gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading UCIYA DA KWANJI Saki Mai Daci 1 By Amierah S man Chapter 5 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hau yi min

"wannan masifar?"" Tsaki taso ta yi,amma ga"

mamakinta sai ta ji zuciyarta na shakkar ta yi

"masa tsaki,dole ta buge da kada harshe,sannan"

ta dubi wani wajen daban. Ya kara fadada

"murmushinsa yana kara nazarinta,ya ce. """

"Sharadin nawa ba fa wani mai tsauri ba ne,"

dama

fada miki zan yi. Nan gidan babu matar da ta ki

"fita sai da izinina,ma'ana idan kina fita a"

gidan

Alh ba tare da neman izini ba a nan gidan lallai

"ne sai da yardata,don haka kar ki sake in ga"

"karfarki a waje ba tare da yardata ba"" Bai bata"

damar magana ba ya kuma dora wani batun

"bayan ya mike ya nufi kofa. ""A karshe in"

"shawartarki da karanta waya da Alh, sannan ki"

"san irin maganganun da zaki yi da shi, saboda"

gudun bacin rana wani cikin gidan nan yasan

"halin da muke ciki,sannan idan akwai hali ki"

dan

"boyewa duniya rashin kaunar da kike min,kin"

"gane ko? Taso ki rufe kofar"". Ba tare da ya jira"

"cewarta v ba ya fice daga falon,tana binsa"

galala

da kallo cikin tsabar rudu. Ta rasa makamar da

zata rika don fara nazari akan wannan ba

izgilen

mutumin wanda ko shakka babu ya riga ya gama

"damarta,ita ma kuma da alama ta fara sallama"

"masa tunda ta ke jin shakkarsa,koda yake"

dama

"can ita ba masifaffiya ba ce, Allah ne kawai"

yake

dorata akan mutane suke shakkarat. To da

alama

"bai dorata akan Abdullahi ba, wanda yake nufin"

"wasu abubuwa masu tsauri a kanta,irin wanda"

numfashinta zai jure da ma wanda ba zai jure

ba.

"""Kar ki sake in ga kafarki a waje..."" Maganarsa"

ke

nan da ta bude mata kofar hasashen me

Abdullahi yake nufi a kanta? Yana son nuna

mata

iyakartaZuciya d kwanji

.32) Yana son nuna mata iyakarta ne ta hanye

mulkarta don tana cikingidansa ko kuma kawai

yana nufin kuntata mata ne don ya sami

wannan

damar? To idan ba ta fita ba me zata ci? Kuma

idan ta fita ba da izinin nasa ba me ya tanadar

mata? Ba ta iya amsa dukkan tambayoyin da ta

"yiwa kanta ba, kuma hakan ne ya taimaka"

wajen

raunana zuciyarta ta barke da kuka. Ta je ta

rufe

kofar sannan ta dawo ta zauna ta ci gaba da

kukanta tana tuno tasirin Alh a

"rayuwarta,wanda"

ba ya iya ja da duk wani zabinta ko da kuwa bai

"wa ransa dadi ba, a hakan kuma kullum yake"

kirarin sauran mata rakota duniya kawai suka

"yi,"

amma yau ga ta a gidan da ake aikata mata ita

"ta rako matan duniya,har da bita da kullin"

takura

da wulakanci. Kusan a nan zaune ta kwana a

nan

"falo,sai da aka fara kiraye kirayen sallar asuba"

sannan wani malalacin bacci ya fara fizgarta.ta

daure ta jira sallar asuba ta gabatar da ita

sannan ta kum kwanciyar anan falo bacci mai

nauyi ya dauke ta A hannu daya sadiya ta fita

daga nata kuncin tun shigowar Abdullahi a

daren

jiya wanda ko kallon kofar dakin amarya bai yi

"ba,ya share guri ya zauna kallon wasan kwallon"

"Kafa,har wannan daren ya yi musu asuba ta"

gari

sannan ya waiwaye amaryar shi ma kamar akan

"kaya,sadiya na duban agogo mintuna ashirin da"

takwas ya yi ya fito ya shige nasa dakin har

wayewar garin nan. Sadiya ta gama yardar wa

ranta wannan amaryar har ta fi Hindatu

kaskanci

"a idon Abu Turab,lallai babu wata mace da zata"

