You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata kallo na biyu, sabida yadda ta ke masa kwarjini da
sanya shi faduwar gaba. Ga harara kala_kala da yake sha daga kyawawan idanun ta.
Maigadin gidan Hon. Usman wanda tasu ta zo daya wato Malam Tajuddeen Bafillace, ya
sha yi masa fatawar cewa,
muddin kana son zaman lafiya da Alhaji, muddin kana son tafiyar ku tayi tsaho,
muddin kana son fadar ka ta fadada a wurin sa kuma tauraruwar ka ta cigaba da
haskawa a idanun sa, to ka kyautatawa mara kunyar yar nan tasa mai soyayyun idanu a
tsakar ka.

Shima ya yarda da hakan don idan ya zauna da Alhaji na minti biyar to hirar sa
ta mintina uku cikin biyar din a kan tilon 'yar sa Amani ne da irin tanade tanaden
da yake yi mata a rayuwa don baya so ko bayan ran sa ta sha wahala ko ta nemi wani
abu ta rasa tunda bata samu soyayyar Uwa data dangi ba.
A irin haka watarana ya taba gaya masa cewa ya gina mata estates har guda biyu
ya kuma mallaka mata su da sunan ta, karkashin idanun lauyoyin sa a cikin Birnin
Katsina da babban birni, Abuja. Watau AMANI FASKARI HOUSING ESTATES. Wadanda
dukkansu ya zuba tenants 'yan haya duk shekara suna biyan Amani miliyoyin da shi
kan sa bai san zai same su a jikin gidajen ba. Hakan ya sa dole ya bude mata hannun
jari a kasar Mexico.
Mukhtar ya kan yi mamaki a cikin ran sa, mugun mamaki don bai san ana haka ba,
wai uba ne ke kaunar dan da ya haifa har haka! Wasu lokutan abun ya bashi sha'awa
ko ya burge shi, don bai taso ya ga ana yin hakan a gidan su ba. Bai san dadin
kaunar Iyaye ba. A nasu gidan ba'a san komai ba sai uwar riko sai 'yan ubanci,
kishi tsakanin iyayen su mata, burin gado da horo mai tsanani da sunan tarbiyya,
wannan itace rayuwar da ya taso ya budi ido ya ga ana yi a gidan su, wadda karfi da
yaji ta koya masa zama independent.
Shi ko alfarmar gaisawa da nasa mahaifin ba ya samu a sanda yake tare da shi,
yana raye ba wai ya mutu ba kuma suna cikin gida daya. Amma sai ya yi wata biyar
suna gidan da shi bai saka shi a idanun sa ba. Ko fuskar sa baya samun alfarmar
gani.
Wannan dan tunanin da ya mika a zaune, yasa kyakkyawar fuskar sa yin jajir, ta
rikide zuwa yanayin ta na tun fil azal da aka san shi da shi wato yanayin sa na
rashin walwala da kwantaccen bacin rai, irin bacin ran nan mai kwanciya a kasan
idanun mutum, ya sauya ainahin kalar su zuwa brown, ya nuna zahirin rudanin da ke
cikin zuciyar dan Adam. Wanda a duk lokacin da ya tuna mahaifin sa ko ahalin sa
hakan ce ke faruwa da shi, ya ji yana son kara nesanta kan sa da Diffa many more
miles away! If possible, har fiye da nisan da yayi da gida a yanzu, don Najeriya ba
nisa da Nijar, zai fi son ya tafi can karshen duniya wato kasar China birnin Hong-
Kong ya yi rayuwar sa a can.
Matsalar guda daya ce yana jin dadin zama da Alhaji Usman don soyayyar Uba
yake nuna masa irin wadda bai san da ita ba, bai san irin ta na existing ba. Shi
kan sa yana mamakin soyayyar Alhajin gare shi a matsayin sa na bare a gare shi. Ba
don haka ba da ya kara lulukawa cikin duniya ya kafa rayuwar sa a can.
Dagowar nan da zai yi da zummar fita daga motar don zaman ya fara gundurar sa
ya hangota tana takowa cikin rangajin ta na halitta, tamkar reshen bishiyar da iska
ke kadawa ko kuwa Dawisun da ya baza adon halitttar sa yake tafiyar takama a doron
kasa, sai kayi tsammanin beauty contest zata tafi.
