You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya rantsewa cewa zuciyar sa ta dade tana son AMANI, ita kuma ba ta son sa
da alaqar aminci dake tsakanin sa da mahaifin ta, wanda ya san shi ya fi komai sayo
masa bakin jini, kishi da tsana a idanun ta.
Alhaji ya soma kokarin kiran Amani bayan sun rabu da Mukhtar a waya.
Tana kallon kiran Daddy nata shigo mata amma ta kai zuciya nesa ta ki dagawa
har ta katse, ya sake kira. Amani sai hada kaya ta ke tana kuka, amma ba ta amsa
ba.
Alhaji ya kira Malam Tajuddeen ya ce masa a rufe gate kada a bar Amani ta je ko
ina in ba tare da su ba.
Daidai lokacin Mukhtar ya shigo gidan, misalin karfe bakwai na safe, suka gaisa
da Malam Tajuddeen da sauran maaikatan gidan, ya wuce maadanar motoci ya fiddo
wadda za su tafi a cikin ta ya zuba mata mai da kan sa, sannan ya ce da Ali ya
wanke motar amma wajen ta ba cikin ta ba, sannan ya karasa sassan Alhajin.
Da sallama ya shiga falon, Alhaji ya amsa ya ce, Yanzu nake so in kira ka ka je
ka turo min AMANI, tana can side dinta a saman bene. Na kira na kira ta ki dagawa.
Mukhtar ya ce, Alhaji ka fara yin wanka tukunna, ka karya kumallo, ka kwantar
da hankalin ka, everything will be alright, in sha Allahu.
Ya taimaka wa Alhaji ya yi wanka, ya fiddo masa manyan kaya ya saka, ya tambayi
Alhaji ina Hajiya Rabi don bai ga ta kawo breakfast ba har yanzu.
Alhaji ya ce, Na ba ta tikitin ta daren jiya ta tafi, tana barazanar danne ni
da filo in ban sake ta ba, daga kan ta na rufe aure in sha Allahu, zan zauna cikin
kujerar nakasa in nemi lahira ta, har zuwa ranar da waadi zai cika, kai dai ka rike
min Amani da gaskiya, ka bunkasa mata dukiyar ta har Allah ya baku zurria.
Dan ku ya girma ya gaje ka kan shaanin kasuwancin mu. Idan na samu wannan na
gama samun duk wani farin cikin rayuwa.
A wannan lokacin Mukhtar ya jona kettle ya hada wa Alhaji coffee mai zafi ya
bashi yana sha, ya yi waya kitchen ya ce Rakiya ta shiryo karin kumallo ta kawo wa
Alhaji, kuma ta kai wa Amani. Ta lallashe ta ta tabbatar ta ci ko kadan ne, don
fita za su yi.
Alhaji na kurbar coffee dinsa yana jin abin da Mukhtar ke ce wa Rakiya, sai ya
ji wani irin dadi ya lullube ran sa. At least Mukhtar bai ba shi matsalar da Amani
ta ba shi a kan hukuncin sa ba. Ya tabbatar wa kan sa ko Mukhtar ba ya son Amani,
to fa ba zai wulakanta masa ita ba duk irin halin fitsarar ta, wanda a yau ya yarda
rashin tashi da uwa ne ya janyo mata, ko wata kwakkwarar uwar riko a gare ta. Kuma
duk hakan ya faru ne bisa kuskuren sa da munanan halayen sa.
Tun farko me yasa ya rabo ta da Sahura? Don kada ta sha wahala da rayuwar
kauye. Me yasa bai barta ta rayu a Funtuwa ta samu tarbiyyar data dace a hannun
kanwar sa ba da cikakken ilmin addini wanda zai sa ta san muhimmancin iyaye da
girman da Allah ya yi musu?
Rakiya ta shigo ta kawo musu karin kumallo mai rai da motsi, sinasir ne da
miyar ganye da ta ji naman talo-talo, sai kunun gyada fari sal mai gardi. Mukhtar
ya cikawa Alhaji plate ya tura masa gaban sa yana ta yi masa hirar abubuwan da ke
faruwa a company kwana biyunnan don dai ya samu ya dauke damuwar da ke kwance kan
fuskar Alhajin. Amma sai ya ji Alhaji ya ce,
Na yi maka izinin hawa sama, har dakin TAFISU. Ka je ka zo min da ita nan cikin
lallashi mu ci abincin nan tare da ita.
