gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading UCIYA DA KWANJI Saki Mai Daci 1 By Amierah S man Chapter 2 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

komai domin ta bata masa, wanda tana"

yin hakan ne domin ya ji zafi ya saki aurenta

kamar yadda ta ke iya keta idonsa ta fada masa.

"""Ba a nemi amincewa ta ba kafin a hada mu"

"rayuwa tare, saboda haka har abada kada ka"

saka ran zaka mallaki karamar kofa ko kamar ta

"allura daga kofofin zuciyata.Raina ba ya sonka,"

"kuma ni mutum ce da ban iya boye kiyayya ba""m"

Bai taba daukar wani mataki akan fatima ba ko

"da na zare ido ne, sai rarrashi da lallabawa tare"

da yi mata manya manyan kyauta masu motsa

"zuciya.gwala gwale,kadarori, manya kudade ita"

"da duk wanda ya rabeta,amma fatima kamar"

"dutse,zata karba ta kalmashe,idan ta ga dama ko"

godiya ba zata yi masa ba. A haka suka yi

"rayuwar,sai su kwashi watanni ba su hada"

"shimfida ba, wanda a nan ma tana kara tafiya da"

imaninsa ya ci gaba da kwadayin zaman har

"abada tare da ita,saboda baiwar da ta ke da ita"

na kasancewa daga cikin matan da ake kira

sa'ida. Shekarun uku tare sannan ta sami ciki

wanda ya bare a lokacin da yake shiga watanin

"hudu,cikin shekarun ukun da suka kuma biyu"

"bayan shidda ke nan da aurensu,ta jera bari sau"

"hudu,har waje ya fita da ita,amma lamarin ya ci"

"tura.wannan ya sa ta kara tsanarsa,musamman"

idan yana lallabata da cewa rabo ne ya kaddara

"aurensu,takan ce ""Rabon wahala ba, tunda akalla"

"ko dan tsako na kasa haifa"". Bayan wannan aikin"

da aka yi mata kawai sai ta dinga munafintarsa

"tana karbar allurar hana daukar ciki,saboda yadda"

"ta tsani mutuwarta haka ta tsani haihuwa da shi,"

saboda ta rayawa ranta haihuwarta zata tilasta

mata zaman gidansa Shakaru da suka yi goma

"tare,bai zama wani sabon abu da zai hana a"

"yanzka kaza ba, don babu abin da ya"

"canja,fatima ba ta fasa nuna masa iyakarsa"

"ba,shi kuma ko kwayar zarra bai rage sonta ba,"

duk da ta dalilinta ya sami hawan jini. Kai ko a

murnar cikar su shekara goma da aure wani

katoton gidan gonarsa ya mallaka mata wanda

kudinsa ya kai miliyo ashirin. Kuma wannan ne

"ya tashi mahaifiyarsa a tsaye wajen farraka su,"

don ta hakikance Alh zai iya mallakawa fatima

"dukkan dukiyarta da ya mallaka,ko da kuwa yin"

hakan ba zai amfane shi da komai ba. Ta dinga

ziyartar bokaye da malaman surkulle amma shiru

"babu labari,dole ta koma wa gaskiya,ta sa aka"

dinga yi mata rokon Allah ana neman idan akwai

alkhairi ya shirya fatima idan babu ya farraka

"auren. Sai da kura ta yi kamar ta lafa,ku san Alh"

bai taba mallakar fatima irin yadda ya mallake ta

"a wannan shekarar,kai kamar ma ita ce shekarar"

"zumarsu,wadda bai dandana a farkon aurensu ba."

Fatima kan yi hira da shi ba tare da bakar

"magana ba,sannan takan yi masa rakiya idan"

"tafiya ta same shi, sannan uwa - uba ta daina"

gudunsa a shimfida duk lokacin da ya bukace ta.

"Allah mai yadda ya so, ranar wata alhamis da"

sasanyar la'asar ta shirya ta fice bikin kanwar

wata kawarta. A lokacin ne wasu miyagun

ma'aikatan gidan suka sami damar shiga dakin

Alh ta hanyar amfani da (master key) suka

kwashe wasu makudan kuadaden waje da ya

shigo da su safiyar ranar. Ya dawo karfe biyar zai

"fita da kudin,amma sama ko kasa ya nemi kudin"

"ya rasa,ya shafa a gidan babu fatima.Haba! Sai"

"hankalinsa ya yi mugun tashi,ya tabbatar kudin"

"nan daukarsu aka yi,ya hada dukkan ma'akatan"

gidan ya fara surfar su da masifa. A karshe ya

tabbatar musu in dai ba su fito masa da kudinsa.

