You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Alhaji Sadi ya kasa barci a tsayin daren bakidayan sa?
Me ya sa yake kishin ganin ta babu lullubi (mayafi?) ta fito waje ma'aikata
maza na kallon ta, don duk lokacin da ya gan ta babu lullubi a gaban maza sai ya ji
zuciyar sa kamar ta tarwatse. Duka wadannan alamu ne na So, don ba a kishi sai da
So, sai dai son bai zo a muhallin da ya dace ya zo ba, wato Amani ubangida ce a
gare shi, sannan ba ta da tarbiyya da cikar addinin da mutum irin sa za ya so ta,
har yayi fatan ta zama uwar yaran sa. Ko ya aura ya kai gaban iyayen sa su karba
cikin sauki.
Ya taso a gidan da ba'a san komai ba sai mutumta Dan Adam, tsatstsaurar
tarbiyyah ga 'ya'ya maza da mata, gidan rikon addini da dattaku, gidan da dan gida
ba shi ne Da ba, gidan da DAN RIKO daidai yake da dan gida har wani lokaci ya fi
shi sakewa.
Amani Faskari ta dade da satar wani kaso mai girma a zuciyar sa, wanda zai iya
cewa daga Allah ne kawai, ban da haka in kyau ne ya baro mata ma su amsa sunan mata
da suka dame ta suka shanye a kyau, dukiya, ilimi da gatan da take takama da shi.
Amma babu wadda ta taba saka shi a irin situation din da yake samun kan sa a duk
lokacin da ya ga Amani. Something like miracle, (abin kamar karama) tana da wannan
boyayyen tasirin a kan sa.
Mukhtar ya shiga ambaton innalillahi wainna ilaihi rajiun, wannan wace irin
masifa ce ke neman hawa kan sa? Ya yarda da auren Amani ya yi ya ya da ita da
rashin kunya da rashin tarbiyyar ta? Wadda ba ya tunanin ko karatun sallah ta iya
daidai. Above all aure a gare shi a yanzu na nufin komawar sa gida, wanda bai taba
shiryawa nan kusa ba. In Alhaji ya dage a kan bakan sa na aura masa fitsararriyar
yar sa wa zai karba masa auren? Tunda ya san babu kowa nasa a kasar Najeriya?
Kodayake Alhaji ya dauka iyayen sa sun rasu ne, shi ya sa ba ya takura masa a kan
zuwa gida, duk lokacin da ya ce ya je ya gaida dangin sa zai ce zai je ne ba ya so
ya tafi ya bar masa ayyuka da yawa ya sha wahala, har Alhajin ya gaji ya daina masa
maganar zuwa ganin dangin sa don ya dauka ma iyayen sa sun rasu.
Yanzu kuwa da Alhaji ya bullo masa da zancen aure sai ya ji wani sako na
zuciyar sa yana missing gida, yana kewar Diffa. Sama da komai yana kewar UMMAMIn
sa.
***** ***** ****
AMANI
Zamu iya cewa yau Amani dan karamin kwancewar kai ne ya same ta a dalilin
furucin Alhaji gareta. Wasu notuka a cikin kan ta ta ji sun kwakkwance tsabar
rudanin da mahaifin ta ya jefa ta. Ta nufi cikin gida tana tafiya tana hada hanya,
saura kadan su yi karo da Hajiya Rabi da ke kokarin hawa benen Alhaji. Ai kuwa ta
bangaje Hajiya sai da ta kusa kai wa kasa don ba ta zaci bangazar ba, duk da ta ga
Amanin ta taho a fusace kamar kububuwa, ta ce a ranta, mai yiwuwa ita da baabzinen
Alhaji ne, don ta san shi kadai ya tsaya wa Amani a makogaro ta kasa fyato shi. Don
ya fi karfin ta a gun Baban ta.
Hajiya Rabi ta dafa bango kafin ta kai kasa, ta ce, Ni ki ka bangaje? Kwaya ki
ka sha da ba za ki dinga lura ba kina tafiya kai a sama kamar zakanya? Ai ba ni na
kar zomon ba, ko ratayar sa ba a ba ni ba, jairar yarinya tatacciya, mara kunya,
goyon namiji.
