ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://arewanovels.com ÿþ"[12/23, 15:51] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/EuFGI1TIgdlAhVJXP2XqPJ"

*³AN ADAIDATA SAHU*

(Masu keken napep)

NA

MAMAN AFRAH

*ASSALAMU ALAIKUM*

Akwai youtube chanel Win da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta

hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp.

"Waya zaSin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA"

RUBUTA SHIRME

kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaWai za ki gwangwaje da karatu.

"a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki"

iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE

"Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ³AR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA,"

"KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA."

Ga no ta ku tura mn screen shrt domin samun shiga paid grp da zarar free pages sun kare

09013181851

Page 1¡'



BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

"Kwance take a saman gadonta ta takarkare sai sakin munshari take hankali kwance, daga can gefe jikanta ne Jabiru Wan kimanin shekara sha takwas yana kwance a tsakar Wakin a kan katifarsa. Idanunsa biyu dama yana jiran Iya Ansai ta yi nisa a cikin baccinta dan ya fara"

mafarkin ™arya babu Sata lokaci ya buWe baki ya ce.

"""Ina za a kai ku ne Hajiya? KuWinki naira Wari bakwai ne"" Haka yake ta faman maimaitawa, tun Iya tana jin abin cikin bacci har dai ta tashi ta wartsake. Jin alamun tashinta sai Jabiru ya ™ara"

kaimi wajen faWin abin da yake faWa wannan karon har yana ™arawa da faWin.

"""Ku hau zan Wan sha mai a wancan gidan man sai mu tafi"""

"""Allahu akbar kabiran, ni dai Ansai ina neman kai kaina wuta wallahi, ina zan kai girman zunubin cin amanar yaro maraya, na kasa cika masa burinsa na siyan arincaSa (Adaidata sahu). Ni yanzu bani da komai da zan siyar na siyawa yaron nan arincaSa ga shi son abin yana shiga ransa har cikin baccinsa mafarkin abin nan yake"" Ta faWa a fili tana share hawaye. Duka abin da take Jabiru yana jin ta kuma yana ganinta ta hasken farin watan da ya shigo Wakin. Fitila ta kunna ta sakko daga kan gadon har lokacin tana kuka tare da jan hanci, ta nufi wajen akwatin ™arfenta ta buWe ta zauna zaman dirshan a gaban akwatin ta shiga Waga atamfofinta da suke a linke, a can ™asan ta Wakko wata leda sai da ta dakata ta waiwaya alamar kar ko wani yana kallonta, ganin dai babu alamar mutum kuma Jabiru har lokacin yana ta maganganu shi a dole"

mai mafarki.

"Ledar ta kunce sai ga wata ledar a ciki haka ta shiga kukkuncewa har dai ta kai ledar ™arshe a ™alla sai da ta since lodoji takwas sannan ta fito da abin. Irin dan™wala-dan™walan sar™ar tsakiyar nan ce irin ta mutanen da, sar™a da Wankunne da kuma abin hannu masu duwatsu rafka-rafka."

ŠaWWagawa ta shiga yi a fili ta ce

"""Ko a ina zan samu masu siyan waWannan? Yanzu lalacewar zamani ta zo har an daina saka murjani, lokacin zamanin da, da a wancan lokacin ne na siyar da sar™ar nan ya isa in siyawa yaron nan arincaSa in fita ha™™in maraicinsa dan bana son abin da za a ce Jaburu (Jabiru) Ya yi maraicin uwa ni ce nan uwarsa ni ce ubansa, dan ubansa da shi da babu duk uwar ubansu Waya ba kula yake yi da shi ba ni kuwa sai Allah ya saka mini so da ™aunarsa fiye da ´a´an nawa ma, amma dai kyakkyawan zato ina ga ma sar™ar nan tafi zinare daraja"" Ta faWa tana mayar da kayan. sar™ar tata ta mayar cikin ledojin nan haka ta saka su a leda cikin leda, ta rufe akwatin"

™arfen ta tashi ta koma ta zauna a bakin gadon hannunta ri™e da ledar da fitilar tocilan Win nata.

