You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan
damar gani na, tunda ya zage shi ya ci mutuncin sa. Alhaji Sadi ya yi tsaki ya
tashi ya fice daga gidan. A ran sa yana cewa ba don albarkar abota ba sai yayi wa
yarinyar nan asiri ta rasa mijin aure.
Mukhtar ya zuba hannayen sa duka biyun a Aljihu, ya zuba ma Amani ido tana ta
kuka, ta cigaba da cewa ka fada ma Alhaji na bashi wuka da nama ya aura min duk
wanda ya ga dama amma ban da wannan mutumin kuma na yi masa lamuni ya saki Haj.
Rabi. Ka rokar min shi ya gaya min inda uwata take, na yi alkawarin maido masa ita
gidannan ko tana so ko bata so. Amma ban yarda ya kara auren kowa ba in dai don
siyasa ne ya hakura tunda bashi da lafiya.
Tausayin ta ya tsirgawa Mukhtar har cikin ran sa, amma Mukhy da taurin rai irin
nasa juyawa ya yi zai bar dakin ba tare da ya ce mata komai ba. Amani ta tsanan ta
kukan ta tana cewa ka taimake ni!
Mukhtar saida ya dafa kofar ficewa ya juyo ya dube ta, da idanun sa da suka
kada suka yi jazir, ba abinda yake gani sai Amani zaune da Alhaji Sadi suna zance,
in the first instance ta san bata son shi me ye na saukowa kasa har ta kebe da shi?
Sai don ya zage ta zata zo masa da wasu zantuka da basu shafe shi ba? A fusace ya
ce me yasa sai ni? Me yasa sai ni zaki aika na gaya wa Alhaji sakon ki? Baki da
baki? Baki fi ni kusa da shi ba? Ko ko ni dan aiken ki ne? Mtsw!
Yasa kai ya fice daga falon, zuciyar sa da gangar jikin sa da Amani ta
makalkale suna vibrating. Kai tsaye mota ya dauka ya bar gidan zuwa nasa gidan da
Alhaji ya bashi wanda babu nisa zuwa na Alhajin.
Mukhtar yayi rigingine bisa makeken gadon dakin barcin sa ya na tuhumar kan sa
akan me ke faruwa da shi haka? Me ke addabar zuciyar sa? Me ke saka zuciyar shi
cikin jin zafin Amani, don kawai ya gan ta kebe da Alhaji Sadi? Shin abinda yayi
mata anya ya kyauta tunda yau ta zubar da makaman yakin ta ta nuna masa da gaske
taimakon sa take bukata???
Why is he so harsh on her??? Duka baya da amsar ko daya, don haka ya ci gaba da
tuhumar kan sa yana nemo hujjar kare kan sa daga tuhumar da ya samu zuciyar sa na
yi wa kana sa da kan sa a kan Amani.
**** ***** **** ****

Amani da zazzabi mai zafi ta kwana, don bata iya ganin Daddyn ta ba sai a
washegari. Shi da Mukhtar suna balcony Mukhtar na bisa fararen kujerun roba da aka
zuba a wurin suna Magana, Alhaji na zaune cikin Wheelchair din sa. Da alama
sensitive magana suke yi domin Alhaji har share hawaye yake yi da hannun sa mai
lafiya. Abubuwan da yake gaya wa Mukhtar yau ko Amani bai taba gaya wa ba. Yana
gaya masa tarihin sa ne da kauyen da ya fito wato Faskari da yadda duniya da dukiya
suka rude shi yayi abondoning dangin sa ko ziyara baya kai musu balle ya taimake
su, bayan dukkan su talakawa ne na gamu kashe mu masu tsananin bukatar taimako.
Yace Mukhtar ban san halin da suke ciki ba yanzu, bani da masaniyar suna raye
ko sun mutu sun bar yayan su na garari cikin babu, ban tashi tuna cewa ban tafiyar
da rayuwa ta dai dai ba sai yau dana nakasa, ina kuma son su yi min wani amfani
wato daura wa Amani aure.
