You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
kansa yae saman desk nashi
"Ayusher ina cikin tashin hankali, nayi rashin d'an uwana mafi soyuwa agareni duk a dalilin son zuciya irin tawa, kullum senayi mafarkin sa amma bayako kallo na, baya kulawa dani be damu daniba har acikin mafarkina baya ko dubana, ban saniba ko yana raye koya mutu, banida tabbacin k'ara sanyashi a idona meze cewa Allah? Mezan gayawa Allah mezance dasu mom, babu abinda nafi tsana arayuwata fiyeda tunanin Lawuri, na tsaneta, na tsani had'uwa ta da ita, tsani tunanin danake akanta na wani so, na tsani hanyar data sadani da k'addarar rayuwa mafi muni" Tausayin sa taji ta masifar kamata fiyeda tunanin me karatu, share hawayenta tae cikin bak'in ciki
"Kayi hak'uri Yaa sufyan, bakada laifi ko kad'an akan hakan, kayi ta adu'a ka fauwalawa Allah lamuranka, inshaa Allah yaa Hurairah ze bayyana" shiru dukkansu kowa da kukan dayake bame tunanin baiwa wani hak'uri ma se zallar damuwa kawai.
**********
Tunda yamma ta gabato jikin na Zuhrah ya k'ara rikicewa gaba d'aya, sallan isha kurun akayi ta nemi wuri ta kwanta, abubuwan da Hurairah yaji ya sanya ya gagara komawa d'akin yau, yanaso yasan halin datake ciki amma besan zuwa yaga abinda yafi k'arfin sa, seda dare ya tsala sannan yaga baze iya sharewa ba, mik'ewa yae tsam daga kwancen dayake a zaure ya nemi shiga d'akin yaji yanda jikin nata yake.
Kamn yanda ya tsammana bakan ce, gata dai anrufe ruf amma htta abun rufar nata rawa yakeyi "Subhanallh" itace kalmar daya furta cikin bak'in ciki da tashin hankalk, da sauri yae gunta ya rungumeta gaba d'aya, jikinta yayi zafi sosai yau kamma batasan inda kanta yake ba
"Jikinne haka zuhra, shine baki gayamun ba da wuri asan abinyi" Bata kulashiba dan batamasan me takeyi ba, haka ta kwanta ajikinsa jikinta se karkarwa takeyi ba k'auk'autawa, ba shiri ya zare suturar sa ya zare tata itama, yau a rikice yasoma bata dukkanin taimakon daya dace da ita, tun yana iya hak'uri harya soma shiga gararin sh'awa, ita kanta mara lafiyan wani dad'i takeji na musamman mara misaltuwa ma, haka yafice a hayyacin sa tun yana iya sanin meyake harya b'acewa tunanin sa, hannunsa dumu dumu asaman dukiyar fulaninta yana dirzarsu kamar ze cizgasu sabida sha'awa, haka yadinga zagayar jikinta yana shinshina yana manna mata sunba awuya dama ko ina, haka dai suka dauwama a farantawa juna cikeda shauk'in sha'awa ta fitar hankali, bakinta ya laluba ya sanya a nashi ya shiga tsotsar shi dama harshen ta tamkar wanda akawa wahayi da aikata hakan, bata hanashi yin yanda yasoba, hakan baya rasa nasaba da yanda yaci galaba akanta tun rungumar farko, bata tab'a sanin tsananin sha'awa ba se akan Hurairah, seda yae yanda yaso da bakin sannan ya shiga baza harshensa inda yakega ze rage masa zafi, tun daga wuyan ta har dukiyar fulanin ta, ajere ajere suke sauke numfarfashi a tare bako k'iftawa, sannan dukkansu nishin dad'i wannan yanayin ya kasa dannuwa a sautin muryoyin su, da haka har Hurairah ya saukewa kanshi wahala ta hanyar tarawa da Zuhrah cikin hanya mafi sauk'i mafi kuma wahala, sabida tasha wuyar sa, abinka ga sabon shiga ya zagayeta a wannan daren yakai so uku, beko dubawa zamtowarta sabuwa ba a harkar dukda yake shi d'inma sabone dal, muryanta harya dasashe ahaka suka k'arayin bacci dukda ita ko gezau batai ba har asubahi tana kukan data rasa dalilin ta nayin sa, na asubar ma kasa tashi tayi duk jikinta yana mata ciwo fiyeda tunani, ga bayan gidan d'ayane kowa yake sharing dama d'akine aka ware musu acikin gida d'aya da sarkin rugar, da k'yar ya lallab'ata tae wanka tazo tayi salla, dukya gama sabuatata ko tafiyarta ka kalla seka gano batajin dad'in jikinta sam.
