ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

YA"

RUBUTA SHIRME

kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaWai za ki gwangwaje da karatu.

"a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki"

iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE

"Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ³AR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA,"

"KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA."

09013181851

Page2



"""Iya Yanzu da kuWin murjanin ne za a siya masa adaidatan, har da fili a yi gini sannan ki je"

"makkah duk a ciki?"" Baba Mamman ya yi ™arfin halin jefa mata tambayar."

"""Au Allah, ni abin da na kasa ganewa ma shi ne tambaya kake yi ko neman sani? Magana aka baka ita a buWe amma kana mini wata magana mai kama da rainin wayo"" Ta faWa tana aika masa"

harara.

"""Ba haka bane Iya abin ne dole a sanya ayar tambaya yanzu waye zai siya wannan murjanin?"""

Baba Umaru ya faWa cike da tsoron maganar da za ta faWa.

"""Yo ni da zan nemo masu siya ma ina zan tara ku ai da sai dai ku ga arincaSar a ™ofar gida, amma ni wannan duk ba damuwata bane, idan kuna ganin a garin nan masu siya da daraja zasu yi wuya sai a ranci kuWin mota a je birni a siyar idan an kawo kuWin sai a biya wanda aka ranci kuWin motar ba shikenan ba dai tun da yake kuWin motar kuke yi wa ido"" Ta faWa tana"

karkata kai gefe.

"""Iya ba maganar babu masu siya da daraja bane..."

"""Yawwa ko da na ji"" Ta katsewa Baba Mamman hanzari."

"""Iya wallahi fa babu wanda zai siya wannan tsakiyar, ban sani ba ko wajen ΄an gwangwan wato baban bola, irin wannan masu yawo da baro suna siyan tsoffin kaya da ™arafe, idan ya siya da daraja wallahi bai fi ya baki Wari biyu ba ita ma sai an kai ruwa rana tun... Baba Umaru da ya ta™ar™are yana rattabo bayani ganin Iya ta tsaya tana kallonsa sai ya yi tunanin fahimta take ashe haushi ne ya turnu™e ta, ya fara ™o™arin ™ara ™aimi wajen mata bayani bai ankara ba ya ji ta wanke"

fuskarsa da mari.

"""Bolo, na ce bolo, dan gwafar ubanka saSo kake so ka yi? Murjanin nawa ne tun na aurena da ubanka za a bawa baban bola ya siya? Abin da nake saka ran samun miliyoyi a jikinsa,dan na san iwar haka darajarsa ta fi ta zinare (Gold) Amma dan ba™in ciki ka ce wai jaka Waya(200) Za a bani sai ka ce wata wacce uwata ta ce in je na gani, sarkar da ko masu ajiye kaya a gidan tarihi suka samu siya za su yi, a ajiye ta a gidan tarihi' Ta faWa tana rushewa da wani marayan kukan takaici dan gani take Umaru ya gama rainata har zai ce ta kai sar™ar da ta kwashe shekara da"

shekaru tana ajiya amma a ce wai baban bola za a kai wa ya siya.

"""Allah huci zuciyarki Iya"" Baba Umaru ya faWa yana dafe da kunci."

"""Iya ki yi ha™uri amma gaskiya ya faWa miki, dan ko baban bolan ko masu kayan gwangwan Win da ya ambata to wallahi ba lallai su siya bama ko da naira ashirin ne, ni ina ganin ki ajiye kike saka kayanki, dan ko ta kwanan baya da aka tsiro yayinta za ki ga ana yin su masu ™ananan tsakiya ne, kuma basu fi Wari biyar ake siyar da setin su ba yanzu ba a yayinsu sosai bare kuma wannan murjanin da yanzu sai kaWan daga cikin yarbawa ne suke sakawa yarbawan ma maza s... Tun kan Baba Mamman ya kai aya shi ma ya samu nasa kason marin Iya sai muzurai take cike da"

Sacin rai ta buWe baki cikin muryar kuka ta ce

"""Amma ™ur'anin Allah kun gama cin tuwo a kaina,dan cin fuska murjanin ne yarbawa suke sakawa yarbawan ma maza"" Ta faWa tana Waga sharSeSiyar sar™ar da idan ta saka sai ta zo har kan cikinta saboda tsawo kallon sar™a da tuna irin burikan da ta daWe tana ci a kanta ya sanyata"

fashewa da kuka tamkar a gidan mutuwar da ba a Wauke gawa ba

Baba Umaru ne ya buWe baki zai yi magana amma ta dakatar da shi ta hanyar Waga masa hannu.

