You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kara binsa da fari ma fushi yayi sai data lallabashi sosai sannan ya fahimta yake kyalesu. Yaran sunada wata 6 sai ga ciki yabayyana ajikin Aicha wanda hakan yadaga mata hankali bakadanba amma ganin yadda Mutallab yayi murna yasanyata sakin jiki kadan tana tausayin yaran nata wannan karan cikin da cin abinci yazo sai kuma wasu abubuwan da bataci Amma amai dai batayisa ba sai zazzabi da kullum daren Allah sai ta kwana dashi ahaka dai rayuwa tacigaba da tafiya yau fari gobe akasin haka har Allah ya sauketa lafiya tasamu yara maza suma ´an biyu wanda yaja mata wata daraja gurin mijin nata dan gaba daya ya kwashesu zuwa Egypt yace adubamasa su da'ita baki daya Arzuki na Allah tafada yau ga ´ar jagora tana cikin daula."" Wani kallo yayi mata yace "" Banahanaki maganar nan ba?"" "" yanzu saboda Allah Abin kauna kaganni da danAllah dayake bakasanni ba lokacin da Ma mere ke fama dani akan inyi wanka da gayu alo.."" "" Banason wannan maganganun naki Allah shike da komai shikeda ikon komai kuma shike kai bawa inda yaso ni kinsanni abayane?"" Ganin idonsa ya cicciko da kwallah yasata rungumarsa tana aika masa da wasu kalar sumbata masu riketar da birkitar da kwakwalwa dan ayanzu itakam duk wani course dinta na kan gado ne dan tasan jarumin nata hakan shine abunda yake mutukar so da ™auna, Nan suka Lula duniyar da ba'a iya bayaninta ko lissafinta. Ashekarar Afrah ta haihu haka suka tafi London har tante sukayi mata sati daya daga nan kuma suka sauka a Niger gurin dada suma sunmata sati kamin su"

dawo gida.

Yau tana tashi tana fitowa palour tatarar Aicha wacce ita ake kira da amal sai Mutallab da suke kira da

"Alhaji sai mazan twins da suke kira da Hanif da aslam kallonsu tayi tana gwalo idanuwa kwai ne kirat daya suka sauke mata shi gaba daya ai nan ta harzuka tashiga du™ansu tana masifa Mutallab da yajiyota yazo yarufeta da fada akan me yasa zata yima yaransa haka bata gani yarane ai basusan abunda sukeyi ba kuma ma menene acikin kwan."" Ai kam yara suka saka masa ihu haka da kansa yayi musu wanka yagyara ganin uwar tasu da bala'i tatashi da kansa ya kaisu makaranta ko da yadawo tana tsaye tanata kuka wanda hakan ya bashi mamakin kukan datakeyi "" Wallahi sai dai nazubar da cikin nan sai kace tunkiya ga yarannan da suke sakani karamin hauka ga..."" "" Wallahi wallahi ko da wasa nakarajin lafazin nan bakinki sai na bata miki rai yafada ya rufeta da fada sosai daga karshe dayaga tabbas tana kokari dan idan ba dole ba masu aiki basa taba mata yaranta ita take musu komai shima yana taimaka mata dan yace wannan shike kawo jin kai da shakuwa ga yara."" Kidaina kukan nan danAllah naji kina kokari Amma ni inason yara kiduba baya faman da mukasha kamin mu samu danAllah kibarmun wannan kyauta."" "" Tausayi yabata sai kuma tace "" Kayi hakuri bazan kara furta hakan ba "" "" Allah yayi miki albarka kishirya zamuje gurin Abba inason muje umara dasu gaba daya."" Murmushi tayi dan kasar da bata daina sin zuwa duk da ashekrar sau biyu suke zuwa shikuma sau uku dan tunda ta auresa bata tunanin akwai shekarar"

da baiyi aikin hajji ba itakam tunda yakaita ta sauke farali shikenan kuma sai takoma sai dai taje umara.

Aicha tana zaune tunanin rayuwar baya takeyi cike da mamaki irin na iko Na Allah da yadda suke bara

suna rufawa kansu asiri da irin nasu talaucin da jarabawar data dinga samunta Amma yau itace awannan daula ta yarda duk wanda yayi da kyau zaiga da kyau dan tunda tayi aure bata taba bari bata sauke hakkin aurenta ga mijinta ba dan dada ta gayamata duk matan da suke gamawa lafiya sune masu sauki

hakkin mijinsu batare da sun cuta musu ba koda kuwa su din sun kasance masu cuta musu...