"sami rabin matsayin da ta ke da shi a zuciyarsa,"

wannan ya sa kashi 70% na kishin amaryar ya

"fice daga zuciyarta,hanka linta kwance ta shari"

bacci har da saleba. Wajen karfe goma Abdullahi

"ya kwankwasa kofar sadiya cikin shirin fita,ba"

shi

"da yakinin zata saurare shi,domin jiya.da safe"

kaca kaca suka rabu. Amma ga mamakinsa ko

"minti daya bai hada ba ta zo ta bude kofar,ba"

"tare da ta dube shi ba ta wuce kai tsaye , ya bi"

bayanta ya zauna hannun kujera yana mai

"fuskantarta,fuskarsa kunshe da walwala,ya ce."

"""Kin tashi lafiya?"" Ta kawar da kai tana shan"

"kamshi,ta ce. ""Kalau"". Ya dan zuba mata ido"

ya

"ce. ""Ina fatan kin ci abinci kafin ki kwanta"

"wannan baccin naki,bana son zamanki da"

"yunwa"". Ta muskuta ta kara gyarawa,wanda"

"hakan na bayyana hasken da zuciyarta ke yi,sai"

dai ba ta son bayar da kai bori ya hau. Ga

jarabar dokin da ya ishi zuciyarta na son ganin

wannan amarya wadda ta buzuz ta fi ta kima. A

"yangance ta dubi kwayar idonsa ta ce. ""Wai fita"

"zaka yi ne?"" Yana yi mata wani tsadadden kallo"

"ya ce. ""Eh,uwargida ran gid,ko in zauna akwai"

"abin da za ki ba ni?"" Ta yi saurin girgiza kai. """

"A'a sauka lafiya,wai ba zaka gabatar da mu ga"

"juna ba ne a wajen amayar taka?"" Ba tare da"

ya

"ba wa maganarta muhimmanci ba, ya ce. ""Har"

"sai na gabatar da ku ga juna sadiya,sai ka ce"

wasu yara? Ku gabatar da kanku ga juna

"mana,ta zo wajenku ko ku uje inda ta ke"". Ta"

"dube shi da gefn ido,ta ce. "" Kawai kuma a"

matsayina na babba sai na zubar da girmanan

na

shiga wajenta ko? Ya tuntsure da dariya ya ce.

"""Sadiya ke nan uwar son girma. To wallahi ta"

"girme ki, ko wannan kika duba kya ba ta girma""."

"Fuskarta ta cika da walwala ta ce. ""Oh tsohuwa"

ka kwaso mana ke nan?

"1 Like React Report May 14, 2015"

Amierah S-Man

Zuciya d kwanji

".33) Ya gyada kai ya kuma girgiza, ya ce. """

"Idan kin ganta idonki ya kwashe miki"". Ya"

"mikamata hannu alamar ta zo gare shi,yana"

"cewa. ""Wai ba zamu gaisa ba ne?"" Ma'ana ya"

basar da wancan zancen. Ta kawar da kai ranta

"na kara haske,tana kada idanuwa ta ce. ""Ai na"

"sallamawa amarya,idan kwana ukunta sun cika"

"ka kara mata wata daya a nawa"". Ya iso gare ta"

"yana girgiza kai. ""Ba zan iya maraicin rashinki"

"ba"". Ya jima suna faranta ran juna,sannan ya"

yi

mata sallama ya nufi dakin hindatu. Yana shiga

kicin dinta ya wuce ya barta a falo ya kinkimo

fulas da kofi ya zo ya zauna tana faman binsa

da

"kallo,ya ce. ""To tashi da sauri mana ki kawo min"

"mahadi,kina ganin zan makara"". Murmushi"

kawai

"ta yi,ta mike zuwa kicin ta zubo masa wainar"

shinkafar da ta yi da kyakkyawar miyar

"albasa,sannan ta kawo masa kayan shayi, sai da"

ta hada masa komai sannan ta koma gefe tana

"cewa. ""Abu Turab ai ban yi tsammanin zaka fita"

aiki yau ba. Haba zaka ragewa amaryarka

"daraja,"

"a kawo ta jiya kuma yau ka barta ka fita aiki""."

