You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ji dadin shi kadai, ko ya samu duniyar shi kadai ya ji dadin, ba
tare da sun raina dan abinda zai basu ba, to ina tabbatar miki Moukhtar na cikin
su.
Amani ta mike don zancen Mukhtar dinnan wanda ta laqabawa suna bare ka fi dan
gida ya fara isar ta, ya gundure ta. Ta kuma san in ba ta bar wajen ba Daddy ba
gajiya zai yi da bata labarin kirkin Mukhtar ba. Daddy ba zai sa comma ba bazai
saka full stop ba kuma bazai gaji ba. Sai idan baka yi zancen Muktar Diffa a gaban
Hon. Usman Faskari ba. Yanzun nan zaka soma jin nassi-nassi, maudhuI maudhui na
kabakin alheri iri-iri daga bakin Alhajin a kan sa. Ta ce,
Daddy, zancen ka ya shiga ta hagu, ya fita ta dama, ko me zaka ce a kan wannan
yaron ni kam bai yi min ba, na tsani mutum mai iko, mai fadin rai da jiji da kai,
alhalin shi din ba kowan kowa ba.
Ta soma taka stairs don komawa dakin ta kada Daddy ya cigaba da gaya mata
abinda ba shiga kan ta yake yi ba.
Alhaji Usman ya yi murmushi, ko yaushe Amani zata fahimci banbancin human
personality? kowa yadda Allah ya halicce shi ta fuskar personality, gashi har
digiri ta yi a kan International Relation amma har yau ta kasa gane personality na
halittar dan adam baya taba zuwa daya, wanda bai da alaqa da facial expression
nasu, yace zo nan Tafisu, ya zaki tafi baki duba takardun Boutique din ba? Amani ta
ce ba tare da ta tsaya ba Daddy in komai yayi maka, nima ya yi min, zan dauki
maaikata da zasu kula da shagon mutum uku cikin yayan dan uwan ka na Faskari, da
wanda ka ce tare aka shayar damu Kamilu yake ko Kamalu? Ka bar su a kauye suna noma
da kiwo cikin wahala ka kama bare ka rike da daraja.
Ni bani da lokacin zuwa wani boutique, ni dai in ji alert na shigowa kullum a
ka yi ciniki, in sayi abubuwan da nake so shikenan.
Cikin sauri Alhaji ya katse ta.
Babu wasu yayan dangi da zaki dauka aiki a shagon nan kin ji na gaya miki, su
zo su yi min rubdugu a kan dukiya ta da basu taya ni tarawa ba, in da na biye musu
da hidimdumun su, da basa karewa, da yau ban tara abinda na tara miki ba.
Ki dauki inyamurai da suka karanci kasuwaci suka kware da kula da shago su
kula miki da shagon karkashin kulawar Mukhtar ba gayyar yan kauye ba, ko ki bar shi
ya kawo maaikatan da suka dace da kan sa, don na san ba zai kawo na banza ba, ko
wadanda basu gogu da harkar ba, ko marasa amana da zasu yi miki almundahana.
Haushi da takaici ya kara kama Amani, na yadda komai na mahaifin ta sai ya
dangana shi da wannan Mukhtar din yake samun aminci a zuciyar sa, wannan wane irin
abu ne? Anya haka farin baabzinen nan ya bar mata Uban ta? Shi kadai ne mai amana a
duniya a wurin Daddy, kamar wani dan sa na cikin sa, ga samari nan fal jinin sa
yayan wan sa baya taimaka musu da komai, suna kauye suna gararramba, wau sun yi
karatu babu aikin yi, kai bata taba jin tana kishin wani dake tare da mahaifin ta
irin Mukhtar dinnan ba, wai har yafi yarda da shi a kan yayan dan uwan sa?
Wadanda lomar abinci kullum sai sun fita sun nemo a kasuwannin kauye, wasu
cikin su da yawa sun yi karatu mai zurfi musamman Kamilu, amma babu aikin yi,
alhalin suna da kanin Uba mai wadata da gwamnati a hannu irin sa a kasar nan, amma
gashi yana fadin a nemo inyamurai wadanda ba lallai su kasance musulmai bane a basu
aikin yi a karkashin sa, su yan uwan sa a bar su cikin wahala, karkashin kulawar
wani bare, wanda yafi jinin sa matsayi a wurin sa da ko asalin sa bai sani ba.
