You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng AMANI




Littafin




SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI)
takorikabara@gmail.com

AMANI
TARE DA NI, SUMAYYAH ABDULKADIR

SHIMFIDA
Safiyar yau wadda ta kasance Lahadi, an wayi gari da lullumin hadari mai hade da
sassanyar iska mai dadi a gidan su Amani, wanda ke cikin rukunin gidajen GRA a
birnin Katsinan Dikko. Kasancewar lokacin ya kasance lokaci ne na tsakiyar damuna,
kada ka so ka ga yadda shuke-shuken dake harabar gidan suka bude ganyayyakin su
suka yi korra sharr, suna bada kamshin furanni da bishiyu kala-kala, musaman da
bada jimawa ana iskar sai yayyafi ya soma sauka, don haka iska ce mai dadi kawai
take kadawa a gidan mai sanyawa alummar gidan nishadi, ciki harda Amani dake can
upstairs, ta bude tagogin dakin ta iskar na tadda har cikin toilet din da takw
wanka.
Dai dai lokacin da aka tsuge da ruwan saman kamar da bakin kwarya. Amani ta
fito wanka, daure da towel a jikin ta, ta karasa ta rufe tagogin ta don dakin ya
soma jikewa, ta zauna gaban mudubin kwalliyar ta dan kasar Mexico mahadin
furnitures na gogaggen katakon kasar waje dake dakin kamar dakin matar aure. Kamar
yadda yake a aladar ta kullum, daga fitowa wanka sai ta bata lokaci tana kwalliya a
zaune a kan stool, kamar mai shirin tafiya beauty contest in ka ga yadda take bata
lokaci wajen tsantsara kwalliya kullum.
To yau ma hakan ce ta kasance, Amani ta kwashe kusan mintuna talatin tana gyara
fuskar ta da serene make-up, bakin nan ya dauki maikon wet lips na Elizabeth Arden
sai sheki yake kamar ka sace bakinka gudu irin wanda ake kira kissable lips, ta
shirya cikin wani dan shafal din swiss lace ruwan gwaiduwar kwai da feshin golden a
jikin sa, duka wannan adon na karshen mako ne bana zuwa wani waje ba, koda-yake
dama tun filazal ita maabociyar ado ce da son kyale-kyalen mata irin wanda ya wuce
kima, musamman a renaku irin wadannan na karshen mako da take wuni a gida, don ita
bata yawace-yawacen gidan kawaye ko bukukuwa don basu ishe ta kallo ba.
An yi mata wani kyakkyawan dinki na zamani na doguwar riga wadda ta kama ta
daga sama ta bude daga kasa sosai kamar (A shape). Kai da ganin dinkin nata kasan
na yayan gata ne kuma ya ja kudi a jikin sa.
Amani tana sakkowa daga matattakalar bene inda dakin ta yake a cikin gidan su,
wata irin tafiya take yi kamar hawainiya, kamar bata son taka kasa, kuma kamar
tsinin takalmin ta bai dame ta ba. Sakkowa take daga benen cikin takun ta na
kasaita da rangaji irin na yan matan da ke cikin lokacin su, suka kuma yi katarin
samun rayuwa ta gata da wadata, dai-dai da yadda suke buri ko suke son samun ta a
duniya.
Daga nesa sai tayi maka kama da matashiyar macen Dawisu saboda iya ado da iya
baza tafiyar kasaita, koko zangarniyar dabinon da iskar hunturu ke kadawa sabida
yadda ilahirin kyakkyawan jikin ta ke rangaji tana zuba kamshi. Kai Amani karshe ce
a class da gayu karshen duk inda zaka iya kwatanta ta. A haka ta isa babban falon
gidan su, inda ta tadda mahaifin ta yana aiki cikin wasu muhimman takardu da naura
mai kwakwalwar bisa cinya (laptop) a gaban sa.
Tun kafin ta gama sakkowa daga benen hankalin mahaifin ta Hon. Usman ya kai
gare ta sabida karar takalmin ta mai tsinin dunduniya. Ya daga ido ya dube ta, sai
ya sunkuyar, yana cigaba da danna naurar gaban sa cikin kwarewa, ita ta san baban
ta Guru ne a computer da lissafi bay a taba yarda kwandalar sa ta bata cikin
lissafin sa, in ma ka sace ta don kana maaikacin sa zai gane, kuma sai ka yi aman
ta.