Ba sai ya salwantar da rayuwarsu. Ya sallame su

kaca kaca bayan ya sanya masu gadi sun

garkame kofar gidan tunda sun tabbatar masa

"babu wanda ya fita bayan Hajiya,wadda ta tuka"

mota da kanta. Bai ko iya halarta sallar magariba

"da isha'I ba,yana ta faman safa da marwa cikin"

"yanayn tashin h [truncated by WhatsApp]11) Alh sannu da gida"". Ya juyo ya dube ta"

"cikin matsanancin bacin rai,cikin tsawa ya ce."

"""Fatima daga ina kike?"" Ta yi saurin juyowa ta"

"dube shi cikin dukan zuciyar mamaki,bacin ran da"

ke fuskarsa ya sa ya kara baki a idonta. Ta ga

kamar babu mutumin da ya kai shi muni a

"duniya,sai ta ga ma babu hujjar da zai mata"

"wannan tsawar ko wannan gizagon,kawai sai ita"

"ma ta taso masa cikin bala'I. ""Ban sani ba,idan"

"ka halicce ni ne sai ka dauki mataki a kaina""."

"Haba! Ta kara hada masa bacin rai, Hankalinsa"

"ba ya tare da shi ya ce. ""Au haka kika ce? To"

zaman uban wa kike yi a cikin gidan tunda ban

"isa na yi iko da ke ba?"" Ita ma cikin tsawa ta ce"

"masa. ""Kai ne ka fi kowa sani,zaman kaddara"

nake ba zaman uban wani ba Ko ka manta ne

ba so da kauna ya kawo ni gidan nan ba.balle

"ban wani ya dinga yi min wannan ihun"". Jikin Alh"

"ya dinga bari kamar mazari, gaba daya fatima ta"

"sauya a idonsa da zuciyarsa,ya ga ma gaba daya"

ba ta da wani amfani a wajensa ya fara mata

"bala'I. ""Ke bana son isakance da rashin tarbiyyar"

da kika saba kin ji! Matukar ba zaki zauna a

"gidan nan kamar ko wace matar ba, to tun wuri"

"ki san inda dare ya yi miki,don ba ki da wani"

"amfani a wajena,kullum ki dinga ficewa kina bar"

wa ma'aikata gida kina janyo min asara ke dai

"ba ki da wani amfani wallahi"". Ta tare shi cikin"

"hawaye saboda tana da saukin kuka,ba domin"

"nadama ba. ""Ai ni ban taba daukar aurenka wani"

"abin a zo a gani ba,balle na yi abin da matan"

aure suke Sai ka daina yaudarar kanka da zan

"yi wani abu da zai yiwa ranka dadi "" Kai"

"tsaye ya amsa ta. ""To shi ke nan,tafi gidanku na"

"sake ki saki UKU, don kin san ni ma na mayar da"

"soyayyarkitarihi don iyayenki bace min da gani!"""

"Shi ke nan, da shigowar fatima da saki nata ba a"

"fi mintina biyar ba,Alh ya haye sama ya barta nan"

"tana kuka matsannanci, sakin ya girgizata"

matuka! Alh ya saketa a lokacin da ta daina

"sha'awar barin gidansa,ma'ana ta yarda karasa"

rayuwa da shi duk da ba ta jin kaunar sa cikin

"ranta. Ita ma ba ta jima a wajen ba ta fice,tunda"

"dama ko mayafi ba ta sauke ba, makullin motar"

"ma yana hannunta,sai gida wai an daki kare a ka"

"kawu ya sami bakin labari, amma bai gaskata"

"fatima ba,sai ya kira Alh a waya,wanda har"

wannan lokacin yana kulle a dakinsa cikin mugun

"bacin rai. "". Da gaske ne ka yiwa matarka saki"

"uku sulaiman? ""Inji kawu. Ba tare da lissafin abin"