"""Da safe sai Umaru ya nemo inda zai siyar da sar™ar nan, ya kawo kuWin nan a siyawa yaron nan"

"arincaSa wallahi ba zan zauna in mutu Allah ya ™ona ni ba, ya kama ni da cin ha™™in"

"maraicin Wan nan, ni kaina na san darajar sar™ar nan ta fi ta daham(Gold) Yo sar™ar da tun ta armena(Aure) Amma har yanzu gata nan kamar sabuwa dal, dan haka ina ga idan aka siyar har sai an samu sauran kuWi wata™ila ma sauran kuWin ya isa a siya masa fege(Fili) A masa gini a sama masa mata ya yi aure tun da shi ma na ga shegiyar jaraba ce da shi"" Ta faWa tana Waga filo ta saka ledar sannan ta sauka daga kan gadon ta je wajen katifar Jabiru ta shiga Wan bubbuga"

shi a hankali. Mi™a ya yi tare da matso hawaye ya tashi zaune.

"""Sannu ka ji Jaburu, wannan aboki naka da ya baka labarin arincaSar nan da ake tu™awa a binni ana samun kuWi, sannan ya nuna maka hoton ta wallahi ya Wau alhakin ka ya shiga ha™™ina, haka kawai ya hana mana zaman lafiya da yin bacci cikin kwanciyar hankali"" Ta faWa tana rushewa da"

kuka irin na tsoffi.

"""Ki yi ha™uri Iya Ansai tun da na yi ido biyu da Adaidata sahun n..."

"""Jaburu ina faWa maka wallahi ka guji yin saSo, tun ba yau ba nake raba ka da kiwon kyallu amma kana cewa kyallu ta haihu, in banda kuna son kuke yin saSo ina ka taSa gani an ce ""sahu"" Idan ba sahun sallah ba haka kawai ka guji fushin Allah a kan ka tam ni dai babu ruwana bana"

"ciki"""

"""Haba Iya Ansai wai sai yaushe za ki fahimta ne"""

"""Sai ranar da ubanka ya fahimta"" Ta faWa cike da faWa. Kafin ta Wora da maganar ya saki kuka irin"

na sangarta.

"""Ash-sha ai ka ji irinta kai kuma baka san wasa ba haba Jaburu ya za a yi na Sata maka rai dan Allah da manzonsa ka gafarce ni, kar ka saka wutar Allah ta ci ni a kan Satawa marayan Allah rai"" Ta faWa tana ro™onsa har da ajiye fitilar hannunta ta haWe hannayenta kamar wanda aka ce ta"

masa wani gagarumin laifi.

"""Zan yafe miki amma gaskiya ni sai kin san yadda za a yi a saya mini, kin ga ni ba sana'a nake"

"ba, amma in kina ganin ba za a saya mini ba sai in ha™ura dama ai in kana maraya sai dai ka ga masu uwa suna samun ab..."

""",Haba dan Allah Jaburu ai kai ba maraya bane uwa ce kawai ka rasa amma ni ai ni ce uwarka ni ce ubanka, kuma tun da har ka ce za ka yi sana'ar arincaSan nan ai dama babu maraya sai rago, na maka al™awarin a gobe ba sai jibi ba za a siyo maka shi sabo fifil a ledarsa dan na Wakko kadarata wacce take ajiye shekara da shekaru wacce darajarta ta fi ta daham(Gold) Ita za a Waga a siyar a siya maka dan ni a kan son da nake maka hatta kaina zan iya yankewa in baka bare abin duniya ai na ha™ura da murjanin nan nawa"" Ta ta fsana dafa kansa, wani shu'umin murmushi ya saki a ransa yana jin daWin tarkonsa ya kama tsuntsu dan dama ya san arina wai an saci zanin mahaukaciya, ya san dama dole duk runtsi sai Iya Ansai ta saka an siya"

masa Adaidata sahun.

"""Allah ya saka ki a aljanna Iya Ansai ki sha jar miya da naman kaza"""

"""Amin, amin Wan nan, ai addu'ar nan da kake minj kaWai ma ta isheni tun da na kyauttawa maraya, ai mJaburu da ranka ya Saci gwara ko tafiya tsirara ne in yi dan cikar burinka"" Ta faWa"

tana Wan darawa ta Wauki fitilarta ta koma ta hau gadonta shi ma ya kwanta.

"""Ai sai ka juya ka sha baccinka mu jira wayewar gari"""

"""Yanzu kuwa Iya Ansai tawa ta kaina gaki ga ni a aljanna"""

"""Kai amin Jaburu da na ji daWi wallahi"" Ta faWa tana Wan matse ™walla ta koma ta kwanta bacci ya yi"

awon gaba da su.

