You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
tsinke kiran zee ta bushe da dariya ta maka wayar da k'asa ta dauki dayarma ta tarwatsa ta da k'asa tasake daukan gudarma ta fasata duka wayoyin ukku sai tayi musu fila fila taga babu mamora ajiknsu reza ta dauka taje saman bed d'insa ta cicira zanan gadon wardrobe d'insa ta bude saida tazabi kaya kala goma masu tsada da kyau Wanda yafi so tayi musu fila fila yada bazasu moruba dressing mirror taje duka turarukansa sama da kwalba goma ta farfasa da maiyukansa na kwalla ko daya bata bariba d'akin ya dauki wani fitinanan kamshi wlh barna tamasa ba tawasaba ga wayoyinsa ukku babu daya da zata taba anfanuwa ihu tai tayi tsalle tana dariya " Dole kaji bakin ciki dan iska mugu banma gama ramawaba Allah da saura bari naje nayi Sallah Astagfirullah Allah ta fada tana tafiya kofar ta bude ta fice tana dab da fita daga cikin parlon taji maganarsa anutse ba hayaniya cikin zazakar muryasa ya damfaro parlon cike da tsoro hankalinta yakai makura tashi sai zaro idanu take tana neman inda zata boye........
*💖💖👩🏻🦱ZEE BABY👩🏻🦱💖💖*
*DAN ALLAH KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE*
*👉🏻11*
....Kafin nayi wani yinkuri naji an murda kofar da sauri na koma bayan kofar na labe yana shigowa tun daga parlo yakejin kamshin turarensa hanyar bedroom d'insa ya nufa ai tanaga ya karya kwanar da zata sada shi da bedroom d'insa ta fito ta zuba da gudu hankalinta atashe karo taci da Mahabeer ya rikota " my zee menene duk kika tsorata haka rumgumesa tayi " Yaya Mahabeer wancan mugun ne nawa barna duk na fasa masa wayoyinsa da turarukansa da kayansa duk na yankasu wlh tsoro nake kar ya kasheni hankalin Mahabeer atashe ya kamo fuskata " haba my zee ya zaki rika shiga zabgarsa yana dokarmun ke ya ilataki kinsan kimanin kudin wayoyinsa da kika fasa shagwabewa nayi " to Yaya Mahabeer kasan irin wahalar da ya bani yau kawai fah dan nayi shaye shaye " wlh nima zamu bata dake idan kina shaye shaye " bari na shiga gida kar yafito jikinta ta janye tayi part dinsu da gudu parlo ta shigo tana maida numfashi gun ghaisha ta nufa ta fada jikinta rumgumeta ghaisha tayi " momy kirage rashin ji kinji? " to ummi naji ummi muje bedroom dinki nayi wanka nayi sallah " to taku fah? shiru tayi Daddy yace " momy bakijin yunwa?