"da zai tafi ya dawo ba,Alh ya ce. ""Kwarai da"

"gaske,ku zo ku kwashe kayanta,ba na kaunar duk"

"wani abu da zai tuna min na rayu da ita,mts!"" Ya"

kife wayar cikin bacin rai. Wannan ne ya kashe

bakin tsanyar kawu dangane da fadan da ya

tanadarwa fatima. Ba sai ya bincika ba yasan Alh

ya gama ganin damarsa bai kuma dauke shi a

bakin kamai ba tunda ya iya keta idonsa ya yi

masa wannan cin fuskar. Kawu ya sauke ido akan

"fatima,idonsa cike da kwallah ya ce. ""Tashi ki"

"shiga gida fatima,Allah ya sa hakan ne alhairi"

"gare ku gaba daya"". Washegari ranar Alh ya fito"

tafiya sallar asuba ya tarar da jakar kudinsa a

"korido,ya dauka ya shigar falo sannan ya fice"

masallaci. Har aka idar da sallah cikin hawaye

"yake, sai da ya dawo gida ya dinga mai dalilin"

kuka kamar wanda aka yiwa albishir din ranar

mutuwa.zuciya da kwanji

12) Ya tabbatar Allah ne ya jarrabe shi akan

"fatima,daukar kudin nan ba ya nufin komai sai"

"rabuwarsa da fatima,wadda a zahiri da badini ta"

fi karfin wadannan kudin a wajensa. Lamarin

"kamar alamara kamar mafarki,ya rabu da"

"fatima,rabuwa mai kama da alamara da ya ya zai"

karbi wannan kaddarar?. Kawu mutum ne mai

"zuciya kwarai,da sanyin safiya ya turo a tattare"

"masa kayan fatima,Alh ya yi tsalle ya ce bai san"

"wannan zancen ba,har sai da ta kai sun kira"

kawu a waya sun sanar da shi. A fusace ya kira

"wayar Alh ya ce masa. ""Ban gane abin da kake"

"nufi ba?"" Kawai sai Alh ya sa kuka yana cewa"

"""Kawu ayi min rai,a binciki malamai ko akwai"

"gyara cikin lamarinmu, wallahi kawu cikin mayen"

"bacin rai na yi sakin nan, sam hankalina ba ya"

"tare da ni "" A kufule kawu ya amsa. ""Shi ke"

"nan,yanzu ka bar su su debi kayan in yaso idan"

malam sun budo maka kofar halaccin ci gaba da

"zamanku tare sai mu dawo da kayan"". Bai jira"

cewar Alh ba ya kashe wayar dole Alh ya barsu

"suka kwashe kayan fatima tas, yayin da kamar"

sun bude kofar kukansa da bakin cikin sa.

Rayuwa ta yi kunci gare shi matuka. A wajen

"fatima ma haka lamarin yake,ranar da aka yi"

sakin ba ta iya runtsa bacci ba. A zatonta zafinb

kalmar da ya hada mata da sakin ce ta ke

"damunta wato. ""Don ki san nima naE mayar da"

soyayyarki mafarki Don iyayenki bace min da

"gani"". A hankali sai ta gane ba kalamar ce ta ke"

"son ta tashi hankalita ba,akwai batutuwa da"

"dama, kuma na shekaru da yawa.yadda ta jima"

tana taka rawar da ta ke so a gida da rayuwar

Alh shi kuma yana saka mata da tarin kauna da

farantawa me yasa ya dawo daga rakiyarta

yanzu? Kuma zata kuma samun namiji mai nuna

mata kauna kamar Alh kuwa? Wadannan lissafe

lisafe ba su barta haka ba sai da suka yi tasiri

"manna mata kaunar Alh,ta dinga yarda wakanta"

lallai ta tafka asarar masoyi. Ta rasa sukuni

"kwata kwata,hakki ne kawai yake dawainiya da"

"fatima,hakki irin na mai laifi cikin ma'auratan da"

suka sami kansu tsakiyar kaifin almakashin saki

uku! Duk da haka ba za a ce fatima ta kai Alh

"damuwa ba, tunda ba ta yi wani yunkurin ba,"

