ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuraina, Allah ka jinkirta mini mutuwata ba yanzu ba sai na aurar da marayan nan Jaburu Allah ka sa mala'ikan nan ya tafi ba tare da ya Wau raina ba"" Ta faWa tana son Wagowa amma tana tsoro ta buWe idanu ta gan shi, har sai da ta zo yin sallama sannan ta buWe idanun ta kalli hagu da dama ta yi sallamar a hankali kamar mai raWa. Yana nan zaune"

kansa a sunkuye bai Wago ba.

"Karkarwa jikinta yake tun ™arfi ta kasa jin ™arfin da za ta iya barin wajen da take ma. ""Ansatu"""

Ta ji ya kira sunanta da wata murya kamar ta larabawa dan ya yi muryar uztazai sai

"hakan ya ™ara bata tabbacin mala'ikan mutuwa ne, musamma da ya kira sunanta na gskiya bai ce Ansai ba kamar yadda ake kiranta da shi ba. So take ta amsa amma kuwwar da cikinta yake"

yi ga shi bakin nata ya ™i ko da ba laSSanta ne damar su buWu bare har ta kai ga yin magana.

"""Ansatu a yau ne wa'adinki ya cika, yau za ki koma ga ubangijinki, dama kwanakin ki suna ™aruwa ne saboda yawan zumunci kin san idan Wan adam yana yawan zumunci Allah yana ™ara masa kwanaki, to kuma kina taimakon maraya amma yanzu kin kasa masa abin da yake so"" Ya"

faWa cikin muryar nan ta ustazanci yana wani ma™ale muryar.

"""Wallahi ban daina zumunci ba wajen kawu RibaWo ma ina yawan zuwa kafin Allah ya masa rasuwa, wallahi maganar Jaburu kuma Wazun nan ya ce a bar siyen arincaSar sai ta sakko"

"saboda ta yi tsada"" Ta faWa cikin rawar murya tana fatan Allah sa kar ya Wauki ran nata."

"""Ai yanzu ma bata Saci ba za ki iya zuwa ki siyar da gonar gaba Waya ma ba sai kin bi ta kan"

"΄a΄anki ba, ko garin ne ku bari ke da marayan da kuWaWen sai ki siyar cikin sirri ku tafi birni a"

"saya masa farin cikin maraya ba ™aramin abu bane"""

"""Wallahi zan siyar a yau ba sai gobe ba zan je wajen Alhaji Audu gobe za mu daka sakko mu tafi"" Ta faWa cikin tsoro da karkarwar baki dan tsoron tana magana da mala'ikan mutuwa har da"

sakin fitsari a zaunen. Sai da ya tsorata ta sosai ya tabbatar ta tsorata sannan ya ce

"""Ki rufe idanunki ki yi sujada saboda kar guguwar Sacewata ta tafi da ke... Tun kan ya ™arasa faWa Iya ta dur™ushe ta yi sujadar idanunta Sam a rufe, laSSanta kaWai sun fahimci halin da take ciki saboda karkarwar da suje suna haluwa da ha™oranta, ta saman bayanta ya lallaSa ya tsallaka ya"

silale ya fice daga gidan baki Waya. Kayan ya je ya mayar wa mai su.

"Tun da ta yi sujadar take ta faman istigfari har Jabiru ya dawo har zuwa lokacin bata ta shi daga sujadar ba. Da sallama ya shigo yana ™wala mata kira, yana cewa ga batir Win da ta bashi kuWi ya siyo. A kiWime ta Wago ta sauke numfashi batir Win ya saka ya kunna fitilar haske ya"

gauyaraye Wakin. Ta haWa gumi jargaf tamkar an she™a mata ruwa har jikin hijabin nata.

"""Iya lafiya dai kika Wago baki salance ba ke da kike sallah?"" ""Jaburu"

"baka ga kowa ba?"""

