gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading UCIYA DA KWANJI Saki Mai Daci 1 By Amierah S man Chapter 1 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://arewanovels.com "zuciya d kwanji1) Kyakkyawar mace matuka gaya! Fara sol,"

"mai kyakkyawan diri na matsakaicin jiki,tsarinta"

ya bayyana matsayin da kuma matakin da take

"kai na rayuwa,wato girman nauyin aljihunta,ko"

kuma na wanda ya dauki nauyinta. Da ganinta

"mace ce mai kasaita gaske,tare da dabi'ar son"

mulki da nuna ita wata ce.Ga ta kuma da karamin

"jiki,sai wancan kyau da yanayin shan kamshinta"

"ne kawai ke sabbaba mata kwarjini, yake sa wa"

"babba da yaro ke shakkarta,mace ko namiji duk"

"wanda ya kalleta sai ta tsuma shi,ya ji kamar ita"

"ta girmi kowa a idonsa,girma ba na shekaru"

"ba,irin na fada a ji,domin dai shekarunta talatin"

da biyu. Tana zaune ne akan farar kujera

karkashin bishiyar dorawar turawa a wani sashe

"na gidan zoo da ke kano,tare da wani mutum mai"

"alamun hakuri da fara'a,dan kimanin shekaru"

hamsin.kallo daya zaka yi masa ka gane inda

wannan kyakkyawar matar ta ci ta tada kai.

Yadda wajen yake da alamun kadaici haka

fuskokinsu ke bayyana damuwa da alamun

"kewa,shi yasa wajen tsit yake sai kukan"

"tsuntsaye iri iri,sannan akai akai mutumin nan"

kan dubi matar nan fuskarsa cike da alamun

"miliyoyin kauna wadda ta zarce misali,kamar"

"jikinsa har bari yake,amma wannan matar ko a"

"jikinta,tata fuskar babu abin da take bayyanawa"

sai gajiya da kuma gundura. Can ya nisa a

tausashe cikin ladabi irin na kwararren masoyi ya

"ce. ""Kar fa wannan ya bata ranki Fatima, ma"

sanki da son sanya wa kai damuwa Kin

"sa "" Sai ya yi shiru yana dubanta kamar zata"

"yi magana,sai kuma ta hadiye abarta,ta kuma"

"kawar da kai. Ya jima yana kallonta,bawan"

"soyayya dai sosai,sai kuma ya sake duban"

"agogon hannunsa,ya kara sayke ido a kanta,a"

"ladabce kamar wata gyatumarsa,ya ce, ""Ki yi"

"hakuri kin ji Binta?"" Nan ma ba ta tanka ba, ba ta"

"ma ko dube shi ba,illa ta dan muskuta. Zai kara"

magana ke nan sai ya hango wani matashi yana

"nufo su,mai kimanin shekaru talatin da uku..2) .wankan tarwada mai matsakaicin tsawo da fadi,akwai"

"alamun kan sharafinsa yake,ama'anayana jerawa da zamaninsa. Yana sanye ne da dakakkiyar shadda ruwan shanshanbale(purple),dinkin bankole da tajajjiyar suma wadda ta yi masa tsari matuka,shi ma yana da alamun fara'a,sai dai mai dakakkiyar fuska ne ta jarumai kuma irin wadanda kallonsu kawai ba zai sa ka iya yanke musu hukunci ba. Da barin jiki mutumin nan ya dubi Fatima,fuskarsa kamar gonar audiga ya ce. ""Kwantar da hankalinki Binta,kin ganshi ya karaso"". Ta dago ta yiwa matashin nan kallo daya,sannan ta kawar da kai gami da karamin tsaki,har ya karaso ba ta kuma sha'awar kallonsa ba. Tana jinsa suna gaisawa da mutumin,sannan ya juyo kanta da muryasa kamar wanda aka yiwa dole ya ce. ""Sunnun madam"" Ta motsa baki,amma sai ta hadiye amsa sannun tasa ta hanyar kyabe baki da kawar da kai,sai wannan mutumin ne ya wofintar da abin da ta yi da cewa. ""Abdullahi har mun gaji da jira,ka san fa ina da sabgogin yi, ita kanta madam ba ta kaunar irin wannan jiran"". ""A tausashe Abdullahi ya ce. ""A yi min afuwa Alhaji,na kai daya daga cikin iyalija asibiti ne,saboda tana fama da ciwon ciki. ""Allah ya sauwake"". Alhajin ya fada gami da sauke kallonsa kan fatima wadda ta mayar da idonta kallon wani sashen daban,kamar ba a gabanta suke ba, A tausashe ya ce. Fatima wannan shi ne Abdul da muke magana a kansa"". Ta juyo ta dubi Alh a kaikaice,sai dai ba ta tanka ba. Ya kara fadada fara'arsa yana dubanta,ya ce. ""Ina fatan ya yi miki?"" A lokacin ne ta kuma daga kai ta dubi Abdullahi wanda shi ma yake duban wani wajen daban.tun shigowarsa kallo daya ya yi mata bai kara marmarin kallonta ba,ko yanzu da"