" inaji bari nayi wanka da sallah ta Mike ta nufi bedroom d'insu saida ta murza key akofar khaleesat na zauna saman kujera zee ta kalleta " my khalisat me kikeyi? murmushi tayi " bakomai Amarya yayamu dariya zee tayi ta nufi bathroom ta sallo wanka ta fito daure da towel abaya ta saka ta shimfida darduma tayi sallolin da ake binta magarib da isha tajima tana neman gafara gun Allah ta Mike ta cire abayar tasa kayan bacci Riga da wando dogaye har kasa, akwatinta ta nufa, ta kwashe kayan mayanta ta boye dan tasan tabbas zai nemesu " my khalisat muje parlo mana kin wani gumshe ad'aki mikewa tayi suka fito kusan Daddy ta zauna ta kwantar kanta kafadarsa " Ammin zanci Shawarma? " to momy yanzu kuwa zakici wayarsa ya dauka ya kira Dr Sardauna amma wayoyin duka akashe mamaki ya kamshi "Najib maza kiramun Dr yazo ina kiransa" to Daddy kanwata ina wayata?? idanu ta zaro " wai bro kaje tana Swimming pool wlh namanta ta tana k'asan kujeran farko " ok yace ya fice zee ko duk hankalinta atashe yake jin za'a kirawo Dr Sardauna, bangaran Dr
Sardauna ya shiga da niyar ya kara cin ubanta ya korota yana shiga yaci karo da irin tijara da zee baby tayi masa idanu yazaro waje wayoyinsa ya nufa ya sunkuya ya daukesu duka yaga har abdan bazasu moruba gaban dressing mirror ya zo ya tsaya yana jinjina kai turare ko daya bata bariba kwalaben duka ta fashesu d'akin tsabar kamshi kar yayi mura saida ya toshe hancinsa ya kalli saman bed d'insa yada tawa tsadadan zanan gadonsa filla filla wardrobe ya nufa abude duk rabin suit d'insa masu tsada da kyau da shadodinsa da jallabiyoyinsa tayi musu kisan gilla gasunan saman bed azube murmushi ya saki yana, ciza lips d'insa na k'asa iska yake busowa mai zafi daga bakinsa " gud hatsabibiya gud tantiriya gud zee baby aikinki yayi kyau mutika amma zakiyi nadama mara anfani kinci bashin Faisal Almahadee Sardauna duk sunanane ni daya zaki biya barnar da kikayi zan azabtar dake ta fanni da bazaki taba manceniba zan gagauta ramuwa ta hanyar da zan dasa miki dafi mai zafi azuciyarki duk da ba hali na bane wlh sai namiki hore ta hanya mai nisan gaske zaki sanine zan gagaguta hakan ne kafin guri ya ya koremun insha Allah cikin gagawa zan hukuntaki narigada na gama gano wacece kedin wlh banajin akwai abunda na tsana sama da yarinyar nan amma zakici uwarki sai na hadasa miki ciwon zuciya dani kike maganar murmushin bakin cikin dauke kan fuskarshi ya shiga bathroom Mahabeer da ya shigo Dr bai fito ba ya Rika bin d'akin da kallo daya bayan daya yaga irin uwar barnar da zee baby
tayima Sardauna hankalinsa ya tashi tabbas yasan bazai yafe mataba abun zuba shara ya dauko dakansa ya kwashe duka tulin kwalaban da ta fasa na turare da maiyuka ya kwashe kayansa da ta yanka kaf cikin rawar jiki ya gyarawa Sardauna d'akinsa tsaf yaje d'akinsa ya dauko wani zanin gadon mai msifar kyau da tsada shikansa tamkar katifa dan laushi dukda Dr yanada amma yaki taba nasan lokacin da yazo Sardauna ya fito da kallo yakebin Mahabeer har ya gama " Dr namu don Allah kayi hakuri wlh zan biyaka wayoyinka yaje ya daukosu babu mamora" Faisal karka hukunta ta da horo mai tsanani yarinyace duk fah 17 year take ciki don Allah kayafe mata ko nasamu nutuswa wlh bansan irin horan da zaka yimataba jikinsa ya goge ya saka jallabiya