Abu hurairah yayi matuk'ar bak'in cikin abinda ya auku tsakanin sa da xuhra, dukda yasani matarsa ce amma beso auren nasu yaje ko inaba, yasone ya sauwaqe mata igiyoyin auren sa dazaran sunbar nan, yanzu babu wanda yasan tayi aure ya soma sakin yarinya azo kuma amata aure miji yaga fanko, shikuma harga Allah be tab'a ze iya aikata mata hakan ba ko a mafarki.
*********
*Bayan sati uku*
Zaune suke dukkansu durk'ushe aganan sarkin rugar ard'o kamar yanda sukaji 'yan rugar suna kiran garin dashi, bayan yagama jawabi yace ya aminta dasu su shirya jibi su kama hanyar dazata sadasu da garin se sanya dai a rakasu su hau motar jalingo, dan nanne babu nisa ko kad'an da k'auyen nan, sunsha mamakin jin wannan zagayen dan itama dama OGUN aka turata wani k'auye a wara makarantar gwnati yin bautar k'asa....godiya sosai sukayi yace,kud'ad'ensu suna nan ze basu su tafi dashi nanma godiya sosai sukayi kafin su koma bukkar su.
Dukkaninsu shiru sukai suna tunanin duniya kowa da abinda yake sak'awa, daga ranar da wannan abin yashiga tsakaninsu Hurairah be k'ara kwanciya a d'akin ba, ita kuwa tsabar kunyar sa ya sanya ko magana ma bata iya masa se dole......
"Zuhrah nasani kina kallona akan na aikata ba daidai ba amma ina me baki hak'uri akan hakan, banyi da niyyan cutarwa agareki ba haka Allah ya tsara mana, idan mun samu fita lafiya zanyi k'ok'ari in kaiki gidan iyayen ki kinji" batace masa komai ba harya k'araci zancen sa dai......
********
*Bayan kwana hud'u*
A jalingo ma a hotel suka kwana kasancewar sunyi shigar dare bayan ya siya musu suturu irin nasu sunci abinci irin nasu, zaman d'akin hotel d'in ma shiru shiru kake jinsu kowa tsit, har sukai bacci, itace akan gadon shikuwa a saman kujera, sallan asuba sukai sabida yanayin sauyin wurin kwanciya suka k'ara kwantawa koda suka farka ma azahar, sunsha mamakin baccin dasukayi koda yake hakan baya rasa nasaba da yanayin gajiya da sauyin masauki bayan wani dogon lokaci, sanda sukaje tasha ma babu motr abuja a wannan lokacin sabida rana tayi, haka suka koma kwana se washe gari suka tashi.
K'arfe 3:pm a abuja ta musu suka samu kansu cikin yanayin jin dad'i mara misaltuwa, haka suka kwashi jiki zuwa gidan su Zuhra duk garin ya gama sauya mata kwata kwata, da wannan suka samu kansu da tarba cikin murna da tsananin mamaki ga ahalain zuhrah, mahaifiyarta ta samu nutsuwa yanzu kam jin komai suke tamkar a amafarki bayan dogon lokaci harsun cire rai da samun 'yarsu, Hurairah ya samu tarba me kyau inda ya tafi akan labarin me tsayi ne saji komai daga bakin zuhra kafin ya dawo tukunna.