jikinsa ya ba shi tana kallonsa sai ya kara yin kicin kicin ya ci magani sosai. Ta kawar da kai daga dubansa

"cikin tabe baki,har da tsartar da yawu,ta ce. ""Alh ya yi mana,tunda ba a kafata zan daura shi ba"". Alh ya yi karamar dariya,sannan ya basar ta hanyar duban Abdullahi ya ce. ""Abdullahi wannan ita ce Fatima,wadda na fara yi maka bayani rannan,matata ce, shekarun mu goma tare,muna son junanmu kwarai! Wata kaddara mai zafi ta gifta mana na yi mata saki UKU a lokacin daya.Rayuwa ta yi wahala a gare mu,domin ba zamu iya rayuwa ba tare da juna ba.Ga shi kuma ba mu da damar kasancewa taren..3) A baya mun dan yi wasu yunkurin na yin auren kisan wuta don mu sami damar mayar da aurenmu, kawunta ya dago mu saboda yanayin wadanda muke gayyatowa su yi mana wannan aikin. Wannan karon sai muka zaboka bayan mun gamsu ka toshe waccan barakar da ta ke sa wa ana dago mu. A yanzun ina mai gabatar da kai gare ta, shin ka amince zaka aure ta amma ka sake ta cikin wata daya? Ya kamata ka dauka mana wannan alkawarin.Ni kuma na yi alkwarin biyanka ladan kudin miliyon uku,ya ya ka gani?"" Alh ya yi shiru yana dubansa,inda shi kuma ya muskuta cikin nuna tsananin girmamawa ya ce. ""Kamar dai yarda na fada maka rannan,na amince da muradinka "" Fatima ta tare shi tana masa kallon goma ahu. ""Ta ya ya zamu"

"gaskata alkwarin ka alhalin yanzu ka gwada mana ba ka san darajar lokaci ba, ka shanya mu kawai kamar wasu kannan yara?"" Abdullahi ya yi kasake cikin dakewa da shan kamshi,yana motsa bakinsa a hankali har ya bar abin da yake son fada ya bi ruwa.sai kawai ya bige da kallon Alh,wanda yake kallonsa daya bayan daya.Tsarin nasu ya burge shi,kamar halayyarsu daya don haka ba zasu taba jituwa a inuwa daya ba. Ya dubi fatima sannan ya kara duban Abdullahi,wanda tuni ya dauki kai,ya ce. ""Ai ya wuce Binta,ban zabo shi ba sai da na amince da shi.Dan manyan gida ne gidan da aka san kimar amana,kuma bai yi kankanci a ce shi kika aura ba.yana da alkibla,yana da sana'a.Ba shi cikin shirgin sawa,duk wadannan makamai ne cikin cimma burinmu wanda za su yi tafiyar ruwa da kwakawar kawu. Ba ta ko motsa ba bare ta tanka,shi ma Abdullahi sai ya ga ba shi da ta cewa. ""To yanzu mene ne abin yi? Ko motsi Abdullahi bai yi ba,sai fatima ce ta dago ta harari Abdullahi,sannan ashagwabe ta ce. ""Gaskiya wata daya ya yi min yawa Alh,don ko sati daya tamkar akan kaya zan yi shi "" Ya tare ta cikin tausasawa. ""Na sani, amma babu"

"wata mafita wadda ta fi wannan ita zata dauke idanun basaldawa "" Yadda ta yi kicin kicin ya sa ya"