Akwana atashi babu wuya gurin Allah Shakaru nata tafiya yau ga Aicha matar mutallab har da yara

"takwas dan tunda tafara haihuwa ´an biyu take haifa haihuwa nafarko sukaci sunansu Nabiyu kuma sunan abba da mahaifinta ta uku kuma da yake matane aka saka musu dada da tante dan aicha kafewa tayi sai ansaka mata tante saboda irin yadda take sonta take kaunarta dan bazaka taba cewa ba mahaifiyarsu bace ba haihuwar da tayi takarshe kuma yasa musu khadija da Bilkisu maganar kulawar da yake basu ba'a magana dan ayanzu idan bakaji sunansa a daya dakacikin manyan kasuwar duniya ba to tabbas zakajisa ana daya akasarsa. Yau ma suna ci™in Airport da yaran baki daya Nan suka hadu da meenal da yaran mijinta mijin nata ne yayi hanzarin karasowa gurin Mutallab yana masa gaisuwa ta girma kamar dai yaro da ubangidansa "" Meenal ina wuni Aicha ta fada tana kallonta"" "" Kinsan Allah ban ganeki ba Aïcha, kece kika zama haka wai?"" meenal tafada tare da gaida Mutallab ya amsa mata ba yabo ba fallasa aicha tace ""Haba nikam kinga naganeku, yan samari yakuke tafada tana ™allon yaran mijin nata."" Gaisheta sukayi meenal tace ""Wannan kyawawan yara haka duk nawane ne?"" Murmushi Aicha tayi kafin ta bata amsa sai taga yaran sunzo suna fadin ""Mumy zamusha alawar can."" Kallon duty free aicha tayi sannan tace ""Kuje gurin dady kuma baku gaisar da mumy ba ta nuna meenal."" Gaidata sukayi hakan yasa meenal ta rungume daya tana kwallah "" ko baki gayamun ba nagane yaranki ne Mashaa Allah saboda ga kamarki nan data dadynsu tare dasu, amma kamar twins duka ko?"" Ta™are zancen tana mika hannu zata karSi Bilksu, ai kuwa yarinyar da yanzu watanninsa biyar da haihuwa ta juya baya tana makalkale Mommynta, dariya Aïcha tayi haWe da cewa, ""Billy rigima, ai bazata yarda ki Wauketa ba saboda la™uwa, eh dukansu ´an biyu ne ai."" Ta™are zancen tana mi™a mata khadija da suke kira Deejah, ai kuwa yarinyar ba kiuwya taje gunta haWe da shigewa jikinta ta lafe, cikin jin daWi Meenal ta lumshe idanuwa tana shafa bayanta haWe da jin wasu ™walla na sauko mata tayi saurin sa hannu ta goge tana cewa, ""Allah ya raya su Aïcha, nikam kinga har yanzu shiru haihuwa ta tsaya"" ""Karki damu Meenal Ai lokaci ne kici gaba da Addu'a, bayan haka ga yarama kin samu ai baki da damuwa zasu ri™a Webe mako kewa."" Murmushi tayi tana tuni halin yaran duk da yanzu alhamdulillah mahaifinsu ya gano halinsu tsaye yake da tsawatar masu da nuna masu darajarta, ko da sunyi wani abun to tabbas zasu bata ha™uri kafin subari yakai kunnensa, da haka Aïcha ta mi™a mata hannu takarSi khadija sukayi sallama"

ganin su jirgin Emirate zasu shiga sukuma Egypt.

Sai k'okarin sake sarrafa al™alummammu mukeyi wajen dak'ko muku wani rahoton muna buWe sabon

"Feji amma sai muka ga ashe pages Win sun zo ™arshe, juyowa mukayi muka kalli juna tare da sakin murmushi muna maida kallonmu ga bangon littafin da muka juyo dake tabbatar mana da ™arewar shafunan dake ciki tare da saurin kai hannuwa ga wani littafin dake gefen da niyar Waukowa ko zamu samu ci gaban labarin sai dai kash! Muna dubawa wani sabon littafi ne dake jiraye da al™aluman namu dan sake kawo maku wani daddaWan labarin mai cike da darussa, dariya mukayi haWe da juyowa tare"

"muka kalli juna muna cewa,"

ALHAMDULILLAH.

Anan muka zo ™arshen wannan littafi tare da yin nazari akan cewa:-

KOMAI NACIKIN RAYUWAR MU BA TABBATACCE BANE BA.