A babban parlor su zuhra dukkansu sunyi tsaye sabo turken wawa zuhra idan nan yayi narai narai yana shirin kawo ruwa, matsawa yae ya rik'e mata hannunta d'aya
"Karki sanya damuwa a ranki, da kaina zan musu bayanin komai kedai ki nutsu ki kwatar da hankalin ki, zanje gobe zam dawo tunda gari d'ayane" batace komai ba dai sabida yace bayason surutu, sake hannunta yae
"Nizan tafi sena dawo tukunna kinji" da k'yar ta iya furta
"To Allah ya tsare hanya Al-hassan seka dawo goben" harya juya tace
"Al-hassan?" Waigowa yae yana saurarenta, so take ta gaya masa cewar kusan lokacin al'adarta ya wuce da sati biyu amma batasan ina zata soma ba, murmushi tayi na yake
"Ka gaishe da mutan gidan" shine abinda tace, murmushi shima yae ya juya yana matuk'ar jin tausayin ta, ita dashi har abada, bazata k'ara ganin saba, idan ya nutsu ze dawo acikin sirri ya baiwa me gadin gidan takardar ta sabida ta samu freedom.
Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins💕❤: *🏇🏇DOGUWAR HANYA....🏇🏇*
*Billy Galadanchi*
*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*
26
Ihu sosai kakeji yana tashi daga wajenngate d'in gidan da sowar sojojin dake k'ofar gate d'in gidan, sunata wak'ensu irin na soja idan abu ya musu dad'i ganin Huraira, kallo d'aya suka ganeshi dukda ya rame sosai sabida sunsan yau Sufyan yana ciki kuma shi kamar ma bashida lafiya, General dake daga ciki da hanzari ya sakko k'asa cikin mamakin wane abu ne yawa sojin dad'i har haka suke zuba wannan uban ihun kamar ba gobe, Wanda ya ganine ya sanyashi yin mutuwar tsaye cikeda mamaki, daga wurin Abu Huraira kuwa da gudun fanfalak'i ya ruga zuwa jikin dad yana k'ugin murna da ihu sosai, rungumeshi dad yae duk yanda yaso ya hak'ura seda ya zubar da k'walla irin na d'a da mahaifi, yana sake Hurairah kuwa anan ya zuba yanawa Allah sujjadar godiya da amsa masa adu'ar sa da yae cikeda farin ciki, Cya da Hanifer da mom ma da gudun su suka sakko, suna ganin huraira dukkansu suka rungume shi, lallai wannan shine ikon me duka, se kukan murna ke tashi, Sufyan dake kwance a parlor na side d'insu jin sowar tayi yawa ya sanyashi sakkowa cikin kasala.... A parlor yae karo dasu cirko cirko sukai suna kallon juna ya gagara k'arasa sakkowa daga kan benen ma, a hankali Huraira ya taka gunsa cikin mamaki, hannayensa duka biyu ya d'aura akan kafad'un sufyan
"Al-hussain lafiyan ka kuwa meya sameka haka ka ganka kuwa?" Rungumeshi sufyan yae gaba d'aya
"Wlhy ba mafarki nake ba kaine Al-hassan, na zata mafarki nake ashe zan ganka a rayuwa Bro ashe kana raye?" Ya saka wani gunsheqen kuka me ban tausayi.... Hurairaha ma kuke yakeyi
"Twin duk ka sauya, meya seka haka ne wai? Hankalinanya tashi daganin ka haka" Takaici ya tasowa sufyan na ganin yanda d'an uwansa ya damu dashi f8ye da yanda ya damu da kansa, be bashi nsaba se janyoshi da yae suka zauna sosai acikin parlor.....