Amani ta sa kafa zata hau bene kenan, jin abin da Hajiya Rabi ta fada ya kara
tunzura ta, da ma ya ya lafiyar Kura? Alhaji ya gama kaskantata da cewa zai bada
sadakar auren ta ga yaron sa da ta fi tsana a duniya, wannan annamimiyar kuma ta ce
mata goyon namiji? Bari ta nuna mata goyon namiji.
Ta wawuri Hajiya Rabi ta maka da kasa, da ma Hajiyar ba ta da jiki sam, Hajiya
ta zuba ihu amma ba wanda ya jiyo ta sai Rakiya mai aikin Amani. Ita ta zo ta rike
Amani da ke huci kamar maciji ya sare ta.
Rakiya ta shiga lallashin ta tana fadin, Uwar daki na mai abun alheri, Hajiya
babar ki ce, a dinga hakuri, uwar ki ce kamar kowacce uwa tunda Alhaji na auren ta.
Ki yi hakuri ki wuce sama, bana so ki karasa gawar da ba taki ba. Ko ba kya ganin
babu tsoka a jikin ta? Me za ki dauka in kin dake ta?
Amani ta soma hawaye, wanda ba ta san yaushe suka zubo ba, zafi biyu ne ya
tarar mata, ta ce, Rakiya bar ni in zubar mata da hakora don ta fi tabbatarwa ni
jaira ce, tatacciya, mara kunya, goyon namiji.
Rakiya ta yi maza ta ce, Wane mutum? Wane ita ta yi miki wannan zagin duk inda
alkhairi yake ga talaka kin iya shi, zagin data yi miki ba zai rage ki da komai ba
tunda ba ya fitowa a goshi. Kowa ya san albarkacin ki ta ke ci da ta yi wannan
dadewar a gidan nan.
Da haka Rakiya ta samu ta lallashi Amani ta raka ta har dakin ta ta dawo sannan
ta tada Hajiya da ke kuka tana fadin, yau sai Alhaji ya sake ta kafin mahaukaciyar
yar sa ta karya ta a banza.
Tana tashi wurin Alhaji ta nufa, lokacin Mukhtar bai dade da shigar da shi
dakin barcin sa ba, shi kuma yayi masa sallama ya tafi gidan sa. Alhaji yana
kakkabe filon sa zai kwanta, Hajiya Rabi ta fado dakin tamkar an jefo ta.
Biro da takarda ta dauko ta kawo masa har kan cinyar sa ta ce, Sakar ni, na ce
sakar ni, kafin in sa filo in danne ka wallahi. Ka haifi jaraba, ba tarbiyya ba
ganin girman na gaba, in sha Allahu ita ce ajalin ka!
Alhaji Usman ya ce, Innalillahi wainna ilaihi rajiun. Kawai sai ya karbi
takardar ya rattaba wa Hajiya Rabi saki. Ya ce, Duk abin da ke sassan ki ki kwashe
ki tafi da shi na ba ki, amma tunda ki ka muzanta Amani da mugun kalami irin haka
na gama auren ki, da ma ita ta ke roko na in zauna da ke.
Bakin halin ki babu wanda ban sani ba da yawon ta zubar da cin amana ta. A
sauka lafiya Umma-ta-gaida-Assha.
Amani da ta shiga daki duk da lallashin da Rakiya ta yi mata amma zuciyar ta ta
kasa yin sanyi, sai tafasa ta ke yi abubuwa goma da ashirin, sai kawai ta hada kai
da gwiwa a tsakiyar gadon ta tana rera kuka tamkar marainiya. Ko da yake ita da
marainiyar da uwar ta ta mutu ta bari tun haihuwa ai ba su da maraba, don ko hoton
mahaifiyar ta Alhaji bai taba nuna mata ba.
A yau tana kewar mahaifiya ko yar uwa mace, ko dan uwan da za ta kai wa kukan
ta, ko wani babba a dangi da za ta kai wa karar Daddy a kan kasksanci da tozarcin
da yake shirin yi mata (a wurin ta).
Aure da Mukhy shi ne mafi kaskancin abin da Daddy zai yi mata da ba za ta taba
iya yafewa ba. Kuma ko sama da kasa za ta hadu, ba za ta yarda ba, za ta gudu kawai
wajen mahaifiyar ta su neme ta su rasa, za ta cire kudade anyhow ta biya mai yi
mata bincike kawai ya turo mata adireshi ta koma wajen mahaifiyar ta. Ta yarda
yanzu Alhaji ya fi son Mukhy tsintacce a kan ta.
