You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mukhy ne yayi parking a kofar falon yana
jiran fitowar Alhaji, amma duk da yadda ya kwantar da kai ya bata hakuri data fito
sai da ta tsarta masa miyau a fuska ta ce donkey, monkey, idiot!
Mukhtar na shirin fitowa ya dauke yarinyar nan da mari sai ga Alhaji ya fito
hanzari yan cewa yi hakuri Mukhy, ina jiran isowar TAFISU ne kada ta dawo bana nan
an tafi dauko ta yana daga ido kuma ya gan ta cikin uiform din ta ta doso shi da
gudu, Alhaji ya bude hannu yana Oyoyo! Da Tafisu na. Ta rungume Alhaji duk da ta
fara kirgen dangi ma a lokacin suka yi ta murnar su kafin Alhaji ya ce mata ta
shiga ciki, ya sa an shirya mata komai, gobe sabuwar matar da auro zata tare
bazatayi kadaici ba wannan hutun. Direban data tsartawa miyau shi ya dauko jakar ta
ya shigar mata da ita bayan yasa hankici ya goge fuskar sa, a ranar kuma ya ajiye
aiki a gidan su Amani.
Mukhy da Alhaji suka kama hanyar Bindawa, Mukhtar ke tukin Alhaji na gefen sa
yana bashi labarin itace tilon yar sa Amani da yake bashi labarin tana makarantar
kwana, ya ce ka gan ta Tafisu akwai rigima ga kyuya, nikadai nake iya mata. Ai
komai nata na uwarta ta debo, yadda Jalan haka Tafisu take, kullum ina godewa Allah
da bata debo kannina ba
Mukhy dai tuki yake bai ce komai ba, amma a ran sa ya ce ai gara da kamannin
naka ta debo, da wannan halin nata na rashin kunya, yar karama da ita da raina na
sama da ita. Shi bai taba ganin rashin tarbiyya irin na yau ba. Imagine in shi ta
yi wa abinda ta yiwa Malam Sirajo, wallahi sai ya mare ta, kuma daga ranar ko nawa
ake biyan shi bai kara aiki a gidan su.
Basu kuma kara haduwa ba har ta koma hutu, don shi ba wani zuwa gidan yake ba
sosai, idan ba Alhaji ya neme shi a gida ba, duk harkokin su a kamfani suke yin su.
Ya zama cewa in tazo hutu sau tari ya kan gan ta ko daga nesa ne, a harabar
gidan ko a falon Alhaji, itama ta kan hango shi daga can saman balcony na saman
benen ta, ko a falon Alhaji in suna ganawa ta sirri, wani lokacin ta kan shigo, in
ta gan shi sai ta koma, bata taba gaishe shi ko yi masa magana ba, shi dai ko
gaisuwa bata hada su tun da ya gane bata da kwalli a idon ta, sannan Alhaji baya
kwabar ta, ta raina duk wani maaikaci na gidan, aka ce hanyar lafiya a bi ta da
shekara, sosai ya kama kan sa, ko ya ganta zai bar wuri shima, don ya san zuciyar
sa ba irin ta sauran maaikatan Alhaji bace, da suke iya shanye duk wani rainin ta
da wulakancin ta saboda Alhaji.
A haka suka rayu tsayin lokaci a gidan Hon. Usman, ko in ce tsayin shekaru, har
Amani ta soma zama budurwa sosai, babu wata sanayya ko wani cordial relationship a
tsakanin ta da Mukhy.
Tana gama sakandire ba jimawa ta samu gurbi a Jamiar Bauchi, da taimakon Baban
Hamida, suka fara karatun su ita da Hamida Hashim Balewa a ATBU, sai rayuwar ta ta
koma Bauchi gabadaya, ko an yi musu hutun karshen zango ba koyaushe take zuwa
Katsina ba saboda bata shiri da Haj. Laura ko kadan, wato sabuwar amaryar gidan su
matar da Alhaji ya auro a lokacin, sai tayi zaman ta gidan su Hamidah sai dai shi
Alhaji da kan sa yayi ta zaryar zuwa ganin ta, don harr aba su dambe aka yi kwanaki
tuni Alhaji ya yanke shawarar sallamar Haj. Laura don itama kamrar sauran, ta kasa
da Amani sabida rashin tarbiyyar ta. A haka Amani ta kammala jamia ta yi hidimar
kasa duk a Bauchi din.