NEMAN TSARIN ALLAH DAGA SHARRIN DUK WANDA KAKE ZAUNE DASHI ABUNE MAI KYAU DAN

DUNIYAR NAN TAMU CIKE TAKE DA MUTANE IRIN ARYAN SUNA KUMA KUSA DAMU SUNFI MASOYANMU MA NUNA MANA KULAWA ADDU'A DA NEMAN TSARI AKOWACCE RANA YAZAMANA

FARILLAH GA BAWA.

ki riqi aure domin jigo ne ga rayuwar mu. Ya ke 'yar uwa ki yi haquri da rayuwar da ki ka tsinci kanki a

"gidan auren ki, ko daci, ko wahala, ko daci, ko"

"zaqi, sanyi, zafi, ku jure ki yi haquri ki roqi Allah ya yi miki sauyi na alkhairi, ki tallafi mijinki da 'ya yanki,"

"idan kina dasu, ki tausaya musu, ki basu tarbiyyar ta gari, ki dora mijinki a hanya ta qwarai idan ya kauce, ya ke 'yar uwa ki yi qoqarin kyautata dabi unki, biyayyarki, haqurinki, sauqin ta tare da Ibada zuwa ga"

Allah shi ne samun Aljannarki..

DANALLAH MATAN AURE AKULA DA SHIMFIDAR NAMIJI ASAN IRIN SALON DA YAKESO AKOYA AKUMA

YIMASA DUK ABUNDA ZAKIYI DA MIJINKI LADANE ZAKI SAMU.

"lallai fitsara da rashin kunya babu inda yake kai mutum sai ga nadama, kuma duk abunda kayi karka"

"manta sai anyi maka fiye da abunda kayi ko kuma daidai da yadda kayi, ku Wauki darasi a rayuwar Meenal."

DUK ABUNDA KAKE GANIN KAYI NAI KYAU KO MARA KYAU TO TABBAS AKWAI RANAR DA KARSHENKA

ZAIZO AKWAI RANAR DA ABUNDA KAYI KHAIRAN KO SHAIRAN ZAI BIYOKA YA DAWO MAKA.

"Sharri mugun abune kuma ya kanbi mai yinshi, komai iya makircinka da sharrin ka karshe kanka dukiyar"

ka Arzukin ka da kyanka bazaiyi maka komai ba indai ba aikata aiki mai kyau kayi ba..

"Yadda da kaddara wajibi ne ga dukkan Musulmi, domin kaddarori na Allah akwai Alheri mai yawa a"

"tattare dasu, idan kayi hakuri zaka samesu, Raki da kuka da dukan jiki basu canza hukuncin Allah, Don haka ya kai dan uwa, hakurta da kanka, ka kore damuwa, ka daina raki, ka nemi taimakon Allah akan duk wata musiba tazo maka, kasani Mahakurci shi ne mawadaci, Rayuwar MUTALLAB abun koyi ce da kuma"

kyakkyawan duba.

Things won't always go the way we want them to. We may need to let things go to build up new ones.

It's painful. But it's part of His plan!

"* May ALLAH SWT Guide our right, ,may HE protect us from all evils,countinue to shower his mercy"

blessings on us.....

ALHAMDULILLAH

*MUTALLAB ASAD MUTALLAB*

(MAM) End in Sha Allah

Time:-11:47

Date: WEDNESDAY 21 FEBRUARY 2024

*11 ga watan Shaban 1445*

GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI TSIRA DA AMINCI SU KARA TABBATA GA MANZON

RAHAMA (SAW)

ABUNDA MU KAYI BA DAIDAI BA ALLAH YA YAFE MANA!

WANDA MU KAYI DAIDAI ALLAH YABAMU LADA!

KU DAUKI ABUBUWA MASU AMFANI DAKE CIKI MARASA AMFANI KUMA KU ZUBAR DASU KUYI MANA

UZURI TARE DA ŠAUKARSU A MATSAYIN AJIZANCI.

MUNGODE

"DA SOYAYYARKU, LOKACINKU, HAKURINKU, KUŠAŠENKU DA KUKA SAYI LITTAFINMU DA KUMA"

"BIBIYAR DA KUKAYI MASA HAR ZUWA KARSHE, ALLAH YA BIYAKU YA SAKAWA KOWANENKU DA"

ALKHAIRI YA ˜ARA MAKU ARZIKI HADI DA BUŠI DA WADATA.

_SAI MUN HADU ASABON LITTAFINMU IN ALLAH YA YARDA_

NAKU A KULLUM BILLY S FARI DA NANA DISO.

_Kar amanta paid book ne ´ar uwa idan kin gama karantawa ki taimaka ki tura mana kuWinsa N500 ta

wannan account 0020428430

"Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 muci goro,"

mungode sosaiÏ%Ï%

*³AN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.

*BAQEER*

Ayusher Muhd

Umm Asghar

*KURMAN ALLO*

Asmy b Aliyu

Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*

Zee Bawa

Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*

Nana diso

Billy S Fari

*KULUWA*

Zee yabour

Sadiya Dan

Duka Biyar Win akan 2k

Hudu 1600

Uku 1200

Biyu 800

Šaya 500

VIP

Duk guda Waya 1k

NORMAL GROUP 500

VIP 1000


Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment