You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jotar da suke magana
ya bashi tare da biro, Alhaji yayi rubutu ya mikawa Amani, da ta karanta zumburo
baki tayi don Alhaji cewa ya yi bai ji dadi ba da bata amsa sallamar Mukhtar ba,
amsa sallama ga musulmi wajibi ne. Ta ce to Daddy in dai amsa sallamar wannan
mutumin ce zan shekara ban amsa ba, tunda shima ba ya amsa tawa. Mukhtar yayi dan
murmushin da ya kara masa kyau, ya matsa gaban Alhaji yace Alhaji ka ga kuma ni
sayayya ma na yo mana har da ita, wai ni mai kanwa, amma ko nagode na tabbata ba
zata ce ba. Amani tayi maza ta ce Daddy ka fada masa kada ma ya kara sayo komai da
ni, kada ya kara alaqanta ni da shi, bamu hada jini ba bamu hada komai ba, idan ina
son abu na san inda zan je na sayo ba shi kadai ya san hanya a garin nan ba.
Mukhtar ya ce a ran sa kin yi da dan halak. Amma saboda ganin damuwar da ke kan
fuskar Alhaji sai bai tanka mata ba, amma ya ji haushi sosai da wannan gorin nata
na basu hada jini ba basu hada komai ba, dama kullum ta tashi rashin mutuncin ta ta
kance masa dan karo, ai Alhaji ba uban sa bane. Sayayyar kayan ciye-ciyen snacks
din McDonalds da ya yo mata da ya lura su take son ci kullum, bata da cin abinci
sai su, ya dauke ledar daga gaban ta ya kaiwa nurses din da ke kula da Alhaji,
bayan duk kamshin pizza ya gama cika ta, ya tado tsohuwar yunwar cikin Amani.
Amma sabida ki-fadi irin nata tabe baki kawai tayi. A ran ta kamar tayi kuka, a
kufule ta ce to da ka fita da abincin ni me zan ci? Ya ce ai na dauka kin san
hanyar inda ake sayowa? Alhaji kan sa sai da ya harare ta don yana jin duk yadda
aka yi. Mukhtar ya zauna yana cin shawarma yana korawa da sassanyan lemon tuffaha
bai kara kula ta ba. Yadda yake taunar sa gentle-gentle ma kadai abun shaawa ne ba
zaka gaji da tsayawa a gefen sa kana kallon kyakkyawan bakin Mukhtar ba.
Ta yi kwafa ta mike don ta dauro alwalar sallahr azahar, amma me? Sai ta ga
bakon watan ta ya zo, ga shi bata yo guzurin kunzugu daga gida ba.
Ta rasa yadda zata yi, ta kasa fitowa daga toilet din, don ta san bada jimawa
ba zata soma staining jikin ta.
Gashi yanzu ta gama cewa kada ya kara sayo mata komai ta san hanya, kuma da
kunya yanzu shi ba mijin ta ba ba komai ba ta aike shi sayen kunzugun mata.
Da taga cigaba da zaman a toilet zai sa har jinin ya soma naso, cikin shagwaba
irin tata sai kawai ta fashe da kukan da ta san yana rikita Alhaji.
Daga Mukhtar har Alhaji ba wanda bai jiyo kukan nata ba, Alhaji har gaban sa
sai da ya fadi don ya dauka wani mummunan abun itama ya faru da ita a toilet din,
tunda shima tsautsayin da ya same shi a toilet ya same shi.