Tana ganin tsayawa yi wa Daddy gyara a kan ire-iren kuskuren da yake tafkawa
bata lokaci ne don ba dauka zai yi ba, ba kuma denawa zai yi ba tunda rowa,
mammako, rashin yarda da wani ya amfana da shi, da rashin son nasa ya rabe shi
halin sa ne zaunanne da ta dade da fahimta tunda ta soma hankali.
Ita kuma duk da halin ta na raina ajawalin kowa saboda iko da mukamin data rayu
cikin sa, da ganin kowa bai isa ba, Allah ya yi ta mutum ce mai yawan kyauta, da
matukar son yan uwan mahaifin ta na kauye duk da talaucin su, tunda bata san na
mahaifiyar ta ba. Wani abu mai kyau da zaa iya cirewa a halayen Amani shi ne abin
hannun ta baya rufe mata ido sam, ke dai bar ta da facaka da kudi wajen kwalliya
mai tsada da gasar hawa motar yayi.
Ai kawai Daddy ka ce shi ka budewa boutique din ba ni ba, tunda shine mai ruwa
da tsaki wajen gudanarwar sa gabadaya, bayan shi ya je Mexico ya shigo da komai,
sai kawai a canzawa boutique din suna zuwa Mukhtar Collection.
Amani ta fada cikin bacin rai ko shagube zaa ce? Kamar ba da mahaifin ta take
magana ba. Tana mai tattaka matattakala don komawa dakin ta.
Murmushi Alhajin ya yi, maimakon ran sa ya baci ya kwabeta a kan rashin kunyar
da ta yi masa, amma sai ya buge da rubuta mata text message din lallashi da wayar
hannun sa.
Zuwa shekaru kadan a gaba, idan Allah ya raya mu, Tafisu zaki zo ki gode min,
for making MUKHTAR DIFFA your Business Mentor, ranar da kika ga Mukhtar ya maida
dan Boutique din nan naki ya rubanya zuwa PLAZA guda.
Domin Allah SWA ya huwwace da ya halicce shi yayi masa hikimar maida taro ya
koma sisi. Trust him my daughter, work with him for a while, give him a try as your
business mentor!.
**** **** ****
Sai da Amani ta zo kwanciya ta ga wannan sakon na Daddy, zumburo baki tayi tana
tunanin mutumin nan ba haka ya bar mahaifin ta ba. Yardar ta isa. Kaunar ta yi
yawa. Ko shi ya haife shi sai haka. Iya shaidar arziki da zai iya masa kenan.
Daddyn ta da duk wanda ta nuna bata raayi nan take zai yanke alaqa da shi ko
waye kuwa, ko da zai kasance jinin sa ne, amma banda MUKHTAR DIFFA. Farin baabzinen
data taso ta gani tare da mahaifin ta, yana rayuwa karkashin sa matsayin mataimakin
sa, kuma yana tare da shi kullum a gida ko ofis. Dan asalin garin Diffa, ta kasar
Nijar, wanda ko asalin sa basu sani ba har shi Daddyn kuwa, banda sunan garin sa da
yake amfani da shi a gaban sunan sa DIFFA.
Daddy dai ya dauke shi aiki ne da farko a dalilin haduwar jini kawai, ta
sanadin wani halin amanar sa da ya bayyana gare shi, rashin zalama da rashin
kwadayin abun duniya, in kana da wadannan halayen, tabbas zaka zauna lafiya da Hon.
Usman Faskari tunda shi bay a so wani ya more shi ko yayi arziki da shi, sannan ga
kyawawan kwalayen ilmi (educational qualifications) din sa masu nagarta, domin
Mukhtar Diffa, ya fitar da kwalayen boko biyu masu darajar farko (B. Sc & M. Sc in
Business Administration) daga jamiar Paris wato (Paris Saclay University).
***** ***** ****
FARKON HADUWAR HON. USMAN DA MUKHTAR DIFFA
Asalin haduwar su da Alh. Usman Faskari a wata tafiya da ya yi birnin Paris ne,
lokacin da ya je shigo da wasu kayan assasa kamfanin sa na farko wasu shekaru kusan
goma a baya.
Cikin tsautsayi Alhajin ya yarda wallet din sa a cikin jirgin kasa, wanda ke
dauke da dukkan katunan sa na banki daban-daban (credit cards), fasfo, ID cards, da
duk wasu muhimman abubuwa da ake sakawa a cikin wallet. Bayan ya sauka daga jirgin
kasan, ya shiga motar da zata maida shi masaukin sa ne ya lura babu wallet din sa a
tare da shi, wadda ba katunan bankin sa kadai ta kunsa ba, akwai kudade (Euros)
masu yawan gaske a ciki.
Alhaji da kudi, ko sadakar dubu guda baya iya yi in ba ta hanyar siyasa ba.
Yayi salati a gigice yana kara laluba aljihun sa yana gayawa direban da dauko shi
su koma, ya yar da abubuwa masu muhimmanci su koma tashar jirgin kasa.
Komawar da bata haifar da komai ba sai bata lokaci, domin train din tuni ya
dade da barin Paris, ya nausa wata jihar dake gaba da Paris wai ita Bourdeaux. Ya
dai bar report a ofishin jirgin kasan da wajen yan sanda.
Hon. Ya shiga damuwa ba yar kadan ba a daren, domin a cikin wallet dinnan kusan
duka sirrin rayuwar sa ne gabadaya. Ga tsabar kudaden da ke ciki wadanda ya fitar
dasu daga banki ne da zummar zai yi amfani dasu wajen accommodation na tsayin zaman
sa a kasar da cuku-cukun clearance na kayan sa har zuwa komawar sa gida.
Damuwar sa tana karuwa in ya tuna identity cards din sa daban-daban na siyasa
da na kasuwanci duk a cikin wallet din sa.
Alhaji kamar ya zare. Amma ko minti goma bai yi da shiga masaukin sa ba ya samu
kira a wayar sa, a lokacin yana kokarin revoking katunan sa na banki don kada a
samu damar yashe shi. Duk da iya abinda ya mallaka ba wai a bankuna suka kare ba,
yana da hannayen jari da kadarori masu yawa da kamfanin sa na FASKARI INVESTMENT
LTD.
Yana dagawa ya ji an yi masa sallama da hausar da bata fita yadda ya kamata, ko
dai Francaise ya rinjayeta ko harshen Espanol, ko kuma abzinanci. Cikin ukun dai.
Duk da haka a kan gane hausar idan aka saurara, kasancewar cikin nutsuwa mai kiran
yake yin ta.
Ina Magana da mai wannan layin ne? In sha Allahu kana tare da mai wannan layin
Engnr. Othman Fass. Ya kasa furta sauran da accent din sa. Amma Alhajin ya gane
yana son cewa Faskari ne.
Sai ya karasa masa da cewa Eh nine Engnr. Usman Faskari.
Alhmdulillah, ina zan sameka in baka wallet din ka yanzu? Na tsince ta a jirgin
kasan da ya taho daga Bordeaux zuwa Paris. Na samu wannan lambar a jikin daya daga
cikin identity cards din ka.
Alhaji a zaune yake amma bai san lokacin da ya mike tsaye ba yana hamdala, yana
hailala, ya gaya masa sunan Hotel din da yake, yace ya kira shi in ya zo reception.
Cikin daren baa kwana ba saurayin ya zo hotel din, suka hadu da Alhajin. Ya
dauko wallet din sa ya bashi. Ya tsaya har Alhajin ya bude ya duba sosai ya kuma
kirga kudin sa ya ga suna nan cif, a jere yadda ya jera su, ko kwarzane basu yi ba,
ya tabbatar ba abinda aka cire.
Babban abun mamakin Alhajin, kudin sa na nan yadda ya bar su ko guda daya baa
cire ba.
Har yaron ya juya ya tafi, Alhaji Usman ya kasa daure mamakin sa. Sai ya bi
bayan sa. Ganin cewa dan Afrika ne ga hausa kadan ya iya, duk da dai alamu sun nuna
ba bahaushe bane Baabzine ko dai dan kasar Nijar ne, wato irin matasan nan na Nijar
wadanda ke tahowa karatun boko kasar goyon su wato Faransa, daga Jamhuriyyar Nijar,
kasancewar kasar Faransa ce ta goya kasar Nijar.
Amanar yaron, exceptional personality, da kuma bravity din sa kai har ma da
character da attitude din sa sun yi matukar impressing din sa.