***********
*Bayan sati uku*
Zaune take tana nazarin halin data tsinci kanta aciki, dukta gama gayawa mahaifanta yanda akayi dakuma meya sameta amma ta gagara sanar dasu zancen auren datayi a ruga, acewarta se Abu Huraira yazo aganansa sesu gayan musu, amma ga mamakinta yau kimanin satuka uku kenan ba Abu hurairai babu labarin sa, ga al'adarta har yau shiru babu labarin ta, ko ba'a fad'aba ta sani ciki ne da ita, sallamar me aikin sune ya k'atse mata tunanin ta ta d'ago ta kalleta
"Anty wai Daddy yace kije parlor ga Faruk yazo" k'irjinta ne yae mugun dokawa ta kalli Hafsat din
"Faruk wanne kenan?" Murmushi yarinyar tayi
"Anty ban dad'e nan gidan ba amma ina yawan ganin sa, duk juma'a yakan zo gaskia" hankalinta ya tashi sosai ta mik'e taje ta sanya hijab ta wuce parlor d'in.....kallon juna sukeyi basako k'iftawa kowa gani yake tamkar mafarki yake dayaga d'an uwansa, runtse idanta tae kafin ta k'araso cikin parlor d'in
"Yaa Faruk Barka da zuwa" shine abinda ta furta masa cikin sanyin jiki yana murmushi sosai yace
"Rose kece kuwa? Kenake gani agabana yanzu? Ina sokoto sanda labarin dawowar ki ya sameni, bansan sanda na ganni a Abj ba, nayi matuk'ar farin cikin ganinki, har kukan rashin ki nake Rose" Zama tae shima ya zauna ya janyo hannunta
"Rose kinyi bak'i, kin sauya kin fige kin zama wata kala bani labarin meya faru dake?" Murmushi tae
"Labarin da tsayi sosai yaa Faruk, amma dai rayuwar jeji ce bako d'aki se bukka, bako suturu se ganyaye da fata, ba komai najin dad'i basu masan annabi ya faku ba" Jinjina kanshi yae
"An gayamun komai Rose karki damu, sannu, nayi alqawarin dama zan jiraki bazan tab'a aureba se sanda Allah ya bayyanar mana dake nayi kewarki, nayi rashinki Rose nagidewa Allah daya amsamun adu'a na akan ki dawo mana" Murmushi tayi cikin fad'uwar gaba
"Nagode sosai da karamci yaa Faruk Allah yabar k'auna" Murmushi yae
"Rayuwar jejin ce ta sanya kika manta da sunan dakike kirana dashi" Cikin hikima ta zare hannunta daga nasa koba komai ita matar aure ce
"Na isa in mata dan Mon cherie na?" Ta fad'a tana murmushi" yanzu nashigo grin kuma gobe zan koma aiki nake dashi sosai a office wlhy, amma inshaa Allah zanyi qoqari in dawo friday kinji" godiya sosai ta masa sannan suka rabu.
**********
Lawuri babu wanda takeson gani sama da sufyan a wannan lokacin, takasa gane me take a nan, tanaso ta kalli TV ma taci shinkafa da spag ba kullum.naman jeji ba, kullum setawa iyayenta kuka sedai su rarrasheta akan tayi hak'uri, haka dukta lalace Barbo dai tana nan tana aikinta na bauta, memory ya gagareta tunano komai sedai zare ido da take, saurayinta kuwa anan nan ana shirin d'aura aurenta dashi.
*********
*Bayan sati hud'u"
*menene yake damunki kike b'oyemun Zuhrah? Sekin sanar dani dalilin ki nayi ramar, na amaye amayen nan dana yawan bacci, alamomi sun nunar mun cewar ciki ne dake, abinda kika mana kin kyauta kenan Zuhra? Cikin shege kika dawo mana dashi?" Sadda kanta tae k'asa cikin hawaye
"Ummana kiyi hak'uri wlhy ba haka bane ba" Wanka mata mari tae
"Ba haka bane ba ubanki ne? Bari Daddynki yazo wlhy asibiti zan kaiki" ta rasa ta cewa, yaya zatace aure tayi a ruga? Yaua zatace hakan bayan zuwa yanzu ta cire ran zata k'ara sanya Huraira a rayuwarta, ga yaa Faruk zancen aure yake shida iyayen sa, ina zatabi taga haske
."baki kyautawa kanki ba zuhrah, kin cucemu wlhy kuma kema kin cuci kanki" Kukan tane ya tsananta ta tashi da gudu zuwa d'akin ta.
**********
Yanzu kusan watanni biyu kenan, duk sanda ya d'aga takarda da biro ya rubutawa zuhra saki seyaji baze iya ba, tayaya ze mata haka batare da shawararta ba? Dole yaje ya gaya mata niyyan sa, to amma idan ta nemi alfarmar ya bar mata igiyar aurenta fa yacewa su dad mene? Ya rasa ta ina ze b'ullo, wannan doguwar hanyar har yanzu yana cikinta tsundum, ina ze kallesu yace yayi aure? Shi dama ace be keta mata haddin taba da abin yazo masa da sauk'i amma tausayinta yakeji, Anya Allah ze barshi da wannan nauyin kuwa? Hakk'in aure ko d'aya baya sauke mata, yanzu katsam se ya aika mata da saki? Yarasa tudun dafawa yarasa dawa zeyi shawara ga zancen hanifer ana masa, ga Lawuri zaune rad'am akan sa ina ze tsoma rayuwar sa shikam?.