ruwan toka yana murmushi yazo ya rumgume Mahabeer " babu komai na barta tunda kace yarintace zan barta ai ko dan kai Mahabeer yaji dadi sosai" Nagode Dr Sardauna Najib ne yayi sallama " bro Daddy na kira kai ya daga Najib ya fice tare suka fito Mahabeer bedroom d'insa ya shiga Dr Sardauna ya nufi part dinsu Daddy, da Sallama ya shigo parlon ai tanjinshi ta boye bayan Daddy ko da wasa bata dago kantaba kusa ghaisha ya zauna " Daddy gani? " Dr Sardauna kanwarka takeson shawarma don Allah samo mata " to Daddy muje da ita sai tazabi irin wacce takeso tana bayan Daddy tace" Ammin abarima nakoshi bazan kai kaina ga halakaba Daddy barna fa namasa dariya Daddy yayi " barna me momy " Daddy bari to naje na sayo mata kala ukku sai tazabi wacce tafi so " yauwa Allah ma Albarka " amin Daddy kiss yama ghaisha ya Mike nanah tazo gunsa " ina zuwa daukarta yai suka tafi Aunty amarya na dariya " momy ke sai tsokana da tsoro ko dagowa tayi tabi Sardauna da kallo yanada yake takunsa gwanin shawa tamkar bai dauki mutum ba akafadarsa ghaisha dariya tayi" momy uwar rigima gunta ta koma tayi kwance jikinta" ummi yau gunki zan kwana? " to naji Nawwara tazo ta zauna kusan zee " aunty kinmun kwacan mama ko dariya tabasu sosai bai jima sosaiba ya kawo mata Shawarma Mahabeer sai godiya yake masa zama yai amma ko da wasa baima kalli inda takeba itama bata kalleshiba dan tasan gabar ci tayi ta koshi abunta tana zuba surutu dan tasan ba yada ya iya da ita ana muk'ewa yayi ya musu sallama ya fice baki ta tabe " Allah raka taki gona dakazo muka ganka ko ajikinsa ya fice Mahabeer yace" babu ruwanki dashi zainab kibar daukan magana gurin da akafi karfinki baki ta turo Daddy yace" wasan da take masa shiru mahabeer yai dan har yanzu bai yada da yafiyar Sardauna ba Hafeeza ta Mike " sister tashi muje mu kwanta " Tab jeki ba yanzuba hira sukaci gaba da yi kowa saida yaje ya kwanta ta tisa Mahabeer GABA sai sangarta take masa yana biye mata sai karfe daya, na dare yasa mu ya lallabata da tace bazata kwana da su Hafeeza ba Dr Sardauna yabiyo dare ya kasheta saida Mahabeer ya rantse mata yace yafe mata ta yada, sakuyi sallam ya rakata har kofar bedroom yace gobe yasayo mata layin Nigeria don surika shan soyayya ko yana kamfani gun aiki da haka yasa ta shige d'aki shiko ya tafi lokacin Dr Sardauna ya jima dayin bacci tana shiga taje gun da ta boye kwayarta ta dauko tasha ta kunna wayarta tana tikar rawa da ihu Dole su Hafeeza saida suka farka tagumi sukayi suna mamakin wannan hali na zee saide yau bata jima ta bingire ana saman carpet sai bacci wayar natayi ita daya khalisat ta sabko ta kashe mata wakar suka koma bacci,
**************************************
*Bayan kwana takwas da zuwan zee baby* yau tacika kwana takwas a Nigeria tun ranar da tama Dr Sardauna barna har yau bata sake yada sun haduba dan duk lokacin da zai tafi aiki tana bacci baccinta bata tashi sai da rana shiko idan ya fita karfe tara na safe baya dawowa gida sai bayan magarib itako lokacin tana cikin d'akinsu dan dede lokacin babu babba a parlon bata fitowa dan tana tsoron irin horan da zai mata idan ya ritsota ba kowa karshanta ma ya kasheta kullum sai ankaita gidajan yan uwa gidan hauwa yar babanta ne tayi kwana biyu Wanda suka shaku da Neesher yarta dama kuma