya sace sa shima.

************

Washe gari koda ta farka tasha mamakin ganinta manne ajikinsa, ya sanya taji wata irin muguwar kunya ba kad'anba, tana k'ok'arin zare jikinta daga nasa ya farka, da sauri ta sauk'e k'wayar idanta k'asa, shine ya zame batare dayace komai ba yae waje, ita d'inma hanyar waje ta nufa domin yin alwala tae salla....

Duk yanda yaso ta kalleshi yae gudun sa takeyi, wasan b'uyane yake shiga tsakanin su tun wayewar garin yau, yanda aka bata breakfast haka ta kawo masa, sunkuyawa tae madarar shanu ce sabuwa dal ta ajiye masa agabansa amma kanta yana a k'asa, hannunsa yakai ya tab'a wuyanta yaji da zafi amma ba sosai ba

"Sannu Zuhrah ya jikinki?" k'ara sauke kanta tae a k'asa cikin jin tsananin kunya tace tana kallon k'asa

"Nasamu sauk'i Alhamdulillah" jinjina kanshi yae

"Madarar fa kinsha?" Girgiza kanta tae alamar aa

"Zokisha wannan kona baki a baki ne?" Mik'ewa tae ta ruga da gudu cikeda tsananin kunya mara misaltuwa, sosai takejin kunyar sa gaba d'aya setaga ya sauya mata gaba d'aya.

******
Lawuri tunda suka isa hanyar dazata sadasu da gida dama Barbo ce 'yar jagora setaji komai ya kunce mata, gaba d'aya bata gane komai ba, abu d'aya ta sani tasan wannan wurin, tasan wannan sansanin ta san yanayin mutanen dake gilmawa a wannan wurin......

Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins๐Ÿ’•โค: *๐Ÿ‡๐Ÿ‡DOGUWAR HANYA....๐Ÿ‡๐Ÿ‡*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*

25

Duk yanda taso ta yakice tunanin Sufyan aranta abun ya faskara, tayi iyakar yinta amma duk sanda ta tunano yanayin dataga sufyan aciki se taji wani uban tashin hankali ya ziyar ceta mata misaltuwa, mik'ewa tae tamkar an tsikareta ta nufi cikin gidansu a gurguje ta shirya cikin bak'ar doguwar riga mara nauyi ta material, tare da yane kanta da mayafi blue kasan cewar zanen blue ne ajikin jallabiyar, tayi kyau dukda ba komai ta sanya a fuskar ba, sabida dama Ayusher kyakyawa ce ajin farko ma kuwa....

Kallon ta yake har sanda ta zauna akujerar da dama aka tanada domin bak'in a offishin nasa

"Pure heart!" Ta ambaci sunan sa cikin murya me raunin ganin halin daya sanya kansa aciki, wutsiyar hannunsa ta kalla yanda agogon hannunsa ya masa yawa ba kamar daba sanda yake cifcif, idanshi yayi wani zuru dama gashi da manya manyan ball eye's masu zurfi a zagayen su, lips nashi dasuke da d'an kauri ramar da yae ta sanya sun k'ara fitowa sosai, ya k'ara fari akan nada amma sumar kansa sekace wani sabon kamun hauka, jikinta ne ya k'ara sanyi jin bece mata komai ba

"Yaa suf haka ka k'ara dawowa, anya kanawa knka adalci kuwa? Tun last week dana ganka bana bacci hankalina da tunanina duk yana zaune ne rad'am akanka, na shiga tashin hankali mra misaltuwa mekenan kake shirin aikatawa kanka haka?" Kwantar da

Please Login or Register in order to submit comment