You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kan ta ba, don ta gaji da aure-auren sa da ake faman kirga
masa akan ta.
Mace ta karshe da Alhaji ya saka wai ita Zaibi, ta fadi maganar data tsaya
mata a rai har gobe ta kasa mantawa, kuma daga kanta ne ta kudiri aniyar hana Daddy
kara sakin kowacce mata duk mugun halin ta. Gara ta bar su da halin su ta nemo tata
mahaifiyar.
Cewa matar ta yi ga gidan nan ta bar mata, karshen soyayya Alhaji ya auri
Amani ya maye gurbin ta da ita.
Don haka tun kafin ya gama daidaita parking ta soma kokarin bude kofar don ta
fice kada ma ya ce suje dauko Hajiya Rabi tare, sai ta ji ta gadagau wato ya rufe
ta automatically.
Kallon tambayar dalili Amani tayi masa. Idanun ta fal hawaye. Mukhy ya daure
fuska sannan ya shafa sumar kan sa ya ce da ita as a brother, zan hore ki da abu
daya, duk rintsi kada ki kasance mai munafuntar mahaifin ki, domin mahaifin ki
extraordinary Uba ne, musamman a kan ki, ban taba ganin uban da ke son yar sa irin
son da mahaifin ki ke yi miki ba. Don haka bai cancanci ki boye masa komai da ya
shafe ki ba.
Mai zai hana ki same shi officially ki gaya masa damuwar ki, akan son ganin
Maman naki? Im sure yadda Alhaji ke son ki da girmama lamarin ki ba zai ki kai ki
ga mahaifiyar ki ba.
Wane irin bincike ne saboda Allah har miliyan biyar? A kasa ake hako kudin? In
gaya miki gaskiya an doki hancin ki, don an ga baki da wayau, kuma you are
desperate, a kan bukatar ki, ni ki bar ni zan lallaba Alhaji ya kai ki gun Maman
naki on koboless (babu ko sisin ki) ba kuma don ke ba sai saboda Alhaji ne ya haife
ki. Wani kwayan mutum guda daya da nake matukar kauna da girmamawa.
Alhaji da kan sa ya fi dacewa ya gaya miki inda take, ba sai kin bi ta
karkashin kasa kin sha wahala ba
Amani ta yi ajiyar zuciya tana jin wani irin relief na zagayeta a zuciyar ta,
yau Mukhy kamar ba shi ba, yana magana ne ta hanyar bata dukkan attention din sa da
concern as a brother, duk da ba kallon ta yake ba wayar sa ya ke dannawa a duka
maganar da yake yi, amma kuma ya dauki zancen yanzu da muhimmanci, ba don komai ba
sai don ya tuno tasa UMMAMIn. Yadda yake son Ummami da yadda yake son zama kusa da
ita bai samu ba, ba don komai ba sai dalilin norms, culture and traditions irin na
gidan su. Ya yarda rashin kulawar ta a tare da shi ne duk yayi mujazar matsalolin
sa a rayuwa da a yau suka saka shi garanranba a duniya. Amani na bukatar tallafin
uwa da gaske. Musamman a kan dabiun ta da tarbiyyar ta, kai har addinin ta ma yana
bukatar gyara, in yayi duba da irin dressing din da take fita da shi da rashin
kunya ga na gaba da irin tabarar data ke yi wa mahaifin ta.
Amani ta ce I wish Daddy din zai saurare ni a kan damuwa ta irin yadda ka
saurare ni yanzu, to ba zai saurare ni ba, ban san abinda ya raba su ba amma ko
zancen ta baya so na yi masa, ya dauki gaba mai tsanani da mahaifiya ta yana fadin
muddin na zabi zuwa gare ta to shikuma zai sallama mata ni ne.
Ta share hawayen ta tace and I love my Daddy more than everybody, saboda da
shi kadai na taso, da kaunar sa gare ni na budi ido. Ban san kowa sama da shi ba ko
yan uwan mu na Faskari sama-sama na san wasu daga cikin su, bani da wa bani da
kanwa.
Cikin tausayi Mukhtar yace me yasa ba zaki neme su ba? Dangi da kike gani suna
da matukar muhimmanci a rayuwar mutum, musamman ke da kike mace, daya tal a wurin
iyayen ki, babu dan uwa babu yar uwa, it is your duty ki nemi dukkan su ki gyara
gurbin rashin zumuncin dake tsakanin ku don hakika kina bukatar su, amma karkashin
yardar mahaifin ki, dont ever try to hide anything from him no matter how bitter,
ba abunda lallashi da ban baki ga iyaye bazai sa su yi maka ba.
