You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa,
Daddy! Dariya ta ci karfin ta in ta tuno kamannin Alhaji Sadi, har ya fi
Daddyn ta muni da tsufa, da kyar ta tsahirta dariyar ta ce wato Daddy kawai kace ka
sayarwa da abokin ka yar ka Amani bisa yarjejeniyar siyasa, to wallahi ko shugaban
kasa zai tsaya maka ka samu bazan aure shi ba.
Ai ba mijin aure na rasa a duniya ba, da sani na nake korar su, don lokacin
aure na bai yi ba.
Duk duniya ban ga mijin da zan iya so ba Daddy, mai yiwuwa ma baa haife shi ba,
saboda ba kowa zan iya aure ba sai wanda zuciya ta take matukar so.
Alhaji ya ce Amani kada ki yi min rashin kunya, tsakani na da Alhaji Sadi amana
ce. abota ce ta kwarai, yafi karfin ya nemi alfarmar auren ki in hana shi.
Amani da yake kunyar ta ragagga ce sai cewa tayi Daddy ka rage son duniya, na
rantse da Allah ba don abota ka amshi wannan maganar ba sai don son Mulki, ka manta
cewa (power is transient), ammma farin cikin yar ka guda daya (has to be eternal),
ban san me kake nema kuma a duniya ba, da zaka mayar da ni hajar siyasar ka.
Ta soma kukan ta na halitta na shagwaba kamar marainiyar da aka fadawa mutuwar
iyayen ta, na yau har da sheshshekar kukan gaske. Kukan da ya fi komai dagawa
Alhaji hankali. Cikin kukan ta ce wallahi Daddy bana so, bazan aura ba, ta yaya
recently na gaya maka na samu admission ina so ka yi min izni in wuce Masters dina
zaka kawo wannan maganar?
Alhaji ya soma fusata yace to in ke kika haifi kan ki sai ki tafi Masters din
mu gani, magana na gama, na baiwa Alhaji Sadi auren ki, don kin ga ina sakar miki
da yawa shi yasa kika raina ni, karatu kin gama shi daga kwalin digiri ba kari,
dama ana ta cewa na barki babu aure. Amani ta mike tana cewa to Daddy sai ka zaba
ko ni ko abokin ka, idan aka takura min kan maganar nan na rantse zan sha poison in
mutu ka huta, da dai in auri wannan mummunan tsohon.
Gaban Alhaji ne yayi mummunar faduwa, exactly irin kalaman da mahaifiyar ta
Jalan ta furtawa nata mahaifin a gaban sa, ranar da ya bashi auren ta. Kuma tabbas
ta sha poison din bayan haihuwar Amani, bashi da tabbacin tana raye ko ta mutu, don
tun ranar da ya kai ta asibiti ya damka wa mahaifin ta takardar sakin ta, bayan ya
dauke jaririyar yar sa, bai kara waiwayar ta ba, a dalilin ta dade tana kunsa masa
bakin ciki mai yawa saboda kawai ita kyakkyawa ce shi ba kyakkyawa ba.
Allah wadaran masu aure don kyau, Alhaji ya fada a fili cikin tuno dararen da
suka shude tsakanin sa da Jal'an. Allah yasa kada Amani ta yo halin mahaifiyar ta
tarihi ya maimaita kansa tsakanin ta da Alhaji Sadi Talle, don shi aure da Alhaji
Sadi ya riga ya gama zartar da hukuncin yin sa ba zai fasa ba.
Amani ta wuce zuwa sama ba tare da ta san halin tunanin data jefa mahaifin ta a
ciki ba.
Ya dade a zaune a wajen yana tunanin mafita ko ta inda zai bullo mata ta yarda
da auren Alhaji Sadi, ba abinda yake hangowa kansa sai gashi a kan kujerar gwamna,
ya tuna Mukhy ma yace zai taya shi lallashin ta, da wannan tunanin ya shiga bayan
gida toilet na dakin sa domin ya yi wanka ya kwanta, yana sanya kafa cikin kwamin
wankan ya zame ya fadi a ciki, wata irin muguwar faduwa da ta yi sanadin kai Alhaji
Usman asibiti cikin daren, Allah ne ya kawo Haj. Rabi dakin taji karar da ya saki,
ta fado bandakin tana salati.