Daga lokacin ne Alhaji ya maida Faskari Investment ya koma da suna Amani
Faskari Investment ya maida hakkin mallakar komai nasa da sunan ta.
**** **** ****
Ta haura sama inda dakin ta yake tana gaya wa kan ta in har Daddy ya dage
lallai sai Mukhtar ne zai taimaka mata wajen gudanar da tafiyar shagon ta, to kuwa
zata hakura da shagon.
Ita ta san kasuwanci ai ba sai mutum ya karanta shi ba ne zai iya tafiyar da
abun sa, karatun ta na International Relation and Diplomacy ya ishe ta komai, kawai
Daddy ya bar ta ya ga iyawar ta, ya daina underestimating din ta don tana mace,
bata bukatar taimakon Mukhtar a dukkan shaanonin ta.
Shi kuma Daddy abun nasa kamar wanda aka camfa, ko aka sihirce, from all
indications, baya samun gamsuwa idan ba ya hada shaanin kasuwancin sa kowanne iri
ne da Mukhtar din ba. Idan Mukhtar yana tsaye akan abu, ji yake kamar shi da kan sa
ne ya tsaya ya kula da abun sa. Tsabar yarda da aminci. Don haka ta san ko me zata
fada a yanzu ba zai yi tasiri ba, kowanne irin bore zata yi Daddy ba zai saurare ta
ba, in dai a kan kada Mukhtar ya saka mata hannu ne a ragamar Boutique din ta.
Tunda shi Ya riga ya yi amanna cewa komai nasa sai Mukhtar ya saka hannu ne zai
tafi dai-dai.
To ita bata son taimakon nasa a kan komai nata, a bar ta tayi irin tata iyawar
da kokarin, a boko-akida irin nata what man can do, a woman can do better.
Ta shaki iska cikin fushi sannan ta furzar ta bakin ta. Ba wanda zata gaya wa
damuwar ta a kan mutumin nan ya fahimce ta sai Hamida Balewa. Aminiya daya kwal da
bata da tamkar ta, duk da nisan gari da ya raba su yanzu, kullum suna tare a waya,
hakannan suna ziyartar juna lokaci lokaci su yi kwanaki a gidajen juna, dama an ce
garin masoyi ba shi da nisa.
Zamantowar Hamida a Bauchi Amani a Katsina bai rage komai na karfin amincin
dake tsakanin su ba. Har abinda ba zata iya gaya wa Daddy ba tana iya gaya wa
Hamida kasancewar bata da yar uwa mace, musamman matsalar matar sa ta yanzu wato
Hajiya Rabi idan ta saka ta gaba.
Ta san Hamida mai fadin gaskiya ce a kullum, kuma mai yi wa kowa adalci. Duk
da raayin su baya zuwa daya. Amma zata yi adalci tsakanin ta da Daddy a kan mutumin
nan, ta kuma bata shawara ta gaskiya na yadda zata yi da zaman sa a gidan su. Wani
banbanci dake takanin ta da Hamida shine an ce sai hali ya zo daya ake abota, amma
ita Hamida kowa dake tare da su ya san ba halin su daya ba, haduwar jini ce ta
mikar da abotar su domin Hamida Hashim, bata da girma kai, bata da dagawa sannan
bata raina kowa duk da kasancewar ta diyar tsohon gwamna.
Wayar ta ta dauka ta kira Hamida Balewa tana tsaye daga can saman balcony na
sassan ta dake saman gidan su. Daga inda take tsaye tana iya hango duk abinda ke
faruwa a yalwatacciyar harabar gidan nasu mai cike da korran shuke-shuke.
Yaya aka yi mutuniyas? Kwana biyu ban ji duriyar ki ba, halan kin fara shirin
tafiya Sierra Leone dinne? Hamida Balewa, ta fada bayan ta daga kiran aminiyar
tata.
Amani ta yi tsaki tana fadin Hamdy, ba ta wannan nake ba tukunna. Don wanda ke
min binciken inda Maman nawa take ta karkashin kasa ya bukaci wasu kudade masu yawa
a hannu na, wadanda ban san yadda zan fidda su ba a yanzu haka, ina nufin, ba zan
iya fidda su ba tare da shaidanin nan ya ga alert ba, kuma tabbas zai gayawa Daddy
a sanda ya gani din, idan kuma ya tambaye ni me nayi dasu bani da amsa don ya sha
ce min in na zabi bin Mama na ko neman inda take, to tabbas in manta cewa ya haife
ni, zai bar mata ni a kowanne hali na same ta, zai yafe soyayyar da yake yi mun
komai girmanta, tunda bai rage ni da komai ba na duka soyayyar UWA da UBA.
Actually har gobe ban san me yayi zafi haka tsakanin Daddy da Mama na ba, kuma
ina so in sani, sama da komai ina so in ga uwata nima kamar kowa in ji dumin jikin
ta tunda dai tana raye.
Amani ta soma hawaye tana fadin Hamdy, I want to see my Mum, ko sau daya ne a
rayuwa ta, koda a bukka take rayuwa a Sierra Leone din zan je gare ta zan kuma iya
zama da ita, ba kuma don Daddy ya min komai ba, ko ya gaza da kulawa da ni ta wani
bangaren, ba kuma don bana son cigaba da zama da mahaifi na ba, aah, shaukin
soyayyar uwa da ban taba samu ba ke diba na, so nake kawai in gan ta a gefe na,
nima in san cewa uwa da uba ne suka haife ni ba Uba namiji shi kadai ba .
Hamida ta ce Da yardar Allah zamu je ga Mama bada jimawa ba duk inda take, amma
bisa yarda da amincewar Daddy. Amma kamar yaya kike nufi in kika fidda kudi masu
yawa daga account dinki Mukhtar din Daddyn ki zai ga alert?
Amani ta numfasa tana fadin ba zaki gane ba Hamdy, Daddy na wani irin SMART
ne, mutane ne ke ganin yana sangarta ni, yana min duk abinda nake so, baya hada
kaunata data kowa haka babu abunda ya kai ni muhimmmanci a gun sa. Eh, hakane da
gaske amma kuma bai yarda da sakin rayuwata sakaka in yi abunda na ga dama ba,
musamman bayan haduwar sa da shaidanin mataimakin nan nasa, kullum sai kin gan shi
da sababbin dabaru na kiyaye dukiyar sa.
Zancen dana ke miki yanzu ko me nake so Daddy zai min, amma dole yaron nan ya
sani, kuma yana saka ido sosai akai na da abinda nake kashewa kullum ranar Allah ta
hanyar wannan fitinannen yaron, mai kwakwalwar huda-huda da ya hada account dina da
lambar wayar sa (corporate account).
Wallahi Hamdy na tsane shi bana ko son ganin shi, ba don komai ba sai don yadda
Daddy ya daukake shi yake girmama shi, yake fifita shi da daukaka shaanin sa a kan
kowa a gidan nan yanzu.
Karo na farko kenan dana kasa samun abinda nake so a gun Daddy; wato yaki yi
min abunda nake so kamar koyaushe na bukaci ya kori maaikacin da bai yi min ba,
wannan karon ya nuna min bai iya rayuwa sai da wannan mutumin, ya shiga gabana da
yawa a gun Daddy Hamdy, ko asiri yayi masa ni ban sani ba, Im extremely jealous of
him!”
Hamida ta soma dariya, dariyar da ta kara kular da Amani don ita tsakanin ta da
Allah take fada mata damuwar ta, damuwar da tafi kowacce girma yanzu a gun Amani
wato zaman MUKHTAR DIFFA tare da mahaifin ta Hon. Usman, Hamida ta hadiye dariyar
ta jin Amani na kwafa, tana fadin Amani ki taka a sannu fa, ki bi abin a hankali,
you are complaining too much about this guy, Kaman kina exaggerating abun ma, in
ban manta ba duk ranar da kika kira ni complain din sa kike fara yi min, baki saka
comma baki saka full stop, anya?
Baki fa san inda rana zata fadi ba, shaaah!
This dislike and hatered you have on him are beyond my understanding (kiyayyar
ki a kan sa ta yi yawa har ta wuce fahimta ta) kuma na rasa dalilin ta, ina laifin
mai son Baban ka, da taimaka masa kan dukiyar sa da shaanonin kasuwancin sa da
zuciya daya irin wannan mutumin, calm, cool and reserve da shi?
Ni wallahi ta koina ya yi min, kin ga dai daga nesa kawai kika taba nuna min
shi last zuwa na KT, kuma ban ga fuskar sa sosai ba sai bayan sa yana shiga mota,
amma ko daga tsayuwar sa da zatin bayan sa kadai mutum ya gani ya san Allah ya
ajiye namijin duniya a nan, haibar sa da kamalar sa sun tafi da ni, da duk nutsuwa
ta, kyawun sa ya tafi da Imani na na dade ban daina tuna shi ba.
Ki ga min mutum kamar shi ya yi kan sa don kyau, ga iya daukar wanka, ga iya
dressing, ga jan aji nna karshe, da iya takun tafiya, yana tafiya gib-gib tamkar
basarake, ga wani special class (aji na musamman), na kasaitattun maza. Watakila
saboda idon ki ya rufe da kishin sa da kiyayyar sa saboda son da Daddy ke masa ne
yasa baki hango abubuwan da ni na hango a tare da shi ba..
Babu shiri Amani ta katse wayar ta, bayan ta lailayo ashar ta yarfawa Hamida.
Haka kwana ta yi tana tsinewa furucin Hamida da Hamidar kan ta a zuciyar ta.
Washegari tun da Amani tayi sallahr asubah bata koma barci ba, ta zauna bisa
dardumar sallahr ta tana tunanin yadda zata yi ta fidda wadannan kudade daga
corporate account din, wanda Daddy ya bude mata shi ne don ajiyar jarin kasuwancin
ta kadai, ya kuma bude shi tare da sunan Mukhtar ne a matsayin Director kuma
sakataren ta, sannan kuma mai kaso daya bisa uku na abinda ke cikin asusun, Hon.
Usman yayi haka ne kawai ba don da gaske ya mallakawa Mukhtar din wannan kason ba
aa, komai na Amani ne, ya yi ne kawai don Mukhtar din ya zama spy din sa a kan duk
wani transaction na Amani da kuma sunan wanda ta turawa, ba don komai ba sai don
ya san ta da almubazzaranci da saurin mika wuya wa mutane, shikuma ga shi da son
abun hannun sa, bai yarda a ci da gumin sa ba.
Tun bayan zuwan Mukhtar wajen sa Hon. Usman ya fito da wannan idea din, ta
joining account din Amani da Mukhtar a matsayin corporate account na kasuwanci,
yardar da ya yi masa mai yawa ce, don ko dan sa na cikin sa ba zai sakarwa sirrikan
sa irin yadda ya sakar wa Mukhtar ba, yana jin takaicin almubazzarancin Amani don
shi ko wane sisi da kowanne kobo abu mai daraja ne a wurin sa, kashe kudin Amani ya
yi yawa, musamman ga dangin sa na Faskari, inda wani abu mai kyau guda daya tak
cikin halayen Amani to kyauta ce.
Amani tana da hannun kyauta wa na kasa da ita kasancewar bata san zafin kudin
ba, abun duniya bai taba rufe mata ido ba kullum hannun ta a mike yake cikin yin
kyauta ga wanda Alllah ya tsaga da rabon sa. Wani zubin tana sanin an cuce ta ko an
dafketa wajen sayen abu, amma bata damuwa don Alhaji kullum kara tara mata yake.
Babbar damuwarta a yanzu tana so ne ta turawa dan sandan cikin dake mata
bincike a kan inda Mama Jalan take a kasar Sierra Leone. Dan sandan ya bukaci
wadannan makudan kudaden da suka wuce hankali ne ganin yarinyar ta zama desperate a
kan neman mahaifiyar ta, kuma ya ga alamar akwai kudin tare da ita sannan bata son
shigar da kowa cikin maganar tasu.
A karshe Amani ta ga cewa babu mafita fa dole sai Mukhtar ya ga debit alert
dinnan, wanda ke nufin sanin Daddy, domin tabbas ne Mukhtar sai ya gayawa Daddy a
irin amanar da ke tsakanin su cewa ta fidda miliyoyin kudi don ta san dalilin
hadasu a account guda Kenan, don ko sau daya Mukhtar bai taba daukar wani abu a
ciki ba.
Don haka ta kai azahar a daki tana qulubi, tana bacin rai, ga shi dan sandan
cikin wato DSS din da ke mata aikin ya tabbatar mata data tura masa kudin da ya
bukatan a take zai turo mata adireshin Maman ta da ke Freetown wato babban birnin
Sierra Leone. Kai har ma da lambar wayar ta ya ce duk ya samo.
Amma sai ta fara biyan sa wadannan kudaden da ya kayyade mata tukunna.
**** **** ****
Abu daya da ta san bazata taba iyawa ba shine rokon Mukhtar alfarma, don tana
ganin bai yi wannan isar a idanun ta ba. Ba don haka ba da ta roke shi ya yi mata
alfarma ya rufa mata asiri sau daya a rayuwa, kada ya gawa Daddynta ta fidda 5
millions ta baiwa wani a boye domin ya nemo mata Innar ta. Idan Daddy yasa ta gaba
da tambaya da kwakkwafi (query) tabbas zai gano shirin da ta ke yi ta karkashin
kasa na son ziyartar mahaifiyar ta a boye.
Tana cikin wannan tunanin wayar ta ta hau ruri. Ganin sunan Daddy a daidai
lokacin da take tunanin sa sai da gaban ta ya fadi. Ta amsa a sanyaye.
My Daddy!
Daga can barin sa Hon. Usman ya ce Tafisu ki sauko falo na yanzun nan.
Iya abinda ya fada kenan ya kashe wayar sa.
Ta zura siraran kafafun ta cikin silifas din bakin gado sannan ta fita ba tare
da ta canza kayan barci farare samfurin Calvin Klien da ke jikin ta ba.

Falon Alhaji Hon. Usman Faskari, wani irin makeken falo ne wanda sai da ya ci
saitin kujeru uku iri daban-daban saboda girman sa. Ya kawatu da kayan alatu da air
condition ta tsaitsaye a kowacce kusurwa, komai na jin dadin rayuwa yaji a wannan
falo mai kama da palace, din wani gwamnan kai ka ce babu ranar mutuwa a zuciyar
mamallakin sa.
Amani ta shiga tako matattakala tana saukowa daga saman benen ta tana tafiyar
nan tata tamkar bata so.
Kallo daya Mukhtar da ke zaune gefen Alhaji ya iya yi mata a lokacin tana
saukowa daga stairs din, cikin takun nan nata tamkar na macen Dawisu mai ji da
kasaita, ya yi maza ya sunkuyar da kai cikin jin faduwar gaba don bai taba yi mata
kyakkyawan kallo ba, yau din ma kamar kullum, a sace ya kalle ta, amma ya ga surar
jikin ta sosai a cikin kayan barcin, sai ya samu kan sa cikin jin takaicin wadannan
sharasharan kuma bingilallun kayan dake jikin ta a matsayin ta na mace kuma Musulma
a cikin mutane, domin kamar kanwar sa ya ke kallon ta.
Har ga Allah Amani bata san da shi a falon ba ta riga ta saba gaida mahaifin
ta da kayan barci in har tana son su gaisa kafin ya fita, kasancewar sa maabocin
sammako. Tana cigaba da saukowar bugun zuciyar Mukhtar na dada karuwa, ba tun yau
ba hakan ce take kasancewa da shi a duk a lokacin da ya hangi Amani ko daga nesa
ne. Duk da dai wata kalmar fatar baki bata taba hada su ba. Amma Tafisun tun
dawowar ta daga ATBU take yi masa kwarjini sosai.

Tafisu na dauka tuntuni kin shirya jiran isowar Mukhy kike ya zo ku wuce ki
duba Boutique din naki?

Amani ta yi kicin-kicin da fuska cikin sakalci irin nata tace Daddy ai ba sai
mun tafi tare ba, yayi gaba, tunda yana da mota a hannun sa, ni inna kintsa na gama
breakfast na yi wanka sai in zo mu hadu a can.
A zuciyar ta kuwa fadi take Allah ya tsare ni da shiga motar sa, Allah tsare
ni hada hanya da shi.
Don dai ita Amani fisabilillah bata yarda hakanan Mukhtar ya bar baban ta ba,
tafi yarda da cewa asirin su na Diffawa yayi masa yake son sa irin haka, kada ta je
itama ya hada da ita ya dinga juyata yadda yake juya Daddyn ta.
Daddy ya ce cikin lallashi, amma kin san bana so kike tuki da kan ki ko Amani?