"""Ya isa! Ku tashi ku fice mini daga Waki bana cikin masu wauta kamar ku banzaye masu tunanin banza da baku da aiki sai bin Wakin matayenku, ku tashi ku Sace mini a gani tun kan ran kowa ya Saci dan idan aka jima kuna cigaba da aibata murjanin nan ina iya Waga muku nono d... Tun kan ta kai aya suka tashi sumi-sumi Waya yana bin bayan Waya Baba Umaru da fitilarsa ko kashewa"

bai yi ba suka buWe ™ofar suka fice.

"""Mutanen banza kowa da kai tun na haihuwa, ana harkar arzi™i suna yin batun tsiya, to wallahi a bakin ku, da kuWin murjanin nan zan cika gaba Waya burikan da na lissafa muku, mu zuba mu gani, murjanin nan tun yana sabo na daina sakawa, bai fi a ™irga ba sakawar da na masa n ajiye saboda na san idan da rai akwai ranar da zai yi dajara ake nemansa ido rufe"" Ta faWa tana Waga sar™ar ta mayar da su cikin ledojin ta ™ulle ranta duk a matu™ar Sace dan babu abin da ya Sata mata rai ya kuma dagula mata lissafi sama da yadda suka ce wai baban bola ne ko ΄an gwangwan za"

"su siya, kuma abin haushin ma wai a bata Wari biyu."

"""Na yi al™awarin babu wanda zan ™ara kirawo wa a cikin ku a kan batun siyar da sar™ar nan, da kaina zan tafi na siyar a yau ba sai gobe ba, a Wuro mini kuWin a ledar viva dan na san sun yi kaWan a ™aramar ba™ar leda, kai sai na siyo buhhunan barkono guda takwas ma dan daga na dawo idan suka ga ana shigo da buhhunan barkono su san kasuwa ta yi kyau dan sai sun ™aryata kansu da kansu na cewa sai baban bola ne zai siya, dan yau har kasuwa sai na je dan sai tayin da ya mini dan ba zan siyar da araha ba in zo daga baya in ji wani zai siya da gwaSi in ke cizon yatsa"" Ta faWa a zuciyarta tana zuwa ta buWe akwarin ™arfen nata ta saka ledar a ™asan"

kayanta.

Tana shirin rufe akwatin sai gani ta yi an bankaWo labule baki Wauke da sallama Aliya matar

Baba Umaru ta shigo Wauke da samirar turon Iya da baban kofi mai koko a ciki. Da hanzari Iya ta rufe akwatin ta yi saurin matsawa daga wajen tana haWe rai ta ce.

"""Na ga ikon Allah faWa da mai gari ranar salla, ke dai Aliya mai hali ba ya fasa hakinsa wallahi yanzu a ce ba za ki yi sallama ba ki fara nemen izini sannan ki shigo ij an baki dama in ba a baki ba ki koma, amma sai dai ki bankaWo labule gidif ki shigo sai kin zo tsakiyar Waki ki yi sallama"" Ta faWa tana aika wa Aliya harara. Aliya kuwa turus ta yi jin maganar Iya dama ta saba da Wora hau a gado irin na Iya shi ya sa ma ko damuwa basa yi dan abu kaWan sai ta ringa"

sababi.

"""A yi ha™uri Iya sallamar nan dai sai da na yi uku ™warara a waje na ji shiru ba a amsa ba, to sai na yi tunanin ko kina bayi shi ya sa ma na shigo"" Ta faWa tana dur™usawa za ta ajiye kwanon tuwon"

da jug Win koko.

"""Ke dakata! Kar ki ajiye mini tuwon nan naku ci kat ka mutu, abu Wanye lagaf baya wani dahuwa"

"ku a duniyar nan a ce baku iya tuwo ba ya nuna, ake ci ana santi a ji turo ya tu™u ya dahu"

"dumurmur da shi kullum abu lagafgaf kamar Wanmalele"" Ta faWa a fili tana yatsina fuska, a"

zuciyarta kuma ta ce

"""TaSWi! Allah tsari gatari da saran shuka, ni Ansai Allah raba ni da aikin da na sani haka kawai ni da zan dam™i sulalla yau, zan zauna cin tuwo da koko haka kawai su ruWe mini ciki in kafa yin kashi ina sawu bayi, ai ni yau sai dai in ci tsire da balangu da lemon kwalba in siyo kayana idan zan dawo, mu yi burunshi (Brush) Ni da Jaburu""Ta faWa a zuciyarta tana kallon kwanon tana"

yatsina fuska kamar ta ga kashi.