sunsa juna ta wata amma ta girmi zee da wajan shekaru biyar karatun lauya take yanzu tana shekarata na karshene Neesher fara ce mai matsagaicin tsayi batada rama kuma bata kiba ita tsaka tsakiya ce kyakyawace amma bacanba dan batada hanci saidai tana idanu suma ba manyaba can masha Allah batada makosa akwaita son yan uwa kowa natane akwai kokarin ziyartar yan uwa itace diyar hauwa ta hudu sai k'anunta uku mace an mata aure sai mazan masu binta yan biyu shiyasa zee da Dr basu haduwa dan kullum tana yawon yan uwa Dr Sardauna ya sake sayan wayoyi masu masifar kyau da tsada iPhone da Samsung tafka tafka masu kudin gaske sai yar karama ta cikon ukkun da yana aiki da karamar waya sosai ranar da yasiya yayi ta Kiran mashakurah bata daukaba hankalinsa ya tashi zatonsa batada lafiya kai tsaye yaje gidansu ya iske lafiyarta lau aiku tasha masifa yace idan bata sonsa afasa auran mana babu Dole ga yan mata burjik na hospital da gari suna adabrshi sun mutu akanshi ai tanajin haka ta fara kuka ta zaiyana masa abunda zee baby tace haushinsa akan zee ya karu ya dauki alwashin bata horon da zai barmata dafi azuciyarta itako ya rufeta da fada wai zancan mahaukaciyar zata dauka yarinya karama ta kitsa mata Abu ta dau wacce yasan abanza zata ba zee baby shekaru 6 cuf hakuri ta bashi suka shirya sukaci gaba da soyayyar su har yamata magana iyayansa zasu zo tambayar aure
Mahabeer ya sayan mata layin MTN kullum waya sukesha sun shaku sosai dan har ta amsawa Daddy ta yada zata aureshi yanzu gobe aka tsayar da maganar za'asa ranar auransu har Dr Sardauna da mashakurah amma zee tace ita tafiyarta zatayi saudia sai sunje dauko Amarya duk sun dauki maganarta wasa Ahmed kamar wasa son zee baby ya masa mugun kamu kullum yana gidansu Dr Sardauna sun shaku da zee sosai so yake yasamu hanyar da zai cusa mata sonsa kafin ayi auransu da Mahabeer, tun azabar da tasha gun Sardauna ta dena shaye shaye da rana sai dare dama ba dayawa bane ta kawo duk ta shanye jiyama bata shaba babu abinda yasa taji k'asar ta isheta Kenan babu kayan shaye shaye so take ta tambayi Ahmed tana tsoron ya fadawa mugu Dr Sardauna tin jiya yake danawa zee tarko yada zai kamata ya rama abunda tame dan gobe ake tsayar da ranar Aure yafiso ya rama kafin goben amma shegiyar ta toshe duk wata kafa dan ta daina zuwa Swimming pool duk dan karya ganta yaci ubanta duk iskancin da take cikin gida yanada labari har tsiyar da tama Aunty amarya ta kame mata idanu anyi anyi ta fadi dalili takiya, saida Daddy da mai ran karfe sukasa baki ta bude mata idanu shine fa suka daku da khalisat aikuwa khalisat ta bugu kunamu ukku ta saka mata Neesher tazo hutu yar gidan Aunty hauwa, tayi ta zugata ahaba ai saida suka kwantar da khalisat suka gamu suka mata duka d'akin suka rufo kai ranar anyi tashin hankali zee baby daket suka lallabata dan borin karya tashiga musu harda su rukiyya aka mata tace gidan kewaye yake da, shaidanu duk su tsorata tace wai bakin aljanine jikin Aunty Amarya shiyasa, ta like mata idanu dan ya fita haka akasha fama Dr yaji takaici da basu kirasa ba aikuwa Neesher yaci ubanta saida ya barta kwance dan yasan itace take zuga zee baby ina taji hausar da zatasan bakin Aljani yau har dare ya tsala Dr bai samu damkar zee baby ba Dole ya kwanta itako tana uwar daka ita da Neesher suna hira zee ko da Mahabeer suke waya sun hana Hafeeza da khalisat bacci dan biyu ce ta gamu saide Aisha bata fiye surutun Zee ba amma akwai fara'a sai tsakiyar dare bacci ya daukesu khalisat sai Allah ya isa take musu,