Ya

"fara taimakon cikinsa yana cewa. ""Aljihuna ne"

"babu ko karfanfana dole sai na fita,ko"

akwai'yan

"kudi a wajenki ki sam min aro?"" Ta yi saurin"

"girgiza kai,ta ce. ""Ba ka dai kyauta ba. Ai ya"

"kamata ka yi tanadi tun jiya"". Bai dube ta"

"ba,ya"

"amsa. ""Za a kori gaba"". Takawar da kanta daga"

"gare shi,ta ce. ""Me ye sunanta?"" Takawar da"

"kanta daga gare shi,ta ce. ""Me ye sunanta?"" Ya"

"dan zuba mata ido,sannan ya amsa ""Sunanta"

"fadimatu,don Allah anjima ki yi kokarin lekawa"

"dakinta ku gaisa,kar ki duba komai,ki duba ni"

da

"na ce ki je din kin ji"". Ita ma ta dan kafa masa"

"ido sannan ta kawar gami da ajiyar zuciya,ta"

ce.

"""Anya ba ka dora min babban aiki ba kuwa Abu"

Turab? Me yasa ita ba ka yi mata izinin ta biyo

"mu dakunanmu mu gaisa ba?"" Ya girgiza kai, ya"

"ce. ""Na fa ce kar ki duba komai"". Sai kawai ta"

tsaya tana kallonsa yana ta faman cin

"abincinsa,dama shi mutum ne mara wasa da"

"cikinsa. Can ta nisa ta ce masa. ""Wai amaryar"

ba

"ta yi girki ba ne,to ita me zata ci?"" Ba tare da"

ya

"dube ta ba, ya ce. ""Yanzu zan fita na nemo"

"mata"". Sai ta ji maganar na yi mata yawo a rai."

"A gidan Abdullahi za a ki dora tukunya,kuma a"

"fita waje a siyo,kuma wai shi ne ma da"

"kansa,anya? Ta dai share har ya gama ya yi"

"mata sallama ya fice,can ta ji tashib motarsa"

bai

fi mintuna ashirin ba ya dawo. Da sauri suka hau

lekensa daga ita har sadiya wadda ta ke son

"sanin abin da ya dawo da shi,yayin da Hindatu"

ke

dokin ta ga kalar abincin da za a tarbi amarya

da

shi. Mai masa share sharen harabar gida ya biyo

shi da manyan kwalayen sunfi a kirga sun fi

kala

"goma dangin kayan sha,tsotse tsotse da tande"

"tande,shi kuma abdullahi na rike da ledoji biyu"

na

take away mai tambarin wani shahararren

restaurant. Sai da Ayuba ya gama shigowa da

"kayan kofar dakin amarya ya fita,sa nan"

Abdullahi ya fara kwankwasa mata kofa. Wani

tokareren bakin abu ya tokarewa safiya a kahon

"zuci,kamar ta hadiyi zuciya ta mutu,Hindatu"

da

sauri ta saki labile zuciyarta na wani irin

bugawa.tunda ta ke ba ta taba jin zafin kishin

"Abu Turab irin na ranar yau ba,duk da kuwa Abu"

turab tuni ya bayyanar mata sadiya ce mai

kyallin goshi. Cikin magagin bacci fatima ta ji

"bugun kofarsa,da sauri ta bude idonta ta dubi"

"agogo,sai ta tarar sha daya har ta gota, nan"

take

"kalamansa suka fado mata. "" Da safe"

kuma

ko ba ranar girkin ba ne zan dinga shigowa mu

"gaisa "" Ta ture bargo ta dau hijabinta ta"

zira

"kirjinta sai harbawa ya ke, saboda fargabae irin"

cin kashin da ya kunso mata mata a wannan

"shigowar, tunda shi dai ya zama annoba, duk"

haduwa sa ya gadar mata bakin ciki

"3 Like React Report May 14, 2015"

Amierah S-Man

Zuciya d kwanji

34) Sai da ta yi ta gwada irin yadda zata

daure fuska da kuma kalaman da zata iya

fansar

"kanta idan ya nemi raina mata hankali,sannan"

ta

"bude masa kofar,ta koma makwancinta ta"

zauna

tana cin magani bayan ta lullube kafarta da

bargo. Sai da ya gama shiga da kayan nan a

"kicin dinta tsab, sannan ya kitsa da ledar take"

"away din, ya ajiye bisa coffe table fuskarsa a"

daure ya fara nazarin falom da shiwadda ko

kayanta na jiya ba ta cire ba ga kuma shaidar a

falon ta kwana. Sai daya gama nazarinta tsab

"cikin sassaucin murya ya ce. ""Kin tashi lafiya?"""

