You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan asiyomiki alimun amma shi ™adan ake sakawa da kaninfari da bagaruwa da sassaken bagaruwa da Wan gishiri da ganyen magarya ki dafasu kiyi sati kina shiga ciki zaki ban labari."" "" aikam wallahi Nagode sosai sai tsumi danAllah tafada tana karya wuya."" Wai "" "" DanAllah nidai ki bani"

"mijina yanason kulawa da shinfida wallahi shiyace ma nagayami komai asiyo inyi gyara bayaso in zauna haka ban kula da jikina ba."" "" To fannah ai sakarar macce zata zauna bata gyara wallahi ai jikinmu sai da kulawa idan bahaka ba sai asamu matsala ai dole mutum ya dage ya kula bama bayan haihuwa. Kinsam cucumber maganin mata ce sadidan a zamanance har ma da likitance to kisameta ki samu abarba ki samu kankana ki samu minannas ki samu kaninfari kisamu cinnamon kisam ki haWesu ki dafasu sai ki markada ko ki murje kisha zakiga ikon Allah fannah."" "" NAgode sosai wallahi Allah yabarki da oga."" "" Bari"

naje inda aji karfe 2 sai nadawo tafaWa tana barin gidan.

Ni wallahi umma kidinga alama idan zakiyi kashi akan wane dalili zaki dinga kashi awando gaki da nauyi

"ke jidda Asiya tafada tana fadin wallahi Nagaji sai dai ki gyara dan ni ba baiwarku bace ba haba fitsari anan kashe ma hakama fa jiya ina bata abinci dai amai kuma ajikina."" Harararta jidda tayi tace "" Ai nayi aikina naga da safe wallahi ke zakiyi."" Anty Amarya dake jiyosu tace "" Menene hakan kukeyi saboda rashin tarbiya? Ba mahaifiyarku bace ba idan bakuyi mata ba wazaiyi mata kamar naku? Bakwaso rayuwarku tayi albarka ? Duk lallacewar uwa uwace kuma wallahi sai Allah yayi fushi daku ahakan zaku samu naku masu tausayi ko abunda kukeyi zakujo dadi idan yaranku keyi muku shi? Narasa gane ™anku"

"kwana biyu aikin ladafa kukeyi ko dankunga abba baya gari to sai na sanar dashi ta waya, Ai yanzu"

yakamaceku ace kun tausayamata kun dubata bawai ku tsya haka ba kuna ganin dai Alhaji mutallab

"Abba ya lallabasa yafito da Jamil daga gidan yari gashi can asubuti shima yana fama da jinya yakukeso tayi saboda Allah? Ita kuwa kome tazama girmamata akeyi sai kuyi hanzarin gyara gurin Nan kunji yan albarka ke Jidda bakincemun zakije gidan afrah ba."" "" To ai babu mai kaini Anty."" "" Ki shirya kije akwai driver gidan yayanki sai ya kaiki ai kema yakamata kicigaba da makarantar idan ya dawo kisameshi ki lallabasa kinji."" "" Allah dai yabiya yaya mutallab gaskiya munyi dacen Wan uwa wallahi."" Jidda tafada tana"

"nufar gurin zata gyara nan asiya tace "" A'a bari nagyara ke jiki taya anty Aiki."

Rungume yake ajikinta yana aika mata da sa™onni masu rikita kwakwalwa tun tanajin kunya har yakai

"da bashi martanin da ya zame mata sai kace yaro saboda shiririta nan tashiga aika masa da nasa karatun har sai da tabbatar ya haddaceshi. Ahankali yashiga sauke numfashi yana faWin "" Afrah na ina kaunar wallahi. "" kamin tabashi amsa wayarsa tayi kara yasanya hannu ya dauka yana karawa akunne haWe da saita muryarsa."" Dady barka da asubahi yafada suna gaisawa "" "" Farouk afwan na kiraku da safe ya diyata dafatan kuna lafiya,"" "" Lafiya laou muke dady Allah yasa nan kalou."" "" Maganar wanda suka sace afrah ne daman nakeso nayi maka ankama wani yaro yanzu haka yana hannun hukuma."" "" Really dad?"" "" Sure farouk yanzu dai suna hannun hukuma idan kasamu dama sai kaje ko?.. "" Badamuwa dad zanje"

"inshaaAllah."""