*DA ASUBA*

"Da faWuwar gaba Iya Ansai ta falka, saboda tinowa da ta yi ta fito da ajiyarta ta kadararta ta ajiye a ™asan filo tsoronta Waya kar ko an shigo tana bacci an yi awon gaba da sar™ar, da yake lokacin da ta buWe idanunta ta kai hannu ta kunna fitilarta sai ta ganta a can gefe Waya filon da ta saka sar™ar a ™asansa ta ™a™ume shi, shi ma yana can da ban. Hakan ya sanya ta yi tunanin ko"

Sarawo ya shigo.

"""La'ilaha ilallahu muhammadur rasulullahi S.A.W"" Ta shiga rafka salati a zuciyarta gabanta yana"

tsanata faWuwa tana Waga filon.

"""Na shiga talatin da tara ni Ansai Wiyar mai siyar da allo jikar mai siyar da tawada, idan aka Wauke sar™ar nan ta murjani nan mai tsawon tarihi an ta™aita ni an sace dukiya mai Winbin yawa, ya zan yi da al™awarin da na yi wa marayan nan jiya cikin sulusin dare?"" Ta faWa a ranta hawaye suna ambaliya ta wurgar da filon a can gefe tana lalumawa ashe zanin gadon ne ya rufe ledar"

shi ya sa bata ganta ba. Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ™warara guda uku.

"""Allah ya taimake ni, da ina zan kai nauyin al™awarin da na yi wa marayan nan, ai da na Wau alhakinsa, ai kuwa da wanda ya Wau sar™ar nan sai na saka an gewaya laya dan Winbin dukiyar nan ba za ta tafi a banza ba"" Ta faWa tana sako ™afafunta ™asa ta sakko sai da ta waiwaya ta tabbatar babu kowa kuma Jabiru yana ta munshari sannan ta Waga zaninta ta saka a cikin aljihun Wan"

tofinta(Siket na tsofaffi da suke sakawa a cikin zani).

"""Ina yin sallah zan kirawo yaran nan mu zauna ai gwara ni in siyar da kadarata in siya masa ina raye ba zan bari ya yi maraici ba"" Ta faWa tana nannaga zip Win Wan tofin sai da ta tabbatar ya zigu sannan ta buWe ™ofar Wakin ta fita. Alwala ta Wauro lokacin duk an shiga masallaci, da yake bayin nata a Sangarenta yake dan haka babu ruwanta da zuwa can tsakar gidan bayan ta gama"

alwalar ta dawo Wakin tana kiran sunan Jabiru.

"""Kai Jaburu ni ina dalilin wannan bacci naka kai kullum baka zuwa sallar asubahi sai dai idan rana ta fito katakau ka zo kana sallah da ™adangaru, yo sallah da ™adangaru mana kana kai sujada ™adangare ma yana gyaWa kai ai shi ma lokacin ne yake sallah"" Ta faWa tana nufar"

shimfiWar tasa ta shiga bubbuga shi amma ko gezau bai yi ba baki ta taSe ta yi gaba

""",Wallahi ba zan biye maka ba, haka kawai kai baka yi sallar ba ni ma in je ban yi ba lokaci ya ™ure a yi ba wan ba ™anin wato babun baWinuhu"" Ta faWa tana shimfiWa sallayar ta kabbara sallar. Har ta idar da sallar amma Jabiru yana ta munshari. Bayan ta shafa addu'ar ta jiyo ™aran ™ofar gida alamun dawowar ´a´an nata daga masallaci, tashi tsaye ta yi ta fito daga Wakin nata ta taho"

tsakar gidan lokacin su duka kowa ya shige Wakin matarsa.

"""Mamman( Muhammad ne ake kiransa da Mamman) Umaru!"" Ta shiga ™walla musu wani kira mai kamar babu lafiya. Shiru kake ji tsakar gidan babu kowa sai muryarta da take ta faman rafka musu kira. Baba Mamman ne ya fara fitowa daga Wakin matarsa, sai Baba Umaru ma ya"

fito da sauri yana gyara zaman hularsa.

"""Oh Allah na tuba waWannan yara da jarabar son mata kuke wallahi, a ce ku bakwa rabuwa da Wakin mata yo ina dalilin an kwana ana abu Waya da safe ma a Wora sai ka ce jaraba, maimakon ku tafi turakar ku amma sai ku ™are a bibiyar Wakin mata dan jaraba kowanne ya kama mace Waya kamar rai kun kasa ™ara aure su ba haihuwa suke yi ba sai cikawa mutane masai da kashi(Toilet) Ai dama wajenku Jabiru ya yi gadon jarabar nan dole ma idan an siya masa arincaSar nan sauran kuWin a gina masa gida a masa aure kar ma a zo yake lalume ´a´an mutane a lungu ake A'i"

"ina indo"" Ta faWa a ranta tana bin ´a´an nata da kallo da suka zo cike da girmamawa."