Maigadi da mai ban ruwan shukoki ta kira suka kinkimi Alhaji suka sa a mota,
Malam Tajuddeen ya tuka motar suka yi asibiti da shi. Sai da suka isa asibitin
Malam Tajuddeen ya kira Mukhtar.
A gigice Mukhtar ya zo asibitin, shi yasa hannu ya biya komai likitoci suka
soma baiwa Alhaji taimakon gaggawa.
Zuwa safe babban likitan da ke duba Alhajin ya tabbatar ma Mukhtar Alhaji ya
samu stroke wato rabin jikin sa ya daina aiki. Kasancewar dama yana da hawan jini
da suga masu tsanani.
Mukhtar ya saka fuskar sa cikin tafukan sa ya na ambaton innalillahi wainna
ilaihi rajioun. Tabbas dan Adam ba a bakin komai yake ba. Jiya jiyan nan suna tare
da Alhaji lafiyar Allah yana kasafta yadda zasu ci duniya da tsinke da kudin
talakawa idan ya zama gwamna yau a ce rabin jikin sa ya mutu?
Amani tana gida bata san abinda ke faruwa ba, tun dare take waya da Hamidah
tana kuka tana gaya mata Daddy ya daina son ta, zai aurar da ita auren dole ga
tsoho, kuma saan sa saboda siyasa. Tace Hamida na tabbata ba zugar kowa bane
wannan aikin annamimi Mukhtar ne, don ni Daddy bai taba yi min zancen aure ba, na
tabbata shi ya zuga shi tunda yanzu baya jin maganar kowa sai tasa, kuma na tsole
masa ido a gidan yana so a kawar da ni ya ji dadin cuta ma uba na. Ta fyace hanci
ta ce Hamdy na shiga damuwa don ban ga alamar Daddy da wasa yake maganar nan ba,
kamar auren da yake son yi min din is based on political aspiration din sa.
Hamidah yarinya mai hankali tace "wato Bestie ba zaki daina tsanar bawan Allan
nan ba babu gaira babu dalili? Zato zunubi ne, how sure are you shi ya zuga Daddy?
Ke da kan ki kin ce is based on his political aspirations sai ki cire Mukhtar a
ciki tunda shi ba dan siyasa bane. Ba lallai ya zama Daddy bai da ra'ayi sai nasa
ba, kamar kina exaggerating alaqar tasu. Sabida kin damu da shi, kuma ba kya son
sa".
Amani ta saki tsaki tace "na damu da shi a gidan wa? Ai ni kawai so nake ya bar
gidan mu" Hamida tace "ki ji da matsalar ki ta auren tsoho ki kyale bawan Allan nan
ya sarara" "shawara zaki bani ko zagi na za ki yi Balewa?" Hamidah na dariya tace
"duk wanda kika zaba shi zamu yi" ta ce "to shawara ta gaskiya nake so ki bani"
"shawara ta itace ki yi wa mahaifin ki biyayya whatsoever hujjar sa na aurar da ke
ga abokin sa, wanda yayiwa iyayensa biyayya baya taba tabewa.
A karshe ina so ni da ke duka muyi istikhara mu nemi dacewa da zabin Ubangiji
ba abinda zuciyar mu tafi karkata ba".
"Menene istikhara!" Amani ta tambayi Hamidah. "Sallah ce ta nafila da Annabi
SAW ya koyar ta neman zabin Allah kan kowanne al'amari da sulusin dare" Hamidah ta
gaya mata yadda zata yi. Ta kuma daure ta yi din. Ita da kan ta tayi mamaki ganin
cewa zuwa washegari data tashi sai taji ta wasai babu damuwa a dalilin istikharar
data yi. Har jira take Alhaji Talle ya zo yayi mata bayanin dalilin sa na kutsowa
rayuwar ta. Da abinda yake nufi da Baban ta, na cewa wani suyi yarjejeniya sai kace
an gaya masa ita hajar sayarwa ce.
Mai aikin ta ce ta kwankwasa mata kofa. Tana budewa a fusace tace "lafiya da
sassafe haka kike damuna da bugun kofa?"
Rakiya ta karya wuya ta langabe cikin lallashi ta ce "kiyi hakuri, Haj. Ce tace
in gaya miki ki fito ku tafi asibiti Alhaji na can babu lafiya". Gaban Amani yayi
mummunan faduwa, abinda ya zo ran ta shine irin rabuwar da suka yi ita da Daddy din
daren jiya, kada dai shi ya saka a ran sa har ya kwantar da shi rashin lafiya?