"""A yi ha™uri Iya za mu gyara"""

"""Ko ku gyara ko ku cigaba da yin Wanyen naku ya rage"" Ita dai Aliya bata ce komai ta tashi ta fita"

daga Waki

"""Idan ma kasuwa ta yi yadda nake so, kayan abincina zan siya in ke girkina in huta da wannan ci kar ka mutun"" Ta faWa tana taSe baki."

"Bayan ta watsa ruwa ta Wauki galleliyar atamfarta ta saka, tana cikin naWa gwaggwaron su na"

tsofaffi Jabiru ya shigo yana tafiya yana kumbura baki lo sallama babu ya shigo ya zauna.

"""Jaburu shalelen Iya Wan gaban goshina waye ya taSa mini kai"""

"""Yo ba yunwa nake ji ba ina can masallaci da na yi sallah na kwanta nake bacci sai yanzu na"

"falka cikina sai ™ugi yake yana ™wallawa ciroma kira"""

"""Kai amma ban ji daWin maganar nan ba, amma ungo jaka guda (200) Ita kaWai ta rage mini amma da yake yau akwai bushasha na san za mu ri™i miliyoyinta, ka je ka siya waina yau babu"

"kai ba cin tuwo"" Ta faWa tana mi™a masa kuWin bakinsa da nata washe kamar gonar auduga."

"""Allah tsunduma ki aljanna Iya, ga shi kin ce yau za a cika mini burina"""

""" Amin Wan nan da yardar Allah kuwa yanzu zan tafi na ci kasuwar sar™ar murjanina, kuWin ma a ledar viva zan sako shi na siyo mana tsire da balangu da lemon kwalba sai mun ci mun ture yau, dag ana dawo za a siyo maka arincaSa kai har gida zan sa a siya maka a maka aure ni kuma in je makka in siyo maka kayayyaki"" Ta faWa tana dafa kafaWarsa. Wani tsalle ya doka"

yana ta murna.

"""Amma gwara mu je in raka ki"""

"""Babu in da za ka je ni kaWai mintina kaWan zan dawo iyayenka na ce su je su siyar suka watsa mini ™asa mai tsakuwa a ido, yanzu da kaina zan je in siyar yanzu kuma zan dawo ka san masu kai kayan irin su barkono da kalwa su ne suke jimawa a kasuwa suna talla da neman mai siya ni kuwa da zan kai kayan ma™udan kuWi ina zuwa za a cake a bani""Ta faWa tana tuna irin daWin da"

za ta ji idan ta dam™i kuWin.

"""Ai kuwa yau ina Wakin nan daga na siyo waina zan dawo in yi zaman jiranki"" Ya faWa yana fita"

domin zuwa siyan waina ransa kuwa fari ™al.

"""Yawwa gwara ka zauna ka jira ni"" Ta faWa tana linke ledar vivan ta buWe akwatin ta Wakko ledar"

sar™ar ta saka a Wan tofinta ta yafa mayafi ta Wauki ledar vivan aka sako takalmi Wan madina aka fito ana wata tafiya irin ta masu jiran zuwan kuWi.

"""A dawo lafiya"" Aliya da Maimuna da suke tsakar gidan suka haWa baki wajen faWa."

"""Allah sa, kuma kar wanda ya sake ya kai mini dambu Waki dan idan na gani ma zuciyata tashi"

"za ta yi wanda kuka kai na safe ma suna nan ajiye yadda aka kai mini ni yau wankin ciki zan yi"" Ta faWa ba tare da ta jira amsar sh ba ta saka kai ta fice."

Tun da ta fito bakinta yake a washe tafiya kaWan ta saka hannu ta taSo ledar sar™ar cikin

"aljihun nata, sai ka ce wanda ledar za ta Sace."