"bayan na fatan ina ma jiya ta dawo yau, ta mayar"

wa da alh raddin soyayyarsa? Ba ta yarda ta yi

zurfi cikin kaunar Alh ba sai da ya nemeta da

tayin yadda za su mayar da aurensu tare da

"bayyana mata fatawar da ta bayyana cewa,saki"

"uku lokaci daya sakin bidi'a ne,kuma a matsayin"

saki daya yake. Sai kawai ta bayar da kai bori ya

"hau,ta kuma iya jure tunkarar kawu da"

"maganar,Allah ya sa kawu ba mai karamin sani"

"ba ne, sai ya dubeta da kyau cikin nazarin ta"

"sosai, sannan ya ce. ""To ni ban gamsu ba,ba"

kuma na karyata fatawar da ya kawo ba ne. Sam!

Ni hankalina ya fi kwanciya ga wadda ta haramta

aurenku har sai kin auri wani namijin kin tare da

shi. Wadda wannan fatawar jamhurun malamai

suka tafi akai kar ki kara kawo min irin wannan

"maganar,ban son rudu. Dole ta karkade zani ta"

mike cikin hawaye. Daga nan ne kuma cira kafa

ita da Alh ta bin hanyar duk suka sa zata mayar

"musu da juna,kawu na dago logarsu saboda farin"

sanin da ya yiwa fatima da irin mijin da ayke

zaton zata zabawa kanta. Sau hudu tana kawo

"masa samari zata aura,idan kawu ya saka su a"

kwana da tambayoyi sai ya dago su. Don haka

"ya tattara dukkan lurarsa akan fatima,ya alkwarta"

wa ransa sai iyakar inda karfinsa ya kare..Zuciya D Kwanji

13) Abdullahi ya hadu da Alh ne a

wani tsadadden asibiti lokacin da ya je dubo wani

"abokinsa da aka yiwa aikin kaba,shi kuma Alh ya"

"je bisa larurarsa ta hawan jini,wadda ta matsa"

masa yanzu. Tun da Alh ya ga Abdullahi ya dora

"dukkan burinsa a kansa,don ya tabbatar in dai"

Abdullahi ne kawu ba zai taba dago yawarsu ba

tunda bai rasa komai da ake bukata kafin a ba

wa mutum aure ba. Ya dinga ribatar Abdullahi

"har ya samu suka kebe,sannan ya koro masa"

"bayani. ""Dan halak ke nan, shekaran jiyan nan ka"

"fado min a rai,dama cikin satin nan nake son na"

"neme ka"". Cikin fuskar rashin fahimta Abdullahi"

"ya ce,"" Allah sarki,ina fatan kalau?"" Fuskar Alh na"

"bayyana jimami ya rangwada kai ya ce. ""To"

"lafiyar mahaukaci ba,wani aikin lada da ceton rai"

"nake son baka,don a duniya ba ni da mai yi min"

"sai kai"". Kallonsa kawai Abdullahi yake cikin"

"rashin fahimta,har sai da ya dure sanan ya kuma"

"dorawa. ""Allah ne mai saka soyayya a zukatan"

"bayinsa Abdul,ya jarrabe ni da son mace daya a"

"duniya,wato matata. Wani tsautsayi yasa na yi"

mata saki uku. To yanzu duniyar ta yi min

"kunci,na gane ba zan iya rayuwa ba tare da ita"

ba Shi ne nake rokon ka tainaka ka halarta

"min ita"". Kallon Alh kawai Abdullahi yake yana"

sauraron wannan rainin hankali da na wayo. Jima

kafin ya shawo kan fushin zuciyarsa sannan ya yi

"magana mai ma'ana. ""Me yasa sai ni zan yi"

"maka wannan aikin?"" Yana rufe baki Alh ya"

"amsa. "" Saboda zumuncin da ke tsakaninmu,"

nasan ba zaka so akan wannan lafiyata ta

salwanta ba Kawunta ne ya matsa matukar bai

"ga mutum mai kamata irin ta gidanku ba,ba zai"

"bayar da aurenta ba, don ya sanya mana ido....."

Ni kuma wallahi ba zan iya hakura da ita ba....