****

Muje ki gyara da™in ko? Mumy tafada tana kallon meenal hakan yasaka tabita abaya tana dan kunnunai

"haka mumy tatsaya akanta ta nuna mata yadda zata gyara da™in hatta bedsheet sai daya koya mata yadda zata gyarashi duk da sai da sukayi gyaran kusan sau 5 kamin meenal din tayi daidai da yadda mumy takeso sannan ta kyaleta nan ma bandakin sai data tsaya akanta ta nuna mata yadda zata wanke ko'ina daki daki. "" Wash wallahi mumy nagaji."" "" Kema kyaji dadi ajikinki meenal ba'a san macce da son"

"jiki ba."""

****

"Akwana atashi babu wuya agurin Allah ´an saudia sun dawo inda karatun Aicha yafara zafi sosai, haka"

"kuma matar walid itama tasamu karuwa ta haifi Wa namiji wanda aka saka masa sunan Abbanta anyi budiri itama ba kadan ba. "" menene naga kinyi tagumi?"" "" Anya wannan matsalar haihuwa ba daga gareni take ba ma chèriè?"" "" Nace miki kidaina damuwa ko? Ai ita haihuwa lokaci ne Amma kamar yadda kikace zamuje muga likitan Amma ba ke kadai ba tare zamuje adubamu duka dan sai ta iya yihuwa"

matsalar ba ke kadai bace ba hardani kokuma ni ne ma.

*MUTALLAB ASAD*

Book 2

SHAFI NA GOMA SHA TAKWAS

Arewabook:- billysfari

"Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER"

0020428430

"Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip"

post 1k ne.

"Zaro idanuwa Aïcha tayi jin abinda ya faWa cike da mamaki, taya zai ce kilan matsalarsu ce bayan matarsa"

"ta taba samun ciki har sau biyu?, ssannan su maza basu fiye yarda cewa matsalarsu ce idan mace bata haihu ba shiyasa sam basa son zuwa asibiti, Waidaikunsu ne kaWai keda ilimin gane cewa ita matsalar rashin haihuwa wato (Infertility) a turance takan iya zama daga wajen namiji ko kuma wajen mace, wani lokacin duka mata da mijin za'a iya samun matsalar daga wajensu, shiyasa a ™a'idance idan ana don magance ta ko samun waraka to dukansu ya kamata suje koda kuwa Waya daga cikinsu Win ya taSa samun haihuwa a baya. ""Min Amour ya akayi naga kin shiga dogon tunani haka?"" Taji Muryar Mutallab ya faWa yana dafata, sai data sauke ajiyar zuciya cikin sanyin jiki sannan tace, ""Mon Amour me zaisa kace ™ilan matsalar taka ce bayan sau biyu ana samun ciki agidan nan."" Runtse idanuwa yayi tunowa da wannan miji haWe da cewa, ""Hakan bazai zama hujja aguna ba da zan tattara duka laifin na maida akanki koda ace ma an haifa mani yara agidan, kawai kishirya zuwa ™arfe sha biyu zanyi waya da Dr Hussain abokina ya haWa mu da kwararriyar likitan mata da zamu gani."" ""To Shikenan bari na hakura da zuwa school yau tunda dama lecture Win sha biyu zamuyi."" ""No Bari nasake kiransu miji ko zata iya bamu wani lokacin."" Ya™are zancen yana mi™a mata hannu ta Wora masa wayarsa dake hannunta, cikin mintuna biyar ya kira Dr khadija sukayi magana, nan tace masa ba damuwa ta sake saka masu appointment zuwa ™arfe goma yayi mata godiya sannan ya kashe wayar yana kallon Aïcha dake faman turare closet din kayansa data gama shiryawa da aka kawo masa wanki, ""To kin ji zamu iya tafiya nan da ™arfe goma, kinga zuwa ™arfe sha biyu Win idan muka kammala sai mu wuce n ajiyeki school ko kuwa?"" ""Eh hakan yayi ranka ya daWi."" Aïcha tafaWa tana murmushi, kamo ™ugunta yai ya janyota ya yimata mazauni akan cinyarsa haWe da cewa, ""Ina son ™amshi Aïcha turaren nan ya yimun daWi sosai."" Ya Wago hannunta yana sumbatar thaWe da kallon cikin idanuwanta. Murmushi ta saki tana shafa gefen fuskar tasa da Waya hannun nata kafin tace, ""Má Chèri ai ™amshi rahamane, wannan haWin musamman nakoyesa dan kai kaWai, kuma ina da tabbacin mijina kaWai ne akeyiwa amfani da irin wannan ™amshin."" Hannunta da take"