Ta yi kyau ba dan kadan ba cikin wani material lace kalar ja da ratsin baki, an
yi mata dinkin riga da siket wanda aka tsaga kafar sa ta baya, babu mayafin arziki
a jikin ta baya ga wani rakani gantalin cantitly sai daurin kai da ta kalmasa
gwanin shaawa da dankwalin kayan kai bazaka ce ta hada jinsi da hausawa ba.
In da abinda yafi bakanta masa rai a dabiun ta bai wuce rashin daukar mayafi da
lullubi da muhimmanci ba, bai taba ganin ta da lullubi a kan ta ba balle a kai ga
zacen hijabi ba.
Amma shi waye da ya isa ya yi mata magana a kai? Zai iya yi wa Baban ta ya yi
mata, amma ya lura Baban ma bashi da katabus a kan ta, tamkar itace uban shine yar,
babban abinda yasa ya tsani Amani kenan.
Duk halayen ta na sangarta, rashin ilmin zamantakewa da rashin sanin addini
basa gaban sa, don ya san masu iya gyaruwa ne in ta samu uwa ko abokin rayuwa
nagari, ba irin Hajiya Rabi ba uwar gantali uwar bisa titi wadda mijin ma baya
gabanta irin kasuwancin ta da yadda zatayi ya bata kudi kullum, amma rashin girmama
mahaifin nan nata da bata yi ko ta wajen magana yasa ya sallama mata, yana roka
mata shiriya a kasan ran sa, don ya lura girman hannun namiji ce. Irin su Amani
suna abu bisa kuskure ne ba tare da sun san cewa kuskure bane, saboda tun farko
basu tashi ana kwabar su ko ana nuna musu girmama na gaba ba, aah, an raine su ne a
bisa tafarkin duk abinda suke so dole su samu karkashin soyayyar iyaye masu duniya
a tafin hannun su, irin mai samar da komai na bukatar rayuwa ga yaro ba tare da ya
yi gumi ko ya fidda hawaye ba.
A haka ta iso motar ta tadda shi, ta tsaya tana jiran ya bude ya fito ya bude
mata yadda direbobin ta ke yi cikin rawar jiki, don da kunnen sa ai yaji Daddy ya
ce daga yau shi zai dinga tuka ta which means yana matsayin sabon direban ta kenan.
Amma Mukhtar sunkuyar da kan sa yayi, kamar bai san da tsayuwar ta a wurin ba
ya dukufa danne- danne cikin tsaleliyar wayar hannun sa amma fa shi kan sa bai san
me yake dannawa ba, saboda kwarjinin Amani mai bi har cikin bargon sa.
Hey! Baka ganin mutane sun iso ne? Ko makaho ne kai?
Mukhtar ya dago cikin slow motion ya zuba mata fusatattun idanun sa masu kama
da an diga zaiba a cikin su. Nan da nan Amani ta daburce, bata san sanda ta bude
kofar motar ta shige ba. Ta kuma rufe kofar motar da karfi. Ko gama rufe kofar
motar bata yi ba ya ja motar, saura kadan ta rufe da kafafun ta.
Wata irin shakkar Mukhtar ta soma shigar Amani, domin bazata iya fassara
alamuran data hango fal cikin idanun sa ba. idanun cike suke fal da abubuwan da shi
kadai ya san su, ga tarin damuwa da fushi da rashin walwala, sannan tuki yake amma
ko kallo bata ishe shi ba.
A rayuwa bata taba haduwa da namijin da bai yi mata kallon kwal uwar daka ba
koko kallon kin yiwa sauran mata zarrah idan ta yi kwalliya sai shi wannan
baabzinen. Koda take ce ma Daddy bata son sunan TA-FISU tana fada ne kawai, amma fa
tana son sunan, domin yana kara mata alfahari da kyawun surar ta mai ruda yaya
maza, wani lokacin har mata yan uwan ta (will not keep wishing they were like her).
Yau ga ta ga namijin da bai yi mata kallo na biyu a duniya ba, ta saci kallon
kan ta kadan, to kyawunta ne bai ishe shi daga ido ya kalla bane ko kuwa kwalliyar
data cancada bata kai ta kawo bane? Ko kuwa shi din ma YA FI SAURAN MAZA ne?