Gaban Mukhtar ne ya yi bugawar dakikai masu yawa, kan sa ya wani irin sara. Ya
dauka Alhaji ya janye kudurin sa na aurar da Amani ga abokin sa? Ya tuna rokon da
ta rika yi masa jiya a kan ya taimake ta ya roki Alhaji ya fasa bata so, ko
cikakken sauraro bai yi mata ba sabida a wajen sa Amani ba mai cikakken hankali
bace.
Shi kan sa Alhaji, sai da yayi noticing canjawar da fuskar Mukhtar tayi.
Mukhtar bai ce komai ba a kan duka abubuwan da Alhaji ke fada masa, Alhaji ya
cigaba da bashi labarin rayuwar sa inda ya ce.
***** ***** ****




ASALIN HON. USMAN FASKARI

Na fito daga garin Faskari ta Jihar Katsina, mu uku ne a wajen mahaifin mu, mu
biyu cikin mu guda ni da Malam Idrisu. Dayar mace ce uwar ta daban wato kanwar mu
Sahura.
Malam Idrisu yana da bataliyar Iyali domin kuwa matan sa uku kowacce tana da
yaya maza da mata sun haura goma. Sahura an yi mata aure a garin Funtua. Ban san
adadin yaran da ta haifa ba.
Asali na fito birni ne neman ilmin boko, sabanin yaya Idrisu da yafi maida
hankali akan sanaar mahaifin mu wato Dukanci.
A rayuwa ta ina da burin in tara kudi, in kuma auri kyawawan mata in cika gida
dasu,duk da ana yawan cewa ni mummuna ne Idrisu ya fini kyau.
Nayi makarantar koyon kanikanci a garin mu Faskari, da mahaifin mu ya rasu sai
nayi wa yaya na da kanwar mu Sahura sallama na ce na tafi karatu birni. Mahaifiyar
mu a lokacin bata tare da mahaifin mu tana aure ne a wani gari Kaita. Duk dai a
cikin Katsina ne.
A wannan lokacin samun gurbin karatu a jamioin Najeriya ba abu ne mai wahala
ba, saboda gwamnati neman masu yin karatun take yi ruwa a jallo.
Na samu gurbi a Katsina state Polytechnic inda nayi HND dina a fannin
Engineering, daga nan na samu gurbi a Jamiar Bayero ta Kano, naje nayi digiri na na
farko akan Architectural Engineering. Na dawo Katsina na fada harkar siyasa.
Na shga siyasa da kafar dama, amma hakan bai hana ni shaawar kasuwacin kayan
gine-gine ba wanda akan sa nayi karatu na.
Alhaji Sadi Talle aminina ne tun na kuruciya a lokacin shi yana kasuwanci da
kasashen Africa. Shi ya sakani cikin harkar fitar da Aluminium Ore da Iron Ore daga
Sierra Leone zuwa kasar France. Kasuwanci ne wanda yayi mana sanadin samun arziki
mai yawa, wanda idan zamu dawo sai in saro kayan gine-gine daga can in taho dasu
kasar Najeriya.
Cikin dan lokaci Allah ya saka min albarka a cikin nema na. Na soma tunanin
wasu hanyoyin kasuwancin daban-daban har na samu na kafa kanfani na na farko wato
Faskari Investment, amma duk da haka ban bar siyasa ba.
Cikin irin tafiye-tafiyen da muke yi ni da Alhaji Sadi ne zuwa kasashen Africa
muka shiga Freetown wato babban birnin Saliyo, wannan karon mun zo ne musamman
neman matar da zamu aura, don mun jima muna shaawar auren kyawawan matan da ke
wannan kasa.
Abokin kasuwancin mu da muka dade tare shi ya gaya ma na hanyoyin da ake bi a
nemi aure a wannan kasa, yace yayan attajiran kasar basa auruwa ga bako sai yayan
talakawa, wadanda iyayen su ke cikin yanayi. Shi ya hada mu da mahaifin Jalan wanda
manomi ne a garin, kuma talaka ne sosai, tun a hoto naga Jalan kuma tayi min dari
bisa dari, na cika mahaifin ta da dukiya mai yawa ba tare da yayi shawara da ita ba
ya daura mana aure, ya kuma ce in dauke ta in tafi da ita. Shi kuma Alhaji Sadi ya
auri wata Jenaba wadda ita ta zame masa uwar yayan sa.