Alhaji Usman ya bi bayan sa da sauri yana fadin;
Ya ka Da na, dakata don Allah, yaya sunan ka?
Cikin halin sauri-sauri don kada ya rasa jirgin kasan komawainda ya fito, da
koin kula irin nasa, kuma ba tare da ya juyo ba, cikin rashin sakin fuska da rashin
annuri ya ce da Alhaji Usman,
suna na Mukhtar.
Daure ka tsaya ka ji Da na Mukhtar in maka godiya don Allah.
Amma bai tsaya din ba sai tafiya yake, Alhajin kuma bai fasa bin bayan sa ba,
yana rokon sa Allah Annabi ya tsaya ya bashi tukuici.
Ya dan tsaya har Alhajin ya cimmasa, juyin duniya Hon. Usman yayi a kan ya
karbi kudin dake cikin wallet din bakidaya don farin cikin taimakon da yayi masa,
amma kyakkyawan matashin baabzinen ya ki, duk kuwa da cewa a lokacin neman kudin
jirgin da zai koma Hong-Kong din China yake yi, saboda ya nemi wani aikin a can,
kasancewar interview din da ya yi ta neman aiki da wani kamfanin turaruka a nan
Paris din bayan kammala karatun sa, bai yi nasara ba.
To na ji bazaka karba ba, na kuma gode da karamcin ka, na kuma yabawa nagartar
ka, samun irin ka a cikin matasa is a blessing. Ka cigaba da wannan halin na
taimako da amana zai kai ka har inda baka taba zato ba.
Na sha gwada samari kamar ka, ban samu wanda ya san amana ba. Ni kuma mutum ne
mai son mutane masu amana. Don ta yi karanci a wannan zamanin.
Still fuska ba walwala ya ce na gode.
Sannan ya juya da sassarfa ya bar reception din. Tafiyar sa kadai abin a bi da
kallo ne, saboda taku yake da sassarfa, amma kamar na kasaita.
Yaron ya tsaya masa a rai har wayewar gari. Don haka washegari ya kira shi da
layin da ya kira shi jiya, suka gaisa.
Alhaji Othman ne ko?
Ya fada da kakkaurar muryar sa bayan sun gaisa. Ni ne Da na Mukhtar, ya ka je
gida? Alhamdulillah ya bashi amsa. In ba damuwa ina so in zo in gan ka kafin na
wuce gida Nijeriya gobe. Yace babu mishkilah, Allah ya kaimu, amma ka bari ni zan
zo in same ka kasancewar daga Clermont-Ferrand City zan taho, bana so ka sha wahala
har nan Baba. Murmushi Alhajin yayi yace na gode Da na sai ka zo, don Allah ina
jiran ka.
Lokacin da yayi masa waya yace ya taso a train daga Clermont Ferrand, Alhajin
yasa aka shirya abinci na alfarma a dakin sa na hotel, dama kuma yayi sayayya ta
sutturu masu tsada, agogon maza na (Swatch) da takalma da turaruka ga Mukhtar din,
da niyyar ya je ya kai masa har gida a matsayin godiya, tunda ya ki karbar makudan
kudin da ya barma shin.
Wannan ya nuna ba karamar alfarma da haduwar jini Mukhtar ya samu a gun Hon.
Usman ba. Kasancewar shi mutum ne mai tsananin kankamo, bi maana, ba kowa ke cin
arzikin sa ba bayan tilon yar sa AMANI sai wanda rabon sa ya rantse, mutum ne mai
rowa kwarai. Tsakanin sa da duk wani maaikacin sa albashi kadai, babu ihsani. Amma
shi wannan yaron ya nuna masa akwai sauran masu amana da rashin kwadayi a duniya,
sabanin daukar da yake yiwa kowa, cewa mutanen yanzu duk kwadayayyu ne masu neman
gasashshen tsuntsu daga sama, shi yasa yake so ko yaya ya gode masa.
Don yana yawan gaya wa Amani yanzu duk mutanen duniya makwadaita ne, shi yasa
suke cewa ya fiya rowa, ya dauki kowa a irin dabiar da yake kai, wato son ci daga
haram ko halak kamar sa.
Sannan a ganin sa mutaen yanzu basa ganin kudi su kyale balle irin wadannan
Euros dake dankare cikin wallet din sa.
Ko a satin da wuce ya kori maaikata biyar daga kamfanin sa, da ya kama su da yi
masa sama da fadi da wasu yan kalilan kudade. Bayan kuma kudaden ma bata suka yi
cikin lissafi amma a hannun su.
Ya iso kofar dakin ya danna kararrawa, Alhajin ya bude masa yana lale marhabin
da shi, sanye yake da farar shirt an rubuta Fred Perry da bakin wandon CK Jeans.
Dogon matashi, kakkarfa, farin baabzinen usli, mai wani irin sassanyan kyau, hancin
sa kamar an sa ruler an ja masa shi an saka masa shi a tsakanin idanun sa, komai na
halittar sa ya zauna a inda Allah Subhana ya ajiye shi, kamar shi ya zaba wa kan sa
zati da kamala, ga wata lallausar suma da ta taru a saman goshin sa ta abzinawan
usli, har ta dan kalmaso a kan goshin sa, ta maida shi tamkar Baindiyen nan mai
farin jini (Shahrukh Khan).
Alhaji ya bashi kujera ya zauna suka gaisa sannan ya nade hannun riga yace ya
sauko kasa su ci abinci tare. Ko kadan rashin walwalar yaron da shan kamshin sa
baya damun sa.
Kamar ba zai ci ba, amma ganin Alhajin da an sa yayi serving din su a plate
guda, sai ya kasa tankwabe kulawar wannan dattijon, wanda ke ta haba-haba da shi
cike da kauna, sai ya sauko kasa ya kalmashe kafafun sa, suka fara cin abincin a
plate daya.
Suna ci, Alhaji Usman na hilatar shi da hira cikin dabara irin ta manya, har
yaji abinda yake son ji, wato inda ya fito da kuma abinda ya kawo shi birnin Paris.
Nan yake gaya masa cewa daga wani yanki na jamhuriyyar Niger ya zo nan, ana
kiran yankin nasu Diffa Region, yau watan sa uku da kammala karatun digirin sa na
biyu a nan kasar, daga jamiar Paris Saclay University. Ya gayawa Alhajin tun baya
kammala masters din sa ya nemi ayyuka na wucin gadi har uku bai samu ba, kasancewar
shi ba dan kasa ba, don haka zai koma Hong-Kong yanzu ya nema a can. An ce suna
bada ayyuka sosai ga yan Afrika, shi neman na kan sa ya fito, ba yanzu zai koma
gida ba.
Kasancewar a lokacin kasar Nijar na fama da matsalar durkushewar tattalin
arziki babu ayyukan yi ga matasa masu ilmi kamar sa a Nijar.
Alhaji Usman ya tambaye shi ko me ya karanta da level din karatun sa duk ya
gaya masa, cewa daga digirin sa har master first class ne. Alhaji Usman became
highly impressed da jin hakan, sai kawai Alhajin ya ce, ina ma za ka iya zaman
kasar Najeriya, da mun tafi tare na baka ragamar kamfani na, in ya so sai ka dinga
zuwa gida kana ganin iyayen ka lokaci-lokaci, saboda ni din bani da Da namiji, sai
mace tilo, ina neman mataimaki a kan harkoki na wanda zan iya ja a jiki na in sakar
masa ragamar kamfani na. Na kuma yaba da halayen ka.
Mukhtar ya ce ban taba zuwa kasar Najeriya ba Baba, amma ina jin labarin ta,
kuma ina son aikin yi kwakkwara wand azan tsaya a kan sa da kafafu na, musamman
wanda ya shafi kasuwancin kamfani, a nan buga-buga kawai nake babu permanent job ga
wadanda ba yan kasa ba, ni kuma ba yanzu zan koma gida ba.
Don haka zan bi ka in gwada in gani, idan naji dadin kasar, zan zauna, don bani
da abun yi ko na koma Diffa. Kuma babu wanda ke jira na a can.
Cikin mamaki Alhaji Usman ya ce ina iyayen ka?
Nan da nan fuskar Mukhtar din ta wani irin sauya, ta rine ta yi jajir abin ki
da farin mutum. Wani yanayi ya shiga na kokawa da numfashin sa da Alhaji Usman ya
kasa karanta. Shi da kan sa ya baiwa kan sa amsa da basa raye kawai. Sai ya shiga
yi musu addua ba tare da shi Mukhtar din ya ce masa komai a kan su ba.