Kwafa tayi tace cikin yar rawar murya Malam ka rage gudu, baa gudu da ni a
mota, I think Daddy ya gaya maka, drive with care. Yayi fumfurus kaman bai ji ta
ba, maimakon hakan sai ma karawa motar sa wuta da yayi yana fadi cikin ran sa ai ni
ba Daddyn naki bane, Mukhtar nake.
Amani tayi kyacci, kamar ta ji me yake fadi a ran sa. Daddy ya san kai makaho
ne kuma kurma ne sannan baka da seti ya saka ka tuka ni a mota?
Sai lokacin Mukhy ya dan juyo a gicciye a dube ta, da idanun sa masu kalar
silver, duban da sai da yasa hantar Amani da hanjin cikin ta karkadawa domin ta yi
zaton kwada mata mari zai yi, don ko da bai yi magana ba ta san kallo ne na
zazzafan gargadi ya yi mata, wato ta san irin maganar da zata dinga furta masa. He
is not that stupid as she thinks.
Suka isa Goruba Estate wato inda boutique din Amani yake. Nan ma jira take ya
fito ya bude mata kofar mota ta fito amma ya bude yayi ficewar sa ya bar ta a
zaune. Masu kula da wajen sai gaishe shi suke yi don su a tunanin su shine
mamallakin shagon, sabida duk wani shige da fice shi ya dinga yin sa har komai na
boutique din ya kammala, tankareren shagon yana daga jerin farko-farko na shagunan
da ke cikin plaza din. Mai gadi ya kawo masa mukullan hannun sa ya bude ya shiga
ciki. Da Amani ta tabbatar ba zai bude mata kofa ba sai tayi kyacci ta bude ta fito
ta bi bayan sa.
Ta tara shi fal a ranta har da karin gishiri da maggi na abubuwan wulakanci da
zata gayawa Daddy ya yi mata, tana shiga shagon ita kanta ta girgiza da irin
dukiyar da mahaifin nata ya narkar mata, takalma ne da jaka na mata na zamani na
yayi da sittiru yan waje na yara da manya, shi kansa wanda ya zabo kayan ta sara
masa wajen iya investing kayayyakin da zasu dauki hankalin kwastoma, a rashin sanin
ta ba kowa bane dan mutanen Diffa ne amanar Alhaji Usman Faskari.
Duk kushen ta da high taste din ta ta kasa kushe tsarin da Mukhy ya yi wa
shagon nan. Ko da suka gama dubawa abubuwa kadan ta iya cewa a kara. Shi din ma
rubutawa ta yi aka takarda ba da fatar baki ta gaya masa ba. Yayi gabas ita kuma ta
yi yamma a cikin shagon don kada ma ta hada hanya da shi. Ta rubuta iya abubuwan da
take bukata a kara sannan ta fice daga shagon ba tare da ta ce masa ta gama ba, shi
kuma yana can zaune bisa wata kujerar roba a cikin shagon yana jira ta gama
gatsine-gatsinen ta tana kallon komai tamkar ta ga kashi, nan kuwa can a kasan ran
ta yabawa take yi komai ya yi mata, ta kuma jinjinawa fasahar wanda ya tsara shagon
nan. Wasu kayan ma da aka zuba duk gayun ta bata san da irin su ba farkon shigowar
su Katsina kenan.
Da ta gama abinda zata yi mota ta koma ta shige ta zauna ta hau danna horn ji
kake biiiiii..biiiii..kamar mai kiran kare. Yana jin ta ya yi kamar bai san tana yi
ba, ya gama danne dannen sa a wayar sa ya mike ya haura zuwa upstairs na shagon
yayi zaman sa. Ya rantse a kasan ran sa sai ya rama shanya shin data yi a gida
cikin mota kafin ta fito. In bai manta ba ai jiran awa biyu kwakkwara yayi cikin
mota yana jiran ta, to itama sai ta yi shi yanzu.
Bakin ciki da bacin rai a wurin Amani abun baa cewa komai, data gaji da zama
sai ta kira Daddy a waya yana dagawa ta hau kuka da balbalin masifa tamkar mai
magana da kanin ta. Daddy kuwa cewa yake me ya faru ne Tafisu? Daga ina kike
magana? Tace.