In haka ne kuwa zata yi masa biyayya iyakar iyawar ta ba Alhaji Sadi ba, ko
kuturu ya kawo ya aura mata zata yi biyayya da dai a ce wani abu ya faru da Daddyn
ta a kan ta.
Sabida gigicewa a haka ta fito da kayan barci a jikin ta, sai Rakiya ce ta biyo
ta da mayafi bakin mota.
A yadda ta ga Mukhtar zaune a reception din asibitin ya hada kai da gwiwa, yayi
jajawur abun ki da farin mutum ainun, hatta idanun sa sun yi jawur ya tabbatar mata
condition din na Alhaji ba mai dadin ji bane.
Ita ta sani ko Uban sa sai haka, a irin halin da ta gan shi a ciki.
Suna hada ido ya sunkuyar da kai, ta karasa da sauri tana tambayar sa me ya
samu mahaifin ta?
Mukhtar ba baki sai ido ya bi ta da shi. Ta koma ga Haj Rabi tana tambaya. Babu
wata damuwa a tare da ita tace "sun ce ya samu stroke ne, barin jikin sa ya shanye,
Amma zasu dinga yi masa gashin kashi har ya samu lafiya".
Daidai lokacin da aka gangaro Alhajin a kan gadon marassa lafiya aka bashi daki
na musamman.
Amani ta rasa inda zata tsoma ran ta, sai kuka take yi a dakin. Haushin ta ya
ishi Mukhtar yace "ko ki yi shiru ki yi masa addu'a, ko ki koma gida" ta galla masa
harara da jajayen idanun ta tace "Uban ka ko nawa?" Ya ce "to zage ni" ta yi tsaki
ta ce "in aka zage ka din me za'a yi?" Kai tsaye yace "banida lokacin ki yanzu,
amma ranar da kika kuskura kika zagenin, zaki ga me za'a yin".
Haj Rabi ta yi salati tace "Amma ku kuwa an yi sakarkaru, ta yaya mutun yana
kwance rai kwakwai mutu kwakwai kuna neman dambe da juna a kan sa? Ku kuma irin
naku hankalin kenan maimakon ku dukufa yi masa addu'a?"
Mukhtar ya juya ya fita daga dakin ya bar su. Amani ta nufi Alhajin da sauri ta
kura masa ido yana barci kamar ba abinda ya faru da shi. Hawaye fal idonta ta soma
magana.
"Daddy in dai a kan auren da kake son yi min ne ka saka kan ka a wannan yanayin
na roke ka ka tashi mu tafi gida, na amince ka aura min duk wanda ka ga dama, don
Allah Daddy". Kuka ya ci karfin ta.
Haj Rabi tace "toh? Ashe ke kika jawo masa? To ta Allah ba taki ba ban shirya
yin takaba yanzu ba, in bai tashi nan da sati daya ba wallahi sai dai ku sallame ni
don ban shirya yin takaba yanzu ba".
Amani ta juyo ta dube ta da fusatattun idanu ta ce "in kika kara shiga sha'ani
na sai na karawa wannan katon bakin naki tsini, ina ruwan ki da ni? Ko ina shiga
sabgar ki? In ni na jawo masa Uban ki ko nawa? Ko kin haifa masa ko gunduren kashi
ne? Ba tumunin takabar kike jira ba me kike so in ba shi ba?"
Haji. Rabi ta kama baki, tace "ke mara kunya, wadda bata ganin mutuncin kowa,
na fi karfin ki yimin diban albarka don uban ki nake aure, shashasha da bata san
komai ba sai sangarta da rashin kunya".
Likita ya shigo dakin ya na cewa "haba! Haba bayin Allah. Yaya zaku tsaya kan
mara lafiya kuna daga murya? To daga yau mun yafe zuwan ku. Mukhtar kawai muka
yarda ya zo har sai ya dawo gida".
Amani da ta riga ta zo wuya, ga haushin Mukhtar ga na Haj Rabi ga kuma na
wannan likitan yanzu. Ta ce "idan uban ka ne shi sai ka hana ni zuwa in gani"
likita ya juya ya fita kafin yarinyar ta soma kai duka, ya fara tunanin tanada
aljanu amma na rashin kunya da rashin tarbiyya.