Jikin Amani yayi sanyi kadan, don ta sani bata lallashin Baban ta sam kullum
sai rigima da rikici in tana son ya yi mata abu dole ya yi, a kan zuwa gun maman ta
ne kawai da korar Mukhy daga gareshi kawai ya taba turje mata, tace cikin murya mai
ban tausayi,
ka ce zaka nemo min Mama na? Mukhtar ya ji wani iri a jikin sa da yadda tayi
maganar murya na shaking, ya bude mata kofar yace cikin basarwa idan na lallashi
Alhaji ya yarda ki je din, ni da kai na zan nemo ta, zan kuma kai ki duk inda take.
Amani ta fita tana dan murmushi, a ran ta tana fadin ashe dai yana da dan kirki
ko yaya ne, ga taushin murya, ga jan class, fuskar ce dai bata taba canzawa daga
yanayin ta na rashin annuri da bacin rai. Tamkar wanda kullum ake yi wa mummunar
bushara ko ake yankan naman jikin sa.
Bai tsaya ta gama bacewa ba ya ja motar sa ya nufi airport don cika daya
umarnin na Alhaji. Wato dauko matar sa.
Ya dauko Hajiya Rabi suka kamo hanyar gida, a hanya tana ta mitar an bar ta a
shanye a filin jirgi, baa zo daukar ta da wuri ba, mota ba tasa ba amma ya tafi
yawon banza da ita yana kwambo a cikin gari gurin yammata, idan yana ikon sa da jin
kan sa ya dinga tsayawa iya kan Alhajin da ya kawo shi ya kuma daure masa gindi
yana baza iko a gidan mutane, kada ya kuskura ya shiga gonar ta. Ita warki ce
daidai kugun kowa yanzun nan zata yi maganin mutum, ko Amani bata isa ta shanyata
ba balle shi wani banza a banza.
Mukhtar ya sunkuyar da kai yana jin ciwo a cikin ran sa, yau wata wadda bata
ko kai matsayin mai gugar takalmin sa ba ke zagin sa haka, wai kwambo! Duk ba komi
ya janyo masa ba sai zabar barin gida da independent life, an ce kuma a kowanne
neman halal akwai challenges, ya cigaba da tuki bai ce mata komai ba.
Ba tun yau ba ba sa ga maciji da Hajiya Rabi, ta fannin ta ba don komai bane
sai don son da ta lura Alhaji na masa. Daga Amani sai shi a wadanda bata so ta bude
ido ta gani a gidan nan, amma fa bata taba nuna hakan a gaban Alhaji ba. Kullum
nuna masa take tana kula da Amani irin kulawar da uwa take yi wa dan ta, tana kuma
son wannan yaro nasa mai hankali da amana da kullum yake yabo a gaban kowa.
Shi kuwa Mukhtar ya san wacece Haj. Rabi sanin da ko Alhaji bai yi mata ba,
shiyasa kawai ya ji baya son matar, wato ya san tana dan taba yawon barbada a waje
don ba sau daya ba ba sau biyu ba ya taba ganin ta a hotels daban daban tare da
wani mutum. Kuma har kofar gidan mutumin ya sha kawo ta. Duk da ba zai ce ga
hakikanin abinda suke yi tare ba jikin sa yana bashi tarayyar banza ce don Alhaji
yana da ciwon suga mai hana lafiyar auratayya.
Yana ajiye ta ya juya ya koma Company, akwai muhimmin aikin da zai yi wa Alhaji
amma tun shigar sa office din sa sai ya kasa zaune ya kasa tsaye.
Mukhtar Diffa, ya hau safah da marwah, hannanyen sa biyu zube cikin aljihun
farar shaddar da ke jikin sa. Ya rasa abinda ke tsaye a wuyan sa ya ki wucewa. Ya
rasa meye ya tsaya masa a rai. Sai da yayi tsam da ran sa ya fafimci ba komai bane
kukan Amani yake tunawa da shagwabar ta, da fyatar hanci cikin yanayin sakalcin ta.
