gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading DUK ƘARFIN IZZATA Yaƙin Sirrika BOOK 2 By Star Lady Chapter 4 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da muke tare da shi ba sai kuma Abba da Ammi tofa ba wan da a gidan nan zai che ga kalan voice ɗin Bgs kai a gidan nan ma akoi wayan da basu taɓa jin voice nashi ba bare ma su riƙe kalar ta" dakatawa da magana Khalid yana kallon Yusuf da ya sunkuyar da kai kasa kamar mai tunani

"Yusuf tunanin me kakeyi kuma? Ɗago kai Yusuf yayi tare da sakin murnushin mugunta yana kallon Khalid "lfy kake irin wan nan murmushin haka Yusuf? "Kasan me yaya Khalid wlh idan na tuna wata rana sister zata fito ɗauke da chikin Bgs sai abun ya rinƙa bani dariya zan ga wan nan lokachin kuma wani irin iskanci zai mana shin zai chi gaba da chewa kallo ɗaya yakewa wace da namiji ne ku kuma alokachin zai fara bamban tasu" "amma gaskiya Yusuf baka da dama wlh wai daman tunanin baby Bgs da sister kake ko to sai kayi kokari ka dage da yi musu sallar dare kana rokon Allah daya sanya soyayyan da tausayi da imani a zuchiyar Bgs dukka dan wani lokaci idan Bgs yayi wani abun ni tunani nake anya yana da imani kuwa "aa yaya Khalid dolefa wata rana Bgs zai hakura ya rungumi kadda ya kama matar sa domin dai kaji me Abba yace ko mutuwa yayi bai yadda Bgs ya saki hiyana ba to kaga zama da ita ya zama masa dole" "eh hakane Yusuf kana da gaskiya zama da ita ya zama masa dole amma yanzu ta yadda sister zata juri zama da shine abun dubawa domin wlh zata sha wahala ba kaɗan ba gashi baya magana baya kallon mutane idan ka masa magana ba zai am saba idan kayi tunanin bai ji bane ka mai mai ta ya daka maka tsawa kai duk wani abun da zakayi ka burge ɗan adam idan ka yiwa Bgs hukun taka zai yi shikam babu wani abu a duniya dake burge sa inaba Gun da bullet ba mutun ne bazaka taɓa gane hagun sa ba bare dama"

"Ai yaya Khalid kai baka ma sani bane wlh gaba ɗaya wajen aikin mu kama daga manya har kananun sojoji masu tasowa da zarar an ambaci sunan Bgs kowa jikin sa rawa yake Hmmm ai a gida ma yana muku sassauci sai kaje wajen aikin mu watara zaka sha mamaki dan akoi wata rana da wani soja yayi laifi yaya Aryan yace Bgs ne zai masa hukuncin wlh sojan nan yana jin anche Bgs ne zai hukunta tashi yasa bindiga ya harbi kansa ya mutu, kai bama wani ba ko ni da kai na idan misali yanzu nayi laifi a che Bgs ya hukun tani to ina mai tabbatar maka harbe kai na zanyi na mutu dan da Bgs yamin hukun chi gara na mutu na huta dan hukunchin sa ba kyau ba zai kashe ka ba amma zaka gwanmachi mutuwa idan ya fara hukun taka, kana gani gaba ɗaya faɗin London idan aka ambaci sunan shi sai kasar ta girgiza daga manya manya masu faɗa aji a kasar har kananan yan siyasa mutuwar tsoron sa suke koda super market kaje chikin wasa ka amince sunan sa nan take zakaji jama'a sun nitsu ba zaka rasa masu furta kallamar shahada a chikin su bama"
"To ai Yusuf wan nan dalilin ne yasa nache maka wani lokaci idan Bgs yayi wani abun sai naga kamar bashi da imani mu dai yanzu sai dai mu dage mu taya sister da addu'a" dariya Yusuf yayi kafin yace "ba dole na taya sister da addu'a ba domin idan Allah ya dai dai ta komai ɗan da zasu haifa ba karamin kyau zai yiba madara da madara ne suka haɗu kyau iya kyau baa magana shiyasa na yanke hukunci first born na Bgs nawane awaje na zai zauna, amma Allah yasa ya ɗauki blue eyes na sister" tsaki Khalid yaja san nan yace "wlh Yusuf kai dai baka da aiki wato har ka tsara yadda ɗan su zai kasan che ko to in ban da kai ma da wani zanche Ai da Bgs da sister kaman nin fuskar su ɗaya basu da wani banbanci idan ba na kalar ido ba" Yusuf zai yi magana kenan idon sa ya sauka a kan Abba dake tsaye a bakin kofar Betroom nashi ya harɗe hannu a kirji ya zuba musu ido yana kallon su