Ta yi tsaki tana fadin "Daddy zan sa a dauke ka daga rubabben asibitin su ka
ji? Jidda zan kai ka a duba ka sosai. Get well soon my Daddy". Ta sunkuya ta
sumbaci goshin sa, ta gyara masa rufuwa da bargo duk Alhaji na barcin allurar barci
bai san me suke yi ba.
Waje ta fito tana tunanin abun yi, tana neman mataimaki da zai taimaka mata
wajen fidda Daddy saudiyyah. Amma Mukhtar shine yafi dacewa da ya taimaka mata din
gashi ta gama caccakar sa ta masa gorin Uba. Da sanyin jiki ta hau neman sa a
reception amma bata gan shi ba.
Bata san ma shi a lokacin yana can yana cuku_cukun samun visar tafiya da Alhaji
kasar Faransa ba.
Ya gayawa Haj. Rabi niyyar sa ita kuma tace bazata jinya ba, saidai Amani ta
je. Ko kwai bata ajiye masa ba bazata jinyar shanyewar jikin sa ba, alhalin ko
tumunin takaba bai rubuta a bata ba komai na Amani ne. don haka ta karata da uban
ta ita kadai.
Mamakinta ya kusa kashe Mukhtar a tsaye, to dama ya bata hakkinta ne a matsayin
ta na matar Alhajin. Amma Shima baya so ta bi shi don baya jin zata yiwa Alhaji
kulawar data kamata, wannan aikin sai namiji kakkarfa.
Yana tsaye a gate din gidan suna magana da Malam Tajudden yana gaya masa
maganar zai tafi Abuja da Alhaji don Nemo visar tafiya asibiti a Paris. Amani ta
shigo gidan tare da Malam Audi Mai baiwa shukoki ruwa wanda shi ya tuka su zuwa
asibiti. Tajudden ya juya ya dan kalle ta sai yace da Mukhtar din ka sanar da
Amani?" Yace "kaima ka san wannan yarinyar bata cikin 'yan shirgi na saboda rashin
kunyar ta. Dazu har zagi na ta kusa yi fa Tajudden".
Malam Tajudden ya dafa kafadar sa cikin lallashi yace "ka yi hakuri ka manta,
na sha gaya maka sai kayi hakuri da ita in dai kana son albarkar Alhaji. Daure ka
gaya mata saboda hakkinta ne ta sani, son samu ma ku tafi tare ta zama a kusa da
mahaifin ta duk sanda ya bude idon sa ya ganta don itace sanyin idaniyar sa".
Malam Tajudden ya karasa inda Amani ke kokarin fitowa daga mota yace "ran ki ya
dade Malam Mukhtar na son magana da ke, a kan lafiyar Alhaji ne" Amani ta dalla
masa harara tace "shi kurma ne? Ko Kai ne bakin sa? Bana son kinibibi bace min da
gani".
Mukhtar ya karaso wurin yana cewa "in kika sake alaqanta ni da rashin ji sai
na buge bakin ki, wannan dattijon bai haife ki ba?" Ai kuwa Amani ta fusata fiye da
farko tace "ka fita hanya ta don ni ba tsarar yin ka bace, mai kama da jan kosai
kawai" ya kusa ya buge bakin nata ya tuna mace ce, ya kuma yarda Amani tayi fama da
juvinile deliquency a shekarun kuruciyar ta, wadanda suka mika mata har zuwa yanzu
da take shekaru ashirin. Bata ganin kan kowa da gashi.
Har ta wuce shi ta tuno maganar asibitin Alhaji sai ta dawo tana sosa keya tace
"for your information inaso zan kai Alhaji asibiti a Jiddah don ban yarda da
kwarewar wannan asibitin da ka kai shi ba".
Mukhtar ya hadiye haushin ta yace "France zan kai shi" tace "a wane dalilin
zaka kai shi inda ban sani ba?" "Saboda ni Dan sa ne idan baki sani ba, daga yau ki
sa a ran ki ba ke kadai ya haifa ba uwar tutiya da uban da bata iya masa biyayya"
"to ban yarda ba Jidda zamu je. Akwai asibitin da suke duba shi a can, tun ina
karama can yake zuwa". Musu ya kaure tsakanin Muktar da Amani, a karshe ya ce "wait
pls, wai in aka bar ki kika kai shi Jiddan zaki iya jinyar sa ne? Alhaji fa yanzu
komai sai an masa har wanka da tsarkin lalura, kina mace me zaki iya kulla masa? Na
fada miki ki sakar min komai kawai, don ba abinda zaki iya kullawa".