Sai ya ji wasu sassa na jikin sa suna respoding. Zuciyar sa na vibrating. Ya
tuna matsananciyar damuwar da ke kwance kan kyakkyawar fuskar ta a kan son ganin
mahaifiyar ta, sai ta kwadaita masa son ganin tasa Ummamin shima, kwarai ya gane da
gaske take son ganin Maman nata, wasu abubuwan data yi a yau sun tsaya masa a rai,
sun kasa bacewa, musamman kukan shagwabar nan nata is arousing something in him
komai dakewar sa don bai taba ganin wanda kuka ya yiwa kyau irin Amani ba.
Tsaki yayi cikin jin matsanancin mamakin kan sa, ya dauki kiran Alhaji da ya
shigo masa a daidai lokacin. Ya ce Mukhy kana ina ne? Ina office Alhaji ya fada a
kasalance. Alhaji ya ce to in ka kammala ka zo zamu yi wata muhimmiyar shawara. Kai
bari kawai in gaya maka. Haka kawai ina zaune wani tunani ya zo min, ina son
tsayawa takarar gwamnan jihar Katsina.

Mukhtar ya yi azamar rufe baki sannan ya bude, yana mai jinjina hadamar duniya
irin ta uban gidan sa, me Alhaji yake nema kuma a siyasa da rayuwar sa bakidaya? A
tunanin sa duk abinda dan adam ke nema a duniya Alhaji Usman ya gama samun sa,
kamata yayi ya maida hankali ga kula da tarin dukiyar sa da neman lahira da aurar
da wannan gansamemiyar sakaltacciyar diyar tasa, ba neman wani mukamin siyasa ba a
yanzu, wand aba lallai yayi nasara ba, a fili ya ce Alhaji bari in zo kawai, wannan
ba maganar waya bace.
Yana tafe a hanya yana tunanin ta hanyar da zai bi ya lallashi Alhaji kada ya
tsaya takarar nan, ba don komai ba sai don ya san mawuyaci ne alummar Katsina su
zabe shi yanzu, don duk wani mukami da ya rike a baya bisa magudi ake bashi ba don
alummah na so ba, sai don kasancewar yana da iyaye a babbar jamiyyah masu karfi a
gindin murhun, jamaa basa son Alhaji Faskari ne saboda kankamon sa, da rashin jan
talakawa a jiki sai ka ce ba dan siyasa ba. Wasu yan jaridar ma kan ce, HON. USMAN
FASKARI; dan siyasar da ya rasa dukkan attributes da qualities na yan siyasa amma
yana da saa a siyasa.
Mukhy na tunanin karshen ta ya salwantar da dukiyar kamfanin sa a banza, wajen
kamfen, kuma ya zo bai ci ba. Mukamin Sanata daban na gwamna daban. Mukamin
gwamnatin jiha tabbas sai da soyayyar talakawa.
A sanin sa ko Zakkah Alhaji baya iya badawa, har sai bayan zuwan sa gare shi,
shi Mukhtar din, da ya tsaya tsayin daka da lallashi da nasiha a kan Alhajin, bisa
dole ya sa shi ya dinga fidda zakka don tsaftace dukiyar sa.
Sau tari, Mukhy kamar shine Ogan Alhaji subordinate, da wuya ya fadi abu
Alhaji ya tsallake, don yayi amanna ba zai cuce shi ba, in Mukhy yayi magana akan
abu, Alhaji baya iya tsallakewa saboda son da yake masa da yardarm da ya yi masa.
Sanda ya iso gida Alhaji na tare da baki. Ya yi sallama ya shiga falon, Alhaji
ya bashi iznin zama, Mukhtar ya gaida hamshakin mutumin dake tare da Alhaji, cikin
ladabi y ace da Alhajin yace zan jira a karamin falo kafin ku gama Allhaji no
Mukhtar, zo zauna, gara a yi shawarar nan tare da kai, you are part of me, samu
wuri ka zauna.
Mukhtar ya zauna bisa kilishi can gefen kafar Alhaji. Alhaji da bakon sa suna
kan kujera, Alhaji yace Mukhy, wannan da kake gani shine aminina Alhaji Sadisu
Talle, shugaban sabuwar jamiyyar data take tamu yanzu a farin jini wato PRC (Public
Relation Congress) da ake wa lakabi da SAWUN GIWA. (ya take na Rakumi). Mun yi
shawara da shi zan bar AC in koma PRC don AC bazasu yarda su bani takara ba. Sun
riga sun tsayar cewa wannan karon yaro matashi mai jini a jika zasu baiwa takara.
Suna cikin wannan maganar kafin Mukhtar ya furta komai Amani ta sauko daga
upstairs da zummar wucewa kitchen (madafi), yunwa take ji, ga mai aikin ta Rakiya
ta je kasuwa, sai idanun Alhaji Sadi suka sauka akan kyakkyawa Amani.