Cikin sigar kirari kamar ba mahaifin ta da ya haife ta ba, sai ka yi tsammanin
wani saan ta ne koko abokin wasan ta, Alhaji shiga fadin TA-FISU YAR GIDAN BABAN
TA! Ya saki dariyar farin cikin ganin ta ba tare da ya dago ba, hankalin sa na bisa
lissafin sa don kada ya bata kwandala, ya ce Ta-fi-sun Daddy an fito?.
In ji Alhajin cikin kulawa, sai yanzu da ya kammala kirgen sa kaf! Sannan ya
dago ya dube ta, ya kuma bata hankalin sa, bayan ya kashe naurar gabadaya, cikin
murmushin kauna da kulawa cikin yan kananun firi-firin idanun sa masu kama dana yan
China.
TA-FISU-KIN FI SAURAN MATA! Ya kara fadi cikin kambama yar tasa, wadda a
kullum ya dube ta surar mahaifiyar ta Jalan ke masa gizo, har kullum yana godewa
Allah da wannan kyakkyawar halitta da ya bashi a matsayin diyar sa, yana godewa
Allah da ta debo komai na Jalan bata ko dauko farcen sa ba, ji yake kamar ya lika
ta a goshi don So da alfahari, banda Allah sarkin hikima da tsara halitta yadda
yake so, wa zai iya hakan? Mai sanya mummunan mutum bakikkirin kamar sa ya haifi
irin wannan kyakkyawar halitta? Ai sai Allah Al Khaliqu Sarkin kaga halitta a yadda
ya ga dama, Ubangijin sammai da kassai. Mai sanya mummuna ya haifi kyakkyawa. Shi
da kan sa Uban yau da ya dube ta sai da ya ce tsarki ya tabbata ga sarki Allah!
Domin gani yayi gabadaya ta rikide masa ta koma mahaifiyar ta Jalan, sau tari
har gizo take masa da Uwar ta, shi yasa har kullum yake kara kaunar ta, duk
soyayyar da yake wa uwar ta kan ta ya koma. Har gobe bai auri macen da yake so yake
darajjawa irin Jalan ba. A yau ganin ta yayi replica din Maman ta, wato kamar Jalan
ce gaban sa shekaru ashirin a baya.
Amma Amani har ta fi ta sheki da daukar ido, don nata kyan ya hadu da gyara da
kyale-kyalen zamani mai tsada.
Alhaji Usman Faskari, baki ne wuluk, tittirna, gajere, kuma mai dagaggen hanci
da kananun idanu mitsi-mitsi kamar na yan birnin Sin. Kai babu wata suffa a jikin
Alhajin da zaa kira kyakkyawa, a cewar sa shi yasa Jalan ta ki zama da shi duk
arzikin sa. Jalan mai kama da matan Hurul-eeni don kyau. Ta sha ce masa firgita ta
yake cikin dare, ya daina shigo mata daki in dare ya yi, ya dinga bari sai gari ya
waye. Ta fannin halayyar Alhajin ma sai mu ce sai a hankali, domin dai a zahiri shi
mutum ne mai mammako (marowaci) kuma mai son kan sa da yar sa kadai. Ya mallaki
mahaukaciyar dukiya da shi kan sa bai san adadin ta ba, wadda ya mallaka ta
hanyoyin duka yaki halaal, da ya ki haraam, tunda kuwa gogaggen dan siyasa ne na
jiya ba na yau ba, wadanda suka dade suna ci da tada kai hadi da birgima cikin
dukiyar alumma da sunan siyasa da cigaban alumma.
A halin yanzu yana rike da shugabancin jamiyya mafi karfi, mafi shahara da
farin jini a wurin alummar kasar Najeriya. Wato jamiyyar AC da aka fi sani da
(Action Congress) ta kasa bakidaya. Ya iso ga matsayin shugaban jamiyya ne bayan ya
rike manyan mukaman Siyasa da baza su lissafu ba, tun daga karamar hukumar sa ta
Faskari, har zuwa matakin jiha, wato jihar sa ta Katsina, har zuwa halin da ake
ciki yanzu da ake damawa dashi a Gwamnatin Tarayya.
Cikin manyan mukamai na karshe-karshe da Hon. Usman Faskari ya rike har da
Sanatan Katsina ta kudu sau biyu.
Idan ka cire harkar siyasa da yafi bada karfi da yin kaurin suna a kai, don da
ita aka san shi, da ita yayi ficce, har ila yau, shi din kuma babban dan kasuwar
ketare ne (International Business Man) wanda koda siyasa ko babu ya riga ya haye
tudun mun tsira.