Ta kada kwadar ido da kawar da kalba tare da

ta

tanka ba. Ya ci gaba da kallonta wasu irin

abubuwa na huda zuciyarsa juriyarsa na shanye

"su. Ya bata murya ya ce. ""Ga kayan kwalam din"

da kika ce min sun ishe ki sati biyun da kike

"zatarwa kanki a gidan nan,idan akwai wani abu"

"da kike muradi sai ki sanar da ni,wannan kuma"

karin kumallo ne na yanzu (yana nuna mata

take

away din) bai kamata na je gidanku na ci abinci

"mai kyau ke a nawa ya gagara ba"". Ta daga a"

"wulakance ta dube shi ta ce, ""Nawa ka kashe na"

biya ka? Ai ba mu shiryo ta zaka yi wata wahala

"da ni ba"". Tana rufe baki ya amsa mata. ""Ni ne"

kawai na shiryowa kaina a wani gefen kuma don

"na nuna miki kudin kawai kika fi ni,amma na ki"

da

"shugabanci daga indallah"". Takre ya bayana a"

"fuskarta. ""Wa kake shugabanta ?"" Ya tare"

ta

"da gadara. ""Ke!!!!"" Ta kada kai tana cije"

"lebe,ta"

"ce. ""Ai na fi karfinka abdul ya ya zaka yi da"

"ni?"""

"Nan ma bai yi kasa a gwiwa ba ya amsa. ""Yadda"

namiji yake da ko wacce mace musamman

jarumi

irina me jarumtar kashi da ta zuciya Ni sam

ban taba yarda wata mace ta fi karfin namiji ba

"duk irin kasaitarta "" Ta motsa baki kamar"

zata

"yi tsaki,sai ta hadiye shi,Nan take kanta ya"

fara

"ciwo saboda tsabar takaici,ta dafe goshi kawai."

Zai kuma dorawa ta dago ta kalle shi rai a

"bace,ta ce. ""Abdul wannan hayagagar taka ta"

"ishe ni, idan ka gama abin da ya kawoka ka fice"

"min,kuma daga yau bana bukatar gaisuwarka da"

bankwananka.Na yarda ba zan fita ba sai da

"izininka, sai dai ba zan taba neman izinin naka"

ba

ma'ana ba zan fitan ba har wa'adin mu ya cika

"mu rabu kowa ya huta,isa kuma na yarda ka isa"

ai ga alama nan tsurut da kai ka ajiye mata

biyu

kana shirin ta uku ko wannan aka suba sai a

sara

"maka "" Kuncinsa kunshe da murmushi ya"

tare

"ta. ""Kin zare kanki daga ciki ne?"" ""Kin zare"

kanki

"daga cikih ne?"" Ta yi fuska,ta ce. ""Ai dama ba"

a

"ciki nake ba"". Ya yi mata wani kallon mai tarin"

fassarori wanda ita kanta duk hikimarta ta kasa

ba shi ma'ana.ya jima yana jan fasali sannan

ya

"kada kai,ya ce. ""Akwai amanarki a tare da"

"ni,wanda shugabancinki a yanzu ya jaza"

"min,saboda haka dole na shigo na miki"

bankwana

"kuma na ga yadda kika kwana "" Sai ta yi masa"

"shiru ranta na kara daci,ya jima tsaye yana"

"kallonta ta rasa yadda zata yi da shi,ta san"

neman abin da zai bakanta mata kawai ya

"ke,kuma ba zai samu ba don ba zata dinga biye"

masa yana sa mata ciwon kai ba. Hai kuwa

bayan ya gama kare mata kallon sai ya bita da

"kulli. ""Wai a nan kika kwana ne? Duk me ya yi"

"zafi?"" Ko motsi ba ta yi ba bare alamar zata"

"tanka,sai ya kada kai ya juya. ""Sai ki tashi"

"haka,ki yi wanka ki dan gyara gurin kara a yi"

baki

"su yi miki kallon kazama ki daga bakin kura""."

Haba wasu hawaye masu radadi suka tunludo

"mata,ba ta iya hadiyewa sai da ta ce. ""Abdul"

"aniyarka ta bi ka"". Ko a jikinsa don yana"

dariya

"ya fice,ta dafe kai a wajen tana maimaita."