In takaice maka labari Mukhtar, ban sha ta dadi ba a hannun Jalan, domin bata
sona ko kankani, ni na san saboda muni na ne, don babu abin da ban mata a rayuwa ba
ita da iyayen ta, amma a cikin shekaru biyu da nayi tare da ita sau daya na taba
morar sadaki na. A wancan lokacin ni kuma son da nake wa Jaian mai yawa ne, don har
gobe babu matar da zan so kamar ta, duk matan da na aura bayan ta don na rufa wa
siyasa ta asiri ne, amma ba don so ba ko neman yaya.
Kullum gorin Jalan gare ni shi ne ba zata taba so na ba, domin tana da wanda
tayi wa alkawarin aure, na yaudari iyayen ta da abin duniya. Da tura ta kai bango
na daina sakar mata bakin aljihu na don na gaji da gorin da take yi min. Rana daya
Allah ya bani saa a kanta kuma ranar ne muka samu rabon Amani. Koda cikin ya isa
haihuwa ta tubure lallai in maida ta kasar su ta haihu a can, ni kuma da bazan iya
barin ta ta koma kasarsu ba sai na dauko mata mahaifan ta suka zo nan Katsina muka
basu muhalli a cikin gidan nan, nace su zauna da ita har sai ta haihu, domin kuwa
Jalan tana ta min rantsuwa da barazanar ba zata haihu da mammunan mutum kama na ba.
Ranar ne na fahimci Jalan saboda muni na take kina, in banda haka dame na rage
ta da iyayen ta? Har Hajji na kai su duka, in banda haka kiyayyar ta tayi yawa a
kaina sai na soma kankame aljihu na nima.
San da ta shiga watan haihuwa Jalan ta ci shinkafar bera don ta kashe kanta.
Allah ya so mahaifiyar ta da suke tare ta fahimta da wuri, muka kaita asibiti
hankali tashe, likitoci suka yi mata tiyatar gaggawa suka cire Amani, ita kuma suka
bata duk wata kulawar da ta dace.
Tun da aka bani ya ta a hannu na, yar da aka ceto da kyar, naji na tsani Jalan,
yau kuma na tabbatar ba zata taba kauna ta ba. Sai kawai na rubuta mata saki na
baiwa iyayen ta. Na kuma basu kudin da zai ishe su koma wa kasar su da kula da
lafiyar ta. Tun a aibiti da na rabu da su ban kara bi ta kansu ba har gobe. Wanda
sai yanzu nake tunanin ban kyauta ba, don ban ma tabbatar da cewa Jalan ta rayu ba
ko ta zarce, ban kuma san ya suka yi suka koma kasar su ba.
Na dauki Amina wadda na sakawa sunan mahaifiyar mu na tafi Faskari da ita,
garin da rabon in shige shi har na manta sai a dalilin siyasa wato lokacin da nake
neman kuriar kauyen namu, Yaya na Malam Idrisu yana can da iyalin sa, har lokacin
kuma da na fara karfi banyi kyan kan taimaka masa ba ko yayan sa. Amma da yake aka
ce naka sai naka, yau da bukatar taimakon su ta kama ni haka na murje kunya na kai
masa Amani nace ya baiwa daya daga cikin matan sa ta shayar min da ita. Amma bawan
Allahn nan bai dubi hali na ba ya karbi Amani ya baiwa amaryar sa Maryama, ta hada
da Kamilu dan da take goyo ta shayar da su. Maryama ba tayi shekaru biyu cikakku
tana shayar da Amani ba ta rasu. Sai Malam Idrisu ya dauke ta ya maida rikon ta
hannun kanwar mu Sahura dake aure a garin Funtua.
Amma zuwa na Funtua na farko naga bazan iya barin Amani ta cigaba da rayuwa a
wannan gidan ba saboda rashin tsafta da cikowa, gashi nifa bawai ina taimaka musu
da komi bane kan rikon da suke yi mata amma nazo na raina kokarin Sahura. Na karbo
Amani tana da shekaru uku na dawo da ita Katsina hannun matar da na sake aura, na
daukar mata mai raino.
Amma hankalin Hajara na kan yar kankanuwar yarinyar nan da yadda zata cutar da
ita, shi yasa da na gane na saketa babu bata lokaci.