"""A ina Iya"""

"""A'a shikenan a bar kaza a cikin gashinta, maza ina so za mu fita da kai fita cikin sirri"""

"""To Iya ai dama da ke muke sirri babu wanda zai ji ""Jaburu za mu tafi gidan Alhaji Audu"""

"""Mai za mu yi a can Iya"""

"""Bakin ka alekum Jaburu"" Da to ya amsa mata, dan ba ya son jan maganar tun da ya san mai"

za su je yi. Babu wanda ya lura Iya da Jabiru suka bar gidan sai gidan Alhaji Audu bayan ta

sanar da su Baba kar su je ta fasa siyar da gonar. Sun tarar da Alhajin a falonsa bayan matarsa

"ta musu iso aka fita aka bar Iya da Alhaji sai kuma Jabiru da yake zaune a gefe, bayan an gaisa Iya ta ce"

"""Alhaji na zo da wata magana ne dama, amma ina fatan ka amince mini ka taimaka ina cikin"

"matsuwa"""

"""An zo wajen da nake son a zo"" Cewar Alhajin a zuciyarsa a fili kuma sai ya ce."

"""Babu komai Ansai ai indai ina da hali zan miki"" Ya faWa cikin kwantar da murya dan ya gama"

gano lagwanta. Jabiru kuwa sai dariya yake a zuciyarsa ganin cikin ruwan sanyi burinsa zai cika.

"""Dama magana nake so na maka a kan gonar gadon nan da ka je da maganarta ranar nan..."

"""Haba ai babu komai tun da noma ta kuke ki bari wata rana idan kuka tashi siyarwa sai a siyar..."

"""Ban tari numfashinka ba amma na zo ka karSi jinginar Sangarena a cikin gonar, ka bani kuWin sai kake noma Sangaren nawa, amma kuma idan na mayar maka da kuWin sai ka mayar mini da gonar ina cikin bu™atuwa kuma kar wanda ya ji maganar nan a sirri nake so a yi kar wanda ya"

"sani. Dan gobe asubanci zan yi mu bar garin nan ni da Jaburu ba tare da kowa ya sani ba"""

"""Gaskiya hakan ba zai iyu ba"""

"""Na shiga uku ni Ansai shikenan mala'ikan mutuwa zai zo ya Wauki raina in har ban cikawa marayan nan buri ba wayyo Allah ka kawo mini Wauki"" Ta faWa a zuciyarta tana jin faWuwar gaba"

dan bata son ta mutu yanzu.

"""Lahaula wala ™uwwata illah billah, ha™ata ba za ta cim ma ruwa ba kenan duk abin da na yi ya"

"tashi a banza kenan?"" Jabiru ya faWa a zuciyarsa kamar ya yi kuka."

"Tun da Iya ta dage tana ta bashi ha™uri dan ganin bai hana ba dan bata son ko kaWan ta mutu,"

shi kuwa Jabiru ya san dalilin da Iyar ta nace a kan cewa sai an karSi jinginar gonar.

"""Sai dai na karSi jinginar duka gona amma ba wani Sangare na gona ba, idan har kin dawo da kuWi a mayar muku gona idan baku kawo ba gona ta zama mallakina"" Shiru Iyar ta yi tana nazari ganin in ta bada gonar duka da mai za suke noma suna cin abinci amma tsoron kar mala'ikan mutuwa ya zo ya tafi sa ranta sai ta amince babu musu dan tana ganin idan har suka bar garin da kuWin hayar adaidaitar za su tara su kawo a biya kuWin gonar. Naira miliyan uku, basu dan dama ya gama sanin wurin dan ranar nan har cewa su Baba mamman ya yi zai ™ara a kan naira miliyan ukun Win amma suka ™i. Hannun Iya har karkarwa yake ta saka ta ri™o jakar miliyoyin kuWin dan dama shi Wan kasuwa ne kuma bai fiya ajiye kuWi a banki ba. Babu wanda ya"

san sun dawo gidan haka suka lallaSa suka koma gida babu wanda ya san wainar da suka