"""Innalillahi wa inna illahi raji'un"" Ta yi"

kukanta ya

"ishe ta, sannan ta bai wa kanta hakuri ta tashi"

ta

"gyara falon,sannan ta fada wanka a gurguje"

don

ta dan fara jin hayaniya a cikin gidan. Ta

shirya

"da shigar turawa,ruwan kasar wando wanda ya"

fito da kirarta da farar vest saboda zafin da ke

gari duk da na'urar sanyaya daki ta wadata a

"gidan,amma ji ta ke komai ya yi mata nauyi da"

"zafi,kamar yadda zuciyarta ta ke.. Ta saki"

ranta

ta kwashi abinci don ta tabbatar babu ruwan

abdullahi da abin da yunwa gauraye da bacin rai

"za su haifar mata,ita kadai wannan asarar"

data

shafa. Cikin kayan da ya zube mata a kicin ta

"tarar da abin da ta fiye so,wato yellow peach. Ta"

balle gwangwani biyu a faranti ta koma falo

zamanta ke da wuya aka kwankwasa mata kofar

"falo,haba gabanta ya yi mummunan faduwa"

don

"ta yi tsammanin dan hayaniyarta ne, tunda"

tasan'yan gidansu babu mai zuwa mata a

wannan ranar. Sai da ta leke ta tagar kicin ta

ga

wasu bakin mata biyu sannan hankalinta ya dan

"kwanta,sai da ta koma mazauninta ta zauna ta"

dauki farantin peach dinta ta tsiro da cokali ta

kai baki sannan ta yi izinin a shigo. Sadiya da

"Hibdatu ne, an kullo tsegumi an taho,amma"

daga

tsomo kafarsu numfashinsu ya so ya dauke

"saboda haduwar falon,sai wani kamshi da sanyi"

mai rahama ke dukan mutum. A kasaice kamar

"yadda ya zame mata dabi'a ta ce. ""Ku shigo""."

Sadiya dai don da kunya ne ace ta koma amma

tana dora ido akan fatima sai ta ji gaba daya

falon ya fara zagaywa da ita.amarya Abu Turab

ke nan? Sadiya da gama tsinkewa don tasan

"mijinta dama can ba sauki,bare ya sami wannan"

'yar mai kama da gwal. Ko hindatu ta ji babu

dadi game da amaryar Abu turab ba zai wuce na

"kasaita da rashin kulawarta ba, sai kuma"

ledojin

abincin da ke gabanta wanda a arharsa da

matsayin resturant din da aka siyo shi ya haura

duba uku.kudin cefane su na kwana biyu a karin

kumallon mace daya! Turkashi! Da gaske

matsayin mace biyu ta ke amsawa... Ko ma ta

haura. Su suka yiwa kansu wajen zama suna mai

"fuskartarta,sannan ta sami damar matsawa a"

"yangance ta ce. ""Ina kwananku?"" Hindatu ce"

ta yi

"kokarin amsawa da murya a bude,amma sadiya"

kusan a ciki ta amsa ta kuma kasa sake daga ido

ta dubi fatima. Sai da fatima ta ci peach yanka

biyu sannan ta dire faranti ta mike cikin yauki

"tana cewa ""Bari na kawo muku ruwa"". Da sauri"

"hindatu ta ce. ""A'a mu fa yan gida ne ba sai"

kin

"ba mu komai ba"". Ba tare da fatima ta dakata"

"ba,"

ta ce

"1 Like React Report May 14, 2015"

Amierah S-Man

Zuciya d kwanji

"35) ""To'yan gida ba za a karrama ku ba, ina"

"zuwa"". Ta zuba lemon mangwaro biyu a dogon"

"farnti,yellow peach biyu da sosa ruwa faro da"

tambulan biyu da kuma choculate cake guda

biyu. Ta kawo musu ta ja wa kowace coffee table

"a ganata,ta bude musu lemo,sannan ta zazzage"

"musu peach ta yi musu bismillah,sannan ta koma"

nata muhallin. Ko kallon kayan sadiya ba ta yi

"ba, sai Hindatu ce ta dauki lemon ta kurba"

"sannan ta dube ta ta ce. ""Abu Turab ne ya"

zubar

"da ladansa bai gabatar da mu ga juna ba, shi ne"

muka yi karambanin zuwa inda kike tunda ke ba

ki nemo mu ba. Ga yaya babba ( ta nuna sadiya)

"ita uwargidanki,sai ni Hindatu na bi bayanta. A"

"kasaice fatima ta juyo ta dube su, da dokin ta"

ga

matan da suka fita.ta yi tsaki a zuci kawai ta

"kawar da kai,haushinsu kuma ya kara turnuke"

"mata zuciya,daman tunda ya ce matansa sun fi"

"ta taji gaba daya ta tasne su, ashe ma burgar"

"banza ce ko kama kafarta ba su yi ba, duk da shi"

ya ce ba a nan ta ke ba. To amma abu a duhu

wa zai dorar? Da kyar ta hadiye tsanar da ta yi

musu ta amsa batun da suka zo mata da shi a

"hagunce. ""Wane ne kuma kuma abu turab"

Kamar

"a kufule sadiya ta ce. ""Angonki!"" Fatima ta"

kawar

"da kai tana kara hadiye takaicinta, kamar dole"

ta

"ce. ""Au,ban sanshi da wannan sunan ba""."

"""Amma"

"ba ku dade tare ba?"" Tamabayar da sadiya ta yi"

"mata ke nan,ita kuma sai ta juyo kawai tana"

kallonta tana ta faman kuma sai ta juyo

kokawa

"da zuciyarta wadda ke karanta,don ta buge da"

kai

"peach a baki ta taune ta hadiye,sannan ta dubi"

"talabijin ta ce. ""Ba ki da labari ke nan?"" A dan"

"zafafe sadiya ta ce. ""Kusan haka ne, don an yi"

abin ne cikin gaggawa kinga zan iya tsammanin

"akwai wani 'yar burum burum"". Duk da fatima"

ba

"ta iya bakar magana ba,sai ta ji yau kamar an"

"kimsa mata,don sadiya na rufe baki ta amsa."

"""To"

ko ma dai odiyo diyo ne ya fice wai tunda ya

"zama dahir,ko a mafarki dai muka hadu"

haduwar

"ta yi amfani tunda mun auri juna,auren da na"

tabbar a yanzu ya fice gaibu. Sadiya ta fara

"murmushin da ya fitar da sauti,ta ce. ""Dama ga"

"abu turab da aure aure,shi har kwallon kafa"

aura

"yake jiya raba dare ya yi yana kallon kwallo,na"

yi

"mamakin yadda kika saki wannan damar""."

"Maganar ta daki zuciyar fatima,amana nan da"

"nan sai ta fanshe. ""Babu wani abin mamaki"

akan

aurensa don in dai namiji bai yi sa'ar auren

farko

"ba to ya gama garari,ba kwallon kafa ba har"

"kwallon ciki ma wataran sai ki ga ya aura,abin"

da

"kuma zai fi saukin yi min ciwo ke nan,wato akan"

gazarwa da zan janyo a cika min gida da

"kishiyoyi"". Sadiya ta yi masifar kuluwa tamkar"

ba

"ita ta fara zunguro fitinar ba,bacin ranta ya"

kasa

"boyuwa tana numfarshi ta ce. ""Wata kishiyar ai"

"suna ta tara,kishiyar da zata yi asarar daren"

farko ai maraba da ita. Wallahi ni a kawo min

"dozen ma"" Numfashin fatima ya yi kamar ya"

"dauke saboda takaici,ta rasa amsar da zata ba"

"wa sadiya ta fashe,sai gaba daya ta tsani kanta"

"ta kara tsanar Abdullahi,wannan babu tantama"

shi ya janyo mata wannan koma bayan da ya ce

sai ta tare a gidansa

"2 Like React Report May 14, 2015"

Amierah S-Man

Zuciya d kwanji

36) Ta dinga gyada kai tsawon

"lokaci,sannan ta ajiye numfashi ta dubi"

"Hindatu,ta ce. ""Ita ta gabatar min da kanta,ke"

kin

"yi shiru ko rakiya kika yi mata?"" Hindatu ta"

bude

"ido ta ce. ""A kan me? Igiyarta daban tawa"

"daban,"

don duk abin da ta fada ita kadai ta

"sanshi,don ni"

"ban san shi ba Ni umarni na bi,don maigidan"

"ya ce na zo mu gaisa,na kuma sauke nauyi """

Fatima ta cije lebe cikin girgiza kai ta tare ta.

"""Kwarai kin sauke nauyi,ina kuma godiya ba"

tare

da na hakkake taki gabatarwar ba tunda tare

na

ganku. Ni ban shigo gidan nan don wata ta

dinga zuwa tana min haushi ba saboda duk

fadin

"dangima babu karnuka "" ""To mun gode""."

Abin

"da hindatu ta ce ke nan, kuma salin'anlin ta"

shi

"da lemonta a hannu ta fice,sai sadiya ma ta ke"

mata baya bayan ta saki katon tsaki tana

habaice

habaice. Fatima ta bi su da kallo kanta na wani

"irin ciwo saboda bacin rai,yau fa ake yinta,rana"

"zafi inuwa kuna,auren sati biyu mijin babu dadi"

"matansa babu dadi,ita zara'u ina ta tsoma"

ranta?

*********** *********** ********* Karfe

biyar

abdullahi ya dawo gidansa ya zauna a falonsa

da

gajiya yana kallon wasan kwallo cikin rabe

"hankali,fiye ma da uku. Amarya fatima ta debi"

"kason mutum biyu,kwallaon kafa daya,ga kuma"

iyayen gida wadanda mintuna talatin ke nan

da

shigowarsa babu wadda ta shigo masa ko sannu

bare ta taushe shi game da radadin gajiyar

zuciya

da ta jikin da ya kwaso. Ya gaji ya fara kiran

wayar sadiya amma har sau uku tana kin

"dagawa,sai ya haura ya kira hindau,ita kuma"

tana

"dagawa don rainin hankali sai cewa ta yi. """

"Lafiya?"" Takaici ya rufe shi,a zafafe ya ce."

"""Wacce banzar tambaya ce wannan hindatu?"

Kuna jina na dawo amma don raini a rasa me

"bullowa ta gaishe ni?"" Kawai sai ta kashe wayar"

"tana tsaki. Ashe ya ji ta, ya sauke wayar cike da"

"mamakin mata, mata fa shaidanu ne, kalau fa"

ya

"bar su,amma yanzu ya je ya dawo duk sun wani"

"birkice masa,wai ma har hindatu da yake da"

garantin ba ta salwantar da mutuncinsa da

kimarsa. Sai ya ji gaba daya ransa ya kara

"mugun baci,kawai sai ya tashi ya sa wa kofarsa"

makulli don ma kar wata ta yi gigin kwaso kafa

ta zo masa ya sauke mata nasa rashin

"mutumcin,don gaba daya haushinsu yake ji. Ya"

"tara lemuka masu sanyi a gabansa,idan ya dure"

wannan gwangwani ya dauki wannan yana

kallon

wasan kwallo wai duk don zuciyarsa ta sami

"sanyi,amma kamar turi don ba abin da ta ke"

"muradi ke nan ba. Fatima ta ke son gani,amma"

"babu wani dalili na ganinta a yanzu,idan ba"

yana

son karyawa kansa tsari wanda Zai iya rushe

masa wata katanga a cikin ginin da ya yi nisa a

cikinsa ba. Haka ya dinga daurewa har daba da

magriba ya yi wanka ya shirya cikin kananan

kaya wadanda suka fito da kuruciyarsa

"fili,tana"

"kuma matukar yi masda kyau,ya fes turaren"

five

eleven sannan ya kullo kofa ya fice masallaci.

Sai

da ya sallaci isha'I sannan ya nemi gida dauke

"da take away din amarya,zuxiyarsa cike da"

sakar

yadda za su bullowa juna yau. Yana shiga ya yi

karo da sadiya a tsakar gidan wanda babu

dalilin

"ganinta a tsakar gidan a wannan lokaci,yasan"

"kwannan zancen,ta fito ne kawai don ta sanya"

masa ido kawai ta sami abin yi masa korafi su

hau rigima. Ya share kamar bai san Allah ya

tsire

"ba,idanunta kan ledar hannunsa ya shiga"

kwankwasa kofar fatima. Ya shafe fiye da

mintina

goma yana bugun kofar ba tare da jin a ransa

zai

gajiya ba idan ya shafe sama da awa daya yana

yi. Can sai gata ta zo ta bude tana sanye da

after

"dress,fuskarta na bayyana shirin ko ta"