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Washe gari misalin karfe tara zee baby ta gama shirinta sanye take da dogon wando bakine yasha adon Wanda ya dame ta hips dinta ya fito sosai rigace pink colour itama ta kamata boobs dinta kamar zaso fasa rigar ta saki gashin kanya yau ta maidasa kallar maroon ta canza barimar hanci ta saka mai dan zirowa kamar ba India tilar kasan labbanta ma ta canza masa barima haka zalika tilar kunnema ta canza kuma suka zinarene tasaka, takalminta kafa ciki tasaka irin nasu na saudia ta dora, abaya kan kwalliyarta tayi masifar yin kyau Neesher da take cikin bargo na sharara, bacci zee ta bugeta da, karfi firgigit ta zabura " dallah can yar rainin hankali tashi muje kiyi rakiya airport mikewa tayi ta sabke " dan Allah el uwata karki barni munsaba ta fadi harda kwallarta zee ta bushe da dariya" kujiki katuwa zatayi kuka akwatinta taja ta fito parlo su Daddy na kan dining gunsu ta nufa " Daddy Allah yamun fitowa da kallo suka bita " momy ina zaki? " saudia mana ai da kunya yau za'asamun aure ina gida daya da ango mik'ewa sukayi Daddy yace" ai sai bayan auren zaku tafi yi hakuri Raiyan ma natafe lokacin biki koma ai ba haka ake tafiya ba babu shiri wayasan dake a Airport din rigima ta kafa harda kuka ita sai ta tafi kewar ummi takeyi da taga lallabar tayi yawa ta fara musu burin karya sai Addu'a suke tofa mata Aljannan suka fara magana wai dan yawo ne akanta haka sunansa dan yawo Mahabeer ya rude ya rikota sai Addu'a suke mata tayi wani far da idanu Neeshar kuka tasaka dan har ga Allah ta dauka zee baby iskar gaskiya takeyi Aunty Amarya ma guduwa tayi khalisat ko kallo hafeeza itama Adu'ar take tofa mata sai ghaisha da Daddy suka, tarema Mahabeer ana tofeta, daide lokacin Dr Sardauna ya shigo cikin shirin zuwa hospital ya had'e cikin Grey Suit Wanda ta kawata kyawunsa mutika gashin sa ya dan sabko kadan sajan fuskarsa da dan gemun ya kara ma kyakyawar fuskarsa kyau sai kamshi yake zubawa yau gani nayi ya kara zama k'aton gaske ga wani irin kwarjini da yayi gun ya ISO cike da mamaki me ke faru ganin zee ce ya zaro idanu hamdala yayi azuciyarsa damar ramuwa ta samu dan yasan iskancine take musu ahankali yayi magana yanda bazata jiba" Daddy ku bari naje da ita hospita abincike inaga ba jinnu bane basirne ke damunta" kanajin Aljanun na magana wai shi Dan yawo" Daddy wlh akwai maganin hospital kubari na tafi da ita " to Allah ma Albarka Mahabeer maza kaita mota aje aduba bai musuba ya dauketa itako sam har ga Allah bata jiba zatonta ko Airport za'a kaita idanunta rufe Mahabeer ya shigar da ita motar Dr Sardauna gidan baya yana tofa mata Addu'a jin ansata mota tayi bacin karya, Dr na shiga motar Mahabeer ya kwantar da ita ya fito jin ya fita ta bude idanu zaune ta Mike tana maida numfashi tana kyakyatar dariya" wlh na iya tsiya ta fada tana sabke ajiyar zuciya dan taci uwar wuya karaf suka hada idanu ta madubin mota ya sakar mata murmushi yama motar key idanu ta zaro ilahirin jikinta Karrrma yakeyi" shikenan na mutu...........