"Sai inda karfina ya kare wallahi "" Abdullahi ya"

"tare shi da cewa. ""Ba ka ganin hakan zai zubar"

"da martabar gidanmu. ?"" Alh ma ya tare shi"

"kamar zai yi kuka. ""Ka fansar Abdullahi,ka ceci"

raina.wallahi na yi maka alkwarin biyanka

makudan kudade Zan daga darajarka a garin

"nan sai ka shiga sahun attajirai"". Abdullahi ya"

"jima yana tunani,sannan ya dube shi da kyau ya"

"ce. ""Ka fa san halin mahaifa,babu yadda za'a yi"

na kawo matar da ta girme min da zummar aure

bai nemi ba'asi ba. Na kuma san duk wahala dole

"matarka ta girme ni"". Cikin doki Alh ya ce. ""Au ba"

"ka santa ba?"" Kallonsa kawai abdullahi ya yi cike"

da takaici. To ta wacce hanyar zai san matar

wani? Musamman alh kawai don yana abokin

"wansa? Sai ya girgiza kai kawai,Alh ya ce."

"""Shekarunta talatin da biyu,kuma da yake tana da"

kyan jiki zaka zaci ba ta fi shekaru ashirin da

"biyar ba"".Zuciya d kwanji"

.14) Abdullahi ya kara jan fasali sannan ya ce.

"""Da yardarta a ciki?"" Alh ya yi saurin gyada kai."

"""Eh,idan ma ka amince sai na gabatar maka da"

"ita kafin ku fara magana"". Kai tsaye Abdullahi ya"

"amsa. ""Ti na amince,Allah ya tabbatar maka da"

"ita kafin ku fara magana"". Kai tsaye Abdullahi ya"

"amsa. ""To na amince,Allah ya tabbatar mana da"

"alhairi"". Farin cikin Alh ya tsananta,kawai sai ya"

rungume Abdullahi yana godiya. A nan suka

"shirya haduwa da yammaci a gidan namun daji,a"

"haduwar tsu kuma suk jaddada kudirinsu,sannan"

suka yi musanyar lambar waya tare da shirya a

washe garin ranar abdullahi zai fara zuwa tadi.

***************** **************** Washe gari da

"yamma bayan sallar la'asar,fatima na kwance kan"

"kujera 3 sitter,a kasalce ta ke kwarai,kasal irin"

wadda ke tasowa daga zuciya sakamakon bacin

"rai da damuwa. Ta sanar da mutum gidan cewa,"

tana da bako kowa murna yake yana dokin ganin

"bakon cikin zakuwa,wanda ta tabbatar da biyu"

suke yi... Kowa sai hidimar tarensa yake daga

"kan masu aiki akan abincinsa,har jama'ar gidan"

masu murna da doki. Wannan ya sa fargabarta ta

kara tsananta Tasan kawu sarai akwai dora

ido. Dazun da safe Abdullahi ya yi mata waya ya

"ce, karfe uku zai zo,amma ga shi hudu da rabi"

"abu labarinsa,sai bacin ranta ya karu,ta kuma"

kara jin tsanar abdullahi cikin ranta.Ta tsani

"mutumin da ba ya daukarta da muhimmanci,ko"

kuma ba ya girmamata. Ta lura da abdullahi

mugun dan tsaurin ido ne Ya iya dizga

mutane. To idan ma halinsa ne dizga mutane ai

"tana jin ta fi karfin hakan,don ba ta rasa duk"

"wani abu da ke janye so da biyayya ba,ko ba"

"domin Allah ba. Tana da kyau,kuma tana da"

"kudi,sannan ta iya takunta. Da damuwar ta isheta"

sai ta janyo waya ta hau facebuk domin debe

"kewa,tsawon mintina goma,sai ga safiya kanwar"

"momi matar kawuta shigo da karadinta ""Anti"

wannan yayan namu zai tilasta ni kuma kwannan

"gidan don ba zan wuce ba sai na ganshi,don Allah"

ki yi masa waya ya karaso mu gaisa. Fatima ta

"dago ta dube ta, sai ta rasa ansar da zata"

"bata,akan me zata yi masa waya,kuma ta ce"

masa me? Sai kawai ta yi shagare tana kallonta

"cikin zancen zuci,safiyya ta bude baki tana"

"kallonta ta ce. ""Anty Wannan mutuwar ido"

"biyun fa? Duk yayan ne da wannan aikin?"" Fatima"

ta yi murmushin karfin halin da ya yi kama da na

"shauki, sannan ta juya baya ba tare da ta tanka"