"dakatar da maganarsa da murya nan shi,ya ce. ""To yi shuru,Abdullahi ma haka. Dukkansu sai numfarfasgin kawai suke,da alama kowa dacin rai na damunsa,sai kawai Alh ya zuba musu ido,a sanyaye ya dubi Fatima sannan ya juya ga Abdullahi a kausashe ya ce. ""Wai me ye haka? Ba na son wannan cin maganin da kuke,kun san fa zaku yi ACTING ne sosai yadda da wahala a gane abin da ke binne,kun gane ko? Ko motsi fatima ba ta yi ba,sai ma kara hararar Abdullahi da ta kara yi,kai tsaye shi kuma ya yi murmushin da har kumatunsa suka lotsa,yana duban Alh ya ce. ""Kar ka ji komai Alh,ai nan ba wajen da zamu yi acting din ba ne, shi yasa duk muke tsaye akan kafafunmu4) Alh ya sauke ajiiyar zuciya,ya gyara zama ya ce. ""Ai shi ke nan,zaka fara zuwa zance.ke ma Fatima ki karbi shi da fuska mai kyau yadda su kawu ba zasu dago ki ba.ku yi acting sosai yadda za a zatar muku kaunar juna.ya yi kamar zuwa biyu sannan ya tura magabatansa ayi maganar aure, idan an zo sa rana,kar a sa lokacin mai tsawo kamar sati biyu haka sai ta tare"". Ya saka hannu a aljihu ya ciro wasu mabudai samfura biyu,na mota da na kofa,sannan ya fito da rubutaccen cek ya hada ya mika wa Abdullahi yana cewa. ""Daya makullin mota ne, ka zo office dina gobe ka dauka,ka fara amafanin da ita tun daga goben, don kawar da idon mutane.wannan mukullin gida ne,shi nake son ta tare a cikinsa tunda nasan ba ka da muhallin da zai dace da ita. Sannan wannan cek ne na kudin dubu dari bakwai ka fara hidimar auren da su dai dai matsayinka ka ji? Idan kana bukatar kari ka zo ka same ni, ladan aikinka kuma ranar da ka sallame ta,ba zaka bar gidan ba sai ta ba ka.kuma muna bukatar ka yi mata saki uku ne,ina fatan kana fahimta?"" Fuskar"

"Abdullahi ta nuna alamun zurfafa a tunanin,yana faman juya mukullan da cek din sai da Alh ta dure,"

"sannan ya dube shi da kyau,ya ce. ""Idan haka ne gaskiya akwai matsala"". Duk suka kara dubansa,har da fatima me shan kamshi,ya dan ja fasali tukunna ya ce. ""Mahaifina yana da matukar dora ido akan 'ya'yansa,abun ne mai wahalar gaske ya ganni da gidan da kuma sabuwar mota bai matse ni na fada masa inda na samo su ba. Kuma wannan dalilin ne da zai kafa min hujjar hana ni auren gaba daya. Fuskar Alh ya bace ya ce. ""Ayya! To ya ya za'ayi ke nan?"" Abdullahi ya yi kasake sannan ya numfasa. ""A bar maganar mota tunda ina da tawa, ko dai ta rainawar ce,maganar gida kuma idan zai samu tunda komai na maneji ne,me zai hana ta yi manejin a gidana? Gidan yana da yalwa dama sashen mata uku ne,sai nawa.yanzu haka matana biyu,kuma ina neman wani auren har an sa min rana,saura wata shida sai ta zauna a sashen amaryar bisa dole tunda ba daukar wani lokaci za'ayi ba,har an yi auren a gama kafin wancan auren ya zo"" Duk suka yi shiru alamun shakku.Da kyar Alh ya nisa,ya ce. ""Anya hakan zai yiwu Abdullahi? Ya ya za a yi ka hada fatima da wasu matan duk matsayinta? Idan a aurena ba ta san bakin cikin kishiya ba, ai bai kamata a naka ta sani ba "" Abdullahi ya yi saurin tare shi. ""To Alh ya ya zaa hada"

"wannan auren da naka? Ai bai kamata matana su dame ta ba,tunda babu wani dalili da zai sa ta yi kishi da su..... Amma in ba haka ba..... Gaskiya ina gudun bacin ran mahaifina "" Ya mikawa Alh makullan yana"