To za ta bar musu gidan, gabanin bashi auren nata. In yaso Alhaji ya maido
Mukhtar dakin ta na gidan sa ya zauna madadin ta karshen kaunar da zai nuna masa
kenan bayan ta bashi sadakar auren ta.
Hamida ta fado mata a rai, ta share hawayen ta dauki waya tana dialling lambar
Balewa. Duk da ta san maganar Hamida kullum daya ce, ta dinga yi wa Daddy biyayya,
yau ta san Hamida ko za ta tsokane ta to kuwa za ta taya ta bakin cikin masifar da
ta ke neman tunkaro ta.
Abokin kuka aka ce shi ake gaya wa mutuwa, duk da Hamida ba koyaushe ta ke taya
ta kuka ba, wani lokacin ma laifi ta ke ba ta, ba ta iya boye mata komai da ya
shafe ta saboda tsananin haduwar jinin su.
Ba jimawa Hamida ta daga waya da sallama, sai Amani ta daddage ta bude murya da
karfi ta fashe da kuka mai sauti, don da can mara sauti ta ke yi.
Kafin Hamida ta ce komai, sai da ta fara toshe kunnuwan ta da yan yatsun ta,
kada a fasa mata dodon kunne, sannan a hankali ta ce, MUKHY ne ko!
Ita ta san Amani ba ta da wata matsala a yanzu da ta wuce Mukhtar. Har ta saba
yanzu in Amani ta kira ta, to ta san Mukhtar ya kunso mata. Ita kuma ko kadan ba ta
ganin laifin sa, ina laifin mai son Baban ka? Mai taimaka masa?
Amani ta gyada kai kamar Hamida na kallon ta, ta ce, Shi ne Hamida, karewa ma
yau komai ya kare, tunda Daddy ya ba shi sadakar aure na.
Wata muguwar dariya ta kutsowa Hamida, ita da ma wannan so da Alhaji ke wa
Mukhtar ta san karshen tika-tika tik! Ko dai Mukhtar da kan sa ya ce yana son
kyakkyawar diyar ubangidan nasa, ko Alhaji ya hada da kan sa, don cikar kaunar da
yake yi wa Mukhtar da kara janyo shi jikin sa har abada.
Hamida ta yi dariya iya dariya, amma bayan ta kashe wayar ta. Sannan ta sake
kiran Amani ta ce,
Afuwan Habibty, network ne, na ji abin da ya faru, amma abu bai yi dadi ba, shi
ko Alhaji mai yasa zai yi haka? Bayan ya san ba kwa jituwa? To amma ke yanzu a
tunani da hankalin ki me ki ka yanke?
Za ki yi wa mahaifin ki mai son ki, mai kaunar ki, mai tattalin farin cikin ki,
mai hidimta miki iya rayuwar sa biyayya ne ko kuwa kasa za ki bada masa a ido?
Maganar Alh. Sadi fa? Ina ta kwana?
Amani ta yi maza ta ce, kada ki daure ni da jijiyoyin jiki na. Ai hakkin sa ne
ya so ni ya kula da ni, amma banda auren dole. Da ne Daddy yake so na Hamida, yake
kauna ta, yake tattalin farin ciki na da gudun bacin rai na amma banda yanzu.
Idan har zaki lura da kyau zaki gane Mukhtar kadai yake so yanzu, tunda har
yana fadin bai iya hada jinin jikokin sa da na kowa sai nashi.
Ta sake rushewa da kuka, ta ce, Hamdy, ina cikin tashin hankalin da Allah kadai
zai iya fidda ni. Tunda har Daddy ya yi wannan tunanin. Kin sani na ki jinin
mutumin nan da duk abin da ya shafe shi, tun yanzu sai abin da ya ce ma Daddy, ina
ga ya zama son inlaw din sa ko ya haifa masa jikokin da baya da su? Ai shikenan
kuma Daddy cewa zai yi ba ni ya haifa ba shi ya haifa.