"shafa gefen fuskar tasa ya janyo yai masa kiss tare da cewa, ""I love everything about you Mon Amour."""

"""Me too má Chèri tashi' muje muyi breakfast kafin lokaci ya karasa."" Ta mi™e tana ri™e da hannunsa har"

"zuwa kan dining ta janyo masa kujera ya zauna, bayan sun kammala ya fice zuwa sashen tánte da ayanzu take ita kaWai ita kuma ta koma ciki ta Wauki mayafinta da handbag Winta ta same shi acan, ""A'a Aïcha yau ba'a fita dawuri ba?"" ""Eh tánte bana da lecture Win sassafe shiyasa, ina kwana?"" ""Lafiya kalau Aïcha, Allah ya tsare yabada ilimi mai albarka"" ""Amin Tánte."" TafaWa tana bin bayan Mutallab daya fice yana"

yiwa tánte sallama.

Zaune suke gaban Dr khadija dake rubuce-rubuce a file kafin ta Wago kanta tana ajiye biron hannunta

"haWe da gyara zaman gilashi idanuwanta tace, ""Ok naji duk bayananka Alhaji Mutallab dana ita uwar gida, ita wannan matsalar ta rashin haihuwa kamar yadda kuka sani ba sabon abubane da zaisa ku tayar da hankalinku ko ku shiga damuwa saboda Allah shi yake badawa aduk lokacin da yaso a kuma lokacin da yake ganin ta dace, wani lokacin matsalar na zuwa ne daga wajen macce idan aka jurewa zuwa asibiti sai kaga daga baya itama andace ta samu haihuwar, wani lokaci daga namiji ne kuma wanda mafi aksari sunfi bada matsala da rashin bada haWin kan da za'a shawo matsalar a asibiti saboda basa don zuwa, wanda da ace zasuyi hakuri su rika daurewa suna zuwa ana dubasu kamar yadda matan keyi sai kaga ´ar damuwar data hana haihuwar kaWan ce kuma ana maganinta sai haihuwar ta samu, ko kuma ya kasance duka miji da mata kowa nada matsalar, idan suka tafi asibiti tare aka dubasu sai a magance matsalar cikin sau™i wanda hakan ne yakamata ace duk wasu ma'aurata dake fama da wannan matsalar sunyi kamar dai yanda kukayi Win nan."" Sai data nisa sannan taci gaba da cewa, ""Yan zu akwai gwaje-gwajen da zamu baku kuke dakai da ita duka kuyi sai ku kawo mana sakamako mu gani, amma kafin nan zan rubuta maku magungunan daya kamata kuje kufara sha dukanku, ""Ok Dr muna godiya."" Mutallab yafaWa yana gyara zamansa, gwaje-gwajen da zasuyi tarubuta takira wata nurse ga mi™a mata tace taje dasu lab, wuWanda kuma ake bu™atar sai sunje gida tami™a masu a hannunsu tace zasu iya zuwa ko wani wajen ne da suke bukata suyi sukawo mata result. Godiya yayi mata sosai sannan sukayi sallama suka tafi, sai da suka fara zuwa lab aka diSi jininsu da sauran abinda ake bukata daga wajen Aïcha kafin suka tafi ya"

ajiyeta makaranta shi kuma ya wuce shago..