"""Gamu Iya"" Kowanne ya faWa yana Wan sunkuyar da kai saboda kunyar da ta lulluSe su dan sun"

san halin Iya yanzu sai ta ce sun je sun ma™alewa matansu.

"""Yo kwa zo ku tsaya mini getse-getse, kamar bishiyar dalbejiya, kuna sunkuyar da kai kamar mararsa gaskiya, ku wuce muje Wakina maganar sirri nake so mu yi tun da yanzu gari ya fara haske kafin kowa ya fito tsakar gida, a mana laSe a ji abin da za mu tattauna, yo kar a samu wani ya ji wannan babban batu a je a bini har gadon baccina a ma™ure ni da filo saboda son dukiya"" Ta faWa bayan ta rage murya kamar mai raWa sai wani dogon wuya take tana kallon"

Wakunan matan ´a´an mata gudun kar wani yaji mai take cewa.

"Duk da sun san halin mahaifiyar tasu amma sai da mamaki ya mamaye musu zuciya, sai dai babu wanda ya isa ya tambayi dalili, dan haka umarni kawai suka bi Baba Mamman ne ya fara yin gaba cikin Wan sauri-sauri dan ya je ya tashi Jabiru ya yi sallah saboda basu da wani kataSus Iya ta hana a tashe shi zuwa masallaci wai har yanzu yaro ne, kuma kar a shiga ha™™in marayan Allah a tashe shi daga bacci a Wauki alhakinsa har sun yi sun gaji sun ™yale. Yana shiga"

ya WaWa masa duka da sauri ya tashi yana muzurai da murza baya.

"""Wuce ka je ka yi sallah sakaran banza da wofi kuma saura in ji ka ce wa Iya ni na tasheka"" Ya faWa yana aika masa wata uwar harara. Tashi ya yi yana gyaWa kai kamar ™adangare yana shirin"

fita daga Wakin sai ga Iya ta kawo kai Baba Umaru yana biye da bayanta.

"""To Jaburu har ka falka da sassafen nan garin ko gama wartsakewa bai yi ba?"" Ta faWa tana tsare"

shi da idanu.

"""Eh ai dama tun fitarki na motsa"" Ya faWa yana ratsewa ya fice ita kuma ta taSe baki ta shiga"

Wakin.

"""Kai Mamman kar dai a ce kai ka katsewa marayan nan baccinsa, wallahi Mamman ka kiyayi"

"fushin ubangiji a kan ka idan kana shiga ha™™in maraicin yaron nan"""

"""Haba Iya ni ma da na shigo zaune na same shi a kan katifarsa"""

"""Ayyo ko da na ji"" Ta faWa tana samun wuri ta zauna daga can gefe shi ma Baba Mamman Win"

dama a zaune yake.

"""Umaru, Umaru, wai ina kake ne kai kamar ba Wakin uwarka ba sai ka raSe a jikin bango kamar wani ™adangare"" Ta faWa cikin Waga murya ganin Baba Umaru bai shigo Wakin ba. Baba Umaru kuwa ya tsaya ne a wajen yana yi wa Jabiru faWan ™in zuwa masallaci yana faWa masa duk ranar da ya mutu Iya ba za ta je kabari ta cece shi a kan azabar da za a masa ta wasa da sallah ba. Yana cikin faWan ya ji ta kira shi da sauri ya shiga bakinsa Wauke da sallama ya samu wuri ya"

zauna.

"""Uhm Bismillahi bari in tashi in saka mana labule rufin asirin Waki"" Ta faWa tana tashi"

"tin™is-tin™is ta nufi ™ofar su dai da ido suka bi mahaifiyar ta su suna mamakin tarasun da ta yi da farar safiyar nan. Bayan ma ta saka labulen sai da ta gar™ame ™ofar ta saka sakata, da kallo suka bi junansu kowanne yana raya cewa abin babba ne tun da har da su rufe ™ofa tamkar za a yi wani munfurci, bayan da safen nan babu kowa ma bare ta ce wani zai shigo."