Mukhtar ya rasa yadda zai yi da wannan umarni mai nauyi a gare shi na ubangidan
sa, amma ganin irin damuwar da ke kwance a fuskar Alhajin sai ya ce.
To Alhaji, amma idan ta ki fa? Zan dauko ta a ka ne? Ka san fa babu shiri irin
wannan tsakanina da ita.
Alhaji ya ce, Da irin haka ne za ku saba da juna. Har watarana ku kaunaci juna.
Yanzu Amani matsayin matar ka ta ke, shaidu kawai ya rage su shaida.
Mukhtar duk sai ya ji maganar ta Alhaji wani irin banbarakwai wai namiji da
suna Hajara.
Alhaji ya kira Rakiya a waya ya ce ta zo ta raka Mukhtar sassan Amani.

Rakiya na gaba, Mukhtar na bayanta har dakin Amani. Ta kwankwasa kamar yadda ta
saba yi wa Amani.
Amani na can abu goma da ashirin ya ishe ta don har zuwa lokacin da ta tura wa
Mr. Balogun kudi da awanni biyu babu adireshi babu lambar waya na Maman ta da ya
turo mata.
Ta yi ta gwada kiran wayar sa tun tana shiga yana kin dagawa har ta daina shiga
kwata-kwata. Ko dai an daina amfani da layin, ko an kashe wayar gabadaya. Sai ta
dora hannuwa bibbiyu a kanta tana son rusa ihu ko ta samu saidah.
Sai ga Rakiya ta murda kofar ta shigo, jin ta yi ta kwankwasawar Amani ba ta ba
ta izinin shiga kamar yadda ta saba ba, sai kawai ta shigo kan ta tsaye don ta ga
ko lafiya.
Amani ta zuba wa Rakiya idanun ta da suka yi jazir da bacin rai, tana kallon ta
tamkar ita ce Balogun.
Rakiya ta karyar da kai gefe ta ce, Afuwan uwardaki na, Alhaji Mukhtar aka ce
na rako wurin ki. Alhaji da kan sa ya ce in rako shi.
Kafin Rakiya ra rufe baki, Amani ta samu zarafin ci mata mutunci, ko kunduma
mata ashar, Mukhtar din ya shigo dakin kan sa tsaye. Daga jikin kofa ya tsaya
hannuwan sa harde da kirjin sa yana kallon Amani da yadda a cikin dare guda duk ta
zabure ta fice a hayyacin ta.
Rakiya ta juya ta fita har da rufo kofar dakin, tana fadin a fito lafiya
Alhaji.
Mukhtar kallon ta kawai yake daga sama har kasa, wani irin kallo da bai taba yi
mata ba. Duk da cewa kayan barci ne a jikin ta gashin kan ta babu rufi, gashin duk
ya tarwatse duk ya yi buyaya da shi kamar sabon kamun hauka, shi a idon sa gani ya
yi kamar an kara mata kyau da kwarjini, duk da idanun ta sun jeme sun yi zuru-zuru
din. Kallon-kallo aka tsaya ana yi tsakanin Mukhy da Amani, kallon da su duka suka
kasa fassara yanayin sa yayin da Mukhtar ya ji wani abu mai kama da tausayi ya
darsu a ran sa game da ita, ganin yadda duk ta sauya kamanni da appearance a kwana
daya.
Amma ya riga ya san Amani zuma ce sai da wuta ake iya sarrafa ta. Kamar ba zai
yi magana ba don ya san kiris ta ke jira ta saki tantrum, amma sai ya tuna damuwar
da mahaifin ta ke ciki a kan ta.
Ya tuna rokon da ya yi masa a kan ya lallaso ta ta zo ta karya kumallo tare da
shi sannan su wuce Faskari.
Alhaji yana da hope na cewa, shi kadai zai iya hakuri da tilon yar sa, mai
tarin nakasu a halayya da dabia, shi ya sa ya damka masa ragamar rayuwar ta ta
hanyar da ta fi kowacce muhimmanci ga dan adam, wato aure. Kuma a istikharar da ya
yi daren jiya shi kam bai ji yana kin alamarin nan ba, ya dai san zai sha wahala
iyakar sha a hannun Amani, tunda Allah bai halicci zuciyar ta da kaunar sa ba.