Idanun ta fal hawaye, don ta tsani a dinga nuna mata gazawa don tana mace.
Shima Alhaji haka yake mata, komai tace zata yi sai yace Mukhtar zai yi don ita
mace ce, shi yasa take kishin sa da cewa he snatched away her father's love from
her.
Mukhtar ya ga ta rasa ta cewa a wannan gabar, sai ya juya zai tafi ya bar ta a
wurin. Sai ji ya yi ta ce da siririyar muryar ta mara amo.
"To ka shirya tafiyar da ni, in ba haka ba hankali na ba zai kwanta ba in bana
tare da shi, ban kuma san halin da yake ciki ba".
Mukhtar ya daga gira ya ce "alright. Yanzu kika yi magana Ma'am".

At long last. Mukhtar Diffa ya sake yin nasara a kanta.
***** ****** *****

Kasancewar Mukhtar, Alhaji da Amani duk suna da 'Schengen Visa' yasa basu sha
wahalar gama shirin fita da Alhaji zuwa Birnin Paris ba. Inda tun kafin su zo
Mukhtar ya gama yi musu kowanne tanadi ta yanar gizo da asibitin Hôpital Saint-
Louis dake tsakiyar babban birnin kasar na Faransa wato Paris.
Ranar Lahadi suka daga zuwa Paris daga birnin tarayya tare da Alhaji wanda zuwa
lokacin yana cikin hayyacin sa sai dai baya iya motsa kowacce gaba ta barin daman
sa.
Tuni asibitin na Hôpital Saint-Louis sun shirya musu dakin da Alhaji zai yi
jinya. Babban daki ne na alfarma ciki da falo a rukunin dakunan physiotherapy
department.
Daga zuwan su kuwa bayan Mukhtar ya gama settling bill din asibitin, likitoci
na musamman suka fara yi wa Alhajin dukkan kulawar data dace da masu irin lalurar
sa.
Mukhtar da Amani dambe ne kawai basa yi kullum saboda sain sa, don a kan baiwa
Alhaji madara ko tea ma kadai kullum sai sun yi fada. Kowanne yace shi zai yi.
Mukhtar a hotel ya kama nasa dakin wanda ba shi da nisa da nan da asibitin. Amma
kullum tun safe har dare yana dakin majinyacin, shi yake yiwa Alhaji alwallah,
wanka, tsarki da komai. Tare da taimakon ma'aikatan jinya maza. Rannan Amani har da
kukan ta, tana fadin duk ya kwashe ladan ya bar ta. Bayan ita ce da uban shi dan
karo ne.
Mukhtar ba kasafai yake tanka mata ba amma a sanda ta fadi hakan sai da ya kusa
yin murmushi, amma ya shanye abinsa, kada ma ta ga murmushin sa, a ran sa ya ce na
ji din. Dan karo kore dan gida kenan!.
Shi ya san da ace gorin Uba na tsiro, da yanzu babu masaka tsinke a jikin sa
sabida gorin Amani na Alhaji ba Uban sa bane. Wani zubin yafi gane yayi mata banza
wanda hakan yafi kona mata rai, har gara ya amsa mata su yi wa juna wankin babban
bargo yadda suka saba tun a gida ta fi ganewa da samun biyan bukata.
Duk fadan nan da suke yi kullum Alhaji na jin su, don wani lokacin har sai ya
daga musu hannun sa mai lafiya alamar yana rokon su yi hakuri su bari. A ran sa ya
rasa dalilin wannan rashin jituwa, gashi yanzu duka burin sa ya taallaka a kan
mayar da su abokan rayuwar juna wato su zama maaurata karkashin inuwar aure shine
kadai burin sa na karshe a duniya. Kuma abinda zai bashi kwanciyar hankali a yanzu,
tunda ya yarda yanzu kam ya nakasa, ba ya jin kuma zai sake tashi a kan kafafun sa
nan kusa yadda yake jin jikin nan nasa. Sannan Alhaji babu baki. A kwance yake
kawai yana karbar treatment amma yana hankalce da duk wani takun sakar Mukhtar da
Amani mai saka shi a damuwa, don shi ba haka yake son gani daga gare su ba, so yake
ya ga Mukhtar na kula da Amani kamar yadda zai kula da kanwar sa ta jini. Ita kuma
ta dinga respecting din sa tamkar Yayan ta. hakan kawai yake so daga gare su.