chikin sauri Yusuf ya miƙe ya kama hanyar fita yana faɗin "my baby na kirana miƙewa Khalid ma yayi batare da ya lura da Abba ba ya bi bayan Yusuf yana faɗin "to ai nima sis love ɗina na jirana binsu da ido Abba yayi har suka fice daga Palon sauke nauyayyar ajiyar zuchiya yayi kafin ya fara magana

"Na tabka babban kuskure arayuwata nayi da na sanin haɗa Bgs da hiyana ido na ya rufe bani da burin da ya wuche in samo wa ɗana mace ta gari batare da na yi la'akari da halin da ita yarinyar zata shigaba, gaskiya da baa ɗaura Auren nan ba da ba abun da zai hanani in aura wa Ahmad ita ni da kaina na jefa rayuwar marainiyar Allah a chikin kunchi da damuwa innalillahi wa inna ilaihir rajiun Ya Allah kana gani ban yi hakan da nufin chutar da itaba ban yi hakan da nufin kun tata ma rayuwar taba,nayi hakan ne da kyakkyawar niya da kuma yakinin wata rana zai sauya ban san chewa abun nashi ya kai har haka ba daga chewa Bgs ne zai maka hukunci kawai sai ka harɓi kanka da bindiga to inaga yarinyar da aka haɗasu dole kuma anya bazan raba auren nan ba kuwa kai dole nayi magana da Aisha tun abu bai yi nisa ba musan abun yi, ya Allah ka kawo min agaji Allah ka kawowa hiyana mafita yana kai karshen maganar ya juya ya koma chikin betroom na shi


Kwanche yake a saman katafaren gadon sa yana latsa waya kiran Aunty farida che ta shigo wayar sai da wayar ta kusa tsin kewa san nan yayi picking tare da manna wayar a kunnen sa, daga ɗayan ɓangaren Aunty farida tace "Hello Prince Ykk Y gida? Shiru ya ɗan yi na yan sakanni kamar ba zai yi magana ba "lfy Ykk?ya faɗa a takaice yayi maganar yana kawar da fiska gefe kamar yana gaban ta "Ina lfy dan Allah prince magana nake son yi da hiyana kuma kaga bata da waya pls ka kai mata wayar ka muyi magana" ta karisa maganar chike da fargaban abun da zai biyo baya, Aunty farida na gama magana batare da ya bata amsa ba ya katse kiran tare da yin block na number Aunty farida yayi wurgi da wayar gefe guda, wani dogon tsaki yaja tare da miƙewa ya fice daga ɗakin ya nufi part na Aryan

Kwanche saman sofa mai zaman mutun 3 ya isko Aryan ya ɗora hannun sa ɗaya a saman fuskar sa dai dai sai tin ido ɗayan hannun kuma ya ɗora a kan chikin sa yayi shiru, shiru Bgs ya tsaya a bakin kofa yana kallon yadda Aryan ya rame sosai yayi baki ya sauya gaba ɗaya ya fita hayyachin sa kamar ba shi ba nan take wani mugun tausayin Aryan ya dira masa a rai