Babu wanda ta gaisar a cikin su ta wuce zuwa kofar da zata kaita kicin, shi kan
sa Alhajin yau sai da yaji kunyar wannan rashin tarbiyya ta Amani. Sabida matsayin
Alhaji Sadi a wurin sa a ce yar sa ta wuce bata gaida shi ba, shi dama Mukhy baya
layin ta. Data damo abinda zata sha wato quaker oat da madarar ruwa ta peak tazo
zata wuce ta koma sama batare da tace musu uffan ba. Alhaji Usman ya yi jan wuya
yace.
Shin Tafisu baki ga Alhaji Sadi Talle bane zaki wuce baki gaida shi ba? Ta
zumburi baki, kafin ta ce da Alhaji Sadi din ina yini? Ba tare da ta juyo ko ta
durkusa ba, ko jira ya amsa bata yi ba tayi wucewar ta sama.
Alhaji Sadi ya shiga yage baki duk sai ya dabarbarce ya rasa nutsuwar sa, sai
mutsu-mutsu da baki yake yi ya kuma rasa abin cewa tun saukowar Amani falon ta tafi
da imanin sa, yana tambayar kan sa ina Alhaji Usman ya samo wannan kyakkyawar diya
haka? Babu kama ko ta farce shi da ita, ko adopting din ta yayi? Ya rasa yadda zai
yi ya tambaya sabida Mukhy da ke zaune ya tsare shi da fusatattun idanun sa don ya
gane canzawar sa da rudewar sa tun saukowar Amani. Shi Mukhtar takaici da haushin
yadda dattijon ya kwalalo ido da baki yana bin Amani da wani mayataccen kallo har
da hadiyar miyau yasa ya mike. Alhaji yace ya zaka tafi Mukhy bamu gama shawara ba?
Yace Alhaji ban yi sallah ba ina zuwa. Nan kuwa ko zancen takarar Alhaji baya son
ji, balle ya bar jamiyyar sa ta amana wato AC da ya dade a cikin ta ana damawa da
shi. Kai shi bai ma yarda Alhaji Sadisu zai sa a bashi takara a PRC ba duk da
matsayin sa na shugaban jamiyya, don ya san bashi da farin jini yafi yarda da cewa
kudin sa zai ci ya wofintar da shi. Duk da cewa ba yau suke tare ba duk da
banbancin jamiyya dake tsakanin su. Abota ce tsakanin su tun ta kuruciya.
Ai Alhaji Sadi kamar jira yake Mukhtar ya bar wurin ya muskuta cikin kujerar
sa bakin sa nata motsi yace shin Hon. Usman wannan kyakkyawar diya taka ce ko yar
riko ce? Hon yayi dariya yace Amani ce fa, Amani Faskari, ita kenan yar daya jallin
jal dana mallaka duniya da lahira.
Sai a lokacin Alhaji Sadi ya hau tuna komai na Alhaji Usman yana bearing
wannan sunan ne wato Amani Faskari, bai taba sanin sunan yar sa ne Amani din ba,
don bai taba jin irin wannan sunan ba.
Alhaji Sadisu ya shafa gemun sa da sajen sa yana murmushi yace ai kawai Hon. Ka
ce ta zo gidan sauki tuwo na mai na, abu nawa maganin a kwabe ni. Ka bani auren ta
ni kuma na maka alkawarin kujerar gwamnatin Katsina sau biyu, ko ana ha maza ha
mata sai ka yi.
Hon. Usman a matsayin sa na uban da bai taba jin wani ya tare shi yace yana son
Amani ba, saboda kowa cewa yake tafi karfin sa saboda izzar ta da irin rainon da
yayi mata, sai ya ji dadin maganar kwarai, ya ga cewa tabbas Alhaji Sadi zai iya da
Amani ba tare da yace tafi karfin sa ba shi, tunda in dukiya da mukamin siyasa ne
da take takama yana da su ne shima Sadi a cikin su yake dumu-dumu har ya dara shi
komai yanzu, in ka dauke yawan shekarun sa da suka zarta nasa, da furfurar data
soma samun muhalli tsilli-tsilli a saman kansa, sai ya ga cewa zai iya bashi auren
Amani muddin zai taimaka masa ya zama gwamnan jihar su.
Babban burin sa na yanzu kenan wato zama gwamnan jihar Katsina.