Kullum Alhaji na hango kujerar gwamna daga nesa a idanun sa, sai ya ji wani
bakin ciki ya rufe shi. Tun farko me yasa ya jawowa kan sa maganar siyasar nan?
Bayan duk daukakar da ya dade yana samu a siyasa karkashin jam'iyyar Action
Congress? Watakila da bai kawo zancen ba da duk bai fada a damuwar data yi masa
wannan sanadin wahalar ba. Ya dade da sanin conditions din sa na hawan jini da
sugar Amma ya zo ya saka damuwar aurar da Amani a ran sa har ta kassara shi. Alhaji
Sadi din bai san suna yi ba, ko irin abinda zancen auren da yayi sanadi ya janyo
masa yanzu.
Bakin Alhaji ya karkace baya iya magana amma kwarai ya ke so ya gayawa Mukhy
maganganu da yawa masu matukar muhimmanci ciki har da son ya kira masa Alhaji Sadi
Talle a waya don ya warware yarjejeniyar su. Ya hakura da kujerar gwamnan, yanzu ta
lafiyar sa yake, zai baiwa Amani dama ta koma karatun da ta ke so a Jamiar da ta ke
mafarkin zuwa wato Queen Mary University of London har Allah ya bashi lafiya idan
ciwon sa na tashi ne. Idan kuma ba na tashi bane zai yi kokari ya cika umarnin da
zuciyar sa ke bashi akan rayuwar Amani dungurungum, wadda yake ganin shine kadai
mafita ga rayuwar ta da tasa!
Wadda ba zai taba bari ta rushe ta hanyar fadawa hannun mijin da ba zai rike
masa ita da so da kauna da amana ba, da kuma kiyaye mata dukiyar da ya karar da
shekarun rayuwar sa yana tara mata ta hanyoyi daban daban na yaki halak da yaki
haram, duk don ta ji dadi kada ta sha wahalar duniya. Wanda ta kowacce fuska ya san
Alhaji Sadi Talle bai cikin wannan tsarin na rukunin mutanen da ya ke yi wa rayuwar
Amani wannan tanadi.
To wa ya dace?
Zuciyar sa a take ta halarto masa da kyakkyawar amsa cewa ba wanda ya dace da
zama mijin Amani wanda zai cika dukkan wadannan attributes din da yake so a tare da
mijin Amani, ya zame mata garkuwa kuma mijin marainiya, ya tallafi dukiyar ta da
gaskiya, ya kuma saita dabiu da tarbiyyar ta da bai samu damar yi ba sabida tasirin
son da yake mata kamar Mukhy din sa. Wato yaron sa kuma mataimakin sa Mukhtar
Diffa.
**** ****** ****

Kamar yadda yake ga cutar stroke saidai a ji sauki ba dai a warke sumul kalau
gaba daya a lokaci guda ba, to hakan ce ta faru da Alhaji Usman Faskari da aka fi
sani da Hon. Faskari. Yau satin su guda kenan a asibitin. Ya ji sauki a cikin jikin
sa don yana gane duk wanda ke kan sa ya kuma fara magana amma bata fita sosai, yana
zama in an jinginar da shi a jikin filo, daga baya Mukhtar ya samu hanyar da zai
dinga jin abinda ke ran Alhaji, wato ta hanyar rubutu da hannun sa mai lafiya don
baa iya gane abinda yake fada.
Mukhy yayi sallama ya shigo dakin asibitin da Alhaji ke jinya hannayen sa rike
da ledoji na sayayyar abinci da yayo musu, a kalla likita ya ce zasu yi wata guda
anan kafin a basu sallama, Amani dake zaune dai- dai kan Alhaji ko ta amsa sallamar
tasa. Ta maida hankalin ta ga hirar da ya samu tana yi wa Alhaji cikin kunnen sa.
Wannan abu bai yi wa Alhaji dadi ba, yayi burun-burun din maganar sa duka basu gane
me ya ce ba amma Amani ta gane fada yake mata kan kin amsa sallamar Mukhtar, tayi
mirsisi kamar bata gane me Alhaji ke nufi ba, sai Mukhtar ya ajiye ledojin da ya
shigo da su akan bed side, daya a gaban Amani, ya karasa gaban Alhaji ya kama
hannun sa yana tambayar sa kome yake son cewa?
Alhaji yayi masa alama da ya bashi biro, Mukhtar ya dauko

Please Login or Register in order to submit comment