"ba, safiyya ta mike ta ita tana tuntsura mata"

"dariya. Sai shidda saura abdullahi ya iso,ya yi"

kiran wayarta tana ta faman kallon wayar sai da

"ta katse ya sake kira, sannan ta daga a kule,kum"

"ba ta tanka ba. Muryarsa a sake ya ce. ""Fatima"

"na iso"". Haushin gatsa sunanta da ya yi kai"

"tsayeya sa ta taso masa da bala'I. ""To me zan yi"

maka? Kane nawa karfe nawa ka ce min zaka

"zo?"" Ya yi sjiru,sannan ya nisa a zafafe ya ce. ""Ki"

"yi hakuri,amma don Allah ki dinga yi min"

"uzuri,bana son masifa wallahi"". Sai ta saki baki"

"cikin al'ajabi,ta ma rasa abin da zata ce"

"masa,koda yake ko tana da abin fadar bai ba ta"

"damar fadar ba, tunda ya kashe wayar......."

Wannan wanne irin dan zafin kai Alh ya hadata

da shi? Duk mazan da ya kawo mata a bayan

"masu ladabi ne,amma wannan yana jin kansa shi"

wata tsiyar ne.

"Like React Report May 14, 2015"

Amierah S-Man

zuciya d kwanji

15) Ta fi mintina ashirin tana faman sacewa

tare da tunanin turbar da zata bi da wannan dan

hayaniya har ta kai ga zargin kanta.Ta gama

babu wani dalilin da zai sa ta dinga damuwa da

"zafin kansa,ya karaci jaridarsa ya gama. Ta sa"

"baki ta yi kiran safiyya,sai gata a guje,tana zuwa"

"ta ce. ""Ya zo ko Anti?"" Ta yi murmushi,tukunana"

"ta ce. ""Ya zo, sai ki shigo da shi,don na ga"

"alamar kin fi ni dokin ganinsa"". Safiyya na"

"dariya,ta ce. ""A'a bazan fi ki ba anti,ke da"

zazzabi ya kusa tsegumi kawai ke dawainiya da

"ni in ga dai dan talikin nan da ya rikita mana ke""."

"Fatima ta hadiye takaicinta,ta ce. ""Nasan ba zan"

ba mara danki kunya ba shigo da shi sai ki kare

"masa kallo"". Safiyya ta fice fatima na binta da"

"kallo cikin kunar rai,haka kawai ta ji sam ba ta"

kaunar ganinsa. Tana jiyo jama'ar gidan na ta

"kara-kaina a kansa.Da akwai alamun sun yaba,"

can sai ga safiyya da sauran 'yanmatan gidan

"sun shigo,suna mata kaudi. ""A'a Anti kin yo"

wawan kamun ya ya muka ganki haka? Don Allah

"tashi ki canja tsari,don ya gane gidan ya tarar""."

Ta yunkura ta tashi zaune ta rafta tagumi hannu

"biyu tana sauraron cagwadar da suke mata. ""Na"

"rantse Anti yanzu kika yi mijin da ya dace da ke,"

"ko babu kudi akwai kyau da iya taku """

"""Sannan ga fara'a da iya shirya zance kalma"

"bayan kalma "" Irin kalaman yabon Abdullahi da"

"suke ta jero mata ke nan, wadanda suke faranta"

"mata,sannan suka bakanta mata,karbuwar da ya"

yi a gurinsu ne ya faranta mata.tana kuma jin

haushin yabon da suke masa don bai cancanci

"yabon na ko dayua,sai dai babu damar ta"

bayyana. Haka suka yi ta ribatarta sai da ta

"canja shiga,ta yi kyau tamkar ranar walimar"

aurenta. Ta same shi a falon momi durkushe a

"gabanta,kamar zai kwanta mata saboda ladabi."