"toya da za su tafi ne ma ya kirawo matarsa dan ta zama sheda sai takarda da ya ba Iya ta saka hannu alamar ta karSi kuWi. Da dare Iya a kan jakar ta yi rufda ciki a kai daga ita har Jabiru babu wanda ya yi baccin kirki dan Iya ko bacci Sarawo ya Wauketa a tsorace take farkawa hannunta dam™e da jakar, amma a ranta ko da na sani bata yi ba na bayar da jinginar gonar, sai dai tana da ya™inin Jabiru zai tara fiye da kuWin a sana'ar adaidaitan wanda za su dawo da shi su mayarwa sa Alhaji Audu ya mayar musu da gonar tun kafin ma damuna ta yi hakan ya sanya ta ce za su yi asubanci domin zuwa birnin Kano a can za a siya adaidaitan a nemi kuWi a can ta san muddin ta zauna dole ΄a΄an za su samu labarin abin da ta yi amma idan ta bi Jabirun suka tafi tun da bai san ko ina ba kamar yadda ita ko Kanon ma bata taSa zuwa ba tana dai jin"

labarinta kuma haka mala'ikan ya bata umarni a kan su tafi birni tare.

Jabiru kuwa ransa fari tas yana jinjinawa kaifin ™wa™walwarsa da ta sama masa mafita a kan

cikar burinsa cikin sau™i.

*DA ASUBA*

"Iya a kiWime ta sakko daga saman gadon nata, tana ™an™ame da jakar kuWin dan ko kaWan bata cikin kwanciyar hankali, gani ma take kamar dai Sarayi za su zo su burma mata wu™a su ™wace kuWi a haka ta kwana cikin taraddadi. A hankali ta shiga tashin Jabiru tana masa magana raWa-"

raWa.

"""Kai Jaburu tashi mu san inda dare ya mana, kar gari ya waye asiri ya tono a samu matsala"" Ta"

faWa masa lokacin da ya tashi zaune.

"""Dan aradu ban shirya mutuwa ba yanzu duk da daman mutuwar ba wai ana mata shiri bane, amma gwara dai in zauna in yi istigfari sauran laifukana su wanku"" Ta faWa a zuciyarta lokacin da tunanin mala'ikan mutuwar da ya ziyarce ta jiya ya faWo mata bata san cewa Jabiru ne ya mata iya shege irin na yaran zamani ba. Jakar kuWin ta zazzage ta yi wani Wauri da wani ™aton Wankwali a ™ugunta ta kwashi kuWin ta Wura a ciki da yake kuWaWen suna WaWWaure da kyaure sai ya zamana saitin mararta ya yi tozo kamar mai ciki saboda kuWin da kuma tudun Wankwalin da ta"

loda.

"""Iya ya kika cire su daga jakar?"""

"""Kai tun kafin a haifi uwar mai sabulu barbela take da farinta, yo har a nunawa na rigingine farin wata ai ka san an ce mugu shi ya san makwancin mugu, yanzu idan muka tafi da su a jaka Sarayi za su iya tare motar mu amma idan na saka a cikina na yi dibarar mu ta manya Allah za"

"su yi tunanin ko juna biyu ne"""

"""Haba Iya tsofe-tsofe da ke za a ga wani juna biyu"""

"""Kai Jaburu bar ni in mutu maza su kai ni ba mata ba, wannan dibarar da ita za mu tafi dan"

"haka mu lallaSa mu bar gidan nan Allah zai kai mu lafiya ka san bahaushe ya ce dogaro ga Allah jari ne"" Ta faWa tana kallon Wakin nata ta cikin hasken farin wata."

"""Allah sarki Wakina saduwar alkairi sai na dawo na san lokacin da za mu dawo da kuWi dumu-dumu a jikinmu wata™ila ma sai dai a gina mini Wakin siminta amma kai ba zan sa a"

"rusheka ba zan barka ko dan tarihi"" Ta faWa a ranta tana le™o waje dan tabbatar da ba kowa, haka suka lallaSa suka bar gidan Jabiru yana ri™e da wata babbar leda mai Wauke da kayansu kala"

bibbiyu.

"Tun da suka fito suka nufi bakin kasuwar ™auyen sai dai babu wata mota da za ta tashi tun da lokacin da duku-duku ne ko sallar asuba ba a shiga ba. Jabiru ne ya je ya tado wani abokinsa mai hayar machine dan dama ko da sun hau motar ma a tashar garin nasu babu wacce za ta kai su Kano kawai dai za ta kai su garin da za su samu motar ne. Su duka biyun suka hau machine Win da yake abokin Jabirun ya ji kuWi da za a bashi mai tsoka da yake Iya ta Wauka musu kuWi a cikin kuWin gonar, lokacin da suka je garin Širani an fito daga sallar asuba dan haka a tashar ya sauke su, Iya ta bashi kuWinsa yana murna ta kuma bashi sa™on wajen su Baba Umaru a kan ya sanar musu tana cikin ™oshin lafiya kuma duk abin da Alhaji Audu zai faWa musu dangane da gona gaskiya ne sai dai ta nannage shi a kan cewa ba zai faWi sa™on ba sai da yamma, ita ta yi hakan ne dan jar su daWe basu dawo ba su kuma su Baba su ™aryata Alhajin duk da tana da ya™inin dawowar su da wuri saboda bahaushe ya ce fata na gari lamiri. A tashar suka yi sallar asuba gari na wayewa aka fara lodi su Iya ne farkon shiga motar amma tun kan su shiga ta sanar da direba cewa ba za a ta biya wa Jabiru kuWin mota ba mai mota kuwa ya ce ba"

zai Wauke shi a kyauta ba. Ko da Jabirun ma ya ce ta biya sai ta ce

"""Kai Jabiru baka da hankali ka san dai kuWin arincaSa ne idan muka taSa kuWin nan da yawa aka zo bai isa ba fa? Daga ni har kai babu wanda ya san kuWin arincaSar"" Ta faWa masa cikin raWa dan haka shi ma sai ya yarda. Da mota ta cika Iya ta gar™ama Jabiru a kan cinya ko da mutane suke"

ce mata ya yi girma ta ri™e shi a cinyarta sai ta ce

"""Ni Ansai na ga Satan nono a ™irjin budurwa, ku dai ΄an adam bakwa mutuwar Wakin ku sai ta wani, ai dama na san a rina wai an saci zanin mahaukaciya to Jaburu dai jikana ne kuma da kuke batun na Wora shi a cinya nawa ma Jabirun yake yaron da ba a daWe da yaye shi ba"" Ta faWa tana sababi babu wanda ya ™ara cewa komai a haka mota ta tashi ta kama hanyar Kano ta dabo tumbin giwa. Tun da tafiya ta yi nisa sai idanun Iya suka raina fata saboda ™agewa da ™afafunta suka yi domin Jabiru ya yi bacci duk jikinsa ya saki, amma a haka ta daure duk da iskar da ake"

yi ta haWa guSi sharkaf ga yunwa babu abin da suka ci.

*KANO*

"Tun da motar su ta shigo garin Kano bakin Iya yake a sake kamar layar mai tafiya, ganin garin"

cike da motoci da machina ga adaidaita sahu sai kuma jama'a kamar me.

"""Na shiga aljanna na ma™ale ni Ansai, ha™i™a bahaushe ya yi gaskiya da yake cewa zo mu ci tuwo ya fi tuwon daWi, dan Allah haka dama Kanon take wallahi yadda ake bada labarinta ta wuce nan, kai jama'a ji yadda motoci suke tari-tari babu adadi"" Ta faWa a fili tana ri™e da haSa mamaki ya cika ta duk abin nan da ake Jabiru bacci yake bai san wainar da ake toyawa ba ΄an cikin"

motar kuwa sai dariya suke jin kalaman Iya.

"""Jaburu, kai Jaburu kai tashi da Allah can kai sai bacci kamar kasa"" Ta faWa tana Waka masa duka dan ya tashi kar take kallo ita kaWai. ˜aran horn na motoci da machine da hayaniyar jama'a su ne suka sanya Jabiru wartsakewa ya saki baki da jajayen idanunsa na masu bacci yana bin"

garin da kallon mamaki.