"""Ai shi batun dukiya abu ne na sirru(Sirri) Komai yana son a yi cikin hikima asiri a rufe"" Ta faWa"

lokacin da ta dawo ta zauna.

Babu wanda ya tanka illa iyaka kowanne mamaki ya kashe masa baki jin ta ambaci dukiya.

"""Umaru maza fita ka Wakko tocilan Win nan taka mai cin batira shida, na ga jiya ka mata sabon"

"zubin sabbin batira"""

"""Iya mai kuma za a yi da fitila bayan gari ya waye tangararai?"""

"""Au Allah Umaru idanu ka fini da har kake cewa gari ya waye yo ai na san da garin ya waye amma na ce ka Wakko ai tun da ka ji haka akwai magana kuma akwai amfanin da za a yi da ita a wannan zama namu, sannan idan ka Wakko fitilar ka kalli gabas da kudu yamma da arewa ka tabbatar babu wani wanda ya ganka"" Ta faWa cikin halin ko in kula. Baba Umaru kallon Baba Mamman ya yi sai Baba Mamman Win ya gyaWa mas kai alamar ya bi umarnint, tashi ya yi yana"

cewa

"""To Iya"""

"""Au Allah, to wallahi Umaru ka fita idona in rufe, kana neman shigar mini hanci da ™udundune yanzu har ni in yi magana saboda ka raina ni sai ka kalli Mamman ya gyaWa maka kai, kamar"

"™adangaruwa"""

"""Allah ya huci zuciyarki Iya ba haka bane"" Ya faWa yana tashi ya buWe ™ofar ya fita jin kaWan sai ga"

shi ya dawo ri™e da fitilar.

"""Mayar da ™ofar nan ka rufe ruSuk bana son tonom silili"" Bai ce komai ba ya rufe ™ofar ya saka sakatar dan dai a zauna lafiya sai dai su duka suna mamakin abin da za a yi da fitila bayan gari"

ya waye kuma ma abin wai har da rufe ™ofa da saka sakata.

"""Ka tabbatar babu wanda ya ganka ko Umaru?"" Ta tambaye shi daidai lokacin da ya zauna."

"""Babu wanda ya ganni"""

"""Yawwa ko da na ji, ai na san ku kaWai ne ´a´ana kuma ku kaWai ya kamata mu rufe mu binne"

"kowanne sirri"" Ta faWa tana tsare su da idanu."

"""Haka ne Iya"" Suka haWa baki waje faWa dan sun ™osa su ji abin da ya sa ta tara su wanda take ta nannago bayan ta ambaci dukiya, bayan kuma a iya sanin su ko kuWin siyan ™osai sai sun bata amma kuma yau Waya tana maganar dukiya sai dai suna ta maganar ko dai shiriftun tsufa ta fara"

duk d sun san ragas take sai dai in yau shiriftun ya same ta.

"""Ko dai mafarki ta yi ta tsinci kuWi a leda"" Baba Mamman ya faWa a ransa dan ya rasa"

mazaunin da zai ajiye maganar tata.

"""Iya dai ko cewa za ta yi bara za ta fara tun da mun kasa cikawa Jabiru ala™awari, take maganar dukiya bayan tana ta neman kuWin da za ta siyawa Jabiru adaidaita kuma yau tana maganar"

"dukiya"" Baba Umaru ma yake maganar a zuciyarsa."

"""Bismillahir rahmanir rahim"" Bismillar da Iya ta yi ta katsewa kowa zancen zucin da yake. Da kallo suka bita ganin ta tashi tsaye ta basu baya ta Waga zani tana ta lalumen siket Win Wan tofinta."

Kowa ya zubawa sarautar Allah ido. Sai da ta gama ta dawo ta zauna tana jan hailala da

salatin annabi S.A.W. Da kallo suka bi ledar hannunta.

"""Iya ba dai tsuntuwar kuWi kika yi ba, kuma irin wannan ai da tun da zamu masallaci kika bayar"

"aka kai cigiya"" Baba Mamman ya faWa yana bin ledar da kallo."

"""Wallahi kuwa dan ma kar a zo a fara yekuwa ana cewa za a gewaya laya"" Baba Umaru ma ya"

faWa yana kafe ta da idanu.

Baki sake galala take kallon su kafin ra yi ™arfin halin cewa

"""Oh Allah na tuba ni Ansai an zo zamanin da yara suke yi wa iyaye hawan ™awara, yanzu"

"bakwa bari in mutu ku binne ni ba, ina abu kuna tarar numfashina, to masu gewaya layar sun daWe basu gewaya ba"""

"""A'ah Iya ba a yi haka ba, mu ai ba ma so mu rasa ki ba"" Baba Umaru ya sake faWa."