*******
Tunda akazo asibiti aka tabbatar cikin ne na watanni biyu da kusan sati uku hankalin iyayen na zuhra ya tashi, duka kam ta shashi agun umma
"Banza dabatasan darajar kanta ba, kinje kin zubar da k'imarki, baki tashi dawo mana gidan ba seda tsarabar shege, me kika nema kika rasa? Wane gatan bama baki? Nasoma tunanin k'arya kike babu wasu mutanen dasuka saceki, damacem yawon duniyar kika zab'a, yanzu me zamu cewa Faruk da iyayensa? Me zamucewa duniya? Kin gama wulak'antamu zuhrah, ban tab'a tsammanin cewar ke d'innan zaki aikata mana abinda kika aikata mana ba, kin sanyamu a rugun tsimi wlhy bakiyi 'yaba zuhra, acewai ke da cikin shege" kuka ta sakawa uwar
"Mom ba haka ya dace kimun ba, kiji tausayi na wlhy ban tab'a aikata zina ba, ba cikin shege bane ba" wanka mata mari tayi
"Baki tab'a aikata zinaba a ruwa kikasha dan ubanki? Ba cikin shege bane cikin uban meye? Idan baki dena magana ba sena hallakar dake wlhy anan, shak'eki zanyi kuma ki sani keda kika lalata rayuwar ki ke zata kwab'ewa ki jira hukuncin daddy wlhy sekin gane shayi ruwane banza mara hankali" duk yanda taso sun gagara saurararta dad ya kalleta cikin qunan rai yace
"Zuhra bari kiji, wlhy bazaki haifen shege agidana ba, kije cen wurin ubansa ki haifa masa shi idan kika haifeshi kika damqawa uban ki nemi wasu iyayen bamu ba, ashe dawowarki ba alkhairi bace agaremu? Ashe ke d'in nan tauraruwace me witsiya ina yabonki salla ki kasa alwala zarah? Lallai kibar gidan nan yau base gobe ba"
Kallon sa tsae
"Daddy wlhy bam tab'a aikata zinaba, ba shege bane ka saurareni kaji" dukanta ya shigayi ba shege bane inaga ubanki ne ko?, zaki tashi ki tattara kayanki ko kuwa?" Haka ta mik'e tanata sharar k'walla, taje ta gama had'a kan kayanta da dama ta bari batasan me duniyar yanzu ta k'unsa ba, hatta wayar da aka bata tana dai dannawa ne, ta d'auki zinarinta da kud'in b'arayin nan da Huraira ya bata ajiya tabar gidan cikin bak'in ciki.
*******
Yaudai Huraira se munanan mafarkai yakeyi da zuhrah, da wannan ya shirya ya d'auki hanyar dazata sadashi da gidansu Zuhran......
Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins💕❤: *🏇🏇DOGUWAR HANYA....🏇🏇*
*Billy Galadanchi*
*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*
*Book nawa na siyar wane, idan kinsan baki biyaba karki karatamun kuma karkiyi forwarding ma wasu groups, idan kina buqatar siya ki neki wannan number 07084161618 kokuma 08030811300
27
Yayi kyau sosai, ya d'auki wanka iya wanka, ya shirya zuwa suyi magana ta fahimtar juna, so yakeyi ya sanar mata cewar ga abinda ya shirya, yayiwa kanshi alk'awarin idan zuhra ta zab'i zama dashi a matsayin mijinta amaimakon su rabu ze karb'i k'addarar sa, a yanda yake gani Lawuri ba Alkhairi bace arayuwar su shida d'an uwansa dukda har yanzu yanajinta k'asan zuciyar sa, Hanifer kuwa se yanda Allah ya tsara be tab'a dama soyayya da itaba itane take k'aunar sa ya zeyi?.