Tunda duk kin kori direbobin saboda masifar ki sai ki shiryo Mukhy yana jiran ki ku
tafi tare, ban yarda ki kara tuki daga yau ba, kada ki manta sau uku kenan kina yin
accident din da sai na biya diyya ga wadanda kike bugawa mota ta baya, tunda tukin
bai karbe ki ba, to a hakura da shi babu dole. Duk inda kike son zuwa ki kira Mukhy
a waya ya zo ya kai ki.
Amani ta hau tumami da kafa cikin shagwaba tana fadin "Ni gaskiya bazan daina
tuki ba, da koyo akan iya Daddy. Kuma da haka ne zan kware da tukin".
Hon. Yace "duk ba na ki ba, ina nufin for the mean time zuwa kafin ki koya din
nake magana, daga yanzu duk inda zaki Mukhy na yarda ya kai ki.
Shi kin ga bayan iya tuki na hankali, harda nutsuwa da sanin ciwon kai a tare
da shi.
Maza shiryo ki zo ku tafi kin ji Tafisu na? Bana son musu. TA FI SU KIN FI
SAURAN MATA!.
Ya fadi kirarin da ya san da shi yake lallashin ta, duk da tana cewa bata son
kirarin amma sosai mahaifin nata yake ciyo kan ta da shi ta yi masa abu idan ta yi
gardama, kamar wata karamar yarinya.
Fuskar nan ta Amani kamar hadarin da ya nausa yayi gabas ya juya yayi yamma.
Wato Daddy na nufin ita bata san ciwon kan ta ba kenan kuma bata da nutsuwa sai
Mukhy din sa. A fusace ta juya zuwa hanyar data fito, bayan ta zabgawa Mukhtar wata
hadaddiyar harara tamkar manyan idanun nata zasu fado kasa.
Mukhtar wanda kansa ke sunkuye yana danna wayar hannun sa bai san tana yi ba,
ya yi sallama da Daddy yana fadin zan jira ta a mota Daddy ya ce ka dai tabbatar da
lafiyar motar da za ku hau din ko Mukhy? Kuma Amani zata so hawan wadda ka zabo
din? Bata so tana tafiya a hanya mota ta samu matsala, kuma bata son dindimemiyar
mota. Mukhtar ya dan cije lebe cikin jin takaici, ya ce Alhaji kai ka ce min farar
Brabus ta fi son hawa, kuma ita na dauko, lafiyayyar mota ce.
Yayi kyau, to sai kun dawo, kada ka manta ka yi tuki a hankali bata son gudu,
ku dauko Hajiya a filin jirgi in zaku dawo, yau zata dawo daga Umrah da zarar kun
gama da boutique din sai ku je ku dauko ta, na san kafin nan jirgin nasu ya yi
landing don sai bayan azahar zasu sauka.
Ba tare da ya ce komai ba yasa kai ya fita daga falon. Takaicin yadda Alhaji ke
sakalta yarinyar sa ya fi komai bata masa rai. Amma shi ya isa yace wani abu? Shi
yasa take ma mutane kallon hadarin kaji kallon kowa banza ne saboda ta san Alhaji
ya daure mata gindin sakarci.
Mukhtar Yafi karfin mintuna sittin zaune cikin motar yana jiran saukowar yar
mulki Amani, har aka rufa awa guda da rabi babu Amani ko inuwar ta, tun yana duba
rantsatstsen agogon hannun sa swatch' dama na motar as well, har ya gaji ya
kishingida a kujerar direba, ya ware sautin radiyon motar yana sauraren waqar
mutumin sa mai debe masa kewa a duk lokacin da yake tuki, wato fasihin mawakin nan
Ba-sudane Mahmoud AbdoulAzeez. A rayuwar sa ba abinda ya tsana irin jira, to amma
ya zai yi? Umarnin Alhaji ne, kuma in an bi salsala Amani itace kamar second Boss
din sa bayan Alhaji. Dole yayi zaman jiran ta a mota, ta shanya shi iya yadda ta ga
dama.
Tun lokaci na farko da suka fara haduwa da Amani da ya fahimci dabiun ta na
sangartattu ne kuma bata ganin kan kowa da gashi yake taka-tsan-tsan da shiga
shaanin ta, yake kokarin kaucema haduwar su a yawancin lokuta, in kuma ta kure sun
hadun baya yarda ya yi

Please Login or Register in order to submit comment