Mukhtar ya nisa, ya kira sunan Amani, ba cikin yanayin da yake mata magana da
shi a baya ba, na nuna halin ko in kula da alamarin ta. Wannan karon akwai kulawa
da dan lallashi acikin sautin sa.
Ya ce, Ki sani cewa komai ya yi zafi ga bawa bai fi karfin Ubangiji ba. Iyaye
suna gaba da komai a rayuwar dan Adam. Mahaifin ki ba yaron ki ba ne, ba kuma dan
ki ba ne da za ki dinga yi masa duk abin da ki ka ga dama ba.
Ya kira ki kin ki amsa kiran sa, kin bar shi a damuwa, anya Amani kina son
gamawa da duniya lafiya?
A hakan kuma ki ke so Allah ya ji tausayin ki ya hada ki da mahaifiyar taki?
Alhalin shi din da ya maye miki gurbin ta ba ki tsaya kin kyautata masa yadda yake
kyautata miki ba?
Me ki ka dauki kan ki Amani da ki ka zabi yin fito-na-fito da mahaifin ki? Ni
da bai haifa ba na zabi in masa biyayya a kan umarnin sa, don na san ba zai ba ni
matar da za ta cutar da ni ba. Sannan yana cikin hali na rashin lafiya yanzu, wanda
kyautatawa da tausasawa kadai yake bukata daga gare mu.
Yau in aka ce babu Alhaji sai kin fi kowa zama abun tausayi, ba ki ga tsuntsu
ba ki ga tarko, baki rabauta daga biyayyar uba ba, sannan uwar ma ba za ki san inda
za ki gan ta ba.
Na zaunar da ke na ce ki bi shi a hankali, ki bar komai a hannu na, amma ki ka
yi kan gaban kan ki saboda ke ba ki da mafadi kuma ba ki yarda kina da na gaba da
ke ba.
Zan iya rantsuwa da Allah kan cewa yan damfara ki ka tura wa kudi, bayan na
gaya miki kada ki tura, gaggawar ta mece ce tunda na ce ni da kaina na yi alkawarin
kai ki ga mahaifiyar ki amma karkashin umarni da amincewar mahaifin ki?
Yanzu ina adireshin da ki ka sayo miliyan biyar sai ki ba ni in gani.

Kuka ya kubucewa Amani, ba kukan shagwaba ta ke yi ba yau, kuka ne na kubucewar
azanci da tausayin kai. In ta ce maganganun Mukhtar ba su yi tasiri a zuciyar ta ba
ta san ta yi karya. Da gaske Daddy ya wuce komai a gare ta, kuma bai cancanci
reactions din da ta ke yi mishi ba, amma zabin da ya yi mata ne ba za ta taba karba
ba, domin ya kaskantata, ya sayar da ajin ta ya zubar mata da ego din ta, muddin
Mukhtar zai bai wa auren ta.
Daga nan har kotun koli za ta je don neman hakkin ta a kan hakan, bazata taba
yarda tayi auren kaskanci ba, auren yaron Alhaji mara asali, mai halayen da ta ki
jini, wato musamman girman kai, da kin yarda a taka shi, ita kuma ta saba taka kowa
da ke kasan ta, tunda ta yi kokarin riskar mahaifiyar ta don ta samu mafaka a gun
ta abun ya ci tura.
Tana ta kuka tana fyace hanci da share ido da gyalen ta, Mukhtar ya ce, Taso ki
biyo ni, mahaifin ki na son ganin ki, in kuma kin ki tashi ko a ka ne zan dauke ki
in kai masa ke, na rantse.
A yadda ta ga idanun sa sun rikide cikin bacin rai ta san sarai zai iya aikata
abin da ya furta, sai kawai ta mike, ta na so ta ce ya ba ta wuri ta canza kaya,
amma ya kasa ya tsare a kofar dakin yana muzurai na ko ta wuce ko ya ciccibe ta.
To ka je zan canza kaya. Ta fada a turbune, fuskar kamar wani kauye wai shi
Durbunde saboda turbunewa. Mukhtar sai ya ga akwai bukatar ta canza kayan, bai
kamata ta tafi har Faskari da kayan barci ba, sai ya juya yana fadin, Na ba ki five
minutes, in ban gan ki a falon Alhaji ba da jakar fita unguwa da trolley din
matafiya da kayan ki da zasu yi miki a kalla kwana bakwai a ciki zan dawo.