Ata wajen gate na gidan yae parkin motar sa ya fito kai tsaye wurin me gadin gidan ya nufa, yana zaune san benci na katako, hannu ya mik'a masa suka gaisa sannan ya zauna akusa dashi
"Malam dan Allah Fatima nake nema" kallon sosai me gadin ya masa sannan ya waiga ya kalli gate yaga bame zuwa
"Bintu wai kake magana?" Tunawan da yae sunan data gaya mai mahaifiyarta na kiran ta dashi kenan ya sanya yace
"Ea ita nake nema gunta nazo" tab'e baki yae ya jinjina kai
"Aikuwa malam dama ka dena wahalar da kanka indai fatima ce dan kuwa da cikin shege ta dawo, nima me aikin gidan ke fesamun tamusu lab'el taji komai, inda na tabbatar da cewan hakanne ganin ta fito janye da jaka tanata sharb'ar kuka, Allah na tuba kowa ya zata saceta akayi ashe yawon duniyar ta taje se yanzu gashi ta dawo wa iyayen ta da tsarabar shege" Cikin hargitsi Abu Huraira ya kalleshi
"Ban fahimce kaba malam?" Ya tambaya yana kallon gate man d'in a yamutse
"Bawan Allah, yarinyar nan gidan Bintu wacce ta b'ata shekaru uku bata nan daga sunan zuwa bautar k'asa, watanni biyu da suka shud'e ta dawo sega ciki yanzu ya bayyana ajikinta rad'am na shege, an tambayeta uban tayi shiru shine aka korata ubanta ya koreta, idan matar aure kake nema tun wuri ka sanyawa dokinka linzami" zuface ta shiga tsatsafo masa tako ina, mekenan ake nufi, tarawar da yae da zuhra kenan rabo harya rantse kumama wai har ansoma zargin ta agidan su shi yanzu mezece a yarda dashi, waye shi dazeje yace dasu shine uban yaron kuma aure aka d'aura musu, godiya yawa me gadin kurin yabar gidan.
**********
Zaman shiru tayi a hotel d'in data kama da kud'in da hurairah ya bata acikin na b'arayin nan, ina zata dosa ko sokoto zataje? Mesa Al-hassan ze mata haka? Meta masa ne arayuwa ze aikata mata hakan? Koda tamasa uzurin nesan tanada ciki ba amma ai yasan bazata dauwama da igiyar aurensa ba, yanda yasan ba santa yake ba haka itama Faruk ne zab'in ta, batasan dalilin daya sa take jin tamkar baze iya aikata mata hakan da sanin saba, wannan rayuwar k'unci da bak'in ciki baze iya taba sanyata aciki da gangan ba, Al-hassan mutumin kirki ne baze aikata mata hakan ba.
Idan tace sokoto zataje tonon asirinta ne, babu yanda za'ayi Faruk ya amince mata, yaya ze d'auki maganar jin cewa tayi aure? Beside bata tashi zancen tayi aureba seda ciki ya bayyana, ko alama bazata iya zubar da cikin taba koda shege ne bare da d'an halas ne da ubansa, toko gun k'anwar mamanta zataje kaduna? Cen d'inma dai tonon asirinta ne tunda tak'i auren kamal yaron k'anwar mamanta bata k'ara samun jittuwa da ita ba dariya zasu mata, wane wawan ne ma ze aminta da maganar ta dama huraira yana kusa ne watak'il daya kareta, kuka kam ta shhi ba adadi, Abuja garine me tsadar gaske babu ta yanda za'a yi wannan d'an kud'in ya rik'eta a hotel, babu k'awar dazataje gidansu da ciki kobe fitoba yanzu ze bayyana ne bada jimawa ba, itakam yazatayi.
**********
*Bayan sati shida*
Babu inda ake neman mutum agarin abuja inda Abu Hurairah beje neman zuhra ba, shi sabida tsabar son ganinta ma harya manta da wata aba wai ita Lawuri, hankalinsa in yayi miliyan toko atashe yake sabida neman zuhra, agun megadin gidansu yakejin bata k'ara dawowa ba tunda ta tafi, yauma kamar kullum tare da Al-hussain sukazo, bayan sun gamajin bata zo gidaba suka dawo mota suka zauna, Abu sufyan ya kallesa cikin kulawa yace
"Abu Huraira so tari mutane suke mun kallon me kafiya da akan al'amura amma azahiri ninasan kafini kafiya akan komai ma, babu abinda iyaye bazasuyi ba, kazo muje mu samu su dad nida kaina zan musu bayanin komai yanda ya kamata nasan zasu fahimceka semu tuntub'i iyayen yarinyar nan susan me ake ciki, wannan b'oyon baze k'are mu da komai ba, kodan tausayin wannan yarinyar ka taimaka ka bayyana gaskiya, bamusan halin datake ciki va ga ciki ajikinta ya dace ayi wani abun gaskiya" Jinjina kanshi yae
"Muje to gidan seka musu bayanin komai"haka suka rankaya zuwa gun dad.