a hankali ya zuro kafafun sa ya shigo chikin palon saman sofa mai zaman mutun 1 ya zauna kasa kasa ya fara kiran sunan Aryan "Aryan Aryan" ɗauke hannun sa Aryan yayi daga kan fiskar sa slowly ya waro Ash eyes nashi da suka sauya yanzu sun kara girma saboda raman da yayi sunyi jaa sosai gaba ɗaya jijiyoyin idon nasa a tsai tsaye suke kallo ɗaya yayiwa Bgs ya kawar da kan sa gefe guda tare da yun kurawa ya tashi zaune "Aryan ka tashi ka shirya dan ina ga yau zamu wuche mu koma bakin aiki ba zan iya zaman Naija ba" chikin kasalalliyar murya Aryan ya fara magana "Bgs ka tafi kawai ni ba zan je ko ina ba tare da matata ba idan kaga na bar Naija to tare da ita ne" "what!!? Aryan kasan me kake faɗe kuwa mace fa kace ni ai na ɗauka duk damuwar da kake chiki saboda rasuwar Aiman ne" "No Bgs zafi biyu ne a lokacin guda suka haɗun min ina rokon Allah daya bani ikon chin wan nan jaraba da ya jarab cheni da shi, wlh zuchiya ta ta fara karaya kwata kwata ji nake duniya ta ishe ni na rasa ina zan saka kaina" "Amin amma yanzu dai katashi kaje ka shirya mu tafi, ka dai na yawan tunani addu'a Aiman ke buƙa ba wani abu ba"
"Bgs nafa faɗa maka babu in da zanje ba tare da matata ba "wai ni kam Aryan kana da lfy kuwa kasan me kake chewa kuwa Aikin naka fa "bgs lfy na kalau aiki kuma idan ba zaka iya ɗaga min kafa har Allah yasa naga matata ba to zan rubuta maka later barin aikin sai kasa hannu domin idan babu my d a rayuwata rayuwar tawa bata da sauran wani amfani, shiru Bgs yayi ya zubawa Aryan green eyes nashi yana kallon sa from head to toe ya san dai iya gaskiya Aryan ke faɗa domin duk wani maganar da zasu yi da Aryan tofa basa saka wasa a chikin ta "Aryan mace kuma kai ina ba gaskiya kunne na ke faɗamin ba "no bgs gaskiya kunnen ka ke faɗama ba karya bane ina son matata ina kaunar ta fiye da rai na tun ranar da na fara ganin ta a duniya na kamu da matsanancin Son ta idan har na bika London yanzu ba tare da ita ba tofa ba zan kai labari ba dan haka ka kyaleni a nan kawai har ta Allah ta kasan che idan Allah ya ƙaddara zan ganta tofa zaka iya dawowa ka sameni idan kuma babu rabon na ganta tofa zaka dawo kasamu gawata yana kai karshen maganar ya miƙe da kyar ya shiga betroom nashi, wani irin bakin ciki ne ya tokarewa bgs makoshi jiyayi ya kara tsanar mace a rayuwar sa yanzu yasake tabbatar wa kan shi mace halittace mai rauni kuma duk lokacin da ta raɓeka kai ma zaka zama mai rauni dobi duk jarumtar Aryan da izza da kuɗi da mulkin da yake da shi jibi yadda ya dawo saboda mace, macen ma yar karamar yarinya no ba zan taɓa bari hakan ta faru da niba wlh mikewa yayi jiki ba kwari yanufi hanyar fita har yakai bakin kofar fita sai kuma ya juyo dan ba zai iya barin Aryan a halin da yake chiki ba bin Aryan yayi chikin betroom ɗin

Zaune a gefen gadon ya isko Aryan ya dafe kansa da hannu ɗaya sai wani huci yake yana murza sai tin zuchiyar sa da hannu ɗaya, karisowa in da yake Bgs yayi gefen sa ya zauna yasa hannu ya chire hannun Aryan da ya dafe kan sa dashi chike da tausayin ɗan uwan nashi ya fara magana "Aryan pls ka daina damuwa kasan dai ba zan iya jure ganin ka a wan nan yana yin bako zan baka hutu har tsawon lokaci da zaka gane matar taka san nan ai na ta ɓata? Chiki rau'nanniyar murya Aryan yace "a Maiduguri ta ɓata" "ok to nama alkawarin in dai tana chikin Maiduguri bata fitaba to In Sha Allah bazata kara kwana biyu bata dawo gareka ba, kayi waya headquarter kace ni na bada izinin abaka sojoji mota 20 naso na taya ka neman ta da kaina amma ba lokachin all the best my blood amma dai ka dai na shiga damuwa dan in kana chikin damuwa nima dole na shiga damuwa kuma ba zan samu kwanchiyar hankali ba" juyowa Aryan yayi ya rungumi Bgs yana faɗin "nagode da ka fahimci ni nagode ɗan uwana" hannu Bgs yasa yana ɗan bubbuga bayan Aryan awan nan yanayin Fahad ya shigo ya same su