Inkiya da buruntun magana ya hau yi wa Mukhtar da hannun sa mai lafiya a kan
don Allah ya duba masa ita ya ga ko menene, shi Mukhtar kunya ce ta kama shi, ta
yaya zai bita toilet alhalin ba matar sa ba ce ba kuma kanwar sa ba? Sai yanzu ya
ga rashin dacewar tahowar su ba tare da sun lallaba Haj. Rabi an taho har da ita
ba, don sau da yawa in ya shigo dakin sai dai ya koma in ya ga Amani ta baza dogon
sassalkan gashin kan ta tana tajewa babu mayafi a jikin ta, wannan gashi yana
matukar kidima Mukhtar, ita kuma ta kasa sabawa da barin lullubi a jikin ta, kamar
yadda take yi a gida a nan ma haka take rayuwar ta babu takura saidai shi ya takura
ko ya rufawa kan sa asiri ya fice in ya kasa jure kallon ta, sabida dalilai na
shariah, ita kuma idan ta zauna da lullubi duk sai ta ji ta takura don bata saba
ba, shi da kansa ya gaji ya yi mata magana jiya da kakkausar murya a gaban Alhaji
ya ce mata ki dinga saka lullubi a kan ki idan ina nan. Me yasa ke baki san duk
wani ya kamata bane? Me yasa Baki gudun fitsarin shaidanu a kan ki? A lokacin
zumbura masa baki kawai ta yi bata tanka masa ba. Bata san cewa wannan zumbura
bakin ba karamin kyau yake yi mata ba, ya kara fiddo zahirin kuruciyar ta a fili,
ko ina ruwan Mukhtar da lullubin ta da zai nemi takura mata? Lullubi zata wuni tana
yi saboda shi ko me? Shi waye dinta? Me ye gamin ta da shi baya ga kasancewar sa
maaikacin Baban ta wanda ya dace a ce respect yake bata? Wannan mutum akwai wuce
gona da iri in ji Amani. Ko an gaya masa don shi ta zo jinyar? Ko zaman sa ta ke yi
a asibitin ba zaman jinyar mahaifin ta ba?
Abinda ta fada a ranta kenan ba tare da ta tsinka masa ba wai aka ce kulawa ma
yabawa ce.
Mukhtar ya san yanzun ma in aka bibiya abinda take yiwa kukan nan bai kai ya
kawo ba, sangartar ta ce kawai don bai ji alamar faduwa ko makamanciyar ta ba.
Alhajin ba lafiya ma ba zata bar shi ya huta da shagwabar ta ba.
Amma yadda ya ga Alhaji ya shiga damuwa sai tausayin sa ya kama shi, wannan ya
tasa ko fitinanniya, ya mike zuwa kofar toilet din ya na kwankwasawa ya ce ke
lafiya? Ki fito menene? Amani ta rasa abunda zata ce masa, dole ta share hawayen ta
fito tana tafiya kamar a kan dan yatsan ta ko wadda kwai ya fashewa a ciki, Mukhtar
ya hau kallon wannan tafiya kamar ta mai koyon tafiya ya rasa me take ciki haka?
Ita kuma bata ce masa komai ba don ta san da kunya kuma ta aike shi wannan hidimar,
bayan gwaleshin data gama yi yanzunnan, sai ta dauki Jakarta ta fita da sauri don
ta taimaki kanta.
Allah ya taimaketa a nan cikin asibitin ta samu akwai pharmacy, ta sayo pad ta
dawo ta sake shigewa toilet wannan karon da gudu-gudu ta rufe, bata ko kula
tambayar da yake yi mata ba daga inda yake tsaye harde da hannuwa a kirji. Are you
okay? Tayi masa banza. Ba karamin haushi ta bashi ba da share shin nan data yi, ya
kudire a ran sa bazai kara shiga shirgin ta ba har su koma gida.
Alhaji ya so a ce yana da baki, ya yi sulhun alkhairi tsakanin Mukhtar da
Amani, baya son wannan rashin jituwar tasu wanda zaman su waje daya tsayin sati
biyu bai saka sun shaku da juna ko sun daina kyarar juna ba, su daina hamayyar nan
mara dalili da shi take sakawa a damuwa da tantamar cikar burin sa a kan su.
Shi dai kullum kunnen sa sain sar su ke tada shi daga barci, idanuwan sa basa
ganin komai cikin idanun su sai tsanar juna, da rashin jin dadin zama da juna da
hantara da kyarar juna. Bai taba jin sun yi maganar arziki a tsakanin su ba tun
zuwan su asibitin, ko sentence daya balle a je ga batun gaida juna. Basa amsa
sallamar junan su sai a cikin cikin su. Babu mai ragawa dan uwan sa. Gara shi
Mukhy yana rage uzzura mata a dalilin kaifin idon Alhaji.
Data fito daga toilet ficewa ta yi ta bar musu dakin ta koma reception din
asibitin ta zauna a kujera nesa da jamaa ta kira Hamida Balewa. Hamida ta ce
mutuniyas ina kika shiga ne? kwana biyu ban ji complain din dan Alhaji ba Da 'yar
damuwa a muryar tace tana asibiti tare da Daddy a France, Daddy na ya samu stroke
Hamdy ki yi masa addua na san ke mai addua ce mai yawan sallah ce da tsayuwar dare
Hamida ta shiga juyayi, a karshe ta jajantawa aminiyar ta, ta ce ke da Haj. Rabi
kuke jinyar kenan?