Daddy daga cikin motar da wannan Dirty Human Being din ya shanya ni, tukun
nama Daddy ka taba zaunar da shi ka gaya masa ko ni wace ce a wurin ka? Shi ba
kurma ba shi ba makaho ba amma wallahi sun fi shi ji da gani, mutum dunkumkum sai
kace dankali ba um ba um um sai bakar zuciya zaka hada hanyata da shi? Ko bude min
mota fa bai yi ba, yanzu haka zaman sama da awanni biyu nake cikin mota har baya na
ya fara ciwo. sai ta koma kukan shagwaba wanda Daddyn kadai take yi wa irin sa.
Tace.
Daddy in baka zo ka dauke ni da kan ka ba ba zai san matsayi na a wurin ka ba,
idan baka kore shi ba dauka zai yi ni yar aikin gidan ka ce, babu wanda ya taba yi
min wulakancin da mutumin nan naka yayi min. Amani ta tsinke da fada kamar
tsinkakken carbi duk a kan kunnen Mukhy da bata ma san yaushe ya bude motar ya
shigo ya zauna ba, bayan ya duba agogo ya tabbata awa biyu ta cika, kuma ko da take
ma Daddy wannan balbalin kara fusata shi abun yayi because he respects Alhaji so
much, ba zai iya jurar jin ana masa wannan rainin ba. Don haka ya fizgi motar a
gujen gaske saida Amani ta zunkuda ta koma ta bugu da kujerar data ke zaune.
Amani ta zuga salati tana cewa Daddy ka cece ni zai kashe ni Daddy ya ce bani
Mukhtar din tace Daddy Allah ya sawwake ya taba min waya ya shafa mata bakin hali
irin nasa abin nata sai ya koma baiwa Alhaji dariya, ya ce alright, bari in kira
shi ya katse kiran nasu ya soma kiran Mukhtar.
Yana ganin kiran Alhaji amma kuma yana tuki don haka saida kiran ya katse. Ya
gangara gefen titi ya kashe motar sannan cikin nutsuwa ya bi bayan kiran Alhajin.
A yadda ya tausasa murya ya kuma russunar da kai duk da Alhajin baya ganin sa
sai kayi tsammanin da mahaifin sa ya ke magana, ya ce Alhaji muna hanyar dawowa
kana son wani abu ne? Alhaji cike da damuwa ya ce No Mukhy, karar ka aka kawo min
kala-kala, ka bi ta a hankali ka ji? Ka san wani lokacin haka take abu na yayan
fari. Mukhtar ya saci kallon ta sai kumburi take kamar zata fashe ya ce Alhaji ai
babu damuwa ina iyawa da ita, musamman da wani lokacin tana abu zayyal majnunah
(kamar mahaukaciya), abinda bazan lamunta daga gare ta ba shine rashin kunyar da
take maka, ka gaya mata ta dinga maka magana with respect irin yadda yaya suke yi
wa iyaye, saboda kai ne gaba da ita ba ita ba. Idan ta cigaba da yi maka magana
irin haka bazan kara daukan ta a mota ba.
Alhaji ya ji dadi, ya ce Mukhtar kada ka damu da shirmen Tafisu ka ji? Ka san
wanda baida mahaifiya a kusa sai ana masa uzuri Mukhtar yace ni ba zan yi ma ta
uzuri da wannan ba, babu uzuri a cikin biyayyar iyaye, in dai a kan daga sautin ta
sama da naka ne zan iya bubbuge bakin ta Alhaji Alhaji yayi murmushi yace to
shariar taku ta fi karfin waya, ku dawo gida sai mu yi ta a zaune. Kuna ina yanzu?
Yace muna hanya ko rabin isowa gida bamu yi ba. Ni gaskiya Alhaji a gate zan
sauke ta, ni kadai zan je na dauko Hajiya, daga can ina da inda za ni Alhaji ya ji
wani iri ya ce Mukhtar ban san ka da rashin kirki ba kada ka fara akan kanwar ka ya
ce Alhaji sai ta daina yi maka fada zan yi kanwa da ita, in ba haka ba kowa ya yi
rayuwar sa cikin gidan nan ba ruwan Yaya da kanwar, bani da zuciyar da zata iya
daukan ana raina min kai.
Daga haka ya kashe wayar sa Alhaji na fadin ka dai shigo da ita kada ka sauke
ta a gate don Allah ba don halin ta ba.