Zama yayi a gefen Bgs yana kwaɓe fuska sakin Bgs Aryan yayi yana faɗin "Fahad lfy na ganka haka, sai lokachin Bgs ya dawo da kallon sa kan Fahad ɗin "yaya Aryan pls wani magani ya kamata na bawa Amrat bata da lfy ne? Dogon tsaki Bgs yaja tare da miƙewa ya fice daga ɗakin

"me yake damun ta Fahad? Shiru Fahad yayi ya sunkuyar da kai dan bai son ya faɗawa yaya Aryan amrat ta fara period "to Fahad lfy ko dai chiwon nata baa faɗa ne? "Aa yaya Aryan kawai irin chiwon sun nan ne na matan kuma chikin ta yana chiwo sosai tun safe takemin kuka" duk da tashin hankali da Aryan ke chiki hakan bai hana shi yin murmushi ba dan Fahad ya bashi dariya eyee su Fahad ma an girma har da mata yanzu kam "tashi gaje ka ɗauko min box bari na baka maganin da sauri Fahad ya miƙe ya nufi wajen da ake ajiye wa ya ɗauko ya kawowa yaya Aryan magani kala uku Aryan ya bashi tare da faɗa masa yadda zai bata chikin sauri Fahad ya ansa tare da faɗin ngd kana ya fice daga ɗakin binsa da kallo Aryan yayi har ya fice san nan ya karisa hayewa kan gadon ya kwan ta ya lumshe ido

KHALID

" Yaya Khalid dan Allah ka barni naje wajen Aunty hiyana mana" chewar Zahra dake kwanche saman sofa ta tada kai da chinyar Khalid "eyeee Auta wato yanzu ba kya tsoron yaya prince ko!? "aa yaya Khalid ina tsoron sa sosaima amma dai gaskiya zanje wajen Aunty hiyana dan wlh ina kewar ta sosai" "to yau she kika fara kiran Hiyana da Aunty kuma?Yayi maganar yana tura hannun sa chikin rigar ta, ɗan buge hannun sa Zahra tayi chikin shogoɓa tace "Kai yaya Khalid jiyama da ka shamin wlh zafi suke min ni ka kyaleni" sunkuyo da kansa yayi dai dai sai tin face nata chike da so da kauna yace "gaskiya ni da kayana ba zan bari ba bazan iya dai na sha da kuma matse suba" rufe ido Zahra tayi ta turo baki tana faɗin "Allah to sai na koma ɗakin Ammi na" yar dariya yayi kafin yace "ai da yafi domin a part ɗin Ammi ma zai fi daɗi abun kinga jiya dan ina sha kika rinƙa min kuka wai zafi to idan a part ɗin Ammi ne ko zan shanye dukka ba zakiyi kuka ba dan kina tsoron wani yaji kuma kin san ni kam ba ruwana ko agabab Ammi zan.. bai kai ga karisa maganar ba Zahra ta rufe masa baki da hannun ta tana faɗin "ai nasan zaka iya to ni babu in da ma zanje yanzu dai pls yaya Khalid ka barni mana naje na ga Aunty hiyana" "to naji idan na barki kikaje kika dubo hiyana in kin dawo me zaki bani? Da sauri Zahra tace Allah ka barni zaje duk abun da kake so zan baka" "kin tabbatar? "Eh yaya Khalid na tabbatar "ok to tashi kije amma karki daɗe minti 30 na baki kawai "yauwa yaya Khalid nagode" chikin zumuɗi ta muƙe

fisgo ta yayi ta dawo ta faɗa saman kirjinsa a tare suka furta ash zafi "yaya Khalid me kuma na maka ka barni na tafi mana pls" "ba zaki tafi baki min kiss ba" turo baki Zahra tayi tana faɗin "to ka rufe ido ka" "aa ban yarda ba gaskiya haka jiya ki kamin ni dai ido na a buɗe zaki min in ba haka ba afasa zuwa wajen Hiyana nan" dukan wasa ta kai masa a kirji bam tana faɗin "Allah yaya Khalid kai ko "amin hot kiss ko kuma afasa zuwa wajen Hiyana ɗago kanta tayi a hankali ta haɗe fuskokin su tare da runtse idonta a hankali ta kamo lips nashi na kasa tafara tsotsa kamar jira yake daman ya tura hannun sa chikin rigar ta ya fara wasa da breast nata sai wani nishi yake Zahra data ga abun nashi ya fara yawa chikin dabara ta shammache sa ta kwache kanta da gudu ta miƙe ta fice daga Palon kwafa yayi yana faɗin "wlh zan kamakine yau bazan ɗaga miki kafaba, ita dai Zahra bata bi ta kansa ba tayi waje abun ta kai tsaye part ɗin Bgs ta nufa gaban ta na dukan uku uku

NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)

💖The Talent Troupe Writer's 💖


*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*


Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

Book 2

*Episode 6*


Saɗab saɗab Zahra take lallabawa kamar ɓarauniya ta shiga part ɗin Bgs sai waige waige take tana tafiya tana juyowa ta kalli bayan ta karaf sai ji tayi tayi karo da mutun chikin tsoro da tashin hankali ta ɗago kai ganin Aunty amarya ne tsaye a gaban ya sa ta sauke nauyayyar Ajiyar zuchiya tare da faɗin "ina wuni Aunty amarya "lfy lau Auta me ki ka zo yi a nan kuma kika bar ɗakin mijin ki? "Wajen Aunty hiyana nazo" jin Zahra ta ambaci sunan hiyana yasa Aunty amarya ta ɗaure fuska cheke da ɓachin rai tasa hannu tawa Zahra nuni da ɗakin Bgs dan mugunta tache hiyana na chikin nan" "to" kawai Zahra tace san nan ta wuche ta haye saman stair case ɗin ta nufi ɗakin yaya prince ɗin

Aunty Amarya kuma sai murmushin mugunta take ta nufi hanyar fita daga palon

A hankali Zahra ta tura kofar kamar wadda bata da gaskiya ta shiga yana tsaye gaban mirrow jikin sa sanye da kayan sojoji yana gyara lallausan kuma bakin gashin kan sa, jin anshigo masa ɗaki ne yasa ya ɗago green eyes nashi ta chikin mirrow yana kallon Zahra dake ta yan waige waige alamar bata ganshiba zuba mata ido yayi sosai
ya kalleta san nan ya kalli kanshi ba shakka Auta tana kama dani sosai, why nake kaunar Auta sosai har hakane? Yayi wa kansa yambayar da ba shi da amsar ta "zo nan ke!!"ya faɗa tare da juyowa yana kallon ta da kyau, chikin tsoro da tashin hankali Zahra ta karisa gaban sa ta sugun na kasa murya na rawa tace "ina wuni yaya prince" "me ya shigo dake part nan!!? banche karna kara ganin ku a nan ba!!? "Kayi hakuri wajen Aunty hiyana nazo, jin an ambaci sunan hiyana yasa ya ɗaure fuska sosai chikin tsawa yace "tashi ki fita ko nayi ball dake!!! Da gudu Zahra ta miƙe ta fito a bakin kofar ɗakin nasa ta waje ta tsaya tana tunanin ina ne ɗakin Hiyana dan ni dai gaskiya ba zan tafi ba har sai na ga hiyana ta

Tayi nisa chikin tunanin da take ne sai taji shesshekar kuka a ɗakin dake kusa da na Bgs kuma muryan Hiyana che ke wan nan kukan, chikin sauri ta tura kofar ɗakin ta shiga turus ta tsaya ganin hiyana a duke tali nill down ta daga hannu sama tana kuka ga zulaihat tsaye a kanta rike da bulala chike da bachin rai da fushi chikin tsawa Zahra tace "ke zulaihat me hakan!! Chike da izza zulaihat tace "ina ruwanki ko kimin shiru ki fita a ɗakin nan ko kuma in haɗa dake, karisowa chikin ɗakin Zahra tayi dai dai gaban hiyana taje tasa hannu ta ɗago ta tare da mai da ta kan gadon chikin fushi ta juyo ta zabgawa zulaihat wani wawan mari ta kwasa a guje tayi waje, a guje zulaihat ta bi bayan ta a dai dai tsakiyar palon kasa ta damko gashin Zahra ta baya da karfi ta ja ta baya wani ihu azaba Zahra ta saki hankaɗata kasa zulaihat tayi ta faɗi ta buge goshin ta a kasa wani razanannen kara ta saki gadan gadan zulaihat ta nufeta a zafafa ta ɗaga hannu zata kaiwa mata naushi a chiki, chak daji a damki hannun nata da karfi kafin ta ɗago taga wanene ya kwashe kafafunta ta faɗi kasa wani wawan mari ya wanke mata fuskar ta dashi wadda yasa gaba ɗaya ta daina gani, baiyi wata wata ba ya sa kasa yayi ball da ita ta tafi luuuu saboda tsantsin wajen ta bugu da jikin stair case wani ihun azaba ta saki lokachin guda kuma ta ɗauke diff kamar an ɗauke wutan nepa