"kwana,ta"

koma baya zuwa tsakiyar dakin tana sauraron

karasowarsa. Ta gama zuwa wuya ba zata yarda

Abdullahi ya jona mata ciwon zuciya babu dalili

ba. Ya karaso ya ajiye ledar kan table sannan

ya

"zuba mata ido,tun ma kafin ya yi magana ta"

riga

"shi. ""Ka ga malam! Matukar rashin arziki ka"

"kwaso ka shigo min ka juya da takunka,don ni"

ma na shaki kamarsa ina ji kum a raina ba zata

"yi mana kyau ba "" Ya dan yi galala yana"

"kallonta cikin murmushi,sannan ya taussa"

harshe

"ya ce. ""A'a,arzikin na kwaso,ba ni hanya na"

"wuce,amma ke ma ki shaki irinsa"". Ta yarfe"

"hannu ta wuce kujera ta zauna tana tsaki,ya"

kara

rage nisan da ke tsakaninsu idanunsa a

"kanta,sai"

huci ta ke kamar wadda ya kashewa dan fari. Ya

dora kafa kan table yana ci gaba da kare mata

"kallo,sannan cikin muryar zolaya ya ce. "" Sannu"

"2 Like React Report May 14, 2015"

Amierah S-Man

Zuciya d kwanji

".37) Ta kada ido ta kawar da kai, ya kuma"

"zungurota da sassaukar murya. ""Ki daina fushi"

"fatima,sam ba ya yi miki kyau wallahi Ina"

"ganin kamar ba ki saba ba "" Nan da nan ta"

"kara cika,ta ce. ""Ai na ga wadanda fushin ke"

yiwa

kyau wadanda babu tantama ka dace da su sun

"dace da kai.idan kana na ka muzguna min,idan"

"ba ka nan ka turo min wakilai,sai dai na yi"

mamaki da ba ka hada wannan kwangilar da su

"ba,ko kuwa kyashin ba su ba nasu kason kake?"

Na ga suna yi min gorin asarar daren farko

alhalin dama can na gaibu ne Ya ji kamar

ta

"dabawa zuciyarsa adda,wato rashin mutumci su"

sadiya suka zo suka yi mata? Ya ji ciwon abin

fiye da duk wani bacin rai da ya riske shi a 'yan

"watannin da suka shude,sai dai juriyarsa ta"

"hanawa fuskarsa bayyanawa,amma muryarsa a"

"sanyaye ya amsa. ""Ni ban turo kowa ba,duk"

kuma abin da wani ya yi ra'ayin kansa ne ba

nawa ba in kuma kishi ne ya sa ki fadar

"hakan,to ki tuna.babu wani dalili da zai sa ki yi"

"kishin matana"". Sanyin muryarsa ya sa ta dan"

"dube shi a tsanake,sannan ta kawar da kai ba"

tare da ta tsira da wani abu a cikin kallon nasa

"ba. ""Ba na bukatar ka yarda da ni,don haka ba"

zan yi kokari goge duk wani fenti da zuciyarka

ta

kagi goga min ba. Amma kishin matanka Allah ya

"tsare ni,sai dai abin da nake musu ya fi kishi,"

"domin kuwa ba na kaunarsu,na kuma raina"

musu

wayo fiye da yadda kuka raina nawa kai da su.

"Ya kara tausasa murya ya ce. ""Yanzu don Allah"

me ya kawo wannan maganar? Ko don kawai na

"yi raddi ki ce na miki rashin arziki?"" A kufule"

ta

"amsa. ""Idan ma zaka yi rashin arzikin ai na"

shirya masa Kai ban ki ba fa a ce a yau na

bar

"gidan nan ba, domin DUHUNSA ya fara munan a"

"idona"". Ba tare da wata shakka ba, ya ce. ""Ga"

shi

"kuma kin yi masa shiga sojan badakkare"". Ta"

"yunkuro a birkice ta ce. ""Me kake nufi?"" Da"

karfin

"gwiwa ya share tambayar tata, cikin kara"

"kyautata murya ya ce. ""Ya ya kadaici? Na damu"

da yawa da kadaicin da nake hasashen kin wuni

"cikinsa,sai komai ya gundure ni a office na"

matsu

na zama abokin dauke kewa gare ki ko da hakan

"na nufin ba zan miki abin burgewa ba"". Ta yi"

"sukuti kirjinta na bugawa tun kafin ta shirya,ta"

"kalubalance shi. ""Wannan dogon zancen

Please Login or Register in order to submit comment