Duk abinda suke fada a kunnen Amani, mamaki da haushi ya hana ta ko kwakkwaran
motsi, anya wannan mutumin bai taki komai ba? Yaya kana zaman yaron gida kake ma
uban gidan ka Gadara irin haka shi kuma yana biye maka sai kace uban da ya haife
ka? Amani ta saci kallon sa sai suka hada ido, ya kashe ta da harara, yana kokarin
cire farin gilashin idon sa don ya sha round din da zai kai su unguwar su. Wani
irin kyau ya yi a idanun ta mutum tamkar shi yayi kan sa, kai kace wani balaraben
Madinah ne idan yana magana, tsafta da wanka sun kama jikin sa radam.
Sai ta tuno alfarmar da take so yayi mata duk da ya bakanta mata rai yadda bata
zato amma wannan ce dama ta karshe da zata iya rokon sa don ba haduwa suke yi ba,
sai dai ta hange shi a harabar gidan daga balcony din ta yana shiga mota zai fita
ko ya shigo gidan. Ko ya zo daukan Alhaji su fita.
Ta rasa ta ina zata fara don kwata kwata babu fuska daga Mukhy, yama kara daure
fuska tamau da suka hada ido don kada ta kawo masa wargi, ya lura da kallon
kurillar da ta ke masa wanda ya wuce shariah. Shikuma baya son ko kalma guda ta
hada shi da Amani don kada raini ya shiga takanin su irin wanda takewa kowa da ke
karkashin ta.
Ya Allah ya zata yi da wannan mutum mara sakin fuska? Sai kawai tayi kundumbala
tace, Man, ina son fidda kudi ne daga corporate account dina? Mukhtar bai san cewa
magana take da shi ba, ya dauka ma a wayar ta take magana da wani daban don haka ko
juyowa bai yi ba.
Amani ta daga murya da dan amo tace na tabbata kai ba kurma bane, but you are
acting kamar baka ji!
Sai yanzu ya san da shi ta ke, ya kuwa kara daure fuska yaci gaba da tukin sa.
Amani sai ta fara hawaye don abun yayi mata ciwo mai yawa, baa saba yi mata irin
haka ba, kowa na gidan girmama ta yake yi yana nan-nan da ita yana rawar jiki idan
ta bada umarni, balle wanda ke matsayin yaron Baban ta ya yi mata irin wann
funfurus din.
Kuka ta soma yi sosai har da sheshsheka da fyace hanci, tace tunda dai na san
kana ji na, halin ka ne shariya da wulakaci, to bari in fadi sako na, ya rage naka
ka yi min alfarmar ko kada ka yi.
Ina so zan cire kudi 5 million zan yi amfani da su bana son Daddy na ya tuhume
ni, idan ka ga alert dinnan alfarma ce kada ka fada masa tunda dai kudi nawa ne, ba
na wani ba.
Mukhtar ya rage gudun motar ya dan juyo kadan ya saci kallon ta, sai kuka take
tana fyatar hanci kamar wadda aka yi ma wani mugun duka, kada ya je ta daura masa
sharri, don ya ji an ce masa mata makirai ne. Ya kashe motar gaba daya a gefen titi
ya ce.
Da ni kike?

Amani ta ce aa da sitiyarin motar ka nake. Karo na farko da Mukhtar ya yi wani
miskilin murmushi, ya ce to kai sitiyarin mota ana maka magana!.
Amani ta kara rushewa da kuka tace Allah yasa ayi maka irin wulakancin da kake
yi min. Allah ya hada ka da daidai kai, Allah ya sakawa mahaifina amana ta da ya
baka kake ci don ka san ka asirce shi.
Mukhtar ya bugi sitiyarin sa ya ce ban da muguwar addua ga wanda baki sani ba
Maam, you will never know what a man like me is going through, I hate hayaniya, ki
gaya min wace alfarma ce kike so? Bana son koke-koken banza me na yi miki? Wane
kudi kike magana a kai? Kuma me zaki yi da su? Ban fahimce ki ba anymore.