***********

"Kwance Mommy take yau tana fama da zazzaSi sosai dan har Asiya tazo dubata, Meenal ce a kitchen"

"tana girki Asiya na tayata suna fira sai ga Kamal ya shigo, yana jin tashin Muryar mutane a kitchen din ya nufi can, atare suka juyo ita da Asiya jin motsin mutum a bayansu, ""Sannu da zuwa ya Kamal"" ""Yauwa Asiya, shigowar yaushe?"" ""Šazu."" Ta bashi amsa ata™aice tare da wanke hannunta data gama tu™a tuwon semovita da take nunawa Meenal, kallon Meenal Kamal yai haWe da cewa, ""Ke kam kinji mugunta"

"Meenaluwa, daga zuwan yarinya har kin sata aiki?"""

"""Da Mommy zakayi ita data sakata bani ba."" TafaWa tana balla masa harara, sai da yayi dariya"

"idanuwansa nakan Asiya sannan yace, ""Ba dole ta sata ba tunda ke baki iya ba, ko da yake ba laifi yanzu"

"naga kina koya."" ""What ever dai ba gareni farau ba itama koya tayi."" Ta bashi amsa tare da sakin tsaki"

"tana barin kitchen Win cikin jin haushin yadda yayan nata ya yarfata, Asiya dai bata ce komai ba ta shiga gyaran kitchen Win dan sun gama girkin, tuwon kawai take jira ya sake silala sai ta kwashe, magana kamal ke son yimata Amma ya kasa, tsawon watanni biyar kenan yana don tunkarar yarinyar ya bayyana mata soyayyarsa amma yakasa saboda rashin samun fuska daga wajenta, ko yaushe zasu haWu zata gaishesa cikin girmamawa amma fuskarta a haWe, wanda hakan ke saka shi jin tayi masa wani irin kwarjinin da bazai iya fuskantarta ba, wani lokacin ma sai yaga fuskarta ta koma tamkar ta Mommy idan tana cikin yanayin rashin wargi tattare da ita, wata irin ragguwar ajiyar zuciya ya sauke yana kallon yadda Asiya ke aikinta cike da natsuwa kafin ya aro jarumtar da shi kansa baisan yana da ita ba haWe dayin gyaran murya yace, ""Amm.. nazo na tayaki aikin tunda ta tafi?"" Yadda ta Wago kai ta zuba masa idanuwa jin abinda yafaWa ya sashi jin gabansa faWuwa tare da Waga hannuwa yace, ""Oh! So.sorry."" yana Wan ja da baya kamar mai tsoronta, dariya ya bata dan haka sai kawai ta juya tana murmushi, tana sane da yadda ya kwaye mata amma ya™i basa fuska don kar yaga damarta duk da itama Win tana sonsa, muryarsa taji yana cewa, ""Pls can i get your number Dan Allah? Akwai maganar da nake so muyi dake mai muhimmanci pls."" Allah daya haWata dashi ya sata juyowa ba tare data ce masa komai ba ta sinne kanta ™asa, da sauri ya ciro wayarsa yami™a mata ta saka masa lambar ta mi™a masa wayar, ""Thanks."" Ya faWa tare da juyawa yabar kitchen Win yana sakin ´ar ™arar jin daWi haWe dayin tsalle yana jinjinawa kansa da hannu, ita kuma ta saki dariya tana buWe tukunyar tuwonta daya gama nuna, dai-dai lokacin Mommy tafito, ""Kamal lafiya?"" Ta tambaya ganin irin tsallen da yayi, cikin jin kunya ya sosa kai yana ficewa ta bishi da kallon mamaki tana shiga kitchen Win, yanayin Murmushin data gani a fuskar ´ar tata yasa tafara tunanin wani abu amma sai tayi shiru tare tana shan alwashin sake sa masu idanuwa dan tabbatar da zargin ta, sai gashi cikin kwana biyu da Asiya tayi gidan ta lura da ala™a mai ™arfi ta shiga tsakanin ´ar tata da Kamal, baza tace bata ji daWi ba dan Kamal ya sauya fiye da tunani tun rasuwar mahaifiyarsu, babu wani aibi tattare dashi a yanzu da zata ™yamaci alakar ´ar tata dashi in har suna son junansu tunda yana da sana'arsa takansa yanzu bai dogara da abun mahaifinsa ba, haka ma tuni ya kammala ginin gidansa yana kan haWa lefe, dan haka sai kawai ta bisu da addu'a idan alkhairi ne Allah ya tabbatar da tare su, idan kuma babu alkhairi Allah ya rabasu cikin sauki ba tare da rayuka sun Saci ba, dan wani bangare na zuciyarta idan yana tuna mata wahalar data sha a gidan sai taji bata fatan ´arta ta shigo ta"

fuskanci irinta tunda dai su ´a´an so ne basa laifi.