"""Bari na fara zuwa gidan Dillaliya dan kar in tafi in siyar a kasuwa ta ga ban biyo ta hannunta"

"ba ta samu alkairi"" Ta faWa lokacin da ta karya kwanar gidan Dillaliyar."

"""Allah dai ya sa tana nan ita Win uwar ΄an yawo"" ,Ta faWa idanunta kafe a ™ofar gidan dan tana zaton"

ko ™ofar a rufe.

"Cikin sa a kuwa a buWe tana zuwa ta tura ™ofar ta shiga da sallama, amsa mata ta yi."

"""Lale marhabin da iya Ansai"" Cewar Dillaliya da take sanye da doguwar atamfa an cokara"

Waurin Wankwali.

"""Yawwa ana gida kenan"""

"""Wallahi kuwa ban kai ga fita ba, amma ina shiri dan yanzu zan fita karSar basussuka"""

"""To madallah"""

"""Daga toi ko daga matoya?"" Cewar Dillaliya tana dariya."

"""Uhmm daga gida nake kuma tafe nake da abin arzi™i na ce bari na biyo ta hannunki kin san ΄an"

"magana sun ce dillalin jariri shi ya san kuWin wada"""

"""Wannan haka yake, amma kuma sai na ganki hannu na dukan cinya Iya"""

"""Eh kin san ba kowace ganima ake gani ba a hannu ba, wannan a aljihu na taho da ita ledar da"

"za a saka kuWin ce ma na rage buri na Wakko viva, dan ba dan na kai zuciya nesa ba buhu zan"

"Wakko"""

"""Ikon Allah na zaune ya faWi, yanzu iya sai ka ce wacce ta ri™o damid(Diamond) ko lu,u-lu,u ko kuwa babban zinare"" Dillaliya ta faWa tana kama haSa cike da mamaki a zuciyarta kuma tana fatan wata banza ce ta faWi ita ma ta kwashi rabonta dan ta san dai dole ta wanki gara dan"

"tsohuwar ba lissafin kuWaWe masu yawa za ta sani ba, dan a nata tunanin Iyar ko tsuntuwa ta yi."

"""Kina kan hanya Dillaliya ai babu maraba to idan ma akwai to sai dai abin da na ru™o ya doke"

"waWanda kika lissafa a kuWi"""

"""Na shiga aljanna na ma™ale ni Dillaliya, bani in sha Iya Ansai saboda na gaji da gafara sa ban ga ™aho ba"" Dillaliya ta faWa cike da ™osawa dan a son kuWi irin nata har ta fara tunanin idan har sar™ar gwal ce ta zo da ita to babu makawa ta dannawa Iyar filo har sai ta daina numfashi, idan ya so idan dare ya tsala ta fitar da gawar ta jefar dan ba za ta bari a yi babu ita ba dan sai ta ci"

karenta babu babbaka.

"Murmushi Iyar ta shiga yi irin na ni kaWai na san abin da na ri™o. ""Iya"

"sai ja mini rai kike"""

"""Bari dai na fiddo ba dan kin nuna kin matsu bama kuma ni ma ina son a je a yi mini hanyar"

"masu siya kema ki samu rabonki da sai kin bani goron albishir"""

"""Kar ki damu daga baya ma zan biya bashin goron albishir Win"" Ta faWa cike da jin haushin tsohuwar. Hannu iya ta saka a aljihun Wan tofin nata bayan ta wangale zanin jikin nata, ledar ta"

fito da ita tana ™o™arin sincewa Dillaliya ta karSe ledar hannunta har karkarwa yake tana sincewa.

"""TaS akwai gwarama kenan tsuntsu daga sama gashashshe ina zaune har gida rabo na minallahi, dole ma ki garzaya barzahu a yanzu ba sai anjima da dan na ji sar™ar da nauyinta Allah kaWai ya san gram in da za ta yi i aka auna"" Dillaliya ta faWa a zuciyarta lokacin da ta kai ledar ™arshe. Tana buWewa suka yi ido huWu da sar™ar murjani irin mai rafka-rafkan nan mai kama da ta yarbawa, sakin ledar Dillaliya ta yi cike da takaici Iya ta bi ledar da kallo rai a Sace ganin"

Dillaliya ta jefar mata da kayan kuWin da take saka ran karSarsa ba kaWan ba.