"""Laaaaaaaaa Iya kin ga adaidaita sahu wallahi sak yadda aka bani labarinta kuma iri Waya da ta hoton littafin nan"" Ya faWa da ™arfi yana nunawa ta window bakin nan a washe kamar gonar"

auduga.

"""Dan Allah Jaburu ka ce har ka hangi arincaSar a ina take?"" Iya ta faWa tana Waga suya dan ta ha ga tun da ita duk wannan faWi tashin da take bata san ma ya adadidaita sahun yake ba dan"

bata ma taSa gani ba ko da hoto kuwa.

"""Haba Iya duk gasu nan sun cika garin ko ina, su ne fa waWannan ruwan Worawar (Yellow) Masu kamar mota"" Ya faWa daidai lokacin da direba ya faka motar a bakin tasha dan ba cikin tasha zai shiga da su ba, wajen kuma iya ganinka masu adaidata sahu ne sun lallaya adaidaitan. Tun da aka buWe motar kowa ya shiga fitowa amma Iya gaba Waya sai jikinta ya yi sanya ga sanyin da ™afafunta suka yi saboda zaan da Jabiru ya yi a kanta ga shi har lokacin mamaki ya ya mamaye"

mata zuciya na ganin adaidaitan a haka ta fito.

"""Baba adaidaita sahun ne?"" Wani matashi mai neman fasinja ya tambayi Iya."

"""Hajiya ina za a kai ki?"" Wani ma daga gefe Wayan ya zo yana tambayar Iya, ita kuma ta saka hannu biyu ta dafe cikinta dan ita ganin jama'ar garin ma duk sai hankalinta ya tashi a nata"

ganin mutane sun yi yawa garin ma ya yi girma.

"""Jaburu yanzu dama a kan wannan abun ne ka sanya na Waga hankalina, na rin™a tada zaune tsaye duk dan ganin ka mallake shi, Jaburu a kan wannan abun ka sanya na siyar da gonar"

gadon da muka gada wajen Malam ni da su Umaru...

"""Wai mai ya kawo wannan maganar ne Iya? Kin manta ni da kaina na ce ki bari sai ta sakko ke"

"da kan ki kika ce mini mu je jiya wajen Alhaji? Kuma dama ai haka adaidaitan take"""

"""Yo mene ne ma bai kawo ba yanzu a ce saboda wannan abun mai ™afafu uku ne na siyar da"

"gonar gado, ka san yadda gonar gado take kuwa, wannan abu riWimWim a kife kamar wani kunkuru sai wani shegen labule da ake sakawa kamar ana munafurci a ciki, kana ganin masu hayar arincaSar ma yadda ka san san almajirai sai suna bi jama'a suna fadanci kafin su samo fasinja, ni ba na Wauka wani abin kirki ne, abin arzi™i duk tunanina zai yi shige da jirgin sama ni wannan abun ko birge ni bai yi ba shi ya sa ma ko farkon shigowarmu garin nan idanuna suna ma™ale a kan motoci da machina, sai kuma mutane da nake kallo dan ni wannan abin ma da na gansu wallahi a tunanina motar lodar agwagi da talo-talo ce"" Ta faWa tana rushewa da kukan"

takaicin an rabo ta da gida ga takaicin ganin adaidaita sahu ba yadda ta tsammata ba.

"""Haba Hajiya ya za ki zo nan ki cika mana kunne da kuka kamar dai ana zaman makoki?"" Wani"

matsashi ya faWa yana kallon Iya da take tsaye da Jabiru yana bata baki.

"""Kai ina ruwan biri da kada?"" Iya ta jefa masa tambayar tana harararsa."

"""Dama babu amma kuma ki sani nan wajen ba wajen kuka bane gwara ku je gida ki samu wuri"

"ki zauna, kowa dai ya san wajen nan ba ya rasa ΄an daba da Sarayi masu ™wace..."