"Wasa-wasa sai ga ™aramar magana ta zama babba, dan tuni Kamal ya sanar da mahaifinsa zancen"

"soyayyarsa da Asiya ya kuma ji daWi ya amince da zancen Wari bisa Wari, da yayiwa Mommy zancen nuna masa tayi itama sai abakinsa take ji tare da tabbatar masa da cewa ba tada abun cewa indai suna son junansu kuma mahaifin ita Asiya ya yarda da auren tana yimasu fatan alkhairi, nan take kuwa Abba ya sanar da ´an uwansa cike da mutuntaka suka je nemawa Kamal auren Asiya, da farko sam iyayenta basu amince da zancen ba sanin kowaye Kamal da sukayi ada, Wanda Wabi'unsa da Asiya ke faWa suna yiwa Mommy da ita kanta momyn da takeyi na daga cikin dalilan daya sa suka ki amincewa har sai daga baya da sukayi bincike sosai suka tabbatar da canzawar halaye da Wabiun Kamal Win, dan har ciwo sai daya kwanta da aka ce baza a bashi Asiya ba Meenal nata yimasa dariya wai yaji yanda take ji lokacin da"

"Mutallab ya™i karSar soyayyarta, gashi shima yanzu ya WanWana sunyi 1-1, Asiya kuwa dama Mommy"

"tafaWa mata kada ta taSa sakawa ranta cewa dole sai ta auri Kamal saboda shi Win ba Sa'ar ta bane, babu"

"kuma tabbacin cewa dole saita auresa tunda suna son juna idan har iyayensu basu amince da aura masu juna ba, dan haka bata bari ta zurfafa ba koda mahaifinta yakirata yace bazata auresa ba cewa tayi Allah yasa hakan shine alkhairi, ta kuma yi ™o™arin datse duk wata ala™a da abubuwan dake kusantata dashi dan nemawa kanta maslaha duk da irin wahalar da take sha, wannan yasa ganin bata daga kiransa, idan yayi mata message bata reply, tadena zuwa gidan Mommy, idan yaje gidansu shi kuma ya aika kiranta bata fitowa ya kwanta ciwo saboda damuwa da tashin hankali ganin zai rasata. Ana cewa iyayenta sun amince daga baya sai ga Kamal ya warke soyayya ta dawo sabuwa tsakaninsu tamkar zasu haWiye juna"

dan har amsa date Win aurensu nan da wata uku..

***********

Aïcha kuwa bayan kwana biyu sun karSi sakamakon gwaje-gwajen da sukayi sun kaima Dr khadija ta

"duba ta tabbatar masu da cewa duka lafiyarsu kalau babu wanda keda matsala kawai lokaci ne baiyi ba, dan haka sai ta basu shawarwari akan su dan yawaita kusanta musamman a ranakun da ake tsammanin fitowar ™wan haihuwarta (ovulation date) a turance ta hanyar amfani da calendar method, wato tafara ™idaya daga ranar data fara al-ada har zuwa rana ta goma sha bakwai, to a kwanaki bakwan ™arshe wato ranar 11 zuwa ranar ta 17 in son samu ne kullum ya zamana ansamu kusanta tsakaninsu saboda sune kwanakin da akafi tsammanin fitowar ™wan haihuwar mace kuma ana kyautata zaton ciki zai iya shiga, ta kuma rubutawa Aïcha folic acid tace kullum ta ri™a shan ™wayar Waya na tsawon wata uku kafin su sake dawowa asibiti, godiya Kamal yai mata sosai sannan sukayi Sallama suka wuce gida suna masu fatan Allah yasa su dace. (kema zaki iya gwada wannan method Win idan kina bu™atar haihuwa, in da rabo sai kiga kin samu, haihuwa Allah ke bayarwa da akwai lafiya da babu, duk wani magani ko tsari da za'a ce ki gwada to kiyi da ya™ini akan cewa Allah zai iya baki ta dalilinsa idan kina da rabon, idan kuma babu rabo"

sai kiga ba shine silaba wani abunne kadai zai zamo silar ta wata hanyar Adamu.)