"mikewa.Alh na nacin kallon fuskar fatima wadda ta kara bata rai,ya ce. ""To me yasa zaka dawo min da cek din?"" Abdullahi ya ce ""Wai kafin ku yanke shawara"". Da sauri Alh ya ce ""A'a ka zauna mu yi komai yanzu mu gama,fatima kina jinmu fa, kina ganin zaki iya ace kin shiga cikin mata biyu,alhalin kin saba da mijinki ke kadai?"" Ya karasa da zolaya. Ta amsa kai tsaye. ""Ko mata goma ne a matsayin na 'yar ci rani bai kamata su dame ni ba. Ni na fi so a fi jaddada maganar iyakar kwanakin da zan yi a gidan ya sallame ni, sannan ko da wasa ba na so ya rabi dakina da sunan mijina,ya yi harkarsa kawai na yi tawa,ranar alkwari ya miko"

"min certificate kawai""Zuciya d kwanji"

"5) Alhaji ya sauke ido akan Abdullahi,ya ce."

"""Ka ji muradinmu"". Babu alamun shakka"

"Abdullahi ya ce. ""Na amsa"". Yana rufe baki"

"fatima da ke kallonsa,kai tsaye ta ce. ""Ban ji ka"

"ce ka dauki alkawarin ba, kuma da wacce alama"

"zamu yarda zaka cika?"" Ya amsa cikin dakewa ba"

"tare da ya dubeta ba. ""Babu wanda zai iya"

shaidar abin da zuciya ta boye sai wanda ya

"kage ta, sai ko in zuciyar ta dan yarjewa fudka"

bayyana alamu.Amma ku yi min hukunci da auren

"da na ce zan yi nan da wata shidda,Nasan kun sa"

"so ba karya ba ne, tunda a cikin mayensa"

"kuke,soyayyar da nake wa yarinyar ta kai mizanin"

"da ba zan iya rasata ta karamin dalili ba,wato"

"aurenki"". Karo na farko da suka dubi juna ita da"

"Alhaji suka yi murmushi,ba tare da ta ware"

"murmushinta ba ta dubi Abdullahi ta ce. ""To in"

"dai haka ne,kai dai ba ka san so ba, tunda ka dire"

mace biyu a gidanka ga ni ta uku zan shiga duk

"da in na kauce wata zata maye gurbina,na san"

kuma ba za a shekara ba ba tare da ka cike gurbi

"ba"". Har yau bai juyo ya dube ta ba,sai dai shi"

"ma fuskarsa da walwala ya amsa mata. ""Ai babu"

"wata me maye gurbinki,tunda naki wasa ne,ki"

"kuma sa wa ranki,ina aure akai akai ne don ban"

"dace da kawata ba,amma ita wannan ina jin a"

"raina daga kanta zan kulle kofa,don zata iya"

"amsa sunan mace hudu ma ba biyu ba""m Ba tare"

"da wani shakka ba fatima ta ce. ""To Allah ya"

"sa,don ni ban ga wani burgewa ba wajen tara"

mata da ya zame muku kamar wata gasa. Suna

"dariya ita da Alh,shi kuma Abdullahi ya ki share"

"maganarta,cikin karsashi ya ce. ""Amin"". Alh ya"

"maganatu ""Wai shekarunka nawa?"" Ya amsa"

"masa. ""22nd na wata mai kamawa zan cika"

"shekara talatin da uku"". Cikin kada kai Alh ya ce."

"""Ka ga ma 'yan watanin ka ba wa fatima saboda"

"haka ka bata girmanta kamar yadda zaka ba ni,"

ko babu wannan shirin ai ba sa'ar aurenka ba ce

"ko? Ko kuwa mutum na auren sa'arsa?"" Shiru"

"Abdullahi ya yi,Alh ya rufe maganar da cewa. ""To"

"don Allah ka zama yaron kirki,kar ka sake inji fati"