A can baya tun kafin ya haifi Amani har kasuwancin fidda Iron ore da aluminium
ore yayi, wato exporting natural resources da ake hakowa a kasashen Afrika daban-
daban irin Saliyo da Madagascar, yana da shahararrren kamfanin sa na kan sa a
Katsina mai reshe a birnin tarayya, Abuja wato FASKARI INVESTMENT amma rayuwar sa
tafi yawa a garin Katsina.
Daga baya bayan Amani ta tasa ya mayar wa da kamfanin suna Amani Faskari
Investment, kamfani ne na komai da ruwan ka a harkar shigo da kayan ginin gidaje
dana sakawa a gidaje, ba irin kayayyakin da basa shigowa da su da suka shafi wannan
bangaren daga kasashen ketare musamman kasar Faransa da kasar Mexico inda ya zuba
mafi rinjayen hannayen jarin sa, har ta kai ta kawo rabin rayuwar Usman Faskari ya
zama na yawo tsakanin Najeriya da Faransa da Mexico, komai na kamfanin sa kowa ya
san daga kasashen nan France ko Mexico yake kawo su, wato daga makerar su sai
kamfanin sa kadai, shi yasa baa fiya samun irin kayan sa a Najeriya sosai ba, abin
nufi, kayan ginin kamfanin AMANI FASKARI INVESTMENT LTD sun fita daban. Kama daga
kofofi, tagogi, tiles, marbles, da duk abubuwan ceramic da ake amfani dasu wajen
ginin gidaje. Masu ginne-ginen estates da gidaje a Katsina da Abuja yawanci duk a
kamfanin sa suke order.
A halin yanzu, Alhaji Usman Faskari, wanda alumma ke kira Hon. Faskari, yana da
shekaru hamsin da biyar amma in ka gan shi arbain zaka bashi sabida jin dadi da
kula da lafiyar sa, bashi da wani buri da yasa a gaba yanzu irin diyar sa Amani da
rayuwar ta, babban burin sa kullum shi ne farin cikin ta, jin dadin ta da walwalar
ta. Hon. Usman ya wadata Amani fiye da kima, tun a kananan shekarun ta Amani ta san
tafi sauran tsararrakin ta gatan aljihu dana Uba, ya kuma fifita ta ya sangartata
wanda hakan ya shafi tarbiyya da muamalar ta da mutane, saboda ya jika ta da komai
na jin dadi da bukatun rayuwa ba tare da ta yi maraicin mahaifiyar ta ba, wadda
Amani bata taba gani ba ko a hoto, alhalin tana raye ba wai ta mutu ba.
Iyayen ta sun rabu tun tana tsumman haihuwa, a cewar sa saboda munin sa ne
Jalan ta ki zama da shi, wanda kullum take cewa yana firgita ta, a zahiri shi yake
tunanin hakan, amma dalilai da yawa ne suka hana Jalan iya zama da shi, ciki har da
halayen sa na kankamo da rowa, dama kuma auren dole iyayen ta suka yi mata da shi a
dalilin ya saye mahaifin ta da dukiya.
Tunda ta koma kasar su (Sierra Leone) bata kara dawowa Najeriya ba, wai da
sunan ganin yar da ta Haifa ta tafi ta bari bata ko shayar ba, shi kuma bai kara
bin bayan ta ba, bai ma san tana raye kota rasu ba. Sai ya maida hankali a kan
rainon kyakkyawar diyar data bar masa wato AMANI, ya kuma maida kafatanin soyayyar
da yake yi wa Jalan a kan ta, bai yarda ta nemi wani abu a rayuwar ta ta rasa ba,
komai darajar sa, bai yarda ta yi kukan babu ba, ba ya ko tunanin ya dace ya aurar
da ita haka, kullum kallon yar kankanuwar yarinya yake mata, yadda take shekaru
ashirin a baya sanda yake goya ta da kan sa a bayan sa.
Shi kan sa bai san iya son da ya kewa yar sa Amani ba, ko iyakar adadin abinda
ya mallaka, kuma komai nasa da sunan tilon yar sa AMANI yake rubuta hakkin mallakar
sa. Wato ita yake sanyawa hakkin mallaka a rubuce gaban lauyoyin sa.