Hamida na ta guntse dariya, ta ce, Fisabilillahi Habeebty me ye abun tashin
hankali a wannan abun arziki? Cewa nake da tsoho zai aura miki saan sa? Da ki ka yi
hakuri kika fawwalawa Allah kika kuma bashi zabi, nima kuma nayi ta taya ki da
addua ba gashi Allah ya amsa ya dube mu ba? Shi da kan sa Daddyn ya fasa ba tareda
rayuka sun baci ba, ya zabo yaro santalele ya baki, son kowa, yaro sabon jini mai
ilmi da nagarta, kuma mafi soyuwa a zuciyar sa?
Ai kawai Amani ki manta da wata kiyayyar ki maras hujja, maras madafa maras
dalili face envy dake damun ki a kan sa, ki bawa Mukhtar dama ki san ko shi waye a
wannan fannin, ta hanyar yi wa mahaifin ki biyayya.
This man is a treasure!.
Hamida ta karasa fadi kasa-kasa ba tare da ta san lokacin da kalaman suka fito
ba, tana jin dan wani kishi-kishi a ran ta. Domin tun ganin ta da Mukhtar na farko
ya tsaya mata a rai, ya kuma shiga zuciyar ta. Har Allah-Allah ta ke Amani ta kira
ta ta bata complain din sa don ita haka nan abun yana saka ta nishadi. Wato tana
son hirar Mukhy da Amani ke yawan yi mata duk da cewa bata arziki bace.
Amma daga ranar yau insha Allahu ba za ta kara saka komai a ran ta a kan
Mukhtar ba, sai fatan daidaita tsakanin sa da sahibar ta.
A tata fahimtar sun yi balain dacewa da juna, kuma ita ma kamar Alhajin tana
ganin ba wanda ya dace da Amani sai shi, ba kowa ne zai iya auren Amani ya kuma
jure zama da ita ba. Sai mai jan wuya.
Gara shi Mukhtar din, tunda ya san mutuncin mahaifin ta, mai yiwuwa kuma ya san
duka halayen ta tunda ba yau suke tare ba. Don haka zai iya hakuri da jure zama da
ita.
Ban gane me ki ke kokarin fada min ba Hamida?.
Hamida ta ce, Eh, ina nufin Mukhtar is a treasure ga duk macen da tayi saar
samun sa a matsayin miji kuma abokin rayuwa, hes a rare gem, sannan gashi mutum na
musamman a halayya da dabia mai dauke da dukkan attributes na cikar mazantaka. Ina
nufin. mutum ne daya cikin dubu, wanda kafin ki samu kamar sa a wannan zamanin sai
an tona.
Kamata ya yi ki gode wa Baban ki for giving you this treasure. Amani ta yi
maza ta katse ta da cewa, Ai sai ki zo ke a ba shi ke sadakar. Na yi rantsuwa duk
yadda zan yi in fidda kudin nan daga yau zuwa gobe zan yi in komawa mai binciken
nan ya ba ni adireshi da lambar wayar Mama na. Na rantse guduwa zan yi Hamida, da
in auri yaron Baba na kuma wanda ban san asalin sa ba, sannan mai mugun hali irin
na Mukhtar gara na gudu gun uwa ta ko a bukka take mu rayu tare.
Dama can na ki tafiya ne sabida Daddy da tunanin kaunar sa gareni, amma yanzu
na tabbata wallahi ya fi son bare a kaina.
Hamida ta kama kai, cikin cewa, Ki daina rantsewa Amani, Uban da ya haife ka
baya hada kaunar ka data kowa sai dai kawaici. Ba zan gaji da ce miki a kowanne
alamari da ya tunkaro ki, ki dinga neman zabin Allah ba, hakan shine daidai, kullum
ina gaya miki haka. Yanke hukunci cikin fushi kuskure ne babba, ki yi sallah rakaa
biyu ki nemi zabin Allah ta hanyar istikhara da Annabi SAW ya koyar, idan Mukhtar
alheri ne a gare ki da addinin ki, Allah ya sanyaya zuciyar ki ki karbi zabin
mahaifin ki da hannu bibbiyu. Idan babu alkhairi Allah ya sa Daddy ya janye da kan
sa, ba tare da kin bata da mahaifin ki ba.