"""Mtsss aikin banza shafa lalle a Wuwawu"" Ta faWa tana fara since ledar. Babu wanda ya ™ara magana illa iyaka sun zubawa sarautar Allah ido, Wakin ya yi tsit baka jin komai sai ™aran ledar da"

Iyar take sincewa.

"""Haba Umaru hasken fitilar taka fa yana barin saitin ledar lai da za kake haska saitin inda nake"

"buWewa"" Ta faWa tana Wago kai ta aika masa wata harara da ta sa ya gyara ri™on fitilar."

"""Kai ma Mamman baka saita sosai ba, yo ni ina dalili ina Wan mafari kowa hankalinsa yana wani wuri, wato kowanne yana tunanin ™e™asassiyar matarsa matan fa ba haihuwa suke ba duk da kun tara mana taron yuyuyu, sai cika mana masai suke da kashi sun kasa haihuwa sai shegen cin abincin tsiya kamar gara"" Ta faWa tana aikawa kowanne su harara. Basu tanka ba dan idan"

da sabo sun saba da halin mahaifiyar tasu.

"Baki a sake suke bin abin da ta fito da shi daga ledar ganin sar™ar tsirkiya irin ta ´an da, wato irin"

manyan tsakiyar nan da ake yin sar™a da su murjani.

"""Iya mene ne wannan?"" Suka haWa baki wajen tambaya da mamaki fal a maganar su. ""˜undun"

"ubanku ne, na ce ™undun ubanku ne, in banda yaran zamani har kun sa na yi suSutar"

"baki ina zagin marigayin ubanku, in fito da kayan kuWi tsababa amma kuna mini tambayar rainin wayo da rainin hankali"""

"""Kayan kuWi?"" Suka ™ara haWa baki a karo na biyu."

"""Aikin Sur in ji tusa, ai ni a nawa ganin duk mai zuwa sama ya taka leda ha™i™a ya ci ™arfin tafiya, to abin da ya gagare ku ne ni na ta™ar™are zan yi, dan ku gane irin so fa ™aunar da nake yi wa"

Jaburu(Jabiru) Tun da kun kasa siya masa arincaSa (Adaidata sahu) Shi ni na ce bari na

"ceto zuciyar maraya daga damuwa ko na samu rabauta ranar ™iyama, wannan kayan sar™o™in a yanzu na san ya ™ara daraja fiye da tunanin duk wani mai tunani yanzu na san ya fi zinari(Gold) Daraja girman nan nasa na san ba ™aramin kuWi zai yi ba. Dan haka na Wakko a siyar a kawo kuWin a siya masa arincaSa, a siya masa fege(Fili) A siyi kayan gini da kuWin masu gini a gina masa gida ka ga ko aure za a masa an huta, sauran kuWin in je makka da madina Wakin manzo"

"ku ma kwa sami kasonku na ladan ganin ido ku ja jari"""

Tun da ta fara magana bakin su yake buWe wanwar kowa sakin baki ya yi kamar layar mai

tafiya yake bin Iya da kallo na tsagwaron mamaki ganin tsakininta da Allah take magana.

Wanda ba za su yi SUBSCRIBE ba idan suna bukatar littafi za su biya 5OO ta acc Faiza

abubakar 9030283375 Opay

TALLAH! TALLAH!!! TALLAH!!!

"Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koWewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai"

"rahusa ki Wora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada."

"Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ™auri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ™amshi da daWewa a Waki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ™amshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa la™abi da"

sumar da mai gida don ™amshi.

"Muna da Toilet cleaner in har toilet Winki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ™amshi da yake yi Waya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ™amshi, turaren wanka luquid soap, izal"

"hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa."

Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da

"na ´a´anta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari "

"Akwai cotton material da lesuka da atamfofi, abaya, takalma, kayan yara siyan Waya ko sari."

TuntuSe ni a wannn lambar 09013181851

"[12/23, 15:51] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/Duq93sLLgjCKV0uuildAH1"

*³AN ADAIDATA SAHU*

(Masu keken napep)

NA

MAMAN AFRAH

*ASSALAMU ALAIKUM*

Akwai youtube chanel Win da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta

hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp.

"Waya zaSin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA

Please Login or Register in order to submit comment