Wannan ne kuma babban abinda ya assasa bakar kiyayya tsakanin Amani da matar sa
Hajiya Rabi, saboda ita bata taba haihuwa da shi ba. Kafin Hajiya Rabi ya auri mata
kusan tara yana sakin su, duk ba a kan komai ba sai a kan rikon Amani, don sun kasa
yi mata irin rikon da yake so na gaskiya da amana, kankanin laifi zasu yi, ya basu
takardar saki in dai a kan yar sa Amani ne, da ya sakawa suna TAFISU. Yake mata
kirari da Kin fi sauran mata.
Haka masu aiki ma basu tsira ba, kullum cikin canzawa Amani su ake, saboda a
cewar sa basa kula masa da ita yadda yake so. Wannan yasa Amani ta tashi yarinya
sangartatta, hamshakiya, mai girman kai, mai yawan alfahari, mai raini ga mutane,
kuma mai izzah da dagawa da son a bata girma koda kuwa mutum ya haife ta.
Ga rashin tauna magana da kowa take Magana, har shi mahaifin nata kuwa wani
lokacin bata masa magana da girmamawa, ka yi mata magana ta mayar maka da harara.
Yadda duk magana ta zo bakin ta haka take furzar da ita ga kowa cikin raini da
gatsali, bazata yi laakari da yawan shekarun da ka bata ba zata iya marin ka ko ta
tofa maka miyau a fuska muddin ka shiga gonar ta.
Sabida girman kai irin na Amani ko kawaye cikin tsararrakin ta bata da su domin
ta raina ajawalin kowa, da an fara kawancen zaa babe, saboda ba kowa ke jure halin
ta na raini da dagawa ba.
Kawar ta daya ce da suka yi karatun sakandire tare a (Ulul Albaab Science
Secondary School Katsina) wato Hamida Balewa wadda itama Baban ta tsohon dan siyasa
ne, da ya rike har mukamin gwamna a jihar Baucin Yakubu.
Hamida ta iya da ita da halin ta, don ta fi ta hankali da hakuri kuma tana son
Amani kamar yar uwar ta, shiyasa suka rayu tsayin lokacin nan basu rabu ba, har
zuwa yanzu suna tare a shekarar nan da suka kammala karatun Jamia tare a jamiar
Tafawa Balewa.
Har zuwa lokacin da mahaifin ta ya auri Haj. Rabi, ita da kan ta Amani ta roke
shi ya rufe aure-aure daga kan Haj. Rabi saboda mutuncin siyasar sa, da kuma
kasancewar tana son ya zama akwai mace tare da su, duk da dai in ya saki baya
jimawa yake kara aurowa, kafin ya auri Haj. Rabi ya dade babu mata, don ta karshe
ta kusa kashe Amani da duka don haushi sabida ta tofa mata miyau a fuska, ita kuma
Haj. Rabi ganin inda raunin Alh. Usman yake wato (son a taya shi kula da Amani da
taya shi soyayyar tilon diyar tasa), sai ta saka kaimi a kai, ta kama Amanin ta
rungume a farkon zuwan ta, har fiye da kima, da ta gan ta zata hau rawar jiki da
hidima da ita a gaban Alhajin, irin yadda Hon. Din yake so matar duk da ya aura ta
yi wa Amani, Haj. Rabi ta shiga nuna mata soyayya har fiye da shi. Hakan yasa ta
shiga ran Alhaji. Amma ba haka abin yake a zuciyar ta ba.
Wannan ne yasa tayi dan nisan zango a gidan Hon. Usman, domin a kalla zuwa
yanzu tayi shekaru kusan hudu a gidan su Amani, sauran matan da ya aura a baya babu
wadda ta rufa shekaru biyu. Amma a zahiri Haj. Rabi ba wanda ta tsana data bude ido
ta gani a duniya irin Amanin.
Babban tashin hankalin ta ranar data fahimci cewa komai na dukiyar Alhajin
sunan Amani yake bearing, mai nufin ya gama mallaka mata komai nasa, duk wadda zata
zo sai dai ta jira dan tumunin takaba (idan ma ta yi nasarar dadewa a gidan kenan).
Musamman hankalin ta ya kara tashi da likita ya tabbatar mata shekarun ta sun wuce
na daukar ciki wato ta isa menopause ba matsalar haihuwa ce da ita ba yadda take
zato.
Haj. Rabi tana da yara biyu mace da namiji da tsohon mijin ta na baya. Ta aurar
da macen, namijin kuma yana jamia yana hannun mahaifin sa a garin su Minna jihar
Neja.