Dawo da kallon sa kan Zahra yayi tare da miƙa mata hannu alamar ta kama hannun sa ta miƙe chike da tsoro da mamaki Zahra ta kama hannun sa jawota yayi ta faɗa kan faffadar kirjinsa da ɗan tsawa yace "ba nache ki bar part din nan ba me ya hana ki tafiya kuma wacece wanchan? Chikin shesshekar kuka Zahra tace "kayi hakuri yaya prince wlh ina son ganin Aunty hiyana che shiyasa amma yanzu zan tafi" " wacece wan chan? "Yar uwan Aunty amarya che" "me ya kawota part nan har zata bugeki? Yayi Maganar tare da raba ta da jikin sa nan dai Zahra ta bashi labari yadda ta shigo ta samu abun da zulaihat kewa Hiyana, tsaki yaja tare da juyawa ya koma betroom na shi

Haurawa sama Zahra ma tayi ta koma ɗakin Hiyana suka bar zulaihat sume awajen

In da ta bar hiyana a wajen ta dawo ta same ta sai kuka take gefenta ta zauna chike da bachin rai tafara magana "yanzu Aunty Hiyana yar zulaihat ɗin nan zaki bari ta bugeki dame ta fiki eh? To wlh tun wuri idan zaki tashi ki dai na zama shiru shiru ki kwatar wa kan ki yanchi gwara ki tashi, wlh ki ajiye ustazan chinkin nan yanzu lokachin fafata yaki ne to bari kiji in faɗa miki ma zulaihat tazo gidan nan ne domin ta samu soyayyar yaya prince shiyasa na tsaneta ranan na shiga part ɗin Aunty amarya na jisu suna shawan yadda zasu bullowa yaya prince ita da Aunty amarya to kinga yanzu tashi zakiyi ki ɗaura ɗamarar yaki ki kwachi mijinki" chikin shesshekar kuka hiyana ta fara magana "Aunty Zahra ai Aunty amarya che tazo tache komai zulaihat ta sani in rin ka yi idan ban yiba sai ta kusan kashe ni shiyasa kuma Ni fa yaya prince ba sona yake ba ya tsane ni bai son gani na dan haka ba ruwana da shi nima, kuma ba wani yaki da zanyi a kansa" Zahra zatayi magana sukaji an buga kofar ɗakin

Da sauri Zahra ta miƙe ta nufi kofar tana faɗin "Allah yasa ba yaya prince bane dan yace na bar part din nan juyowa hiyana tayi ta zubawa kofar ɗakin blue eyes nata, chike da tsoro Zahra ta buɗe kofar ɗakin ganin yaya Khalid ne yasa ta sauke nauyayyar ajiyar zuchiya "my wife zo ki wuche kije ki ɗauki duk abun da kike bukata nan da 10mins jet ɗin yaya prince zai tashi zamu koma London ɗan leko da kansa ɗakin yayi chike da kulawa yache "hiyana tashi kema ki shirya yanzun nan muna palon Abba muna jiran ku yana gama faɗin hakan ya juya ya nufi hanyar fita

Juyowa Zahra tayi ta kallin Hiyana chike da farinchiki tace "to Aunty Hiyana yaki da su zulaihat ya kare kiyi sauri ki shirya "Aunty Zahra taya zan tafi ba tare dasu diyana ba? ina diyana na take? wani hali take chiki yanzu? shin tana raye ne? ko ta mutu? "Aunty Hiyana kiyi hakuri kisani Abba ba zai taɓa barin rayuwar diyana ya salwanta a ban za ba zasu nemota In Sha Allah yanzu dai ki tashi ki ɗauki abun da kike so kiyi sauri dan kinsan halin yaya prince baya son jira "to Aunty Zahra, da sauri Zahra ta bar wajen ta sauko kasa ta fice daga palon ta nufi part ɗin

Please Login or Register in order to submit comment