Amani ta dan ji dadi, at least hargagin ta ya sa ya kula ta, ta share hawayen
ta da gefen mayafin ta, ta ce ba damuwar ka bane abun da zanyi da kudi na, kawai
bana so Daddy ya ji ne, da ba zaka san ma na cire ba
to kin san ba damuwa ta bane kuma bai shafe ni ba don me zaki sako ni ciki? An
gaya miki ina shiga abunda baa sa ni bane? Ai kawai ki yi abinda kika ga dama nima
in yi aiki na na daukar zance in kai gaba, tunda shi aka sa ni, ba sai kin saka ni
cikin shaanin ki ba, mind your own business and leave me alone.
Ya ja motar suka cigaba da tafiya Amani na gayawa kanta ta gara ta canza taku,
tunda har kuka yana karya zuciyar sa ya saurare ta, ko baya so, ya bata amsa ko
yaki Allah to zata rage izza tunda ta lura izzar ta ke tunzura shi ya ki sauraron
ta.
Tabbas yau ta gamu da wani sabon mutum a cikin rayuwar ta, wanda bata taba
ganin mai hali irin nasa ba.
Bawan Allah ko wa kake da suna? Na yi rantsuwa ba ta hanyar banza zan kashe
kudin nan ba, kawai bana so Daddy na ya san da fitar su.
Ta sassauta murya ta ce kayi min wannan alfarmar, ba don ni ba ba don hali na
ba.
Mukhtar ya yi mata kallon kin ishe ni haka kafin yace zan yi miki only in kin
gaya min gaskiyar ko me zaki yi da kudin nan, bana backing munafurci da rashin
gaskiya komai kankantar su, in kina da gaskiya ba zaki nemi a boyewa mahaifin ki
wani abu da zaki aikata ba.
Amani ta share ido da bayan hannun ta ta marairaice, sai ta dan bashi tausayi,
ta ce wallahi ina da gaskiya ta, trust me, kuma ta hanya mai kyau zan yi amfani da
su yanda ba zai gane ba, don bai san irin ciwon da na ke ji in naga kowa a jikin
uwar sa ba.
Ta cigaba da cewa Malam COO (Chief Operating Officer) ni din ban taba ganin uwa
ta ba sai a hoto, ban rasa komai ba amma ina so in je gare ta, ba don kuma na raina
kulawar Daddy na a kaina ba, sai don kowannen su matsayin sa daban a gare ni.
Zuciyar Mukhtar ta dan yi laushi, laushin da shi kan sa bai zaci tana da shi
ba, yafi zaton zuciyar sa tafi dutse tauri amma ashe akwai sauran tausayi a cikin
ta, akalla ya gamsu, tunda ba shaye-shaye zata yi da kudin ba don tafi masa kama da
masu banka kwaya, yace I will think over it. But remember always zaman Alhaji nake
ba zaman wata Amani ba!.
Maganar shi ta karshe bata yi mata dadi ba. Ta yi kuta ta ce kai a rayuwar ka
baka da humanity ne? baka da concern? Baka da sabo da mutane kuma baka daukar kowa
da muhimmanci sai Daddy?
Ya murmusa kadan, har beauty point din fuskar sa ya lotsa ciki sosai yace ban
san ta ba humanity din, concern kuwa ko maanar ta ban sani ba, mai yuwuwa sanda
ake rabon su ni ina Diffa. Kin san ni dan Diffa ne, Diffa region, ta kasar Nijar.
Amani ta kulu iya kuluwa, ta yaya ba zai dauki abinda ta gaya masa da
muhimmanci ba bayan sirrin ta ne da bai kamata ma ta gaya masa ba? Zai bi ta da
bakar magana bayan ta bude masa sirrin ta? Maganar mahaifiyar ta fa take masa,
wadda bata taba gani ba, yana mata maganar wani garin su.
Daidai lokacin da suka iso tangamemen gate din gidan su Amani. Dama bata son
zuwa dauko Hajiya Rabi. Ba tun yau ba ta fahimci matar zal wajahaini ce (mai fuska
biyu) a gaban Daddy kawai take nuna kaunar ta, a bayan idon sa kuwa kashi ya fi ta
daraja a gidan nan. Shi yasa itama ta kama kan ta, sam bata shiga shaanin Haj. Rabi
ko hanyar sassanta bata bi, ta kuma yi wa kanta alkawarin bazata bari Daddy ya sake
ta ko ya san halin ta a

Please Login or Register in order to submit comment