*💖💖👩🏻🦱ZEE BABY👩🏻🦱💖💖*
*DAN ALLAH KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE*
*👉🏻12*
....ko kallona baiba yaja motar bakin get ya tsaya mai gadi ya bude masa ya fice nutsuwata na tataro na cire tsoro cikin tsiwa nace" malam meye hadinka dani da zaka wani daukoni bakace kowa yayi rayuwarsaba na fita sabgarka to meye hadinka dani kuma inane zaka kaini ko kawai jaraba son ayi fada to ni yau banayi zaman lafiya nakeso asaukeni ko ci kanki bai ceba ya harba motar kan titi yana tukinsa cikin nutsuwa wayarsa ta dauki ringing hannusa daya ya tura cikin kwantacciyar sumar kansa yana shafawa bai daga kiranba saida ya katse aka sake ya dauki wayar yai picking ya Kara akunne cikin amon muryashi mai dadin sauraro yace"hello ya akayi ne? OK ina saman hanya ya tsinke kiran yaci gaba da driving dinsa tsaki naja" aikin banza wlh idan nutum yaci zalina Allah yana ganinsa baima San tanayi ba har suka isa hospital honr yayi aka bude masa babban get ya cinno hancin motar cikin asibitin parking space ya shigar da motar yai parking " wai malam lafiya kakawoni mustashfar ko wata cutarwar zakamun wayoyinsa ya kwashe ya fito daga cikin motar bude mata motar yai fuskarsa babu alamun rahma ya kalleta bai maganaba ya mata nuni ta fito duk taji tsoro ta dake Dan yau taci alwashin bazata bari ya zalumcetaba irin wancan Karo cike da rashin kunya tace" baza'a fitaba ko Ana Dole bai maganaba Dan lokaci zata bata masa ya duko ya janyo hannuta da karfi ya fizgota waje buge hannu tayi " wlh malam ka kiyayi tabamun jiki ta fada cikin fitsara motar ya rufe dan yasan tsiwar karfin hali take zuciyarta fal tsoro gaba yasata
sai tsoki take masa bai dai kulataba Dan yasan daga yau bazata iya masa abun da take masaba haka suka ratso tsakiyar hospital d'in kowa sai kallinsu yake cike da shawarsu dan sunyi mugun dacewa ga tsantsar kamar da sukeyi saide ita zaka gane balarabiya ce duk fatarta tasa duhu ko ina sai gashesa akeyi amatsayinsa na babban doctor hannu yake daga musu yana wucewa itako sai harare harare take Office d'insa ya saka key ya bude har an gyara tsaf sai kamshi yakeyi kin shigowa tayi hankadata yayi da karfi saida ta fadi ya murza key bai kalli inda take " Allah ya isa mugun banza kawai meye hadinka dani murmushin gefen baki yai yaje ya zauna kan lumtsumemiyar kujeran da ke gaban katon table din mai cike da takardu laptop ya kunna yakira waya banji me yaceba ya kashe takaici ya cikani ganin ya maidanin banza na Mike tsaye ina kallonsa " idan kai ka haihu ka budemun kofa na fice waya ya dauka ya danna wata number bugo daya aka daga " murmushi yai morning my sweet baby ya gida kansa ya dafe " oh wlh na manta sorry bari zan biyo idan na taso daga gun aiki OK bye zan kiraki da rana love you too ya fada yana murmushi ya tsinke kiran ko kallo bai ishanba gu na nema na zauna naga iya gudunsa Dan yau nayi alkawalin kirta masa rashin mutumci Nima knocking din kofar akayi ya Mike ya nufo kofar cikin takunsa na kasaita da isa farin gilashin yamasa kyau cikin isa yake takunsa kana ganinsa kasan karkarfan Namijine tsayaiye ko kallo bata ishesaba hararasa tayi baima san tanayi ba tsaki taja" aikin banza kawai mai kyan Dan miciji yajita sairai amma ko kallonta baiba ya saka key ya bude kofar hamzane dauke da tire kayan breakfast " good morning Yallabai " morning hamza ykk?? " Alhmdllh doctor ya bashi hanya ya shigo yaje ya ajiye ya gaishe da zee baby yai kin amsawa tayi tabisa da harara har ya fice kofar ya rufe ya dawo ya zauna cup din tea ya dauka yanasha anutse mik'ewa tayi ta nufi gunsa Dan yunwa takeji " malam likita ni yunwa nakeji banci komaiba ganin bazai kalletaba