Dididimdim gaban Iya ya bada wani sauti dan ta tsorata sosai da ya ce ΄an daba ne da masu

™wace dan bata manta da karon su da wanda suka raba ta da sar™ar murjaninta ba bare kuma yanzu da take Wauke da ma™udan kuWi in aka ™wace mata an ta™aice ta.

"""Dan Allah yaro ka yi ha™uri da kalamina dama mu ba™i ne a garin nan babu inda muka sani babu"

"kuma wanda muka sani ka taimaka mana edan Allah"""

"""Iyeee taS sai dai ku biya mu je gidan da nake kwana amma fa gaba Waya maza ne a gidan sai"

"mata maza """

"""Zan biya yaro kuma batun maza ma ka ajiye a gefe na san duk basu fi jikokina ba, mata maza kuma ai su ma halittar Allah ne zan biya na sati guda kafin in samu in fara wanke wanke da"

shara sai in ke biya duk wata...

"""Haba Iya wane wanke wanke kuma?"" Jabiru da bai san manufar Iya ba da ta faWi hakan ya"

tambaya.

"""To ina ruwanka ita ma ai sana'a ce kuma ma ke samun abin zubawa a bakin salati"" Iya ta faWa jin Jabiru zai mata Saran Sarama dan ta san zai iya nuna wa akwai kuWi a jikinta aje a mur™usheta"

a ™wace cikin dare.

"""To kya samu kike kwanan dai amma batun wajen aiki sai dai ki fita ki nemo da kan ki"""

"""Wannan ba abin damuwa bane"" Ta faWa a fili a zuciyarta kuma sai ta ce"

"""Mun kawo kan mu ni Ansai yanzu muna zaune a cikin mutunci da sutura amma mun zo wajen"

"kwana ma zai ke gagararmu, ni ban san mai ya Wauki hankalina ba ma ban yi tunanin mazauni ba"" Ta faWa a zuciyarta tana Wan jin da na sanin tahowar amma kaWan dan har yanzu bata saduda ba dan ta ci alwashin cikawa Jabiru burinsa duk da dai ta ga adaidaita sahun ba kamar yadda ta"

tsammata ba.

"Yana gaba suna biye da shi, Iya kuwa sai aikawa Jabiru harara take tana masa kashedi da idon wanda shi ko kaWan bai gane manufar hakan ba ita kuma tana masa hakan ne dan ar ya yi suSul da baka wajan bayyana dalilin zuwansu Kanon da kuma abin da suka ri™o dan ta san ba"

™aramin aikinsa bane.

Šan sahu ya kira ya faWa masa inda zai kai su suka shiga amma Iya dakyar ta shiga. Sun

zauna shi abokin tafiyar tasu a aljihu ya zauna wato can kusa da direban a bayan kuma Iya da Jabiru.

"""Oh inda ranka ka sha kallo, taS dama in ka ji makaho yana cewa a yi wasan jifa to ya taka dutse ne"" Cewar Iya cikin al'ajabin idanunta ™urrr a saman adaidaitan daga ciki bayan ta kama"

™arafan jiki da hannu biyu ta rirri™e tamkar mai tsoron faWuwa.

"""Ke tsohuwa kar fa ki zage mu muna zaune ah to na ji sai yada magana kike"" Abokin tafiyar ya"

faWa cikin muryar gagararre.

"""Allah ka rufi bakina ka.Soyi muryata ni shegiya in ji kaza haba Wan nan ni ina na ga ™arfin halin zaginku wallahi karin magana ne dai na yi, ka san ban taa shiga arincaSar nan ba hasali ma ban taSa ganinsa ba sai yau wallahi ko a falsafar hoto ban taSa gani ba shi ne fa nake ta al'ajabi lallai Allah buwayi ne gagara misali"" Iya ta faWa cikin sanyaya murya dan ita tsoron Kanon ma duka"

ya kama ta bare kuma shi wannan mai zubin ΄an sara sukan

"""Ah ko da na ji ai na Wakko da ni kike ne"""

"""Ah wallahi"" Jabiru kuwa sai dariya yake dannewa ganin Iya tana kaffa-kaffa da saurayin tamkar"

wani ubanta.