Wani mikakken tsaki ya fito kai tsaye daga bakin Amani, tace cikin dan daga
murya kema kin san ko da waye, ko baki tambaye ni ba, ni da waye kuwa banda bare ka
fi dan gida, yana nan ya hana ni sakat, ya hana ni samun ladan uba na, masifar yau
daban ta gobe daban, ke sai ki rantse da Allah yana da gadon Daddy ko tare Alhaji
ya haife mu, tare kuma yake so mu rayu dole, ya shiga komai na gidan mu yayi kane-
kane ya fi ni iko da uba na yanzu sai ta kama matsar kwallah, Hamida tana so ta yi
dariya sabida wannan sakalci na Amani, amma ta san Amani bata cikin mood din da
take bukatar a yi mata dariya, don tsakanin ta da Allah take sharing mata damuwar
ta, don bata da inda zata je ta fada ta ji sanyi, wannan Mukhy! Ya addabi aminiyar
ta, ita kuma haka nan yake burge ta, bata ganin laifin sa ko kankani, da kullum
Amanin ke nanatawa, wanda duk ciki in ka saurareta zaka fahimci ba komai ke damun
ta ba sai kishin son da mahaifin ta ke ma Mukhtar din.
Hamida ta nisa tace kin san Allah Amani, idan har na isa in baki shawara ki
dauka to ki koma girmama Mukhtar, ki kaunace shi matsayin dan uwan dake taimakawa
Daddyn ki, ki bashi gurbin Yayan da baki da shi, ku zamawa Alhaji Yaya da kanwar
sa.
I'm sure duk da ban sani ba Alhaji haka yake so ya gan ku, musamman a yanzu da
bashi da lafiya ku biyu ne a kans a kuke jinyar sa.
Idan ya bar miki jinyar bazaki iya ke kadai ba dole sai namiji dan uwan sa idan
ana maganan stroke.
Kuma kin ga wannan fadan da kuke ta yi a kan idon Alhaji yana saka shi a damuwa
musamman cikin yanayin da yake a yanzu, shi fa Daddy in na fahimta saboda Allah
yake son Mukhtar din nan. Hayagagar ki bata isa tasa ya kore shi ba, da zai kore
shi da tuntuni ya kora don gudun bacin ran ki.
To fadan da yafi karfin ka hausawa suka ce ka maida shi wasa, sai ka zauna
lafiya.
My friend I want you to stay cool and healthy, kada Mukhy yasa jinin ki ya hau,
zuciyar ki ta buga a banza ya yi wa Alhaji da kan sa asara. Ta karasa cikin dariya
ta kuma yi maza ta kashe wayar ta. Amani na kururuwar sai tagaya mata me take nufi
da hawan jinin ta ta ko bugawar zuciyar ta zata zamo asara ga Mukhtar. Meye
manufar ta?
Hamida nata dariya ita kadai ta tura mata text. Ga abinda ta rubuta mata.
kan ki ake ji kullum a kan sa, kin hana kan ki zaman lafiya saboda shi, watch
your actions over him, you care too much for him, listen to your heart and
understand the actual feelings.
-Yours Hamdy.

Amani ta kusa zagin Hamida, ta kira ta back yafi sau biyar Hamida ta ki dauka,
kamar ta yi hauka ita kadai wai Hamida ta zageta, zagin da baa taba yi mata irin sa
ba, ta rasa wanda zata ce ta saurari zuciyar ta a kan sa sai Mukhtar? Me zata
saurara din banda bugun zuciyar ta dake karuwa kullum a kan bacin ran da yake sanya
ta kullum?
Hamida daga inda take sai murmushi take yi rike da wayar hannun ta, ta dubi
fuskar wayar kamar Amani take kallo tana mata murmushin karfafa guiwa, haka kawai
ta samu kan ta tana ma aminiyar ta shaawar auren Mukhy din nan, duk da kasancewar
sa a karkashin mahaifin ta, ta shiga yi ma Amani adduar samun daidaiton raayi da
fahimtar juna tsakanin ta da wanda take ganin ya shige gabanta. A ganin Hamida ba
wanda zai iya da ita da halayen ta duk duniya sai wannan Mukhtar din, da tun yanzu
yake juya Amani wanda hakan ke nuna zai iya jarumtakar zama da Amani da dukkan
halayen ta, ta san zama da Amani sai jarumin mutum, duk kawayen su na makaranta
babu wadda Amani bata yi fada da ita ba itama don ta zame mata kamar 'yar uwa ne ko
sun yi fada ita da kanta Amanin zata zo ta nemo ta su shirya. A ganin Hamida babu
mai iya auren Amani ya juya ta sai jarumin namiji saboda izzar ta. Ta kuma yabawa
Mukhtar wajen jure rayuwa kusa da Amani alhali kullum tana kyarar sa da gori kala-
kala. To amma Alhaji ya riga ya karbi maganar abokin sa ta kuma ce mata ta yi masa
biyayya a kan maganar Alhaji Sadi, yanzu kam ta fi mata shaawar auren Mukhtar yaro
dan uwan ta mai halin manya.
Zata dukufa taya Amani adduar samun zabi mafi alkhairi a matsayin ta na aminiya
ta kwarai. Miji wanda zai taimaka ya saita musu hankalin ta, tarbiyyar ta, addinin
ta da nutsuwar ta. Wadanda duk ta rasa a dalilin rashin tashi gaban mahaifiya.
Sanda ta koma dakin maghriba ta kawo kai, Mukhtar na yima Alhaji
alwallah zai yi sallah yadda yake yi daga kwance, sai ya tabbatar Alhajin ya tada
sallah sannan ya shiga ya dauro tasa ya fito, sai ya tadda Amani ta ja ledar nashi
abincin tana ci ba kunya ba tsoron Allah fuska tamke, an ce yunwa ba kanwar uwa
bace.
Girgiza kai yayi ya shimfida dardumar da yake sallah a kai ya tada sallah a
gefen gadon Alhaji.
Ko da ya idar da sallah bai ce mata don me ta ci masa abinci ba, ya san dama in
yunwar cikin ta ta kama ta zata ci ne kullum haka take masa, ba don komai ba sai
don kada tace ta gode a duk lokacin da ya sayo masu abinci.
A haka sauki ke ta samuwa ga Alhaji Usman, bakin sa da ake ta gasawa ya fara
fidda magana sosai, likitocin sa sun ce duk bayan watanni shida zasu dinga zuwa
check up, duk da tafiya da kafafu bata samu ba don haka suka ce Alhaji zai dinga
amfani da wheelchair.
Watan su guda kenan suna jinyar Alhaji amma ba abinda ya canza a alaqar su. Yau
suka sauka a gida Mukhtar na turo Alhaji a wheelchair inda Haj. Rabi taje ta taho
dasu daga filin jirgi tareda sauran ma'aikatan kamfanin Faskari. Kowa ya zo falo ya
jajantawa Alhaji yayi masa sannu da dawowa.
Malam Tajuddeen shi ya gaya musu zuwan Alhaji Sadi Talle uku bai samu Alhajin
ba, yace kuma layin Alhajin da yake da shi baya tafiya, sun gaya masa Alhaji
asibiti yaje babu lafiya, ya ce duk ranar da suka dawo Malam Tajuddeen ya sanar da
shi.
Ba Alhaji ne kadai fuskar sa ta sauya ba har da ta Mukhtar. Amani tunda ta
haura sama ta bar su bata kara saukowa ba.
**** **** ****
Washegari kuwa tunda safe Alhaji Sadi ya zo cikin rantsatstsiyar motar sa
Acura, kai da ganin irin kwalliyar da ya caba cikin sassalkar shadda fara kal, zaka
san ba dubiya kadai ya zo ba har da zance na saurayi ga budurwa don fara kafa
gwamnatin sa.
Mukhtar baya gida yana company don gudanar da ayyukan da suke jiran sa duk da
cewa yana rage ayyukan sa daga can asibiti ta kwamfuta wadanda sakataren sa ke tura
masa, musamman in Alhaji na barci, zaka same shi yana aiki cikin kwamfuta yayin da
zaka samu Amani na harkokin ta cikin wayar ta cikin dakin ba ya ko daga ido ya dube
ta, amma a zuciyar sa ya na takaicin ace mace bata da abun yi sai shiga social
media, babu lazimi sam babu karatun Alqurani, Amani fa ko addua take son yi sai dai
ta roki Hamida tayi mata don a cewar ta bata iya hana idon ta barci, kuma Hamida ta
fi ta juriyar tsayuwar dare. A hakan da yake yi ya samu ya rarrage ayyukan kamfani
da yawa ta yadda yanzu da ya dawo ayyukan basu cude masa ba, ko da yake yanzu
ayyuka sun karu masa tunda shi yake gudanar da duk wanda Alhaji ke yi da kan sa a
lokacin da yake da lafiya.