Don tafiyar tamu ba mu san har yaushe za ta kai mu ba, tunda neman sulhu da
gyara zumunci ne zai kai mu.
Ya fice a dakin ya bar mata daddaddan turaren sa na sirnanawa a kofofin hancin
ta.
Tana kuka tana komai ta canza kayan jikin ta, ta sanya doguwar riga sannan ta
yi maza ta yayibo mayafi ta jefa kaya kala uku da man shafawa da deo spray a
trolley da yan sauran abubuwan bukatar ta. A gurguje ta rufo dakin ta fito kada ya
kara dawo mata daki, don ko turaren sa ba ta son ji, balle ganin cunkusasshiyar
fuskar sa mara annuri da rashin walwala.
Sai da ya taimaka wa Alhaji ya gama kintsawa ya debar masa duk abin da zai iya
bukata har nan da kwanaki bakwai kama daga magungunan sa da kayan sanyawa ya kai
komai mota. Ya dawo kenan ya tadda ita a falon na Alhaji, da jakar tafiya a gaban
ta. Alhaji na ta faman lallashin ta kamar shi ne yar ita uban, yana gaya mata duk
abin da ta ga ya yi mata soyayya ce, idan kuma har ta zabi ta bijirewa umarnin sa
ta hanyar tozarta shi a idon Mukhtar, to kuwa zai yi hakuri da duk son da yake mata
ya sallama ta, zai kwace komai da ya mallaka mata ya kai ta wajen mahaifiyar tata
su karata.
Mukhtar ya yi kamar bai ji me Alhaji ke fada ba a karshe, ya ce, Alhaji komai
ya kammala, mota an mata full tank an kuma wanke ta sai tafiya ya rage.
Allah ya yi maka albarka Mukhtar, dauki kayan ta ka sa mata a mota, jakar
hannun ma karba mata.
Yar murmusawa ya yi, a ran sa yana fadin, Alhaji ke kara lalata yarinyar nan,
ya karba mata jakar hannunta wato ga mijin Hajiyar Faskari ko? Ko Alhaji ba ya
karba wa briefcase in za su fita balle wannan fitsararriyar.
Tana jira ya daukar mata har jakar hannu kamar yadda Alhaji ya yi masa umarni,
sai kawai ta ga ya dauki trolley dinta da hannu daya ya bar falon. Ita ta kai
zuciya nesa ta dauki jakar ta rataya sannan ta turo Alhaji a kan keken sa.
Ita da Mukhtar din suka yi kici-kicin saka Alhaji a mota, ya nade keken nasa ya
saka a boot din motar. Gidan baya ta shiga ta zauna gefen Alhaji don tana ganin ta
fi karfin ta jera kafada da Mukhtar a gaban mota, alhalin yana matsayin yaron
Alhaji ko kuwa ta ce direban ta. Zuciyar ta ba za ta taba ba shi wani matsayi bayan
wadannan ba.
Alhaji zai yi korafin muhallin da ta zaba don zama sai gani ya yi Mukhtar ya
tada motar, ko a jikin sa, shima baya so ya hada kafada da ita, ko ba komai ta kula
da Alhaji a bayan motar wanda suka yi masa kujera ta musamman suka sanya mishi belt
sosai.
Kamar ya san a karkashin zuciyar ta ta so ya yi magana ta gaya masa mara dadi,
ta gaya masa har abada shi yaron gidan su ne, kada wani zancen aure da Alhaji ya
furta ya rude shi. Sai aka yi saa bai tanka mata ba, ya ja mota cikin tukin sa na
nutsuwa, na kwarewa da kamala suka yi reverse, wanda ba haka ta so ba.
Mukhtar ya sa a ran sa ba zai dinga biye mata ba yanzu kamar da, saboda jiya da
ya yi wa Alhaji b.p ya ga ya hau sosai. In ta rasa wanda za ta yi wa rashin kunyar
dole za ta yi shiru ta bar su su ji da abin da suka fuskanta yanzu, wato gyara
tsakanin Alhaji da yan uwan sa.
Malam Tajuddeen ya bude musu kofa tare da daga musu hannu yana fadin, a sauka
lafiya. Mukhtar ya dan daga masa hannu shima, sannan suka fita gate din gidan.