Haka Aïcha taci gaba da shan maganin da Dr khadija Win ta bata tare da ci gaba da gwada tsarin calendar

"method har na tsawon watanni uku amma har lokacin shiru, wasu watanni biyu Dr khadija ta sake ™ara masu suka koma gida Aïcha cike da damuwa, p.t strip kuwa sun ™arar da yafi kwali daya wanda aduk lokacin da sukayi taga negative hakan na sake sakata cikin damuwa, tánte ce ta basu addu'o'i tace su rika tashi sunayi duk dare in Sha Allah zasu samu nasu ´a´an suma ganin yadda abun ya dan dami Aïcha, dan yarinyar Fannah kullum tana wajenta ko gajiya batayi da reno dan Fannah ta sake samun ciki wata uku kenan yanzu da kwanaki dan tana dawowa arba'in ta samu wani cikin bata sani ba sai kwanaki, tasha kuka sosai lokacin data san tana dauke dashi ganin lokacin babynsu watanta biyar aduniya batayi wayau ba. yanke shawarar zubar da cikin sukayi ita da Jalil amma fir Mutallab ya hanasu saboda ganin yadda yake son ´a´an shi bai dasu su kuma sun samu zasu ce su zubar, ba yadda suka iya dole suka hakura taci"

gaba da renon cikin Aïcha na tayata renon Baby Anam..

A Sangaren Meenal ganin har ta gama idda Mutallab bai waiwayarta ba asalima yaki saurararta yasa da

"masoya suka taso mata tafara kula su dan bata so mahaifinta ya haWata da wanda baiyi mata ba, sosai an samu sauyin wasu halayenta da Wabiunta musamman wajen tsafta da iya girki duka ba laifi tana ™o™arin gyarawa, jikinta ma tana kulawa ta dawo asalin Meenal Winta tafarko mai don kwalliya da gayu, wanda sai a yanzu ne take mamakin wai duk me ya hanata yin hakan agidan Mutallab musamman tsabtar jiki da suka fi samun matsala dashi. (Karku manta ko akwai halinta to akwai asiri da Umma tayi da bokanta yace zaiyi tasiri ne akan matar da Mutallab zai aura dan suyi nasarar jefasa cikin ba™in ciki wanda sanadiyar rashin tarbiyar Meenal ya janyo sukayi nasara akanta saboda asiri gaskiya ne, annabin"

Allah ma ya kama balle kuma mutum.)

"Islamiya ma tana zuwa yanzu ba laifi sai dai har yau ba iya kalamai da tausasa zance, haka ma idan"

abunta ya motsa bata fasa gayawa Mommy magana tunda hakan aka Worata tun farko kuma da hakan ta taso..

#Mutallab Asad

#³an Tagwaye

#Nana Diso

#Billy s Fari

*MUTALLAB ASAD*

Book 2

SHAFI NA GOMA SHA TARA

Arewabook:- billysfari

"Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER"

0020428430

"Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip"

post 1k ne.

Akwana atashi babu wuya agurin sarki gagara misali A yanayin da kwanaki suke tafiya haka watanni ma