Na sake aure, saina daina baiwa mata na hidimar Amani, na daukar mata mai raino
daya kwakkwara mai suna Rakiya, na sata a makaranta mai tsada, na ke kuma kirata
AMANI don boye sunan mahaifiya ta.
In takaice maka ko Mukhtar, kafin Amani tayi wadannan shekarun nata na yanzu
aure na goma, babu wadda na cika shekaru biyu da ita, don sun kasa kaunatar min yar
nan, wadda soyayyar da nake yiwa mahaifiyar ta ce bakidaya ta koma kanta.
Suma masu rainon kullum cikin canza mata su nake, Rakiya kawai na bari mai
dafa mata abinci har gobe, har Allah ya raya ta ta isa kula da kanta. Ita ta roke
ni in daina aure-aure in kuma daina korar masu aiki saboda ita, shi yasa muka dade
da Haj.Rabi.
To ka ji Mukhy, wanan shine labari na da ya ta Amani, a yau ina cikin damuwar
irin dabiun ta da irin tarbiyyar da nayi mata, amma yaya zanyi? Ni da mahaifiyar ta
Allah yayi ba masu rayuwa tare bane na tsayin lokaci, kuma ban kyauta ba da ban
kara bibiyar rayuwar Jalan ba, su kuwa dangi na na Faskari wallahi sai dai Amani
tayi masu kyauta amma ba dai ni ba, bana kai ta wurin su, amma ita tana kai kanta
lokaci-lokaci bama tare da na sani ba. Ba yabon nawa ba, Amani ta fini kirki, ta
fini son zumunci kai dai bar ta da sangartar ta wadda rashin tashi karkashin
kulawar uwa ko wata shaqiqiya mace ta jiki yayi mata sanadin sa.
Mukhtar ya jinjina kai ya shafe gumi daga goshin sa. A hankali yace Alhaji
labarin ka akwai darussa mai yawa a ciki Alhaji, sannan akwai tarin kurakurai a
cikin sa.
Na farko Alhaji, ban yarda da abin da ka yarda da shi bana cewa Mama Jalan na
kin ka ne saboda baka da kyawun suffa wannan ba haka bane Alhaji. Hanyar da kabi
wajen auren ta bata dace ba, kamar ka sayo akuya a kasuwa ka kawo kasar ka ka ajiye
ne, duk da mahaifin ta shi ya aura maka ita, akwai bukatar ka nemi soyayyar ta da
fahimtar juna tsakanin ku, kafin akai ga maganar aure ba duka mata ake saye ba.
Amma irin wannan auren dama baya wata kima tunda da bakin ka kace min akwai
wanda take so da suka dade tare, har suka yi alkawarin aure.
Don haka ka cire maganar wai don munin kane bata son ka, kuma Alhaji da bakin
ka kace kana yi mata kankamo, mata da yawa musamman na kasashen Africa suna aure ne
a inda zasu samu wadata da kwanciyar hankali fiye da na kasar su ta asali.
Mu koma maganar dangin ka na Faskari, zan iya cewa kayi wa Yaya Idrisu da
Sahura butulci da rashin daukar zumunci da daraja. Dukiyar ka ta rude ka ka
wulakanta zumunci domin sun cancanci ace a irin wadatar da Allah yayi maka kamata
yayi ace ka rungume su ka zama kaine komai nasu tunda kace basu da karfi.
Muhimmin abin da zaka yi a yanzu Alhaji shine gyara tsakanin ka da yan uwan ka,
neman yafiyar su, da janyo su a jiki, ka saka su a cikin niimar da Allah yayi maka.
Alhaji yana girgiza kai yace haka ne, haka ne Mukhtar, In sha Allah zan gyara,
gobe-goben nan ka shirya mana tafiya Faskari don Allah ni da kai da Amani da yardar
Allah zan gyara komai.
Mukhtar yace naji dadin jin hakan Alhaji, saura iyayen Mama Jalan da ita kanta
ya kamata ka neme su ka sada su da Amani.
Mahaifiyar ta na da hakki a kan ta fiye da wanda kake da shi. In ta mutu baka
sada su ba sai Allah ya tambaye ka Alhaji, Amani (is desperate) ga son ganin
mahaifiyar ta, har taso ta bi ta wata hanyar da baka sani ba don ta kai kan ta ga
mahaifiyar ta ba don na hana ta ba, duk da togaciyar da kayi mata akan zuwa gare
ta.