Sannu a hankali ya hau bisa kwalta, sannan ya soma shimfida gudu da su kamar zai
tashi sama dasu, abin da ya san Amani ba ta so, wato gudu da mota musamman a babban
titi irin wannan, baa cikin gari ba.
**** ***** ****

Suna tafe kan titin da zai shiga garin Faskari Mukhtar ya kunna karatun
Alqurani mai tsarki ya kure a radiyon motar cikin Suratul Baqarah, duk yadda ta ke
so ta yi masa korafin gudun da mota da yake yi da su albarkar wannan karatun da ya
kure sai ta kasa, ta samu kan ta da nutsuwa tana sauraron ayoyin na karshe na
suratul Baqarah da taji sun mata dadi, kasancewar ita bata saba sauraren karatu ba
sai music.
Mukhtar na tafe yana tambayar kan sa shin ko Amani ta taba yin islamiyya? Balle
a je ga batun sauke Alqurani? Ya nisa, umh. A lokaci guda Alhaji na tuhumar kan sa
da ka sa a ran sa da sakaci mai yawa da ya yi a kan tarbiyya da kuma upbringing din
Amani in general. Ya tuna ko hizfi biyar ba ta da shi a kan ta, don tun tana karama
da ya dauki wani bayerabe yake zuwa gida yana koya mata karatun Alqurani, da ta yi
wayo ta kai munzali sai ta nuna ba ta raayin koyarwar malamin. Dole Alhaji ya
sallame shi. Daga wancan lokacin kuma Amani ba ta kara shaawar tahfiz ba, dan wanda
ta samu a gun bayeraben nan da shi ta ke karatun sallah har yau.
Alhaji ya nisa yana fadi cikin ran sa,
na yi kuskure mai yawa a rayuwa ta. Allah ka bani ikon gyarawa kafin ka dauki
rai na. Allah ya sa Mukhtar ya rike min Amani da dukkan nakasun ta, ba tare da ya
goranta mata tarbiyya, ilmin addini da goyon gatan da na yi mata ba.
Yau ga shi ga dukkan alamu Amani na so na kasa lankwasa ta. Wa ya janyo komai?
Alhaji ya kara kudirewa a ran sa sai dai Amani ta mutu, amma sai ya cika
kudirin sa, in yaso ya wanke gawar ta ya fara kaiwa gidan Mukhtar kafin ya
danganata da kushewar ta, amma ba ta da miji insha Allahu sai Mukhtar din sa. Idan
ta bijire masa wannan karon zai ba ta mamaki. (Alhaji ya manta icce tun yana danye
ake tankwara shi).
Daidai lokacin da Mukhtar ya karya kan motar suka hau burjin da zai shigar da
su garin Faskari, Alhaji na ta kallon garin iyayen sa da kakannin sa with
nostalgia, yana kokarin tuna ko yaushe ne last shigowar sa Faskari? In zai iya
tunawa daidai tun lokacin da yake nema kujerar sanatan Katsina ta Tsakiya yana
neman kuriar karamar hukumar tasa. Da ya zo ya dan yarfa musu. Ya tuna lokaci na
karshe da Yaya Idrisu ya kira shi a waya yana gaya masa Kamilu dan sa ya kammala
karatu an turo shi hidimar kasa cikin jihar Katsina ko zai ba shi muhalli ya zauna
a gidan sa yayi hidimar kasan?
Yadda ya balbale shi da fada kamar kanin sa yana fadin ba ya son a zo a cika
masa gida shi bai iya jaye-jayen yayan dangi ba. Ya tuna cewa uwar Kamilun ita ta
shayar masa da Amani, ba don ita ba da bata rayu ba, ko sai da madarar gwangwani.
Yau ga shi ya dawo Faskari babu kafafu sai dai a tura shi a keken guragu, rabin
jiki ba ya aiki, kuma kai tsaye gidan Yayan nasa ya dosa, wato gidan su na gado,
wannan abun kunya da kayan nadama har ina?