"suke shudewa zuwa shekaru Mu muke lissafi Amma komai Namu ubangiji madaukaki ya riga ya gama kaddaramana dagon Numfashin naja ina Kara godiya ga Allah abisa Ni'imomin danake ciki Oh ni Aicha yau nice Har nagama service Nafada ina gyara kwanciyata amakeken palon na da yaji sabbin kaya da sabon fasali a gogon da™in Nakallah ina Tunanin Yau ko gobe Ma chèriè zai dawo kenan To amma Suprise yakeson yimun kenan tunda dazu mun dade muna waya Amma ya™i gayamun, wani farin ciki nakeji aci™in raina da samun miji mai kula dani sosai da ace Nabiyewa wasu kawayena dasuke zugani akan cewa indage sosai gurin bin malamai dan amallake mun shi batare da ya kara auren wata macce ba da na tabbatar nasaka rayuwata acikin gararin da bazan taba wanyewa lafiya ba. Shiyasa nake yawa gayamusu cewa "" ubangijin da yakaddara aurena da mijina yafikowa sannin komai akaina bazan zauna bana addu'a Allah yakaramana kaunar juna ya tsaremu ba Amma bana asarar da kudina agurin dan adam irina wanda na tabbata bazai taba iya tashi shi ™adai ya rokamun Allah bukatuna ba amma ni zan iya zama ni™adai Na rokawa kaina duk abunda nakeso gurin Allah shiyasa ma kwatakwata bana saurarar su aci™in maganganunsu ."" Shekarar dana fara makaranta abubuwa dayawa sunfaru daga ciki harda mutuwar jamil wanda ta girgiza mutane dayawa kuma ta haddasa rigima mai girma dan sai bayan mutuwar tasane akejin bashin dayaci kanana da manya wanda asanadiyar hakane sai da abba ya kwanta cuta sosai ganin yadda aban yadamu akan lamarin yasanya Mutallab yabiya kowanne bashin dan'uwan nasa. Ganin har lokacin Allah bai kaddara samun haihuwata ba sai nashiga damuwa sosai tsorona guda dayane kishiya Nabi na rame harma kakan iya fahimtar ina cikin damuwa dan duk lokacin da ma chèriè yabani wayarsa to akallah sai naga messages na mata sunfi a kirga Amma abun mamaki bana taba ganinsa yana chatting dasu hakan yasa dai nakasa kwanciyar da hankalina na damu sosai dan gani nakeyi mai wadata irinsa ai karyane ace baya soyayya awaje shiyasa wata rana bayan mungama level 100 yayimun fada akan ban fito da wani abun kirki ba bayan da fari yaga na dage Nan nasaka masa kuka nace nidai danAllah dayake yana bin ´ammata awaje gwara ya auro wacce yakeso. Ranar yayi murmushi ya kalleni baice komai ba "" daman nasan kana kule kulen mata dan ina ganin sakonninsu aci™in wayarka ai dole kayimun murmushi ai Nidai ko meenal ce kadawo da'ita da™inka tunda nasan yadda kake kaunar haihuwa ai."" "" Meenal ai tayi aure yafaWa yana kallona."" Adan firgice nace wanne aure kuma."" "" Am serious yafaWa."" Sai naji tausayin kaina kawai dan ganowa nayi idan nice ita ina zan samu wannan gatan"

sai shedan yashiga rayamun nima idan fa nayi masa wani karamin laifin zai iya aikani gida daga ranar na

takure kaina duk da tante tana min faWa sosai akan nadaina saka lamarin haihuwar nan akaina tunda

"anyi na asubutin anyi na gidan amma shiru. Bankara shiga damuwa ba sai ranar da fannah tazo da yaranta guda hudu wanda ranar naga yadda mutullab yake masu saboda kauna dan yaran dady suke cemasa ma kamar yadda suke gayawa jalil duk da naso abani amira tana jaririya wanda har jalil din ya amsamin amma ganin yadda naga kamar fannah din bataso ba yasanyani jan bakina nayi shiru bankara magana ba bansan dalilinta nahaka ba shiyasa tsakani na da yaran wasa da alkhairi dan yadda mijina ke yimusu hidima ko yaransa karshe kenan dan sai yazamana ko umara zamuje hardasu yake biya amma ni ko da wasa bai taba yimun maganar haihuwata ba a wannan lokacin ne afrah ta haihu itama namiji akasa sunan uban mijinta ansha buduri badankarami ba dan ashekarar suka bar kasar ma suka koma London ita da mijinta da yaronta wanda da ki tayi sai da yan uwan suka sakamata baki, ganin yadda yaga inashiga damuwa wata asabar yadawo daga tafiya ya rukunkumeni yana fadin "" DanAllah kidaina dagamin hankalinki mon amour Wallahilazim ko zamu shekara dari baki haihuwa ba ban tuhumarki nasan ubangiji babu ta inda baya jarrabar bawansa mu cika da Addu'a kawai sannan ina rokonki da Allah kidaina damuwa da matan da suke aikamin sako a waya dan ko inaso banaso sai sun aiko koda banda kudi Aicha kyauna da Allah yayimun

Please Login or Register in order to submit comment