Amana ce ta hada mu, naji ina kaunar ka kamar dan da na haifa saboda halayen ka
da suka burge ni, ina fatan wannan amanar tayi ta yado da yabanya a tarayyar mu.
**** **** ****
Mafarin zuwan Mukhtar Diffa kenan gidan su Amani, tarayyar da ta zamewa Alhaji
Usman sanadin alkhairori masu yawa.
Bai sakar ma Mukhtar ayyukan sa na sirri ba sai da ya cigaba da gwada shi
iyakar gwadawa ta hanyar yawan aiken shi kai kudade banki, domin da farko kamfani
ya kai shi, ya bashi ofis, a matsayin Chief Operating Officer (COO) ya kuma bashi
gidan zama a kusa da gidan sa wanda babu nisa da kamfanin Faskari Investment cikin
birnin Katsinan Dikko.
Excellent Performance din da Mukhtar Diffa ya soma nunawa daga zuwan sa ya
razana kowa, domin yana zuwa ya canza akalar komai zuwa na zamani, ya kawo sababbin
innovations masu tafiya da zamani na yadda zaa bunkasa hanyoyin da kamfanin ke
amfani da su wajen shigo da kayayyakin da kamfanin ke shigo dasu Najeriya daga
Faransa da sauran kasashen Europe irin Mexico. Har ila yau, COO Mukhtar Diffa, ya
kawo hanyoyin samun cigaba ga maaikata ta hanyar karawa maaikata sani da dabarun
kasuwanci a zamanance, ta hanyar shirya (capacity building programs) iri-iri da
yake shiryawa a kai-a kai ga kananan maaikatan Faskari. Ya tsame masu lalaci daga
ciki ya kai su kasa, ya maye gurbin su da masu hobbasar cikin su.
Ya kuma takura wa Alhaji a kan kara albashi da welfare din maaikata da yake
kankamewa. Kan ka ce meye wannan hakan ya sayo ma Mukhtar farin jini gun kananan
maaikata, ya kuma kara musu himma da maida hankali, sannan ya kawo conducive
working atmosphere ga dukkan maaikatan Faskari Investment.
Shi ba hausa ce ta ishe shi ba, amma da zuwan sa Katsina ba jimawa sabida
cudanya da hausawa da maaikata a company, da kuma shi kan sa Alhajin da ke masa
magana kullum da hausa don ya kware, a sannu bakin sa ya fara iyawa sosai, a
hankali a hankali kuma accent dinsa na Francaise da abzinanci ya fara barin bakin
sa sabida rashin abokin yi.
Mukhtar Diffa, ya soma rikidewa yana koma wa zallan Ba-katsine, in ka cire
nannadaddiyar sumar kansa da launin jar fatar sa da ke fallasa shi, matsayin
kyakkyawan Baabzinen mutum dan hutu kuma dan zamani, hatta hausar bakin sa kafin
shekara guda ta koma ta Katsinawa.
****** ****** ******
Sanda Alhaji Usman ya kawo shi gidan tana makarantar kwana aji daya a Ulul
Albaab, ya dade a gidan ma bata san da shi ba, a lokacin Alhaji bai mayar da
kamfanin da sunan ta ba, so ko ta zo hutu ba wani haduwa suke ba ko a ce bata san
shi ba ko da ta hange shi, don bai cika zuwa gidan ba a Kamfani yake rayuwar sa,
daga gida sai ofis, Mukhtar ko aboki bai da shi, sai Malam Tajuddeen mai gadin
gidan Alhajin.
Ranar da ya fara ganin ta wata asabar ce, direba ya dauko ta daga makaranta
yana cikin motar Alhaji a harabar gidan yana jiran fitowar Alhajin zasu wuce duba
wata gona da Alhajin ya saya a garin Bindawa, ji yayi yarinyar wadda fitowar ta
Kenan daga mota tana zagin direban ta cikin daga murya wai yayi parking ba a kofar
shifa falo ba, yana nufin da kafar ta zata taka har kofar falon ko yaya? Ga zakin
murya cau ga zare ido kamar tana yi wa dan ta fada, shi kuma Malam Sirajo yah au
rawar jiki yana bata hakuri tare da cewa

Please Login or Register in order to submit comment