Alhaji Sadi bai bar gidan ba sai da suka kulla yarjejeniya a rubuce da shi da
Alhaji Usman cewa zai tsaya masa a matsayin sa na shugaban jamiyyar PRC a bashi
takarar kujerar gwamna shi kuma kafin nan ya aura masa yar sa Amani.
Ya so a yi maganar nan a gaban Mukhy, amma Mukhtar din tunda ya zame da sunan
zai je yayi sallah ya ki dawowa.
Haka kawai ya kasa jure mayataccen kallon da Alhaji Sadi ke bin Amani da shi,
kuma in zaa kashe shi bazai ce ga dalili ba. Shi kawai yana ganin ba girman Alhajin
bane.
Basu kara haduwa da Alhaji ba sai washegari. Lokacin da Alhaji ya gaya masa
yarjejeniyar da suka yi da Alh. Sadi washegari suna hanyar zuwa ofishin Alhajin,
Mukhtar suman zaune yayi.
Ya yarda neman Mulki yana fidda wasu dattijan a hankalin su.
Ina Amani yar shekaru 20 ina tsoho dan shekaru 65 banda kwadayin Mulki da neman
sa ido rufe irin na Honourable Usman? Kai bama wannan ba wani dunkulallen abu ne ya
zo ya tokare shi a makogaron sa ya kasa cewa Alhajin sa komai, sai kawai ya maida
hankali ga tukin da yake yi zuciyar sa na wani irin bugawa fat-fat.
Alhaji Usman yace baka ce komai ba Mukhy, ko shawarar tawa bata yi bane? Na san
ka da tsinkaye, amma nima ina da amfanin da zan samu a cikin auren, ai wato komai
mutum zai yi a rayuwa yanzu ya fara hangawa ya auna ya gano ribar da zai samu a
cikin sa.
Kaga in ya auri Amani zai taimakamin na zama gwamna, zai tsaya min kan duk mai
son taka ni a jamiyya, abinda na tsara shine sai in nada ka mataimaki na amma ko
shi ban gayawa hakan ba, ka nemo mata kayi aure kai ma mu tara dukiya iyakar
tarawa, mu Mulki Katsina tare, mu ci duniyar mu da tsinke, amma na yi rantsuwa ba
mijin da zai ci min dukiyar Amani, don ita na tara mawa, komai nata zai koma
karkashin kulawar ka da amanar ka ko da ta auri Alhaji Sadi.
Hatta kayan daki ka ga ba sai mun yi mata ba gidan Alhaji Sadi duniya ne; babu
abinda babu cikin sa. Kudin komai dana tanada don auren ta sai a kara jari dasu a
boutique din ta ka ga dadin auren mai akwai kenan.
Gashi babu mace yanzu tare da shi tun rasuwar uwar yaran sa bai kara aure ba,
yaran bakwai duk sun manyanta, biyar daga ciki sun yi aure. Don haka Amani bazata
yi masa rainon yara ba. Ya ka gani?
Mukhtar Diffa dai ya zama mutum-mutumi a zaune. Tuki kawai yake ya rasa amsar
da zai baiwa Alhaji. Bai san cewa ya bar hanyar da zata kai su company ba ya dauki
wata daban da bai san inda zata kai su ba, har sai da Alhajin ya ankarar da shi,
sannan ya koma da baya ya dauki hanya daidai.
Da Alhajin ya takura sai ya ji ta bakin sa sai ya ce ni me zan ce Alhaji? Banda
Allah yayi zabi mafi alkhairi?. Tunda kun riga kun rubuta yarjejeniyar a rubuce ai
bani da say. Kome zan ce is too late.
Sai dai naso ace Amani din da yardar ta aka zartar da komai. Saboda ina tsoron
maka halin yaran zamani, kada ta baka kunya Alhaji. Yaran yau baa sha musu alwashi
irin wannan.
Shima sai a lokacin yayi wannan tunanin na cewa ba lallai Amani ta yarda ta
auri Alhaji Sadi ba in aka yi laakari da yawan shekarun sa.
A sanin da yayi wa Amani bata taba nuna tana shaawar a yi mata aure ba, tafi
shaawar cigaba da rayuwar ta cikin hutu a gidan su, cigaba da tabara da wadaka da
dukiyar mahaifin ta, ta hanyar yin kwalliya ta kece raini da sanya sitturu masu
karshen tsada da hawa duk kalar motar data ke so wato yawan canza mota new mdel duk
shekara, burin ta kenan.