yasa ta saka hannu ta dauki plate mai soyayen dankalin turawa da kwai da cinyar kaza asoye ta koma gun zamanta abayar jikinta tacire ta ajiye tayi zamanta da dogon wando da guntuwar rigarta gashinta ya sabka har gadon bayanta rabi ya rufe mata fuska anutse yakeci har ya gama hamdala yai ya Mike yaje toilet ya wanko bakinsa da hannusa danna wata yar na'ura yayi ba'afi muntuna biyar ba aka fara shigowa ganin Dr wata latijuwa ta fara shigowa acikin girmamawa zee baby ta gaisheta ita ya fara dubawa nabiyu ko namijine saurayi Wanda zuciyarsa dab take da bugawa sosai Dr Sardauna yai masa fada ya rubuta masa maguguna yace zai kwantar dashi har kwana biyu ta ukku ce da ta shigo wata zankadediyar budurwace asuma ke damunta Dr Sardauna na tsaka da dubata zee takeson mata rashin kunya babu gaira babu dalili ta fara zaginta ganin basu kulata ba ta iskosu tayi tsaye kansu fur ta hanashi yaba yarinyar kulawa saboda bayason surutu Dole ya dago ransa abace" ke matsa kiban guri jikinsa ta matso ta rumgumeshi ta fara kukan shagwaba " wlh Dr bazaka dubata ba danme zaka rika tabata nadamar kawota hospital yai amma da ya tuna zai kunsa mata bakin cikin da bazata iya mantashi ba wuyanta ya damko ya kifa mata Mari ya hankadata wani daki ya murza key yaci gaba da aikinsa saida ya duba mutum sama da ashirin tun tana ihu da buga kofa har tagaji ta bari sai karfe sha biyu ya samu ya huta su Daddy sunzo amma yace ya mata magani Allura bacci ta awa biyar yamata bazasu samu ganintaba Mahabeer sawunsa biyu Dr Sardauna yace sai yamma zata farka Dole ya hakura ya koma gun aiki, Dr Sardauna ya shiga duba marasa lafiyar dasuke kwance a asibitin duk da yasa an dubasu amma yabi su daya bayan daya yana dubasu cikin fara'a yake duba kowa yana kara musu kwarin gwiwa hakan nama marasa lafiyan dadi ba kadan ba
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
karfe daya da rabi ya fito daga masallaci yin sallah Office ya bude ya shiga ya dauki abayarta ya bude ya wurga mata " maza tashi kiyi sallah kafin watan cin ubanki ya kama yanaji ta rama k'asa k'asa yana ciza bakinsa ya jinjina kai fitowa tayi taje tayi Alwalla ta shimfida dadduma sai Allah ya isa take masa" kuma yanzu zanyi Addu' Allah ya hadaka da cutar dan kanoma ka kasa zaune ka kasa tsaye ko kallo bata isheshiba tsadaddan agogon hannusa ya kalla saura minti ashirin yashiga tiyata wacce itace ta hanashi cin uwar zee baby soyake sai ya fito bayan mintina goma akayi knocking din kofar ya bada izinin shigowa Dr Ruma ce ta shigo da sallama sai wani lankwasa take amma cikin taitayinta dan tasan halin Dr Sardauna " doctor mun gama shiryama komai lokaci yayi Dr Nabil yace na kiraka ka fara fuskarsa ahad'e yace " Ok bai sake maganaba ta juya zata tafi " kallon banza zee tama Ruma " ke bazawara wlh kunji dai kunya ke yanzu haka kike yawon tsakiyar maza idan ba salon iskanciba da tallaar jiki kalli wani breast dinki duk ya saki sai kace mai shayarwa koda yake bazawarce ai dukda hausarta bawai ras take yintaba amma Ruma ta fahimta idanu Dr Sardauna ya zaro kallonta ruma tayi dan
Book Chapters
Chapter 8
Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50