Amani ta ce cikin hargagi. Daman na san ba za ki taba bin bayana ba a nan, ke
kadai ki ka rage min da zan ji sanyi daga gare ta. Ba irin bayanin da ban miki a
kan waye Mukhtar din nan ba, da rashin mutuncin da yake yi min, kamar ba a karkashi
na yake ci ba.
Amma kin ki ganewa da gangan, kullum sai dai ki yabe shi, saboda farar fata da
bakin gashin kan sa na rudar ki. Insha Allahu daga yau ba zan sake kiran ki in kawo
miki kuka na ba, don na san ba za ki share min hawaye ba in dai a kan Mukhtar ne.
Zan nemo mahaifiya ta da kaina in koma inda ta ke duk yanayin da zan same ta,
na san ita ba za ta taba yarda a yi min auren dole da wanda ba na so kuma ba zan
taba so ba, har duniya ta nade.
Ta kashe wayar ta tana kuka ta bar Hamida da mutuwar jiki. Ta fara yarda da
gaske Amani ba ta kaunar Mukhtar, ba yin kanta bane, tunda yau ta zabi ta koma gun
mahaifiyar ta bayan duk gatan da Daddyn ta ya yi mata a rayuwa. Yau ta zabi ta bar
shi. Ba ta san ya za ta yi ta ceto kawar ta daga fadawa fushin iyaye ba. Ko kadan
Hon. Usman ba irin uban da yaya za su bijirewa umarnin su ba ne domin bai ragi
Amani da komai ba, sai ma dai a ce soyayyar sa gare ta tayi yawa, har babu kawaici
a cikin ta. Ta yanke shawarar tahowa Katsina don ta taimaki kawar ta, don da gaske
tana kan dokin fushi wanda zai iya saka ta aikata da na sani ko ya raba ta da
mahaifin ta dungurungum.
A daren Hamida ta hau shirin tafiya Katsina a washegari.
Amani ta manta shaf da maganar tafiyar su Faskari, kuma ba ta san Daddyn ta ya
saki Haj. Rabi ba, ta bar gidan tun daren jiya. Ta kwana cikin mawuyacin hali da
tunanin Daddy ya daina son ta. A daren ta cire wadannan kudade naira miliyan biyar,
ba tare da tunanin komai ba, sai na son ganin mahaifiyar ta, ta tura wa mai
binciken kwakkwafin ta. Ta tura masa shaidar receipt ta layin wayar sa, tana yi
tana tuna alkawarin bogi da Mukhy ya taba yi mata na cewa shi da kan sa zai nemo
mata mahaifiyar ta on koboless. Amma ya nemo din? Tun daga lokacin har zuwa inda
yau ke motsi bai kara tada zancen ba, saboda ashe sun hada baki da Daddy za su
nakasta farin cikinta ta hanyar aura masa ita.
Allah Sarki rashin sani, domin kuwa ko a daren bayan ya koma gida, duk da halin
da yake ciki ya rubuta cikin schedules din sa na gobe cewa daga Faskari zai saka
Daddy a gaba da magiya da lallashi da ban baki irin nasa, ya yarda su wuce su kai
Amani ga mahaifiyar ta. Ba zai yarda Daddy ya yi mata aure ba da sani da sanya
albarkar Innar ta ba, in har tana raye.
Wannan wani alkawari ne da ya yi wa Amani, da yake da kyakyawar niyyar cika
shi, duk da rashin jituwar da ke tsakanin su. Ba ya daukar alamarin mahaifiya da
sauki, ko don irin son da yake yi wa tasa Ummamin, wadda bai samu tata soyayyar ba
shima, so he can feel for Amani, a kan rashin soyayyar uwa, wannan wani abu ne da
ba ya son tunawa a yanzu. Cikin kurakuran da yake so ya taimaka wa Alhaji ya gyara
ko hakki ya ragu a kan sa, har da kai Amani ga mahaifiyar ta.
Kuma alhamdulillahi tunda ya yi saa Alhaji ya amince, a lokacin da nadamar
abubuwan da yake aikatawa na kuskure ta zo masa.
To amma me? A washegarin ranar da asubahi yana kunna wayar sa da alert din
banki ya fara cin karo, mai nuna an cire kudi miliyan biyar, zuwa akawun din wani
Balogun Sunday. A take ya gane me Amani ke shirin yi, da ya tuna maganar su ta
rannan a mota.