Kafin Alhaji yace komai suka hango Amani na tahowa inda suke da hanzari da
sassarfa, suka yi shiru suka maida hankalin su gare ta. Tana isowa ta nufi Alhaji
ta zauna kasan kafafun sa ta saka kuka.
Alhaji yace ni fa dadi na dake shagwaba da sakarci maras dalili, yaya zaki zo
muna magana ki saka mu gaba kina kuka? Mutuwa aka yi ko dukan ki aka yi? Amani ta
dago jikakkun idanun ta ta dubi Baban ta cikin ido ta ce Daddy sona ke ka saki Haj.
Rabi, kuma kada ka kara auren kowa, ba zasu taba son ka saboda Allah ba, dukiyar ka
kawai suke so Daddy.
Muddin kuma suka fahimci ba zasu samu ba na rantse zasu iya halaka ka ko ni su
sabauta ni. Daddy don Allah ka sake ta, ni zan kula da kai, na fasa zuwa karatun,
zan kare rayuwa ta gaba daya cikin kulawa da hidimar ka da lafiyar ka, in dai ka
yarda zaka rabu da Haj. Rabi kuma zaka fasa aura min Alhaji Sadi.
Alhaji yace cool down Amani, duk me ya kawo wannan? Maganar auren ki da Alh.
Sadi tana hannun ki yanzu, na bashi dama ne ya nemi soyayyah daga gare ki, wallahi
in baki so duk amincin dake tsakanina da shi bazan miki dole ba. Haj. Rabi kuwa ai
zaman ki take yi, ke kika hana ta tafiya tuntuni.
Ni da ke cikin rayuwa a wheelchair yanzu, rayuwa ta bata mata bace yanzu. Ko
dama saboda siyasa nake aure-auran nan amma tun daga kan Jalan na gama auren biyan
bukatar rai da kauna.
Share hawayen ki kin ji Amani? Gobe in sha Allahu zamu tafi Faskari da wuri zan
maida ke cikin yan uwan ki na jini.
Amma Amani ta yaya zaki iya kula dani alhalin kina mace? Da zaki yi min alfarma
irin wadda baki taba yi min ba ki amince ki auri da na Mukhtar, ya zauna tare da
mu, ku cigaba da kulawa da ni tare har Allah ya bani lafiya.
Na hanga na duba duk duniya ban ga wanda zan iya baiwa auren ki ba sai MUKHTAR
Amani, da shi kadai na amince in yi surukunta, kuma da shi nake son jini na ya
gauraya, koda kuwa ace daga sama ya fado, wato ba yan Adam ne suka haife shi ba.
Amani da Mukhtar a lokaci guda suka daga kai suna kallon-kallo, kallon son
fahimtar ko me Alhaji ke nufi? Sun shiga rudani mai yawa dukkan su, amma Amani ta
fi Mukhtar gigicewa. Mikewa tsaye ta yi zumbur tana kallon Alhaji a tsorace, kafin
ta soma ja da baya, da kyar ta iya cewa,
Daddy ai gara min Alhaji Sadin, da dai wannan mara mutuncin mara tausayin kuma
mara jin kan mace. Gara min Alhaji Sadi bakikkirin mummuna da wannan mai kyan dan
macijin. Gara min Alhaji Sadi tunda ba a karkashin uba na yake cin abinci ba, kuma
yake min keta da Gadara ba.
Na rantse da Allah gara in auri Alhaji Sadi sau dubu da wannan sumumu-kasau din
wanda bai san darajata a wurinka ba, saboda takamar yana da fada a wurin ka.
Tana gama fadin haka ta juya ta bar wurin da gudu-gudu, sauri-sauri babu inda
ba ya kyarma a jikinta saboda dimauta.