Aka yi wa Alhaji Sadi iso falon Alhajin, bisa umarnin Alhajin. Yana shiga ya ga
Alhaji cikin wheelchair a zaune yana kallon talabijin. Alhaji Sadi ya ce Ya salamu
sallim, ashe ciwon babba ne haka? Yanzu da wadanne kafafu zaka yi takara? Kai bana
jin ma jamiyya zata yarda in tsayar da mai shanyayyen barin jiki kan kujerar gwamna
tunda ba ni kadai ke da jamiyyar ba.
Sannan ya zauna gefen sa ya bashi hannu yana fadin sannu, sannu yaya jikin
naka? Kana iya magana dai ko?
Alhaji ya ji ciwon wadannan maganganu na Alhaji Sadi, amma ko a fuskar sa bai
nuna ba, sai yayi murmushi yace ai ba sai ka gaya min na zama mara amfani ba yanzu,
nima na sani, na kuma yarda duniya da dan Adam duka ba a bakin komai suke ba, yau
ne kake mutum gobe zaka iya zama rabi gawa ko duka gawa, na yi kurakurai masu yawa
a rayuwa ta dana ke neman yafiyar ubangiji a yanzu ba takara ce a gaba na ba, tuni
na dade da janyewa.
Yanzu zan maida hankali na ne akan ibadah da neman guzurin lahira da nemawa
diya ta kyakkyawan Future.
Da kyau. In ji Sadi Talle, wannan tunani ne kayi mai kyau, amma ina fatan ba
zai shafi yarjejeniyar mu ba. Ka fadi duk abinda kake so daga gare ni in yi maka,
koda tsayar da wannan balaraben yaron naka ne na ga alamun sa jajirtacce ne kuma
namijin duniya ne ko daga takun sa, yana da leadership appearance, amma bayan ka
bani auren Amani, yau da shiri na na zo don muyi ganawa ta musamman da ita.
Alhaji yayi murmushi ya ce yadda na fasa takara haka na fasa aurar da ya ta,
zan bata yancin ta ne na tafiya karatu ta kuma kawo duk wanda take so da kanta na
aura mata, ko da kuwa kai din ne, don haka a adalci irin nawa, na baka damar ganawa
da Amani yau, ka ji raa yin ta a kan ka, ka nemi soyayyar ta, in ta amince zan fi
kowa farin ciki tunda ba yau muke tare ba na san baka da matsalar da zaa hana ka
aure.
Idan kuma Amani ta ce bata yarda ba sai kayi hakuri ka nemi wata. Ina Mukhtar
ina tsayawa takarar gwamnan Katsina shi da ba ma dan kasar Najeriya ba? Baabzine ne
fa!

Alhaji Sadi sai ya rasa abin cewa, amma tabbas ya ji dadi da Alhaji ya bashi
damar ganin Amani.
Ya dauki wayar sa ya kira Amani, da kyar ta daga cikin magagin barci, ta fara
korafi Daddy ka san gajiyar da ke jiki na kuwa ka tashe ni da safen nan? yi hakuri
Tafisu, sauko yanzun nan amma kisa mayafi don na san ki da shirme. Kafin ta ce
komai ya kashe wayar sa ya barta da mamakin ko lafiya yake fadin tasa mayafi?
Saboda ya ji Mukhtar din sa na korafi shine shima yau ya koya, wato duk inda
takurawa take sai Mukhy ya nemo mata ta hanyar juya kan baban ta da irin raayoyin
sa na akida.
Tana mitar tana komai ta saka Abaya da mayafin ta da silifas din bakin gado,
tana saukowa suka hada steps da Haj Rabi saura kadan Hajiyar ta bangaje ta, Amani
ta kauce. Haj. Rabi ta ce ji mana? Amani ta dan dakata da sauka daga steps din ba
tare da ta juyo ba. Haj. Rabi ta tako ta iso bayan ta ta soma magana cikin zafin
murya.