"ta yi kuka da kai,ka lallaba ta don Allah ka ga"

marainiya ce ko a zato ba na son bacin rantaZUCIYA d KWNJI.6) TUNA BAYA. Mahaifin fatima 'yan asalin

karamar hukunmar gwarzo ne a cikin garin

gwarzon mahifiyar fatima bafullatana ce gaba da

baya kusan a wajenta ma ta gaji kashi 70% na

kyawunta.A bangaren ginshira da shan kamshi

kuma sai ta gaji mahaifinta wanda yake jinin

sarauta. Kakan fatima wanda hakimi ne na

"wannan karamar hukuma,'ya'ya uku kacal ya"

"mallaka,mahaifin fatima sai kannensa biyu,prof"

alkasim da karamar kanwarsy Dr maryam. Fatima

ta taso ne marainiya gaba da baya.sakamakon

rasuwar mahaifanta duka biyun a ranar da za'a yi

bikin cikar shekarunta uku a duniya. Daga nan ne

rukonta ya dawo hannun kanin mahaifinta

"prof,wanda a lokacin wataninsa uku kacal da"

aure. Kawu (prof) muntum ne mai tsantseni

"kwarai, kuma masanin yakamata,sai kuma ya yi"

dacen mace ta gari kamar shi.Don haka har zuwa

yau fatima ba ta taba dan dana wani dacin da ya

"yi kama da maraici ba, sai ma da hankalinta"

tasan cewa ba su suka haife ta ba. Gidan su

"gidan jama'a ne matuka,don karamcin ma'abotan"

"gidan,don haka duk wanda zai taso a cikinsa sai"

ka tarar da shi wayayye ma'abocin iya

"mu'amala,sannan mara kyashi ko kadan,saboda"

"sabo da jama'a"". Kawu na da 'ya'ya"

"shidda,babba cikinsu safiyya wadda ta ke kamar"

"sakuwa ga fatima,tare suka yi fadi-tashin"

"kurunciya,sai maza biyu suka biyo baya, Najib da"

"Abdullahi,sai kuma Nasiba sannan auta"

khalid.Don haka duk cikin manyan 'ya'yansa

fatima yake kallo san kuma taba bambantata

cikin 'ya'yansa ba. Ya bata ilimi mai kyau kamar

"su,sannan ya jajirce cikin tarbiyyarta iyakar"

"kokarinsa,duk da dai gatan da yake mata saboda"

maraicinta ya ba ta damar sangarta.ta zama

wata me murdadden ra'ayi wadda ake shan

wahalar canjawa manufa ko da karmatacciya ce.

Tun fatima na karamarta kowa ya dubeta yasan

an sami kyakkyawar mace mai sanumfashin maza

"sassarfa,kyawun da ya hadu da ilimi da kudin,sai"

ta zama wata zara'a cikin mata.Ta yi matukar

"farin jinin a wajen maza,har ma da matan da"

"Allah ya zare wa kyashi da hassada,don ma"

kasaitarta da miskilancinta na wahalar gaske

fatima ta fita wani masoyi bai biyo bayanta ba.

"Shekarar da ta kammala sakandire,kawu ya fara"

"koyarwa a jami'ar bayero,sai faduwa ta zo dai dai"

da zama domin a shekarar ta fara nata karatun a

nan inda ta karanta (biochemistry) suka tattara

suka bar tarauni zuwa gidajen malamai na nan

jami'ar.ZUCIYA D KWANJi

.7) Dai-dai

wannan lokacin Alh sulaiman karansa ya kai

tsaiko bayan doguwar gwagwarmaya wadda

kokawar tarar da buri ya haifa. Nasa mahaifin

"karamin ma'aikacin gwamnati ne,bayan ya yaki"

"jahilci,sai dai mai jar zuciya ne,wanda ko za a"

kwanta ba a ci ba ya laminta ya gabatar da

bukatar karatun sulaiman sai kuma ya yi dace

mahaifiyarsa ta zama mai tawakkali da goyon

"baya,har ya kai ga hada digiri dinsa a (business"

administration). Tun tasowar Alh mutum ne mai

"manyan burika,sai dai yana da juriya da jarumtar"

shanye wahalhalu wajen cika su. Bayan kammala

"karatunsa,ya yi zaman fiye da shekaru biyu yana"

neman aiki kasancewar bai sami wanda yake buri

"ba,a karshe ma kawai sai ya koma makaranta ya"

"yi masters dinsa akan Economic,shekaru biyu ya"

"kuma dawowa ya zauna jiran tsammani,sai ma"

"aikin ya fi tsauri a wannan lokacin,saboda"

"karatunsa ya yi zurfi, guraben da zai shiga sun yi"

karanci. Shekara daya da wannan karatun ne

mahaifin wani abokinsa ya hada shi da wani

"kwara,wanda harkar kasuwanci ta kawo Nigeria,"

inda suka fara gwada shi kan shigo da wasu

"injina,kwazonsa da kwarewarsa akan wannan"

harkar ya sanya ba a shekara ba sai da suka

bude wani katafaren kamfani suka dora shi akai.

"Labarin ya canja,Alh sulaiman ya fara cimma"

wasu daga cikin manyan burinkan da suke bunne

"a ransa,kamar mallakar manyan motoci,kama"

"kudi,da kosassun gidajen da suka yi kama da"

"aljannar duniya,daga nan kuma ya fara hangen"

"kyakkyawar matar da zata dace da shi,don tun"

yana sakandire ya yiwa kansa alkawarin ba zai yi

"aure ba sai ya mallaki gida da mota,sannan ya"

auri kyakkyawar mace. ***************

****************** Mahaifin Abdullahi wani

"shahararren malamin ne, kuma alkali ne,mai suna"

"Ustaz ukashatu Mohammad,mutum mai adalci da"

"yawan dattako,yana da tarin 'ya'ya maza shidda,"

"mata ashirin da uku,wadanda matansa hudu suka"

"haifa masa,duk da yanzu saura uku,don"

mahaifiyar Abdullahi Allah ya yi mata rasuwa

shekaru biyu da suka wuce. Abdullahi ne dansa

"na goma,kuma auta cikin mazan nan,kuma a cikin"

"mazan nan shi kadai ne bai gado gida ba,wato"

"karanta shari'a ko koyarwa,sai ya karanci mass"

"communication, amma sai ya buge da aiki a"

(ministry of rural & community development) ya

kai matakin albashi na goma. Abdullahi mutum

"ne mai hikima da dankaren wayo,hangen nesansa"

na taimako kwarai a rayuwarsa wajen mallaka

masa dukkan buri.jarumi ne kwarai wanda ba'a

"taba gane lagonsa,ba ya fushi a inda ya fahimci"

"fushi nasa ba shi da ma'ana,sannan ba ya dariya"

a inda ba a san darajarta ba.8) Don haka kankantarsa ta tsaya a jikinsa ne

"kawai,amma zuciyarsa dattijiya ce.azancinsa"

kuma tsoho ne mai rankarfe. Matarsa ta fari

"sadiya,wadda ya aura shekarar da ya kammala"

"karatu ko fara aiki bai yi ba,makociyarsu ce"

wadda soyayya mai zafi ta shiga tsakaninsu kafin

"auren,wadda kuma ita ta taimaka wajen"

amincewar mahaifinsa akan auren sadiyar da

"shi,kasancewar sadiya ba ta fito gidan tarbiyar"

"da ta gamsar da malam ba,sai dai dole kunyar"

idon mahaifinta tasa ya amince wanda takanas

ya ishe malam din ya ce ya bai wa Abdullahi

auren sadiya. Sai dai kash! Sadiya ba ta wa

"masa dan malam kunya ba,sai au enta da"

"Abdullahi ya dinga haifar da matsaloli,matsakaita"

"da kanana,wasu kishiyoyin juna,sadiya"

mafadaiciyar mace mai yawan kuncin zuciya da

tsarguwa.Ga kuma Abdullahi miskilin mutum

"kuma mara daukar raini,sannan mara daukar"

"korafi da muhimmanci, wadannan dalilin suka sa"

zuciyoyinsu suka canja daga masoya juna zuwa

wani abu daban. Kullum su ke nan cikin

"hayaniya,sadiya ta dauki kafa ta yi yaji,shi kuma"

ya yi zuciya ya share ta har sai manya sun shigo.

Da abin ya ishi malam sai kawai ya nemar wa

Abdullahi wani auren. Hindatu ke nan matar

"abdullahi ta biyu, wadda ya aura ba bisa doron"

"so ba,sai dai ta sami filin karamci a zuciyarsa"

saboda hakurinta da saukakawa kai buri.tana

nuna masa wadatarta akan iyakar soyayyarsa da

adalcin da ya yi mata duk da kuwa ba ya iya

boye bambancin da zuciyarsa ta ke nunawa

tsakaninta da sadiya wadda za a iya kira

mowarsa duk kuwa da tambelenta. Shekarun

"hudu ke nan da auren fari,kuma shekarun biyu da"

"auren Hindatu,amma cikinsu babu wadda tataba"

"ko batan wata, wannan ma sai ya bi layi cikin"

matsalolin da suka dami duniyar Abdullahi.

****************************************** Alh

sulaiman abokin ne na kud-da -kud ga yayan

"Abdullahi,mai suna Abdulawahab.sun yi karatun"

"sakandire tare,kuma daga nan abotarsu ta samo"

asali. Ba za a ce abdullahi ya yi masa farin sani

"ba, kasancewar lokacin da ya yi wayo"

"sosai,sabgogin sun yiwa Alh sulaiman"

"yawa,ma'ana ya yi wuyar gani,amma ya waye da"

Alh ya kawo wa yayan abdullahi lokacin da ya yi

aure na biyu. Abdullahi na tare da yayan nasa

yana sauraron hirarasu. Abdulwahab yana zolayar

"Alh da cewa. ""Sulaiman burinka fa kamar ya wuce"

"mallakar makudan kudin,gidaje da motocin hawa"

"kafin ka ajiye iyali,me kake yiwa kanka kawa ne?"""

"Alhaji na dariya ya ce. ""Wallahi har yau na kasa"

"samun matar da zata da ce dagida na,watanin"

baya na so auren wata balarabiya wani abokina

"ya dinga kwabata,wai tatike maza suke su"

"tsere,dole na hakura tunda an ce mutum ba ya"

"kin ta mutane"". Abdul wahab ya ce. ""Haka ne,"

amma ya kamata ka yi taka tsantsan a cikin

"sha'anin mata,sun fi kowacce kawa"

"hatsari,musamman kyawawa don yawancin su"

"nagartasu ba ta kai masu karamincin kyau ba,sai"

ka zauna da matarka mai karancin kyau ka dinga

"sarafa abarka son ranka,amma awajen"

"kyakkwayawr mace ka yi kadan,komai kudinka da"

"mulkinka,wuyarta ta kalli kanta a madubi sai ta ji"

"ta girme idonka,kuma ko yau kuka rabu zata sami"

"wanda ya fi ka,don haka ba ka isa ka sa ba,balle"

"ka hana"". Kamar a sanyaye Alh sulaiman ya ce."

"""To,Allah ya zaba manaZUCIYA D KWANJI"

9) Alh sulaiman

ya hadu da fatima ne ranar bikin kammala

"karatunta,gaba daya ya sakwarkwarce,don"

fatimata kusan zarce tanadin da yake wa kansa

game da mace. Sunanta ya nuna masa daga inda

"ta fito,sai ta kwanar masa gidansauki,domin"

"kawu malaminsa ne tun a sakandire,sannan ya"

koyar da shi a digiri dinsa na farko.sun shaku

matuka suna ganin mutumcin juna kasancewar

kawu mai son jarumin namiji mai hazaka da

juriyar cimma burin abin da ya sa a gaba.To

"Allah ya horewa sulaiman wannan,mutum ne mai"

"kaifin kwakwalwa,wanda duk abin da aka zuba"

"mata sai ta kwashe,shi yasa yake ji da shi tun a"

sakandire. Kwana uku da ganinta ya wanke kafa

ya tafi gidan prof.bayan ya nemi izininsa a waya.

Pro ya karbe shi cikin mutumci kafin ya shiga

"rudanin abin da ya zo masa da shi,wato neman"

"auren fatima. ""Ko akwai matsala ne?"" Alh ya"

tambaya saboda ganin yadda kawu ya shiga

damuwa. Prof ya sauke numfashi ya ce.

"""Sulaiman fatima ta dade tana dauko min magana"

"wallahi,manyan mutanen da nake jin kunya ba"

zan iya kirga maka wadanda suka zo da kokon

bararsu gare ni na son auren fatima ba.Amma sai

"ta watsa mana kasa a ido ni da su,na rasa inda"

"yarinyar nan tasa gaba,kowa ya zo ba ta so.A"

bayanta fa kanwarta ta biyu ake shirin

"aurarwa,amma ita ko a jikinta maraicinya ke sa"

"ni tausayamata,amma tabbas da ni na haife"

"fatima da na tilasta mata aurenka"". Wannan to"

"gaciyar ba ta sa sulaiman ya dauke kafa ba,sai"

ya ci gaba da kawo gaisuwa da rokon iri har aka

kai matakin da kawu ya ba shi damar bayyana

kansa ga fatima.Amma kash! Sai aka yi rashi

sa'a cikin masu son ta ba ta taba tsanar wani

"sama da Alh sulaiman ba, ba ta kaunarsa ko"

kadan kuma ba ta iya boyewa kowa ma ya sani.

"Shekarunsu biyu a haka, fatima ta kammala"

"service,ta kuma nemi izinin kawu na neman aiki.A"

nan ne kawu ya yi ta maza ya ce sam bai san

"wannan zance ba, ya ma ba ta wata guda na ta"

"fito da miji, idan ba haka ba sai dai ta ji taron"

dauran aure. Fatima ta dauke maganar kawu

"wasa,har ta bare watan ya share a wasa,sai rana"

"tsaka ta ga taron jama'a a gidansu,labarin ya zo"

mata an daura aurenta da Alh sualiman. Tarihun

"auren ke nan,wanda labarin zamansa sam babu"

"dadi,Alh sulaiman ya cimma burinsa na mallakar"

"""KYALLI HUDU"". Sai dai kash! Kyalli daya ya hana"

"shi natsuwa,wato fatima,ta hana shi kwanciyar"

hankali sam. Ta kwakware dukkan farin cikin da

sauran kyallin suka samar masa.Ga shi Allah ya

"jarrabe shi da masifar kaunarta,shi yasa ta ke"

dama garinta a sha yadda ta ke so ko da babu

gasara balle sukari. Duk abin da fataima ta

"shimfida kpo ba ya so sai ta aiwatar,ga jarabar"

"kasaita kamar 'yar sarkin santanbil,sai ya yi"

"magana hamsin fatima ba ta tsinka daya ba,idan"

"ma ba ta so ba, sai su kwashi kwanki ba su ga"

"juna ba,don babu ruwanta da duk wani abu da ya"

"shafe shi, cinsa ko shansa da kula da"

dawainiyarsa duk ta sallamawamasu yi masa

hidima. Kamar yadda bai isa sanin wani abu

game da shige da ficenta ba bu ruwanta da

"daukar damarsa,ko yana cikin gidan sai dai ya"

"hangi ficewarta da mota,ko kuma duk sanda ya"

"shigo gida ya binciki masu gadi,""hajiya na ciki,ko"

"ta fita?"" Kai kansu ma'aikatan gidan hakan na"

"bala'in bakanta masu rai,ballantana danginsa"

wadanda fatima ba ta dauke su a bakin komai

"ba,ko gidan suka zo kashi ma ya fi su daraja a"

"idonta.Gaisuwa kadai ke hada su, babu duka"

"babu zagi,amma babu ruwanta da mutum har ya"

karaci kwanakinsa ko wuninsa ya bar gidan.

Mahaifiyarsa ce kawai ta ke samun arzikin kallon

"kirki,shi ma a wani yanayi na kamar dole don ita"

kanta mahaifiyar tasa tasan fatima ta tsane

"ta,kamar yadda ta tsane dantaZUCIYA D KWANJI"

.10) Duk wadannan munannan dabi'u na fatima

"ba su taba rage matsayinta a zuciyar Alh ba, da"

"zata yi mugun bata masa rai,idan ya hangi"

murmushinta ko tsakainta da wani ne sai ya ji ta

wanke masa zuciya.Don haka duk yadda

mahaifinyarsa da sauran danginsa ke nuna masa

"illar fatima ba ya gani,idan ma ba a yi wasa ba"

"sai reshe ya juye da mujiya,ma'ana ya tsani me"

"kawo sukar,har dai kowa ya fahimci shi aka daina"

"kawo masa sukar,illa addu'ar ganewa. Duk wata"

biyayya da mace ya kamata ta yiwa mijinta

fatima ba ta santa ba a tsakaninta da Alh kuma

"ta kan yi

Please Login or Register in order to submit comment