Mukhtar kuwa komawa ya yi tamkar mutum-mutumi a wurin, ko kwakkwaran motsi bai
iya ya yi ba. Haka ya kasa dago kansa da ya sunkuyar saboda kunya. Ga mamakin sa
sai ya samu kansa da jin kunyar Alhaji mai tsanani. A can wani sako na zuciyar sa
kuma ya samu kan sa da jin dadin wannan tayi da yayi masa. Shi ma ya san ba ya
kyautatawa Amani yadda duk maaikatan Alhaji ke mata, haka ba ya bata respect din da
maaikata suke bata, kullum jin kan sa yake sama da ita, ba ya yarda da
subordination, shi mutum ne da ba ya yarda da raini ko kaskanci, wannan kuma a
cikin jinin sa ne na iyaye da kakanni.
Maganar aure da Alhaji ya yi yanzun kuwa tsakanin sa da Amani sai ta kashe duk
wani kuzarin sa, ta jefa shi a wani yanayi da bai taba shiga ba na zurfin tunani da
mutuwar jiki.
Maganganun Amani wadanda suka zamo raddi ga mahaifin ta, kuma zagi a gare shi
ko kadan ba su dame shi ba. Fassarar da ta dade tana yi masa a zuciyar ta ne yau
Allah ya matsi bakin ta ta fada a gaban sa.
Da kyar ya iya mikewa tsaye lokacin da Alhaji ya ce ya tura shi a kujerar sa ya
maida shi falo ya huta.
Har suka yi sallama da Alhaji, bayan ya bashi magungunan sa na yau ya sha,
Mukhtar sanyin jikin sa da bugun zuciyar sa basu koma daidai ba. Da kyar ya iya
takawa zuwa gidan sa wanda bai da nisa da gidan Alhaji. Ko motar sa a gidan ya bar
ta don ya san ba zai iya tuki ba.
**** **** ****
MUKHTAR
Mukhtar ya yi kwance a tsakiyar lallausar gadon sa yana sake tariyo maganganun
ubangidan sa Alhaji Usman Faskari, kauna ce zallah ya nuna masa wadda babu algus,
kuma wani bare bai taba yi masa irin ta ba, kuma bai taba samun kwatankwacin ta ko
daga iyayen sa da suka haife shi ba.
Ya soma laluba lungu da sako na zuciyar sa don son gano stand din da ya ajiye
Amani, a zahirin gaskiya wannan yarinyar ba tun yau ta ke fizgar zuciyar sa ba, ta
dade tana saka shi a faduwar gaban da bai san dalilin sa ba, sai ya bar wa ran sa a
cewa kyawun halittar ta da kwarjinin ta ne yake razana shi, yake sanya shi faduwar
gaban, kamar yadda duk wani lafiyayen namiji bazai iya kauda kai a kan ta ba ba
tare da ya ji zuciyar sa ta motsa ba. Ya sha zama a cikin dare yana tuno wasu
abubuwa da suka shafe ta a duk lokacin da wata alaka ta hada su suka fita a mota
tare ya kai ta wani wuri, bisa umarnin Alhaji. A irin wadannan lokutan kwana yake
da tunanin ta a ran sa. Fitsarar ta, rashin kunyar ta, hararar ta da tijarar ta duk
basu bace masa. Ba don murmushi yayi kaura daga rayuwar sa ba da yace wadannan
halaye nata duk da baya son su, to fa hakika suna saka shi murmushi a yawancin
lokuta. Amani Faskari, tana da babban alamari a tare da shi wanda ya dade da kasa
ganewa.
A yau da Alhaji da kan sa ya yi masa tayin auren ta ya shiga rudu, ya shiga
dimuwa da tunani mai yawa, wanda hakan ya saka shi tono duk wasu tsofaffin feelings
din da ya san yana ji a kan Amani; and he realized for himself cewa ya dade yana
son Amani, in dai pleasant feelings din da yake ji a can kasan ran sa a kan ta
shine SO, to ya dade yana ninkaya a cikin sa ba tare da ya ankara ba, har sai yau
da tayin Alhaji da kan sa ya ankarar da shi, amma kuma halayen ta sun sa ba ta
burge shi, kuma ba ya son ko daya cikin dabiun ta. Ya na son ta a kasan ransa a can
wani lungu da bai taba dauka da muhimmanci ba. In ba haka ba me ya sa ko kadan ba
ya son zancen auren ta da Alhaji Sadi? Me yasa ranar da Alhaji ya gaya masa ya bada
auren ta ga

Please Login or Register in order to submit comment