Jiya na nemi saki a gun Baban ki don na fi karfin yi wa mai shanyayyen jiki
takaba ko jinya, ni ba gado ba ba komai ba, ya ce magana tana hannun ki, ke kika
hana shi sallama ta da tuni ya sallame ni. To don uwar ki ke kike aure na da zaki
hana a sake ni?
Da sauri Amani ta girgiza kai don bata taba jin wanda ya zagi uwar da ko gani
bata taba yi ba sai yau, wadda duk da bata san ta ba, zuciyar ta cike take da
kaunarta.
Haj. Rabi ta cigaba da cewa.
idan kin haifu cikin Usman da Jalan yau ki sa ya rubuta min shika uku, idan
kuwa kin ki, in kun ki ji ba kwa ki gani ba. Don wallahi sai na saka masa filo a
hanci na karasa shi, ko in saka masa shinkafar bera a abinci ya ci ya karasa, kuma
dole a bani tumunin takaba. Amani bata iya ta karasa jin maganganun Hajiya Rabi
masu neman fasa mata kwanya ba, ta wuce falon Alhaji da sauri. Ta fado dakin cikin
gigita tamkar an jefo ta.
Zata yi magana ta ga Alhaji Sadi a zaune, ai kuwa fushin ta ya kara ninkuwa, ta
juya za ta koma. Alhaji ya ce Tafisu bakon ka Annabin ka.
Ba don jikin ta yayi sanyi ba ta dawo ta zauna, sai don bata son kunyata Baban
ta a idon Sadi Talle. Ta daga ido tace me kake so a wajena Malam? Alhaji ya soma
gurgura kujerar sa mai tayoyi ya koma cikin dakin barcin sa ya bar su a falon.
Babu kunya babu tsoron Allah fuskar sa kamar gonar auduga ya ce me kuwa na ke
so ban da soyayyar ki Amani? Wadda nake fatan ta kai mu ga aure nan ba da jimawa
ba?
Amani ta yi kuta, ta ce ina maka kallon Babana ba don haka ba da na ce an yi
furfurar banza, ka so hada ni rigima da Babana Allah ya fi ka, yana zaman zaman sa
ka sa shi a damuwar data kai shi ga faduwa, wani ya baka aure na ka bashi takara
shin Katsinar taka ce? Halan bai gaya maka cewa ta lafiyar sa yake ba yanzu ba ta
sayar da yar sa ba? Aikin banza aikin wofi to bana son naka, ko a kafa aka daura
min kai zan kunce in zura da gudu Alhaji Sadi ya ce ke mara kunya! Ya ishe ki haka,
kada kimin gorin halitta don duk muni na ban kai na uban ki ba. gara ni ina iya
auren shi kuwa me yake kullawa matar sa sai dai ta je waje. Don haka kada ki sake
ki zage ni yanzu in tattaka ki a wurin nan.
Sai gani suka yi an daga labulen dakin an shigo da sallama. Mukhtar ya bayyana
a falon cikin bakaken shirt da wando na NEIMAN MARCUS, sumar nan nannadaddiya ta
sha gyara da Argan Oil tayi lub a kan sa har ta sauka kadan a kan wuyan sa. Amani
na ganin shigowar sa, bata san me yasa ba, sai taji duk wani rauni na duniya ya
rufto mata, ga bakin cikin aj Haj. Rabi da tsoron kalaman ta, ga na wannan mutumin,
ji tayi tamkar wani savior ya zo gabanta don ya kawo mata dauki, kawai sai ta mike
ta nufi Mukhtar da azama ta rungume shi ta fashe da kuka mai karfi.
Mukhtar ya kusa suma a tsayen da yake, sai kawai ya tsaya kamar an kafe shi a
bakin kofar ya rike Amani dake kara neman mafaka a kirjin sa, yana kokarin zamewa
tana kara rike shi, sai ya ga abin kamar a cikin mafarki amma duk da haka ya iya
saita kan sa. Tsawa ya daka mata ya ce sakar ni nace, bana son sakarci.
Cikin jin kunya ta cika shi tana kuka tana nuna Alhaji Talle. Ka roki Alhaji ya
yi min iyaka da su, shi da Haj. Rabi, ka roki Alhaji kada ya kara bawa mutumin

Please Login or Register in order to submit comment