"Momi na ganinta ta hau zolayarta. ""Kin gaji da"

"jira kika biyo bayansa ko?"" Ta yi murmushi"

"kasaita,ba ta tanka ba ta nemi kujera ta zauna"

tana kallon ikon Allah. Momi ba ta jira cewarsa

"ba,ta juya ga Abdullahi ta ce. ""Ina fatan ka shirya"

"da kyau,wannan yarinyar shan kamshinta ya yi"

"yawa"". Ya kara kan - kan da kai,muryarsa a"

"ladabce, ya ce. ""Na sani momi,a taya mu da"

"addu'a"". Cikin fara momi ta ce. ""Idan Allah ya"

"so,kar ka ji na ce haka,fatima na da saukin kai ga"

"wanda ya iyawa dabi'arta da tarbiyyarta,ina"

tsammatar muku zaman lafiya da saukin fahimtar

"juna,domin dukkanku kun fito daga gidan tarbiya"

"da sanin ya kamata. ""Mun gode"". Kalmar da"

"Abdullahi yake ta maimaitawa ke nan,ya yin da"

fatima ta yi shagare tana kallon momi zuciyarta

cike da tambayoyi.A ina momi tasan

"Abdullahi,kuma dan gidan waye? ""Don Allah ka"

"rike amana,ka ga marainiya ce, nasan kawunta"

ma nasihar da zai yi maka ke nan. To kafin ka

ganshi ma ni na fara yi maka. Ka rike ta amana

don Allah ku zama masu hakuri hat ku fahimci

"juna"". Abin da momi ke ta jaddada masa ke nan,"

"idon fatima a kanta,yayin da kunnuwanta ke"

sauraron Abdullahi cikin ladabi yana amsar

amanar yana kuma tabbatar mata da yarda Allah

ba zasu yi nadamar ba shi aurenta ba. Har cikin

ran fatima ta yarda yana kirari yana dabawa

"kansa wuka nekawai,don bai kamata ya furta ko"

kalma daya a cikin maganar momi ba matukar ba

zai iya toshe kunnensa daga saurare ba.

"Tsawomn wasu mintuna,sannan momi ta yi musu"

"iznin su tashi.Abdullahi ya fara mikewa,sanna"

fatima ta bishi a baya har zuwa katafaren falon

da aka sauke shi. Suna shiga falon ya soke

"hannu a aljihu ya kuma canja fuska,sannan ya"

juya mata baya. A gajiye kuma fuskarta a bace ta

nemi kujera ta zauna tana faman harara a

"duhu,tunda bai san tana yi ba. Suka kwashe fiye"

"da mintina goma a haka,sai da ya jiyo"

maganganun su safiyya a kusa da falon sannan

"ya juyo ya dube ta,duba irin wanda duk kwakwar"

mutum ba zai iya karanta abin da zuciyarsa ta

boye game da ita ba.Zuciya d kwanji

".16) Sai ta kara bata rai,shi kuma bai damu ba,"

ya tako har zuwa gabanta ya sunkuya

hannayensa dafe da ahnnun kujerar da ta ke

"zaune,yadda ta ke jin hucin numfashin sa"

"sosai,ya dubi tsakiyar idonta da kyau, sannan ya"

"fara magana kasa kasa. ""Duk wata halitta mai"

motsi a cikin gidan nan tana da kirki matuka! Ba

"kamar ke ba ba abin ya daure min kai sosai"". A"

"tunzure ta taure shi ta mike,ta dinga nun shi da"

"yatsa,amma ta kasa cewa komai,bakinta sai"

"motsin yake,ya rungume hannu kawai yana"

"kallonta,ko kadan fuskarsa ba ta sauya ba, abin"

da ma ya kara kular da ita ke nan. Da kyar ta

"hadiye ta sami abin cewa. ""Oh,abin da ya kawo"

"ka ke nan?"" Ya yi saurin gyara kai tare da"

"mokade lebe, ya ce. ""Eh,tunda da fuska biyu na"

"zo,idan muna cikin mutane nake masoyinki,a irin"

"wannan filin ban gane sunan da zan kira kaina ba,"

kuma ban san matsayin da ya kamata na baki

ba. Kuma ban san matsayin da ya kamata na

baki ba. Ga shi kuma bana son barin lokutana su

"tafi a banza,shi yasa nan fada miki abin da yake"

"hakkun.Ba laifi ba ne don ne ce,ba ki da kirki,ko"

"kina da shi?"" Zuciyar fatima ta dinga bugawa"

"saboda tsabar bakin ciki,ita ce dazu har da girin"