Rana daya azo a ce an bada auren ta ga tsoho abokin baban ta don cimma wani
kuduri na siyasa, abin zai zo mata banbarakwai, shima ya san ya daukowa kan sa Dala
babu gammo. Dama Amanin ga ta nan ga kamar ta wajen hankali da tarbiyya.
Har suka iso ofishin Alhajin babu wanda ya kara magana a cikin su, Alhaji na
cikin taraddadin yadda zai fuskanci Amani da maganar. Mukhtar da ke tuki na kokawa
da numfashin sa dake faman kai kawo a tsakanin kirji da zuciyar sa.
Kwana biyu a tsakani Alhaji na ta nan nan da Amani, ya rasa ta inda zai bullo
mata da zancen Alhaji Sadi, ya tuna lokacin canza motar ta yayi bari ya nemo motar
da take mafarki in yaso yace mata Alhaji Sadi ne ya kawo mata a matsayin goron na
gani ina so, ga Alhaji Sadin ya takura yana so ya bashi izni ya fara zuwa zance. Ya
san in bay a yi da gake ba zai sha kunya idan Alhaji Sadi ya tare ta da zancen
kafin shi. Don haka yau dai yayi kundumbala ya kira Mukhtar falon sa.
Suka zauna shi da Alhajin cikin dakin sirrin Alhaji, Alhaji Usman yace Mukhtar
na yi abinda ya zo ya dame ni, har yanzu na kasa gaya mata zancen nan, jiya ta zo
min da admission na son tafiya karatu a jamiar Queen Mary, ta ce tana so in yi mata
iznin tafiya karatun digiri na biyu, ga Alhaji Sadi na maganar aure nan kurkusa, so
yake in bashi izni ya fara zuwa ganin ta na rasa ta inda zan bullo mata.
Mukhtar kamar yayi dariya ya dai gintse ya ce Alhaji Amani yar ka ce, me yasa
kake shayin ta? Hakan bai dace ba ko kadan Alhaji yace rikicin ta nake tsoro, baka
san ta bane, wanizubin kamar sarka take fadi ki rikice ta fannin rikici, sau da
dama in ta rikice min kamar mahaifiyar ta take komawa, bana sanin ta ina zan shawo
kan ta. Mukhtar na so ya ce ita siyasar dole ce da zaa saida farin cikin ya domin
ta? A fili kuma yace Alhaji kamata yayi ka kirawo ta ka zaunar da ita ka gaya mata
hujjojin ka kamar yadda ka gaya mini, na tabbata bayan rikicin, zata zo ta fahimta
tunda dai kana son takarar nan, in ya so daga baya in ta gama rikicin zata yi
biyayya, zan taya ka tausar ta.
Da wannan shawarar ta Mukhtar ya dogara, washegari ya kira Amani, ya kawo
takardar sabuwar mota da mukullin ta ya bata, ya ce Tafisu na ji kina korafin injin
motar ki yana kara, nace bari kawai a sake wata, kafin ki zama Amarya. Amani ta
karbe mukulli da murna tace My Daddy like no other, godiya nake, kamar ka san na
dade ina son Lamborghini, Allah ya bar mini kai Baba na yace ai yau kyautar ba daga
ni ta fito ba, daga Alhaji Sadi ne, ai kin san shi ko? Wannan abokin nawa da yazo
satin da ya wuce?
Amani ta ce ni kuwa na san shi, wannan mai katon cikin kamar kwaryar kindirmo,
da idanu kamar na soyayyar gyada, yana kallon mutane tamkar mage ta ga bera.
Alhaji ya kama baki yace Amani ban san ki da cin zarafin na gaba ba, shi da ya gan
ki ya yaba da ke ya nemi auren ki cikin girma da daraja a hannu na da alkawarin zai
tsaya min sai inda karfin sa ya kare in samu takara. Idan na samu kujerar ai ke
zaki fi kowa morewa da jin dadi.
Amani tayi sakale! Tana kallon bakin Alhaji tana cewa a ranta ko Daddy ya fara
shaye-shaye ne? A fili tace Daddy ban gane komai cikin maganar ka ba, wace Amanin?
Ni? Kuma takarar me ka ke magana? Alhaji ya sassauta murya cikin lallashi ya shiga
yi mata bayanin yarjejeniyar su yadda zata fahimta. Sai Amani ta sunkuya ta rike
ciki ta daddage ta hau zuba dariya tana

Please Login or Register in order to submit comment