"""Haba Dillaliya wannan irin jefarwa ai sai ki rage musu farashi haba ke da zan ga kina murna kina tsalle kina sanya mini albarka na kawo miki kayan arzi™i har gida""Takaici ya hana Dillaliya"

magana sai da ta haWiya wani malolon ba™inciki sannn ta buWe baki ta ce

"""Ina kayan kuWin? Wannan ne abin arzi™in ko dai na tsiya ni amma tsinta kika yi a bola ko?"""

"""A kakar bola na tsinta bana son iya shege Dillaliya ni za ki wa tonon silili, da cin fuska, ki kalli"

"sar™ar miliyoyi ki ce a bola na tsinta to wannan tun ta aurena ce """

"""Ai ni ba zan biye miki ba sai dai in ce ki kwashe tarkacenki ki fice mini a gida dan duk wanda na kai wa ya siya sarkar nan cewa zai yi bani da hankali dan wannan ko ΄an gwangwan da baban bola ba za su siya ba, su ne dai masu siyan tarkace, saboda son banza har da wani"

"Wakko ledar viva za ki sanya kuWi to ai ko naira biyar babu mai siya"""

"""Ke kuwa Dillaliya Allah wadaran naka a lalace in ji jakin gida da ya ga jakin daji, ke ma ta su Umarun za ki mini da suka ce sai dai a kai wa baban bola, dan wula™anci sar™ar tawa ta mutan da"

"wacce na daWe ina tanadi"" Haushi ya sanya Dillaliya tashi tsaye tana nuna wa Iya hanyar waje."

"""Ko baki faWa ba tafiya zan yi kuma wallahi kin yi wa arzi™i dundu, aikin banza jiran jirgi a tashar"

"mota"" Iya ta faWa tana tashi daga zaunen da take ta saka ledar sar™arta a ajjihunta ta fito daga gidan tana sababi."

"""Wai ko dai akwai ™amshin gaskiya lamarin nan, ya za a yi a ce bakin su ya zo Waya da su"

Umaru? Wani Sangare na zuciyar Iya ta jefa mata tambayar.

"""Babu wani nan kawai tsabar ba™inciki ne da hana ruwa gudu"" Wani Sangaren na yaudararriyar"

zuciyarta ya bata amsa.

Hankali kwance ta kama hanyar kasuwa tana addu'ar Allah sa ta samu masu siya da daraja. Tun da ta shiga kasuwar take yawo abinka da kasuwar ™auye duk sai Iya take ganin kuWin da

take hari za a bata gaba Waya zai iya saye kayan kasuwar gaba Waya.

"""Malam nawa-nawa"" Cewar wata budurwa da ta Waga abin hannu na tsakiya mai ™anana."

"Hankalin Iya gaba Waya kan su ya koma ganin mutumin sana,arsa siyar da kayan tsakiya na"

wuya da kunne da na hannu duk ya rarrataye wasu kuma suna zube a kan tabarmar gabansa.

"""Naira hamsin -hamsin"" Ya faWa yana kallon yarinyar Iya kuwa gabanta ne ya shiga faWuwa ya"

saki baki tana kallonsu.

"""Yo ke ai taki ta mutane da ce kuma mai manya -manya"" Wani Sangare na zuciyarta ya bata"

"amsa, wata ajiyar zuciya ta sauke dan har ta ji hankalinta ya Wan kwanta."

"""Uku Wari idan ka siyar"" ""kawo"""

Ya faWa ko musu babu.

"""Yanzu abin hannun ne guda uku Wari, saboda ma rashin darajar su ko musu bai yi ba?"" Iya ta"

faWa a zuciyarta tana Waga ™afafunta da suka yi sanyi ™alau ta nufi wajen mai kayan.

Wanda ba za su yi SUBSCRIBE ba idan suna bukatar littafi za su biya 5OO ta acc Faiza

abubakar 9030283375 Opay

TALLAH! TALLAH!!! TALLAH!!!

"Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koWewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai"

"rahusa ki Wora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada."

"Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ™auri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ™amshi da daWewa a Waki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ™amshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa la™abi da"

sumar da mai gida don ™amshi.

"Muna da Toilet cleaner in har toilet Winki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ™amshi da yake yi Waya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ™amshi, turaren wanka luquid soap, izal"

"hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa."

Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da

"na ΄a΄anta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari "

"Akwai cotton material da lesuka da atamfofi, abaya, takalma, kayan yara siyan Waya ko sari."