Ita dai Amani da ke gefen sa tana danne-danne a waya, sai gani ta yi Daddyn ta
yana hawaye, ya kuma bar su suna ta zuba akan kundukukin sa ba ya ko sharewa wasu
na korar wasu. Idan ya kara tuna cewa uwar Kamilu ita ta shayar masa da Amani, amma
shi ya kasa daukar ko Kamilun ne ya yi yan watanni tare da shi na hidimar kasa duk
irin arzikin da Allah ya yi masa da girman gidajen sa a Katsina. Yailahi! Da wace
fuska zai doshe su yanzu? Da wane azancin harshe zai nemi gafarar su? Ba tare da
sun yi tunanin sai da lafiya ta kare masa ba ne ya neme su? Don in bai manta ba
daga waccan wayar da suka yi da Baba Idrisu har gobe Baba Idrisu bai kara neman sa
ba, ya rike talaucin sa da mutuncin sa, ya rike yayan sa a kauye ko birnin Katsina
ya haramta musu shigowa don ma kada su nemi kanin uban nan nasu da bai san
muhimmancin zumunci da girman zumuncin Allah ba.
Alhaji shi ke nuna wa Mukhtar hanya har kofar gidan iyayen sa, soron gidan duk
ya zube, kana iya hango tsakar gidan da duk abin da ke ciki duk da an kare da
zangarniyar dabino da azara.
A nan ya umarci Mukhy ya yi fakin motar, daga can hanyar masallaci Alhaji ya
hango Yayan sa Malam Idrisu na tahowa, Mukhtar ya fito ya bude but ya fiddo kujerar
Alhaji ya warware ta ya dauko Alhajin daga mota ya sanya shi cikin kujerar. Amani
ta fito tana ta cin magani da yatsine-yatsine, har da zumbure-zumburen baki, ita ta
tura Alhajin zuwa kofar gidan su, yayin da Mukhtar ya tsaya kici-kicin fiddo kayan
su.
Daga nesa Malam Idrisu ya hango su babu bata lokaci kuma ya gane Amani tare da
wani farin balaraben mutum da bai sani ba. Amma dattijon da ke cikin kujerar
wheelchair ko kusa bai kawo cewa kaninsa Usman ba ne.
Amani ta jira rike da hannun kujerar har ya iso, sai a lokacin ya gane dan
uwansa.
Innalillahi wainna ilaihi rajiun. In ji Malam Idi, yana fadin, Me ya same shi?
Me ya faru da shi haka?
Zuciyar yan uwantaka! Tuni ya karbe shi daga hannun Amani, da kan sa ya tura
shi zuwa cikin gida.
Kai Isya je ka kasuwa ka kira Kamilu ya zo ya bude wa baki dakin sa su aje
kayan su.
Yaron da aka kira Isya ya zura da gudu yana waiwayen Mukhtar don ya dauka
bature ne ko wani balarabe, fatar sa ta wanku da boko, ya karya hula damanga a
saman kansa wadda ta dace da launin shaddah getzner lemon green da ke jikinsa, kai
ba za ka ce haihuwar Africa ba ne shi ya fi kalar larabawa.
Uwa, ku ne tafe? Sunan da yake kiran Amani, kasancewar sunan mahaifiyarsu ta
ci, wato Inna Amina mai rasuwa.
Amani ta zumburo baki, kafin ma ta furta wa Yayan uban nata gaisuwa ta alada
sai da ta saki korafi irin na rashin kunyar da ta saba yi wa Alhaji.
Za ka fara ko, daga zuwa na? Kira na da UWA? Shi ya ce min wani TAFISU kai ka
ce min wani UWA, bayan ga suna na mai dadi na yanka.
Dariya Malam Idrisu ya yi don shi a duniya yana son Amani, duk da halin ta
kuwa, ya sa matar sa uwargida Talatu ta yi musu shimfidar tabarma karkashin katuwar
dalbejiya da ke tsakar gidan.
Mukhtar ya gaishe shi cike da girmamawa, ya gaida Baba Talatu, Baba Idi na son
tambayar Amani inda suka samo kyakkyawan mutum haka, shi kuma ba balarabe ba, don
ga hausa ras a bakin shi, amma ya fi damuwa ya ji yadda aka yi dan uwan sa ya koma
rayuwa a wheelchair.
Faduwa ya yi a bandaki, ka san yana da hawan jini, shine ya samu stroke. An
fidda shi asibiti har kaar Faransa Allah bai sa ya mike ba. Amma yanzu a hakan da
sauki sosai, tunda yanzu yana magana ras, yana kuma iya motsa duka hannayen sa.


Please Login or Register in order to submit comment