*******
Tunda Lawuri ta dawo hayyacinta ta tariyo duk abinda ya faru se hankalin ta ya mugun tashi, tanaso taga Abu Hurairah ko yaya ne, da gaske tayi murnar ganin iyayenta amma bata farin ciki barin su Abu hurairah tana me aka dawo da ita gidan? Ta tuna komai ta gane komai ta fahimci komai daya faru rad'am!! Ina zataje taga haske, tundaga sannan kullum seta yiwa mahaifinta kuka akan ya sanya a mayar da ita ta masa alk'awarin zata dawo, da wannan yace babu damuwa ze bada dama taje wani satin, tunda tasan hanya inyaso gardawa sesu rakata....... Tofa!!!!!!
**********
Dad shiru yae yana tunanin wannan zancen dasuka zo masa dashi, mom ma tarasa ta cewa, sunyi shiru na wasu en dak'ik'u kafin General yae gyaran murya cikin b'acin rai yana me kallon Huraira yace masa
"Kai yanzu da hankalinka da komai Abu Hurairah zakayi wannan sakarcin, ni bama zancen auren ya dameni ba, na tabbatar bazakayi aure da gangan ba abu mafi ban haushi da takaici yanda ka b'oye mana 1, 2 kuma yanda ka cutar da yarinyar mutane, wani shegen ne yasanya ka tara da ita bayan kasan basanta kake ba, idan ma hakanne bazaka sauwaqe mata iymgiyar aurenka ba batare daka koda tab'a taba se tsabar rashin hankali ka daddage kawa matar ka ta sunna ciki sannan ka barta da ganin garari? Ni yanzu me kakeso nayi? Idan da siyama aka mawa zakaji dad'i ne? Eh nace zakaiji dad'i ne?" Hakuri ya hau bayar wa, ita kuma mom ta wani b'ata rai
"Haba Ganeral yaran nan sunmaka bayani akan cewar itace da kaud'in d'aura auren ma, bayaga haka aisunce maka so d'aya ne wani abu na auratayya ya gifta a tsakanin su? Abu na k'arshe kuma baya santa koda ganinta akai ni zan saka ya saketa" wata uwar k'ara ya saka irin ta tsofaffin sojoji
"Kee!! Adama wlhy duk rabar daya rabu da ita kema nan gidan zaki bari, kuma seya nemo 'yar mutane, ni zaku kawowa rainin hankali ku mayar dani k'aramun mutum, duk kanin abubuwan dasuka faru kece sila, an kawo yarinya yaranki suna so kince arniya ce babu wanda yazo a musulmi dan gatan sa, Allah ne yaso ya kuma zab'emu, dan ya zab'i wasu bawai illa bane ba, shibe guji bayin sa amma ke duk kin jagula maganar, tun Anan zaki gano cewar Allah mabuwayi ya nuna miki ikon sa, danma be bashi bamaguzar ba, kikakai aya, daya ya bashi musulma yarinyar dayake magana zuhra nasan mahaifinta farin sani, case na b'atanta ma nasan dashi harni anje nemanta dani, Allah ne ya nuna miki abinki kuma wlhy na bashi sa'o'i 72 ya nemo 'yar mutane kona mai hauka nima, zanje in gana da ubanta yanzu shima ya b'ata raina da wayon sa da komai aida ya tuhumeta yaji". Mom shiru tamkar ruwa ya cinyeta d'anya ko motsinta baka ji ko kad'an tsit kakeji.
********
*Bayan kwana biyu*
Daga asibitin ta fito sun koreta akan batada kud'in magani bazasu karb'eta ba,fitowa tayi abin duniya ya dameta, ga d'akin datake zama a hotel kaf har kud'in sark'arta data siyar ya cinye