**** ***** *****
Amani ta karasa saukowa daga matattakalar benen, ta karaso ta zauna a jikin
mahaifin nata yadda ta saba duk girman ta, kai ka ce yarinyar goye ce a yadda take
masa magana cikin shagwaba.
Daddy, saboda Allah ba zaka daina kira na da sunan tsofaffi ba ko, bana son
wannan Tafisun da kake kira na da shi, kullum sai na gaya maka ka bari bana so,
amma ba dama ka ga na yi ado sai ka sake kira na da Tafisu-Tafisu. Amani ta fada
cikin zumburo baki, tana kallon takardun da ya kammala sakawa hannu, sakamakon
ganin sunanta baro-baro a kan takardar shaidar mallakar boutique na kayan sanyawa
na mata mai suna AMANI COLLECTION.
In bata manta ba tun shekarar data gabata Daddy yake shirye-shiryen bude mata
boutique din nan, wato sai yanzu Allah yasa aka kammala kenan.
Alhaji ya ce ba sunan da ya dace da ke irin Tafisu, saboda ai kin fi sun ne da
gaske, ina nufin kin fi tsararrakin ki gata, kin fi sauran yaya gatan Uba, kin fi
su komai tunda kina da Uba iri na, wanda ke tsaye a kan duk abinda kike so, da son
tsaya miki kan duk mai son shiga hancin ki. Ya fada babu wasa a maganar sa, ita ta
san Daddy yana nufin abinda yake fadi, a shirye yake ya tsaya mata a kan kowa da
komai. Shi yasa itama bata hada kaunar sa da ta kowa a rayuwar ta.
Hon. Usman Ya mika mata takardun yana fadin amshi ki duba Tafisu. Boutique din
ki da na dade da yi miki alkawarin bude miki a nan Katsina ya kammala, yana nan a
jerin shagunan Goruba Road, gobe sai kuje da MUKHY ki gani, idan da abinda bai yi
ba, ko baa kawo ba, ko zaa canza cikin kayan da kika bada list aka yi odar su, sai
ki fada masa, in ya so sai a kara yin sabuwar order, don yana da wata tafiyar dama
nan da watanni biyu zuwa Mexico, ina saka ran zai shigo min da wasu samfurin
marbles, sai ya karo miki abunda babu din.
In yaso sai ku je tare ki gani, kina dubawa kina fada masa yana rubuta min
komai a tsanake.
Ai kuwa nan da nan fuskar Amani ta yi kicin-kicin, ta zama kamar hadarin da ya
nausa ya yi gabas, ta yi mugun bata rai kamar bata taba fara a rayuwar ta ba, ta
kirne kyakkyawar fuskar nan tata ta wani irin yamutse ta, fuskar ta a wannan
lokacin sai ta koma masa exactly ta Jalan, wato mahaifiyar ta, idan kiyayyar ta ta
motsa a kan sa; wata kwayar mace guda daya da ya taba so a rayuwar sa, kuma daga
kan ta bai kara son kowacce mace ba, yanzun da Amani tayi hakan sai ya ga ta rikide
ta koma masa Jalan har sai da gaban sa ya fadi sosai. Yanayin ta a irin wannan
lokacin yafi kama da na yayan nan da baa kwaba, baa hantara, wadanda saidai iyayen
su su bi abinda suke so ko basa so, fadi take cikin shagwaba, hassala da zumburo
baki.
Allah ya tsare ni hada hanya da shi, Allah ya raba gatari da saran kuka, shin
Daddy sau nawa zan gaya maka ka manta ne? Magana ta gaskiya ka daina hada sabga ta
da ta wannan mai cunkusashshiyar fuskar da halin sumumu-kasau din.
Ina dalili mutum kullum yana faman kirnewa mutane fuska kamar malaikan daukan
rai, alhalin da bazar su yake rawa? Mutum dan siriri da shi sai kafirin girman kai
da bakin hali kamar na mutanen farko.
Daddy yayi kasa da murya duk da yana son yin dariya amma ya hadiye, saboda
yadda ta fitittike tana furzar da maganar zaka san an tabo fushin Tafisu, cikin
lallashin yar tasa yake cewa.
Uwa ta. Kullum ina gaya miki ki daina damuwa da yanayin fuskar Mukhtar cikin
shaanin kasuwancin mu ko muamalar mu ta yau da kullum da shi, kowa da kika gani a
rayuwa, yana da damuwa, mai yuwuwa damuwa ce a kasan ran sa take bayyana a kan
fuskar sa, yanayin walwalar sa ko rashin ta ni ba zai shafi alaqa ta da shi ba, o
neman kobo na because its obvious I cant do without him (a fili yake ban iya rayuwa
sai tare da shi).