"Sai da mai adaidaitan ya tsaya a daidai gidan da saurayin ya nuna masa, baki sake Iya take ganin wani wawakeken gidan ™asa wanda kamar saukar damina yake jira ya ruguje saboda"

yadda ya tsufa duk ya rufta.

"""Ba dai a wannan ruSaSSan gidan za mu sauka ba kamar wasu masu gudun hijira ai da wannan gida gwara gadar da ake cewa ana kwana a ™asanta a garin legas duk tsiya dai ita babu alamar rugujewa a tare da ita amma wannan gida daga ganinsa kabari salama alaikum ne ko kuma a"

"kira shi shiga da likkafaninka"" Iya ta faWa a ranta lokacin da take ™o™arin fitowa."

"""Nawa ne kuWinka?"" Saurayin nan ya tambayi mai napep Win dan saboda ™arfin hali ma ko ciniki"

bai yi da mai napep Win ba kan cewa a nawa zai kawo su.

"""Dubu Waya ne"""

Iya kuwa tun lokacin da ta ji yana tambayar kuWin sai ranta ya cika da murna ganin banza ta faWi sun zo a Sagas za a biya musu kuWi kyauta tana shirin buWe baki ta fara jero masa godiya ta ji

ya ce

"""Iya sai gare ki na tambaya miki kuWin sai ki biya shi"" Baki sake Iya take kallonsa jin abin da ya yi kallon Jabiru ta yu da ya yi saurin Wauke kai yana danne dariyarsa dan tuni ya hango jirginta"

ya san ta Wauka banza ce ta faWi sai kuma ta ji wani batun da ban.

"""Na ji abu bambarakwai wai namiji da suna hajara, wannan ai shi ae kira hajaran majaran, ashe dai da ya yi gwargwaWan a gaban araincaSar ba shi zai biya kuWin ba"" Ta faWa a zuciyarta tana"

Wakko kuWin ko ragi bata da damar nema ta mi™a. Har ya tada napep Win zai tafi Iya ta ce

"""Dan Allah tsaya Wana zan maka tambaya"" Dakatawa ya yi yana kallonta sai da ta ™arasa wajen"

kamar mai raWa ta ce

"""Ka yi ha™uri da tambayata, ni ba™uwa ce a garin nan, dan Allah duk waWannan arincaSar da na"

"gani a can bakin tasha bila adadin kamar jamfa a jos dukansu akwai masu su?"""

"""Mene ne arincaSa?"""

"""Irin wannan kunkurun da kake tu™awa"""

"""TaS lallai tsohuwa an gaishe ki wallahi kin ci gaisuwar ban girma"""

"""Dama girman ne ya kama ni Wan nan amma ka san an ce matambayi ba ya Sata"""

"""To nan da kika gani kowa da nashi kuma kowa ya san wannne ne nasa a wajen nan wani abu"

"ne aka yi?"""

"""Ikon Allah na zaune ya faWi, babu abin da aka yi kawai dai cewa na yi Allah ™ara muku kaifin basira da kowa daga cikin ku yake iya gane wanne ne nasa duk kuwa da yawansu kuma kaloli"

"Waya ne"""

"""To mun gode"" Ya faWa yana jan napep Win a guje ya bar wajen. Tsayawa ta yi tana bin sa da kallo tana ta mamaki wai a kan wannan kunkurun abun suka baro gida ita bata taSa kawowa"

cewa haka adaidaita sahun ma yake.

"""Amma kuma ana samu wallahi, ji fa yadda sawu Waya ya yi aka bashi naira dubu guda ko canji"

"babu kuma ko ragi ban ji an nema ba duk da unguwar tasu akwai nisa kuma lungu ce, yanzu mu idan muka fita tun safe ai ina ga kafin dare mun yi cinikin da ba lallai mu iya lissafa su ba"""

Ta faWa a ranta.

"""Iya ki zo mu shiga

Please Login or Register in order to submit comment