"gidinshin jin haushin ya gats sunanta,ashe rabin"

lamab ne cikin rashin mutumcinsa? Ta fara tafiya

da baya a hankali har ta riski wata kujerar ta

"zauna,sannan ta dube shi cikin yanayi barcin"

"rai,ta ce. ""Haka ne, rashin kirkina ya zarce inda"

"kake tsammatar masa,musamman a muhallin da"

na tabbatar yin kirkin da barinsa ba zai amfanar

"min komai ba, wato muhalli irin naka,me yasa zan"

"maka kirki? Fada min dalilin don Allah"". Tana"

"rufe baki ya amsa. ""Ni ma dan ba ni da dali """

Ta yi saurin dakatar da shi da hannu hade da

"masifa. ""Ka ga bana son rashin arziki don"

"Allah,kirkin idan a gidanku ake rabawa gobe ka yo"

"min guzirinsa"". Ya jima yana kallonta ba tare da"

fuskarsa ta bayyana bacin ran da ta ke ciki ba.

"Sannan ya murza hannu yana fuskantarta. ""Ki"

dinga yiwa harshenki linzami ya zama mai furta

alkhairi kinji? Ko don ki ci gaba da kasancewa

cikin shahararun mata a duniya masu sanyin hali

"da sanyi kyau,mace na da kima kwarai bai"

kamata ta dinga salwantar da ita wajen yin

hayaniya da ihu kamar na karnuka a gaban namiji

"ba, mata masu irin wannan halin ina musu kallon"

"ballagazaye wallahi "" Wannan karon zuciyarta"

"ba ta buga ba, mamakinta da tsaurin idon"

"Abdullahi kuma ya yi. Sauki, sai dai ya fara sa"

wa tana raina kanta Ashe tana da sauran

gibin da ba ta cike ba? Ta rasa da lafazin da zata

"kalubalance shi ko ta tsawatar masa, tunda nasa"

harshen ya fi nata kaifi Idan ta fadi daya sai

"ya fada mata goma,sai ta tsaya kawai tana"

"kallonsa tana huci,ya bude baki zai yi magana ta"

"dakatar da shi.A sanyaye ta ce. ""Ka ga ya isa kar"

"ka sa min ciwon kai,ban son dogon surutu"". Ya"

"fara murmushi har kumatunsa suka loba,bai"

tanka ba sai ya dauko magazine table ya dire a

"gabanta. Sannan ya zauna suna fuskartar juna,"

"amma idanunwansu na wani muhallin daban, ita"

"ta kurawa talabijin ido,shi kuma yana kallon tile"

din da ke shimfide a falon. Suka kwashe sama da

mintuna goma a haka sai da ta ga ya fara

"hararar agogo,sannan ta harari kayan kwalam din"

da aka shirya masa a tsakiya dakin. A kuntace ta

"ce masa. ""Idan fa ka tafi ba ka dan taba wani"

abu daga cikin kayan abincin nan da suka jera

"maka ba zaka bar zuciyarsu da zargi"". Shi ma ya"

"sha kamshi,sannan ya tanka. ""Haka ne,sai ki dan"

"bani wani abu na ci idan kina gudun zargin""."

Haba! A hanzarce ta juyo tana masa wani

"wulakanctaccen kallo,aka yi sa'a shi ma yana"

"dubanta,sai ya yi saurin dafe kai,ya ce. ""Ash!"""

Sannan ya kuma dubanta yana daga mata

"hannu,ya ce. ""Yi hakuri na manta sunan boyi"

"nake amsawa a wajenki,sai dai kar ki manta Alh"

"ya ce mu yi acting sosai,na tabbatar kuma zamu"

fa di assigment idan wani ya shigo ya tarar da ni

ina be bude a kwanuka ke kuma kina kallon

"talabinjin"""

"Like React Report May 14, 2015"

Amierah S-Man

Zuciya d kwanji

"17) Ba ta kop dube shi ba,ta zabga tsaki,ta je"

ta zuba masa gasassun 'yan shila wanda

kamshinsu ya gauraye falon. Ta kwashe

"lemunkan da suka zube wanda ya fara hucewa,ta"

mayar fridge ta dauko masu sanyi duk ta dire kan

"center table.A cunkunshe ta ce. ""Ga shi nan"".

Please Login or Register in order to submit comment