Mukhtar ya kama kai cikin mamakin taurin kan ta. Wato ta yanke hukuncin data ke
ganin ya fi mata. Tafiya Sierra Leone ko ta halin kaka, da dai ta amince Alhaji ya
hada ta rayuwa da shi, don su kula da shi tare a kan lalurar sa har muddin ran sa.
A fili ya ce.
“Why Amani?
Gaggawa daga shaidan ne!.

Ya kuma tabbata don ta guje wa auren sa ne da mahaifin ta ya furta ta yanke
shawarar guduwa any how, ba ta kuma da inda za ta je da nisa in ba can din ba.
A take ya kira Alhaji, wanda a lokacin yana sallar asubahi a kan gadon sa daga
zaune kamar yadda yake yi. Ganin kiran Mukhy a daidai wannan lokacin ya san ba
lafiya ba, sai da wayar ta tsinke ya kuma idar da sallah, sannan ya kira shi da kan
sa.
Alhaji ka kula da takun Amani, kada a bar ta ta fita, ka sa ta a gaba mu tafi
Faskari tare da taki da ta so.
Ta fidda kudin nan da na gaya maka tana son fiddawa don a nemo mata Maman ta.
She is desperate Alhaji. A taimaka mata. Bayan ni da kai na na yi mata alkawarin ni
zan kai ta da kaina, zan nemo adireshin daga gare ka.
Na tsara in mun gama da Faskari, in roke ka mu bi jirgi zuwa Sierra Leone din
mu dangana ta da mahaifiyar ta. Ta yanke wannan hukunci cikin fushi, don haka ka bi
ta a hankali ka rarrashe ta mu tafi Faskari tare, sauran ka bar komai a hannu na.
Alhaji ya nisa, ba ya son kai yar sa ga Jalan da iyayen ta, don ya san Jalan
bata son sa, kuma bazata taba son sa ba, don haka bazata so jinin sa ba, amma ya ya
zai yi da Mukhtar tunda ya dage ya tsaya wa Amani a kan hakan? Jalan ta taya shi
rainon diyar sa ne ko ko ta taba tunanin ta tako ta zo ta gan ta ko sau daya?
Ai ta san inda ta bar yar in dai ba kiyayyar da ta ke masa ce ta shafe ta ba,
ya ci a ce ko sau daya ta waiwaye ta ta ga cewa ta rayu ko ta mutu?
Alhaji ya manta cewa shi ya raba tsakanin uwar da yar tun ranar da ta kawo ta
duniya, shi y araba wannan kaunar da hannun sa, ya bar Jalan a halin da ita ma ba
shi da tabbacin ta wuce ko ta rayu, Hausawa suka ce, laifi tudu.
Alhaji ya ce, Kada ka damu, I will take care of her kafar mu kafar ta zuwa
Faskari, in ka ga ta je wani waje bayan Faskari, to sai tana a matsayin matar ka,
bisa yardar ka da amincewar ka.
Biyayyar da ka yi min da kyautatawar ka gare ni Allah ya ba ka masu yi maka kai
ma. Allah ya sa Amani ta zamo alkhairi gare ka da addinin ka. Allah ya ba ku zuria
masu irin halin ka, ba masu irin nata halin ba.
Dan murmushin mamaki Mukhtar ya yi, yana so ya ce, Alhaji na furta maka na
amince ne? Amma kunya ta hana shi cewa komai, don karamcin Alhaji gare shi ya zama
abin kwatance, tunda har ya amince ya ba shi auren tilon yar sa ba tare da ya san
asalin sa ba, ba tare da ya san iyayen sa ko wani nasa ba, ba kuma tare da ya ga
mahaifar sa ba. Sannan ba tare da amincewar yar tasa ba, wadda kowa ya san ba ya
son bacin ran ta amma a kan sa ya yarda ya bata wa Amani karshen batawa da kan sa.
Ko don wadannan dalilan, da wasu da dama, sai ya ji ba zai iya badawa Alhaji
Usman kasa a ido ba. Zai rike masa amanar yar sa da dukkan halayen ta ababen ki, da
dukkan tijarar ta da rashin kaunar ta gare shi.
Zai

Please Login or Register in order to submit comment