Duk yadda yanayin halittar sa yake zan iya going da shi a haka, haka kema nake
so ki fara, saboda babu mai iya yi min hidimar da yake yi min da jiki da kwakwalwa
da lafiyar sa da zuciyar sa gabadaya hidimtawa dukiyata yake, haka Allah ya yi shi
da rashin walwala, ba ke kadai yake yi mawa ba Tafisu. Kowa ma! Ki je office din mu
ki gani, zan iya rantse miki ba wanda ya taba ganin dariyar sa.
Kuma banda abin ki Tafisu, ina ruwan ki da faraar sa ko rashin ta? Amfanin da
yake yi min, da rikon amanar sa a kan dukiya ta zaki duba, kafin a samu mai amanar
sa da gudun duniyar sa da rashin zalama akan KUDI, zaa jima Amani.
Na sha gwada Mukhtar ta hanyoyi masu tarin yawa da tawa hikimar da Allah ya
bani ta testing mutane, amma ban taba kama shi da wani hali na son cuta min, ko yi
min almundahana, ko munafurci ba. Hasalima amanar sa ce ta hada ni da shi ta hada
wannan bond din mai karfi tsakani na da shi. Wanda ya wucde na ubangida da yaron sa
nake masa kallon dan ciki na.
A baya in kin tuna maaikata nawa nayi kafun shi, cikin su babu wanda bai cuce
ni ba in one way or the other.
Ban taba samun matashi nagartacce kamar sa ba, kuma kafin a samu yaro nagari
irin wannan a zamanin nan abu ne mai wuya Tafisu. Inada dalilai na a kan son yaron
nan, da bazaki fahimta ba.
Ai ba komai yasa kika ga na jure masa yana bata miki rai da halayen sa ba, sai
don in muka sallame shi kamar yadda kike so ba zamu taba maida asarar rashin sa ba,
akwai maaikatan da kai kake amfana da su, ba su suke amfana da kai ba, ko me zaka
biya sub aka iya biyan su. Ki saka Moukhtar Diffa a cikin jerin irin su.
Saidai in ke zaki dinga yimin ayyukan da yake yi min din idan kika takura na
sallame shi, which is impossible. A matsayin ki na mace ba zaki iya abinda Mukhtar
yake yi min ba, irin su yawon kasashen ketare shigo da kaya da handling kamfani
bakidaya, banda sauran wahalhalun da yake yi min (personally) a cikin gida, a kan
dan albashin da bai taka kara ya karya ba, kuma cikin amana, girmamawa da
tsantseni.
Ga ilmin kasuwancin Allah ya bashi, ga kwakwalwa kamar kwamfuta, duk wata hanya
da kika sani da zata maida min kobo ya koma dari cikin shekarun nan da suka gabata
ina tabbatar miki daga Mukhtar ne nake samun Theory, tun zuwan sa gare ni ban san
faduwa ba sai dai riba.
Ya numfasa sannan ya dubi Amani wadda ke sauraron sa da kunne daya don kuwa
hankalin ta na kan wayar hannun ta, bai damu ba don ya san tana jin sa, ya cigaba
da fada mata cewa. Duk wata hanyar samun riba mai tsafta da kike gani yanzu a
kamfanin nan shi ke kawo min ita.
One impressive thing about Mukhy, baya taba waiwaye da cewa ina kwarar sa da
dan albashin dana ke bashi kowanne wata, amma wallahi bai taba korafi ba, dan kuwa
albashin dana ke biyan sa ko kusa bai kai kimar yawan ayyukan da yake min ba, da
abinda yake nemo min, in aka yi laakari da cewa, ya mallakawa dukiya ta lokutan
rayuwar sa baki daya, da kuma tarin fasahar ilmin kasuwanci dake cikin kan sa. Ko
iyayen sa bai taba ziyarta ba tun zuwan sa hannu na.
Kullum na yi masa maganar zuwa gida cewa yake Alhaji in na tafi wahala zaka
sha, don ba lallai a bar ni in dawo ba.
Kin san akwai wasu jinsin mutane da sam-sam basu san wani abu wai shi jin dadin
duniya da da shagaltuwa da kyale-kyalen ta ba, irin wadannan mutanen su sai dai su
taimakawa wani ya

Please Login or Register in order to submit comment