TuntuSe ni a wannn lambar 09013181851

"[12/23, 15:51] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/Duq93sLLgjCKV0uuildAH1"

³AN ADAIDAITA SAHU

(Masu keken napep)

NA

MAMAN AFRAH

GARAASA GARAASA

Akwai youtube chanel Win da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta

hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp.

"Waya zaSin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA"

RUBUTA SHIRME

kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaWai za ki gwangwaje da karatu.

"a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki"

iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE

"Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ³AR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA,"

"KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA."

09013181851

Page3



Sai da ta tsaya ya sallami yarinyar sannan ta matsa kusa da shi kamar za ta masa raWa.

"""Ala gafarta malam ina son magana da kai"""

"""Sar™ar za a baki ko abin hannu"""

"""Abin da na zo maka ya fi gaban wannan"" Ta faWa tana waiwaya wa hagu da dama kamar wata"

"munafuka, ganin kowa yana sabgar gabansa sai ta ji hankalinta ya kwanta."

"""Kamar yaya?"""

"""Babu komai sai alkairi dan haka ka kwantar da hankalinka ni ba da sharri na zo ba, taimakon juna za mu yi, wato ina Wauke da kayan kuWi ne a jikin nan nawa, to shi ne nake so mu yi sirri tsakanina da kai Allah ya zame mana shaida"" Ta faWa har lokacin tana masa maganar kamar raWa amma kuma ana iya jin duk abin da take cewa, daga gefe guda wasu samari ne guda uku a zaune a wani benci Waya daga cikinsu yana zu™ar sigari kana ganinsu ka ga ΄an jagaliya, dan duk kamar ma sun shayu idanunsu jawur. Duk abin da Iya take yi suna kallonta a fakaice kuma suna jin abin da take faWawa nutumin sai dai babu wanda zai ce ma suna sauraron su, domin"

dama duk wanda ya iya allonsa sai ya wanke.

"""Wane irin abu ne na dukiya a jikin ki amma ni ban ga alama ba"" Ya faWa yana wani washe baki har da saka harshe ya lashi leSSansa saboda ya ji maganar kuWi shi kuma dama mayen kuWi ne duk da ya san ™uda wajen kwaWayi akan mutu, amma dai yanayin yadda Iya take magana ya"

fahimci gaskiya ce babu sirkin ™arya dan haka sai ya ji ya amince da ita.

"""Ba zan iya ambata maka ba saboda cikin kasuwa bashi da sirri, wuri ne na jama'a kuma wuri ne na ka zo na zo, sai dai ina maka albishir da cewa idan har ka nuna mini inda aka siyar da kayan nan to na tabbatar za ka samu abin da za ka gina kan ka da shi, dan ba lallai ma ka ™ara kasa sana'ar tsakiya ba, saboda ni kaina ina tunanin za a siyi hajar da mafi darajar kuWin da ba"

"lallai su lissafu ba"""

Mutumin mai kimanin shekara sittin ya zaro idanu dan gaba Waya mamakin Iya ya kashe shi

hakan ya sanya ko dogon tunani bai bari ya wahalar da kansa ba take yanke ya amince.

Gaba Iya ta shiga ya take mata baya ko takan kayan sana'arsa bai bi ba dan yana ganin banza ta faWi. Da yake daga inda ya kasa kayan nasa akwai wajen da wata ™ofa take fita sai kawai suka bi ™ofar da ta fito da su daga kasuwar sauri Iya take yana binta iska sai kaWa babbar rigarsa take

wacce ya saka babu ko ΄ar ciki.

"""Mu tsaya mana a nan"""

"""A'a baka ganin daga ni har kai girma ya fara mana sallama kar a je wani ya warce kafin mu nemi Wauki ya gudu gwara dai hanyar lafiya a bita da shekara"" Sai da suka zo ™ofar wani gida suka tsaya Iya tana son fito da sar™ar tana tsoro saboda idanun jama'a duk da babu wanda ya"

kawo su a ka amma ita ganin ta ri™o kayan kuWi sai take jin bata yarda da wajen ba.

"""Malam mu shiga daga zauren gidan nan in nuna maka mu yi komai cikin sirri in ya so idan ka gani ka faWi wajen

Please Login or Register in order to submit comment